Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Yana auro saratu ko wata d'aya banyi ba na samu ciki. Lokacin da ciki na ya cika wata 8 lokacin baban ahmad wato wanda ya haife shi ya sake aure sanan kuma yazo ya d'auki ahmad. Sai yace ai na kusan haiwuwa kuma yana so ahmad ya cigaba da karatun sa a kano. Lokacin daga ni har mijina bamuji dad'i ba sabida mun saba da ahamad amma dole haka muka haqura sabida mun san yayi mana kwai ci sosai a hakan ma.

Bayan tafiyar ahmad da wata d'aya na haifi d'iya ta mace. Ranar da aka sallamo ni daga asibiti ko kwana ba tai ba 'yar ta rasu. Munyi baqin cikin hakan sosai amma ba yadda muka iya haka muka haqura muka fauwalawa ALLAH. bayan shekara d'aya na sake haihuwar d'a namiji, shima ranar da na haife shi washe gari ya rasu. Shima bamuji dad'in hakan ba amma ba yadda muka iya haka muka haqura ra.

Daga nan ban sake samun ciki ba har sai da nai shekara biyu, na sake samun wani cikin,. Cikin yana wata takwas ranar naji na gaji da zama ni kad'ai shiru, kawai sai na yanke shawara naje wajan kishiya ta saratu muyi hira da yake tana da faran-faran da sakin fuska. Ina zuwa qofar d'akin zanyi sallama kenan naji tana cewa! Hmm ke dai bari yaya halima wlh yanzu cikin nata ma ya tsufa ta kusan haiwuwa.

Amma karku damu yadda na kashe wa'an can haka zan kashe wanan ai bazan ta6a bari ta haife 'yaya ba ni ban haiwu ba Kawai ta cinye gado abanza, tana haiwuwa zan sake dannawa 'yar ko d'an da ta haifa asiri ya mutu kamar yadda nai wa saura. Hankalina ya tashi sosai da jin hakan dan haka ko hirar da suke ban gama ji ba na juya a hankula ba bar wajan, na koma 6angare na.

Ina komawa na bigawa mamana waya na gaya mata, sai tace min ba komai kawai na cigaba da addu'a, ALLAH yafi qarfin su. Bayan mijina ya dawo da yamma na sanar da shi sai ya cemin shi bai yadda ba kawai kishin na ne irin na mata karna sake gaya mai wanan maganar. Daga haka dai na haqura na cigaba da addu'a, ana saura sati biyu na haiwu mijina ya tafu saudiya domin zuwa ka'aba yayi addu'a akan Allah ya raya mai abinda zan haifa.

Yana tafiya ni kuma nacewa mamana bazan iya zama ba tsoran saratu nake ji, hakan ne yasa mamana ta dawo gidan har lokacin haiwuwa ta yayi. Na fara naquda sosai kamar dai zan mutu aka kai ni asibitin, tun da rana muka je asibitin amma bani na haiwu ba sai da daddare a taqai ce dai nasha wahala sosai fiye da yadda nake sha in zan haiwu..........

Yau single page ne ba double.

Mu had'e a next page gobe.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing............

*page 106*

tun da rana muka je asibitin amma bani na haiwu ba sai da daddare a taqai ce dai nasha wahala sosai fiye da yadda nake sha in zan haiwu..........

Lokacin ne na haifi zahra maman ahmad ta fad'i sunan zahra kamar yadda taji mutan gidan suna fad'a. Yarinyar ta shiga rai na sosai da sosai gashi tana kama dani dama duk haiwuwar da nake ban ta6a haifar mai kama da ni sak irin ta ba. Hakan ne yasa nai ta tunanin ya zan tsiratar da ita daga halaka. Daran ranar dak aka na kwana a asibiti ina ta tunani.

Dama lokacin da na haiwu ban gayawa kowa ba ko mijina ban gayawa ba bare saratu sabida ina jin tsoron kar itama a kashe min ita. Washe gari ma haka dai nai ta tunani ya zan tsiratar da jaririyar nan. Da na yanke shawarar zan gudu da ita mu tafi wani garin amma sai nai tinanin ko na gudu baza su barta a raye ba sabida sun san tana raye.

Haka dai nai ta tunani har yamma tai, can kuma sai na yanke shawarar kawai naje na bayar da amanar 'ya ta ga duk wanda ALLAH ya had'a ni da shi ko ta samu ta tsira da rayuwar ta. Hakan ne yasa na samu fefa da biro nai rubuta address d'in gidan na da number ta a ciki sanan kuma nace a riqemin ita amana tana ciki matsala zuwa nan da shekara uku a dawo mun da 'yar ta.

Bayan kiran sallah magriba mama na ta sauka qasan asibiti domin wanke zanuwa, shine ni kuma tana fita na d'auki jaririya ta da wanan fefar na fuce daga asibiti. Bayan na fita nabi bayan asibintin duk da dajine haka na ringa ratsawa ciki har na fita bakin titi. Na dad'e la6e a baki dajin, ina jiran wani yazo can naga hajiya ita da wani qaramin yaro sun tsaya wajan.

Shine na qasa wajan bayan mun gaisa cikin dafara nace ta riqe min ita zan kar6e ta. Bayan ta kar6e ta na nace ta riqe min ita amana sanan na bawa wanan yaro da yake tare da ita takaddar hanuna nace duk wani bayani yana ciki. A lokacin hajiya ta nunamin cewa bazata kar6i 'yar ba ko na kar6i yata ko ta ajiye min ita anan. Ni kuma a lokacinnaji hajiya ta shigar min rai sosai jiki na ya bani bazata cutar min da 'ya ta ba.

Da na gaji da yi mata magiya kawai sai na gudu cikin dajin nan na 6uya a bayan wata babbar bishiya, duk da wajan abun tsoro ne amma banji tsoro ba a lokacin. Inaji hajiya ta shigo jejin hannu rike da jaririya ta tana nema na amma bata kula da niba. Bayan ta fita na cigaba da tafiya cikin jejin nan ina kukan rabuwa da 'yar ta.

Ina cikin tafiya a cikin jejin nan kawai na had'u da wata tsuwuwar mata tukuf dan da kyar ma take tafiya. Lokacin ban tsorata ba sabida ina cikin tsantsar baqin cikin rabuwa da 'yar ta, amma da haka nan ba had'u da matar ko da rana ne kuma ba a jeji ba dole zanji tsoro. Har zan wuce ta cemin baiwar ALLAH tsaya mana, ba musu na tsaya kamar yadda matar ta umar ceni.

Sosai ta kalle ni sanan tace bawar Allah kiyi haquri kinji mai yake damunki haka kike kuka da a tsakiyar dajin nan da daddaran nan. Shiru nai wa matar dan a lokacin na d'an farajin tsoro kad'ar girgiza kai matar tai sanan tace min karna ji tsoran ta ita ba cutar dani zatai ba.

Tana gama fad'in hakan ta ruqo hanun ta duba tsakiyar hannu na. Bayan ta duba tace duk taga abinda yake damuna kuma daga yau in sha ALLAH in dai na sake haiwuwa baza a qara kashe min d'ana ba sai dai in kwanan sane ya qare. Daga haka ta sa bakin ta ta lashe min tafin hannu na. Sanan ta shafa gefan ciki na daga haka bata sake cemin komai ba ta juya ta fara tafiya.

Ni kuma nai ta nazarin anya wanan matar mutum ce?. Da sauri na juya dan sake ganin matar amma ina juyawa baya na ban ga ko giftawar matar ba ta 6ace min 6at duk da kuwa dajin yana da stayi dogo ne ba kwana. Daga haka na cigaba da tafiya ta zuciya cike da zullumi. Ina komawa asibiti na tarar da mahifiyata ta hankali tashe, cikin tashin hankali take tambaya ta ina naje kuma ina jaririyar take. Ban wani bata lokaci ba na gaya mata abinda na aika.

Mahaifiya ta nunamin 6acin ran ta akan haka tayi fishi tayimin fad'a sosai. Haka dai nai ta bata haquri har na shago kanta, ta amince zamu koma kano tare ni kuma zancewa majina da kishiya na koma kano gida kuma 'yar ta rasu a kano. Daga asibiti bamu koma gidan na ba muka wuce kano kamar dai yadda na tsara haka na sanar da mijina da kishiya ta akan 'ya ta rasu.

Lokacin da na dawo kano hankali yana can kaduna sabida tsoran kar hajiya ta karanta address d'in gidan ta mayar min da yarinyar, haka dai nai ta bigawa mai gadi na waya ina tambayar shi, baqin fuska sun zo da jaririya, sai yace min aaa haka dai har wajan sati muna haka, daga qarshe dai na dena kira ina tambaya.

Bayan kwana arba'in da haiwuwa ta na koma kaduna gidana. Bayan na koma da wata uku na sake samun wani saban ciki,. Lokacin da cikin ya tsufa na kusan haiwuwa a lokacin na gayawa mijina gaskiyar zancan akan waccan 'yar ba mutuwa tai ba amanar ta na bayar. Duk dai abinda ya faru na kwashe labari na gaya mai. Shima lokacin yayi fishi sosai dan har sai da ta kai ya mre ni yayi fushi dani sosai a lokacin.

Har dai na haiwu baya kulani, sabida bai ji dad'in abinda na aika ta ba.
shekara d'aya tsakanin zahra da qanwar ta nana hafsat itama dai a lokacin ban wani sa rai na ita ba, amma abin mamki sai naga har suna anyi amma bata rasu ba kamar dai yadda ragowar suke mutuwa. To tin ina cire rai da nana har kuma na dena cire rai da ita sabida har tama fara wayo.

Bayan nana tayi shekara uku na sake samun wani cikin a lokacin ne nai ta jiran ganin dawowar 'yata da na bada amanar ta amma dai naji shiru ba a dawo min da itaba har na sake haiwuwar d'a na namiji. Daga haka dai haka na ciga ba da haiwuwa har na haifi yara uku bayan nana da qaninta fawas. Amma dai kullum burina d'aya na had'u da 'yar ta kullum ina addu'a daga qarshe ma sai na fara da na sanin bayar da ita da nai.

Ya zamana ina yawa mafaran kan ta iri-iri duk da ban san taba, kullum abinda yake damuna kena na kaza manta ta a rayuwa ta duk da kuwa ina da 'yaya biyar bayan ta. Duk nabi na damu na kasa sukuni watara na ma in tinanin ta ya motsa sai na wini banci abinci sai naji sam ban mata adalci ba, ban kyauta mata ba amma dai jikina yana bani tana raye bata mutu ba shi yasa nake yawan tunanin ta na kasa mantawa da ita. Kuma kullum ina addu'ar in tana raye ALLAH ya had'a ni da ita.

Duk da kuwa nasan in na ganta ba lailai ne na iya gane ta ba. Yan zuma ALLAH ne yayi da raban zan had'u da ita, tinda ni bada son rai na nazo nan d'in bama kawai dai mijina ne ya takuramin akan sai nazo. Ina zuwa naga abdul sai naji kamar na ta6a ganin sa amma sai na manta inda na ta6a ganinsa da yake lokacin da na ta6a ganin sa yana yaro sosai.

Daga qarshe kuma da naga hajiya lokaci guda na gane ta duk da kuwa lokacin da na bata amanar 'yar tawa wajan ba wani haske kuma bata kai tsofan haka ba amma tabbas bazan ta6a manta fuskar ta ba, maman zahra ta qarasa maganar tana kuka mai ban tausayi. Kai nan da nan kowa sai yaji duk ya tausayawa maman zahra, zahra kuwa tuni ta gane ba mafarki take ba kuma ba kwakwalwar tace ta samu matsala ba gaskiya ne wanan..

Lokacin guda zahra taji tana qaunar maman tata ko dan yadda taga suna kama da ita da yadda taga tana son ta. Duk sai taji matar tabi ta birge ta sosai,. Baban zahra cikin jimami yake tambayar wai sabida mai ba'a dawo da zahra ba bayan ta girma?. Nan da nan dady da ammi harma da hajiya kaka suke labirta musu yadda akai su mashkhur suka qona takaddar address d'in a rashin sani.

Jinjina kai baban zahra yayi tare da cewa, gaskiya ne ALLAH ya rubuta anan zata cigaba da rayuwar ta ba a wajan muba.
saratu kuwa cikin kuka take cewa, dan ALLAH ku yafe mana wlh sharrin shed'an ne bazamu qara ba. Momy kuwa tuni ta koma abin tausayi tana jiran hukuncin da ya kamata ai musu sabida tasan yanzu ita mai babban laifi ce.

Ta cancanci ai mata hukunci kisa ma, sabida har sanadiyar kashe rai tai. Falo ya kacame da hayaniya kowa yana fad'in albarkacin bakin sa, mashkhur kuwa zahra kawai yake kallo sabida abun da momy ta aikata ya d'aure mai kai ya hana shi sakat shi yama manta har da shi akai niyar kashewa a Zuciya shi yana cewa yanzu da an kashe min matata zahra ya zanyi?.

Zahra kuwa ta rarraba ido sai qarewa wanda akace iyayan ta ne kallo take da kuma saratu qanwar momy. Ahmad kuwa hankalin shima in yayi dubu ya tashi jin mugunta momy da kuma niyar ta ta raba shi da masoyiyar shi ilham, cikin rud'ani ahmad yace kai gaskiya mashkhur matar nan bata da imani ita da qanwar ta ko kad'an.

Amma bai sai yaji mashkhur bai bashi amsa ba sabida shi bai maji maganar da yake ba hankalin sa duk yana kan zahra. Da sauri ahmad ya juyo cikin mamaki yace mashkhur wai bakaji mai nace bane?. Ai kuwa ahmad jiyowar da zai yi kawai sai yaga mashkhur ya saki baki ya zubawa zahra ido kamar ba shi aka gama ba da labarin irin cutar da akai masa ba. Hannu ahmad yasa ya ta6a mashkhur yana cewa kai!.

Firgigit mashkhur yayi ya dawo daga hayyacin sa, yana kallon ahmad. Ahmad cewa yayi lafiya mashkhur ko dai ka fad'a ne?. Ajiyar zuciya mashkhur yayi tare da cewa, hala dai ahmad bakaji abinda akace ba? Cikin mamaki ahmad yace naji komai mana mashkhur. Cikin tsoro mashkhur yace dafa haka momy tace zahra tai niyar kashewa bakaji bane?.

Cikin mamaki ahmad yace ai bama iya zahra ba har da kai tai niyar kashewa koh?. Sai a lokacin mashkhur yace oh hakane fa na tina mantawa nai. Duk da halin da ahmad ciki na tashin hankali sai da mashkhur ya bashi dariya. wani shu'umun murmushi ahmad yayi a zuciyar shi yana mamaki yadda lokaci guda mashkhur ya canza. Mashkhur kuwa ya d'an tsargu da kallon da ahmad yake mai, dan haka cewa, yayi ahmad lafiya ko kana tinanin wani abun ne?.

Da sauri ahmad ya girgiza kai tare da cewa ina kwai ina tunanin yadda zan yiwa qanwata zahra saban mijin ne bayan kun rabu. Wani sirrin tsaki mashkhur yaja tare da cewa, daga ganin sarki fawa sai miya tai zaqi kawai dan kaji ance qanwar kace. Murmushi ahmad yayi tare da cewa, to ya san ranka ni kagama tinda naga suna jituwa da ilham kawai aure su zanyi duka su biyu, ai tuwo na mai na.

Mashkhur kuwa wani dogwan tsaki yaja tare da cewa, ai kuwa sai dai ka za6i d'aya daga cikin su dan in ka matsama ilham d'in ma bazaka a baka ba bare ita zahra kaga sai kayi biyu babu uku ba ko d'aya tinda naga alama ka cika son zuciya mashkhur ya qarasa maganar yana watsawa ahmad wani mugun kallo.

Da sauri ahmad ya qunshe dariyar da take son kwace mai sanan yace haba mashkhur mai yayi zafi haka? naji ni nahaqura da zahra amma zan mata miji in ka sake ta. Wani dogwan tsaki mashkhur ya sake ja tare da cewa to kaji sai na sake ta, har yanzu dai karka manta matata ce mashkhur ya qarasa maganar yana kawar da kai gefe, duk abinda momy taiwa mashkhur bai 6ata mai rai ba kamar yadda ahmad yake cewa wai zai auri zahra ko kuma ya aura mata wani bayan sun rabu.

Kai haka dai falon nan akai ta hayaniya kowa yana fad'in albarkacin bakin sa banda yaran gidan. Daga qarshe dai mahaifin zahra yayiwa saratu saki uku rass. Zo kaga tashin hankali wajan sartu kamar tai hauka da kyar dai momy ta jaza suka tafi part d'in ta. Maman zahra kuwa da sauri ta taso ta rungumo zahra tana sake godewa Allah da ya cika mata burin ta.

Zahra kuwa ran ta fass tana so itama ta rungume maman tata ta fad'a mata yadda take son ta da son ganin ta, amma sai take jin kunyar ammi da dady sai take ganin kamar in tai hakan ba tai musu adalci ba. Sakin zahra maman ta tai sanan tace zaki bimu ko mu tafi kaduna dake kikaga sauran 'yan uwan ki?. Zahra kuwa girgiza kai tai tare da cewa aaa ni dai gaskiya bazan bar yaya abdul ba.

Ahmad kuwa kallan zahra yayi tare da cewa, haba zahra ki bi su mana kuje kaduna kije kiga qanwarki nana mai surutu, kina da qanne fa da yawa acan harma mai kama da ke sunan ta kaulat. Nan da nan yaran gidan suka fara magana kowa yana fad'in albarkacin bakin sa. Faruq cewa aa gaskiya mu dai bamu yarda a d'auke mana zahra ba.

Ilham tace ai kuwa dai tana nan baza mu yadda taje ko ina ba, haidar kuwa cewa yayi ai kuwa dai sai dai qanan nata suzo har nan su ganta. Haba dan ALLAH ku bari taje ko shekara d'ayane tayi sai ta dawo, abban zahra ya fad'a fuska cike da Murmushi, mashkhur kuwa da sauri ya d'ago dan jin ance zahra zata tafi tai shekara d'aya yana tunanin wai iyayan ta sun manta tana da aure ne?.

Ilham kuwa sake cewa kai shekar d'aya kuma uhmm gaskiya ni dai ko wuni d'aya bazan barta taje tai ba bare shekara. Zahra kuwa bata san sanda ta d'ago ido ta sheqawa ilham wani kallon baki isa ba, nan da nan su ilham suka kwashe da dariya, zahra kuwa har lokacin bata dai na yiwa ilham wanan kallon ba.

Faruq ne yace zahra dady fa yana kallon ki, da sauri zahra ta juya suna had'a ido da dady da sauri zahra ta rufe fuskar ta tana dariya. Shima dady dariya yayi tare da cewa uhmm mamana haka zamuyi dake kenan koh?. Girgiza kai zahra tai alamun aaa, ammi kuwa cewa tai kuji yara ku zaku ma bata izini tafiya kenan, ni dai na yadda kije kiyi shekara uku ma.

Nan da nan su ilham suka fara cewa kai ammi gaskiya aa, mashkhur tinani ya farayi wai shi yanzu meye makomar shi kenan yana zaune ana bawa matar shi umar a gaban sa kuwa wai mai aka mayar da shi kenan?......................


Ni kuwa amina bayero nace tab lalai mashkhur ka ban mamaki na tuna mai sakin zahra zau yi ko na barshi muga iya gudun ruwan sa?.😂😂😂😂😂😂

Ina jiran amsar ku, mu had'u a next page.

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing...............

*page 107*

mashkhur tinani ya farayi wai shi yanzu meye makomar shi kenan yana zaune ana bawa matar shi umar a gabansa kuma to wai mai aka mayar da shi kenan?......................

Mashkhur da baqin ciki ya ishe shi miqewa yayi zuciya ba dad'i ya fuce daga falon. Ahmad kuwa shima miqewa yayi yabi bayan mashkhur d'in. Suna gama fita daga falon ahmad ya ruqo hanun mashkhur tare da cewa haba mutumina meye kuma na saurin yin zuciya, ko abinda na fad'a ne bai maka dad'i ba. Rai ba dad'i mashkhur hmmm ahamd kenan bazaka gane ba wlh sam na rasa mai yake min dad'i.

Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Mashkhur kenan ai kowa bai ji dad'in abinda ya faru yau ba gaskiya na tausaya maka sosai a she duk shaye-shaye da kake ba yin kan ka bane. Ajiyar zuciya mashkhur yayi tare uhmm kai da bari ahmad ai momy sam bata da imani amma ni ba wanan ne yake damuna ba.

Murmushi ahmad yayi a zuciyar shi yace anzo wajan amma a fili sai yace to mai yake damun ka. Kallan ahmad mashkhur yayi sanan yace uhmm ahmad wai mai yake kawo yawan tinani mutum sai kaji Sam in baka ga mutum ba baka samun nutsuwa a zuciyar ka. Cikin basarwa ahmad yace haba mashkhur sai kace ba namiji ba ai in dai kaji kana tunanin mutum musamman ma mace ce kawai ka kamu da son ta.

Zaro ido mashkhur yayi ciki razani yace ahmad so kuma?. K'warai mashkhur so ne yake sawa ka ringa tinanin mutum sanan kaji in baka ga wanda kake so ba sam bakaji dadin rayuwar ka, sanan kuma kana ganin ta zakaji duk damuwar ka ta kau, hmm mashkhur wace kuma ka samu haka, kace ka fara son wata?. Da sauri mashkhur ya girgiza kai sanan yace aaa ko d'aya kawai dai na tambaya ne.

Murmushi ahmad yayi tare da cewa in tai tsami maji, girgiza kai mashkhur yayi sanan yace uhmmm bama abinda zakuji, ni ba wanda nake so, daga haka mashkhur ya wuce yabar ahmad tsaye da tunani iri-iri. Wani irin tsoro ne lokacin guda ya Kama mashkhur, shi da yake tunanin zahra da yana tinanin kawai sabo ne ashe so ne. Wata zuciya tana rayawa mashkhur qarya ahmad kawai yake mai ko tsokanar shi yake.

Haka dai mashkhur yayi ta tambayar kansa amma ba amso shi, zuciyar mashkhur tana so ta amince son zahra yake amma mashkhur ya hanata sabida tsabar qarfin hali. Ga mugun mamaki da yake ta d'a wainiya da mashkhur na ganin iyayan zahra, shikenan yanzu zahra nisa zatai dani? Mashkhur ya watsawa kansa tambayar, amma ina ba mai bashi amsa.

Abban zahra ya wuce kaduna zuciya cike fal da farin ciki, maman zahra kuwa tace itafa bazata koma gida ba tana tare da zahra har sai zahra ta amince taza bita gida.

Nights.

Baki d'auke da sallama zahra da ilham suka shiga d'akin da aka sauki maman zahra hannu riqe da tire. Fuska a sake cikin Murmushi maman zahra ta amsa musu sallamar tare da tace sanun ku da zuwa 'yaya na ALLAH yayi muku albarka. Murmushi zahra da Ilham sukai har suna had'a baki wajan cewa ameen. Daga haka wayar maman zahra ta fara ringing.

Da sauri maman zahra ta duba dan ganin wace take kira. Sunan NANA ta gani ya bayyana akan screen d'in wayar murmushi tai sanan ta kalli zahra tana cewa kuzo ku zauna mana bari kiji qanwar kice nana ta bugo min, maman zahra ta qarasa maganar tana d'aukar wayar tare da sata a hans free tana cewa hello nana.

Cikin zazzaqar muryar nana ta fara magana da cewa, mama Ina kuka tsaya hakane nifa kin san bana son zaman da yara duk sun takuramin twins sai fita suke ga kaulat ta takuramin wai yaushe zaki dawo. Murmushi maman zahra tai sanan tace bazan dawo yau ba sai zuwa gobe ko jibi. Kai mama nifa bana son irn wanan wasan dan ALLAH kuna ina kun kusan qarasowa.

Au wasa kika d'auka kenan da gaske nake amma abban ku zai dawo in kuma baza ku iya jira ya dawo ba ku tafi gidan kakar ku kuzauna. Kamar nana zatai kuka tace haba mama sabida mai zaki kwana kuma gwaggo ta barki ita

Please Login or Register in order to submit comment