Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

“ADALILINTA”
ADALILINTA





BY AMINA BAYARO💜❤💜







WhatsApp number 09162226240



*FREE BOOK*



Barkan ku da wannan lokacin, ma' abota karatul novels. ina muku fairi alkhairi. Kuma da fatan zaku biyoni a sannu domin karatun littafin ADALILINTA.....



* Page 1*

Bismilla



`ADALILINTA`

baban gidane sosai, yana d'aya daga cikin gerin manyan gidajan G. R. A, d’in area. kana ganin gidan tun daga qofar gidan zaka shaida dukiya tai kuka a gidan, sabida tsaruwa gidan da kuma kayan alatin da suke qofar gidan.



tom bara mushiga muga waca wainar ake toyawa.



Duk family din gidan sun hallara a katafaran babban falan gidan, Wandda gayawa masu karatu littafi tsaruwar falon ma, b'ata bakine.



ALHAJI ABUBAR DUKIYA (dady ) ne zaune shida da matan shi biyu, da mahaifiyarsa da yaranshi. HAJIYA MARYAM itace uwar gida, wanda iyalan gidan suke kiranta da AMMI, sai HAJIYA HALIMA amarya wanda iyalan gidan suke kiranta da MOMY.



sai mahifiyar alhaji abubakar wato HAJIYA FATIMA, wanda iyalan gidan suke kiranta da HAJIYA KAKA. sai kuma ragowar yaran gidan guda tara(9).



MUHAMMAD (MURSHKUR) umar(faruq) Aliyu(haidar) sakina(ilham), sai abdullahi(amir) wato d'an auta, sai kuma FATIMA (ZAHRAH) wanda ta kasance kamar 'ya a gidan sakamakwan tin tana zanin goyo hajiya maryam wato ammi take rainon tah,



yaran hajiya maryam kenan wanda ta kasance uwar gida a wajan alhaji abubakar. ABDUL MAJID,(abdul) rukkayya ,rumaisa'u duk yaran hajiya halima ne wato amarya alhaji abubakar

Wannan kenan.



Dady muskuta wa yayi tare da gyaran murya cikin nutsuwa da dattaku. Bud'e taron dady yayi da addu'a sannan ya fara magana kamar haka.



Abidda yasa na taraku anan shine inaso ku nutsu kubani hankalin ku dukan ku sabida inaso muyi muhimmiyar magana, dady Ya qarasa maganar yana bin kowannan su da ido.



Sai da yayi shiru na wasu daqiqo kafin ya cigaba da cewa, ba komai ne yasa na taraku anan ba illa abu d'aya, da nake so na sanar daku. sai da dady ya qarayin shuru na wasu daqiqu sanan ya cigaba da magana.



Hajiya, maryam, halima, da kuma kai mashkhur , sai kuma ke mamana, dady ya qarasa maganar yana mai da kallansa wajan da zahra take zaune a kusa da sakina wato ilham.



Dauke idanunsa yayi daka kan zahra sanna yaciga ba da cewa, da kuma sauran yaran gidan nan gaba d'aya. Inaso ku shaida NI abubakar zan had'a AURAN ZAHRA da MUHAMMAD wato MASHKHUR.



Ai duk falon ba wanda gaban sa bai wad'i da jin maganar dady bah, in ka dauke hajiya kaka da amir auta da kuma dady mai maganar.



Ai mashkur ji yayi kan sa yayi mugun sarawa lokaci guda yaji duniya ta tsaya mai cak, tinanin ya farayi anya dady yasan maganar da yake fad'a? anya ma naji dai dai? inaga dai banji dadi ba, ko kuma dady su6utar baki yayi abdul yake so yace.



Shi kuwa abdul majid ai tuni numfashinsa ya tsaya cak, wani gumi ya fara keto mai ya fara ganin dishi-dishi da wani irin mugun jiri. Dan shi gani yake kamar rayuwar sa tazo qarshe.



Zahra kuwa mutuwar zaune tai, dan maganar dady tazo mata a on expected , gani take anya dady yasan abinda yake fad'a kuwa? anya dady ba zaulayarsu yake ba kuwa?.

ita dai ammi ta rasa mai zatai baqin ciki zatai ko farin ciki, dan abin ya bata mamaki sosaii.
ko mai dady ya hango yayi wannan had'i?ohoo. Ammi tana sauqe idanunta akan hajiya kaka ta,tabbatar da itace ta hada komai.
saka makwan ganin fuskar hajiya kaka bawani mamaki.



itama momy bataji dady zancan ba, dan bata son kwata-kwata zahra ta auri mai gata da ilima da galihu kamar mashkhur, dan so take ta auri talaka rayuwar ta qare a wahala.



suma ragowar yaran gidan maganar mahaifin nasu ta dake su sosai, kuma ba qaramin mamaki lamarin ya basu ba. musanman ilham da take tausayawa 'yar uwarta zahra wanda duk duniya take ganin bata da kamarta.



maganar mashkur ce ta dawo da kowa daga tunanin da yatafi. inda yake magana cikin rawar murya.
da!! da!! dady am!! am!! mai kace dady kamar banji dai-dai bah mashkhur ya qarasa maganar a gigice.



Abinda kunnan ka ya jiyema hakane, in kuma so kake na mai-mai tama sai na sake mai-mai tawa ka sake ji. so nake na had'a ka aure kai da mamana, kuma UMARNI nake baku kai da mamana ba shawaraba. cewar dady.



momy ce ta katse dady cikin firgici da tashin hankali, ta hanyar cewa haba dady abdul ya za kace haka? karfa ka manta mashkhur da zahra!!! dady da dakatar da momy yayi ta hanyar d'aga mata hannu da cewa................



Typing........



''ADALILINTA''💜❤💜



BY AMINA BAYERO💜❤💜



*free book*💜❤💜



*ina godiya da masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. ina muku fatan Alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜❤



*Dan Allah in kun karanta ku dinga comment....... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa...💜❤💜



Ga masu buqatar a sasu a group d’in littafin ADALILINTA saisuyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. free book ne bana kud’i ba, kuma new book ne. In kun karanta ku tura wasu groups d’in pls.

Typing......



ADALILINTA💜❤💜



AMINA BAYARO💜❤💜



*Page*2

Ta hanya d'aga mata hannu tara da cewa.......



Bana san jin komai da ka bakin kowa, kuma na riga da na yanke hukunci, kuma bazan canza magana ba, dole kuma abi tsarina shine kwanciyar hankalin kowa a cikin gidan nan. Dady yana gama fad'in hakan ya fuce ya bar d'akin.



Dady yana futa shima mashkhur ya tashi fuuuuuu a fusace ya fuce. yana fita ya nufi part dinsu,ko kallan gabansa bayayi sabida tsabar tashin hankalin da yake ciki.



Itama hajiya kaka tafiyarta tai part dinta cike da farin ciki. Dan tabbas tasan abubakar d'an ta ya haifu. Tindda har ya aikata abidda ta umarce shi da shi, duk da hatsarin da yake tattara da hakan.



Itama ammi jiki ba kwari ta wuce part dinta. Momy mah a fusace ta wuce nata part din, cikin tunanin abinyi. Itama zahra d'akin su ta nufa aguje tana kuka, ilham tana biye da ita a baya, dan ta rasa ta inda zata fara bawa zahra baki.



D'aya bayan d'aya yaran gidan suka fara watsewa, jiki a sanyaye sabida suma maganar ta basu mamaki sosai. Kowa sai jimami yake a cikin zuciyarsa, dan duk cikin su ba wanda ya iya cewa uuufan.



Falo ya raqe daga abdul majid sai amir auta. Shima amir tashi yayi ya nufi wajan auntynsa zahra. Hankalin amir ya tashi sakamakwan gananin aunty zahransa tana kuka.



Shi kuwa abudul majid bawan ALLAH mutuwar zaune yayi, dan ya kasa wani kwakwaran motsi, dan halin yanzu ji yake bashi da sauran farin ciki a rayuwa. Sabida an raba shi da MOSOYIYARSA zahra.



da kyar ya tashi yana tafiya yana layi ga jiri da yake qoqarin kifar da shi. A daddafe ya koma part din nasu cikin matsanancin tashin hankali. Da kyar ya iya murd'a handil d'in qofar dakin nasa, yana bud'awa ya shige a gigice...



MASHKUR....

Yana zuwa qofar dakinsa ya murd'a handel ya shige. Yana shiga ya kulle d'akin da key, ya fara safa da marwa cikin tashin hankali. Ji yake duniyar ta tsaya mai cak.



qarasawa yayi gaban wani glass table da yake gefan gado a d'akin. A zuciya ya dun qule hannunsa ya kaiwa gilas table d'in duka, ji kake tassss. Ai kuwa gliss din ya fashe kwatsa-kwata.



Kafin kace me tini jini ya fara malala a qasan tiles, d'in dakin. Dan ba qaramin ciwo yajiwa hannun nasaba. amma shi kwata-kwata bayajin zafin ciwan, sabid baqin cikin da yake ciki.
A dai-dai lokacin wayar sa da take kan bed ta fara ruri.

Da kyar mashkhur ya iya d'aga kyawawan idanun sa ya dora akan wayar. Ai kuwa sunan ZEE ya hango b'aro-b'aro a kan screen d'in wayar.



Kau da kansa mashkur yayi daga duban wayar tare da jan wani tsoki .
Ya mai da dubansa kan hannun nasa da yake ta tsiyayar jini.



Da kyar ya d'aga qafarsa ya nufi hanyar toilet jiki ba kwari. yana zuwa ya sakarwa haninsa ruwa, ai sai a lokacin mashkhur yaji wani gigitachan zafi. Runtse idanuwansa yayi tare da futar da wani huci mai zafi daga bakinsa.



Sai da yayi wajan minti 2 sanan ya kashe ruwan ya dawo kan bed. Amma stil har yanzu jinin bai tsaya ba, tashi yayi cikin azabar ciwan, ya fara tafiya.



Wata qaramar durowa ya bud'e ya zaro bandeji, sannan ya dawo kan bed. A hankula ya fara nad'e hannun nasa. Yana cikin nad'e hannin nasa yaji wayarsa ta sake ruri.



Ko kallan wayar mashkhur be yi ba ya cigaba da abinda yakeyi. Yana gamawa ya nufi kwaba dan canza kaya. Wata blue din jallabiya ya d'auko yasaka.



Yana zirawa ya nufi kan table ya d'auki key d'in mota, sanan ya wuce kan gado dan d'aukar wayar sa da har yanzu bata dena ringing ba.



Still haryanzu zee ce take kira. Ko ta kanta bai biba ya dauki wayar ya zura a aljihu ya nufi hanyar fita daga bedroom d'in. Yana fita yaci karo da qaninsa faruq



Kallansa yayi a sanyaye tare da cewa yauwa faruq shiga bedroom d'ina ka gyaramin Tom yaya amma naga jini a hannunka ciwo kaji? Ehh ciho naji gilas table ne ya fad'omin.............



Typing........



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYARO💜❤💜



*Free book*💜❤💜



*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yimuku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment............ pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.........💜❤💜

Ga masu buqatar a sasu a group d’in littafin ADALILINTA sai suyimin magana ta wannan number 091622262340 WhtsApp kawai bandda kira. Free book ne bana kud’i ba, kuma new book ne. In kun karanta ku tura wasu groups d’in pls...



Typing.........



ADALILINTA💜❤💜



AMINA BAYARO💜❤💜



*page3*

Ehh ciwo nagi glass table ne fad'omin............



yanzuma hospital zani amma banaso kowa ya sani, karka fad'awa kowa. Ok yaya ba damuwa a dawo lafiya. Daga haka mashkhur bai sake cewa komai ba ya Juyawa ya nufi hanyar fita daga part d'in.



Yan fita ya nufi parking space d'in gidan. Motocine kala-kala kuma rantsatu a jere a parking space d'in. Motocin sunfi kala ashirin, wata baqar mota ya nufa mai rai da nunfashi, Ya zura key ya kunna.



Yayiwa mai gadi hroon , ai kuwa mai gadi ya wangale get. yana bud'ewa mashkhur ya fuce da gudu. Bai nufi ko ina ba sai asibiti. Yana tafe yana tinanin abinda ya faru.



Ji yakeyi kamar a mafarki, wai shi zai AURI zahra. Wani dogwan tsaki yaja tare da furta BANZAR yarinya kawai, Wai yarinyar da na fi TSANA a rayuwata ita zan aura, impossible, wlh.



Sanbatu yake kamar wani zautacce harya qarasa asibitin. Yana isa ya kashe motar tare da cewa ADALILINTA komai ya kwab'emin wlh zan iya KASHETA in aka bani auranta. Yana gama fad'in hakan ya bud'e murfin motar ya shige asibitin...........



ZAHRA....

Tana qarasawa bedroom ta fad'a kan gado tare da sakin kuka maicin rai. Itam ilham d'in rab'awa tai gefan gado ta zauna cike da jin tausayin 'yar uwar tata. wayyo Nashiga uku iliham na mutu na lalace.



Abinda zahra ta iya fad'a kenan cikin muryar kuka. ilham ajiyar zuciya tai murya a dashe tace zahra kiyi haquri, tana fad'ar hakan wasu hawaye suka gangaro mata.



Harga ALLAH tana tausayawa zahra sabida ba tai dacan abokin zama ba. sabida tasan MUGUNTAR yayan nata. Nunfasawa tai tare da cewa sister kiyi haquri nasan baki dacan miji ba, sabida yaya mashkhur MUGUNE.



A dai-dai lokacin amir ya murd'a handel d'in qofar ya shigo. yana shugowa ya nufi inda zahra take kwance tana kuka. Zama yayi a gefan kanta yana share mata hawayan fuskarta da tafin hannunsa.



Tare da cewa aunty na ki dena kuka kinji. Amma zahra ina kamarma tunzirata ilham take, ta sake saki wani saban kuka mai cin rai. Aunty na kidena kuka nima zakisa nai kuka. Amma ina zahra tayi nisa.



Juyawa amir yayi, ya kalli ilham yace aunty ilham kiyiwa auntyna magana ta dena kuka. Itama ilham zubawa yaran ido tai, taqi tace komai. Sabida batasan abinda zatace mai ba.



A ganin ilham ko tayiwa amir bayani ba fahimta zai yiba, tinda yaran ko shekara shidda bai kai ba. Amir kuwa da yaga duk sunqi yimai magana ya tashi ya nufi hanyar fita.



Tare da cewa bari naje na gayawa ammina tazo ta bawa auntyna hakuri, ya fad'a fuska shab'e-shab'e da hawaye. Yana futa zahra ta sake rushewa da wani saban kukan.



Ilham sake matsawa tai dab da zahra tare da dafata, tana cewa zahra dan ALLAH kidena kukan nan, kinsan bana san damuwarki tana tayarmin da hankali. Ta qarasa maganar tana zubar da hawaye.



Haba ilham ba dole nayi kuka ba, ni kuwa wana laifi nayiwa dady da zai yanke min mummunan hukuncin nan? Ya had'ani aure da azzalimi nan haba ilham kiduba lamarin nan.



Zahra ta qarasa fad'ar haka cikin shasheqar kuka. Ilham dai tagumi ta rafka dan batasan yadda zata shawo kan zahra ba. Ilham wai dududu ma shekara ta nawa har da dady yake qoqarin yimin aure.



Shekarata fah shabiyar (15 years) nida ko secondary school ban gama ba, rukkayya ce fah babar mace a gidan nan ko ita ba a aurar ba sai ni.



Ilham dai shiru tai dan tasan tabbas yau ran zahra yayi matuqar baci, Dan zahra bata da fad'a kuma ga kawaici da haquri. Da kyar dai ilham ta iya cewa hakane zahra amma kiyi haquri muje muyi sallah, Lokacin sallah yayi.

Alokacin ake ta kiraye-kirayan sallar la'asar dan haka zahra ba musu ta miqe jiki a sanyaye ta shiga toilet dan yin al-walah, dan ita zahra bata wasa da lokacin sallah.



Tana futowa daga toilet d'in itama ilham ta shiga ta d’aura al-walah. zahra kuwa bayan ta idar da sallar la'asar tai ta nafilfilu tana roqan uban giji ya dakatar da maganar auranta ita da azzalimi mashkhur...............



Typing........



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYARO💜❤💜



*free book*💜❤💜



*inga godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yimuku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment............ pls sabida hakan shi zai bani qarfin guwar cigaba da rubutu........💜❤💜

Gamasu buqatar a sasu a group d’in littafin ADALILINTA sai suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. In kun karanta ku tura wasu groups d’in pls..

New book on 2023.
[11/06, 22:23] Maman Xuhra: “ADALILINTA”




ADALILINTA💜❤💜



BY AMINA BAYERO 💜❤💜



*page4*



Ya dakatar da maganar auranta da azzalimi mashkhur................



MYMY..............

tana shiga d'akita ta fara safa da marwa cikin tashin hankali. Tunanin momy duk ya kulle, ta rasa ta ina zata biyowa lamarin. Gashi kuma tasan halin dady da kafiya. In yayi magana baya JANYEWA.



Yanzu duk AIKIN da nakewa mashkhur in ya auri zahra zai tashi a banza kenan? Abidda momy take tinani kenan. A fili ta furta inah wallahi, hakan bazai tab'a yuyuwaba mah.



bari na kira SARATU dan musan abinyi, inma gun BOKAN zamu koma sai muje. Wayarta momy ta d'auka ta fara kiran number saratu qanwar ta dan neman abinyi, amma wayar cikin rashin sa'a wayar a kashe. Wani baqin cikine ya sake turniqeta momy.



Ajiye wayar momy tayi tana tinanin abinyi. Kamar an tsikare ta, tai zunbur ta tashi ta fuce daga d'akin. Tana ficewa kuwa ta nufi hanyar part d'in ammi.........



AMMI.........

Ammi tana shiga d'aki ta zauna a bakin gado jiki a sanyaye. Ba abidda take furtawa sai innalilahi'wa'inna'ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fimusubati' wa'akilifni' khairin'minha.



Ammi tinani take kala-kala game da auran nan.Tabbas in aka had'a auran nan zanfi kowa farinciki, tindda daga mashkhur har zahra duk 'yayana ne, amma fa auran nan yanada babban HATSARI.



Tana cikin zancan zuci taji ana murd'a handel d'in qofar d'akin da qarfi. Ammi mai da kallanta tai kan qofar, dan ganin waye. Momy tagani ta shigo kamar an hankad'ota.



Haba halima ya zaki shigo d'aki ba neman izini ba sallama?.
Kiyi haquri hankala nane ba' a kwancaba. Ok mai ke tafe da ke? Ammi ta tambaya fuska ba annuri.



Kema kinsan mai ketafe dani, ai ba zai wuce abinda ya faru ba. Toh halima ni yanzu mai kikeso nayi ne?. Haba maryam ya za'ai kina gani za'a bawa mashkhur wacca banzar yarinyar kuma kinqi magana?.



Ammi kuwa kallan momy takeyi cikin mamaki, wai ita da d'anta amma ta ringa nuna mata iko da fin qarfi. Nunfasawa ammi tai tare da cewa haba momy nifa bana san ki ringa aibatamin d'iya fa.



Zahra 'ya tace kuma haryanzu ban dena mamakin tsanar da kikewa zahra ba, nasan dai ba laifi tai miki ba, kuma banajin dad'in hakan fa. Kuma zahra na d'auke ta dai-dai da duk d'an dana haifa a cikina,.

itama nasan zahra duk duniya bata da uwar da tafini. Kuma zancan auran da kiketa d'aga jijiyar wuya akai nima ai ban san auran nan nake ba. Tom barima na gaya miki abinda ba ki sani ba



Wannan maganar auran hajiya ce ta had'a kuma kinsan hajiya kaka uwace a wajena ko? Tun ina jaririya take d'awainiya dani harna kawo haka. kuma bazan iya ja da maganartaba, bare shi dady data haifa da cikinta.



Ammi tana rufe bakinta taji qarar bud'e qofa. Amir ne ya shigo fuska jiqe da hawaye ya qaraso wajan ammi. Ammi ruqo shi tai tare da d'ora shi akan cinyarta tana cewa babyna mai ya saka kuka?



Amir share majina yayi yana cewa ammina kije ki bawa auntyna hakuri ta d'ena kuka banasan ta ringa kuka.
Ai kuwa momy da take tsaye tanaji haka wani baqinci ya turniqe ta, tsaki momy taja tabar d'akin cike dajin haushin kaka.



Ammi kuwa ko kallanta batayi ba tafara yiwa amir magana. Kayi haquri babyna kaji auntynka zata dena kuka, kaima ka dena kuka. Tom ammi wayasata kuka?. Ba wanda yasa auntynka kuka



Bata da lafiya ne shiyasa. Tom ammina ki bata magani. tom shikenan babyna zan bata, zaka sha bobo ko? D'aga mata kai amir yayi alamun ehh. tashi tayi ta bud'e firij ta d'auko mai bobo tare da bud'e mai murfin.



Shidai amir ya karb'ane amma tunanin auntynsa kawai yake.
Ammi kuwa bazata iya bawa zahra haquri ba sabida batasan mai zatace mata ba, shiyasa ma bazata wajan ta bah. Tana cikin fad'ar haka a ranta taji an fara kiran sallar la'asar.



Da sauri ammi ta, d'aga hannuwanta guda biyu sama tana roqan ALLAH, kamar haka.
Ya ALLAH in wannan auran muhammad da fatima al khairi ne, ka tabbatar da shi nan kusa kuma ka kore mana fituntinin ciki.



Ya ALLAH in kuma auran nan ba alkhairi bane, ALLAH yasa karya faru, ka kawarda maganar auran, Dan darajar annabi Muhammad (S.A.W). Tana gama fad'in hakan ta shiga toilet dan d’aura alwalah...............



Typing.........



"ADALILINTA💜❤💜



BY AMINA BAYERO 💜❤💜



*free book*💜❤💜



*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai sun ADALILINTA. Ina yimuku fana alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment.......... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutu.



Typing.............



ADALILINTA💜❤💜



AMINA BAYERO💜❤💜



*Page5*

Tana gama fad'in hakan tashiga toilet dan d’aura alwala............



HAJIYA KAKA..........

Cikin farin ciki ta qarasa part din ta. Tana zama ta d'auki wayarta, ta danno Number MALAM IBRAHIM. Ringing uku wayar tayi mlm Ibrahim ya d'aga tare da sallama. Wa'alai'kassalam, mlm ibrahim ya aiki.



Alhamdulilah hajiya binta ina cikin qoshin lafiya fatan nan haka?. Nan ma lfy malam, yauwa to masha ALLAH. Hjy kaka cigaba da cewa tai yauwa dama inaso na gayama na yanke shawarar zan had'a auran zahra da muhammad ne,,. Masha Allah hajiya gaskiya kinyi tinanin mai kyau ALLAH ya sanya alkhairi.



Ameen sai kayimin addu'a da istahara nima zanyi tawa anan, insha ALLAH zuwa gobe zan iso. Tom hajiya ba damuwa ALLAH ya kawoki lafiya. Ameen mlm ibrahim, daga haka sukayi sallama.



Hjy kaka tana katse waya ta fara addu'a da roqan ALLAH kamar haka.
Ya ALLAH kana ganin bada wata mummunar manufa na had'a auran zahra da mashkhur ba kuma ba da niyar ya zalince ta ko ya cuceta na had'a auran ba.



Da niya mai kyau na had'a kuma nasan ALLAH kafini sanin da niyar da na had'a. Ya ALLAH kana ganin fatima zahra AMANACE awaje na, ALLAH Kada ka bada dama muhammad ya cuce ta.



Kasa ya zamar mata farinciki a rayuwa, ya ALLAH kasa ADALILINTA ya shiryu, Ya ALLAH duk wata fitina ka koreta. ya ALLAH Kasa auran zahra da muhammad ya zama alkhairi duniya da lahira,



ka basu zuri'a d'ayyiba ka basu zaman lafiya mai d’aurewa, kasa su qaunaci junansu, ya ALLAH ka kawar da tsanar da kiyayyar da take tsakanin su. tana gama addu'ar ta nufu part d'in dady...........



MOMY...........

Azuciya ta koma part d'inta. Tana shiga ta haye sama, ta fara maganganu kamar haka. Shegiyar tsowuwa uwar kinibibi mai taurin kai da taurin ran tsiya jarababiya kawai, insha ALLAH sai naga BAYANKI.



In ma banda makirci irin naki ina ruwanki da auran su makira kawai. Tana gama fad'ar haka ta janyo wayarta. Ta sake daily d'in number saratu, ai kuwa cikin ikwan ALLAH ta shiga amma har ta katse bata d'auka ba.



Momy sake kiranta tai ai kuwa akaci sa'a wannan karan ta d'aga. Ko sallama babu momy magana, haba saratu tin d'azu ina kiranki waya a kashe yanzu kuma na kira kinqi d'auka?



Afuwan yaya halima wlh wayata tace ba caji sai yanzu nasa ne yanzu na dawo daga asibiti na dubo KISHIYATA wai ta haifi 'yan biyu maza kinsanta da haiwuwa kamar akuya wlh, sai nayi maganinta.



Ke dallah matsa, wayake ta wannan banzar kishiyar taki kinsan mai yake faruwa kuwa? Ah lpy yaya halima mai ke faruwa ne? Nan momy ta kwashe abinda ya faru ta fad'awa qanwarta saratu.

Tare da qarawa da, ko zamuje wayan BOKA BUTU ne gobe?.
Wata uwar dariya saratu ta saki. Haba saratu wannan wana kallar iskanci ne ehh? Ina neman shawara, a wajanki kuma kina yimun dariya?.



Ai yaya halima fad'uwace tazo dai-dai da zama. Momy tace mai kike nufi ban gane ba? Haba yaya halima ai wannan ba abin tayar da hakali bane. Kai saratu kimin bayani yarda zan fuskanta.



Yaya ai mu wanna auran alkhiri ne a garemu,. Momy tace yaza ai kice haka saratu? Bari kiji yaya, kin san dai mashkhur basan zahra yake ba ko? Momy tace ehh hakane.



Tom kinga ai aka had'asu aure kutumar ubanta zaici, daga qarshe kuma ya kashe 'yar iska, kinga daganan sai gidan yari, kud'in da zamu kai wa boka yayi mana aiki ya huta.
Na biyu kuma kinga shikenan, mun huta da kawowa Abdul majid harin auran zahra.

Hhhhhhhhhhhhhhhhhh wata shu'umar dariya momy ta saki. Tare da cewa gaskiya saratu kwakwalwar ko tanaja sosai, hehehe ai kema boka ce mai zaman kanta.



Hhhhh kai yaya halima baki da dama. Momy nunfasawa tai tare da cewa amma fa saratu naso zahra ta auri d'an iska wlh. Kai yaya halima to in badda abinki mene marabar mashkhur da dan insakan.



Kinsan dai mun mayar dashi cikakyan D'AN ISAKA, shine SHAYE-SHAYE shine BIN MATA, ko yaje qasar wajan ma abinda yake yi dan ba karatin yake ba.



Ke dai bari saratu ai wlh yadda d'ana abdul majid bai

Please Login or Register in order to submit comment