Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da qasa ya watsawa marshkhur sannan yace da izinin wa zaka koma?.

Mashkhur gabansa ya fad'i Sai da yayi jim kafin yace ba da izinin bakowa bah.

Dady yace to bazaka koma ba yanzu sai qarshan watan nan.

Man yan idan nunsa ya ware akan dady yana d’an zarosu, hakan ba qaramin kyau ya qaramai ba. Sanna yace dady ina da abu mai mahimmanci fa da zanyi acan.

Dady yace ko menene ka sokeshi qarshan watannan zan d'aura auran ka da zahra.

Mashkhur a gigice yace ehhyee yana sake zaro manyan idan nunsa alamain maganar ta raza nashi. Dady yace eee,
Am!! Am!! Ma! Amma dady ai dana d’auka sai nagama karatuna na dawo Nigeria gaba d’aya za ai maganar auran.

Dady yace to bah haka na tsaraba.
Amma dady naga!! Katse shi dady yayi ta hanyar cewa Kai ya isa banasan jin komai da ka gareka kabi umarnina shine kwanciyar hankalinka. Mashkhur a zuciya ya juya ya koma part din da ya futo, cikin tashin hankalin da yafi najiya.



A falan kuwa Maganar ta bawa kowa mamaki. Ita dai ammi taji dad'in hana shi tafiyar da dady yayi sabida tasan halinsa, in yatafi bashi da ranar dawo wa. Ita kuwa momy farin cikine ya tur niqeta, domin haqarta zata cimma ruwa.

Hajiya kakama taji dad'in hakan sosai.



Itama ilham wucewa tai jiki ba kwari, kuma tana godewa ALLAH da yasa ba a gaban zahra dady ya fad'i maganar ba, dan ta san zata iya qara shiga damuwa da matsanancin hali fiye da wadda taka ciki in taji maganar . Itama ammi tashi tai da flat ta nufi d'akin abdul majid domin kai mai breaker fast d'in shi.



Dady shima tashi yayi ya tafi. Ita hajiya kaka haka. Suma 'yan makaranta tafiya sukayi amma bandda amir da yace bazai jeba tindda auntynsa bazataba. Momy ma cike da murna ta wuce d'akinta dan sanar da saratu abindda ya faru.

Momy tana shiga d’akin ta’ ta lalubo wayarta ta dannawa saratu kira ta hau ringing, ringing biyu tai hjy saratu ta d’auka.
Salamma’alaikum yaya halima an tashi lpy? Cewar saratu. Momy tace Wa’alaikissalam saratu labari mai dadi.

Momy Ta fad’a tana murmushin mugu ta. Haba yaya ai kyabari mu gama gaisawa ko? Murmushi momy tayi tare da cewa hmm ai saratu bazan iya bari ba. To yaya halima bani nasha.

Momy gyara zama tai tare da cewa kinsan mai yafaru yanzu kuwa? Aa sai kin fad’a.
Waii yau da sanyi safiyar nan mashkhur ya had’a kayansa waii zai koma rasha, Rasha kuwa yaya amma dai baki bari ya tafiba ko? Dan Wallahi in ya tafi ba dawowa zai ba.

Inafa aka bari ya tafi ai mahaifin sa ya hana shi zuwa yace sai an d’aura aure. Ahayye chass wlh aunty burunmu yana daf da ciki in aka d’aura auran nan. Hhhh ke dai bari saratu, amma yanzu ya kike ganin za’ai

Dan kinsan halin mashkhur dataurin kai zai iyaguduwa ba da sanin kowaba.
Nunfasawa saratu tayi kafin tace, ehh zai iya fatiya ba da sanin kowa ba amma kafin haka ta faru ke zaki hana.

Amma taya zan iya hanashi hakan saratu?
Haba yaya karki badani bana, ke da kike uwar d’akin sa, kin riga da kin mallake mashkhur duk abidda kikace dole yabi, karfa ki manta koh maganar iwarsa bayaji kamar taki.

Ajiyar zuciya momy ta sauke tare da cewa hakane, amma kinsan mashkhur yana da tauri kai ba lallai ne ya yadda bah, tindda tun farko na dasa mai tsanarta a ransa. Ehh hakane amma ai lallab’a shi zakiya sai ki nunamai in ya aure ta UBANTA zaici.

Ehh hakane fah wallahi kin bada shawara mai kyau, bari na bari ya wuce zuwa anjima sai naje na fara kitsa mai harsa ya yadda da auran. Yauwa yaya koke fa yanzu naji magna. Daga haka sukayi sallama.

AMMI......
A hankula ta murd’a handil d’in qofar ta shiga da sallama. Akwance a bad ta hango abdul majid yana ta sharar bacci. Sauke ajiyar zuciya momy tayi tare da furta Alhamdulilah, dan harga ALLAH taji dad’i samu abdul majid ya samu bacci sosai.

Qarasawa tai ta ajiye plate da cup d’in akan table. Doya da kwai ne acikin plate d’in cup d’in kuma shayine mai kauri ya sha madara da milo.
Ta juya kenan zata fita abdul majid ya farka, cikin sanyayiyar murya ya kirata

Ammina, ammi juyowa tai tana kallansa cikin kulawawa tare da cewa, Na am baban d’ana. Sunan da momy take kiran shi kenan, cikin murmushi da kulawa ta qarasa wajan sa.

Zaunawa tai a gefan bed tare da cewa ya jikin naka? Ajiyan zuciya yayi ya gunqura ya zauna da kyar tare da cewa da sauqi ammi. Nunfasawa ammi tai tare da cewa yanzu mai yake damunka?

Murmushin yaqe yayi tare da cewa ba abidda yake damuna ammi na samu sauqi. Haba baban d’ana dubifa yadda jiya zuwa yau ka zafge ka fita hayyacin ka amma kace ba abidda yake damunka?

Hmm ammina ki dena tayadda hankalin ki na samu sauqi kawai rashin kwarin jikine ke damuna. Haba babban d’aya ba dole na ta yarda hakalina ba kana sa damuwa aranka, koh so kake ka d’orawa kanka ciwan zuciya da hawan jini?...........

Typing.........

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA, ina yi muku fatan Alkhairi. Kuma da fatan zaucigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.........💜❤️💜

*Dan Allah in kun karanta ku d’inga comment........pls, sabida hakan shi zai bani qarfin guwar cigaba da rubutawa.......💜❤️💜

Typing...........

ADALILINTA💜❤️💜

AMINA BAYERO💜❤️💜

*Free book💜❤️💜

*Page 11*
,Ko so kake ka d’orawa kanka ciwan zuciya da hawan jini?.............

Girkiza kai yayi tare da cewa kiyi haquri ammi insha ALLAH zan dena. Aaa ba zaka denaba ka dena nakeso kace, murmushi yayi tare da cewa na dena ammina. Yauwa ko kai fa, kayi sallar asuba koh?

Ehh nayi, yauwa kaje ka wanke bakinka kazo kayi breakfast. Tom ammi, ba musu ya tashi jiki ba kwari kamar ya fad’i. Ammi kuwa da taga haka da sauri ta yunqura ta riqe shi, tare da cewa muje na raka ka toilet d’in.

Tai maka mai tayi ya wanke bakinsa da fuskar sa sanna suka fito. Koda suka fito ita ta ringa bashi breakfast d’in a baki, cikin kulawa da qauna. Bayan ya gama ci ta fashi magani yasha ya sake kwanciya.

_Mutane kenan basa tsoran ALLAH dubi yadda ammi take kula da d’an momy, amma ita momy tana can tana shiryawa d’an ammi makirci. Allah ya tsaremu da ai kata hakan. Ameen ya Allah..

Ko da ammi ta fita haka abdul yay ta juyi akan bed zuciyarsa ciki da damuwa, da kuma tinanin zahra a wane hali take yanzu. Da haka bacci ya sake awan gaba da shi.

Wannan kenan.

MASHKHUR............
Yana zuwa room d’in sa ya fad’a bed cike da takaici da baqin ciki. Wai shi dady zaiyiwa haka? Abidda yake ta furtawa kenan. Can kuma yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya. Zurfin tinani ya tafi so yake ya nemawa kansa mafita tun kafin lokaci ya qure maii.

Tina nine ya shiga fad’o ma kala-kala.
Amma yafi amincewa da wandda zuciyarsa take ta Tunzira shi yayi. Zuciyar mashkhur tana ta tsara mai ya GUDU ya koma wata qasar da zama. Bayan wasu SHEKARU in an manta da maganar ya dawo. Kafin nan ma dady ya aurawa zahra wani.

Haka yayi ta shawara kala-kala, daga qarshe ya yanke shawrar sai ya samu UWAR D’AKINSA, MOMY ta basi SHAWARA. Yasan baza tab’a bashi shawarar auran zahra ba. Ajiyar zuciya ya sauke sai yanzu ya d’an samu sukuni.

Tashi yayi ya canza kayan jikin sa zuwa singlet da three kwata. Bayan ya kammala ya fara sana ar’ sa ta shan kwayoyi da magan mura, nan da nan idanunsa suka fara lumshewa alamun bacci. Lafiyar gado yabi ya kwanta. Bacci yayi awan gaba da shi..........

ZAHRA.........
Haquri ilham take ta bata akan taci breakfast amam qiri-qiri taqici.
Haba zahra wanna abidda da kikeyi bashi zai hana auran ki da yaya mashkhur ba haba sis dan ALLAH kici breakfast d’in nan koh kad’an ne.

Haba tin jiya da safe raban da kici abinci Karki d’orawa kanki cutar olsar.
Zahra da ta gaji da magiyar da ilham take mata, juya mata baya tayi tare da cewa ni ki rabuda ni bazanci abincin nanba wallahi kwarama cutar ta kamani na mutum.

A razane ilham tace kaii wallahi bazaki mutuba in kika muzu zahra bazan iya rayuwaba, kidena fad’ar hakan. Ko rufe bakinta batayiba sukaji an turo qofar dakin.
Ammi ce ta shigo bakin ta d’auke da sallama.

Juyawa dukan su sukayi suna kallan ammin. Har suna had’a baki wanjan amsa mata sallamar. Qarasa wa tai indda suke zaune itama ta zauna a gefan bed d’in. Tana zama ilham tace yauwa ammai gwara da ki kazo, wallahi tin d’azu nayi-nayi da ita taci abinci taqi,

Dan Allah ammi kiyi mata magana wai har haka tace gwara ta musu ta huta. Ammi da sauri ta kalli zahra tana zaro ido tare da cewa a uzubillahi haba mai sunan mamana, da bakin ki, kike fad’ar munanan kalamai kamar haka.

Haba mamana ina haqurinki yake? Karki manta in qaddara ta samu bawa addu’a ya kamata yayi ALLAH ya yaye mai ba mumminan furiciba.
Zahra wasu siraran hawaye ne suka zubo mata fuska duk ta kunbira, tayi jawur. Amma ammi kina jin dai abidda dady yace koh,

Tafad’a murya a shaqe. Ammi tashi tayi ta koma kusa da zahra ta zauna sanna tace, naji abidda yace, amma kinsan ba yadda muka iya dole ne ayimai biyayya koh?. D’aga kai tayi alamin ehhh sannan ta fashe da kuka.

Ammi nunfasawa tai tare da cewa banasan naga kina kuka mamana, ko so kike wani ciwan ya kamani ne?, da sauri zahra ta girgiza kai tana cewa haba ammi ki dae na fad’in haka insha ALLAH ba ciwan da zai kamaki.

Toh zahra ya kike so nayi da mae zanji ne.nasan ke zakiji maganata, amma mashkhur kuna fad’a mai baji zai yiba sai dai yaji magar momy, ko kema so kike ki koma marajin magana ta kamar shi? Girgiza kai zahra tayi alamin a’a. Yauwa mamna kiyi haquri kinji, kisa ta wakkali a zuciyarki,

Kuma ki cigaba da addu’a ALLAH zai gyara komai, ki dae na damun kanki, ko so kike ki b’ata ranar farin cikin ki, karfa ki manta nan da 1 week zaki saukar al qur’ani, kinga ai bai kamata ki b’ata lokacin farin cikin kiba ko?.

Hakane ammi insha ALLAH na dae na kuma zanta addu’a ALLAH yasa a fasa auran.
Murmushi ammi tayi tare da cewa in kuma alkhairi ne auran naku fah?. Zahra kuwa zaro idan ta tayi tare da cewa haba ammi ai kema kinsan ba alkhairi bane.

Haba mamana ki dae na yanke zato, ai ALLAH yafi qarfin komai, yanzu dai ki zauna kici abincci kinji. Ammi nifa na qoshi. Ammi bata rai tayi tare da cewa mai kikaci da zakice kin qoshi? Ahh ammina karki fishi dani zanci. Yauwa koke fah.

Ilham kuwa da take gefe tana sauraran su cewa tai au’ni ammi ba za’a rarrasheni naci abincin ba. Ammi kuwa harara ta watsa mata tare da cewa karki ci, mumurshi ilham tai tare da cewa zancima koh ba’a rarasheni ba.

Dariya ammi tai tare da cewa da kin rufawa kanki asiri kuwa. Zahra kuwa cewa tai ni bari na rarrashe ki kici, tafad’a tana murmushi dole. Yauwa ‘yar uwata, bari nazo ki bani a baki.
Sai da ammi ta tabbatar zahra taci abincci sosai
sannan tabar bar d’akin.

Zahra bayan ta gama cin abincci kwanciya tai a kan bed, har yanzu batajin dad’i zuciyar ta kawaii dauriya takeyi, haka tai ta tunanin kala-kala tana addu’o’i Azuciyar ta ALLAH yasa kar ayi auran daga haka baccin da taci bashinsa jiya da daddare ya kwashe ta.

HAJIYA KAKA.......
Bayan ta koma part d’inta shiryawa tai sanna ba bugawa malam Ibrahim ta sheida mai tana tafe. Bayan ta gama wayar ta fita farfajiyar gidan ta samu drive da yake kai ta unguwa suka fita.
Hajiya kaka ina zan kai ki cewar malan bala drive.

Wajan malam Ibrahim zaka kai ni. Tom shikenan. Daga haka bawandda ya sake cewa komai. Wajan tafiyar minti ashirn da biyar yayi kafin su qarasa. Hajiya kaka mun qaraso, tom bari na futa, tom hjy sai kin dawo.

Da sallama hjy kaka ta shiga runfar kwanan malam Ibrahim. Amsa mata yayi fuska d’auke da fara’a tare da cewa hjy har kin qaraso kenan?. Ehh wallahi na qaraso. Tom ga wajenan kizauna ya fad’a yanai mata nuni da tabarmar da take shinfid’e a r wajan.......

Yau kunga nayi 2 page ko. Daga yanzu 2 page zan d’inga ki muku posting . Sabida typing d’an yana yimin yawa, kuma na qara muku yawan pages d’in.

Typing..........

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*free book*

*Ina godiya da masoyana masu buqatar littafin ADALILINTA, ina yi muku fatan alkhairi. Kuma da fatan zauku cigaba da bibiyata harna saike littafin ADALILINTA........💜❤️💜

*Dan ALLAH in ku karanta ku d’inga comment........pls sabida hakan shi zai bani qarfin guwai cigaba da rubutu......💜❤️💜

*ga masu buqatar littafin ADALILINTA sai suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. Free book ne bana kud’i ba, kuma new book ne.

New book on 2023
[11/06, 22:23] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing...............

*Page 12*
Tom ga wajenan ki zauna ya fad’a Yanar mata nuni da tabarmar da take shinfed’e a wajan............

Tom malam nagode. Sai da hjy kaka suka gama gaisawa da malam Ibrahim kafin tafara gabatar da abidda ya kawo ta.
Yauwa malam Ibrahim dama jiya na sanar da kai abidda ya faru koh? Akan auran Muhmd da mai sunana.

Kwari hjy fatima kin sanar dani, amma da fatan kinyi istaharar da kikace zakiyi?
Eee nayi jiya da daddare. Yauwa tom da kikayi ya kikaji zuciyarki ta amince da aura. Kwari malam naji zuciya tayi sanyi kuma na qara son auran biyeda da. Masha ALLAH, kinga hakan yana nufin alkhairi ne,

Amma hajiya fatima wani anzari ba guduba!! Malam Ibrahim Mai kake hangowa sanar dani. Ni dai a ganina ke da mahaifiyar yarannan Muhammad sai kun miqe tsaye da addu’a a kansa, dan kwata-kwata baya jikin hanyyacinsa.

Dan Wallahi sammu da sihiri kala-kala ake mai so ake aga ya lalace gaba d’aya, a hakanma da sauqi. Hjy kaka gyara zama tai tare da sauke ajiyar zuciya sannan tace, kwaraii malam Ibrahim hakane dan so ake a lalatamim Muhammad ta qarfin tsiya,

Kuma nida mahaifiyar sa harma da mahaifin kullum addu’a mukeyi, Wallahi ni nasan wacece take mai haka kuma da zan iya rabasu tun kafin su shaqu da tini na rabasu amma duk da hakan Allah yafi qarfin tah . Kuma da akwai ranar tonan asiri.

Hakane Hajiya fatima dan gaskiya sai kun miqe tsaye akan Muhammad.
Kwari malam Ibrahim shiyasama nake san had’a auransa da zahra. Kuma so nake in zai koma rasha ya TAFI DA ZAHRA.

Jinjina kai malam Ibrahim yayi tare da cewa amma hjy fatima bakya ganin za’a iya samun matsala, in yatafi da ita. Kuma nagama a gaban ku ba raga mata yakeba zalintatta yake ina da sun bar gaban ku sun tafi wata uwa duniya.

Gaskiya ne malam Ibrahim. Kuma abidda yasa nake so zahra ta auri mashkhur harya tafi da ita shene, sabida inaso a dalilin zahra ya shiryu kuma ya dena duk wasu munanan halaye da yakeyi. Kaga zahra maca ce mai ilimi da tinani

Ga haquri, Inaso tayi ammfani da ilimi ta na addini wajan gyara munanan d’abi’un sa, duk da dae nasan abin da kamar wuya amma indae zamu riga addu’a komai zai zo da sauqi.

Hakane hajiya fatima ai ba abidda yafi qarfin addu’a. Kuma insha Allah zanyi mai addu’ar da bazai iya cewa bazai tafi da zahra ba. Yauwa malam Ibrahim hakan yayi kyau sosai.

Kuma in tafiyar tazo kusa kizo da zahra ko kuma ke da kanki gizo. zan bata wasu addu’o’i da zata ringayi ko suntafi can, insha ALLAH in dae tanayi zuciyarsa zatayi sanyi a hankali zai fara rage munanan halayan sa, kuma duk asiri da sammun da aka yi mae zai fara karyewa.

Yauwa malam Ibrahim ingodiya, yanzu nawane kud’in sadakar da zan bayar.?
Haba hajiya fatima ai Muhammad kamar jikane a wajena ki dae na yimin godiya, kuma ni da kud’i na zan masa sadaka.

Haba malam Ibrahim kabari zan biya, ta fad’a tare da janyo jakarta, ta bud’e ta curo 50k ta ajiyewa malam Ibrahim tare da cewa dan Allah ayi haquri da wannan. Haba hajiya fatima nace ki barshi ai mun dad’e a tare tsakanina dake ba biyan wani kud’in aiki kina kyautatatin sosai hajiya fatima

Nima ai sai ki bari na kyautata miki koh?
Aa wlh malamu Ibrahim ai bazan tab’a biyan ka abidda kakemin ba. Ta fad’a tare da miqewa tsaye tace tom malam Ibrahim ni zan wuce gida.

Tom Hajiya fatima ALLAH ya Tsare hanya ya kiyaye, kuma ya shirya mana ‘yaya da jikiko, kuma a dage da addu’a insha ALLAH, ALLAH zai yaye mae. Ameen malam Ibrahim, insha ALLAH zamu dage da addu’a. Daga haka sukayi sallam.

Ta qarasa wajan drive suka wuce gida.
Bayan hajiya kaka taje gida tayi wanka ta wuta ta wuce part d’in ammi.

Tana qarasawa bakin qofar ammi ta fara nock. Daga ciki taji ammi tana cewa ashigo. A hankula ta fara murd’a handle d’in qofar ta shiga.
Tana shiga taga ammi akan sallaya da alama sallah ta idar. Amir kuwa da yake ta tsalle- tallansa akan gado da gudi yazo ya rungume kaka.

Dariya kaka tayi tace mai qiriniya, shima dariya yayi kafin yace ina alawata kinsiyo min?. Kaka tace aa bansuyo mah, kwab’e baki yayi alamin zai yi kuka tare da cewa sabida mae baki siyomin ba?. Sabida kanayin b’arna da qirinniya, kuka ya farayi tare dacewa na dae na.

Murmushi hjy kaka tayi tare da cewa da wasa nake mah ka dae na kuka gashi na siyo maka, ta fad’a tare da miqa mai laidar hannunta. Da murna ya karb’e tare da cewa bari naje wajan aunty zahara musha tare. Yana gama fad’ar haka ya fita da gudu.

Daga hjy kaka har ammi sai da sukayi dariya. Kafin ammi tace hajiya sannu da shigowa ki zauna mana. Gefan gado hjiy kaka ta samu ta zauna kafin tace, sannu da gida gaskiya maryam ina mamakin shaquwar da take tsakanin amir da zahra.

Duk gidannan ba wandda amir yakeso fa kamar zahra. Murmurshi ammi tayi sannan tace nima hajiya naga hakan fa gaskiya sun shaqu sosaii. Tom Masha ALLAH, ALLAH ya barsu tare, cewar hajiya kaka, ammi tace Ameen.

Sae da hajiya kaka tayi shiru na wasu lokita kafin tace yauwa maryam dama nazo ne muyi wata mahimmiyar magana. Ammi gyara zama tayi ta mai da hankalinta wajan hajiya kaka tare da cewa inajinki hajiya, mai ya faru?.

Ehhh dama akan mashkhur ne nakeso muyi maganar. Tom hajiya inaji.
Maryam dama inaso ki dage da yiwa mashkhur addu’a akan wadda kikeyi, koh ya rage munanan halansa. Sunkuyar da kai ammi tayi tare da cewa,

Wallahi hajiya bansan mai yake damun yaran nan ba kullum cikin addu’a nake mae amma abin kamar gaba yake sakeyi, koh shekaran jiya dana shiga bed room d’insa, samunshi nayi a bige sai bacci yake ga kwalaban kwayoyi da totalin, maganin mura a baje akan table,

Gashi yanzu koh na gayamai magana baji yake ba, wai yanzu nida d’ana ban isa na gaya mae mgana yajiba sai dae kishiya tace zata gaya mae yaji. Kuma duk irin laifin nan da yake ai katawa tai ta goya mai baya bata ganin laifin sa, ta qarasa maganar tana zubar da zafafan hawaye..............

Wanna page d’in na sadaukar da shi ga
pretty💔💔💔🥰🤗☺️. Karfa kuce nayi sanka abidda yasa na sadaukar da shi ga pretty💔💔💔 sabida kullum innai posting sai tayimin comment........

Sai ku biyoni page na gaba kuga wa zan sadaukarwa🥰...

Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA, Ina yi muku fatan alkhairi. Kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan Allah in kun karanta ku d’inga comment...........pls. Sabida hakan shi zai bani qarfin guwar jigaba da rubutawa.💜❤️💜

Typing............

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Free book.💜❤️💜

Typing..........

*Page 13*
Ta qarasa maganar tana zubar da hawaye.......

Nunfasawa Hajiya kaka tai tare da cewa haba maryam yanzu in kina zubarwa da Muhammad hawaye ai qara lalacewa zai yi. Gaskiya bana san ki d’inga kuka. Share hawayanta ammi tai tare da cewa Wallahi hajiya in banyi kukan nan ba bazan samu sauqi ba.

Kiyi haquri maryam. Kuma bari nagaya miki wani abu da baki saniba Wallahi mashkhur ba a cikin hayyacinsa yake wanna abubuwan ba . Da sauri ammi ta d’ago tana cewa ba’a cikin hayyacinsa yake ba hajiya mae ke damunsa?.

Jinjina kai hjy kaka tayi tare da cewa maryam tunba yau ba nasan Muhammad ba’a cikin hankalin sa yake ba. Kuma da banyi niyar na gaya mikiba so nake nabar zancan iya zuciya ta amma tindda naga kina shiga ma wuyacin halin na yanke shawarar in gaya miki.

Tabbas duk abidda Muhammad yake ba yin kansa bane bah, asiri da sammu ne kawaii ke d’a wainiya da shi. Zaro ido ammi tayi tare da dafe qir jinta, tana cewa asiri kuma hajiya?. Jinjina kai hajiya kaka tayi tareda cewa kwarai maryam asiri ne.

Innalilahi’wa’inna’illahirraji’un hajiya yanzu wazai iya yiwa mashkhur wannan muguntar haka?. Girgiza kai kaka tayi tare da cewa karki damu da sai kinsa wa yakewa Muhammad asirinnan kawai dai ki dage da yi mai addu’a.

Harga ALLAH hajiya kaka tana so ta gayawa ammi, momy ce take wa mashkhur wanna aikin amma bazata iyaba. Sabida bataso a samu sab’ani a tsakaninsu, kuma bata so ta raba kan matan d’anta, bugu da qari kuma bata san had’a fadan da zai ta da hankalin family d’in gidan.

Maganar ammi ce ta dawo da hajiya kaka zurfin tinanin da ta shiga, Hajiya dan ALLAH ki gayamin wa yake yiwa d’ana mugun asirki haka?. Tana tanbaya hawaye na zubo mata.

Kiyi haquri maryam ranar tunan asiri zatazo zaki sani nan gaba. Kuma bana sanki qara tanbaya ta akan sanin waye kewa Muhammad asiri, kuma ko da wasa karki gayawa mahaifin muhammad maganar nan koh wani can daban, inaso wannnan maganr ta zama sirri a tsakanin mu,

Kuma ki dage da yiwa Muhammad addu’a komai zai sai-sai ta. Kuma ki dae na sa damuwa a zuciyarki, ko wane d’an adam da akwaii tashi irin qadda rar, kinjini koh?.
D’aga kai ammi tayi tare da share hawayan fuskar ta, tace insha ALLAH hajiya zan dage da addu’a,

Dama ni ina tantama da canzawar mashkhur lokaci guda ashe asirine. Hakane maryam ke uwace addu’a uwa bata fad’uwa qasa banza insha ALLAH watarana sai labari. Haka Hajiya kaka tai ta rarrashin ammi har sai da zuciyarta tai sanyi. San nan ta koma part d’inta.........

WANENE ALHAI ABUBAKE WATO MAHAIFIN MASHKHUR?. WACECE AMMI?. WACECE MOMY?. MAE YA KWAWO QIYAYYA MAI ZAFI TSAKAIN MASHKHUR DA ZAHRA?. MAE

Please Login or Register in order to submit comment