Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasan ammer yana yi ba haka ammer ya qaraci kukan sa ya gama. Ammer da zahra sunfi awa d’aya a wannan yanayin kafin su dady su dawo.

Da sallam ilham ta shigo d’akin fuska babu walwala sabida rabuwar da sukayi da yayan ta mashkhur. Mamaki ne ya kama ilham ganin zahra ta kifa kanta a mudubi tana kuka cikin da shashiyar murya, shima ameer yana kan bed yana ajiyar zuciya alamun yayi kuka. Da sauri ta qara inda zahra take ta dafa ta tare da cewa zahra me ya faru ke da ammer ku ke kuka? Shiru zahra tayi batare da tabawa ilham amsa ba. Ameer kuwa yana ganin ilham ya cigaba da kuka tare da cewa ilham kizo ki sauke ni.

Da sauri ilham ta qarasa kan bedroom d’in tare da sauke ameer daga kan bed d’in, tana sauke shi ya fuce daga bedroom d’in. Ilham kuwa komawa tai wurin zahra tare da cewa haba zahra yanzu sai ki zauna kita kuka a d’aki ke kad’ai pls ki gayamin mai aka yimiki, kokuwa dai sai na kira miki yaya abdul ne?. D’agowa zahra tayi Fuska jiqe da hawaye, ta kalli ilham tare da cewa dan Allah ki rabu dani ilham pls.

Cikin mamaki ilham tace zahra ni kike cewa na rabu dake koh? Ta qara maganar tana nuni da kanta fuska cike da mamaki. Shiru zahra tayi mata batare da ta bata amsa ba, murya a sanyaye ilham tace shikenan zahra tinda baki d’auke ni yanda na d’auke ki ba, kinsai dai duk duniya ke nake iya gayawa damuwata kema ki gaya min taki amma sai gashi yau kin juya min baya, ilham tana qarasa maganar ta juya zata futa rai a 6ace.

Da sauri zahra ta ruqo hanun ilham, rai a 6ace ilham tace dallah sakar min hanuna. Zahra kuwa riqe hanun ilham tayi gam tare da sake fasa wani saban kukan. Jike a sanyaye ilham ta juyo tare da dafa kafad’ar zahra tana cewa haba zahra kukan nan naki yana tayar min da hankali dan ALLAH ‘yar uwata ki gayamin me yake damun ki kinga duk duniya baki da ‘yar uwar data fini, nima bani da wanda ta fiki, ta qarasa maganar idonta ciki da kwalla.

Da kyar zahra ta tsagai ta kukun da take murya tana rawa tace ilham ashe ni ba ‘yar GIDAN NAN bace ba?. Razana ilham tayi tare da cewa haba zahra wanan wace irin magana ce, to in ke ba yargidan nan bace ai nima ba ‘yar gidan bace. Wasu hawaye ne mai zafi suka sake zubowa zahra, cikin shasheqar kuka tace Wallahi ilham da gaskiya nake miki ke ‘yar gidan nan ce amma ni ba ammi da dady bane suka HAIFENI.

Wani razanan nan kallo ilham ta watsa mata tare da cewa gaskiya zahra bansan wanna shirman anya kwakwalwar ki bata samu matsala ba?, dan gaskiya daga gani kina buqatar ganin likita. A zuciye zahra ta miqe cikin 6acin rai tace haba ilham wai ya zan ringa gaya miki magana bakya yadda ne?, itama ilham d’in cikin fad’a tace tom akan mai zan yadda da shirman ki. A zuciye zahra ta janyo hanun ilham, tare da tsayar da ita a bakin mudubin, tana cewa!! Ilham ki kalle ni sanan ki kalli kanki ki a mudubi dan ALLAH ki gayamin muna kama da ke? Ko kuma ki gaya min ina kama da d’aya daga cikin ‘yan gidan nan? Ko kuma ina kama da dady ko ammi?.

Sosai ilham ta tsaya ta qarewa kanta kallo ita da zahra, tabbas ilham ta fara jiyo qam shin gaskiya maganar zahra sabida ko ta hanci basa kama, kuma zahra bata kama da kowa a gidanan tinda ilham take bata ta6a kula da hakan ba sai yau. Ilham kuwa bata tsaya bawa zahra amsa ba ta fuce da gudu daga bedroom d’in. Ilham bata tsaya ko ina ba sai falon ammi da duk mutan gidan suka baje suna mai da maganar tafiyar mashkhur.

Ammi ce ta kalle ta tare da cewa ilham mene haka kika tawo a guje lafiya?. Bata tsaya bawa ammi amsa ba tace dady hajiya kaka ammi da gaske wai zahra ba ‘yar GIDANNAN BACE?. Mumunar fad’uwar gaba ce ta samu dady da hajiya kaka da kuma ammi harma da abdul da yake gefe. Momy kuwa murmushin mugunta ta saki d’an ko ba’a fad’a mata ba tasan mashkhur ne ya fad’a wa zahra, dama kuma ranar da momy take jira kenan tazo. Sukuwa sauran yaran gidan mamaki ne ya kamasu.

Duk falon yayi shiru ba wanda yayi magana. Muryar ilham ce ta sake karad’e kunnuwan kowa, cewa tai, dady kenan da gaske ne zahra ba ‘yar gidan nan bace?. Wata razananiyar tsawa dady ya dakawa ilham! Kee ilham bana san rai nin wayo uban waye ya gaya mike cewa zahra ba ‘yar gidan nan bace?. Jiki yana rawa ilham tace wlh dady zahra ce ta gaya min da bakin ta yanzu ma haka tana zaune a d’aki tana kuka.
Nan fa su ammi da hajiya kaka harma da abdul ido ya fara raina fata, dady kuwa dakewa yayi tare da miqewa ya nufi bedroom d’in su zahran.

Suma su ammi da sauran yaran gidan harma da momy bayan dady suka bi dan idon su ya gane musu gaskiya zancan. A durqushe dady ya samu zahra tana ta rafsa uban kuka. Yana qarasawa kusa da ita suma su ammi da yaran gidan suka fara shigowa d’akin. Tsugunawa dady yayi tare da dafa kafad’ar zahra yana cewa mamana mene haka ne?, duk wanda yace miki ke ba ‘yar gidan nan bace to wasa yake miki, amma ke ‘yar gidan nan ce kuma ‘yata ce ta cikina, kuma ammi ce ta haifi ki kamar yanda ta haifi su Haidar.

Cikin shasheqar kuka zahra tace dady mai yasa kuke 6oye min GASKIYA ne?, wallahi dady ni yanzu nasan ba ‘yar ku bace. Tsawa dady ya daka mata wanda sai da ta firgita ta, karo na farko kenan a duniya da dady ya ta6a dakawa zahra tsawa kenan. Wai uban waye ma ya gaya miki cewa ke ba ‘yar gidan nan bace, dady ya fad’a rai a 6ace, cikin rawar murya zahra tace yaya MASHKHUR ne. Har ammi da hajiya kaka suna had’a baki wajan yin salati. Dady kuwa dakewa yayi tare da cewa to qarya yake miki ai kinsan mashkhur bakwa shiri dashi shiyasa ya gaya miki haka, kiyi haquri kinci mamana.

Ciki kuka zahra tace dady kawai ku gayamin su waye iyaye na? Dan a halin yanzu nasan baku kuka haifeni ba. Ji kake tasss tasss wasu kyawawan maruka har guda biyu dady ya sakarwa zahra tare da cewa mamana ashe baki da hankali? Harni zan gaya miki magana kice faki yadda ba, sai maganar wancan mara mutunci wato (mashkhur) zaki yadda da ita?.shiru d’akin yayi babu mai magana sabida kowa ganin lamarin yake kamar al mara, dan wasu daga cikin suma tinanin suke anya ba mafarki suke ba.............

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing...........

*page 47*

Shiru d’akin yayi babu mai magana sabida kowa ganin lamarin yake kamar al mara, dan wasu daga cikin suma tinanin suke anya ba mafarki suke ba................

A zuciye dady ya tashi ya fuce daga d’akin, a cikin zuciyarsa yana Allah wadarai da mugun hali irin na mashkhur. Haka kowa ya ringa silalewa yana barin d’aki one by one, har abdul shima fita yayi sabida yasan in dai ya tsaya rarrashi zahra dole tayi mai tambayar wacece ita? Shikuma bazai iya gaya mata ba. Bedroom ya rage daga faruq sai haidar sai kuma ilham, hatta su ruma sun fice suda mahaifiyar su momy. Haidar ne ya qarasa gaban zahra jiki a sanyaye yana rarrashin ta.

Duk su ukun rarrashin zahar suke, akan tayi haquri ba gaskiya yaya mashkhur ya gaya mata ba, amma ina zahra ko kallo bata ishe suba. Da suka takura mata da magiya mah a fusace ta daka musu tsawa tare da cewa su rabu da ita. Dukkan nin su sunji tsoran yanda lokacin d’aya Zahra ta cansa harda tsawa, ita da bama ma abociyar fad’a face. Jiki a sanyaye suma suka fuce daga d’akin ilham ce kad’ai ta rage a bedroom d’in, su faruq da haidar duk sun fita.

Haba zahra dady ya gaya miki cewa ba gaskiya bane amma kwata-kwata kinqi yanda wai sabida mai kike haka ne, ke ma dai kinsan halin yaya mashkhur, cewar ilham da take zaune a gefan zahra. Ido jajir zahra ta d’ago cikin tsawa tace dallah ki rabu dani bana san surutun banzan nan pls ilham ki tashi ki futa. Jiki ba qwari ilham tabar d’akin, fuskar cike da hawaye. Ilham tana fucewa zahra ta sawa d’akin key tare da dawowa kan bed ta cigaba da kuka mai cin rai.

To yau fa zahra wuni tayi a d’aki tana kuka, kuma gashi taqi bud’e d’akin magiyar duniya ammi da hajiya kaka harma da sauran yaran gidan suka yi mata amma ina taqi bud’e wa. Abu kamar wasa har goman dare zahra taqi bud’e d’akin, hakan ne yasa ammi ta wuce part d’in dady domin sanar da shi mai ke wakana. Tana shiga part d’in dady taga dady ya raf ka uban tagumi ya tafi duniyar tinani. Sai sallama ammi take kwad’a wa dady amma ina bai mai san tana yiba.

Jiki ya sanyaye ammi ta qarasa kusa da Dady ta zauna, tare da dafa kafad’ar dady tana cewa yaya Abubakar?. Firgigit dady ya dawo daga dugan tinanin da ya tafi. Ammi kuwa bata tsaya 6ata lokacin ta wajan tambayar dady abinda yake damunsa ba , dan tasan akan matsalar zahra ce. Murya a shaqe ammi tace yaya Abubakar tun d’azu fa zahar ta shiga d’aki ta kulle sai kuka take kuma taqi bud’e wa. Ajiyar zuciya dady ya sauke tare da cewa hmm dama nasan hakan zata faru d’an haka ku rabu da ita kawai.

Cikin mamaki ammi ta kalle shi tare da cewa mu rabu da itafa kace yaya Abubakar? D’aga kai dady yayi alamun eeh. Haba yaya ko abincin safe ba bataci ba taya zamu kyale ta?, kallan ta dady yayi tare da cewa ammi bari kiji mamana tana da haquri sosai, amma yau tai fishi da zuciya sosai, ni nasan bazata ta6a bud’e qofar nan ba, dan haka ku rabu da ita zuwa gobe in ta wuce, kuma zancan abincin da kike magana bazata ta6a iya cin abinci a wannan halin ba.

Shiru ammi tayi dan bata da tacewa. Cikin rararunar murya dady ya cigaba da magana da cewa!! amma mai sunan baba sam bai kyauta mana ba ban ta6a tinanin rashin mutuncin sa ya kai haka ba sai yau, yanzu dama sai da ya gayawa mamana maganar da akayi shekara da shekaru ana 6uye mata? Dady ya qarasa maganar kamar zai zubar da hawaye. Ammi kuwa tini hawaye sun wanke mata fuska, cikin murya kuka tace wlh sam ban ta6a tinanin mashkhur zai mana haka ba yanzu ashe bai haqura ba sai da ya 6allo mana ruwan da bazamu iya tsayar da shiba.

Cigaba da magana ammi tayi cikin kuka! To yanzu kuma gashi bamu da amsar da zamu bawa zahra in ta qara tambayar mu suwaye IYAYANTA. Da sauri dady yace it is okay ki yi haquri kinji ki dena kuka in sha ALLAH komai zai zo mana da sauqi, yanzu ki tashi ki je, kicewa kowa yaje ya kwanta ita kuma ilham da ameer sai suje bedroom d’in ki ko wajan hajiya su kwanta kafin gobe muga abinda ALLAH zai yi. Jiki ba kwari ammi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta sanan ta bar bedroom d’in.

Tana zuwa ta tarar da hajiya kaka da yarin gidan sunyi jigum-jigum suna yiwa zahra magiya ta bud’e qofar, mu samman ma abdul da ilham da kuma hajiya kaka wanda hankalinsu yafi na kowa tashi a gidan. Da sauri ammi ta qaraso tare da cewa abdul faruq haidar ku tashi ku tafi 6angaranku ku kwanta, da sauri abdul ya kalleta zai yi magana, itama ammi da sauri ta katse shi da cewa abdul bana son musu kawai ku tashi ku tafi. A ala dole abdul ya tafi kawai dan bazai iyayiwa ammin musu bane shiyasa, suma su faruq d’in haka sukabi bayan abdul d’in hankali a tashe.

Mai da kallanta wajan hajiya kaka tayi tare da cewa hajiya kije ki kwanta dare fa yayi, fuska ba walwala hajiya kaka tace haba maryam ta ina zan iya bacci mai sunana tana cikin halin nan?.Dan Allah hajiya kije ki kwanta kafin gobe kin sai dai ko ma kin tsaya a nan zahra bazata bud’e ba, haka dai ammi tai ta lala6a hajiya kaka har ta haqura. Ammi mai da Kallanta kan ilham tayi tare da cewa ilham kema kibi hajiya ke da ameer ku kwanta, ba musu ilham taja hanun ammer domin subi hajiya kaka, amma qiri qiri ammer yasa kuka wai shi a wajan Aunty zahra zai kwana, hakan ne yasa ammi tace ta rabu da shi ita ta tafi.

Haka ilham ta fi bayan hajiya kaka fuska ba walwala kana ganin ilham zaka sheda taci kuka ta godewa ALLAH. Itama ammi jan hanun ammer d’in tayi suka wuce part d’in dady domin kwanciya.
Ranar dai duk mutan gidan ba wanda yayi bacci sai momy, rukee, ammer. Dan ko ruma bata samu ta rintsaba, da yake ita irin halin abdul ne da ita tana da tausayi ba kamar rukee ba wanda ta kwaso halin momy sak.

Washegari gari.......

Yauma mutan gidan sun taru maqil a qofar bedroom d’in da zahra take ciki, magiyar duniya sunyi mata amma ina zahra taqi bud’e qofar. Abu kamar wasa har kusan magriba taqi bud’e wa. Ai kuwa ana cikin haka sai ga dady ya qaraso. Cikin mamaki dady yace au wai kuna nufi har yanzu mamana taqi ta bud’e qofar nan? Har yaran gidan suna had’a baki wajan cewa eeh wlh dady, a hanzar ce dady ya qarasu ba 6ata lokacin kowa ya matsa domin bawa dady damar tsayawa a baki qofar.

Murya a kausashe dady yake cewa mamana! Mamana! Mamana! Amma ina zahra shiru ba amsa. Kwantar da murya dady yayi tare da cewa haba mamana magana nake miki fa, yanzu ya kamata kiyawa dady ki haka. Murya a sahaqe suka jiyo muryar zahra tana cewa inajin ka dady. Cewa dady yayi yauwa mamana to zo ki bud’e wa dady ki qofa. Tasuwa zahra tayi tare da zuwa dai-dai qofar ta tsaya yanda dady zai ji abinda zata ce.

Cikin da shashiyar murya zahra ta fara magana kamar haka!! Dady zan bud’e qofar nan amma sai kayimin al qawari zaku gayamin suwaye iyaye na, in kuma ba haka ba bazan ta6a bud’e qofar nan ba gwara na mutu a ciki. Shiru dady yayi dan yama rasa mafita.muryar hajiya kaka ce ta karad’e wajan! Abubakar kawai ka amince da hakan, dan komai zai zo mana da sauqi. Shiru dady yayi na wasu lokutan kafin yace tom mamana na amince.

Sautin muryar zahra dady ya jiyo tana cewa dady kayimin al qawari? Ehh mamana dadyn ki yayi miki al qawari. Abin mamaki kuwa gani sukayi zahra ta fara qoqarin bud’e qofar, tana gama bud’ewa dady ya tura tare da shiga ciki. Duk zahra ta koma wata abar tausayi ta rame fuskarta duk ta kumbura abin tausayi. Da sauri dady ya qarasa tare da bud’e mata hannu alamun hug ba musu zahra ta fad’a jikin dady ta rungume shi tare da sakin wani kuka mai cin rai.

Sosai dady ya fara rarrashin ta yana bibiga bayanta kamar wata baby. Duk mutan gidan sunyi zuru-zuru suna kallan zahra da dady. Sai da dady da zahra suka fi minti goma a haka sannan suka saki juna. Dady cewa zahra yay tayi wanka taci abinci amma ina zahra taqi yadda ita tace sai an gaya mata suwaye iyayanta, momy kuwa sai zabga mata uwar harara take. Kallan zahra dady yayi tare da cewa tom zo muje mu zauna sai a sanar dake komai, ba musu zahra da dady suka zauna akan gado.

Itama ammi da hajiya kaka qarasowa sukayi suka zauna, sauran yaran gidan da momy kuwa sun tsaya a tsaye carko carko. Dady ne ya kalli hajiya kaka tare da cewa hajiya bismillah ki fara yi mata bayani. Gyaran murya hajiya kaka tayi tare da yin bismillah, ba 6ata lokaci hajiya kaka ta fara yiwa zahra bayanin ko ita wace. Tin daga lokacin da dady ya kai su hajiya kaka gidan mutuwa ita da abdul, da kuma yanda akai abdul ya takura mata akan su dawo gida.

Da kuma yanda akayi suka tawo da daddare kuma har motar su ta lallace, haka hajiya kaka tai ta bada labarin zahra, har yanda akai suka futu kuma suka had’u da maman zahra, da kuma takaddar da tabawa abdul da kuma bayanin da tayiwa hajiya kaka akan zahra da kuma yanda ta bawa hajiya amanar zahra nan da wasu lokuta . har yanda akayi ta gudu a tsakar dajin nan. Haka dai hajiya kaka tai ta bawa zahra labarin komai, har yanda akayi aka had’a su da ilham aka rai nesu, har sai da ta gaya mata ammi bata shayar da suba ita da ilham, sakama kwan lokacin ruwan nono ya d’aukewa ammi.

Kuma ta gaya mata sun sami addres d’in gidan su zahra da numbar waya acikin ta kaddar da mamanta bawa abdul. Haka dai hajiya kaka tai ta yiwa zahra bayani har yanda akayi su mashkhur suka qona takaddar. Hajiya kaka tana zuwa nan zahra ta fashe da wani matsanancin kuka, kowa abun ya abashi tausayi musamman ma su faruq da ilham harma dasu rukee sai da abin ya girgiza su. Janyo zahra jikin sa dady yayi ya fara rarrashin zahra cikin kulawa. Dady ne yace hajiya kaka ta rabu da zahra ba sai ta bata labarin zamanta a gidan ba, abar zahra haka kawai.

A dai dai lokacin aka fara kiran sallar magriba, da sauri dady ya miqe tare da cewa abdul faruq haidar ku tashi muyi alwala mu tafi masallaci, jiki ba kwari suka tashi faruq da haidar fuska ciki da hawaye. Suna fucewa momy tace aikin banza ke ki godewa ALLAH ma kin fad’o hannu na gari zakizo ki cikamu da kuka ke kalar wannan gatan da ake nuna miki a gidan nan ai ko a gidan ubanki albarka.

Da sauri ammi ta katse ta da cewa haba halima wanna wace kalar magana ce, dan ALLAH ki fuce daga nan kibar yarinyar nan ta shaqata. A zuciya momy ta kalli ruma da rukee tare da cewa kukuma uban mai kuka tsaya jira kuna gani ana korar uwarku kuna nanewa dalla kuzo mu wuce, jiki a sanyaye ruma da rukee suka wuce sukayi hanyar fita, ita ma momy bayan su tabi. Suna fita ruma tace amma gaskiya momy bai kamata abinda kika yiwa zahra ba, da sauri rukee ta cefe zanacan da cewa ehh mana momy dama baki tanka ba, wlh yau zahra taban tausayi.

Da sauri momy tace wlh in baku rufemin baki ba sai na zubar muku da haqora anan wajan, dama tinda nasan ke ruma baki gaji halina ba ke kuma rukayya da kika gaje ni kina qoqarin ki sauya halinki, to dan ubanki yarinyar nan ba abin tausayi bace, kuna ganin yanda ubanku yake fifita ta sama da ku, ko kuna zaune a gefe kamar marasa uba. Kokuma kuma so kuke ku zama watsatsu kamar wancan yayan naku abdul ni da d’ana amma anfi qarfina an mallake min shi dan yanzu abdul bai d’auke ni a matsanyin uwa ba.

Sam abdul ya manta nina haife shi yafi d’aukar wancan banzar matar uwa wato ammi. To bari kuji ni bazan yarda yanda aka mayar da abdul sallamamme kuma a mayar da ku haka. Haka dai momy tai ta balbala bala’i da mita har suka qarasa part d’in su, su dai su ruma suna jinta sukayi qum, sabida tsoran ta dan sunsan yanzu sai ta zanesu a banza.
6angaran su zahra kuwa momy tana futuwa ammi tacewa ilham kema ki wuce bedroom d’in na kiya sallah ba musu ilham ta fuce.

Hajiya kaka ma miqewa tayi tare da cewa bari nima naje nayi sallah. D’aki ya rage daga ammi sai zahra, itama ammi toilet ta wuce ta had’awa zahra ruwan wanka, daga nan kuma ta d’auro alwala ta futo. Sai da ammi ta zauna ta qara rarrashin zahra sanan tace mata ta shiga toilet tayi wanka, sanan tayi alwala, jiki na rawa zahra ta miqe da kyarma take tafiya, sabida rashin kwarin ciki da rashin cin abinci.

Da sauri ammi ta riqe ta tare da cewa zahra anya zaki iya wankan nan ko dai nayi miki ne? Girgiza kai zahra tayi tare da cewa zan iya ammi, sai da ammi ta raka zahra har toilet sanan ta futa ta fara gabatar da sallah, tana idarwa ta futowa da zahra kayan da zata sa sannan ta fuce.
Lokacin da zahra ta futo daga toilet har ammi ta futo mata da kayan da zata sa, dan haka ba 6ata lokacin zahra ta fara shiryawa bayan ta shirya ta zira hijab itama ta fara gabatar da sallah ta . Zahra tana idar da sallah ta yi addu’o’i sannan ta koma kan bed ta kwanta.

Kimanin wajan minti ashirin zahra tayi a kwance sai ga ammi ta shigo hannu riqe da cup. Zahra miqe kisha shayi hanjinki ya warware, jiki ba kwari zahra ta miqe hannu na rawa zata karb’i cup d’in shayin, girgiza kai ammi tayi tare da cewa naga jikinki ba kwari bari na baki a baki. Haka ammi tai ta bawa zahra shayan a baki. Zahra tana shan rabin cup tace ta qoshi, amma sai da ammi ta takura mata ta shanye shi tass.

Daga haka ammi ta miqe ta fuce da cup d’in a hanunta. Bayan minti goma sai ga ammi ta dawo hannu riqe da plat d’in shinkafa da wake, qarasowa tayi tare da cewa mai sunan hajiya tashi kice abinci, girgiza kai zahra tayi tare da cewa ammi na qoshi shayi da nasha ya cika min ciki, haba mai sunan hajiya ai shayi ba abinci bane, abinci da kika fiso fa na dafa miki, haka dai ammi tai ta yiwa zahra magiya akan taci abinci amma sam zahra taqi.

Suna cikin haka sai ga dady da abdul sun shigo hannu riqe da ledeji. Suna qarasowa suka zub e ledojin a gefe, dady ne yace mamana tashi, na siyo miki abinda kike so, da sauri ammi tace gaskiya dai gwara da ka siyo mata, dan kamar kasan tun d’azu nake da ita taci abinci taqi. A ala dole zahra ta tashi sabida sam batasan cin komai a halin da take ciki. Haka dady da ammi suka ringa bawa zahra abinci a baki kamar wata ‘yar baby.

Sai da dady ya rarrashin zahra sosai sanan ya fuce yabar d’akin, itama ammi fucewa tai tabar zahra da abdul a bedroom d’in. Kallan abdul zahra tayi tare da cewa yaya abdul da gaske kasan mamana, d’aga kai abdul yayi tare da cewa Wallahi zahra da gaske nasan mamanki kuma kamar yanda hajiya kaka ta gaya miki har dafa kai na tayi ta cemin na dai na jin tsoro ni namiji ne kuma sannan tace na kula mata da ke.

Nan da nan idon zahra ya sake cikowa da kwalla, da sauri abdul ya fara sharewa zahra hawaye tare da cewa har yanzu zahra in ganin fuskar mamanki in na rufe ido na, kuma in sha ALLAH watarana zaku had’u da ita. Cikin kuka zahra tace haba yaya abdul tayaya zan sake had’uwa da mahaifiyata bayan yaya mashkhur ya riga da ya yarda takaddar addres d’in gidan namu kuma an qona.

It’s okay zahra dan ALLAH mubar maganar nan kuma ya kamata ki ringa sawa zuciyar ki watarana zaki had’u da iyayan ki, haka dai

Please Login or Register in order to submit comment