Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka sani tinda ba'a gaban mu akayi ba,. Ke ai da ya saba wlh jikin sa bazai ringa 6arin nan ba. Ehhh kuma hakane dan baki gani ba har wani gumi yake. Tom muje sai akyi yaya? Daga nan kukan baqin ciki na sa mana, ke wai kinsan wani abun mamaki, da sauri ilham ta girgiza kai, dariya zahra tai tare da cewa, kinji abin mamaki wai ni yaya mashkhur ya bawa haquri.

What's haquri kuma zahra? Hhhhhhhhh kai wlh zahra kin cuceni da baki bani labarin nan da wuri ba ni tinda nake na ta6a ganin yaya mashkhur ma yana bada haquri kuwa?. Ke bayan ma fa ya mayar da ni bed sai da ya sake bani haquri, ke na uzzira mai da kuka kinsan ai bayasan hayaniya sosai kinga shima yadda ya koma kamar yasa kuka ke ranar har sai da ya bani tausayi wlh, dan lalla6ani yi ringayi kamar kwai.

Wata uwar shewa ilham ta saki tare da cewa, zahra dama zaki iya aikata wanan aiki kuwa. Haka dai zahra ta cigaba da bawa ilham lbari har lokacin da mashkhur yayi amai, washe gari ta koma bedroom d'in ta. Daga haka zahra ta kame bakin ta. Wai shikenan labarin ne? Gyad'a ka zahra tai alamun ee, wani kallo ilham tai wa zahra tare da cewa! Ke fad'i dai gaskiya 'yar nan?.

Hmm ilham wlh sauran bazan iya fad'a miki ba sunyi nauyi. Haba zahra ki gayamin, tom zan gaya miki ki bari ba yau ba amma ki biyoni bashi. Murmushi ilham tai tare da cewa, ai kuwa zan biyo ki ko dai ma abin akayi ne kike 6oyeni. Dariya zahra tai tare da cewa, ke daran da zamu dawo nigeria lamarin ya faru to da shi akayi ma zaki ganni garau haka ne.

Dariya ilham tai tare da cewa, kuma fa hakane amma zahra wanan lamarin yaban mamaki yaya mashkhur ne yayi miki jinya sanan ya baki haquri daga karshe har lala6aki yake. Ah karma yayi mana bashi ya jazamin ba, hmmm duk da dai hakan abun da mamaki. Ke dai bari ilham bari na fita kicin ko zan samu abun sha mai sanyi wuyana ma ya bushe sabida tsabar magana.

To sai kin dawo zama ki samu ko nazo na raka ki ne? Girgiza kai zahra tai tare da cewa, aa gidan nan baqona ne zani ni kad'ai, ilham tana qoqarin magana taji wayar ta ta fara ringing. Cikin sauri tace zahra miqomin wayar nasan yaya ahmad. Zahra data sauko daga bed d'in wayar ilham ta d'auka tare da cewa, ai kuwa mayan ne. Dariya ilham tai tare da cewa, wlh sai na gaya mai.

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Thursday page.........

Da sauri zahra ta janye wayar tace ai kuwa bazan baki ba, ya haquri karta tsinke wlh bazan fad'a ba miqa mata wayar zahra tai tace gashi karki cinye ni. Da sauri ilham ta kar6i wayar ta d'aga sanan tace ai kuwa sai na fad'a. Zahra kuwa cewa tai wlh kika fad'a bazan baki labarin da kike bina bashi ba. Tom shikenan wasa nake bazan fad'a ba. Daga haka ilham ta kafa wayar a kunan ta itama kuma zaha tai fucewar ta.

Bayan ilham da ahmad sun gama sallama ahamd cewa yayi pretty ke dawa kike ta magana haka. Murmushi ilham tai tare da cewa, nida masoyiyata abar qaunta mana, murmushi ahmad yayi tare da cewa, wacce daga ciki ammi ko hajiya kaka. Girgiza kai ilham tai kamar yana ganin ta sanan tace aa baka canka ba ka ta6a ji nayi musu wanan kalaman ne?.

Eh kuma hakane pretty na to wace?, aa gaskiya bazan fad'a ba sai da ka canka, a iya sanin ka wace masoyiyar tawa farin ciki na. Shiru Ahmad yayi na wasu lokutan kafin yace to da dai qanwata tana nan sai nace ita kikewa, amma ban sani ba ko a cikin sauran 'yan uwan naki kikewa. Murmushi jin dad'i ilham ta saki sanan tace to ka canka zahra ce.

Cikin mamaki ahmad yace dama sun dawo ne? Eeh mana tun dazu da rana ma Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa, gaskiya bansan da zuwan su ba ai yayan naki bai gaya min ba, kuma kema baki gayamin ba d'azu da mukayi chat ai da tuni nazo wajan qanwata dan na matsu na ganta. Ilham ta gano in da zancan ahmad ya dosa so yake yazo yaga jikin zahra.

Amma a fili sai tace muma ai basu gaya mana zasu dawo ba kawai ganin su mukayi ba tsammani, ni kuma nayi tinanin yaya mashkhur ya gaya ma ne shi yasa ban gaya ma bai. Okay ba damuwa ki gai da zahra kuma kice gobe zanzo na ganta,, murmushi ilham tai tare da cewa, zakazo ka ganni ku gaisa ko kuwa ita zakazo ka gani ni kuwa mu gaisa.

Dariya Ahmad yayi tare da cewa, kai ilham baki da dama tom shikenan duk yadda kika za6a haka zanki kinsan fa farin cikin ki shine nawa.............

Zahra a hankula take sauka daga kan benan, tana tafiya har d'an kwalin kanta ya zame ya fad'i bata sani ba da ya ke kan nata yana da santsi sosai. Duk girman fallon ba wani haske sosai da yake an kashe globes d'in falon gaba d'aya, kawai blue aka bari shima blue d'in bamai haske ba.

Kai ammi kenan ai kuwa na dawo yanzu zamu fara wasan kashe globes ina kunnawa kina kashewa, zahra ta qasa maganar tana wucewa wajan kunna globe d'in d'akin. A jere socket d'in kunna globe d'in suke, wajan guda shida, in aka kunna socket d'aya biyu ne zasu kawo. Haka zahra ta ringa kunna socket d'in one by one, harta gama tass, falon ya karad'e da gaske kamar da rana ba dare ba.

Haba haske ai rahma ne yanzu wanan mutum ya futo da daddare ai in ba haske duk girman falon nan ai tsoro zai ji. Zahra kamar ance ta kalli gefan ta, tana kallon gabanta ya d'an fad'i. Saka makwan ganin mashkhur akan kujera ya zuba mata manya idanun nan nasa ga kuma plate d'in abinci a gabasa, ga dukkan alamu abinci yake ci.

Wata siririyar ajiyar zuciya zahra ta saki a zuciya ta tace ko taya ma yake cin abinci a cikin blue light oho, kai ka sanarwa kan ka zahra ta fad'i hakan a zuciyactana kama hanyar kicin. Mashkhur kuwa cigaba da bin zahra yayi da ido, sai wani juya boobs take kamar wata uwa, duk da kuwa ba wani girma ne da su ba, tana dai dasu dai dai gwargwado, ga gashin nan nata ya bazo ka fad'a sai kyalli yake.

Zana shigewa kicin d'in mashkhur ya saki ajiyar zuciya tare da mai da idanun sa kan plate yana tinanin wani abu. Zahra kuwa tana shiga kicin ta bud'e firinji tana bud'ewa tiririn sanyi ya bigeta d'an matasawa tai sanan ta d'auko cup ta tsiyaya leman kwakwa da madara da biyo. Sai da zahra ta cika cup d'in ciki fam kamar wadda zata iya shanyewa.

Bayan ta gama zubawa ta mayar da glass jug d'in cikin firinji sanan ta rufe ta ruqo glass cup sabida sanyi zahra sai data d'ora cup d'in a kan plate sanan ta iya d'aukowa. Zahra tana futowa ko kallan indo mashkhur yake batai ba ta fara tafiya abinta. Zahra tana tana cikin tafiya taji muryar mashkhur yace kee!! Shiru zahra tai bata juyo ba bare ma ta dai na tafiya.

Kee! Zahra taji mashkhur ya sake cewa, nan ma zahra bata jiyo ba bare ta tanka. Ke ba magana nake miki, zahra tana shirin hawa step ta juyo tare da cewa! Magana kake? Ban saniba mara kunya wlh kika bari na taso sai kin gane baki da wayo, ta6e baki zahra tai sanan tace! Ai da nayi tinanin bada ni kake ba tinda naga ba sunana ke ba.

Mashkhur kuwa jinjina kai yayi tare da mayar da kansa kan plate ya cigaba da cin abincin. Zahra sai taji kamar ta hau sama amma ta d'an jin tsoro dan tasan zai iyu biyo ta gwarama taje, dan yanzu dare ya raba basu ammi bare su ceceta in ya fara jibgarta. Haka zahra ta juya hannu riqe da plate d'in glass cup.

Tana zuwa ta tsaya a gefan mashkhur tare da cewa, gani sauri nake. To tinda sauri kike mai zai hana ki tashi sama banza mara kunya mai tafiyar 'yan iska. Mamaki ne ya kama zahra cikin mamaki tace tafiyar 'yan iska kuma? Kawar da kai mashkhur yayi tare da cewa, zauna magana zamuyi.

Shiru zahra tai tana nazari can kuma ta samu waje a gefan mashkhur ta zauna. Mamaki ya kama mashkhur yadda lokaci guda zahra ta raina shi sam bata shakkar mayar mai da magana. Muryar zahra yaji da take gefan sa tana cewa inajin ka. Wani irin mugun kallo mashkhur ya watasa mata ta gefan ido.

Zahra kuwa kallan ya d'an bata tsoro amma sai ta d'anyi murmushi tare da d'aga cup d'in leman kwakwar ta kai bakin ta ta zuqa kad'an sanan ta dan rintse ido sabida sanyi da taji har kwakwalwar ta gashi sanyi ya kashe mata hawori.

Rai 6ace mashkhur ya riqe hanun zahra wanda ta d'auki leman da shi ya murd'a, wani siririn ihu zahra ta saki tare da cewa mene haka kuwa. Murd'e hanun ta mashkhur yayi sanan ya kar6i leman da d'ayan shannu sa yana kar6a ya d'aga cup d'in ya kai bakin sa. Ba mashkhur ne ya aje cup d'in ba sai da ya shanye tass. Zahra tayi mamaki yadda lokaci guda mashkhur ya shanye tass duk sanyi sa ko saukewa bai yi ba bare rintse ido.

Ajiye cup d'in mashkhur yayi akan plate d'in daya cinye abin cin sanan ya zubawa zahra ido. Lokacin gudan tsoro ya bayyan a fuskar zahra saka makwan yadda taga mashkhur ya riqe mata hannu gam kuma ya had'e rai, ke ki shiga hankalinki ni ba sa'an wasan ki bane wlh in banda rainin hankali ke tunda kike kin ta6a gani wasu daga cikin qanne na sun zauna a kusa dani in ina kan kujera, sai ke fitsararriya ko faruq da haida da suka girme kin basayi.

Da sauri zahra ta girgiza kai cikin tsoro, to ke ubann waye yace ki zauna akan kujera ina kan kujera kuma wai a kusa dani sabida rai ni. Mamaki ya d'an kama zahra ita da a russian yake yawa zama a kusa da ita dan harma ta saba amma yau ya nuna bai san zancan ba. Ba magana nake miki ba? Turo baki zahra tai tare da cewa! To ni ai ba qanwar ka bace.

Sake matsa hanunta mashkhur yayi tare da cewa, to in ba qanwar tawa bace wace? On expected, zahra tace matar ka mana. Itama kanta zahran batan san ta fad'awa ba. Dan zaro ido mashkhur yayi yana mamkin magar zahra dan bai ta6a tinanin zata bad'i hakan ba. What mai kikace mashkhur ya fad'a yana zarowa zahra ido.

Shiru zahra tai tare da d'an ja da baya, bazaki maimata mai kikace ba?. Cikin tsoro zahra tace haka nace jakar ka mana. Shiru mashkhur yayi yadda idon zahra yayi luwu-luwu kamar tai kuku sai ya d'an bashi dariya, tana son yi mai rashin kunya amma tana jin tsoro. Danne dariyar mashkhur yayi tare da cewa, ke kin isama kizo ko a jakar tawa ne?.

To ai naga daga zaki sai duka sai hantara da harara kaga ai jaki ake duka, kai gwarama jakar nasan ta fini daraja a wajan ka. Hakan da zahra tai sai ta bawa mashkhur tausayi sosai feyema da ko yaushe, da sauri ya saki hanunta tare da cewa! Duk wani d'an adam yana da daraja a wajan ALLAH, da zaki gane da kin dai na had'a kanki da dabba mafi qasqanci,.

Shiru zahra tai tana sauraran mashkhur hakan da yayi mata sai taji dad'i wani qasaitaccan murmushi ta saki tare da cewa, tom ngd sosai da shawa ashe ba yadda nake tinani ka d'auke ni ba,. Murmushi mashkhur ya saki a cikin zuciyar shi a fili kuma cewa yayi, magana nake so muyi kina ji koh?.

Da sauri zahra ta gyad'a kai tare da cewa! Inaji, d'azu mai kike so ki gayawa dady?. Au ai nayi tinanin ka sani shi yasa ka hanani fad'a. Had'e rai mashkhur yayi tare da cewa, wlh ki shiga hankalinki kika sake gayamin maganar da bangamsu da ita ba sai dai kiji mari a fuskar ki. Zahra tanaji mashkhur ce wlh ta shiga tai tayin ta.

Gayamin mai zaki gaya mai, yadda zee ta wullo ni daga sama tai yimin lahani shi zan gaya mai. Mene amfanin fad'ar abinda ya wuce? Mashkhur ya watsawa zahra tambayar. Ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan tace! Kai ne kace fa ka yadda in muka dawo na gaya mai amma karna gaya mai a russian. Jinjina kai mashkhur yayi sanan yace hakane, amma yanzu ba na so ki gayawa kowa maganar.

Cikin mamki zahra tace sabida mai? Sabida haka naso mashkhur ya fad'a yana tsare ta da ido. Da sauri zahra ta girgiza kai sanan tace gaskiya yay mashkhur ni bazan iya qin fad'a ba a cuceni ace bazan fad'a ba yanzu ta daki banza kenan. Murmushi mashkhur ya saki sabida yadda zahra tai maganar sanan yace bata daki banza ba ai an rama miki yanzuma tana gidan yari.

Cikin mamaki zahra ta d'ago da kai tace da gaske? Zan miki qaryane mara kunya in baki yadda ba ki tambayi ahmad ai shi ya sani. Ni dai duk da haka sai na fad'a,, to ki fad'a amma dai zaki shirya zama da ni a matsayin mijin ki ba din din din kuma can abuje state zan kai ki daga ni sai ke, wlh dukan asuba da ban na safe daba na rana daban na dare daban na tsakiyar darema da ban.

A one month sai na mayar da ke tsowuwa mara haqora kamar kakar hajiya kaka har sai kinfi kakar hajiya kaka ma tsofa mashkhur ya qarasa maganar yana qonshe dariyar shi, sabida yadda yaga zahra tana zazzaro idanuwa. Wlh bazan fad'awa kowa ba in sha ALLAH sanan ta miqe, tana shirin tafiya a tsorace. Ruqo hanunta mashkhur yayi tare da cewa, ai ban gama maganar ba dawo ki zauna.

Zama zahra tai tare da cewa! Dan ALLAH yaya mashkhur kayi haquri karka cigaba da gayamim irin azayar nan ni wlh bazan fad'a ba har abada koma ka sake ni bazan fad'a ba. To kima fad'a mana inna sake ki tsoran mai zanji dad'in ta dai ba wanda zai sake d'auramin aure dake a rashin sani saki uku zan miki rasss. Murmushi zahra tai tare da cewa, ashe da gaske na kusan komawa mrs ABDUL MAJEED.

Mashkhur ji yayi nunfashi shi ya d'an d'auke zuciyar shi ta wani buga. Mashkhur yana mamakin yadda lokaci guda yake tsintar kansa a wanan halin in yaga zahra ta ambaci sunan abdul ko wata alaqa ta had'a su. Da kyar ya iya d'ago sanan yace ki bari sai na sake ki an d'aura, har yanzu kina mrs Muhammad mashkhur.

Zahra ji tai zuciyar ta ta biga rass saka makwan yadda taji sunan yayi mata dad'i ko dan mai shine ya furta oho. Kinji abinda nace koh? Gyad'a kai zahra tai sanan tace naji. Okay next kuma shima karki fad'i d'ayan abun. Cikin mamaki zahra tace me kenan? Jim mashkhur yayi na wasu lokutan yana qarewa zahra kallo, sabida yadda yaga gashin ta yabai qafad'a tai masa kyau sosai ba d'an kwali. kafin yace au harkin manta abinda ya faru koh?.

Ehh gaskiya abubuwan ne da yawa na manta, dame dame kenan? Mashkhur yayi tambayar yana zubawa zahra ido. Punishment d'in da ka ringa bani kala-kala mana. Kwarai shima karki fad'a sai kuma d'ayan ki tina mana,. Shiru zahra tai tana nazari can tace ni dai har yanzu na kasa tinawa. Okay abinda ya faru daran da zamu dawo nigeria har na kwana a bed room!!!!!!

Da sauri zahra ta rufe fuska sare da cewa! Ehh na tuna iskancin kenan kake nufi, ai ko baka ceba bazan iya fad'a ba tinda ni ba 'yar iska bace. Murmushi mashkhur yayi a zuciya shi yace, ke zahra baki da dama kenan nine d'an iskan. A fili kuma cewa, yayi duk ma yadda kika d'auke shi, shi nake nufi, sunkuyar da kai zahra tai tare da cewa tom yanzu zan iya taya, cikin ko in kula mashkhur yace jeki. Zahra tana qoqarin miqewa sai ga ammi da dady suna saukowa daga sama.

Ga dukkan alamu daga bedroom d'in ammi suka fito, zahra kuwa ji zai tama kasa miqewa. Kamar wadda aka sa mata gam aka manne ta. Sai da suka gama saukowa sanan ta miqe ta kama hanyar tafiya. Zahra cikin ta duk yayi sanyi kamar wadda aka kama tana aikata ba dai-dai ba, har ta qaraso wajan su dady.

Ammi da dady cike da mamaki suka kalli junan su sanan sukai mai da kallon su wajan zahra. Zahra mai ya fito da yake da tsowan daran nan ko d'an kwali babu akan ki? Ammi ta watsawa zahra tambayar. Shafa kanta zahra tai sanan tace! Au ni bansan ba d'an kwali a kai naba inga samewa yayi a kicin, ammi abinci na fito ci, okay shine kukaci tare da yayan naki? Ammi ta watsawa zahra tambayar. Girgiza kai zahra tai tare da cewa, nima anan nazo na same shi, ba tare da shi naci ba.

Okay mamana koma ki zauna daga inda kika taso zamuyi magana, dady ya fad'a fuska a sake. Tom dady zahra ba musu ta koma ta zauna a kusa da mashkhur cike da jin kunyar dady da ammi. Suma ammi da dady wace su kai suka samu waje a akan kujera suka zauna suna zama mashkhur ya miqe tare da cewa sai da safe ammi da dady.

Ina zaka ka dawo ka zauna kai ma dakai za'ai magar. Okay dady ba damuwa daga haka mashkhur ya zauna inda ya taso wato kusa da zahra. Dady ne ya fara magana da dama inaso zuwa gobe in kun huta muyi magana to sai gashi cikin ikwan ALLAH yanzu na same ku, dama inaso na tambaye ku duka ku biyun.

Ina so naji zaku iya cigaba da zaman aure kamar yadda muka za6a muku ko kuwa?, ammi cafe zancan tai da mu dai gaskiya a so samun mu ku cigaba da zaman aure tinda auran nan harya wuce shekara, kuma kunsan dai bakyau rabuwar aure shine nake ganin kawai ku cigaba da zaman aure a shawara ta.

Kwarai maryam wanan shine son ranmu amma bari tinda su zasuyi zaman auran, kar mu shigar musu hanci da qudindine muji ra'ayimln su kafin mu yanke hukunci, yanzu inaso naji ra'ayi kowa a cikin ku. Mai sunan baba, d'agowa mashkhur yayi tare da cewa, na'am dady? Ka amince zaka cigaba da zama da mamana a MATSAYIN MATA ko kuwa?.

Hmmm ku na ganin mashkhur zai amimce kuwa?.

Hmmm ku na tianin itama zahra zata amince kuwa?.

Hmmm mu had'u a next page ranar mondy happy weekend.........


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing.........

*page 98*

Mai sunan baba, d'agowa mashkhur yayi tare da cewa, na'am dady? Ka amince zaka cigaba da zama da mamana a MATSAYIN MATA ko kuwa?...............

Dady yana rufe bakin sa mashkhur bai wani tsaya dogwan nazari da tinani ba cikin kwarin guiwa yace! Aa dady ba amince na cigaba da zama da ita a matsayin matata ba har yanzu ALQAWARIN mu yana nan. Rass, Rass, Rass, gaban dady da ammi ya fad'i dan basu ta6a tinanin haka daga mashkhur ba dan a tunanin su tuni ya yar da makaman yaqinsa ya rungumi zahra a matsayin mata.

Ammi da dady juyowa sukai suka kalli junan su cikin mamaki. Zahra kuwa a zuciyar ta sai taji dad'in hakan, dan ita burinta kawai ta auri yaya abdul. Jinjina kai dady yayi tare da mai da kallan sa wajan zahra, cikin kulawa yace! Mamana ke fa kin amince ko kuwa, sunkuyar da kai zahra tai qasa cikin siririyar murya tace dady nima ban amince ba.

yah ALLAH abinda ammi ta iya furtawa a zuciyar ta kenan, dady kuwa cewa, yayi okay mamana tashi kije ki kwanta ALLAH yayi miki albarka sai da safe, miqewa zahra tai tare da cewa, to dady da ammi good night. Murmushi dady yayi tare da cewa, good night too my dear. Itama ammi qaqalo murmushi dole tai tare da cewa, good night my daughter ki d'aure kanki.

Itama murmushi zahra tai tare da cewa, tom ammi daga haka tai hanyar step ta haye sama abinta zuciya cike da tinani kala-kala. Tana shiga bedroom d'in su taga har yanzu ilham waya take, kawar da kai zahra tai sanan ta nufi wardrobe ta bud'e ta d'auko kayan bacci ilham tasa, dan ita har yanzu trolley d'in ta tana motar yaya abdul.

Bayan zahra ta sa kayan qofar d'akin ta rufe sanan ta canza globe d'in d'akin daga white zuwa green, bayan nan ta haye gado kusa da ilham ta kwanta tana sauraran hirar ilham da ahmad, har dai bacci yayi awan gaba da zahra...........

6angaran su dady kuwa zahra tana 6acewa daga wajan dady ya kalli mashkhur tare da cewa, wai mai sunan baba sabida mai har yanzu bakai hankali ba kamar yadda muke tinani?. Cikin mamaki mashkhur yace! Dady mai nai kuwa? Harara ammi ta watasa mai tare da cewa, au bama kasan mai kai ba koh?. Kallanta mashkhur yayi tare da cewa, ni dai ammi iya sanina da ku tinda na dawo banyi wani laifin ba kuma.

Gyara zama dady yayi tare da cewa, mene ribarka in ka rabu da zahra wai?, cikin mamaki mashkhur yace dady iya gaskiya ta na gaya ma har yanzu bana son ta dady kuma karka manta kai fa kace in muka dawo har dai bama son junan mu za'a raba auran nan ALQAWARI fa mukayi dady. Jinjina kai dady yayi tare da cewa, ai ban manta da ALQAWARIN ba amma yanzu so kake ka mayar da zahra babba bazawara koh?.

Cikin mamaki mashkhur yace babba bazawara kuma dady dudu nawa take da har zata zama babbar bazawara?. Cikin mamaki dady yace! Yanzu sai da ka gama tarayya da ita har ciki ya shiga sanan dan baka da imani zakace zaka rabu da ita, bafawai dan bama son ta ne muka baka itaba, kawai dan mu cika burin hajiya ne muka aura ma ita,.

Ammi ce ta cafe zancan da cewa, qwarai kuwa muma muna son 'yar mu ba nema kai muke da ita ba. Cikin mamaki mashkhur yace ciki kuma dady, wlh zahra bata da wani ciki, nan ma mamaki ne ya rufe su dady cikin mamaki ammi tace kai da ba likita ba taya zaka san bata da

Please Login or Register in order to submit comment