Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki kai mashkhur ka dai na raina mana hankali fa.

Shima mashkhur cikin mamaki yace wlh ammi ba raina muku hanki nake ba to ni hasalima ba abinda ya ta6a shiga tsakanina da ita bare ma ai zancan ciki. Nan da nan mamaki ya sake rufe ammi da dady ko ta ina, wani kallon rainin hankali dady ya watsawa mashkhur tare da cewa, sannu sarkin maqaryata. Haba dady ammi ku yadda dani mana, wlh da gaske nake mai ne amfanin yi muku qarya kasan dai ban saba yima qarya ba, I swear I'm very seriously dady.

Ammi dai fuskar mashkhur tana nuna mata da gaske yake amma bata son mai yake zuciyar shi ba, ammi sabida tsabar damuwa da rashin sanin abinyi uban tagumi ta rafka. Dady kuwa jinjina kai yayi tare da cewa, okay ina result d'in naka yayi kyau ko kuwa dai. Mashkhur zaro wayar shi yayi daga aljiwu sanan ya shiga gallery ya nemo hoton result d'in shi ya miqawa dady wayar.

Dady qar6a yayi sanan ya fara karantawa, ammi kuwa sabida damuwa ko ta kan ruselt d'in bata biba d'an ita sam bata so a raba auran zahra da mashkhur gashi lamari yana son faskara. Jinjina kai dady yayi tare da cewa, congratulations ashe dai auran nata yayi ma amfani tinda gashi ADALILINTA ka mai da hankali ka fito da ruselt mai kyau har da offer.

Dady ADALILINTA kuma? Kwarai ai da badan kana so ku rabu da ita ba nasan bazaka mai da hankali wajan karatun ba tinda naga kwanakin baya ba karatun ne a gaban kaba. Mashkhur shiru yayi bai sake cewa komai ba. Dady kuma cewa yayi yanzu burinka ka sake ta koh? Da sauri mashkhur ya d'ago kai tare da cewa, haka be dady.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa, zaka sake ta amma sai na tabbatar da abubuwa biyu. Cikin mamaki mashkhur yace dady wana abu kuma?, miqamai wayar sa dady yayi sanan yace na farko sai na tabbatar ba abinda ya ta6a shiga tsakanin ku da ita in da gaske kake, na biyu kuma zan sama ido naga da gaske ka dai na shaye-shayan ko kuwa, daga nan har rana ita yau ko nan da qofar gida karka fita.

Kallan dady mashkhur yayi sanan yace haba dady sai kace yaro kuma sai a hanani fita?. Mashkhur kenan har yanzu baka wuce yaro a wajan iyayan kaba, amma bawai dan na takura ma na yanke hukuncin nan ba sabida nasan da gaske ka dai na shaye-shayan, ba dai kawai CCTV camera a gidan nan ba, ai zan tabbatar.

Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa, yanzu dady in har ka tabbatar da abubuwa biyun nan zaka cikamin ALQAWARIN mu kuma har nan da kwana nawa?. Kwarai mai sunan baba ai kyan alqawari cikawa in sha ALLAH zan raba auran, nan da one week wato rana ita yau, in dai na tabbatar da abu biyun nan, auran ku da mamana kamar an raba an gama bazan sake jan wani lokaci ba rana ita yau zahra ta dawo ba matar kaba dan nima lamarin ya isheni haka.

Lokacin da mashkhur yaji ance haka wani qasai taccan murmushi ya saki sanan ya miqe tare da cewa good night haka ya kama hanyar fucewa daga part d'in gaba d'aya. Dady kallan ammi yayi tare da cewa, mene kuma na tagumi ai hukuncin da na yanke yayi koh?. Kamar ammi zatai kuka tace yanzu yaya in da gaske ba abinda ya shiga tsakanin su kuma ya dai na shaye-shayan raba auran za kai da gaske?.

Janye mata hanu daga tagumin da tai dady yayi tare da cewa, to maryam ya kike so muyi in hakan ta kasance gaske dole a raba su tinda basa son junan su. Amma yaya a qara musu lokaci ko zasu so junan su. Hmm maryam kenan taya zasu so junan su har ke6ewa sukayi su biyu basu so junan su ba sai yanzu.

Hmm amma yaya ai baza su gane suna son junan suba sai sunyi nesa da juna koh? Maryam kenan ke dai karki dorawa kanki ciwan zuciya akan wanan lamarin ALLAH ya bamu d'a mai taurin kai ne, amma da abdul ne ai bazamu sha wahala sosai ba. Amma yanzu abinda zaki shine! Kije ki binciki mamana da gaske ba abinda ya ta6a shiga tsakanin nasu?.

Dady taya zan gane? Ko tayaya nema zaki gane in dai kika tambaye ta kina ganin mood d'in ta zaki sanan gaskiyar zancan. Kuma yanzu zaki tambaye ta basai gobe ba naga kamar sun samu wani good relation ita da shi, in kika bari zuwa gobe tam zasu iya canza zancan. Kwarai nima naga hakan kuma la lura da suna boye wani abu a tsakanin su wanda mashkhur baya so a sani.

Kwarai kuwa nima la lura da hakan ALLAH yasa alkhairi suke 6oyewa. Fuska ba walwala ammi tace ameen bari naje na binci ka daga haka ammi ta miqe tare da cewa, sai da safe. Shima dady miqewa yayi tare da cewa, ALLAH ya tashe mu lpy bari na wuce 6angare na zo ki rufe part d'in ki. Haka suka ranka suna tafiya suna qara jimamin wanan lamarin.

Dady yana fita ammi ta rufe qofar part d'in ta sannan ta juya ciki. Tana hawa sama drect bedroom d'in zahra da ilham ta wuce. Tana qarasawa ta fara knocking. Ilham tana jin ana knocking d'in qofa ta cewa, yaya ahmad hubby na sai gobe knocking d'in qofar ake inaga ammi ce kuma batasan yawan wayar dare by take care, daga haka ilham ta gintse kirana sanan ta miqe ta nufi qofa.

Tana zuwa ta bud'e qofar, ammi ta gani tsaye fuska ba walwala matsa mata tai tare da cewa, ammi sannu da zuwa?. shigowa ammi tai tare da cewa, zahra tayi bacci ne?. Gyad'a kai ilham tai tare da cewa, eh tun dazu da ta shigo ta kwanta. Wani irin kallo ammi tai wa ilham sanan tace ke mai kika tsaya yi har yanzu baka bacci ba?.

Shiru ilham tai ba amsa dan tasan ammi batasan qarya kuma ta nai mata qarya zata 6aro ta. Hmmm waya kika tsaya yi da shi kenan koh? Gyad'a kai ilham tai tare da cewa kiyi haquri. Hmmm kin san dai bana son wayar daran nan koh? ilham ki kiyaye karki qara bari nai miki magana akan haka kiyaye, jeki ki taso min zahra kice ta same ni a bedroom d'i na.

Tom ammi, daga haka ammi tai fucewar ta daga room d'in ita kuma ilham wucewa kan bed tai ta fara qoqarin tashin zahra. Ke zahra!! Zahra!! Cikin bacci zahra tace menene haka ilham ina bacci kike tashina?. Ammi ce take kiran ki, zahra tana ji ance ammi ta tashi tare da cewa, ammi amma bata ga ammi ba kallan ilham tai tare da cewa, ina amin take?.

Ta tafi haka tace ki same ta a bedroom d'in ta. Miqa zahra tai sanan ta miqe tace to sai na dawo in da raban bacci ya d'auki ni acan sai da safe. Tom shikenan ki rufe qofar amma dai ki dawo bana son kwanciya ni kad'ai wlh. Daga haka zahra tace to sanan ta fuce tare da rufo qofar, tana fita direct ta miqi hanyar dakin ammi.

Tana qarasawa tai knocking d'in qofar ammi da take kan gado a zaune d'aga murya tai tare da cewa, zahra shigo mana qofar a bud'e take. A hankula zahra ta murd'a handel d'in qofar ta shige baki d'auke da sallama. Da kyar ammi ta iya qaqalo murmushi dole tare da cewa, qaraso mana. Itama zahra murmushi tai sanan ta qaraso ta zauna kusa da ammi.

Mene haka kike sunkuyar da kai ko 'yar kunyar surukar nan kike min. Dariya zahra tai tare da cewa kai ammi ta fad'a tana kallan ta. Itama murmushi ammi tai bayan ta tsagai ta tace zahra magana nake so muyi dake banason qarya, duk da nasan bakyamin qaryar. D'agowa zahra tai jiki a sanyaye tace tom ammi inaji in sha ALLAH zan gaya miki gaskiyar abinda na sani.

Da gaske ba abinda ya ta6a shiga tsakanin da yaya ki mashkhur?. Zahra jin magana tai on expected dan haka ba shiri ta sunkuyar da kai. Mene haka zahra kunya ta kike ji kuma? Girgiza kai zahra tai tare da cewa, ammi ban gane abinda kike nufi ba. Wani siririn murmushi ammi tai tare da cewa, hmm zahra wai ke mai wayo koh? D'agowa zahra tai tare da kallan ammi tana cewa ammi da gaske nake fa.

Jinjina kai ammi tai sanan tace ina nufin bai ta6a saduwar aure dake fa kin gane ko nai miki 6aro-6aro da manya baki yadda zaki gane? Girgiza kai zahra tai tare da cewa, basai kinyi hakan ba na gane. Tom gayamin naji, ammi ta qarasa maganar tana zubawa zahra idanuwan ta. Girgiza kai zahra tai tare da cewa ni bai ta6a yimin hakan ba ammi.

Rass gaban ammi ya fad'i cikin zuciyar ta tana tattamar maganar zahra. Zahra ki tabbatar gaskiya kika gayamin kuwa?. Gyad'a kai zahra tai tare da cewa, ehh gaskiya na gaya miki ammi. Mai kuke 6oyewa tsakanin da mashkhur wadda mashkhur bayaso mu sani?. Girgiza kai zahra tai tare da cewa! Ba abinda muke 6oyewa ammi.

Ammi tana jin haka ta fara jin shakkar maganar da zahra ta gaya mata dan haka cewa, tai taso muje toilet na ganewa ido na gaske zancan da gaskiya lamarin da abin dubawa. Kallanta zahra tai tare da cewa, kai ammi. Harara ammi ta watsa mata tare da cewa, mene ko kunyar ammin taki kikeci ne, ai har yanzu baki wuce nai miki wanka na goye tasss a bayana ba. dariya zahra tai tare da cewa, hmm gaskiya ne ammi, amma dai baki yadda dani ba yanzu.

Na yadda dake mana zahra amma inaso na tabbatar da hakan ne. Miqewa zahra tai tare da cewa, tom shikenan ai zaki gani. Daga haka suka rankaya suka shige toilet d'in ammi. Suna shiga ba 6ata lokaci zahra ta cire dogwan wandda ta da pants sanan ta tsuquna kamar yadda ammi ta umar ce ta. Haka ammi tai checking d'in zahra in and out.

Amma abin mamaki shine, ammi gani tai zahra tana nan a rufe 6am a tsuke take ba alamun wani abun ya ta6a ciga ko kad'an. Jiki a sanyaye ammi tace nagani tashi kisa wandan ki. Daga haka ammi ta futo zuciya cike da zullumi ta haye kan gado tasan dai shikenan auran zahra da mashkhur ya qare. Sanan tana sake jinjina taurin kai irin na d'an nata mashkhur.

Zahra tana futowa ammi tace ta kashe musu globe d'in bedroom d'in, haka zahra ta kashe globe d'in ta kunna mara haske sanan ta hau kan bed kusa da ammi ta kwanta, gefe guda kuma ga ameer yana ta shar6ar baccin sa. Sun d'au kamar 5 minutes ba wada yacewa kowa komai kowa da abinda yake saqawa a zuciyar shi............

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Double page...............

Matsowa zahra tai sosai kusa da ammi suna face d'in juna tace ammi wai mai yake damunki ne naga lokaci guda kin canza?. A jiyar zuciya ammi tai sanan tace meye baya damuwa zahra nifa sam bana son a raba auran ki da yayan ki. Zahra sai taji bataji dad'i ba har zuciyar ta, amma a fili cewa tai to ammi yaza ai tinda kinga yaya mashkhur baya so.

Murmushi ammi tai sabida yadda zahra ta langwa6e murya kamar itama tana son abin wai duk dan ammi tace ba lefin tane ba. Ammi cewa tai to ke kina so kamar yadda nake so ne da zaki ce shi baya so duka ku biyun ai bakwa so. Ehh hakane ammi amma ai tinda kuna so da yaya mashkhur zai amince sai nai haquri kawai, dan ni inason ina faranta muku.

Zahra ba har cikin zuciyarta ta fad'i hakan ba kawai dai ta fad'ane dan ta wanke kanta, dan a daina ganinta da laifi. Aa zahra ai bazamu so ki cigaba da zama da abinda bakya so ba, muma muna son farin cikin ki. Murmushi jin dad'i zahra tai har cikin zuciyar ta, sanan ta rungumo ammi tare fa cewa, hmm ALLAH ya bar mana ke ammi.

Humm zahra naga alamun kwana biyu kinyi wayo sosai ba kamar da ba, ko da yake kin sha rainon mashkhur ba dolen ki ba. Aa ammi ba wani wayo kinsan ance mutum yana girma yana sake hankali koh? Itama ammi rungumo ta tai tare da cewa, hakane kewai dai so kike ki cemin kin qara girma koh? To na gani ai basai kin fad'a ba.

Kwanciya zahra ta zake yi a jikin ammi sanan tace aaa ni ba haka nake nufi ba. Shafa bayan zahra tai ammi tare da cewa, to zahra ALLAH yayi miki albarka ya kawo miki mijina na gari mai kirki in kun rabu da mashkhur. Harda zahra zata cewa ammi baga yaya abdul ba amma sai taji kunya tai shiru. Bazaki ce amin ba ko kunya kike ji ne, ammi ta fad'a cikin zaulaya.

Lumshe ido zahra tai tare da cewa, ai na fad'a a zuciya ta, aaa ni ban yadda ba a fili nake so ki gaya. Murmushi zahra tai tare da cewa, to ameen. Itama ammi murmushi tai tana qaraji son zahra yana shiga zuciyar ta sosai da sosai dan ita ammi har yau gani take kamar ita ta haifi zahra da kanta sabida yadda take soyuwa a zuciyar ta. Haka dai zahra da ammi bacci ya kwashe su rungume da junan su.

Washe gari.................

ASUBAYI.

Kiran sallah asubaye ne ya tashi ammi a hankula ta bud'e idanuwan ta sanan ta fara addu'ar tashi daga bacci. Bayan ta gama addu'ar tashi tashin tai zahra ta somayi wadda take kwance a gefan hanun ta da qirjin ta. Zahra!! Zahra!! A hankula zahra ta bud'e idan ta tare da cewa na am ammi. Tashi ki sallah asuba tayi. Jiki ba kwari zahra ta bud'e idanuwan ta har ga ALLAH bacci bai isheta ba.

Ammi tana miqewa ta canza globe d'in d'akin daga mara haske zuwa mai haske sanan ta shige toilet. Bayan ta futo itama zahra miqewa tai jiki ba kwari ta shige toilet d'in, bayan ta d'aura alwala dawowa tai sanan ta bud'e wardrobe d'in ammi ta d'auki hijab da wata daddumar sanan ta shinfid'a a gabas ta tayar da hiqama.

Bayan zahra ta idar da sallah ta gama lazami ko azkhar d'in safiya batai ba ta koma gado kusa da ameer tai kwanciyar ta. Ammi kuwa bayan ta gama sallah tai azkhar d'in safiya addu'o'i tai kala-kala. Misalin qarfe 7 na safe ta miqe da ka daddumar ta kashewa zahra da ameer globe sanan ta fuce daga d'akin tana fucewa ta sauka qasa ta wuce kicin domin fara had'a breakfast.

MASHKHUR................

ASUBAYI

kiran sallah asubayi ne ya tayar da mashkhur daga baccin da yake, yana tashi ya shiga toilet ya d'aura alwala sanan ya fito. Bayan ya fito ya sa jallabiya sanan ya fuce daga bedroom d'in. Yana zuwa qofar part d'in su ya tarar da abdul yana qoqarin bud'e qofar part d'in. Cikin sakin fuska yace yaya mashkhur barka da asuba. Murmushi mashkhur yayi cikin sakin fuska yace barka dai abdul,.

Yanzu mashkhur ba laifi ya dai na jin haushin abdul kamar jiya zuciyar shi ta wuce. Juyawa mashkhur yayi tare da cewa, bari naje na tashi su haidar, tom yaya mashkhur bari na raka ka. Ai kullum basa tashi sallah sai na tashe su yauma mantawa nai, haka suka ranka suna tafe suna hura har suka qarasa qofar d'akin su faruq. Hannu mashkhur yasa ya murd'a handel d'in qofar sanan ya shiga shima abdul ya biyo bayan sa.

Kowa yana kwance akan bed d'in sa, haidar gefan sa ga littattafan tarihin rayuwar 'yan ball shi kuma faruq gefan sa hoto nan 'yan ball, ga tv sun kamo tashar 'yan ball ga dukkan alamu ma tv a kunne ta kwana. Tsaki mashkhur yaja tare da kallan abdul yace! Kaga iskanci koh? Hmm kai dai bari yaya mashkhur ai haka nake ta fama dasu har na gaji na zuba musu ido, in dai akan 'yan ball d'in nan ne kullum su suke kallo watarana ma kwana suke suna kallan ball.

Tsaki mashkhur yaja tare da qarasawa kan table ya d'auki cup ya tsiyayi ruwa a glass jug sanan ya nufi haidar da yake bed d'in shine a farko ya watsa mai rabin ruwan a fuska. A firgice ya tashi tare da cewa, haba yaya abdul kayi haquri mana. Mashkhur qarasawa wajan faruq yayi shima ya sharara mai ragowar ruwan a fuska a firgice ya tashi tare da cewa! Kai haidar wanan wana kalar iskanci ne wlh sai na Rama.

Kuwa da wanda yake zaso zai gani ya watsa mai ruwan haidar yana zatan yaya abdul ne shi kuma faruq yana zatan haidar ne kwatsam sukaga yaya mashkhur tsaye fuska a d'aure. Gaba d'ayan su shiru suka suna kallan mashkhur. Fuska a d'aure mashkhur yace sannu 'yan iska muna fukai kawai, da sauri suka d'ago suna kallan sa. Ehh mana munafukai mana bakusan alamomin muna fukai ba har da rashin son sallah asuba.

Inaga duk cikin ku ba wanda yayi addu'ar bacci amma kunsa hotonan kafurai da littafan su a gaban ku ga tv a kunne kun kunno tashar 'yan ball koh? Su suna can basu san da zaman kuba ku kunan kuna 6ata lokaci. Wlh daga yau sai yau na sake ganin kun kunna tv ko kun ajiye abinda ya danganci 'yan ball in zakuyi bacci sai jikin ku ya gaya muku.

In sha ALLAH zamu kiyaye haidar ya fad'a hakan , mashkhur kuwa cewa yayi karma ku kiyaye ya rage naku ku kwana kuna kallan kafurai ku kasa fita gai da uban gijin ku sabida iskanci masallancin ma a cikin gida yake amma ku kasa fita kullum sai an tashe ku, has from today ba wanda zai qara tashin ku sallah asubayi.

Kuma in baku tashi da kan kuba na shigo da ruwa zan ringa tashin ku kubar ganin yau na tashe ku da wannan ruwan in na dawo next time da ruwa mai sanyi wadda ya fara qanqara zan tashe ku. In sha ALLAH daga yauma mun dena koh haidar faruq ya fad'i hakan yana kallan haidar gyad'a kai haidar yayi tare da cewa, hakane yaya mashkhur bazamu sake ba.

Ku tashi kuyi alwala ku wuce masallaci kuma karku bari ko raka'a d'aya ta wuce ku daga haka mashkhur ya kalli abdul tare da cewa, abdul tawo mu tafi. Suna fita haidar ya kalli faruq tare da cewa, shikenan kuma yanzu mun dai na abinda muke so. Sosai ma kuwa ai tinda yaya mashkhur ya dawo mun gama watayawa a gidan nan kuma sai dai muyi karatun qur'ani cewar haidar.

Jinjina kai faruq yayi tare da cewa, ai in bamuyi wasa ba har filin boll d'in ma mun dai na zuwa. Haidar cewa yayi oho ai mu muka jawa kan mu. Faruq cewa yayi kai dai ka jaza mana sai da nace ka kashe tv in zaka kwanta kaqi. Kaji qarya kace ni na kwaso littattaffan 'yan ball d'in na kawo ma kan bed nace ka karanta har kai bacci ka barsu ya shigo ya gan su kawai malam kace mu muka jazawa kan mu cewar haidar.

Faruq cewa yayi Hmmm gwara mu shiga toilet muyi alwala kar a tayar mu jawa kan mu wani laifin da wanan musun da muke, daga haka faruq da haidar suka shige toilet domin 'yan alwala. Bayan sun fito suka fuce suka wuce masallaci. Ni kuwa amina bayero nace hmm yara kenan sai kace ba 'ya'yan ammi ba da kun kwaso halin mashkhur yana yaro da kun huta ga karatun addi ni dana boko gashi baya wani supporting d'in 'yan ball.

MASHKHUR...........

bayan ya dawo gada masallaci dakin motsa jiki ya wuce, ba shi ya fito ba sai qarfe 7 na safe. Yana fitowa ya koma d'akin sa yayi wanka sanan ya shirya ya fuce daga bedroom d'in. Yana fita daga part d'in su direct part d'in ammi ya wuce, mashkhur yana shiga ya wuce sama domin zuwa wajan ammi ya gai da ita. Mashkhur ya dai ji qarar mutum a kicin amma bai yi tinanin ammi ce a ciki ba, shi yasama ya haye sama.

Mashkhur yana qarasawa bedroom d'in ammi ya ya murd'a handel d'in qofar, sanan ya shige. baza ido mashkhur yayi akan bed amma bai ga ammi ba sai zahra da ya gani kwance da ameer a kusa fa ita. Mashkhur yayi tinanin ko ammi tana toilet dan haka globe d'in d'akin ya kunna mai haske sanan ya zauna akan sofa da take feces d'in bed. Mashkhur zubawa zahra ido yayi yana kallon ta, kwance take amma ta bawa mashkhur baya, mashkhur in idanuwan sa dai-dai suke gani sai yace!

The same irin kwamciyar da zahra tai a Russian daran da ya shiga bedroom d'in ta. Rigar nan tata ta yaye ana iya ganin ugun ta, lumshe ido mashkhur yayi ya kawar da kai yana d'an tinanin dare da suka ai kata wanan lamarin shida zahra. Mashkhur dayaga shirun ammi yayi yawa hakan ne ya tabbatar mai da ammi bata nan, da lm haka miqewa yayi da niya fucewa.

Mashkhur yana qarasowa wajan bed mai ma kwan ya fuce kamar yadda yayi niya, sai ya tsaya cak yana qarewa zahra kallo. Zuciyar shi tana saqa mai abubuwa kala-kala ga wani feeling d'in ta da yake ji yana taso mai. A hankula mashkhur ya qarasa kan bed d'in ya zauna a bayan zahra yana qarewa kyakyawan ugun nan nata kallo.

Mashkhur bai san sanda ya kai hannu ya shafa ugun zahra ba, yana shafawa rigar zahra ta sake yayewa har ana iya ganin cikin ta da cibiyar ta. A hankula mashkhur ya shafa shafafan cikin zahra ya kai hannu kusa da cibiyar ta kenan yaji muryar ameer yana cewa! Yaya mashkhur kai ne? Da sauri mashkhur ya janye hanunsa daga cikin zahra tare da cewa, eh ameer har ka tashi.

Cikin aunty zahra kake ta6awa koh? To sai na gayawa ammi da dady da aunty ilham da yaya abdul da hjy kaka da aunty ruma da aunty rukee da ya faruq da ya haidar, harda 'yan makarantar mu. Cikin mamaki mashkhur yace kai ameer mai zaka ce musu? Haka zance yaya mashkhur yana ta6awa aunty zahra ta ciki da cibiya. Zaro ido mashkhur yayi tare da cewa, kai ameer ba fa ta6awa nake ba.

Tashin ta zanyi, to sabida mai zaka tasar min auty zahra ta tana bacci? Ameer ya watsawa mashkhur tambayar, sabida safiya tayi mana. Aa ni dai gaskiya sai na gayawa su ammi suyima maga karka sake tashin aunty zahra ta tana bacci. Haba ameer karka gaya musu ko baka so na siyarma alawa ne, noqe kafad'a ameer yayi tare da cewa,

Please Login or Register in order to submit comment