Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har ta fara bacci.

Zahra tanajin qarar shigowar mashkhur tai sauri ta miqe zaune. Mashkhur yana qarasowa ya miqawa zahra wayar dama a hans free take, hannu na rawa zahra ta kar6i wayar tace hello dady?, muryar dady ce ta rasa wajan!! mamana mai ya saki mura? Da sauri zahra ta kalli mashkhur, zuba mata ido yayi alamun gargad'i murya na rawa zahra tace no dady kawai dai kasan garin yana da sanyi sosai ba kamar Nigeria ba kuma ban saba ba shiyasa. Okay da fatan dai kin fara zuwa school koh? Aa dady banfara ba, sai zuwa jibi in na warke.

Okay mamana ALLAH ya baki lafiya, ameen dadyna, duk abinda yake damunki ki gayawa Ahmad abokin mijinki in dai bazaki iya gayawa mijinki ba ko mene in sha ALLAH zai miki. Tom shikenan dadyna in sha ALLAH zanyi haka, take care my special daughter, murmushi zahra tayi tare da cewa take care too my really dady. Daga haka dady ya gintse wayar, zahra kuwa sunkuyar da kai tayi tare da miqawa mashkhur wayar tasa, da qarfi mashkhur ya fincike wayar tasa sanan yayi fucewarsa daga bedroom d'in.

Ajiyar zuciya zahra tai tare da furta alhamdulilah, tabbas tunda zahra ta sauka garin rasha bata ta6a farin ciki ba sai ranar da tai waya da yaya abdul sai kuma yau da tai waya da dady. Wani farin ciki ne ya lulu6e zahra tabbas zahra tana qaunar dady kamar yanda yake qaunar ta, dan harya ma zahra bata gama yanda cewa dady ba shi ya haifetaba, kuma har yau bata dai na kallon dady da ammi a matsayin iyayanta da suka haifeta ba. Ranar dai zahra tayi bacci mai dad'i zuciya cike da farin ciki..........

Washegari.............

Misalin qarfe takwas zahra ta tashi dama tun asuba tayi sallah ta koma. Zuciya fass zahra ta tashi toilet ta shiga, sai da ta wanke kanta tass sanan tazo tai wanka. Tana futowa ta nufi bakin mudubi ta zauna akan kujerar merro d'in , ta jona drayer busar da kai ta busar da gashi ta. , bayan ta gama tai parking d'in sa waje d'aya, dama ga zahra da gashi sosai kamar 'yar fulani. Daga haka ta tashi ta nufi drowar ta d'akko riga da sket na atanfa tasa. Wow zahra tayi kyau sosai kana ganinta kaga cikakiyar bahaushiya kyakyawa sajan nan nata yabi goshinta ya kwanta luf.

Tinani zahra ta farayi yau su mashkhur sun tafi school ko kuwa? Sam yanzu ko hanya bataso ta had'a da mashkhur, barema tai mai wani laifin. Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da furta yauwa lokacin da zahra ta tuna da ventilation d'in bedroom d'in ta da take leqawa, tasan in dai taga motar mashkhur yana gidan, in kuma bata ganiba baya nan. Da sauri ta nufi ventilation d'in dan ganin motar mashkhur d'in tana nan?. A hankula ta bud'e labilan waja bayan ta bud'e ta zuge glass d'in wajam a hankali.

Tana bud'ewa wani sanyi ya ratsata har kwakwalwarta da yake ana sanyi a garin sosai. A sannu zahra ta qarasa ventilation d'in tare da leqawa qasa, murmushi zahra ta saki tare da furta alhamdulilah, sakamakwan rashin ganin motar mashkhur d'in. Ba 6ata lokaci zahra ta fuce daga bedroom d'in ta wuce kicin domin samarwa kanta abinda zatasa a cikinta. Hakanan zahra taji tana sha'awar cin airish wato dankalin turawa, dan haka ba 6ata lokaci ta shiga store ta kwaso dai-dai yanda zata iya cinyewa sanan tazo ta fara ferayewa.

Bayan zahra ta gama feraye dankalin sliz d'in shi ta farayi yanda takrson shi, tana gamawa ta wanke ta zubamai gishiri da magi ta fara soyawa. Bayan ta gama soyawa, kwashe shi tai sanan ta yanka albassa ta fara soya kwai, bayan ta sauke t ta d'ora a kettle, ba'a d'auki lokaci mai tsayiba ya tafasa bayan ya tafasa ta juye a cup sanan ta kwashi kayan abinci ta koma falo. Akan draining ta zauna, madara da shuger, da milo ta zubawa shayin sanan ta fara cin abinci.

Tsaf zahra ta cinye abincinta tassa rabum da taci abincin mai yawan irinbna yau har ta manta, sabida tsabar firgici da razanin da mashkhur yake sata. Kwanikan abinci ta kwashe ta kai kicin, dama jiya bata samu damar wanke-wanke ba sabida bata da lafiya gashi wanke-wanke ba laifi ya d'an taru da yake ta dafawa zee abinci, kuma ga cup da plat d'in da mashkhur da yake cin abincin da su birjik ba'a wanke ba. Haka zahra ta wanke kwanikan nan tass sanan ta mayar da su mazauninsu.

Bayan ta gama ta gyara kicin d'in tass, tana gama gyara kicin d'in ta koma falo ta gyara shi shima tass. Dama bedroom d'in ta a gyara yake, zahra ji tai kamar ta shiga bedroom room d'in mashkhur. Haka nan taji tana san shiga bedroom d'in mashkhur, duk da kuwa zahra bata cika karan bani ba. Kamar mai sand'a haka zahra ta nufi qofar bedroom d'in mashkhur tana zuwa ta tura ta shiga. Tsaf bedroom d'in yake kamar maca ce a ciki a gyara tass komai yake.

Dama mashkhur bayasan qazanta ko waje a 6ace yake baza iya zama ba. Ga wani daddad'an qamshin turare da ya saba sawa a jikinsa yana tashi. Zahra ta tsani mashkhur a rayuwar ta, kuma duk wani abu da ya dangance shi bata so, amma tun tana 'yar shekara goma take qaunar turaran mashkhur d'in ta rasa sabida me take son qamshin turaran, zahra tana cikin wanan tunanin ta hangi kwalabar turaran mashkhur d'in a kan merro.

Murmushi zahra tai a zuciyar ta tace hmm kamar kuwa kasan maganar ka nake. Da sauri zahra ta qarsa gaban merro d'in domin d'aukat turaran. Tana d'auka ta bud'e tare da d'aga shi tana karanta sunan sa. Turaran larabawa ne da larabci ma aka rubuta sunan, ajiyar zuciya zahra ta saki tare da fesa turaran a jikinta. Wani sanyi qamshi taji ya ratsa sassan jikinta gaba d'aya har kwakwalwarta takejin qashin turaran. Lumshe ido zahra tai tare da rungume turaran a qirjin ta.

Zahra tafi minti goma a hakan bata motsaba, tama tafi wata duniya ta daban. Sama-sam zahra ta farajin motsi kamar ana shigo gidan, tunanin zahra ta tafiyi karfa taje yaya mashkhur ne ya dawo?. Zahra tana cikin wanan halin kamar daga sama taji ana qoqarin bud'e qofar bedroom d'in mashkhur. A gigice zahra ta saki kwalabar turaran ta fad'i qasa ji kake tasss. A dai-dai lokacin mashkhur ya bud'e Handel d'in qofar ya shigo. Da sauri mashkhur ya shigo bedroom d'in amma ganin zahra yasa shi yin turuss, wani kallon mamaki da alhajibi yake watsawa zahra....................


Kuyi haquri Yau banyi muku typing da yawa ba inada abunyi shiyasa, ayi hutun mako lpy, jumma'atul kareem.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240.


Typing............

*page 57*

A dai-dai lokacin mashkhur ya bud'e Handel d'in qofar ya shigo. Da sauri mashkhur ya shigo bedroom d'in amma ganin zahra yasa shi yin turuss, wani kallan mamaki da alhajibi yake watsawa zahra............

Kafin kace kwabo zahra jikinta ya hau tsima gumi ya fara keto mata. Ai kuwa karaf mashkhur idonsa ya sauka akan kwalabar turaransa da zahra ta fasa, cikin mamaki yace what?, ai zahra tanajin hakan ta qara gigicewa, mashkhur kuwa zuba mata wanan kwala-kwalan idon nasa yayi kamar maye yana mata kallo mai cike da fassara da yawa. Zahra tana ganin haka ta fara kuka a duniya ta tsani taga mashkhur yana mata irin wanan kallon yana kid'imata oder.

Jinjina kai mashkhur yayi tare da nufar wajan gado, wasu ta kaddunsa ya kwasa tare da juyawa ya fice. Tabbb ai ba iya zahra ba koni amina bayero sai da abin nan ya ban mamaki, wai mashkhur zahra tayi mai babban laifi haka harta shigo mai bedroom kuma ta fasa mai turare, bai d'auki mata ki akan taba? Lalai wanan abun da ayar tambaya akai. Wata nannauyar ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da furta alhamdulilah, wani sanyi ne ya ratsata har zuciyar ta, tabbas yau ta kafa tariyi, wai tayiwa mashkhur laifi bai mata hukunciba, a karan banzama yake dukanta.

futowa zahra tai ta d'auki abin shara da mofa ta koma cikin bedroom d'in mashkhur, sai da ta share kwalabar turaran tass, sanan ta goge wajan, wani mugun qamshi ne yake tashi a d'aki, sabida turaran da ya fashe, bama iya d'akin ba har ita kanta zahra qamshin turaran take. Daga haka ta fuce da fasasun kwalaben turaran tai shara dasu ta zubar. Daga haka bedroom d'in ta koma ta hau karatun qur'ani. Ba ita ta idar da karatunba sai qarfe d'aya da rabi, lokacin sallar azahar.

Toilet ta shiga ta d'aure alwala sanan ta gabatar da sallar azahar. Daga haka ta wuce kicin ta d'ora abincin, pride rice ta dafa, dama ita take sha'awa ta had'a da ragowar dan kalinta na rana taci, bayan ta gama ci bedroom d'in ta koma tai kwanciyar ta bacci, duk jikinta qamshin turaran mashkhur yake, haka nan taji bacci mai dad'i ya kwasheta sabida qamshin turaran.
Zahra ba ita ta tashi daga baccin ba sai da aka fara kiran sallar la'asar, tana tashi taji jikinta duk ya mutu ga qamshin turaran mashkhur data fasa ya ratsa ko wace kafa ta jikinta. Turaran bashi da qarfi sosai kawai dai sabida zahra ta fesa shi sosai ne ajinta kuma ta kwashe kwalaban da ya fashe da hanunta shi yasa qashin turaran ya zauna a jikinta, dama tiraran akwai zama a body.

Jiki a mace zahra ta wuce toilet tai alwala, sanan ta dawo tai sallah tare da addu'o'i neman tsari da daga sharrin yaya mashkhur. Mashkhur bashi da hayani ya sam in yana gida bazaka gane ba shiyasa zahra ta kasa ganewa ya dawo gidan kokuwa? sai da ta leqa taga, tana ganin motar sa tasan ya dawo gida. Zahra kuwa batai gigin fita daga bedroom d'in taba, dan tasan yau tai masa lefi sosai. Sam zaman d'akin baya yiwa zahra dad'i, tana san fita amma ta kasa dole haka ta haquri ta zauna ita ka d'ai a bedroom kamar tai kuka kuma gashi batajin bacci barema tayi, ta rage ta kai ci........

Tofah zahra har wajan isha'i tana son fita sam ta kasa, data gaji ma sai ta tafi ventilation kawai ta tsaya tana ganin yanayin gari duk da kuwa sanyi da ake a gari. Tana cikin kalle-kalle ta hango mashkhur ya futo ya shiga part d'in ahmad, wata ajiyar zuciya ta sauke, sanan tai sauri ta koma d'aki ta zuge glass d'in ventilation d'in sanan ta fuce daga bedroom d'in. Kicin ta nufa, ragowar abincinta ta zubo domin taci, tana zubowa ta wuce bedroom d'in ta, ta fara ci.

Tana gama ci ta fuce a hanzarce domin mayar da plate d'in kincin ta dawo ta kwanta da wuri tinda yaya ahmad yace gobe zai kai ta makaranta. A hanzarce zahra ta shiga kicin d'in, har zata futo taga ya kamata ta wanke plate d'in da taci abincin tinda shi ka d'ai ne a wajan, dan haka ba 6ata lokaci ta wanke, sanan ta futo domin tafiya bedroom d'in ta. Zahra Tana futowa ta daga kicin d'in mashkhur yana shigowa cikin gidan, zahra ji tai gabanta ya fad'i rasss, amma duk da hakan ta dake ta cigaba da tafiyar ta.

Mashkhur kuwa Tsayawa yayi daga gefe, ya kama ugu yana kalon zahra cikin mamaki a zuciyar sa yace au tama manta da laifin da ta aikata kenan?. Har zahra ta kai rabin falon taji mashkhur yace KEE, zahra ji tai kamar karta tsaya ta cigaba da tafiya tunda ba sunanta kee ba amma tasan, tabbas ta cigaba da tafiya yau sai jikinta ya gaya mata dan haka tsayawa tai cak bata jiyoba. Tabb lali kice ke iskancin naki ma ya karu koh? Mashkhur ya fad'a hakan cikin mamaki, juyowa zahra tai tare da sunkuyar da kai tana cewa kayi haquri.

No bayanzu ba tukunda dai tun da wuri kin karaya haka? Ai da kin bari mun qarasa wasan, ya gama fad'a yana jifanta da harara mai ciki da zaki gane. Zahra kuwa shiru tai dan bataji dad'in kalmar iskanci da mashkhur ya daganta ta da itaba, amma ba yarda ta iya bazata iya ramawa ba, bama mashkhur ba ko wani sa'an tane ya gaya mata haka ba laillai ta mayar mai da martani ba sabida ita ba mai san hayaniya bace. Gani tai mashkhur ya faravtunkaro inda take, nan da nan gabanta ya ciga da fad'uwa amma ta dake, ta tsaya qam a wajan.

Da mamakin zahra gani tai ya wuceta ya barta a tsaye a wajan, zahra harta tafi tinanin sai ji tai yace in kin yi niya zaki iya biyoni bedroom d'in. Zahra kuwa ba 6ata lokaci ta bi bayan mashkhur d'in dan tasan baqar magana ya gaya mata yanzu in bata bishi ba sai jikinta ya gaya mata. Tana zuwa qofar bedroom d'in kawai taji ta kasa shiga sai a lokacin ma ta tina ba mayafi a jikinta dan haka juyawa tai domin komawa bedroom d'inta ta d'auko mayafin ta. Tana zuwa ba 6ata lokaci ta d'auki mayafinta ta yafa sanan ta nufi bedroom d'in mashkhur d'in.

Lokacin data shiga a tsaye ta ganshi a bakin merro yana waya. Duk bedroom D'in ya karad'e da qamshin turare, ga sanyin a. c sai tashi yake duk da kuwa ana sanyi a garin a zuciya zahra tace oh shi ko sanyima bayaji. Yamutsa fuska zahra taga mashkhur yayi yana cewa okay zee see you tomorrow, cikin qosawa yake maganar daga haka ya yanke wayar, jinjina kai zahra tai a zuciyar ta tace hmm ashe da wanan karuwar zee d'in yake waya. Daga haka mashkhur zama yayi akan kujerar merro d'in yana kallon fuskarsa kamar wata mace. Kamar ma bai san da zuwan zahra ba, sunfi 10 minti a hakan mashkhur yana bakin merro yana kallon fuskar ta ko kwakwaran motsi baya yi ita kuma zahra ta tsaye.

Azahirin gaskiya mashkhur ba kallon fuskar ta yake ba kawai duniyar tinanini ya tafiyi kuma duk akan zee ne. Tinani yake wai sabida mai zee take maqale mai haka? Kuma sabida mai take neman sai sun kasance a tare? Sam ya kasa ganewa zee tana mace amma tana kawo mai tallan kanta?. Muryar zahra ce ta katse mashkhur daga dogwan tinanin daya tafi. Cikin rarauniyar murya yaji tace yaya mashkhur gani, ta mudubin ya zuba mata wata uwar harara, sunkuyar da kai qasa zahra tai.

Muryar mashkhur zahra taji yana cewa ohoo lali har cemin kike kinzo ko? Shiru zahra tayi ba amsa, tasowa mashkhur yayi tare da qarasowa inda zahra take tsaye. Gab da ita ya matso ya tsaya, amma ba ita yake kalloba wani gefe na daban yake kallo. Uban waye yace ki shigomin d'akina ya qarasa maganar yana zuba mata kwala-kwalan idanuwan nan nasa masu kid'ima zahra. Jikin zahra rawa ya farayi tama kasa cewa komai, kee karki sake bari na tambaye ki uban mene ya shigo da ke bedroom d'in na.

Zahra kuwa tana jin haka murya na rawa tace tsau-tsayi, saura qiris mashkhur ya tuntsire da dariya, sabida amsar da zahra ta bashi, amma ya danne dariya ya tsare gida ya sake zaro mata mayyun idanun nan nasa yace ke kishiga hankali haka ake tsautsayi ko sai na fara ball dake ne zaki yimin bayani. Allah sarki zahra nan da nan ta sake rud'ewa bata iya qarya ba amma ayau dole ta kwakulo domin tsiratar da kanta daga sharrin mashkhur. Murya na rawa zahra tace dama zuwa nai na gyara bedroom d'in, wani mugun kallo mashkhur ya watasawa zahra tare da cewa okay nina ce miki ki gyara min?.

Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa, toh dama kika shigo bedroom d'in uban waye yace ki ta6amin turare na? Girgiza kai zahra tayi tare da cewa bakowa kawai tsau-tsauyi ne da qaddara. Wlh kika qara cemin stau-tsayi sa na zubar miki da haqora, haka ake stau-tsayi kawai kice mugunta ce tasa kika fasa. Shiru zahra tayi idonta ya ciko da kwalla tab, wani tsakin baqin ciki mashkhur yaja wani irin haushi take bashi duk abinda tai haushinta yake ji. Kee!!! mashkhur ya furta da sauri ta d'ago tare da cewa na am.

Tana ganin idon mashkhur tasan ba sassauci, dan sai wani lumshewa suke lumshewar mugunta, zaro mata idon yayi tare da cewa au had'a ido zaki dani koh? Da sauri zahra ta janye idon ta daga nasa shi bai masa tsoran wanan idanuwan nasa take ba. Tun d'azu na kasa zama a bedroom d'in nan sabida mugunta irin taki kin fasamin tirare qamshi ya ishe ni to wlh na baki 10 minti duk yarda zaki kiyi bedroom room d'ina ya daina qamshi turaren nan ya dai na in ba haka ba hmmmm, yana qarasa fad'in hakan yayi wucewarsa ya barta a tsaye.

Zahra bata tsayawa wata-wata ba tai sauri bin bayansa domin d'auko abin mofin. Ruwa zahra ta zuba da omo da hyppo sauri air freshener na moffin ta fara mofe wajan data fasa turaran, sai da zahra ta mofe wajan nan sau biyar ga sanyi a c bedroom d'in mashkhur yana damunta. Dan har glass d'in ventilation ta bud'e duk sabida qamshin ya fita. Zahra fa ta goge wajan nan yafi sau goma dan waja ma har ya fara dena qashin turaran. Data gaji da gogewa rofomai glass d'in ventilation d'in tai sanan ta fita da ruwan moffin din ta zubar.

Yana kan kuje yana chatting d'in shi hankali kwance. Kamar wata munafuka haka zahra ta ra6e daga gefe ta tsuguna tare da cewa yaya mashkhur na gama. Shi kuwa mashkhur ko kallo bata isheshiba duk da kuwa yanajin abinda take cewa. Can kuma yace banace karki qara kiran sunana ba? yanzu karo na biyu kenan kina fad'a bayan na hanaki to kika kuskura kika qara kiran sunana sai kin gane baki da wayo. Tashi muje naga wana iskanci kika aikata min a bedroom, ba musu zahra ta miqe mashkhur ne yayi gaba ita kuma ta bishi a baya.

Suna shiga bedroom d'in mashkhur ya yamutsa fuska tare da cewa okay kawai kicemin ba gyara kikayi ba ba 6arna kika sake yi. Nan da nan zahra ta fara zaro ido, wata harara mashkhur ya watsa mata tare da cewa, ina kwalbar tiraran da kika fasa?, murya na rawa zahra tace tana dustbin, Uban waye yace ki zubar min da kwalabar? Murya na rawa zahra ta sake cewa bakowa! okay ke kika sa kanki kenan? To na baki nan da minti uku kije ki tattaro kan kwalabar da kika zubar ko 6antare d'aya karki bari.

Yana gama fad'in hakan ya juya ya fuce ya koma falo, what's yanzu yaya mashkhur shara yakeso naje na kwaso kwalaban nan? Haba zahra tsira da mutunci yafi tsira da kud'i kawai ki rabu da shi kije kiyi abinda yasaki , kinga dai zai iya dukanki!! duk zuciyar zahra, ce take gaya mata hakan. Haka zahra ta kwashi qafa ta fuce fallo, tana ganin mashkhur a zaune a kujera haka ta wuce dustbin d'in falon ta fara tsuntu kwalaban duk da kuwa ba lailai ne ta iya had'a su yanda suke ba.

Zahra sai da tai wajan minti biyar tana tsunto kwalaban nan kafin ta gama tsinto su tass. Hanunta cike da kwalabe ta nufi inda yake zauna akan sofa, tsugunawa tai a gabansa tace gashinan, d'ago kansa yayi ya galla mata harara tare da cewa au ni zaki bawa kenan?, girgiza kai zahra tai tare da cewa I'm sorry, shan kunu mashkhur yayi tare da cewa sorry for what? Murya a sahaqe zahra tace sorry for you!! Jinjinakai mashkhur yayi tare da cewa sorry for your self. Shiru zahra tai bata sake cewa komai ba.

Abinda nake so kiyi da kwalaban nan inaso ki mayar da kowacce in da take kamar ba'a fasaba, mashkhur ya qarasa magana yana mayar da hankalinsa kan wayar sa cikin yanayi na ko in kula. Zahra tanajin hakan gabanta ya fad'i inma banda muguntar yaya mashkhur taya zata iya gyara kwalabar turarran nan?. Nan da nan zahra ta fara kuka, tana cewa dan Allah kayi haquri wallahi ni bazan iya mayarwa ba, shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba.

Sun d'auki 20 minit a haka ita zahra tana kuka mashkhur kuma yana danna wayar sa. Zahra ta gaji da kukan dan haka shiru tai tana sauke ajiyar zuciya, tana d'agowa mashkhur ya dago suka had'a ido dashi. Wata uwar harara ya banka mata tare da kawar da kai gefe. Pls yaya forgive me, zahra ta fad'a tare da had'a hanunta waje d'aya. Nan ma mashkhur bai ce mata komai ba, zahra kuwa qara cewa tai wlh bazan iya gyara kwalabar nan ba banma san yanda zan gyara taba.

Mamaki ne ya kama mashkhur yadda yaji zahra tana tai mai magiya alhali yasan bata cika magana sosai ba musamman ma in suna waje d'aya. Murya zahra ce ta sake katseshi! dan Allah ka yafemin wallahi bansan yarda zan gyara ba. Wata uwar tsawa mashkhur ya dakawa zahra wanda sai da ta gigitata tasa tayi shiru. Kee dallah rufemin baki, kin isheni uban waye yace ki fasa kinsan bazaki iya gyarawa ba?, wlh kika qarayimin magana sai na 6alla qafafuwanki na faffasa miki baki, duk abinda nasaki kawai kiyi that is all.

Zahra kuwa duk jikinta ya farayi mata rawa sam batasan fad'a ko hayaniya, bare tsawa! Stawarma ta mashkhur dodonta. Cikin 6acin rai mashkhur yace okay bazaki iya ba ko? Yanzu zan saki abinda zaki iya kuwa. (Go and take plate for me) wato jeki ki d'aukkomin plate, jiki na sassarfa zahra ta wuce kicin dan ai wata da abinda mashkhur yace. Ba 6ata lokaci zahra ta futo hanunta d'auke da plate, tun kafin ta qaraso ta stinkayi mryar mashkhur yanace wa!! maza ki sauka qasa, ki tafi parking space ki kwaso qananin duwatsun da suke wajan ki ciko plate d'in, in kuma kika d'ebo kad'an sai jikinji ya gaya miki, in kika dawo ki sameni a bedroom d'in na, yana gama fad'in haka yayi wucewarsa bedroom d'in sa.

Mamaki ne ya kama zahra, to mai yaya mashkhur zai yi da duwatsun? Hmm karfa naje wata muguntar zai min dasu? Zahra ta watsawa kanta tambayar. Amma ba amsa, d'aga kai tai ta kalli agogon falon, misalin qarfe goma da rabi na

Please Login or Register in order to submit comment