Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa komai sabida ciwo sai qaruwa yake mai makwan yayi baya.

Ammi zubawa zahra rubutun tai a cup sanan ta miqa mata. Da kayr zahra ta iya kar6a hannu na rawa ta shanye da kyar. Zahra ko wani abun yana damunki ki gayamin? Duk naga kin canza. Aa ammi ba komai kawai nace miki zafi nake jine kuma yanzu na fara jin dede. Tom shikenan bari na shiga toilet na futo.

Daga haka ammi ta wuce toilet, ammi tana shiga toilet zahra taji mararta ta sake d'aurewa tanayi mata wani azababban ciwo ba shiri zahra ta gangaro ta sauko daga bed d'in ta durqushe a qasa tana faman nunfashi. Ammi kuwa tana futowa mai zata gani gabanta ne ya fad'i rass ganin zahra durqushe riqe da cikin ta tana ta murqususu.

Da sauri ammi ta qaro tare da cewa lafiya zahra meye haka ki gayamin me yake damun ki, ammi ta qarasa maganar cikin tashin hankali. Zahra kuwa cikin azaba tace ammi marata kamar ta tsinke ta qarasa maganar tana sake riqe cikin ta.
Zahra ai naquda kikeyi amma shine tun dazu kike 6oyemin sannu bari na kira abdul mu tafi hospital.

Jiki na rawa ammi ta miqe ta d'auko wayarta hankali tashe ta lalubo number abdul dan yanzu tasan mashkhur ya tafi gida. Ammi tana kiran abdul kira uku ya d'auka baki d'auke da sallama. Ammi ko amsa sallamar batayi ba tace! Abdul kana ina ne? Ammi ina gida ko nazo?. Ee kozo mukai zahra hospital haiwuwa zatai.

Abdul ko amsawa bai bawa ammi ba ya ajiye wayar ya fuce a hanzarce, ammi taba katse wayar abdul ta bugawa dady bayan ya d'auka tace zahra ta fara naquda zamuje kai ta hospital nida abdul. Dady yana jin haka ya miqe da sauri tare da cewa! Okya nima gani nan futowa. Dady wayarsa ya zira a aljiwu tare da kallon mashkhur da yake gefansa a zaune suna tattaunawa.

Dady lafiya? Taso mu fita mamana ce take naquda. Nan da nan mashkhur ya zabura ya miqe, gabansa ya yanke ya fad'a rasss, a fili yace na shiga uku. Addu'a dai ya kamata kai mata zo mu tafi ko?
Ammi kuwa tana katse wayar ta d'auko hijab tasa a hanzarce sanan ta d'auko jakar kayan haiwuwar zahra.

Ta nufi zahra hankali tashe ta roqota ta tare da cewa sannu zahra kinji. Haka ammi da zahra suka sauka da qasan benan da kuar, adede lokacin abdul ya shigo hankali tashe, abdul yana qarasowa zahra ta riqe hanunsa tare da cewa wayyoo yaya abdul ka temake ni zan mutu, shima abdul hanun zahra ya riqe cikin tashin hankali yace sannu zahra, in sha zaki haiwu lafiya bazaki mutu ba.

Haka ammi da abdul suka qarasa fitar da zahra da kyar, zahra suna qarasawa tsakar gida ta tsuguna ta sake riqe mararta tana ta fama ash da wayyo. A dede time d'in mashkhur da dady suka qaraso suma hankali tashi. Suna qarasowa suka tuguna suna 'yar rige-rigen yiwa zahra sannu, mashkhur kuwa ya riqe zahra gam kamar zai cire mata ciwon da yake damun ta.

Dady ne yace yanzu dai ya kamata a tafi hospital kafin lamarin yayi worst, sai dai ku kawo motar nan dan bazata iya qarasawa ba da nisa. Hankali tashe abdul yace to dady bari naje na d'auko key d'in mota, na manta ban futo da shima. Da sauri mashkur ya dakatar da abdul ta hanyar cewa! bari na baka nawa key d'in. jiki na rawa mashkhur ya zira hannu a aljiwu ya zaro key d'in motar sa ya miqawa abdul.

Shima abdul da sauri ya kar6a sanan ya wuce jiki na rawa, ba 6ata lokaci ya d'auko lafiyayyiyar motar mashkhur d'in ya kawo ta inda su ammi suke tsaye hankali tashe. Yana kawo ba 6ata lokaci ammi da mashkhur suka temakawa zahra ta shiga bayan mota suka sata a tsakiya mashkhur a gefan dama ammi a na hagu, shi kuma dady a gaba abdul kuma shi ke driven, ba 6ata lokaci abdul ya fuce daga gidan a guje, ya nufi hanyar hospital mafi kusa..............

Hmmm wayyo zahra.

Me kuke ganin zahra zata haifa?.

Kuna tinanin zahra zata sauka lafiya ko akasin haka?.

Mu had'e a next page ranar monday dan jin yarda zata kaya.

Ina yi muku barka da jumma'a da fatan zamuyi wuton mako lafiya.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING..........

*Page 142*

ba 6ata lokaci abdul ya fuce daga gidan a guje, ya nufi hanyar hospital mafi kusa..............

Haka abdul yay ta sharara uban gudu har sai da ya qarasa hospital. Suna qarasawa asibiti ba 6ata lokaci aka tabbatar musu da zahra haiwuwa zatai. Dan haka a hanzarce aka shigar da ita room d'in haiwuwa. 6angaran su ammi kuwa suna zaune jigum-jigum hankali a tashe.

Mashkhur kuwa bai ma iya zaman ba yana daga tsaye ko motsi ya kasayi. tsayawama na gaya muku tashin hankalin da mashkhur ya shiga 6ata page ne, zuciyarsa cike fal da razani da tausayin zahra. Kowa da irin addu'a da yakewa zahra a zuciyarsa. Hmmm hankalin su ammi bai sake tashi ba sai sanda sukaji zahra tana kwad'a uban iwu sautin muryarta na tashi.

mashkhur da yake tsaye kuwa nan da nan tsigar jikinsa ta fara tashi ji yake kamar yabi zahra room d'in haiwuwa. Zahra kuwa sai qara kwad'a iwu take wanan karan harda sunan abdul take kira! Wayyo yaya abdul d'ina ka temake ni zan mutu yaya abdul d'ina kana ina wayyo ALLAH na kazo yaya abdul. Abdul ji yake kamar ya shiga ya temaki zahra amma ba hali, hawaye ne kawai yake zubuwa daga idanun yaya abdul.

6angaran mashkhur kuwa lokaci guda ransa ya 6ace fiye da tinani, sakamakwan yarda yaji zahra tana kiran sunan abdul sa6anin nasa. Mashkhur ji yayi bazai iya jurar jin iwun zahra ba kuma tana kiran wani bashi ba dan haka ba 6ata lokaci ya fuce daga wajan zuciya ba dad'i. Mashkhur yana fita bai tsaya ko ina ba sai wajan da suka ajiye mota.

Hannu mashkhur yasa ya bud'e mazaunin driver ba 6ata lokaci qofa ta bud'e, dama abdul bai rufe motar ba dan ko key bai zare ba, kawai kashe motar yayi. Mashkhur yana shiga ya zauna akan kujerar driver da kyar tare da kwantar da kujerar motar sosai. Bayan mashkhur ya kwantar da kujerar ajiyar zuciya ya sauke, zuciya cike da damuwa da kuma baqin ciki fall.

Babban baqin cikin mashkhur matar shi tana room d'in haiwuwa amma tana kiran wani namijin sa6anin shi. Nan da nan wani namijin kishi ya lulu6e zuciya mashkhur har lokacin muryar zahra bata dena yimai gizau ba tana iwu tana fama kiran yaya abdul. Nan da nan kwallar tausayi da kishi ta cikawa mashkhur ido.

Duk da abinda zai sa mashkhur kuka babbane to amma yau shi da kansa yake neman kukan ya zubo a idansa amma ya kasa. Mashkhur yana cikin wanan halin yaji wayar shi da take aljiwu tana ta faman ringing, hannu na rawa mashkhur ya zura hannu a aljiwu ya zaro wayar tasa. Sunan ahmad abokinsa ne ya gani 6aro-6aro akan wayar, wata siririyar ajiyar zuciya mashkhur yayi sanan ya ajiye wayar a gefe.

Haka wayar tai ta ringing harta katse amma mashkhur bai samu damar d'auka ba. da kira ya katse sai wani ya shigo har sau uku, sai a na hudun ne mashkhur ya d'auka da kyar tare dasa wayar a hands free yayi shiru yana sauraran abinda ahamd zai ce. Sallama ahmad ya farayi, mashkhur da kayar ya iya samu ya amsa sallamar.

Ah mashkhur yakake naji gaba d'aya muryaka ta canza ko wani abunne yake damun ka? Ahmad ya tambayi mashkhur cike da mamaki. Jim mashkhur yayi bai ce komai ba har sai da ahmad ya sake cewa! Hello mashkhur kanaji na kuwa. Da kyar mashkhur yace no im not fine ahmad, a d'an razane ahmad yace meke faruwa da kai mashkhur.

Lumshe jajayan idanuwansa mashkhur yayi tare da cewa! Zahra ce, abinda mashkhur ya iya fad'a kenan zuciya cike da damuwa. Adede time d'in ilham ta shigo bedroom d'in riqe da cup d'in tea a hanun ta,. Ahmad kuwa bai ankare da shigowarta Ba dan haka, hankali tashe yace! Zahra kuma mashkhur meke faruwa da zahra, ko haiwuwa zatai?.

Ilham tanajin haka ta saki cup d'in hanun ta ya fad'i qasa warwas, sanan ta qaraso bed d'in da ahamd yake zaune a hanzarce. Mashkhur da kyar ya iya bawa ahmad amsa da ee, sanan yayi reject d'in kiran, dan gaba d'aya ya fara fita daga hayyacin sa. Ilham tana qarasowa tace innalillahi hubby meke faruwa da zahra ta?.

Ilham tana fad'a a razane dan har time d'in baby cikin ta bai dena juyawa ba sabida tsabar tashin hankali. A hankula ahmad ya miqe tare da riqe ilham yana cewa! Sannu zauna ba abinda yake faruwa da ita, ilham data zauna da kyar wani kallo ta watsawa ahmad tare da cewa! Kamarya yaya ahmad ka fad'amin gaskiya mana Ilham ta qarasa maganar fuska cike da hawaye.

Ba wani mumunan abunne ya faru da itaba fa, haiwuwa zatai kinga kuwa addu'a ya kamata kiyi mata. Haiwuwa kuma d'azu fa mukayi waya da ita, kuma wana asibiti take taso mu tafi yaya ahmad dan ALLAH karkace aa. Sake riqe hannun ta ahmad yayi jiki a sanyaye yace aa ilham ki kwantar da hankalin ki yanzu fa addu'a ya kamata kiyi mata ba tashin hankali nan ba.

MASHKHUR........

Mashkhur bayan yayi reject d'in kiran ahmad, hankali tashe jiki ba kwari ya bud'e murfin motar ya fuce. Yana so ya shiga ciki amma yana tsoron halin da zai tarar da zahra, ku kuma yaji tana kiran abdul d'in nan sam zuciyar shi bazata d'auka ba. Bayan mashkhur ya qara 5 minutes a tsaye yanke shawarar gwara ya shiga ciki yayi, dan sanin a wana hali zahra take.

Da kyar mashkhur yake d'aqa qafarsa yake saukewa. Mashkhur yana qarasawa wata doctor ta qaraso tana tambayar 'yan uwa zahra. Nan gaban mashkhur ya sake yankewa ya fad'i rass, dan haka bai qarasa shigabatsayawa yayi kamar dazu zuciya tana fat-fat yana jiran yaji mae zatace. Lokaci guda kuma mashkhur ya sauke ajiyar zuciya sabida yaji tambayar kayan baby ake.

Kuma gashi sam ya dena jin kukan zahra ba kamar yarda yabarta tanayi.
Bayan ammi ta miqawa doctor jakar juyawa tai da sauri. Jim kowa yayi yana jiran futowar doctor, mashkhur de ya sake ra6ewa a qofa har lokacin hankalinsa bai kwanta ko kad'an ba. Nan da nan waje yayi tsit kowa yana jiran me zai je ya dawo.

Bayan misalin 10 minutes doctor ta futo hannu riqe da towel d'in baby fuska sake sai an murmushi take. Da sauri ta qaraso inda su ammi suke dama abdul ne a farko ta miqamai babyn tare da cewa congratulations. Hannu na rawa abdul ya qar6i babyn tare da cewa masha ALLAH me muka samu?. Bayan ta gama miqamai babyn cewa tai! An samu baby boy.

Dan haka yanzu sai a bani goran albishir d'ina. Nan da nan waje ya karad'e da hamdalah bakajin tashin komai sai hamdalah. 6angaran mashkhur kuwa hmmmmm shi kad'ai yasan yarda yake ji a zuciyar shi sabida farin ciki. Yana nan a ra6e ko kwakwaran motsi baya iyayi sai godewa ALLAH kawai a zuciya.

Abdul kuwa zaro wayarsa yayi a aljiwu domin yiwa doctor transfer. Hannu na rawa abdul ya miqawa doctor wayar tasa tare da cewa sa account number d'in ki, da sauri doctor ta qar6a tare dasa account number sanan ta miqawa abdul. Kar6a abdul yayi tare da cewa which bank?, da sauri tace access.

Nan da nan abdul yayi select bank sanan ya tura mata 200,000. Na tura abdul ya fad'a yana saukre idon sa akan babyn fake maqale a hanun sa. Thank you so much dady nogode ALLAH ya raya baby dadyn baby murmushi abdul yayi tare da cewa ameen nagode. Ammi ce tace to doctor ya jikin nata ita kuma da fatan komai lafiya.

Ah mama komai lafiya ana gama yi mata abinda ya dace zamu dawo da ita d'akin wutu to sai ku shiga ku qanta, nan bada jimawa ba za'a gamayi mata komai kuma tana ciki qoshin lafiya. A tare ammi da mashkhur suka sauke ajiyar zuciya. Doctor kuwa juyawa tai ta koma ciki zuciya cike da farin cikin kyautar da abdul yayi mata dan ita duk a tinanin ta tasha shine mahaifin yaron.

Mashkhur da kyar ya iya qarasowa sabida farin ciki jiki ba kwari ya zauna kusa da abdul zuciya cike fall da qaunar zahra. Yaron masha ALLAH kyakyawa da shi gashi babba ne, kana ganin sa zaka sheda yana cikin qoshin lafiya. Farine qall dan kumatunsa da qoshinsa hancinsa bakin sa har wani ja suke. Gashi kyakyawa ajin farko kamar sa d'aya da mashkhur.

Kamar mashkhur yayi kaki ya ajiye, amma babyn harma yafi mashkhur kyau idonsa har lokacin a rufe yake bai bud'e ba yana sauke nunfashi a hankula tare da motasa 'yan yatsun hannayan sa da suka sha safar hannu. Hmmm abdul kenan ka kasa ka tsare bazaka barmu mu d'auke shi musa mai albarka ba kenan? ammi ta qarasa maganar fuska d'auke da murmushi.

Hmmm ammi nifa ban gaji da d'aukar shiba ku bari sai na gaji tukunna sai na baku, murmushi ammi da dady sukai, ammi tace tom shikenan amma kaje ka duba motar daga baya akwai zamzam da dabinu a wata farar leda ka d'auko a bashi kaji. Miqawa ammi babyn abdul yayi badan yaso ba sanan ya miqewa yace tom bari naje. A hanzarce abdul ya fita zuciya cike da farin ciki dan shi gani yake kamar shi zahra ta haifawa babyn ba mashkhur ba.

Abdul sai da ya qarasa ya bud'e murfin motar sanan ya tina bai kai da cire key d'in motar ba a jiki ya barshi. Gyara kujerar da mashkhur ya kwanta yayi sanan ya bud'e gidan baya ya d'auko ledar zamzam da dabinan. Sannan ya rufe qofar bayan ya zagayo mazaunin driver ya bud'e domin cire key d'in. Bayan abdul ya cire yana qoqarin rufe qofar yaji ringing d'in wayar mashkhur.

Da sauri ya koma tare da ciro wayar ya zuba mata ido yana kallon mai kira. Sunan ahmad abdul ya gani dan haka rufe murfin motar yayi sanan ya d'auki wayar tare da karawa a kunnan sa baki d'auke da sallama. Bayan ahmad ya amsa sallamar cewa yayi mashkhur ya jikin zahra ta haiwu ko kuwa?.

Murmushi abdul yayi tare da cewa ba shi bane abdul ne yabar wayar mota ne, amma zahra ta haiwuwa lafiya qalau. Da sauqi ilham da take gefan ahmad tana ji, ta kar6i wayar cike da zumun farin ciki tace hello yaya abdul da gaske zahra ta haiwu to mai ta haifa?. Ilham zahra ta haiwuwa mana, namiji ta haifa kyakyawa mai kama da ke.

Murmushi ilham tai sanan tace yauwa alhamdulillah, yanzu zanzo naga babyn kuna wana hospital ne?. Ke ilham dare yayi fa yanzu wajan dayan dare ta kusa ki bari zuwa gobe tinda kema kinga baki da ishanshan lafiya koh?.
Hmmm nifa gaskiya bazan iya jira ba yaya abdul na matsu, aa ki bari sai gobe mana kamar yanzu ne lokaci zai yi kinga yanzu kika zo ammi zatai miki fad'a ma tace kin fito da daddare.

Jiki a sanyaye cikin rashin jin dad'i ilham tace tom shikenan yaya abdul ALLAH ya kaimu goben amma ka d'aukar min hoto da video babyn nawa ka turomin ta WhatsApp na gani kafin goban. Tom shikenan ilham baki da damu ki kwantar da hankalin zan turo miki yanzu in sha ALLAH, tom yaya abdul ina jira, daga haka ilham da abdul sukai sallama.

Bayan sunyi sallama, da sauqi abdul ya qarasa ciki, yana qarasawa ya miqawa ammi ledar sanan ya zauna a wajan da ya tashi. Bayan ya zauna miqawa mashkhur wayar tashi yayi tare da cewa gashi ka barta mota. Hannu mashkhur yasa ya qar6a tare da cewa okay. 6angaran ammi kuwa bud'e ledar tai ta fara bawa babyn zamzam a hankula.

Ba lefi ya sha ruwan zamzam d'in sosai kamar ba saban haiwuwa ba. Bayan ya sha ammi ta tauna dabinan a bakinta sosai sanan tasa mai a bakin sa. A hankula babyn zahra ya bara tsotsar dabinun a hankula, abunde gwanin ban sha'awa. Daga haka ammi miqawa dady babyn tai zuciya cike da qaunar jikin nata.

Dady fuska a sake cikin farin ciki ya kar6i babyn, har lokacin babyn bai bud'e idansa ba ya rufe gam kamar mai bacci amma sai dai ba baccin yake ba sabida har lokacin bakin sa bai dena motsi ba alamun yana tsotsar dabinan da aka bashi. Dady yana qarbarshi sunkuyar da kan sa dai-dai kunan babyn yayi sanan ya fara yimai kiran sallah a kunanshi.

Bayan dady ya gama yimai d'ayan kunnan nasa ya juya yayi, bayan dady ya gama zubawa babyn ido yay, lokaci guda yaji son jikin nasa ya shigar mai zuciya, dama gashi babyn da shiga rai. Bayan dady ya gama d'aukar shi miqawa ammi yayi, ammi kuma ta miqawa abdul, abdul kuma ya miqawa mashkhur wanda yayi tsit kamar baya wajan, ya wani dake ya basar kamar ba shi akayiwa haiwuwar ba.

Alhalin a zuciyar shi yafi kowa farin ci da samun babyn kawai dai yana yiwa su ammi da dady kara ne. Hannu mashkhur yasa ya d'auki kyakyawan babyn nasa tare da zubamai idanuwa. A dede lokacin babyn ya bud'e idanunsa tasss sukai 4 eyes da mashkhur yaro dai kamar yasan yazo hanun uban sa, kallin kallon mashkhur da baby suka fara. lokaci guda so qauna bege yaron ya cikawa mashkhur zuciya.

Ah inyeee yaya mashkhur an zama dady congratulations 🎆 ALLAH ya raya.

Mu had'e a next page.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING..........

*Page 143*

A dede lokacin babyn ya bud'e idanunsa tasss sukai 4 eyes da mashkhur yaro dai kamar yasan yazo hanun uban sa, kallin kallon mashkhur da baby suka fara. lokaci guda so qauna bege yaron ya cikawa mashkhur zuciya.

Haka mashkhur ya zubawa babyn ido ya kasa ko qiftawa shima babyn sai kallon mashkhur d'in hake tayi kamar ya san shi. abdul kuwa daga gefe yana ta d'aukan babyn sabida ya turawa ilham ko hankalinta ya kwanta. Haka dai mashkhur ya bawa abdul babyn badan yaso ba kawai dai sabida yanajin nauyi su ammi.

To misalin wajan 20 minutes doctor ta dawo ta shedawa su ammi an kai zahra d'akin wuto zasu iya zuwa su ganta. Kafin kace kwabo gaba d'aya kowa ya miqe yabi bayan doctor domin ta nuna musu d'akin wuto. Suna qarasawa bayan doctor ta nuna musu room d'in zahra, mashkhur ne ya fara shiga a hanzarce daga mashkhur sai ammi sai abdul dake riqe da baby.

Sanan dady yabi bayan su daga qarshe, suna shiga suka nufi zahra da take kwance hanun ta jone da ledar ruwa, nan da nan suka farayiwa zahra 'yar rige-rigen sannu. Zahra kuwa da bata cikin hayyacin ta da kyar ta iya d'ago idanu ta kalli su sau d'aya sanan ta mai da ido ta rufe ba jimawa bacci mai nauyi yayi awan gaba da zahra.

Haka kowa ya samu waje ya zauna, mashkhur kuwa sai bin zahra da ido yake kamar zai cinye ta shi kad'ai yasan halin da yake ciki na farin ciki da tausayawa zahra. Abdul kuwa miqawa ammi babyn yayi sabida ya fara kuka, haka ammi tai ta rarrashin shi har shima bacci ya d'auke shi. Bayan sun kai wajan 20 minutes da zama, dady ne yace to yanzu ya kamata mu koma gida tinda munga halin da take ciki ko.

Ammi cafe zance da! Gaskiya kam dan dare yayi abdul qarfe nawa? Abdul zaro wayar shi yayi a aljiwu ya duba sanan yace qarfe daya da minti goma. Okay yanzu sai ku tashi ku tafi, amma abdul in ka koma zaka dawo ka d'aukowa zahra blanket mai kauri sabida naga kamar tanajin sanyi. Sanan ka d'auko mata tea da bread sabida nasan in ta tashi zata ji yunwa.

Tom ammi abdul ya amsa cikin ladabi, yauwa sanan kuma ka d'aukomin wayata akan gado ka mai da ameer wajan su haidar ya kwanta. Tom shikenan ammi, abdul ya fad'a tare da miqewa, shima dady miqewa yayi suka fuce. Ammi kallon mashkhur tai tare da cewa kai kuma fa naga ka zauna.

Ee anan zan zauna, aa ka tashi ka bisu ka koma gida ka kwanta zuwa gobe ka dawo. Mashkhur bai so tafiya ba amma baya son musu da ammi dole shima haka ya miqe zuciya cike fall da kewar zahra ya fuce. Bayan sun fita ammi gyara zama tai hanun riqe da babyn mashkhur tana qare mai kallo, tana ganin yarda yake kama da mashkhur da kuma Ilham.

Bayan abdul ya qarasa dasu gida, mashkhur ba 6ata time suna fita ya koma mazaunin driver ya bud'e ya shige sanan ya fuce daga gidan ya wuce nasa. Bayan ya qarasa yana shiga yayi parking d'in motar sanan ya shige ciki da sauri. Yana shiga ya ajiye mukullin motar shi da wayar shi sanan ya cire a gogan sa ya ajiye a bed sad sanan ya raqe kayan sa ya wuce toilet domin wanka..........

ABDUL.........

Abdul ya d'auki wajan 40 minutes sanan ya koma asibiti. Baki d'auke da sallama ya shiga ammi da take zaune riqe da baby a hanun ta amsa mai tai tare da cewa! Yauwa abdul har ka dawo sannu fa, yauwa ammi abdul ya fad'a tare da dire ledar blanket d'in da basket d'in kayan tea d'in da bread a qasa.

Bayan ya ajiye hannu ya zura a aljiwu sanan ya zaro wayar ammi ya miqa mata. Ammi kar6a tai tare da cewa yauwa sannu fa,. Daga haka abdul yasa hannu ya d'auki babyn da yake kwance a cinyar ammi sabida sam baya gajiya da gani ko d'aukar babyn. Ammi miqewa tai ta bud'e ledar bayan blanket harda dadduma abdul ya d'auko mata.

Yauwa abdul kaga kuwa sam na manta bance ka d'aukomin harda dadduma ba, gashi kuma ka d'auko. Murmushi abdul yayi idon sa akan baby yace ee ai nasan zaki biqace ta wajan sallah asuba. Tom na gode ammi ta qare maganar tana ciro blanket, bayan ta ciro rufe zahra tai sanan ta dawo ta zauna.

Miqewa abdul yayi sanan ya miqawa ammi babyn tare da cewa to ammi bari na tafi gida dan naga har 2 tayi. Tom shikenan abdul ALLAH ya kiyaye hanya ka kula sosai banda gudu. Murmushi abdul yayi tare da cewa to ammi ta in sha ALLAH, ai na riqe wanan nasihar taki ko da rana ma bakya so ai driven da gudu bare da daddare in sha ALLAH bazanyi gudu ba zan tafi a hankula yarda kike so.

Itama ammi murmushi tai tare da cewa to yaran kirki sai da safe ka kula da kanka sosai, tom ammi na kema haka ina qaunarki, daga haka ammi sukai sallam da abdul zuciyoyin su cike da qaunar junan su, irin sanan nan na son and mother.

Hmmm ni kuwa amima nace ko ina momy maman abdul take? Inaga fa abdul ya manta da ita koh?. 🤔

Bayan fitar abdul da muntina kad'an, ammi miqawa tai ta kwanta da babyn kusa da zahra ta sake rufe su sanan ta shiga toilet ta d'auro alwala domin tai sallah ta godewa uban giji da ya sauki zahra lafiya qalau, bayan ammi ta gama godewa uban giji ta fara addu'a Allah ya sauki ilham itama lafiya ita da ruma 'yar gidan momy.

Haka dai ammi tai ta yiwa yaranta addu'a kala-kala, dama ita uwa ta gari kullum a cikin addu'a takewa yaran ta. ALLAH dai ya sakawa iyayan mu da gidan aljannah.
Bayan ammi ta idar da sallah wajan qarfe uku dare ta koma gadon da aka tanada domin mai jinya ta kwanta ba jimawa itama bacci ya d'auke ta.

ASUBAYI.

Kiran sallah asubar fari ne ya tashi ammi daga gajeran baccin da ta tafi. Bayan ta tashi ta shiga toilet tai alwala sanan ta futo ta zira hijab ta zauna akan dadduma, tana jiran lokacin sallah yayi,. Wayarta ammi ta

Please Login or Register in order to submit comment