Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin kamo ni a girma, ilham ta qasa maganar tana mai da kallon ta kan wayar. Tsaki zahra taja sanna tace oh sai ma kin bani umar ni, ai ba yau muku fara sharing d'in kayan ba.

Murmushi ilham tai tare da girgiza kai dan ita gani take ma bazata iya tsayawa ta tankawa zahra ba 6ata lokacin ne. A hanzarce zahra ta zaro doguwar riga sanan ta dubawa qasa ta d'auko saban pants da bireziya sababbi ilham ma bata ta6a using da suba ba ta fara qoqarin sawa.

Zahra bata sha wahalar sa breziyar ba kamar dai yadda take fama a russian lokacin da ta qara qiba. Zahra tana gama sa kayan ta dawo kusa da ilham ta zauna a hankula, sanan ta fara karanta chat d'in da suke ita da yaya ahmad. 6angaran ilham kuwa an duqufa baji ba gani dan bama tasan zahra tazo kusa da ita ba.

Zahra ji take wata nutsuwa tana zuwa mata da take karanta kalaman soyayyar ahmad da ilham yadda kasan da ita ake soyayyar sai wani faman saki murmushi take. Ahmad suna sallama da ilham, ilham ta ajiye wayar a gefe tare da lumshe ido ta bud'e. Tana bud'ewa taci karo da zahra, a gefan ta. Cikin mamaki tace kai yaushe kika zo har kika zauna ban sani ba?.

Dariya zahra tai tare da cewa! Lokacin da yace in kunyi aure zai ringa yi miki shara da wanke-wanke. Itama dariya ilham tai tare da cewa! Ah lallai kin dad'e kina karanta mana sirri kice. Murmushi zahra tai tare da cewa! Hmm duk a cikin dad'in soyayya ne yarinya wlh ba namijin da zai tsaya yi miki wanke-wanke da shara malama zama zaki ki tiqi aiki, dama shi yasa kike ALLAH-ALLAH a aurar dake ko, to in baki guntun akin gidan nan na ammi ba zakiyi na gidan miji.

Dariya ilham tai tare da cewa! Ehh naji nacan ma in nayi lada zan samu, zahra tana qoqarin yin magana taji ana knocking d'in qofa. Miqewa tai tare da cewa! Bari baje na bud'e, a hanzarce zahra ta qasa bakin qofar tana qarasawa ta murd'a key sanan ta bud'e. Ruma da rukee ta gani tsaye a bakin qofar, fuska sake zahra tace ku shigo mana ta qarasa maganar tana matsa musu.

Suna shigowa zahra ta mai da qofar ta rufe sanan tace kuzo mu zauna, ba musu suka bi bayan zahra. Sanan suka zazzauna a gefan bed kamar yadda ilham da zahra suka zauna. Wata saban gani yau kune kuka zo da daddare, ni yaushe raban dana gan ku da daddare gaskiya ban gane ba ni kenan baza ku zo waje na ba sai wajan zahra koh?.

Murmushi ruma tai tare da cewa! Ai kuwa kamar kin sani wajan naki ne baza'a zo ba yanzuma wajan zahra mukazo. Hura hanci ilham tai tare da cewa! To mara kunya, kin san dai gaba nake dake ki shiga hankalinki ko na sauke miki ya tsuna biyar a fuska ta qarasa maganar tana sakin dariyar tsokana. Tab dame kwad'o yafi gaya dududu month nawa kika bani?.

Zahra kuwa cewa tai hmm kema dai ruma kyafad'a ilham shegen son girma ne da ita. Ruma cafe zancan tai da cewa! Ehh mana kuma duk mai son girma saurin tsofa yake, yarinya kije kita son girman ki, ki rigamu tsufa kuma ki rigamu mutuwa. Dallah can duk wanda yakewa d'an uwansa fatan mutuwa shi yake fara mutuwa ilham ta fad'i hakan. Da sauri zahra ta cafe zanca da cewa! Kai dan ALLAH kuyi haquri, da cacar bakin nan ALLAH ne yasan gawar fari, muyi hirar arziki mana.

To wai ke baki yadda ba babba dad'in ta dai ga aunty rukee ita ya kamata tai mana magana tunda duk ta girme mu, ilham ta qarasa maganar tana gallawa zahra harara. Kingani zahra bana gaya miki ba kwata-kwata ilham bata son zaman lafiya, ruma ta qarasa magar itama tana hararar Ilham d'in. Hmm ai ni zan gaya miki ruma ilham tsokanar bala'i ne da ita.

Rukee ce ta cafe zancan da cewa! Dan ALLAH kuyi haquri da wanan cacar baki bata da wani amfani. Murmushi ilham tai tare da cewa! Aunty Rukee yau kece da nasiha gaskiya abin babba ne. Ruma ce tace ilham dan ALLAH kiyi haquri da zancan nan haka yanzu ma momy bata son mun fito ba sauri muke kin sai dai halinta ki bari muyi abinda ya kawo mu.

Ilham a zuciya ta cewa tai dama wanan fala'yar'iyar mata ina zata barku ku fito. A fili kuma cewa tai tom shikenan nayi shiru, mai ke tafe da ku. Kallan zahra ruma tai tare da cewa! Zahra wajanki aunty rukee tazo fa. Fuska sake zahra tace aunty rukee inajin ki mai ke tafe da ke. Fuska ba walwala rukee ta fara magana da cewa!.

Zahra dan ALLAH dan annabi ina mai neman yafiya da gafara a gareki akan a binda na ringa yi miki a baya, zagin ki da hantarar ki da baqar magana da nake miki na gane kuskure na, zahra dan ALLAH kiyi haquri wlh ba laifi na bane momy ce ta sani kuma sai yanzu naga rashin dacewar hakan, Kuma kinga abinda naga mahaifiyar bataso nima banazan so shi ba da nayi tinanin kina da wanu mugun hali ko wani hatsarin shi yasa kikaga ina miki haka.

Amma daga qarshe dana mallaki hankali na sai naga baki da wani aibu pls zahra ki yafemin duniya da lahira, in sha ALLAH daga yau ko kallan banza bazai qara had'a ni dake ba, rukee ta qarasa maganar tana riqe hanun zahra fuska sha6e-sha6e da hawaye. Nan da nan tausayin rukee ya mamaye zahra da ilham musamman ma dai zahra.

Da sauri zahra tasa hannu tana sharewa rukee hawaye sanan tace! Kiyi haquri aunty rukee ki dai na kuka ni dama can ban riqe ki a zuciya ta ba da na d'auka dai wani laifin nai miki, itama momy nasan ba haka nan ta tsane ni ba nasan da akwai wani abu da nai mata, amma aunty rukee in dai akan wanan ne ki daina kuka na yafe miki duniya da lahira, kuma da fatan zaki d'auke ni 'yar uwarki kamar dai ilham da ruma.

Ajiyar zuciya rukee tai tare da cewa! Ngd sosai da sosai zahra, kuma in sha ALLAH daga yau na d'auke ki 'yar uwa dama can ke 'yar uwata ce, kema da fatan zaki d'auke ni hakan, kuma bazaki dinga kallo na a matsayin da kike kallo na daba komai ya wuce. Murmushi zahra tai tare da rungume rukee tana cewa! In sha ALLAH aunty rukee.

Murmushi ruma tai tare da cewa! To zahra ina taya aunty rukee godiya, aunty taso mu tafi kar momy ta gane bama nan. Ke uwar azar6a6i da rawar kai bazaku tafi ba yau anan zaku kwana, ilham ta fad'a tana watsawa ruma kallon banza. Eh dama tinda kina nan hankali a kwance, sanda za'a jibgemu baki sani ba ai dole, taso-taso mu tafi aunty rukee, ruma ta fad'a tana jawo hanun rukee.

Miqewa rukee tai tare da cewa! To zahra mun tafi kin sai dai halin momy karta dake mu amma gobe zan dawo musha hira ki bani labarin 'yan rasha rukee ta qarasa maganar tana sakin murmushin. Itama zahra murmushi ta saki tare da cewa ai kuwa dai bazan so a dake ki ba, ALLAH ya kai mu gobe sai kuzo musha hira, bama labarin su ba har hoton su zan nuna miki.

Murmushi rukee tai tare da cewa! Tom ALLAH ya kaimu zahra sai da safe ilham sai da safe. Murmushi ilham tai har suna had'a baki waan cewa! ALLAH ya kaimu. Ruma kallan zahra tai tare da cewa! To aunty zahra sai da safe, ke kuma uwar san girma bazan ce miki aunty ba bare ma nai miki sai da safe na sanki da shegen kishi sai dai zuciyar ki ta buga, ruma ta qarasa maganar tana yiwa Ilham uban galo sanan ta fuce a guje dan karma taji amsar da ilham zata bata.

Itama rukee bayan ta tafi tana dariya tare da cewa! Kai wlh fad'an ku yana bani dariya sai anjima, ta qarsa maganar tana fucewa daga d'akin. Ilham kuwa cewa tai zaki zo ki same ni ne mara kunya kawai. Suna gama fita zahra tace kai wlh ilham sai suka bani tausayi, wai sabida mai momy bata son su zo nan ne?.

Ta6e baki ilham tai tare da cewa! Oho mata ai wanan matar ba dai baqin hali ba gaskiya suna qoqarin zama da ita ni yaushe raban da ammi taso hannu ta dake ni harfa na manta. Dariya zahra tai tare da cewa! Kai ilham badda qarya ke da bakyaji ai dole a dake ki. Wlh da haske nake tunda kuka tafi Russian bai fi sau biyu ammi ta dake niba.

Oho dai ai ta dake ki, eh kema ai tana dukan ki ko kin manta sanda nai miki wankan manja a kai da jikin ki, kuma nace ki kika zuba abinki har ta zane mu tare. Dariya zahra tai tare da cewa! Ai ilham ba dai sharri ba na tina lokacin. Gyara zama Ilham tai sanan tace kai wanan mata ALLAH na godema da ba itace uwata ba, da ita ce ta haife ni da ban san inda zan sa kai na ba zahra. Zahra jinjina kai tai tare da cewa! Hmm kwarama su ruma sun san uwar su nida har yanzu ban san iyaye na ba fa.

Dogwan tsaki ilham ta saki tare da cewa au ammi da dady ba iyayan ki bane koh? Ta qaras maganar tana tsare zahra da ido. Girgiza kai zahra tai tare da cewa! Aaa ni karki had'amin zance ba haka nake nufi ba ni yanzu ko iyaye na na gani ai bazan so su kamar yadda nake son ammi da dady bare ma ba ganin su zanyi ba.

Ilham cewa tai wlh zahra da dai ace irin momy ce uwata gwara ace ban ma san iyayan nawa gaba d'aya ba wanana fala'yar'iyar matar da ko fara'a batayi, ga dukan 'yaya kamar jakai. Hmm ilham banda sharri amma kinsan ina mamakin yadda yaya abdul yake da kyan hali da zuciya bai kwaso halinta ba ko guntu. Jinjina kai ilham tai tare da cewa! Ai kuwa dai amma ai dan ammi ce ta raine shi da halinta zai kwaso inaga, ko da yake ALLAH ya tsare yaya abdul d'in mu da kwasar halin ta.

Ameen dai amma ilham ai ana kwaso hali ko ta nono ne, duk da dai haka yaya abdul yana da kyan hali, ko dai ma ammi ce ta haife shi bamu sani ba. Dariya ilham tai tare da cewa! Nima haka nake cewa wataran ke shima yaya abdul, baya so a ringa cewa momy ce babar sa fa hai yanzu, ALLAH dai ya tai make shi bai kwaso fuskar shanuwar matar nan ba.

Dariya zahra tai tare da cewa! Kai ilham baki da mutunci wlh, amma ya abdul dama ai baya kama da momy wlh kamarsu d'aya da haidar da faruq musamman ma faruq kamar kara aka tsaga. Ehh mana shi yasa wasu mutanan suke yadda d'an ammi ne, amma ni yaya mashkhur ne ya d'an kwaso halin momy, da basa kamar da ammi da nace wata qila momy ce ta haifi yaya mashkhur.

Dariya zahra tai tare da cewa! Wlh kuwa dai, ke zahra amma dai yaya mashkhur kawai matsalar shi rashin son magana da rashin son mutane da shiga cikin su, amma shi ba ruwan sa wlh, ba munafiki bane kamar momy, ai wanan da halinta ya kwaso mu shinga uku. Hmm ke dai bari ilham ALLAH ya shirye momy yasa ta gane.

Ameen dai zahra, zahra cewa tai wai zahra anya momy tana son yaya abdul kuwa naga kwata-kwata basa jituwa kamar ba itace maman shi ba. Kee wlh tana son shi sosai kawai basarwa take baki ga dah in ta ganku tare yadda take wani kunbura fuska kamar bread, wlh tana son d'in ta. Hmmm ai kuwa tayi ta gama ni da yaya abdul mutuwa ce kawai zata raba mu.

Zahra ta qasa maganar tana murmushi, wata uwar dariya ilham ta saki bayan ta gama tace! Wlh kika aurar wa momy d'a sai tayi farfesun naman ki ta cinye, ubanki zaki ci gwarama ki tsaya a wajan mijin ki yaya mashkhur dan wlh ya feye miki d'an momy, dan momy bata da sauqi bata qi ta zo har gidan ku ta zane miki jiki ba,..................

Page d'in nan double ne sosai to naga dare yayi ba qarasa rubutawa ba shi yasa na yanke na turo muku iya wanan d'in amma zuwa gobe da safe ko can dare zan turo ragowar.

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Double page.

Bakin ki ya sari d'an yan kashi, koma ai yaya abdul bazai bari ta dake niba. A haukan ki ba, shima kansa bai wuce ta dake shi ba tinda uwar sace, dan ALLAH Ilham ki fad'i alkhairi ko ki shiru. Ni yanzu mubar wanan magar zahra dan ALLAH hau akan gado sosai, dan muji dad'in magana, ilham ta qasa maganar tana hawa da qafafuwan ta kan bed d'in tare da gyara zama.

Itama zahra hawa tai da qafafuwan ta fara face d'in ilham tace yauwa inajin ki fad'i karta kashe ki. Qara gyara zama ilham tai sanan tace wai zahra mene gaskiyar abinda hajiya kaka naji tana fad'a kuma kamar naga ammi tasan da zancan, cikin mamaki zahra tace wana zance?, zancan ciki da akace kina da shi mana zahra.

Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa wlh ilham bani da wani ciki a tattare dani. Da sauri ilham ta girgiza kai tare da cewa zahra kar kimin qarya yaushe kika fara 6oyemin abubuwa haka? Baki da cikin kinga yadda fatar ki tai fresh kinyi qiba kinyi kyau ana ganinki anga mai ciki amma kice min baki da ciki.

Ke ilham ki yarda dani bani da ciki wlh ko sati biyu banyi da gama jini na ba, kuma dai nasan ance mai ciki batayi koh?. Girgiza kai ilham tai tare da cewa, ana d'an samu kad'an wasu sunayi adai yadda naji kika san ko kema kina cikin su?. Tsaki zahra taja sanan tace to taya ma zan samu cikin ilham nifa yanzu yadda kike haka nake wlh har yanzu ban san waye d'a namiji ba bare ma ta kai da zancan ciki.

Tsaki ilham taja tare da miqewa tana cewa! Ke wanan qaryar taki ta ishe ni haka zahra, gwara naje na samu wani abun yi na gaji da qaryar nan wlh. Janyo hanunta zahra tai tare da cewa, ilham wlh da gaske nake miki dawo ki zauna mana. Zama ilham tai tare da cewa ko dai zahra bakyaso na tambaye ki mai ya faru a first night d'in ki ne? ni naji wlh ba sai kin gaya min ba amma ki gayamin gaskiya har yanzu kina nan a budurwar ki?.

Ilham wai sabi da mai lokaci guda kike dai na yadda dani in na gaya miki magana wlh na rantse da girma ALLAH yaya mashkhur bai ta6a wata auratayya dani ba. Shiru ilham tai tana nazari magar zahra, can kuma tace lallai yaya mashkhur ya wuce inda ake tinani zahra raban da naga mutum mai taurin kansa har na manta, kina nufin har yanzu dai bakwa jituwa.

Gyad'a kai zahra tai tare da cewa, ke ko da mukazo airport d'in garin nan sai da ya cemin banza shashasha mara kamun kai. Zaro ido ilham tai tare da cewa, kuma dai mai kikayi mai?. Wlh ilham ban sani ba amma kuma daga baya sai nai tinanin kodan yaga ni da yaya abdul munyi hugging d'in juna ne oho. Ajiyar zuciya ilham ta sauke tare da cewa, ko dai kishin ki yake kin sai dai in yaya mashkhur bai damu da kasuwa ba ko sauti baya bayarwa inaga kishi yake.

Tsaki zahra taja tare da cewa, ba wani kishi ilham kawai iskanci ne irin na yaya mashkhur. Amma zahra sai naga kamar ke da yaya mashkhur kuna boye wani abu yaya mashkhur baya so asini mai ne shi?. Cikin mamaki zahra tace mai kika gani kuwama ilham?. Dazu mana da kina qoqarin gayawa dady abinda yasa kukaqi dawowa naga yana wani kashe miki ido alamun karki fad'a.

Shiru zahra tai tana nazari can kuma tace, ilham nayi niyar gaya miki ko mene tun muna russian amma ALLAH bai nufa ba ke kad'ai zan iya gayawa sabida ba zan iya boye miki ba, amma ki bari ba yanzu ba na gaji bacci zanyi, zahra ta qarasa maganar tana miqewa tsaye. Ke ina zuwa dallah dawo ki gayamin yanzu wlh baki isa ba.

To bari nai sallah isha'i sai na gaya miki, kwanciya ilham tai tare da cewa, tom shikenan ina jira. Daga haka ilham tai male-male a kan bed tana mamakin taurin kai irin na yaya mashkhur. A ganin ta ko wana namiji da aka had'a da zahra yadda take da diri da kyau d'in nan wlh sai ya sauke makaman yaqinsa tuni zai afka mata.

Zahra tana idar da sallah ta canza globe d'in bedroom d'in daga white zuwa green sanan ta kwanta a gefan ilham. Ilham kuwa sake matsowa tai sanan tace gayamin nasha. Hmm ilham da san gulma wlh irin kune matan nan masu bin kwakwafi tsiya, da fad'in sirrin mijin su. Dariya ilham tai tare da cewa, ina zahra ai ba wanda zai ta6a jin sirrin mijina wlh.

Murmushi zahra tai tare da cewa, harda ni? Eh to kema zaki iya shiga cikin su da kyar in zan gaya miki ilham ta qarasa maganar cikin zaulaya. Oh ke bazaki iya gayamin sirrin mijin ki ba amma ke zaki titsiye ni na gaya miki sirrin nawa mijin?. Wata uwar dariya ilham ta sauke harda riqe ciki. Bayan ta gama tace wlh zahra kin bani nishad'i kuma abun ya birge ni tinda aka d'aura miki aure da yaya mashkhur ban ta6a ganin kince mijin ki ba sai yau.

Itama dariya zahra tai tare da cewa, ai kece da wani rainin hankali wlh ni ban masan na fad'a ba. Hmmm shikenan kema kinsa bazan iya 6oye abinda yake damuna ba, maza ki gayamim mene?. Gyara kwanci zahra tai tare da cewa, ina wanan zee d'in qawar yaya mashkhur?, da sauri ilham ta d'aga kai tare da cewa eh na gane ta.

Yauwa itace ta cillo ni tin daga benen sama har qasa, za bura ilham tai tare da cewa, kai yaushe. Haba ilham karki tara mana mutanr mene na firgita haka nifa amana na baki bana so ki gayawa kowa a gidan nan daga ni sai ke. Gaskiya zahra baki da hankalin yanzu wanan ne zaki iya 6oyewa ammi da dady.

Kinga irin halinki koh? Wlh bazanma cigaba da baki labari ba. Sassauta murya ilham tai tare da cewa, ya haquri ina ji. Haka zahra ta zauna ta bawa ilham labarin yadda akai tinda daga, yadda zahra ta dawo daga makaranta ta zubar da giyar har yadda akai ta cinllo ta. Cikin razani ilham tace to waye ya kai ki asibiti, bayan kince ba kowa daga ita sai ke?.

Gyara kwanciya zahra tai sanan tace wlh ilham ban sani ba sabida suma nai, daga qarshe dana farfad'o na ganni a asibiti, qafata d'aya qashinta ya goce, dan yatsan hanuna ma haka d'aya kuma ya karye ga kai na daya fashe. Nan da nan hankalin ilham ya sake tashi sai zabga salati take, cikin razani tace zahra kuma kika rayu anya wanan ba qarya kika had'amin ba.

Ban sani ba karki yadda d'in tinda na saba miki irin wanan qaryar. Ya haquri dan ALLAH wlh hankali na ya tashi sosai da sosai wau duk yaushe akai hakan?. Hmmm wlh bawani a jima ba lokacin da nai offline d'in nan ne kuka ringa toromin message, lokacin ne fa. Jinjina kai ilham tai tare da cewa, to yanzu ya akai da zee d'in girgiza kai zahra tai tare da cewa, wlh ban sani ba.

Amma ina tinanin ba abinda akayi mata, amma gaskiya dana dawo daga asibiti har na gama jinya ban sata a ido na ba. Cikin mamaki ilham tace yauwa to ya akayi batun jinya kuwa wa yayi miki jinya zahra?. Wani qasai taccan murmushi zahra ta saki tare da cewa, wa kuwa zai min in badda shi. Cikin mamaki ilham tace shi kuma shiwa?.

Da farko dai a asibi wasu likitoci mata ne suke kai ni toilet sanan suke goge min jiki, da safe kuma in su yaya mashkhur sun zo shida yaya ahmad, yaya ahmad ne yake bani abinci. Cikin mamaki ilham tace dama yaya ahmad ya son zancan amma bai ta6a gaya mim ba. Kai kema ilham in badda abinki taya zai gaya miki, ai yasan abokin sa zai jefa cikin matsala yanzu ma karki ce mai na gaya miki.

Tom shikenan bazan fad'aba cigaba da bani labarin. Murmushi zahra ta sake saki tare da cewa, to daga qarshe kuwa ranar yaya mashkhur bai zo hospital d'in ba, na sawa yaya ahmad da likitoci kuka naqi ci naqi sha, nace nifa gida nake son komawa dama sauaran ma zama haquri nai kin san dai banason zama hospital.

Ehh na sani muje sai akayi yaya to ranar dai haka na wuni baci ba sha har suka rubutamin takaddar sallama aka dawo da ni gida. Ai kuwa ranar yaya mashkhur yaji haushi sosai da sosai, zahra ta qarasa maganar tana saki dariya. Murmushi ilham tai tare da cewa, dan ALLAH ina jinki sai akayi yaya. juyawa ilham baya zahra tai tare da cewa, jinya ta da yaya mashkhur sai gobe zan baki labari na gaji.

Wani sirrin ihu ilham ta saki tare da cewa, yaya mashkhur da jinya wlh baki isa ba kin lasamin zuma a baki sanan kice sai gobe to baki isa ba wlh. Dariya zahra tare da cewa, ai kuwa an kwashi dirama a jinyar nan wlh, nima kai na wani abun na tina dariya yake bani. Wayyoo ALLAH dan annabi juyo ki gayamin 'yar uwata.

Juyowa zahra tai tare da fara bawa ilham labarin jinyar su, da irin wahalar da ta ringa bawa yaya mashkhur, har lokacin data 6ata blanket da jini a rashin sani da time d'in da ta fad'i a toilet ta saki qara mashkhur ya shigo. Zahra tana zuwa nan ilham itama ta saki siririyar qara tare da cewa wayyo haka ya shogo ya same ki ilham ta qarasa maganar tana sakin dariyar mugunta.

Ke dai bari ilham yadda kikasan qasa ta dare na shige sabida kunya, ga abin haushi yama kasa d'agani da kyar ya iya ta6a jikina jikin sa sai wani rawa-rawa yake kamar fa wata mace. Dariya ilham tai tare da cewa, ke kuwa anga abinda ba'a saba ganin ba dole ba. Ke ilham ban san iskanci fah, wlh ba wani iskanci gaskiya na fad'a kinga hakan ma ya tabbatar mana ba wani abun suke aikatawa da zee ba.

Oho su

Please Login or Register in order to submit comment