Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacina yayi, kawai dai ki tayani da addu'a in kuma na mutu wajan haiwuwa, sai ki rainar min babyn ki had'a da naki koh?. Gaban ilham ne ya fad'i tace kai haba zahra in sha ALLAH zaki sauka lafiya lau ki haifa mana baby kyakyawa mai kama dake.

Jiki a sanyaye zahra tace to allah yasa ilham, ke yanzu saura wata nawa kema ki haiwu?. Gyara zama ilham tai tare da cewa ah ni yanzu saura wata biyu na haiwu ai kuwa kinga da saura ba yanzu ba. Ah haba dai ai wata 2 kamar yaune kawai dai kice tare yaran namu zasu taso suyi wasa kamar dai ni da ke. Murmushi ilham tai sanan tace aikuwa dai zahra kinga abu kamar wasa dai, wai mu zamu haiwu.

Hmm ilham ki dena mamaki ba'a mamaki da lamarin uban giji dama komai lokaci ne. Ai zahra dola na yarda komai lokaci ne dan ban ta6a tinanin ke da yaya mashkhur zakuyi aure kuzo kuso junan ku kamar haka ba kai, ikwan ALLAH kenan, kin san sai yau na gazgata zance, qiyayya zata iya juyewa ta koma soyayyah, soyayyah kuma zata iya juyewa ta koma qiyayya ikwan ALLAH kenan.

To ranar dai haka zahra da ilham suka wuni suna ta shan hirar su abun gwanin ban sha'awa.
Misalin qarfe 5:00pm na yamma bayan ilham ta gama waya da mijinta ahmad miqewa tai tare da cewa zahra bari na fara shiryawa yaya ahmad yace min yana kan hanya. Itama zahra miqewa tai sanan tace tom dama nima zan fita waje na dan taka sabida na motsa jikina kinga sai ki rakani kafin ya qaraso koh?.

Jinjina kai ilham tai tare da cewa tom shikenan tawo mu sauka. Daga haka zahra da ilham suka sauka sanan ilham taiwa hajiya kaka da ammi sallama  suka fuce waje fuska d'auke da farin ciki. Suna fita ba 6ata lokaci suka fara zagaya garden d'in gidan suna tafiya suna hira abun su. Bayan sun zagaya garden d'in sosai zama zahra tai akan kujerar lambu tare da cewa kawai ilham na gajifa sosai da tafiyar nan.

Kallon wayarta ilham tai tare da cewa kai haba zahra kin cika lalaci dudu tafiyar 20 minit mukayi fa kuma a hankula muke tafiyar. Yamutsa fuska zahra tai tare da cewa kai bawani nan, a haka ne lalaci kibar ganina arha banza muna hira da shewa amma wlh tunda cikin nan ya shiga watan haiwuwa haquri nake tafiya da kyar tashi da kyar nake, amma na rabu dake kema zakiji abinda nakeji in cikin ki ya tsofa kamar nawa.


Murmushi ilham tai tare da cewa hmmm gaskiya zahra cikin nan naki yayi girma sosai ko twins zaki haifa mana ne?. Itama zahra murmushi tai tare da cewa aa ba wani twins nifa hospital sun
shedamin baby d'aya ne a cikina. Ilham tana qoqari magana wayarta ta fara ringing, da sauri ilham ta zaro wayar ta daga jaka sanan ta zuba mata ido.

Murmushi ilham tai saka makwan ganin sunan hubbyna ya bayyana akan scream d'in wayar. Ba 6ata lokaci ta d'auka tare da kara wayar tata a kunan ta, Jim kad'an ba tare da 6ata lokaci ba ilham tace ok ganinan futowa nan da 5 minutes, daga haka ta kashe wayar ta mayar da ita jaka. Kallon zahra ilham tai sanan tace!  Kinga yazo taso na rakaki ciki sai na tafi koh?.

Girgiza kai zahra tai tare da cewa! Aa ai ni zan rakaki ke da kikazo, bari na raka ki sai mu gaisa dama na dad'e ban gaisa da yayan nawa ba zahra ta qasa fad'in hakan tana miqewa da kyar. Tom shikenan zo mu tafi ilham ta qarasa maganar tana riqe hannun zahra. Ba 6ata lokaci suka bar garden d'in hanun su riqe dana juna. Suna fita daga garden d'in ba 6ata lokaci suka nufi parking space d'in gidan.

Suna qarasawa ahmad ya futo daga mota fuska sake yace qanwata kwana biyu yakike ya jikin naki?. Murmushi zahra tai tare da d'an rage tsayin ta tana qoqari tsugunawa domin gai da ahmad d'in, da sauri ilham ta ruqo ta tare da cewa aa haba zahra a tsayan ma ya isa tinda baki da lafiya. Shima ahamd cafe zancan yayi da cewa ah haba qanwata sai kace wani baqo yayan ki nefa ai ba se kin hawalar da kan kiba tinda baki da lpy.

Murmushi zahra tai tare da cewa tom ngd yaya ahmad ina kwana. Lafiya qalau qanwata ya jikin nake?  Da sauki yaya ahmad, ok tom ALLAH ya qara lafiya ya sauke ki lafiya. Cikin 'yar jin kunya zahra ta sunkuyar da kanta qasa tare da cewa ameen yaya ahmad nagode, ku gai da gida. Tom shikenan qanwata sai anjima a gai da mutumin nawa koh?.

Murmushi zahra tai tare da cewa hmm kawai ka fad'a ne abinda kullum sai kunyi waya, in baku waya ba zaku had'u, amma dai tinda kace haka zan gaya mai in yazo. Murmushi ahmad yayi tare da cewa tom shikenan amma dai gwara ki ringa miqamin gaisuwa wajan sa ko ya qara ganin girma na tinda yanzu kice gimbiyar zuciyar tasa.  Murmushi zahra tai tare da sunkuyar da kanta qasa dan ita tama kasa cewa komai.

Hmm ai dole ki kasa cewa komai qanwata tinda kinsa ya zama mijin tace kullum bashi da aiki sai yabanki da zancan ki. Hmmm yaya ahmad kenan sai anjima dai kuje kawai, dariya ahmad yayi tare da cewa hmm ai nasan bazaki iya cewa komai ba. Gaskiya bubby ka rabu da ita haka, ka ganni fa agefa yanzu sai na shige mata fad'an nan bazan bari ka fita zaqewa ba.

Hmm shikenan ranki ya dad'e ai tinda kikasa baki zance ya qare nayi shiru zo mu tafi. Murmushi ilham tai sanan tace! Okay byee zahra sai munyi waya, haka zahra da ilham suka rabu zuciya cike da farin ciki had'uwa da juna. Motar su ahmad tana fita ta mashkhur kuma tana turo kai gidan, zahra kamar ance ta juya dan har ta fara tafiya ta hango matar mijinta mashkhur.

Wani murmushi farin ciki ta saki sanan ta juya ta fara takawa a sannu. Mashkhur yana parking ya futo da sauri zuciya cike fall da tausayin zahra ya qaraso. Yana qarasowa ya bud'ewa zahra hannu alamun hugg, zuciya cike da kewar mijinta zahra ta qarasa a hankula ta rungume mashkhur, shima mashkhur rungumo ta yayi tare da sauke ajiyar zuciya.

Sun d'au wajan 5 minutes a haka sanan suka saki junan su, cike da kulawa mashkhur ya kalli zahra tare da cewa! Teady na mai ya futo dake haka da yamma kuma ke kad'ai ko d'an rakiya babu. No bani kad'ai na futo ba nida ilham ne ta rakani na d'an motsa jiki na kamar kullum, so ni kuma daga  nan sai na rako ta suka tafi gida basu dad'e da fita ba yanzu, okay to sannu my teady bari na rakaki ciki sai na wuce masallaci..............

KU TSAYA KUJI BA FA LITTAFI ADALILINTA BANE WATA QARAMAR MAGANA CE.

abinda yasa nace ku godewa ummu farhan shine! Kunga tun daga page 115 wato feji na d'ari da goma sha bakwai wlh bata sukai.
Bayan na rubuta 'yan group Dina sun gama Karantawa to sai nai offline.

Nai wajan 2 month bana hawa sabida WhatsApp dina sunyimin banned, sai da na canza sabuwar waya.

To ni duk a tinani na ajeye page 23 a gmail dina ko na ajeye a telegram ashe ban ajiye ba na mace, sabida bansa page din a document ba, kwata-kwata ban hade su da ragowar ba.

Wlh na rasa yarda zanyi, nace wlh in dai ban samu page 23 din nan ba sai dai ku masu karanta document ku haqura da page d'in da suka 6ata. 😂😂

To sabida nasan kozan sake rubutawa wahalar da kai na zanyi nama manta abubuwan dana rubuta, to abu ba ba feji 'd'aya ba, ba biyu ba, ba biyar ba, ba goma ba, feje ashirin da bakwai fa.

Daga qarshe dai na yanke shawarar na tambayi 'yan group dina nai musu cigiya ko za'a samu wanda WhatsApp din shi be goge ba. Abu wajan 3 months fa dan wlh banyi tinanin za'a samu mai complete page din da suka 6ace min ba.

Bayan na tambaya banma sa ran zan samuba wasu sucemin wlh WhtsaAp din su yayi expiring sun goge sun turawa wani, wasu sucemin basu da shi wasu su turomin 3 page, sabida rainin hankali nida nake neman page 23.😂😂😂

Qarshe dai na samu wata yar albarka ta turomin wato ummu Farhan❤, inata farin ciki ashe shima ba complete 23 page d'in nan da dasuka 6ata bane ba a ciki ba 7 page wlh.😂

Ba page 116,117,118,119,120,121,122. Ni kuwa nace ai wlh da sauqi da page 23 ya 6ace ai gwara page 7 ya 6ace duk da shima de lbr zai wuce ku sosai wlh.

Sai nace bari na sake tambayar ta, bayan nai mata godiya nace allah yasa kar mijinta ya qaro mata kishi ya sake had'e kawunan ku waje daya da soyayyah. Sanan sai na sake ce mata dan Allah ummu farhan ki sake dubamin saura 7 page baku turoba, daga page 116 zuwa 122.

Sai tace tom bari in duba miki, sai naji wani dad'i, bayan few minutes sai ta turomin ragowar page 7 din, yah ilahi dad'i mutanan arziki wlh naji dad'i shiyasa nace bari na gaya muku sabida ta temake ku sosai.

Karkuce nacika ku da surutu ko bai shafe kuba😂 dan wlh ya shafe ku da lbr da dama ya wuce ku, duk da na samu qalu bale akan rubuta littafin nan da dama 😢😢 amma dai muje zuwa zan dan sanar daku wasu daga cikin qalubalan daga fuskanta amma sai ba yanzu ba sai na gama rubuta littafin.

Continue...............

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing...............

*Page 139*

Sun d'au wajan 5 minutes a haka sanan suka saki junan su, cike da kulawa mashkhur ya kalli zahra tare da cewa! Teady me ya futo dake haka da yamma kuma ke kad'ai ko d'an rakiya babu. No bani kad'ai na futo ba nida ilham ne ta rakani na d'an motsa jiki na kamar kullum, so ni kuma daga  nan sai na rako ta suka tafi gida basu dad'e da fita ba yanzu, okay to sannu my teady bari na rakaki ciki sai na wuce masallaci..............

A hankula mashkhur da zahra suka jera cike da qaunar juna suke tafiya, mashkhur yana raka zahra ciki ya dauro alwala sanan ya futo ya tafi masallaci. Bayan ya dawo zama yayi suka sha hirar su shida zahra, misalin qarfe 10 na dare ya tafi shima badan yaso ba zahra ce ta tirsasa shi. Ko da ya koma gida wanka kawai yayi ya kwanta ya dauki wayar sa suka cigaba da shan soyayyah su ta waya.

Sun kai misalim qarfe 2 dare suna chat, daga qarshe dai bacci ya kwashe zahra, shima haka mashkhur ya kwanta bacci bada son ransa ba.
Washe gari bayan zahra tai sallah asubayi ba komaw bacci tai ba ita ta tashi ba sai wajan qarfe 1 na rana. Tana bude ido ta tashi zaune da kyar ta d'auki wayar ta. Kamar yarda tai tsammanin ganin kiran mashkhur haka kuwa ta gansu barka tai.

Nml call 10 text message 20, WhatsApp kuwa videos call 5 audio call 15 voice note 10 chat message 20. Sauke ajiyar zuciya zahra tai tare da sakin wani siririn murmushi a zuciya ta tace hmmm yaya mashkhur kenan sai kace wanda na 6ata. Zahra tana qoqarin kiran mashkhur taji kiran sa ya sake antayowa.

Da sauri ta d'aga tare da kara wayar a kunan ta cikin sanyayiyar muryar mai bacci tace hello my hero. Ajiyar zuciya mashkhur ya saki tare da cewa teddyna gaskiya kin sani a tinani, tun dazu nake fama kiran ki da turo miki message shiru, kin ganni ina qoqarin tawowa ma. Bacci fa nake ban tashi da wuri bane, amma ka bari zuwa anjima sai kazo.

Hmm hanani zuwa ma kike ko dan baki san yarda na damu dake bane shi yasa kike min haka. Aa kaga yanzu na tashi daga bacci, sai nayi wanka naci abinci kuma zan koma bacci zuwa dai anjima da yamma sai kazo. Tom shikenan gimbiya yarda kika ce ai dole nabi, ya kike ya baby. Shafa qatan cikin ta zahra tai tare da cewa ina lpy baby ma yana lpy gashi sai motsi yake.

Hmmm gaskiya dai ai gwara ya motsa sosai tinda har yanzu kinqi haifa mana shi yazo duniya. Murmushi zahra tai tare da cewa yaqi futowa dai, duk sanda yake so ni ba haifar shi zanyi ba. Shima mashkhur murmushi yayi tare da cewa tom shikenan allah ya sauke ki lpy dai amma fa ni kam na matsu ya fito sosai ki gayama mai pls.

Wata gajeriyar dariya zahra ta saki tare da cewa cewa ai tana jinka amma zan sake gaya mata. Hmmm shikenan tinda tana jina, ko yana jina. To sai dai an haiwu zamu tabbatar da itace ko shine. Haka dai mashkhur da zahra sukai sallama cike da qaunar junan su, abun gwanin ban sha'awa.

Zahra tana ajiye wayar ammi ta shigo bedroom din baki d'auke da sallama. Fuska d'auke da murmushi zahra ta amsa tare da cewa ammi sannu da aiki. Murmushi ammi tai tare da cewa ai zahra ke zancewa sannu da aiki, nayi tinanin zan shigo naga kin haiwu kin yankewa cibiya kinwa babyn wanka amma shine zanzo na ganki akan gado yarda na barki.

Wata siririyar dariya zahra tai tare da cewa kai ammi kin fiya zaulaya, taya zan iya haiwu ni kadai a d'aki kema dai kinsa abinda bazai ta6a yuwuwa ba. Zai yuwu mana sai dai baki sa kan ki ba, to tin dazu nake shigowa ko kin tashi yanzu sau shida kenan ina shigowa sai yanzu kika tashi fa. Hmmm na gaji ne shi yasa ammi.

Ba dole ba kin raba dare kina abu guda, sunkuyar da kai zahra tai ba tare da tace komai ba. To kin fara kenan yanzu dai me kike so abinci zaki fara ci ko sai anyi wanka. Kai ni dai bazan iya cin abinci ba sai nayi wanka. Tom bari naje na had'a miki ruwan zafi, daga haka ammi ta wuce toilet.

Bayan ammi ta gama had'awa zahra ruwan zafin futowa tai tare da cewa to zahra taso. Dafe bayan ta zahra tai tare da cewa wlh dai yau jikina yafi na kullum nauyi ammi bazan iya tashi ni kad'ai ba. Qarasowa ammi tai tare da cewa to sannu bari na tayaki ki ki miqe, amma zahra ya kamata ki sawa kanki jarumun ta ke da haiwuwa ko yau ko gobe, kuma kin san ita haiwuwa babu dan tai mako ke kadai zaki haiwu.

Kai ammi sai kuma kisa nai tajin tsoro nifa kina d'agamin hankali., hmmmmmm shikenan na dena gaya miki inkinzo haiwuwar Kyagani. Wash zahra ta fad'a wanda ta mike da taima kwan ammi, sannu ammi ta fada tare da ruqo hanun zahra suka nufi toilet. Bayan sun shiga kamar dai kullum ammi ta temakawa zahra ta cire kaya sanan ta wanke mata bayan ta.

Dama bayan tane zahra bata iya wankewa tun sanda cikin ta ya cika wata takwas, kullum mashkhur ne yake taimaka mata wajan wanka. Haka zahra ta qarasa wanka da kyar sanan ammi ta shigo ta daura mata zani suka fita. Bayan haka ammi ta zauna ta shafawa zahra mai a qafa da baya, ita kuma zahra ta shafa a hannu da jiki.

Bayan sun gama tasa kaya miqewa tai da kyar suka sauka qasa domin taci abinci. Zahra tana sauka ta hangi yaya abdul akan kujera yana ta danna waya. A hankula zahra ta qarasa kusa da shi nesa kad'an a kujerarr da yake zauna ta zauna sanan tace yaya abdul sannu.

Da sauqi Abdul ya juyo tare da cewa ah zahra sannu da fitowa tun dazu nake cigiyar ki, da baki fitoba har d'akin zan qaraso tunda yau rowar ganinki kike. Murmushi zahra tai sanan tace aa ai ko zanyi kowa rowar ganin kai na ai banda kai yaya abdul kawai dai ban futo bane.

Tom shikenan ykk da fatan kina lpy? Ina lpy qalau hala da mutuniyar kake chat shi yasa bakaji na sauko ba har na zauna a kusa da kai. Murmushi abdul yayi tare da cewa hmmmm ni dai bance ba, hmm ai dai an kusa a shafa fatiha koh, saura wata nawa ne ma zahra ta qarasa maganar tana zubawa yaya abdul ido.

Au harkin manta kenan to sai kin bani ladan tina miki yau saura wata daya da sati biyu da kwana uku. Murmushi zahra tai tare da cewa lallai kam yanzu yaya abdul harda kwanakin kake irgawa kenan, ni kam bana ma irgawa kawai shirya-shirya muke. Murmushi abdul yayi tare da cewa aa ai nida amaryar muna irgawa tinda bikin mu za'ai.

To yaya abdul allah uban giji ya nuna mana lokacin da rai da lpy. Amen hjy zahra Allah uban giji ya saukar mana dake lafiya bari na tashi dama fita zanyi me kike so yau na siyo miki?. Zahra kuwa kamar jira take tace gyad'a zaka tawomin da ita in ka ganta.

Murmushi abdul yayi tare da cewa karki damu ai ko ban ganta ba sai na lalubo miki ita baki da case, andul ya qarasa maganar yana mikewa, tom shikenan yaya abdul a dawo lpy allah ya tsare hanya, ameen my zahra ki kula da kanki sai na dawo, daga haka abdul ya wuce.

Abdul yana fita ammi tazo hannu d'auke da plate d'in abinci. Miqa mata ammi tai tare da cewa gashi nan ki cinye tass kinjia. Girgiza kai zahra tai tare da cewa bana son jin abu mai kwai yanzu gaba d'aya bana son cin abinci breakfast, baki dafa na rana bane?.

Eh na dafa tuwo mana zakici ko wani abun zan dafa miki. Ee zanci mana amma dai zuwa anjima ammi in baki gaji ba kunu da qosai nake so kimin. Tom shikenan ai kona gaji sai na dafa miki bare ma ban gaji ba, zuwa da yamma zanyi miki abinda kike bari naje na zubo miki towan. Tom ammina nagode sosai, shafa kumatun ta ammi tai tare da cewa ba godiya dai tsakanin 'yar da uwa ko.

Fatana ALLAH uban giji ya saukar minke lami lafiya kinji, bari naje na zubu miki abinci daga haka ammi ta kowa kicin hannu ta dauke da plate. Ba jimawa ta qara futo hannu dauke da plate d'in tuwan shinkafa da miyar taushe, tana qarasawa ta miqawa zahra sanan ta koma ta dauko mata rawa da lemo mai sanyi amma ba sosai ba, sanan ta dauki cup ta fuce...............

Magriba........

Misalin qarfe 5 na yamma zahra tana saukowa a hankula daga step d'in bene da qatan cikin ta, tun kafin ta qarasa saukowa ta hango dady zaune akan kujera da qur'ani a hanun sa yana karanta wa a amma ba a fili ba cikin zuciyar shi. A hankula zahra ta qarasa saukowa sanan ta nufi inda dady yake a zaune.

Tun kafin zahra ta qaraso dady ya rufe qur'ani hanun sa sannan ya ajiye a gefe fuska sake yace, mamana sannu da futowa, itama zahra fuska a sake tace yauwa dady barka da yamma. Barka dai mamana zo ki zauna kinji, a hankula zahra ta qarasa tana qoqarin zama yauwa mamana kibi a hankula sannu.

Da kyar zahra ta iya zama kamar kullum, sabida cikin nata ya tsufa sosai. Zahra tana zama dady yace yauwa mamana sannu ya jikin naki da fatan dai ba abinda yake damin ki. Uhmm dady komai lpy qafata ce de take min ciwo tai tsami sabida ban taka ba yau musamman ma 'yan yatsun kafatar, wajan hajiya kaka ma na futo zani dan ta matsamin qafar tawa tinda ammi aiki take.

To mamana sannu ai hajiya inaga tayi bacci bamu jima da sallama da itaba suka tafi ita da amir tace bacci zatai amma ni bari na matsa miki qafar kinji mamana. Kai dady zaka iya kuwa? Zahra tai tambayar tana tsare dady da ido. Dan dukan ta dady yayi kadan a kumatu da yatsa biyu tare da jan kumatun yana cewa kai wanan maman tawa mai ta d'auke ni ne? to ai ban tsofa ba sai ki bari sai na tsufa.

Dariya zahra tai tare daja baya sosai bayan taja baya can qarshe kujerar ta miqawa dad'i kunburariyar qafar ta da kyar, wash dady gashinan 'yan yatsun dai zaka fara matsamim sunfi min ciwo. Tom shikenan mamana, daga haka dady ya fara matsawa zahra yatsunqafar kamar yarda ta buqata haka yayi ta matsa mata yana matsa mata kunburarrun qafafuwan ta suna hira sama-sama.

Kafin kace kwabo yawun zahra ya tsinke sabida yarda taji part din ya karad'e da qamshin qosai, nan da nan hankalinta ya sake tashi. Dady kuwa har time din bai dena matsawa zahra qafafuwan nata ba, kuma ba lefi sun d'an sace. Zahra tana cikin yanayin sha'awar kunu da qosai ta hangi ammi ta fito daga kicin hannu riqe da plate da cup.

Wata siririyar ajiyar zuciya zahra ta saki ta had'iye tsinkake yawan ta. Baki dauke da sallah ammi ta qaraso sanan tace sanun ku kice yau dady ne yake matsa qafar. To yaza'ai tinda ba me matsawa mamana qafa ai ni sai na matsa mata, hmm gaskiya to allah ya temaka ammi ta fad'a fuska a sake sannan ta miqawa zahra plate din qosan bayan haka ta dauko qaramin table ta dorawa zahra cup din kunun.

Zahra yau qafar taki tafi ta kullum kunbura ko de haiwuwar ce tazo, ammi ta fad'a cike da zolaya, hmmm kai ammi kawai dai dan ban taka bane shi yasa, to zuwa anjima sai na rakaki ko wani ya rakaki ki taka, tom shikenan ammi. Daga haka ammi ta wuce zahra kuwa ta cigaba da cin qosan ta hankali kwance ga dady yana matsa mata kafa, ita dai kawai burun ta yanzu taji mijinta mashkhur ya iso gidan, dan wata kewar shi take kamar wanda tai shekara bata sa shi a idon taba.......

Hmmm lallai kam zahra iyayan soyayyah abinda ko jiya sai da kika gan shi.😏

Kuyi haquri kunji kwana biyu shiru ba typing ko, wlh banned WhatsApp sukai min, kuma sai cikin azumi ya bud'e shi yasa, gashi bana posting da azumu shi yasa na bari sai bayan sallah.

Amma yanzu na dawo in sha ALLAH ina nan tare da ku har sai mun sauke littafin ADALILINTA.

Mu had'e a next page


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

typing..........

*page 140*

Daga haka ammi ta wuce zahra kuwa ta cigaba da cin qosan ta hankali kwance ga dady yana matsa mata kafa, ita dai kawai burun ta yanzu taji mijinta mashkhur ya iso gidan, dan wata kewar shi take kamar wanda tai shekara bata sa shi a idon taba.........

Zahra haka tai tacin qosai tana shan kunu har sai da taji ya ishe ta sanan ta ajiye. Bayan ta ajiye kallon dady tai tare da cewa yauwa dady yanzu dai komai nml sun dena yimin zafi. Masha ALLAH ai haka ake so mamana yanzu bari na bari haka ki wuta tunda sun d'anyi miki zafin. A hankula zahra ta janye qafafuwan ta da suka d'an saki sanan ta gyara zamanta.

Da gudu ameer ya qaraso hannu riqe da leda yana zuwa ya miqawa zahra tare da cewa auntyna wai gashi, kar6a zahra tai tare da cewa injiwa?. Inji yaya abdul, tom shikenan nagode, zauna kaji qosan in ka gama sai ka kaiwa ammi kicin, sai kazo muji kayan dad'i tare koh?.

Fuska cike da farin cikin ameer yace to, zahra kuwa a hankula ta fara bud'e ledar dan ganin mene a ciki, dan tasan ba gyad'a bace ka dai a ciki, sabida taji wasu abubuwan a ciki ledar tai nauyi sosai. Bayan gyad'a a ciki harda alawar madara da aya da kwakwamiti kai abubuwa dai da yawa na maqulashe ya suyo mata.

Murmushi zahra tai a zuciyar ta tace yaya abdul kenan,

Please Login or Register in order to submit comment