Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da izinin su naje. Su suke auran ki ko ni?, ta6e baki zahra tai tare da cewa babu ko d'aya a ciki ni bani da wani aure. Cikin mamaki mashkhur yace oh iskanci ki har ya tashi daga rungume maza da auren ki ya koma baki da aure.

Oh ai da gaske nake bani da wani aure a yanzu da ne dai nasan a d'auramin aure da kai, amma a halin yanzu nasan ka dad'e da saki na kamar yarda kake fad'a takaddata kawai nake jira. , kiyi uban mai da takaddar? Ah shedar ina da lasisin yin wani auran mana. Oh to bazan sake kin ba, cikin mamaki zahra tace kai sabida mai ba haka kake cewa kullum zaka sake ni ba yau kuma kace bazaka sake ni ba?.

Kwarai haka nake cewa da amma yanzu bazan sake kin ba zama dani da ke yanzu muka fara ke ko mutuwa nai bazaki aure ba. Tabb lallai yaya mashkhur da ma ka dena wasan nan dan wlh bana ganewa nake ba kawai ka ban takadda ta ni na matsu ka sake ni na wuta aa. Hmmm ai kuwa zaki gaji da jira dan bazan ta6a sakin ki ba. To sabida mai bazaka sake ni ba zahra ta fad'a hankali a d'an tashe.

Shiru mashkhur yayi na wasu lokutan can kuma yace zan gaya miki dalilin amma ba yanzu ba. Oh kaji da shi saki kamar anyi an gama, lallai zahra yanzu rai ni ya fara shiga tsakani na da ke, ko da yake bazan yi mamaki ba tinda kina tare da wanan mara kunyar qanwar taki. Cikin mamaki zahra tace to itama ta shigo list kenan mai tai ma. Ban sani ba zo ki raka ni.

Wani kallo zahra tai wa mashkhur sheqeqe sanan tace na raka ka ina?. Kizo ki gani sace ki zanyi ne ko kuwa?, oho wa ya sani ko sace nin za kai. Ai kuwa dai nayi asara tinda na rasa wanda zan sace sai matata. Kai mata kuma ni kar ka sake cemin matar ka kai ko kunya ma bakaji in kace ni matar kace?. Taya zanji kunya tinda na san gaskiya na fad'a.

Ah wace gaskiya ko ka manta sanda kace kar na sake cewa kai mijina ne to ni ma kar ka qara cewa ni matar kace. To yanzu na amince ki ringa cewa ni minin ki ne, to bazan fad'a ba d'in kai ba mijina bane. Hanun ta mashkhur ya ruqo tare da cewa tawo dai mu tafi kar ki 6ata min lokaci. Hanunta zahra ta fizge tare da cewa ni ba inda zani kam.

Wlh kika sake bari nace kizo mu tafi d'aukar ki ma zanyi a hannu. Hmmm lallai yanzu sai ka d'auke ni a hannu kenan? Wani kallo rainin hankali mashkhur ya zubawa zahra. Zahra kuwa cewa tai nifa ban gane ba sai kace nazo na raka ka wai na raka ka ina?, mene abin mamaki kike raka wasu ma bare mijin ki dallah ni zo mu tafi.

Zahra turo baki tai tare da cewa hmmm ka dai je can ka nemi matar ka ba dai ni ba. Hanun ta mashkhur yaja suka fara tafiya. Zahra tayi-tayi ta fizge hanun ta kasa, ni sakar min hanuna naji zan raka ba sai kayi min dole ba. Sakin ta mashkhur yayi tare da cewa to muje dai bakin mota fa kawai zaki raka ni ai gwara na koya miki rakiyar miji kafin mu tare.

Tabb wlh sai dai ka nemi da wanda zaka tare ba dai ni ba ko kaje ka d'auko zee ku tare. Mashkhur jin maganar yayi unexpected amma sai ya basar da zancan kamar dai bai ji abinda zahra tace ba, sabida shi sam ya manta da wata zee ma sai da yanzu zahra ta fad'a sunan ta ya tina da ita. Haka mashkhur da zahra suka cigaba da tafiya gwanin sha'awa har suka fita daga part d'in su suka nufi parking space d'in gidan.

Suna isa zahra tace to gashi nan dai na raka ka zan koma. Ruqo hanun ta mashkhur yayi tare da cewa aaa haba mene na sauri ki qarasa rakani bakin motar mana. Wani siririn tsaki zahra taja tare da cewa kai nifa ka ishe ni haka. Nan da nan mashkhur ya had'e rai lokaci guda annurin fuskar sa ya 6ace cikin kakkausar murya mashkhur yace daga rana mai kama ta yau karki sake yi min tsaki.

Sai a lokacin ma dai zahra ta tina ashe mashkhur baya son tsaki, hmmm lallai ma ta auna arziki da bai sharara mata mari ba kamar yarda yakewa sauran yaran gidan in su kai mai tsaki. Kawar da fuska zahra tai tare da cewa to, daga haka dai suka qasa bakin motar har mashkhur ya bud'e ya shige, zahra kuwa sai taji tsoran shi ya d'an kama ta ya had'e ran nan nasa kamar da yarda yake mata a rasha.

To a dawo lafiya zahra ta fad'a a taqai ce, juyowa mashkhur yayi tare da sakarwa zahra wani qasai taccan murmushi mai sace zuciyar masoya yace ALLAH yasa hakan matata. Ta6e baki tai tare da cewa gaskiya ni ka dena cemin matar ka nifa ba matar ka bace sabida mun kusan rabuwa. Hmmm lallai yarinya kenan ni da ke mutukaraba ta kalmin kaza wlh ko mai zai faru bazan ta6a sakin ki ba har abada muna tare..................

Mu had'e a next page gobe.

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 113*

Hmmm lallai yarinya kenan ni da ke mutukaraba ta kalmin kaza wlh ko mai zai faru bazan ta6a sakin ki ba har abada muna tare..................

Cikin mamaki zahra tace tab to sabida mai baza ka rabu dani ba? nifa ba son ka nake ba bare kace zakamin dole. Oh ALLAH koh? to nima ai ba son naki nake ba kuma ni ban ce ki so ni ba amma saki ne bazan ba zama dani dole ko kina so ka bakya so. Hmmm to mu zuba mu gani ai da da yanzu ba d'aya ba so kake na cigaba da zama da kai, kai ta muzguna min kamar da kenan to wlh bazan iya ba kuma dole ka sake ni.

Zahra tana gama fad'in hakan ta juya ta bar wajan rai ba dad'i. mashkhur bin zahra yayi da ido yana qare mata kallo cikin zuciyar shi yana tinanin mafita, hmmm zaki gane baki da wayo yau ba sai gobe ba sai na aika ta miki abinda dole sai an bani ke na cigana da zama da ke ko kina so ko bakya so. Daga haka mashkhur ya tayar da motar shi ya fici daga gidan zuciya fall cike da so da qaunar zahra.

Zahra tana tafiya daga wajan mashkhur bata zame ko ina ba sai bedroom d'in yaya abdul. Baki d'auke da sallama zahra ta murd'a handel d'in qofar ta shige. Zahra tana shiga kamar yarda tai tinanin ta tarar da nana da ya abdul harma da ilham suna hira, zama tai a gefe ba tare da tace komai ba zuciya cike fall da baqin cikin abinda yaya mashkhur ya gaya mata akan wai ba zai sake ta ba.

Baby na waya ta6a min ke haka kika 6ata rai nifa bana so naga kina fushi bama yayi miki kyau abdul ya fad'i hakan yana tsare zahra da kyawawan idonuwan sa. Murmushi dole zahra ta qaqalo tare da cewa ah ba komai yaya abdul waye kuwa zai 6atama ni, bayan kuma ina da kai ba abinda yake damuwa. Hmmm haka nake son ji my zahra ALLAH ya kare min ke kyakyawa ta.

Murmushi zahra tai tare da cewa ameen yaya abdul daga haka ta miqe tare da cewa to nana aku sarkin magana kuzo muje muci abinda ni yunwa nake ji. Murmushi nana tai tare da cewa to aunty ilham taso mu tafi yaya abdul in muka gama zan dawo mu cigaba da hirar ko, fuska a sake abdul yace to shikenam nana sai kin dawo ina jira. Daga haka zahra ta fuce ilham da nana suka bi bayan ta.

Suna fita nana tace kai amma gaskiya wannan yaya abdul d'in yana da kirki sosai aunty zahra. Murmushi zahra tai tare da cewa kad'an ma kika gani in dai yaya abdul d'i na ne ai yaya abdul yana son mutane sosai ga kirki halin sa kenan. Murmushi nana tai tare da cewa gaskiya dai kam naga alama gashi kyakyawa da shi. Murmushi ilham tai tare da cewa to nana ko dai ko dai.

Wah ita tama isa ilham kin manta dani ne zahra ta fad'a tana zaro ido. Tsaki ilham tai tare da cewa kai zahra kina da matsala ina kika baro mijin naki. Hmmmm nifa wanan rai nin hankalin naku ya ishe ni sai ku ta cewa zahra tana da miji kuma nasan ba haka bane. Murmushi ilham tai tare da cewa to shikenan nana tinda baki yarda ba zo muje ki tambayi ammi.

Yauwa da kyau ai kuwa sai na tambaye ta. Nana tana gama rufe bakin ta suka hangi faruq da haidar sun dawo daga school, tsayawa su ilham suna jiran su qaraso, tin daga nesa faruq da haidar suke sakin murmushi farin ciki sabida ganin su zahra. Bayan sun qaraso suka gaisa fuska a sake nana taji dad'in hakan sosai yarda taga faruq da haidar sun sakar mata fuska kamar dai sun san ta.

Bayan su faruq sun wuce 6angaran su nana cewa tai kai gaskiya wanna suma suna da kirki sosai, qanan yaya abdul ne suna kama da shi maman su d'aya koh?. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aaa wanan fa suma ammi ce ta haife su, shi abdul momy ce ta haife shi shida rukee da ruma kuma kin san yanzu rukee ta rasu. Cikin tausayawa nana tace hmm abin tausayi ai momy bata da kirki ban son yarda akayi abdul ya zama mai kirki ba.

Wlh ni a tinanina ma wanan ne d'an momy, ga kyau iya kyau amma ba shi da sakin fuska sosai,. Murmushi ilham tai tace wai yaya mashkhur kike nufi?. Da sauri nana ta d'aga kai tare da cewa shifa wlh yana da kyau kamar shi yayi kansa amma bashi da kyan hali yayi ta shawa mutane kuna baya son magana fuskar nan tasa a tamke kamar fuskar shanu. Dariya ilham da zahra suka saki a tare.

Kai amma nana baki da kirki yaya mashkhur d'in kike cewa haka zahra ta fad'i hakan tana sake sakin dariya. Hmmm ai wanan da kika gani shine mijin yayar ki zahra ilham ta fad'a tana sakin murmushi tsokana. Nan da nan ta had'e rai it am kuma nana cikin mamki ta zaro ido tare da cewa au haba shine babban yayan naku da kuka cewa shi aka aura zahra ni kuma naqi yarda. Gyad'a kai ilham tai tare da cewa eee shine mana.

Zahra kuwa nan da nan ta sake had'e rai kamar zatai kuka, kai aunty lfy naga kina had'e rai ko dai ba shi bane?. Rai ba dad'i zahra tace shine mana nana qarya za'a yi miki ne?. To amma naga kina shan kunu? Hmmm wlh nana wai bata son shi cewar ilham. Kai aunty zahra sabida mai bakya son shi, ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa hmmm nana kenan bazaki gane ba amma ni bana son shi ki taya ni da addu'a ALLAH yasa ya sake ni bana son shi wlh.

Kai aunty yanzu wanan kyakyawan zaki ce bakya so jibe shifa kamar shi yayi kan sa duk inda ake neman cikakyan namiji mai kyau da zati ya kai amma zaki rabu da shi?. Tsaki zahra taja tare da cewa ke kikaga kyau a tattare da shi amma ni ban gani ba kuma ba son shi daga haka zahra tai gaba rai a 6ace. Jinjina kai nana tai tare da cewa wai lallai abun babba ne ni tinda nake ban ta6a ganin aunty zahra ta 6ata rai ba sai yau.

Murmushi ilham tai tare da cewa hmm ki rabu da ita zata sauko da kan ta. To ALLAH yasa amma gaskiya ni bai birge ni ba sabida bashi da sakin fuska ba fara'a ba magana, murmushi ilham tai tare da cewa ke dai bari nana haka yake ba iya ke kad'ai ba yakewa hakan ba shi sam baya son magana da hayaniya ne haka halinttassa take.

Tabbb aunty ilham wayaga zaman bebaye ai yanda zahra take shiru-shiru d'in nan shi ma baya son magana, wlh zaman bebaye zasuyi akai tafiyar. Dariya ilham tai sanan tace to nana zama na nawa su da suka zauna a russian sukayi shekar da watanni,. Cikin mamaki nana tace haba aunty ilham ai ni baku bani labarin nan ba amma naga bata haiwu ba?.

Kai nana haiwuwa kuma suda basa son junan su akayi auran daga shi har ita ba wanda yake so akayi auran amma yanzu dai gani nake kamar yaya mashkhur ya fara son ta. Hmmm tab gaskiya dai ni bana son su rabu sabida sun dace sosai kawai dai dan shi baya son magana ne kuma baya sakin fuska. Hmmm ke dai bari nana nima bana son auran nan ya rabu kullum addu'a nake ALLAH ya sasanta tsakanin su.

To ameen dai amma ni ko sun sasanta in suka tare a gidan su ba lallai ne na ringa zuwa gidan sosai ba sabida bashi da sakin fuska sai naga kamar ma shawa mutane kunu yake haka kurum wataran ya dake ni. Dariya ilham tai tare da cewa kai nana bakya rabo da abin dariya wlh. Daga haka nana da ilham suka rankaya part d'in ammi suna tafe nana tana ta kawowa ilham complain d'in mashkhur.

Bayan sun qarasa ciki suka zauna suka ji abinsu suka sha hira da ammi. Shima bayan dady ya dawo yayi farin ciki da zuwan su zahra sosai da sosai kuma sun sha hira sosai. Zahra da taso su kwana ammi tace yau zasu koma tinda dai mama batace su kwana ba. Dama ammi tayi hakan ne sabida mashkhur, kar ya 6allo masu ruwa tasan zai aikata hakan tinda ya fara son zahra. To ammi kafin su tafi ta kira zahra ta ja mata kunne sosai game da mashkhur, akan ko waya ya bugo mata karta yarda ta amince da soyayar shi da wuri sai yayi laushi sosai.

Zahra tayi mamaki da taji ammi tace mashkhur yana son ta dan ita bata ba6a tinanin ko a mafarki mashkhur zai so mai kama da ita ba bare ita. A zuciyar zahra kuwa ta d'au alwashin baza ta ta6a amincewa da mashkhur ba dole ya sake ta ta auri yaya abdul tinda shine za6in ran ta ba yaya mashkhur ba.

Nana kuwa lokaci guda suka saba da abdul da yake ita nana tana son mutum mai sakin fuska kuma gashi fari haka su kai ta hirar su kama da can sun san junan su.
Misalin qarfe 5 na yamma driven su zahra ya d'auke su domin komawa kaduna, zuciyoyin abdul da zahra cike da kewar junan su.

Mashkhur...........

Sai bayan kiran sallah magriba sanan ya dawo gidan,. Zuciyar mashkhur cike fall da qudirin sa akan zahra, yau mashkhur ya qudirta a ransa ko mai zai faru sai ya kau da abinda yake tsakanin shi da zahra, ko ya samu a bar mishi matar sa su koma gidan su, su tare. Bayan mashkhur ya futo daga motar shi direct part d'in ammi ya nufa dan yasa zahra a idanuwan sa kafin ya aika ta mata aika-aika.

Mashkhur yana sa qafarsa a qofar babban falon ammi da niyar shiga shi kuma abdul yana fitowa. Oh yaya mashkhur sai yanzu ka dawo kenan sannu da dawowa. Yauwa abdul wlh sai yanzu na dawo, jinjina kai abdul yayi tare da cewa kai aikuwa kayi dare gashi har su ilham sun tafi bakuyi sallama ba, a zabira mashkhur yace yaushe suka tafi kuma.

Mamaki ne ya kama abdul ganin yarda mashkhur ya zabura daga jin ance su zahra sun tafi, amma sai ya d'an basar yace wlh tin dazu wajan qarfe 5 suka tafi sabida kar suyi dare a hanya. Mashkhur danne zuciyar shi yaya ya d'an basar tare da sakin fuskar sa yace okay to ALLAH ya sauke su lfy ALLAH yayi bazamuyi sallah ba. Ameen yaya mashkhur, daga haka dai mashkhur ya shige ciki zuciya cike da baqin ciki shi kuma abdul ya wuce part d'in su.

To fa mashkhur yau bacci ya gagara da ya rufe ido yake ganin zahra ya gama tamawa yau zasuyi first night d'in shi da zahra amma kashh ALLAH bai ba. Ga wani irin mugun son zahra da yake addabar mashkhur. Can mashkhur yace to yanzu kuma sai yaushe zan sake ganin ta? Zuciyar mashkhur ce tace mai tabb ai kuwa ba rana sai dai kaje kaduna. A fili mashkhur yace tabb ALLAH ya sauwaqe na bita kaduna dan ina son ta. To ranar dai haka mashkhur ya kwana bai rintsa ba sabida so da tinanin zahra.

KADUNA.

To su zahra sun sauka garin kaduna lafiya, bayan driver yayi parking, suka sauka sanan suka shige ciki. suna shiga ciki gidan zahra ta wuce bedroom ta shiga toilet tai wanka sanan ta fito ta gabatar da sallolin magriba da isha'i, bayan ta idar ko abinci bata nema ba ta bi lafiyar gado ta kwanta. Jikin zahra yayi sanyi sosai da jin cewa wai mashkhur yana son ta abin ya girgiza ta kuma ya bata mamaki sai, duk da har lokacin bata gama yarda da cewa mashkhur son gaskiya yake mata ba kwai tafi karkata da so yake su tare ya cigaba da zalin tar ta, abinda zahra take ayyanawa a ran ta kenan.

To haka dai zahra tai ta fama da tinane-tinane kala-kala. Har nana tazo tai bacci amma zahra ta kasa runtse ido ta rasa mai ke damun ta, abin mamaki har ilham ta gama wayar dare ita da ahmad itama tai bacci amma zahra ta kasa. Zahra tana rufe ido magaganun mashkhur suke dawo mata kwakwalwa. Yarda ya ringa cewa bazai ta6a sakin ta ba har a bada da kuma yanda ya ringa cewa mata matar shi hakan ba qaramin tayarwa da zahra ankali yake ba, ranar dai zahra itama bata iya rintsawa ba.

Washe gari.......

Yau zahra haka ta wani sukuku a gidan nan sam ta kasa walwala abu biyu zuwa uku ne suke damun zahra. Na farko mamakin wai mashkhur yana son ta na biyi kuma baqin cikin mashkhur yace bazai sake taba, na uku kuma tana kokwan tan anya mashkhur ba wata gadar zaran mugunta yake shirya mata ba. Haka dai zahra ta wani ranar ba walwala, wini tai a kwance akan bed tana tinani sallah ce da cin abinci kawai yake tashin zahra kamar dai wata mara lpy.

6angaran nana kuwa tini ta bawa maman ta labari akan zahra da mashkhur ba son juna suke ba amma wai yanzu kamar dai mashkhur d'in ya fara son ta. Hakan ya bawa mama mamaki sosai, ita da take ganin d'iyar ta tana da ciki an kusan haifa mata jika ashe zancan ba haka yake ba. Amma sai ta yi addu'a a zuciyar ta akan ALLAH yasa zahra da mashkhur su fara san junan su sabida ita bazata so a raba auran ko dan halaccin su ammi.

Washe gari.

Tini zahra ta saki jikin ta ta fara walwala kamar da duk tabi ba watsar da maganar mashkhur gefe kuma tana sake addu'a akan ALLAH yasa da wasa yake, kuma ALLAH yasa ya sake ta ta wuta da wanan wahalar.

One week a go.

MASHKHUR.

Abu kamar wasa ya koma gaske mashkhur yanzu mugun son zahra yake, in yana cin abinci tinanin zahra in yana drive tinanin zahra yake in yana zaune tinanin zahra in yana kwance tinanin zahra in yana bacci mafarkin zahra. Wani irin mugun son zahra ne ya kama mashkhur ta ko ina sai yayi kwana biyu bai yi magana da kowa ba sabida tsabar qaunar zahra, kuma gashi mashkhur yace bazai je kaduna ba, ammi da dady kuwa sun ce ba ruwan su, yaje ya dawo da zahra da kan sa in yana son su cigaba da zaman aure..................

Hmmm kuna ganin mashkhur zai je kaduna kuwa?.

Ko yaje kaduna kuna ganin zahra taza amince da soyayar shi kuwa?.

Yau naso nayi muku double page amma ALLAH bai yi ba, mu had'e a next page gobe dan jin ya zata kaya.

Sorry mashkhur. 😂😥


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing...........

*page 114*

Wani irin mugun son zahra ne ya kama mashkhur ta ko ina sai yayi kwana biyu bai yi magana da kowa ba sabida tsabar qaunar zahra, kuma gashi mashkhur yace bazai je kaduna ba, ammi da dady kuwa sun ce ba ruwan su, yaje ya dawo da zahra da kan sa in yana son su cigaba da zaman aure..................

Kamar dai kullum mashkhur yana kwance a bed yana tinanin zahra. Wani irin mugun son zahra ne yake damun mashkhur, har takkaddar gurbin samin aikin mashkhur ta fito amma ko ta kanta bai biba sabida ba itace a gaban sa ba zahra ce kawai a gaban sa. Da kyar mashkhur ya iya miqewa ya shiga toilet ya d'auro alwala sanan ya fito ya saka jallabi ya wuce masallaci. Bayan mashkhur ya fito daga masallaci yana shigowa gida bai tsaya ko ina ba sai wajan ammi.

Murd'a handel d'in qofar d'akin mashkhur yayi baki d'auke da sallama ya shige ciki. Zaune ya tarar da ammi akan sallah ga dukkan alamun bata dad'e da idar da sallah ba. Jiki ba kwari mashkhur ya qarasa wajan ammi ya gai da ita, bayan ya gama gai da ita samu waje yayi gefan ta ya zauna. Bayan wasu lokutan mashkhur yace ammi?, na'am mashkhur menene?.

Ba 6ata lokaci mashkhur yace ammi zahra, kallan sa ammi tai cikin mamaki tace zahra kuwa mai tai ma. Ni ba abinda tai min kawai so nake ta dawo ammi wlh zaman nan nata acan ya isa haka. Hmm mashkhur kenan zancan kake so ban gayama zahra bataza ta6a dawowa da kan ta ba in ka matso ka bita har kaduna ni dan ALLAH ka barni na wuta da maganar zahra nan.

Haba ammi dan ALLAH kuce ta dawo haka nifa na gaji da wanan abu. Ta6e baki ammi tai tare da cewa sai kuma kayi mashkhur, gwara ka canza wani zancan. Rai ba dad'i mashkhur ya tashi ya fuce daga d'akin. Yana komawa d'akin sa ya d'auki wayar shi ya kira ahmad. Bayan sun gama gaisawa mashkhur yacewa ahamd dan ALLAH yazo yana son ganin sa, ba musu ahmad yace to.

Bayan awa d'aya da wayar su sai ga ahamd yazo ya samu mashkhur har bedroom d'in shi. Bayan sun gama gaisawa ahmad yace mai yake faruwa haka mashkhur ka kwad'a min wanan kiran gaggawan. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa yaushe zahra zata dawo?. Cikin mamaki ahmad yace tabb wata sabuwa mene na damun kan ka da dawowar ta

Please Login or Register in order to submit comment