Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai sun tafi tare. Mashkhur yaqi amincewa da hakan har sai da dady yayi mai alqawarin, bayan sun dawo daga rasha in dai mashkhur ya gyara halayarsa zai raba auran, sa da zahra,
hakan ne yasa mashkhur ya amince zai tafi da zahra. Zahra bataso tafiyar ba, amma yanda dady ya ringa yi mata magayi hakan ne yasa ta amince.

Dady da abdul harma da ilham sunyiwa zahra da mashkhur rakiya zuwa rasha. Kuma sun kawana biyu har dady ya sa zahra a makaranta, sannan ya siyi sabuwar motar ya bawa Ahmad, akan ya ringa Kai zahra makaranta, sabida dady yasan mashkhur bazai kai zahra makaranta ba. 6angan mashkhur kuwa ya d'au alwashin sai ya azaftar da rayuwar zahra ta hanyar duka da quntatawa.

Mun tsaya a dai-dai in da mashkhur ya tafi raka su dady airport yabar zahra a gida tana ta shar6ar kuka. Bayan ya kai su dady airport jirginsu ya tashi, jiyowa yayi gida zuciya cike da farin ciki dan yasan ko ba komai zai quntatawa rayuwar zahra..........
YANZU ZAMU CIGABA.




ZAHRA..

Kuka take sosai, dan tinda su mashkhur suka fita take wajan a zaune take kuka. Babban abinda yake d'agawa zahra hankali da kuma qarasa ta, kuka tasan yaya mashkhur baya santa kuma ya tsane ta, dan haka tasan sai kuma ta ALLAH dan tasan sam bazai raga mata ba. Bayan haka kuma ga jimamin rashin yaya abdul, da ilham dasu ammi da amir, dama sauran 'yan uwanta.

Sam zahra bataji qarar shigowar motar mashkhur ba sabida ta tafi doniyar tinanin makomarta a wajan mashkhur.
Qarar turo qofar ne yasata zahra dawowa daga tinanin data tafi, da sauri ta d'ago ta zubawa qofar ido, a razane. 4 eyes sukayi da mashkhur yana watsa mata wani mugun kallo. Nan da nan zahra ta dabarbarce, gabad'a jikinta ya d'auki rawa.

Fuska ad'aure mashkhur ya fara qoqarin tinkaro zahra. Zahra kuwa da taga hakan a firgice ta miqe, ta kwasa da gudu domin, neman mafaka, dan tabbas tasan ko ba'a gaya mata ba, mashkhur dukanta zai yi. Zahra bata tsaya ko inaba, sai cikin bedroom, tare da fad'awa kan bed tana mayan da nunfashi, dan ko ba komai tasan tinda ta gudo bedroom ta tsira, dan tasan mashkhur bazai ta6a biyota bedroom ba domin ya dake ta.

Mashkhur yana ganin zahra ta watsa da gudu ya jinjina kai tare da furta, yaro kenan in yau kin gudo, gobema ranace ai. Daga haka ya juya ya rufo qofar ya nufi bedroom d'in sa. Mashkhur yana shiga bedroom d'in sa yayi tiris saka makwan abinda ya gani. Zahra ce zaune akan bed d'insa tana mayar da nunfashi. Kamar ancewa zahra ta kalli bakin qofa, taga mashkhur a tsaye fuska ba wasa. Sosai zahra ta zaro, idanuwanta suka futo waje, ai sai yanzu zahra ta tinama wai ashe d'akin mashkhur ta shigo.

Muryar mashkhur taji ta daki dodan kunana ta, yana cewa! Kwarai, ai basai kin nunamin ke cikakiyar mara kunya bace, ko da yake ai banga laifin kiba, jikinkine kawai bai yi tsamiba, ya qarasa maganar yana qoqarin zare belet d'in ugunsa. Gumine ya tsinkewa zahra, dan tasan tabbas ta shiga hannun mashkhur tofa, sai yanda ALLAH yayi. Ganin zahra bata da mafita kuma ga mashkhur yana gab da, gama cire belet d'in ugunsa, hakan ne yasa zahra ta nufi toilet a guje ta shige tare da banko qofar.

Shima mashkhur da sauri yabi bayanta tare da banka qofar da qarfi. Amma sai dai kashhh zahra ta sawa qofar toilet d'in saqatar , hakan ba qaramin 6atawa mashkhur rai ya sakeyi ba, kwafa yayi, tare da juyawa ya koma kan bed d'in. Zama yayi yana tinanin yau wana kalar duka zaiwa zahra, dama abu kad'an mashkhur yake jira ya daki zahra kuma gashi ya samu.

Miqewa yayi ya d'auki wayarsa, miss call d'in zee ya gani a jere. Ajiyar zuciya ya saki tare da ajiye wayar a gefansa, Yana ajiyewa yaji wani kiran ya sake shigowa, juyawa yayi tare da zubawa wayar manyan idanunsa Stil zee ce take kira. Miqa hannu yayi tare da janyo wayar, sanan ya d'aga ya kara a kunnan sa. Shiru yayi baiyi magana ba yana sauraran ta.

Cikin English take mai magana da cewa!! Gaskiya baby nifa nagaji, wai yaushe su dady zasu koma Nigeria ne?, shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba. Hmmm ni dai honey gaskiya na gaji, da rashin ganinka yanzu zanzo na ganka, kaga daga nan sai na gai da dady koh?. Murya a sanyaye mashkhur yace aa zee ki bari zuwa gobe sai kizo, karkizo yau.

Wani siririn ihu zee ta saki cikin farin ciki tace wow really my honey?. Cikin qosawa mashkhur yace yes im really zee, thank you so much my honey i really miss you, da fatan bazakai min iyaka da kanka ba kamar yanda ka saba?. Kitt mashkhur ya kashe wayar, sam bayaso zee tazo, sabida takurawa rayuwar sa take, shiyasa yace ta bari zuwa gobe.

Daga haka mashkhur ya d'auko laptop d’in shi, ya fara, dannawa. Har misalinqarfe qarfe d'aya na rana zahra bata bud’e qofar toilet d'in ba. Kuma gashi mashkhur yana san shiga toilet yayi alwala domin tafiya masallaci. Ba yanda mashkhur ya iya haka ya wuce toilet d'in falo yayi alwala sanan ya dawo bedroom d'in nasa.

Yana shiga bedroom d'in qofar toilet d'in ya zubawa ido ba qiftawa. Can kuwa ya qarasa bakin toilet d'in, tare da qara murd'awa key, d'in da yake jiki qofar yanda bazata iya futowaba. Daga haka ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya ya d'auki dadduma ya fice daga bedroom . Lokaci da ya sauka qasa shima ahmad ya futo dan haka ba 6ata lokaci suka wuce masallaci.

Bayan sun dawo ahmad biyo mashkhur yayi sama, suka zauna a falo, Suka hau hira. Suna cikin hira ahmad yace gaskiya mashkhur yunwa nake ji, ya qarasa maganar yana qoqarin d'aukar wayar sa, mashkhur kuwa kallansa yayi tare da cewa to yanzu da kake gayamin, so kake na dafama kokuwa?. Zaro ido waje ahmad yayi tare da cewa tabb, ni na isa nace ka dafamin abinci kai da ko amaryarka baka dafawaba bare wani.

Cikin mamaki mashkhur yace waca amarya kuma?. Harara Ahmad ya watsamai tare da cewa matarka mana, shiru mashkhur yayi yana nazarin zancan Ahmad. Wani dogwan tsaki mashkhur ya saki lokacin da ya tina da zahra, dan shi sam ya manta da rayuwar wata zahra ma. Kai mashkhur amma baka da kirki yanzu har ka manta da amaryar taka?. Ko kallansa mashkhur bai yi ba, ya lumbe ido kamar wani mai bacci.

Murmushi ahmad yayi tare da cewa bari nayi mana oder abinci mai kake son ci ne?. Shiru mashkhur yayi na d'an wasu lokutan kafin yace duk abinda kai oder in dai inaci zanci. Okay tom ita matar taka mai takeson ci?. Shiru mashkhur ba amsa, haba mashkhur, tambayarka nake fah cewar ahamd. Oho nima I don't no mashkhur ya fad'a a taqaice.

Okey go and ask shi pls?. Bud'e ido mashkhur yayi tare da cewa wai kai meye damuwarka da yarinyarce ne? Ya qarasa maganar yana tsare ahmad da ido. Damuwata da ita shine, taci abinci, okay ai tinda kasan hanya sai kaje bedroom d'in ka tambayeta mai take so. Girgiza kai ahmad yayi tare da crwa ai ni ba maharraminta bane da zanje d'akinta kai ya kamata kaje tinda kai ne mijinta.

Wani banzan kallo mashkhur ya watsawa ahmad da yaji ya ce wai shine mijin zahra. Look Ahmad pls don't disturb me, live me a Alone. Daga haka ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu. Ahmad dai yana zaune yayi musu oder shi da mashkhur harma da zahra. Ko 30 mint ahmad bai yi da oder ba, sai gashi ankawo musu.
Zama sukayi shida mashkhur suka faracin abincin.

Bayansun gamaci Ahmad yacewa mashkhur!! mashkhur pls tashi ka kai mata abinci nasan tanajin yunwa. Kallansa mashkhur yayi tare da cewa wakenan?, matarka mana Ahmad ya fad'a a dake. Kaga Ahmad daga yau karka sake cewa waccan banzar yarinyar matata, kaji ni ba?. Cikin mamaki Ahmad yace banza kuma? Shiru mashkhur yayi ba amsa. Jinjina kai Ahmad yayi yace to yasunan ta?, shiru mashkhur yayi yanaso ya gayawa Ahmad sunan zahra amma, sam bayaso kwata-kwata ya ambaci sunan ta, shiyasama yayi shiru.

Miqewa mashkhur yayi ya wuce bedroom yabar ahmad cike da mamaki. Tabbas Ahmad yasan mashkhur bayasan auran nan amma bai san mashkhur ya tsane ta kamar haka ba. Tinani ya tafiyi lokacin da mashkhur ya bugomai waya yana sanar da shi za'a aura mai zahra, tinanin lokacin da mashkhur yake cemai dady ne sukace dole sai ya aure ta, har ahmad yace mai yasan su dady bazasu za6amai matar banzaba, bud'er bakin mashkhur yace amma ahamd bakasan wace zahra ba shiyasa.

Shiru Ahmad yayi a zuciyar sa yace gaskiya tabbas da akwai dalili da yasa mashkhur ya tsani zahra, dan ruwa baya tsami banza. Daga haka Ahmad miqewa yayi yabar part d'in mashkhur d'in gaba d'aya.
6angaran mashkhur kuwa yana bari falan ya wuce bedroom d’in sa. Ko takan toilet d'in da zahra take cike bai biba, ya haye kan bed yayi kwanciyar sa. Wani iri ya ringa jin jikinsa yana mai ba dad’i sabida bai sha kayan mayan daya saba ba.

Wayarsa ya d'auka ya turawa zee message d'in in zata tawo gobe, ta tawo mai da kayan mayan da suka saba sha, daga haka ya kashe wayar gaba d'aya, bacci mai nauyi ya kwashe shi.
6angaran zahra kuwa tinda taji mashkhur ya qarawa toilet d'in key hankalinta ya tashi sosai, duk da kuwa toilet d'in, a wanke yake tass ba datti kamar ka zuba ruwa a qasa ka kasha. Hankalin zahra bai sake tashi ba sai lokacin da taji kiran sallah azahar , dan babban tashin hankalin zahra lokacin sallah yayi kuma batayi ba.

Da taga lokaci yana qoqarin qurewa zare saqatar tayi murya na rawa ta fara bawa mashkhur haquri akan ya bud’e ta tayi salah. Alokacin kuwa mashkhur bama ya gidan dan sun tafi sallah da Ahmad, kuma da suka dawo, zama sukayi a falo sukai hira sanan suka ci abinji. Lokacin da mashkhur ya dawo bedroom d'in har zahra ta gaji da magiya, qafafuwa sunyi jajjin sun suntuma sabida tsayuwar da tai. Da zahra ta gaji da tsayuwa jakuzy ta shige ta zauna, da yake ba ruwa a cikin jakuzy d'in. KifaI kanta tayi a guiwowinta ta fara kuka mara sauti.........

A guje mashkhur yake bin zahra, tana gudu yana binta, bedroom zahra ta shige, tana shiga ta fara qoqarin rufe qofar, amma ina kafin ta rufo mashkhur ya danno kai cikin bedroom d'in, shima ya shigo yasawa qofar key. Kuka zahra ta farayi tana ja da baya, sabida tsoran hukunci mashkhur a gareta. yana qoqarin dukan zahra, yaji muryar dady yana cewa mashkhur zoka bud'e qofar nan?.

Wlh mashkhur ka sake ka daki zahra sai ka gama da 6acin rai na. Dady yana rufe bakinsa ammi ta d'ora da cewa! Au mashkhur haka mukayi da kai? Sai da na roqeka akan karka daki zahra, amma bakaji ba, wai sabida mai bakajin magana tane?, wlh har dai ka daki zahra ALLAH ya isa ban yafema ba, kuma in sha ALLAH sai Allah ya bi mata haqqinta, sanan daga yau BANI ba KAI sai dai ka nemu wata UWAR.....

A firkice mashkhur ya farka daga nannauya baccin da ya tafi saka makwan kiran sallah la'sar d'in da ake, hankali a tashe yake furta haba ammi, karki min haka mana akan wanan yariyar, da kinsan ASA. Shiru mashkhur yayi bai qarasa maganar ba, da ya fahimci mafarki yake. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki. Karaf idanunsa suka sauka akan toilet d'in da zahra take ciki, sai a lokacin mashkhur ma ya tina da ya rufe wata zahra a toilet.

Da sauri ya miqe ya nufi toilet, yana zuwa ya murd'a key d'in toilet tare da turawa. Da mamaki sai ya qofar ta bud'e, azuciyar sa yace kenan ta bud'e saqatar?. A hankula ya fara tura kai toilet d'in. Yana shiga Suna 4 eyes hankalin zahra ya sake tashi, tanaso ta futo daga jakuzy d'in amma ina sabida tsoro ko miqewa ta kasa. Nan da nan magaganin da ammi tai gaya mai a mafarki suka shiga dawo mai kai. Rintse idanuwansa yayi sabida tsabar baqinci da tsanar zahra, haka nan yaji bazai iya dukan zahra ba, sabida gani yake kamar abinda ammi ta gaya mai a mafarki da gaske ne,.

Wani siririn tsaki yaja tare da zubawa zahra wata uwar harara, da sauri zahra ta sunkuyar da kanta jiki sai kyarma yake sabida yau tasan kashinta ya bushe. Wata gigitacciyar tsawa mashkhur ya sakarwa zahra wanda sai da ta kusan sakin fitsari a wando. Dallah banza zoki fice daga bedroom d’in nan, ko wlh na karya qasusuwan ki gutsi-gutsi, yanzu yanzu nan.

Nan da nan jikin zahra ya hau tsima, qafafuwa na rawa ta fara qoqarin fuzowa daga jakuzy , saura qiris, ta su6ale a qasa sabida tsoro da kuma santsin jakuzy. Wata tsana da haushin zahra ne suka rufe mashkhur, wani dogwan tsaki, yaja tare da juyawa ya fuce daga toilet d'in sabida sam bayasan ya qarasa had'a ido da ita. Jiki na sassarfa zahra ta fara qoqarin fita daga toilet d'in tana zuwa qofar toilet d'in ta tsaya, tare da sa kanta ta leqo, domin taga mashkhur d'in yana nan ko kuwa?.

a tsaye ta ganshi ya juya mata baya tare da riqe ugunta da hannu biyu kamar mai shirin dambe. Shiru zahra tayi tana tinanin taya zata fita, dan tasan halin mashkhur da mugunta ko kwakwaran motsi tai wanda bai gamsar dashi ba sai jikinta ya gaya mata. Kamar mashkhur yasan zahra tana bayansa tana leqe, cikin d'aga murya yace, wai uban me kika tsayayi ne aciki, ko sai na shigo na yi ball dake, na 6a6alaki ne Zaki fito? Wlh ko minti d'aya kika qarayi a cikin toilet d'in nan sai na baki mamaki banza yarinya kawai.


Ai kuwa zahra tana jin haka ta kwasa a guje tabar bar toilet d'in. Wani dogwan tsaki mashkhur yayi har ya juya zai shiga toilet d'in ya fasa sabida zahra ta zauna a ciki, toilet d'in falo ya wuce yayi alwala, sanan ya koma d'aki yayi sallah da yake lokacin tafiya masallaci ya wuce.
6angaran zahra kuwa tana futowa daga bedroom d’in mashkhur a guje ta wuce d'ayan bedroom d’in tare da qara mai key.

Fuskarta duk ta kunfura tayi ja, ga qafafuwanta duk sun sage, sunyi sanyi. Jiki ba kwari zahra ta wuce toilet tai wanka, bayan ta gama wanka ta d'auro alwala ta futo. Tana futowa ta zira kayanta sanan ta shinfid'a dadduma. Dakyar zahra ta iya tsuyuwa ta gabatar da sallah da ake binta, bayan ta idar da sallah, azahar, zama tayi sanan ta fara la'asar sabida bazata iya tsayuwa ba, qafafuwanta zafi suke mata.

Zahra tana gamawa zayi addu’a sanan ta hau kan bedroom ta shige bargo ta fara kuka mai cin rai, mara sauti. Tinani take taya zata cigaba da rayuwa da wanda baya qaunar ta, kuma yake zalintar ta. Ji tai duk duniyar ta fita daga ranta, ga tsanar mashkhur data ke qara nukuwa a zuciya. Duk duniya ba wanda zahra ta tsana kamar mashkhur, dabadan dady ba wlh ba abinda zai sa ta baro cikin 'yan iwanta ta biyu mashkhur rasha l.

Haka dai tai ta kuka tana tinani, ga wata uwar yunwa da take addabar ta, da yake rabanta da abinci tun jiya da daddare, da sukaci ita da ilham, ko abincin safe bata samu taciba. Zahra tana so ta fita ko zata samu abinda zata sa a cikinta amma ina tsoran mashkhur ya hanata futa, haka dai ta qudidine har bbacci yayi awan gaba da ita.

6angaran mashkhur kuwa bayan ya idar da sallah bai koma bedroom d’in saba a falon ya zauna ya kunna kallo. Sam hankalinsa baya kan kallo, kawai tinani yake ta waca hanya zai hukunta zahra? Dam wlh ya d'au alwashin sai ya quntatawa zahra. Dan gani yake ADALILINTA komai yake faruwa da shi. Wani dogwan tsaki mashkhur yaja, a zuciyar sa ya ce wai ni za'a aurawa ita?, kai gaskiya dady bai yi min adalci ba, ya lalatamin rayuwata.

Zuciyar mashkhur duk sai tai mai badad'i can kuma da ya tinada yarjejeniyar da sukayi da dady akan zai rabuda zahra bayan sun koma Nigeria sai kuma yaji zuciyarsa tai mai sanyi. Haka mashkhur ya zauna yanata saqa da warwara. Yanzu mashkhur ya gama tinanin hanyoyin da zaui bi ya takurawa zahra ba tare da ya dake taba. Magariba tanayi mashkhur yayi alwalaya fice masallaci, bashi ya dawo ba sai, bayan sallar isha.

Misalin qarfe goma na dare zahra ta riga da ta gama galabai ta da yunwa, dan haka ta riga da ta yanke shawarar ko kasheta mashkhur zai yi sai ta fita, ta samu abinda zataci, dan yunwa bazata kasheta ba. Jiki na rawa ta sakko daga kan bed d’in, sanan ta nufi qofar fita tana qarasawa ta bud’e qofar sanan ta fice. A hankula ta fara sand'a domin kar mashkhur ya jiyota.


Taci sa'a baya falon tv ce a kunne sai kuma globs akune da suka gaske d'akin , a hankula zahra ta kama hanyar kicin. Karaf idon zahra ya sauka akan takeaway d'in da ahmd yayi musu oder abinci. A fili zahra ta furta Alhamdulilah tare da nufar table d'in da aka ajiye abincin. Tana qarasawa hannu na rawa ta fara qoqarin bud’e ledar. Tana bud'ewa ta ajiye takeaway, d'in a baganta tare da d'ebo abincin da hanunta takai bakinta, ai zahra bata qarasa kai abincin bakintaba tayi 4 eyes 👀 👀 da mashkhur yana watsa mata wani razanannan kallo
Fuska a tamke...............


ADALILINT 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240

Typing............

*page 52*

Tana qarasawa hannu na rawa ta fara qoqar bud'e ledar. Tanada bud'ewa ta ajiye takeaway d'in a gabanta, tare da d'ebo abincin da hanunta ta kai bakinta, ai zahra bata qarasa kai abincin bakinta ba, tayi 4 eyes 👀 👀 da mashkhur yana watsa wani mata razanan nan kallo fuska a tamke................

Nan da nan zahra ta nemi yunwar da take damunta ta rasa tare da saurin zube abincin hanunta a cikin takeaway d'in. Mashkhur yakai wajan minti uku a tsaye yana watsawa mata mugun kallan nan, ita kuma zahra baiwar Allah ta sunkuyar da kai gumi yana ta tsa-tsafo mata. A hankula mashkhur ya fara qarasowa inda zahra take, ita dai zahra ta rufe indonta gam tana jiran jin saukar duka a jikinta.

A zuciye mashkhur yasa hannu tare da fuzgo ledar takeaway d'in, ai kuwa abincin ya watse qasa gaba d'aya. Sam mashkhur bai ji dad'in zubewar abincin ba, sabida bayasan asarar abinci tun yana yaro ammi ta ta6a gaya masa bakyau zubar da abinci ALLAH bayaso shiyasa shima baya yin hakan. A tsawace mashkhur yace wallahi kashedi na qarshe zan miki daga yau kika qara ganin abinda kikasan banaki bane kuma baki ajiyeba, kika d'auka wallahi sai jikinki ya gaya miki.

au wai ke har ma kina tinanin zaki iya cin abincin dana ci na rage, ai baki kai wanan matsayiba, ke ko bani naci na rage ba baki isa anyu miki oder abinci a gidannan kinciba, sai dai ki dafa da kanki kici, in kinga dama kenan in kuma baki dama ba ko baki iya dafawaba sai dai ki mutu da yunwa, na rage mugun iri kenan ya qarasa magana yana zabga mata harara. Zahra dai shiru tai kuma har yanzu bata bud'e idon nata ba sabuda tsoro.

Wani dogwan tsaki mashkhur yaja tare da juyawa zai koma room. Har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya tare da cewa koma ki gyara wajan nan, tass kafin na fito dama hakan ne ya dace dake, dan karma ki tinanin hutu kikazo yi nan, yana gama fad'ar haka ya cigaba da tafiyarsa, ya shige bedroom d'insa tare da banko qoafar da karfi. Wasu zafafan hawayene suka silalowa zahra a kumatu ta, sabida har ga ALLAH taji zafin magagani da mashkhur ya gayamata har cikin ranta.

Hannuwanta biyu tasa ta share hawayanta tare da miqewa ta nufi ventilation. Abin shara ta d'auko ta share abincin da mashkhur ya zubar sanan ta goge wajan, ta fesa mai air-freshener, waje yayi tass kamar ba azubar da komai ba. Daga haka ta wuce kicin a hanzarce, tana shiga ta fara bud'e drowar kayan abinci. Da akwai kayan abinci kala-kala, dama dady ya zuba komai na kayan abinci ba abinda babu.
Nazari zahra ta farayi mai zata dafa, wanda ba zai d'auke ta lokaci ba.

Har ta yanke shawarar ta dafa indomie sai kuma ta fasa, sabida tasan halin mashkhur da mugunta yanzu yana qara fitowa sai ya hanata jin abinci gaba d'aya. Dan haka Cornflakes ta d'auka guda biya da kuma biscuit shima guda biyu. Sanan ta d'ora ruwan zafi na shayi a cttle ko minti biyar bai yi ba ya tafaso. A cup ta zuba sanan ta zuba mai shuger, bayan ta zuba mai shuger ta zuba madara a wani cup din na daban, sannan ta dakko ruwa.

A madai-dai cin plet ta jera kayan sanan ta d'auka ta nufi d'akinta a salale6e, ko kwakwaran taku bata iya yi sabida mashkhur karyaji ta. Tana shiga ta ajiye plet d'in sanan ta kulle qofar ta qara mata da key, daga haka ta dawo ta zauna kusa da plet din. Kallan agogon tayi, qarfe goma da rabi na dare jinjina kai zahra tai tana mamaki wai yau itace tin da safe bataji abinciba har qarfe goma da rabi, kuma ita ba azumiba ai koh azumi tai bazata kai haka ba. Afili zahra ta furta gaskiya yaya mashkhur mugune ta fad'a murya qasa-qasa.

Hannu tasa ta d'auk cup din t d'in ta fara sha sabida ya warware mata hanji. Sai da tasha rabin kofi sanan ta fara had'awa biscuit d'in, bayan ta gama shanye t da biscuit d'in sanan ta had'a confilask da madara ta fara sha. Sai da zahra ta cinye komai tass sanan ta had'a da ruwa tasha. Ajiyar zuciya ta sauke, tare da furta alhamdulilah. Daga haka zahra ta miqe tayi alwala tai sallah isha'i dama batayiba sabida yunwar da take damunta, bayan ta idar da isha'i raka'a biyu tayi tare da kaiwa ALLAH kukunta, akan mashkhur.

Bayan ta idar kayan jikinta ta canza zuwa kayan bacci. Sanan ta kwanta akan bed tare da lili6e jikinta da bargo, tinanin zahra ta tafi, na kalar rayuwat da zatai da mashkhur harna tsawa shekara d'aya da rabi. Ya salam abinda zahra ta furta kenan sabida tasan tabas abu mai wuya suyi rayuwa tare da mashkhur ba tare

Please Login or Register in order to submit comment