Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya munzguna mata ba. Jinjina kai tayi tare da furta ALLAH Ya fika, na dogara da ALLAH da manzansa dan haka ba abinda ka isa kai min.
Daga haka zahra ta fara salati, haka dai bacci mai nauyi ya kwasheta.............

MASHKHUR.....

Yana shiga d'aki ya kure a. c wani baqin ciki ne yaake tur niqe shi duk sanda ya d'ora idonsa akan zahra kuma ya tina matar sace. Kayan jikinsa ya fara ragewa sabida tsabar zafin da yake ji har kwakwalwarsa da zuciyarsa yake jin zafin, daga shi sai boxser ya kwanta ko riga babu duk sanyi da akeyi a garin sam bayaji sabida tsabar 6acin rai. Tinani mashkhur ya fara taya zai dai na abubawan da dady yace masa?. Sam bazai iya dai na shaye-shaye ba sabida mashkhur in dai bai sha kayan maye ba sam bayajin dad'in rayuwarsa ji yake kmar ya mutu abinka da aikin sihiri da sammu.

Kuma sam mashkhur bayajin zai iya rabuwa da zee a rayuwarsa duk da kuwa basanta yake ba, kawai dai dan itace mace ta farko wanda ya fara bawa dama ta shigo rayuwarsa. Dama mashkhur haka yake kafin mutum ya shigo rayuwarsa da wuya amma koya mutum ya shigo rayuwarsa ko wata ma'a mala ta daban, mai qarfi ta shiga tsakaninsu tofah tabbas da wuya ya iya rabuwa da kai. Haka dai mashkhur yay ta juyi akan bed har bacci yayi awan gaba da shi...

Kiran sallar asubar farine ya tashe shi duk da kuwa bai samu wani ishashan bacci ba, idon sa sai lumshewa yake, haka dai ya tashi ya d'aura alwala ya nufi masallaci. Bayan ya idar da sallar ya dawo gida ya koma bacci...

ZAHRA......

Da kyar ta iya farkawa sakamakwan kiran sallar da taji da yake masllacin bashi da nisa da Gidan. Jikinta duk yayi tsami, da kyar ta iya miqewa ta d'auro alwala, tana d'aura alwalar, taji bacci gaba d'aya ya saketa. Dadduma ta shifid'a ta fara gabatar da sallar asuba, tana idarwa ta fara lazimi, bayan ta gama lazimi ta fara azikat d'in safiya. Misalim qarfe shida na safiya zahra ta kammala azkar d'in ta tass, sanan ta miqe ta nad'e dadumar ta mayar, sanan ta koma bacci......

Cikin bacci Sama-sama yake jin qararawar biga gidan tana qara, daga qarshe kuma yaji an dai na danna qararawar ana bugu mai sauti. Hakan ne yasa ya farka firgigit daga bacci, tinani ya farayi waye haka da safiyar nan yake bugu ko dai ahmad ne?. D'aga kai yayi ya kalli agogwan bedroom d'in qarfe goma na safe, shi bai masan lokaci yaja haka ba. Miqewa yayi ya fara qoqarin zura jallabiya da yake boxser ne kawai a jikin sa da singlet.

6angaran zahra kuwa tana cikin bacci ta fara jin bugun, da batayi niyar bud'ewa ba, amma dataji bugun yayi yawa sai tayi tinanin koh mashkhur ne ya fita ya dawo?, gabanta ne ya fad'i tana ayyanawa a ranta in dai mashkhur ne yake bugun nan ta shiga uku. Da sauri ta miqe ta d'auki hijab d'in ta har qasa ta zura tare da kama hanyar fucewa daga bedroom d'in a hanzarce. Tana fita bata tsaya ko ina ba sai a bakin qofar, hannu na rawa ta fara qoqarin bud'e qofar.

A dai-dai lokacin mashkhur ya futo daga bedroom shima ya nufo falon domin bud'e qofar, amma sai ya hangi zahra ta qoqarin bud'ewa, sam zahra bataji motsin futuwar mashkhur da yake a tsure take, duk ta bayar shi yake buqa qofar. A hanzarce zahra ta qarasa bud'e qofar tare da wangale ta sanan tai baya da sauri a tsorace, kartaje mashkhur ya zuba mata mari tana bud'ewa. Mamaki ne ya bayyana a kan fuskar zahra qarara saka makwan abinda ta gani a bakin qofar, sakin baki zahra tai tana kallan bakin qofar.

Wata doguwar maca ce jiki sanye da riga da wando, wandan jeans ne ya kama jikinta sosai da kuma farar riga da dai-dai ugunta ta tsaya mai gajeran hannu a jiki an rubuta i miss you, da manyan baqi. Siririyace sosai kamar ka hure ta fad'i, ita ba faraba kuma ba baqaba, ga shinta yana da tsayi sosai irin na turawa fararan fata tayi fakin d'insa a tsakiyar kan ta. Ba laifi tana da kyau kana ganinta zakasan bata yau bace duk da kuwa bata da girman jiki. Ta saqalo back d'inta a hannu, d'ayan hanun kuma wata ledace wanda zahra batasan mene a ciki ba.

Muryar matar ce ta dawo da zahra daga tinanin data tafi, a stawace matar ta cewa zahra!! HOW? fuska a d'aure. Firgigit zahra ta dawo daga tinanin da ta tafi, wani mugun kallo matar take watsawa zahra tana wani zazzaro mata ido kamar zata cinye ta. Nan da nan zahra ta fara rawar baki tama rasa mai zatace mata. Muryar mashkhur zahra taji a bayanta yana cewa your welcome my ZEE Come in wato (barka da zuwa zee d'i ta, shigo ciki) yamutsa fuska tayi wanda ya kira da zee tare da cewa, no.

Zaro ido waje mashkhur yayi tare da cewa because of what? Wato (sabida mai) ya watsa mata tambayar yana tsare ta da ido . Honey who is she, wato (zuma wace wanan?) zee ta tambayi mashkhur cikin tuhuma. Oho Don't mind just come in, (oho karki damu shigo kawai) noqe qafad'a zee tai no start explain me, wato (aa sai kayimin bayani) . Had'e rai mashkhur yayi sosai, zee tana ganin hakan tai sauri ta shigo tare da furta sorry my honey.

Zahra kuwa 'yar kallo ta koma bawai dan batajin abinda sukecewa ba, aaa tsaf taji abinda sukecewa, kawai dai mamki take dama mashkhur ya san wanan?, kuma mene halaqarsu? Ita dai zahra yanda tasan mashkhur tasan tsam bayasan ma'a mala da mutane barema maca da ko hanya bayaso su had'a, amma sai gashi yau ta ganshi tare da wata, kuma da alamu sunsan juna sosai.

Juyawa mashkhur yayi ya nufi kujera, itama zee binsa tai, yana zama itama ta fara qoqarin zama a kusa da shi, tana zama a kusa da shi tace honey see, ta fad'a tana nunamai rigarta. Kallo d'aya mashkhur yayi ya janye idonsa daga rigar tare da cewa I see. Ba komai zee take nuna mai face rubutun I miss you da yake jikin rigar. Honey kai bakayi missing d'ina ba shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba, sabida harga ALLAH bai yi Missing d'in zee d'in ba, sabida Ta takurarta, shiyasama bai bata amsaba, sabida baya son yi mata qarya.

Matsowa zee tayi gab da mashkhur din zata kwanta a kafad'ar shi. Da sauri mashkhur ya matsa tare da cewa no zee I don't take theses. Da sauri zee ta matsa tare da furta sorry my honey. Amma honey wanan wace tayi maga ta nuni da zahra da take tsaye a gefen qofa tana kalan ikwan Allah. Cikin harshan turanci take tambayarsa?, shiru mashkhur yayi can kuma yace wai mene damuwarki da ita ne, ya fad'a shima cikin yaran English.

Sosai zee ta had'e rai kamar zatai kuka, tace honey ka gayamin gaskiya ko dai matarka ce? Ko kuma budurwar?. Da sauri mashkhur ya watsawa zee kallan banza tare da cewa, MAI ZANYI DA WANNA aa karki qara ce mata matata, ba matata bace, kuma ba budurwata bace. Duk da English suke maganar amma hakan bai hana zahra jin abinda sukecewaba da yake itama ta iya turancin sosai. Lokaci da zahra taji mashkhur ya ce mai zaiyi da ita hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba duk da kuwa zahra bata qaunar mashkhur, amma baji dad'in hakan da ya fad'a ba.

Murmushi zee ta saki sabida abinda mashkhur ya gaya mata tasan mashkhur bai fiya yin qarya ba dan haka ta yarda zahra ba matarsa bace. To my honey wace?, it's my si!! si!! Oho it's my HOUSE GIRL. Jinjina kai zee tai tana mamakin abinda mashkhur ya gaya mata wai zahra 'yar aiki kin gidan sace, Sam zee bataga zahra tai mata kama da 'yar aiki ba. Zahra da take gefe kuwa shiru tai dan tama dai na jin haushin abibdda mashkhur yake fad'a, sabida inda sabo ai ta saba da rashin mutuncin sa.

Amma honey kyakyawace fa batayi kama da 'yar aiki ba, duk cikin yaran English suke maganar. Ok baki yarda dani ba kenan? Aaa honey na yarda da kai fiye da kai na ta qarasa maganar fuska d'auke da murmushi. Yauwa honey bari na baka kayan da kace na tawoma da shi ko? Da sauri mashkhur ya dakatar da ita da cewa aa zee ina zuwa. Mashkhur Mai da kallansa kan zahra yayi tare da cewa, fita kibar gidan nan yanzu. Ba musu zahra ta fice tabar musu wajan.

Zee kuwa kallan mashkhur take ciki da sha'awa dan yana birgeta sosai in dai taji yayi Hausa. Honey yaushe zaka koyamin yaran nan?, girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa bazan iya koya miki ba?, kai honey sabida mai?, cikin qosawa yace sabida ba aikina bane. Jinjina kai zee tai tana jin haushin wannan shariya da rashin kulawar da mashkhur yake nuna mata. Daga haka zee ta futowa da mashkhur da kayan mayen da tazo mai, da shi....

6angaran zahra kuwa tana fita, ta fara sauka daga kan step d'in benan, sai da tazo matatakala ta biyun qarshe ta zauna zuciya ciki da qonci, bawai dan mashkhur yana kula zee ba aa kawai dai yunwa takeji kuma gashi ko wanka batayi ba, ga cin mutuncin da yayi mata a gaba zee. Kifa kanta tai a guwarta, tana kewar su dady da ammi musamman ma ilham da amir da kuma yaya abdul d'innta. Ji take kamar ta rufe ido ta bud'e ta ganta a gida Nigeria. Kamar daga sama zahra taji ana cewa amarya bata lefi kota kasha d'an masu gida..................

Kwana biyu kunga bana yi muku posting ko? Dan Allah kuyi ha quri walahi bana hawa online d'in ne shiyasa, sabida wayata ta samu matsala, amma in sha ALLAH yanzu zan cigaba da yi muku posting kullum banda weekend dama kunsan bana yi muku posting weekend ranar hutu ce........


ADALILINT 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

MY NUMBER 09162226240

Typing............

*Page 53*

Ji take kamar ta rufe ido ta bud'e ta ganta a gida Nigeria. Kamar daga sama zahra taji ana cewa amarya bata lefi kota kasha d'an masu gida.

Da sauri zahra ta d'ago dan ganin wake mata magana, Ahmad ne abokin mashkhur fuska d'auke da murmushi. Da sauri zahra ta ce ina kwana antashi lafiya?. Lafiya qalau amarya kema da fatan kin tashi lpy? Gyad'a kai zahra tayi alamun ehh. Kallanta Ahmad yayi tare da cewa amarya lafiya na ganki da sanyi safiyar nan kin futo ina kika baro angon naki?. Shiru zahra tai ba amsa! Ahamd qarawa yayi da cewa koh dai wani abun ne ya faru?

Girgiza kai zahra tayi tare da cewa ba komai kawai dai na futo shan iska ne. Okay taso mu koma ciki, shiru zahra tayi ba amsa, tsugunawa Ahmad yayi kusa da ita tare da cewa, haba amrya ki taso mu shiga ciki. Murya a sanyaye zahra tace banason sunan dan Allah ka dai na cemin haka? Murmushi Ahmad yayi tare da cewa tom shikenan qanwata, wanan sunan yayi koh? Da sauri zahra ta d'aga kai alamun ehh. Taso mu shiga ciki qanwata bai kamata ki zauna a nan ba.

Girgiza kai zahra tayi tare da cewa shi yace na fita fah, cikin mamaki ahmad yace shi yace ki fita kuma? Gyad'a kai zahra tayi alamun ehh. Sabida mai ya koreki ko wani laifin kikayi mai ne? Aaa ba laifi nayi mai ba BAQUWA yayi shi yasa yace na fita. Shiru Ahmad yayi dan ko ba'a gaya mai ba yasan zee ce tazo. Kallan zahra yayi ya tausaya mata sosai ace qaramar yarinya kamar zahra ta fad'a tarkwan mashkhur mai wuyar sha'ani. Kiyi haquri kinji qanwata dama haka mashkhur yake yana da wuyar sha'ani.

Murmushi takaici zahra tayi tare da cewa ba komai ai inda sabo na saba. Mamaki ne ya kama Ahmad da yaji abinda zahra tace wai inda sabo ta sata, taya akai ta saba ko dai tasan mashkhur ne tun farko?. Kawar da zancan Ahmad yayi da cewa tom shikenan qanwata yanzu mai kike buqata na kawo miki? Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa ni bana buqatar komai, kawai dai so nake na tai makamin ka kiramin dadyna na gaisa da shi, da kuma sauran 'yan uwana.

Tom shikenan ya fada yana zaro wayarsa daga al jihu, kin riqe number dadyn naki koh? Da sauri zahra tace eh nariqe. Miqa mata wayar Ahmad yayi tare da cewa tom shikenan zaka number sai mu kira shi, cikin farin ciki zahra ta miqa hannu sanan ta fara sa number. Lokacin da zahra ta gama rubuta number dadyn, number taga anyi save da dadyn mashkhur, miqa masa wayar tayi tare da cewa a shema kana da number.

Mamaki ne ya kama Ahmad shida yasan wanan number ta dadyn mashkhur ne, amma sai gashi itama zahra tace number dadyn tace. Ahmad yana son tambayar zahra amma sabida karta yi tinanin ya cika kwakwafi shiya yayi shiru ya dannawa number dady kiran, amma sai dai kash number dadyn a kashe take. Kallan zahra ahmad yayi yace qanwata wayar dady a kashe take sai dai zuwa anjima.

Jiki a sanyaye zahra tace tom amma ka bigawa yayana, sai mu gaisa. Ba musu Ahmad ya miqawa zahra wayar ta fara sa number yaya abdul, ai kuwa akaci sa'a kiran ya shiga, amma sai ringing take ba'a d'agaba. Zahra kuwa harma ta cire rai dan wayar ma ta kusa tsinkewa, tana gab da tsinkewa yaya abdul ya d'aga cikin muryar bacci yace hello. Wani siriri ihun farin ciki zahra ta saki tare da cewa, yaya abdul d'ina na, nice.

Abdul kuwa yanajin muryar zahra ya watsake daga bacci gaba d'aya, cikin zumud'i yace babyn abdul kece, nice mana yaya abdul na kira wayar dady a kashe, shine na kira wayar ka. Ehh dady bacci yake sabida yanzu kinga anan dare yayi sosai, kuma jirginmu bai dad'e da sauka ba. Au yaya abdul nan dare ne, kaga nan kuma ranace amma ina amir d'ina yake nayi kewarsa sosai, amir yana nan ammi tace kullum sai yayi kuka wai a kai shi wajan aunty zahra.

Allah sarki my amir, zahra ta fad'a murya a sanyaye kamar zatai kuka, abdul kuwa cewa yayi ki bari zuwa gobe da safe zamuyi waysa sai na baki ku maga da shi. Tom shikenan yaya abdul, yauwa zahra da fatan dai yaya mashkhur baya dukanki koh? Ehh yaya abdul baya dukana! Ah babyna ki gayamin gaskiya, wlh yaya abdul tinda mukaso bai dake niba, yauwa baby haka nake son jin to ALLAH ya sake had'a kanku, shiru zahra tayi batace ameen ba. 6anran abdul kuwa cewa yayi to shikenan my beb ki kula da kanki sai da safe bacci nake ji, murmushi zahra tayi tare da cewa okay yayana by take care too, daga haka ta katse wayar.


Ahmad kuwa ya tafi duniyar tinanin magaganin da yaji zahra tana yi da abdul da yake wayar a hans free take. Wai mene dangatakar zahra da su mashkhur? Kuma waca irin halaqace take tsakaninta da abdul, har yake ce mata babayn sa? Anya zahra ba 'yar uwar su mashkhur bace?, duk amso shin nan ba mai bawa Ahmad amsa, shide an barshi a ciki duwo kawai. Muryar zahra ce ta dawo da shi daga duniyar tinanin da ya tafi!! Yaya ahmad ga wayar na gama.

Da sauri ya kalli zahra tare da cewa, yauwa qanwata taso mu shiga ciki koh?, girgiza kai zahra tayi tare da cewa, aa yanzu na shiga wani laifin zanyi. Miqewa Ahmad yayi tare da cewa, karki damu ba abinda zai miki ai ni nace ki shigo tawo muje yana gama fad'ar haka ya wuce kan step. Itama zahra bin bayansa tayi zuciya cike da zullumi, ahmad yana qarasawa ya tura qofar anci sa'a qofar a bud'e take basu sa mata key, tura kai ahmad yayi tare da cewa, qanwata shigo.

Haka itam zahra ta tura kai tabi bayan ahmad. Suna shiga suka samu mashkhur akan kujera ga kodin da kwayoyi baje akan table d'in kusa da shi, da alamuma yasha yayi nak, ita kuma zee tana kan carpet tana danna wayarta. Zahra kuwa ba qaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin mashkhur da kayan maye a gabansa. Dama yaya mashkhur yana shaye-shaye, ko a wani ne yazo ya gaya mata hakan baza ta ta6a yarda ba sai gashi ta gani da idon ta.

Muryar Ahmad ce ta katse zahra daga dogwan tinanin data tafi, qanwata shiga ki zauna bari nayi miki oder abinci mai kike son ci?. Karaf muryar mashkhur ta qare de falon da cewa karka sake kayi mata wata oder abinci sai dai ta dafa da kanta, a zuciye Ahmad yace sabida mai zakace bazan mata oder abinci ba, ai ba dole bane sai ta dafa koh?. Cikin muryar isasu mashkhur yace sabida banga dama ta ciba ba dan haka bazata ciba, kuma wlh ka sake ka kawo mata abincin nan bazata ciba kuma sai jikinta ya gaya mata.

Da sauri zahra ta katse maganar da cewa yaya ahmad dan Allah kabar shi ni zan dafa da kai na, na iya dafawa. Shiru Ahmad yayi dabadan yasan zai jawowa zahra matsala a wajan mashkhur ba sai ya yiwa zahra oder abinci. Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa, okay ba damuwa yanda kikace, gobe qarfe bakwai na safe ki shirin makaranta ya zan kai ki makaranta ya qarasa magana yana watsawa zee harara wanda ta zuba musu ido tana kallan su kamar wata tsowuwar mayya!! Tom shikenan yaya ahmad ALLAH ya kaimu nagode.

Daga haka ahmad bai sake cewa komai ba ya fuce zuciya ciki da haushin mashkhur. Zahra kuwa tafiya ta farayi kamar wanda bata san taka qasa, sam zahra bataji dad'in kayan mayan da mashkhur yasha ba, duk sai taji jikinta yayi sanyi. Harta kusan shiga bedroom taji muryar zee tace house girl come here? Tsayawa zahra tayi qeqam tana tinani mai zataiwa zee?. Muryar mashkhur ce ta daki kunanta yana cewa!! Ke ba kiranki ake ba, ba musu zahra ta qarasa inda zee take. Cikin English zee tace jeki ki dafamin coffee?.

Tin kafin zahra tayi wani kwakwaran motsi taji mashkhur yace, ke ki bud'e kunanki kiji da kyau kashedi na qarshe zan miki! Duk abinda tace kiyi mata to kiyi mata In ba haka ba sai jikinki ya gaya miki, daga yanzu bazan sake yi miki magana ba sai dai jikinki ya gaya miki, dan ni bazan d'auki iskancin kiba ya qarasa maganar fuska tamke. Jiki na sassarfa zahra ta shiga kicin d'in. Sai da ta fara dafa indomei taci, sanan Ta had'awa zee coffee. Sanan ta wuce fallon domin kai matawa zee coffee d'in.

Tana isa ta ajiye coffee d'in ta juya zata wuce karaf indonta ya sauka akan qafar zee duk tasha sarqoqin qafa. Nan da nan zahra ta tuno watarana da ta ta6a cewa ammi ta siyo mata sarqar qafa, ammi tace aa bazata siyo mata ba sai zahra ta tambayi ammi sabidame?. Ammi kuwa cewa zahra tai sabida 'yan lesbian ne suke yawan sata ko karuwai. Zahra kuwa cewa ammi tai ammi mene lesbian kuma? Ammi kuwa cewa zahra tai iskanci mace da mace, cikin mamaki zahra tace ammi dama ana iskanci mace da mace?.

ammi amsawa tai da cewa ehh anayi mana amma ba kyau duk sanda akayi lesbian sai alarshin ALLAH ta girgiza. Zahra kuwa cewa ammi tai Tom ammi ya akeyi? Girgiza kai ammi tai tare da cewa, karki damu da sai kinsan yadda ake tinda dai ba kyau. Kenan hakan yana nufin ita 'yar lesbian ce? Ko dai karuwa ce? Zahra ta watsa kanta tambayar amma ina bamai bata amsa. Jiki a sanyaye zahra ta wuce bedroom d'in ta. Tana shiga ta wuce toilet tai, tai wanka bayan ta gama wankan mai ta shafa sanan ta wuce drowar da ilham ta shirya mata kayanta.

Riga da skirt d'in atanfa tasa, bayan ta gama shiryawa Quran ta d'auko ta fara mara ji'a.
6anran mashkhur da zee kuwa! Bayan zee ta gama shan coffee, dataga bacci ya kwashe mashkhur a kujera, itama kayan mayan da kwayoyo tasha ta tsallake mashkhur tai ta wuce bedroom d'in sa ta kwanta bacci akan bed d'insa.
Tofa mashkhur bashi ya tashi ba sai qarfe hud'u na yamma, lokacin ana kiran la'asar.

Mashkhur yana tashi ya kalli agogwan d'aki, da sauri ya miqe tare da furta astagfirullah!! Sam mashkhur hankalinsa Ya tashi ganin bai yi sallar azahar ba, kuma gashi la'asar tayi. A hanzarce ya nufi toilet d'in falon ya d'auro alwala, sanan ya dawo ya gabatar da sallar azahar da la'asar bayan ya idan ya gama addu'o'i bedroom d'in sa ya wuce. Kwance ya tarar da zee akan bed d'insa tana bacci, wani siriri tsaki mashkhur yaja sam bayasan wanan halin zee na rashin kamun kai.

Nan da nan yaji haushinta ya cika shi sam ya kasa sanin wai sabida mai ya kasa rabuwa da zee?. Firij ya nufa ya d'akko gorar ruwa mai sanyi gaske, ba 6ata lokaci ya bud'e robar ruwa ya cika hanunsa tab da ruwan,, ruwan har wani tiririn sanyi yake, ya watsawa zee a jikinta. A firgice zee ta farka tare da tashi daga kwanciyar da tai, mashkhur ta gani tsaye da robar ruwa a hanunsa. Had'e rai zee tai sosai tare da cewa honey mene haka ta qarasa maganr tana watsa mai wani kallo mai cike da 6acin rai.

Tashi ki tafi gidan ku mashkhur ya fad'a rai a had'e, honey ni kake cewa na tafi gidan mu koh?. D'akai mashkhur yayi alamun ehh, a zuciye zee ta miqe tare da sunkutar jakarta tabar d'akin, ta fita falo ta saka takalminta tabar gidan a zuciye, dama da motar ta tazo. Somotimes mashkhur da zee suna yawan samu sa6ani irin hakan sabida halayarsu batazo d'aya ba, ita zee karuwace ta sa6a d maza sosai shiyasa kullum take qoqan ta6a jikin mashkhur ko kuma tace zata kwanta ko hugg.

Shi kuma sam mashkhur bayasan hakan, dan yana tsoran gamuwarsa da ALLAH. Shi yasa yake nesanta kansa da zee Dan yasan shi'umancin zee tabbas in zai biye mata dole watarana ta ribace shi su aikata alfasha, duk da kuwa mashkhur bai ta6a sha'awar hakan daga zee ba, dan ahi sam bama ta cikin tsarinsa. Mashkhur bai damu da fad'an da sukayi da zee ba sabida yasan sai ta dawo bata da zuciya kwata-kwata. Dama haka zee take bata iya zuciya da mashkhur, ko sunyi fad'a haka zatazo tai tai mai

Please Login or Register in order to submit comment