Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so naga wannan yarin yar da dadyn abdul yake qaunar ta haka, kuma gashi abdul ya maqale mata. Hmmm ke dai bari saratu Wallahi na tsani yarinyar nan sai nayi maganin ta. Ajiyar zuciya saratu tayi tare da cewa amma yaya halima ke mene na tayar da hankalin ki dan mashkhur zai bar qasar ai wlh ancuce shi duk shekarun da yayi yana karatu kinga sun tashi a banza.

Hmmm amma saratu bakya ganin da matsala nifa banason d’an maryam yafi nawa kuma bana so naga mashkhur yaci gaba a rayuwarsa karfa ki manta na d’au alwashin sai naga bayan mashkhur. Murmushi saratu tai kamar momy tana gaban ta, haba yaya halima dad’i na dake garaje, ki rabu da shi mana ya tafi karatun, wahalama ta ishe shi, ai haka zai qare a karatu kullum ba cigaba, kuma kinga tundda ga farko zai fara” wai shekara nawama zai yi?.

Nunfashi momy ta sauke kafin tace shekar hudu zai yi. Dariya saratu tayi tare da cewa kingama kafin ya dawo duk mun gama shirya-shiryan mu yana dawowa sai dai muga bayan sa koh?. Dariya momy tayi tare da cewa shegiya saratu shiyasa fa nake sonki sabida kin iya tunggu, itama saratun dariya tayi, haka sukai ta hira, sai da sukayi wajan 10 minit sannan sukayi sallam, haka momy ta kwanta zuciyar ta wasai.

6angaran mashkhur kuwa baqin ciki yabi duk ya ishe shi, yama rasa mai zai yi zuciyar sa tayi mai zafi ji yake kamarma ya kashe kansa ya huta. Tinani ya shiga yi taya zai dakatar da tafiyar sa qasar rasha?. Duk tunanin mashkhur ma ya kulle sabida yasan halin dady magana d’aya yake, in dai dady yayi maga baya janyewa. Tinani mashkhur ya farayi Wai yanzu duk ADALILINTA nake cikin wannan damuwar, kuma ADALILINTA zan bar gidan ubana?.

Washegari......

Bayan yaran gida sun gama breakfast makaranta suka tafi, har ma dasu zahra yau sun koma makaranta, abdul kuwa dama tunda sassafe ya fuce sabida yau suna da lecturer. Dady mah tun da safe ya fita. Gida ya rage daga ammi sai hajiya kaka da momy sai kuma mashkhur.
Mashkhur yana cikin damu dan ko abinci ma ya kasa ci, dan sam har ga ALLAH baya son tafiya RASAHA, ga kuma baqin cikin rusa mai karatu ya dawo baya.

Jiki ba qwari ya shiga toilet yayi wanka, bayan yayi brush ya futo ugu daure da towel. Yana futowa ya fara shiryawa cikin farar riga t-shirt anmata gwara-gwaran rubutu da black color ansa MOOD a gaban rigar, rigar tana da kauri sosai sabida yanayin garin an tashi da sanyi. Shima wanda rigar black ne, sai kusma hular sanyi black. Hmmm ai koni amina bayero da naga mashkhur sai da ya birgeni sabida yayi kyau kuma ya had’u sosai.

Key d’in motar sa ya d’auka sanna ya fice daga part d’in. Yana futa bai nufi ko ina ba sai part d’in hajiya kaka. Da sallama ya shiga falon nata, ai kuwa yaci sa’a tana zaune tana jan carbi. Qarasawa yayi kusa da ita yayi ya zauna har jikin su yana gogar na juna. Addu’a hjy kaka ta shafa. Kallansa tayi tare da shafa kuma tunsa” fuska ta d’auke da murmushi tace haba mai sunan malam ka saki ranka mana sai wani 6ata fuska kake.

Kallanta yayi da idon sa da yake ta faman lumshewa sabida rasahin ishashan bacci. Hmmm hjy kaka kenan ina cikin wannan baqin ciki zakice na saki rai na, haba mai sunan malam to mene na baqin ciki kuma?. Marairai cewa yayi tare da cewa dan Allah hajiya kaka ta taimako na zakiyi. Kallansa tayi cikin mamaki tare da cewa tai mako kuma mai sunan malam?, da sauri mashkhur ya d’aga kai alamun ehh.

Jinjina kai hjy kaka tai tare da cewa to inaji ka mene? A jiyar zuciya mashkhur yayi kafin yace dan ALLAH hajiya kaka ki tai maka kiyiwa dady magana akan tafiya ta RASHA karatun nan, Wallahi sam bana son naje, kuma kinga saura shekara guda na gama karatuna, amma Wallahi in na fita wajen nan daga farko zan dawo kinga ai wahala zan sha, nasan dady yana jin maganar ki, in dai kika bashi haquri zai haqura.

Gyara zama hajiya kaka tayi sanna tace gaskiya ne nasan tabbas na gayawa abubakar magana yana ji, amma mai sunan malam sai da kayi HAQURI sabida sam bana so na hana Abubakar abinda yake so, tinda ya riga ya yanke hukunci kaga bai kamata nasa baki na ba. Da sauri mashkhur ya riqe hanun hajiya kaka yana yimata magaya amma ina hajiya kaka sam taqi amincewa, dan tace ita baza tai wa dady dole. Jiki ba kwari mashkhur ya fuce daga part d’in hajiya kaka ya wuce na ammi.

Yana shiga part d’in ammi ya haye sama bai tsaya a ko ina ba sai bedroom d’in ammin. Da sallam ya shiga, a zaune akan bed ya same ta tana ninke kayan ta. d’agowa ammi tayi kafin ta amsa mai da kyar kamar wanda batason magana, da sauri mashkhur ya qaraso ya zauna suna faces d’in juna. Ammi kuwa had’e rai tayi sosai, tare da cigaba da abinda take.

Shima mashkhur d’in hannu yasa ya fara tayata ninke kayan. Dama mashkhur tun yana yaro yana yawan ninkewa ammi kaya ko ya tayata, haka ammi tai ta tananin lokacin. Har mashkhur ya qarasa ninke kayan yakai wardrobe amma ammi bata dawo daga tinanin da ta tafi ba.dawowa yayi ya zauna a inda ya tashi tare da riqe hanunta, sai a lokacin ammi ta dawo da hayya cinta, da sauri ammi ta kwace hanunta daga hanun mashkhur tare da juya mai baya tai kwanciyar ta.

Lumshe kyawawan idanun sa yayi tare da shafa kefan fuskarsa da hanun hagu. Ammi, ammi, ammi? Shiru ammi tayi mai bata amasa mai kiran da yayi mata ba. Kwantar da murya yayi tare da cewa ammi pls forgive me. Amma shiru ammi taqi bawa mashkhur amsa, ammi nah ki saurare ni mana pls. Da ammi ta gajiya da magiyar mashkhur rufe ido tayi kamar mai bacci. Tagumi mashkhur ya rafka dan sam baya so yaga ammi tana fushi da shi, dan da momy ce ko wani bazai tsaya naci da magi ba kawai dai dan mahaifiyarsa ce kuma bazai jure fushin taba sabida yana qaunar mahaifiyar tasa.

Matsawa yayi ya zauna a kusa da kanta, yaci sa’a, d’an kwalin ammi ya zame, hannu yasa ya fara wasa da jelar gashin ammi, dama sometimes in ammi tana fushi da mashkhur, kwanciya take ta juya mai baya, shikuma in dai ta juya mai baya ta kwanta wasa yake da jelar gashin ta tun yana yaro har yau bai dai na ba, abinda mashkhur yake nufi da hakan haquri kawai yake bata. Sunyi tsawan minti goma mashkhur yana wasa da jelar gashin ammi, sam yaqi ya dai na kuma itama taqi ta juyo.

Can ammi ta bud’e idon ta tare da cewa sakar min gashina, shiru mashkhur yayi yana kallan fuskar ammi amma har yanzu yaqi dena wasa da jelar gashin nata, au ba magana nake mah ba ne?. Marairaice murya mashkhur yayi tare da cewa haba ammi in ban ta6a gashin kanki ba nawa zan ta6a?. Fuska ammi ta sake d’aurewa tare da cewa na uwar d’akin ka halima wanda bata gayama gaskiya.

To ai ita ba mahaifiyata bace, kece fa wanda ta haifeni, kinga kuwa ke yakamata nayiwa hakan. Okay ashe kasan ni na haifeka ai da nayi tinanin ka manta. Dan ALLAH ammi kiyi haquri ki tashi ki saurareni pls. Shiru tayi na wasa daqiqu daga baya kuma tace to zan tashi sakar min kai na, da sauri mashkhur ya saki jelar gashin ammi ya dai na wasa da ita. Fuska a had’e ammi ta miqe ta zauna tana faces d’in shi tare da cewa ina jinka.

Hanunta ya riqe tare da cewa ammi dan ALLAH ki tai maka kiyiwa dady magana akan tafiya ta RASHA nan wlh bana son tafiya rasah nan. Zuba masa ido ammi tayi tana kanlansa,har sai da ya bata tausayi, ga idanuwansa sai lumshewa suke alamun bai yi bacci ba. Dakewa ammi tayi tare da cewa gaskiya bazan iyaba, da sauri ya kalleta kamar zai yi kuka yace dan ALLAH ammi ki tai makamin kiyi mai magana.

Nifa bana son in dadyn ka ya yanke hukunci nasa baki kaga sai yaga kamar ina goyama baya. Marai raice murya mashkhur yayi tare da cewa pls ammi kinga fa saura shekara daya na gama makaranta anan, amma kinaji yana cewa sai na sake tindaga farko. Shiru ammi tayi na wasu mintina kafin tace okay, zan jarraba nagani, amma har yanzu taqi sakin fuskarta . A jiyar zuciya mashkhur ya saki, tare da sake qanqame hanun ammi yana cewa, dan ALLAH ammi kiyi haquri ki dai na fushi dani, wlh in kina fushi dani banajin dad’i sam bana iya jurewa.

Zuba mai ido tayi tare da cewa wai mashkhur sabida mai sam bakajin magana ne? Shiru yayi tare da sunkuyar da kai. Cigaba da magana ammi tayi da cewa yanzu sabida ALLAH dukan da kayiwa zahra ka kyauta? Kawai akan ta fasama laptop cikin rashin sani?. Dagowa yayi ya zuba mata ido tare da cewa kiyi haquri ammi na dai na. Harara ta watsa masa tare da cewa, kullum haka kake cemin ka dai na abu, amma sam ba dai nawa kake ba.

Kwantar da murya yayi tare d cewa in sha ALLAH ammi nah na dai na, jinjina kai ammi tayi tare da cewa ALLAH yasa, murya can qasa ya amsa da ameen. Sabida me bakayi bacci ba jiya? ammi ta tambaya shi. Ammi mai kika gani? Kallansa shi tayi tare da cewa ga shinan ina gani, kallifa idan ka yanda yake lumshewa. Rausayar da kai yayi kafin yace, ammi taya zan iya bacci bayan abinda ya faru jiya, zuba mai ido kawai tayi ba tare da tace mai komai ba.

Dan ALLAH ammi na ki saki fuskar ki, noqe kafad’a tayi kamar wata yarin ya alamin aa. Cikin shagwa6a yace pls smile my mom, miqewa tayi ta koma kan kujerar mudubi, alamun har yanzu bata gama saukowa ba. Da sauri mashkhur yabi bayan ta, tare da tsayawa a bayan ammi” ita tana zaune a kan kujera shi kuma yana tsaye a bayan kujerar, duk kansu suna ganin fuskokin junan su ta cikin mudubin.

Saqalo wuyan ammi yayi da hannayan sa tare da rage tsayin sa, ya kara fuskar sa da ta ammi , wani irin mugun kama sukeyi, kamar tayi kaki ta ajiye, abinda ya rabasu kawai shine mashkhur yana da hasken fata ammi kuma baqa ce, kuma mashkhur yaso yafi ammin kyau, kamar wata yaya da qaninta, dan in kaga ammi bazaka ta6a tinanin ta ajiye d’a kamar mashkhur ba. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa wow gaskiya ammi ke kyakywa ce fa, harara ta watsa mai tare da cewa yaban kai aka ce, bata qarasa ba tayi shiru.

Dariya yayi wanda ba qaramin kyau ta qara mai ba tare da cewa, ashe kin yarda muna kama kenan, shiru tai mai bata fashi amsa ba. Sosai ya qara saqalo wuyanta da hannu biyu tare da had’e fuskar su waje d’aya kamar zasuyi hoto. Waqa ya fara yiwa ammi cikin dadad’ar voice d’in sa, ba komai yake cewa acikin waqar ba face!!! Hajiya ta hajiya ta hajiya ta ni kunga hajiya ta, hajiya ta ohoo hajiya ta, ammi batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba, har sai da dimple d’in ya motsa, wushiryar ta bayyana.

Shima mashkhur murmushin jin dad’i yasa ammi dariya yayi tare da furta Alhamdulilah Hajiya ta fah tayi smile, gaskiya ammi nah bakya tsofa wai mene sirrin ne?, murmushi ammi ta saki tare da cewa au wai kai dan kaga na ajiye ka shine kake tinanin zan tsofa, to dududu nawa kake? Zaro ido mashkhur yayi tare da cewa haba ammi ki ajiye santalelan saurayi kamata 23 to 24, sanan kice nawa nake, gaskiya fa ni ammi ba yaro bane.

Lalai mashkhur girman jiki ne kawai fa shiyasa kake ganin kanka saurayi koh? Murmushi yayi tare da d’aga kai alamun ehh. Hararasa tayi tare da cewa au ko kunya tama bakaji kake cemin ka zama saurayi, dariya yayi tare da cewa ai bada bakina na fad’a ba d’aga kai fa nayi. Girgiza kai ammi tayi tare da cewa wlh baka da dama ni dai bazan biye ma ba sake ni ina da abinyi, shima girgiza kai yayi makar yanda ammin tayi tare da cewa nima ina da bainyi fita fa zanyi yana gama fad’in hakan ya sake ta tare d kallan mudubi yana gyara hular sanyin sa.

Ina zaka haka? Shiru mashkhur yayi sabida sam baya son yacewa ammi wajan cin abince zai je dan yanzu sai tace sai yaci na gida. Kawai gani yayi ammi tayi murmushi tare da cewa okay na gane inda zaka je shiyasa ka d’auki, wanka kenan? Cikin rashin fahimar in da ammi ta dosa yace, nifa ban gane abinda kike nufi ba, ina kike tinanin zani?, cikin kallan tuhuma tace wajan surukata mana!!! Cikin rashin gane maganar inda ta dosa yace ammi wacce surukar taki kike nufi bayan hajiya kaka kuma yanzu daga wajanta na zo nan ai.

Okay tinda baka gane ba bari na futoma a mutum ina nufin ZANCE zaka ta qarasa maganar tana jifansa da kallan tuhuma. Sosai mashkhur ya had’e rai tare da cewa ALLAH ya sauwaqe naje wajan wata budurwa zance ya qarasa maganar yana ta6e baki. Au yanzu fa kace min ka zama saurayi kuma kaga in mutum ya zama saurayi sai ya nemo budurwa koh? Sake had’e rai yayi tare da cewa to ai ni ammi ba irin wannan saurayin nake nufi ba.

Dariya ammi tayi harda riqe ciki, da sauri mashkhur yayi hanyar fita tare da cewa ni gaskiya ammi bana son irin zance nan nifa ba wani aure da zanyi barema nayi budurwa, dan haka sai na dawo. Har yasa kai zai fita yaji ammi tace hmm anaso ana kaiwa kasuwa. Da sauri ya jiyo ya kalle ta, ai bai san sanda dariya ta kubuce mai ba.

dariyar kuwa ba qaramin kyau tayi mai ba dan sai da dimple d’in sa da wushiryar sa suka bayyana, da sauri yasa tafin hannu ya rufe fuska tare da juyawa ya fuce dq sauri, murmushi ammi tayi sabida tana sane tayiwa mashkhur zance budurwa, sabida tasan sam mashkhur baya so ace yada budurwa ko ayi mai zancan ta. Wani farin ciki ne ya lili6e ammi sabida duk sanda ta shiga damuwa ko 6acin rai, in dai ta kasance da d’anta mashkhur sai ya sata cikin farin ciki..........

Yauwa yau su Hallom ba complen d’in banyi typing da yawa ba...😂 yau full typing nayi muku harma da qarin layi biyu.😂🙌🏻

Ayi hutun mako lafiya.... sai kuma monday, ALLAH ya kai mu da rai da lafiya, Ameen🙏🏼.

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”


ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

Typing........

*page 45*

Wani farin ciki ne ya lili6e ammi sabida duk sanda ta shiga damuwa ko 6acin rai, in dai ta kasance da d’anta mashkhur sai ya sata farin ciki...........

Mashkhur yana fita bai tsaya ko ina ba sai saban wajan cin abinan nan mai suna CALIDO. Coffee da snacks kawa yaci. ‘Yan mata kuwa sai kallan ta suke, sabida tsabar kyansa da tsaruwar sa, harma da masuyi mai sannu, amma mashkhur ko kallan su baiyi bah, daga qarshema daya gaji da nacin su tashi yayi ya fita daga calido d’in. Bayan ya futa super market ya wuce domin yin shopping, bayan ya gama shopping d’in gida ya wuce......

Misalin qarfe tara na dare ammi ta gama shiryawa tsaf domin zuwa part d’in dady da yake yau kwanan tane.
Baki d’auke da sallama ammi ta shiga bedroom d’in dady hunaun ta riqe da tire d’in abinci.
Cikin saki fuska dady ya amsa mata sallamar tare dayi mata sannu, ita ammi ciki sakin fuska ta amsa da yauwa.
Sai da dady ya shiga wanka ya futo sannan suka fara cin abincin a tare.

Bayan sun gama cin abincin hawa kan bed dady yayi ya zauna, itama ammin zama tayi a kusa da shi tare dacewa!! In ba damuwa inaso muyi wata maga?. Mai da hankalin sa dady yayi kanta tare da cewa inajin ki?. Gyara zama ammi tai tare da cewa dama akan maganar mai sunan babane, naga ka yanke mai hukunci tafiya qasar rasha karatu, amma sai nake ganin kamar hukuncin yayi tsauri, kuma kaga ya kusan gama karatun sa a Nigeria, yanzu in ya koma rasha ai kaga karatunsa zai dawo baya kuma za’a kashe kud’i a banza ne.

Mamaki ne ya kama dady akan abinda ammi tace sabida yasan tunda take a duniya bai ta6a yanke hukunci akan mashkhur tasa baki ba sai yau. Ammi kuwa cigaba da magana tayi kamar haka!! Shine nake so dan Allah yaya na roqa masa al farka akan kayi haquri ka barshi ya qarasa makarantar sa tinda kaga saura shekara d’aya ya gama.
Shiru dady yayi na wasu lokutan daga bisani ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa!!! Gaskiya ammi sai da kiyi HAQURA,.

Kuma nayi baqin cikin karo na farko kin roqe ni akan mai sunan baba kuma na kasayi miki, ina mai baki haquri. Shiru ammi tayi sabida tama rasa mai zata cewa dadyn. Dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa ammi kinga in dai muka bar mashkhur ya cigaba da zama anan, zai iya illata mamana (zahar) kuma kinga in dai mukayi hakan bamuyiwa mamana adalciba, kuma kinga mamana amace a wajan mu bai kamata muyi hakan ba.

Kingama har, nasa a kawo mai takaddun barin qasar dana makarantar da zai fara zuwa kuma an kawo min, yanzu maganar da nake miki na gama biyan maqudan kud’ad’en makaranta. Kuma nan da kwana biyar in sha ALLAH zai wuce rasha abinda nake so dake shine ki ringa yi mai addu’a kinga ke uwace yana buqatar addu’a ki. Girgiza kai ammi tai tare da cewa am!! Da sauri dady yasa hannu ya rufe mata baki tare da janyo ta jikinsa yana cewa kiyi shiru zomu kwanta dare yayi.

Tofa tin daga ranar ammi take bin dady tana mai magiya akan yabar mashkhur ya zauna a Nigeria karya tafi rasha, amma ina dady yaqi amincewa, yau kwana uku kenan ammi tana yimai magiya yaqi yadda. Daga qarshe ma da ammi ta takurwa dady da magiya fishi yayi da ita ya dai na kulata, gaba d’aya, ko tayi mai abinci ma baya ci. hakan ne yasa ammi ta lalashi dady ta bashi haquri kuma tace mai ta amince da tafiyar mashkhur. Dady kuwa yaji dad’in hakan sosai, kuma yayi firin ciki shiya kullum yake qara son matar sa ammi, sabida sauqin kanta da biyayya ba kamar halima (momy) ba, da in aka gaya mata baji.

Washegari..........

Baki d’auke da sallama ammi ta shiga d’akin mashkhur. Yana kwance yayi ruf da ciki yana danna laptop. Yana jin sallamar ammin da sauri ya mtsar da laptop d’in gefe ya miqe tare da amsa mata sallamar. Qarasawa bed d’in ammi tayi tare da zama akan bed d’in tana cewa amma dai mashkhur kasan bakyau kwanciyar ruf da jiki koh? Kwanciyar ‘yan wutace fa. Matsowa kusa da ita mashkhur yayi tare da cewa mantawa nai wlh ammi.

Jijina kai ammi tayi tare da cewa to gaskiya ka kiyaye, banaso?, tom shikenan ammi in sha ALLAH zan kiyaye.
Gyara zama ammi tayi suna facing d’in juna tare da cewa yauwa mashkhur dama inaso muyi wata maga ne?. Qara matsawa yayi gaf da ita tare da cewa tom ammi ina jinki. Zuba mai ido tayi tare da cewa mashkhur, nasan ka yarda da qaddara mai kyau da mara kyau a matsayin ka na musulmi. Karka manta duk abinda ya faru da bawa ALLAH ya riga da ya tsara hakan zai faru da bawansa, kuma komai sai da amincewar uban giji yake faru.

Shiru mashkhur yayi yana sauraran mai ammi zata gaya mai haka, tun kafin ta gayamai me ke tafe da ita kawai yaji jikinsa duk yayi sanyi. Cigaba da magana ammi tayi kamar haka!! Dan haka mashkhur kayi haquri kayiwa mahaifin ka biyayya akan tafiya rasha nan kawai ka tafi.
Gaban mashkhur ne ya yanke ya fad’i rass, sabida shi duk a tinanin sa dady ya haqura da tafiyar rasha nan, ashe ba haka zance yake ba.

Jiki a sanyaye mashkhur ya kalli ammi tare da cewa amma ammi kin bawa dady haquri kuwa?. D’aga kai ammi tayi tare da cewa wlh mashkhur ba yanda banyi da dadyn ka bah akan yayi haquri da zuwa rasha nan amma yaqi. Dafa kafad’ar sa ammi tayi tare da cewa kawai kayi haquri ka d’auki wanna a matsayin kaddarar ka ,da kuma darasi akan abinda kayiwa ZAHRA.

Murya a shaqe mashkhur yace yanzu ammi duk ADALILINTA wanan abun yake faruwa dani?. Haba mashkhur ka ringa yadda da qaddara mana ba wani ADALILINTA, hakan yake faruwa da kai dama ALLAH ya riga da ya tsara hakan, cewar ammi. Tagumi mashkhur ya raf tare da sunkuyar da kansa sabida har ga ALLAH baya san tafiyar rasha nan. Kwantar da murya ammi tayi tare da cewa haba mashkhur, ka kwantar da hankalinka, in sha ALLAH hakan ne zai zamar ma alkhairi, yanzu in kana cikin damuwa nima tayar min da hankali na zakai.

Dagowa mashkhur yayi fuska ba annuri, yace tom ammi na ALLAH yasa hakan ya zama alkhairi. Yauwa mashkhur ko kai fah, dan ALLAH ka saki ranka kaji?, d’aga kai mashkhur yayi alamun tom, jan kumatunsa ammi tayi tare da cewa smile. Ba’a san ran mashkhur yayi murmushin ba kawai sabida ya kwantarwa da ammi hankalin shiyasa, itama murmushin tayi tare da bud’e mai hannuwanta biyu alamun suyi hugging.

Jiki ba kwari ya fad’a jikinta suka rungume juna, haka ammi dai tai ta rarrashi mashkhur tana jansa da hira, har sai da zuciyar sa tayi sanyi.
To fah mashkhur bai gama gazgata gaskiya tafiyar tasa ba sai da gaya dady ya dawo, yayi mai niqi-niqi siyayyar tafiya rasha, kuma ya bashi form d’in babbar makarantar rasha yace ya cike, nan fa hankalin mashkhur ya sake tashi. Bayan ya gama cike form d’in dady ya tura mai maqudan kud’i a account yace ya siya abinda yakae buqata, nan da kwana uku zai wuce rasha.

To fah yanzu duk gida ya d’auka mashkhur nan da kwana uku zai bar qasar nan, masu alhini nayi masu kewa nayi masu kuka sunayi masu jimami sunayi. Abdul dai bai ji dad’in tafiyar da yayan sa mashkhur zai yi ba sabida suna qaunar junan su sosai, amma ina ba yanda abdul ya iya dole ya haqura.....

Misalin qarfe goman dare (10:00 pm) mashkhur yana kwance akan bed yama rasa mai yake mai dad’i sai juye-juye yake. Abinda zai baka mamki da mashkhur she sabida tsabar taurin kai da kafiyar zuciya, har yanzu bai ta6a yin nadamar dukan zahra ba ko sau d’aya, sam baya nadama dukan zahra, sabida tsabar tsanar da yayi mata.
Tinani kala-kala mashkhur yake a zuciyarsa, ba abinda zuciya take gayama face, kafin ya tafi rasha, ya d’auki FANSA akan zahra, sabida duk abinda ya faru ADALILINTA ne ya faru.

Mashkhur ya kai wajan d’ayan dare (1:00 am) yana tunanin wana mataki zai d’auka akan zahra kafin yabar gidan ammi ina sam ya kasa samun idea. Runtse ido mashkhur yayi zuciya cika da baqin ciki, ya rasa idea da zai d’auki fansa akan zahra. Har mashkhur ya fara tinanin kawai yayi addu’a bacci ya kwanta. Kamar saga sama kawai mashkhur yaji wata idea ta fad’o mai. hannuwansa biyu yasa ya daki kan bed d’in da qarfi tare da cewa dat is good idea, wanna shine fansar da zan dauka akan yarinyar nan.

Wani irin mugun farin ciki ne ya kama mashkhur nan da nan yaji zuciyar sa tayi sanyi, kamar ba abinda yake damun sa. Addu’a bacci yayi sannan ya rufe idon sa domin yin bacci, in

Please Login or Register in order to submit comment