Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ya futo ya shige part d'in shi jiki ba kwari, yanaijin wata irin muguwar kewar masoyiyar shi ilham.

Zahra tana shiga bata samu mashkhur a falon ba, dan haka dreact bedroom d'in ta nufa zuciya cike da kewar su dady, tana shiga ta baje a kan bed tana mai da ajiyar zuciya. Haka tai ta tunanin kala-kala tana qara nazarin shawarwarin da ilham ta bata, game da zee da kuma mashkhur daga haka bacci yayi awan gaba da ita.........

Washe gari.

Kamar yadda zahra take kafin su dady su dawo haka tai, bayan tayi sallar asubayi kicin ta nufa ta, fara girka abinda zataci kafin ta tafi school. Bata d'au wasu mintina ba ta gama dafa abinda zataci, bayan ta gama ta wuce bedroom d'in ta, tana shiga ta ajiye plate d'in breakfast d'in nata sanan ta shige toilet tai wanka. Bayan ta futo daga wanka kayan makaranta ta tasa sanan ta zauna ta fara cin abincin ta. Tana gama cin abincin ta ta d'auka bag d'inta tai fucewarta, tana fita ta nufi motar yaya Ahmad domin jiran shi.

Ta d'au wasu time d'in tana jiran yaya ahmad bai futofa, can kuma sai gashi ya futo fuska d'auke da fara'a amma dai kana ganin fara'ar nan kasan ta dole ce, yana qarasowa fuska a sake zahra tace yaya ahmad ina kwana da fatan ka ta shi lpy?. Qaqalo murmushin dole ahmad yayi tare da cewa lpy qalau qanwata, kema da fatan kin tashi lpy? Gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Na tashi lpy qalau yaya ahmad, ajiyar zuciya ahmad ya sauke tare da cewa! Masha ALLAH.

Daga haka ba wanda ya sake cewa komai a cikin su suka shige motar suka fara tafiya, shiru ne ya baquncin su na wasu lokutan kafin zahra tace yaya ahmad naga yau kamar bala da lpy? Murmushin dole ahmad ya sake kwakwalowa a karo na biyu sanan yace wlh qanwata ina lpy mai kika gani? Dan gyad'a kai zahra tai cikin tsokana tace ko tinanin ilham kake ne, yadda zahra tai maganar kamar wani mugun kama ta sakewa ahmad da maman shi, ji yayi ma kamar ita tai maganar.

Amma ahmad sai ya kawar da hakan a zuciya shi, sanan yace ai kuwa kamar kin shiga zuciyata tun jiya tinanin ta muke sam na kasa bacci santa ya addabamin yadda bakya tinani. Jinjina kai zahra tai tare da cewa! To yaya ahmad mene na d'aga hankalika da tinanin ta bayan ta amince ma?, girgiza kai ahmad yayi tare da cewa hmmmm qanwata kenan bazaki gane ba, amma kina ganin anya ilham zata kirani, nifa hankalina bazai ta6a kwanciya ba sai naga ta kirani, dan sai na ringa jin kamar bata amince da soyayayar ba.

Da sauri zahra tace haba yaya ahmad ka dena wanan tinanin mana nasan ilham baza ta6a yima hakan ba, sabida da bata sanka da bazata ta6a saurarar kaba barema ta amince ma. Ajiyar zuciya ahmad ya sauke nan da nan yaji damuwarsa ta fara raguwa da yaji batun zahra dan shi da tinani yake anya ilham ba shigo-shigo ba zurfi take mai ba? Gani yake kamar ta bishi a yadda yake sone kafin su kuma Nigeria bata amince da soyayyar shiba, yanzu kuma da zahra ta fahimar da shi sai hankalinsa ya kwanta. Daga haka ba wanda ya sake magana har ahmad ya kawo zahra school, sallama sukayi kamar yadda suka saba sanan zahra ta shige school.........

Lokacin da ahmad ya d'auko zahra daga school suna shigowa, suka hangi motar zee a parking space d'in gidan, zahra kuwa cikin zuciyarta tsaki taja tare da cewa wanan zee d'in kamar mayya haka take, daga haka ta bud'e murfin motar ta futo hannu riqe da jakar makarantar ta, tana futowa ta wuce hanyar step d'in benan. A hankula zahra take taka step d'in benan, gabanta sai fad'uwa yake haka nan taji tana wani mugun jin tsoran zee amma duk da hakan ta dake ta tura qofar ta shige fallon. Can gefe ta hangi zee akan sofa tana kallan tv ta dora qafa d'aya kan d'aya, shi kuma mashkhur yana kan draining yana shan lemo hankali kwance suna hira.

Zahra kuwa kawar da kai tayi ta kama hanya shiga bedroom d'in nata, zata gifta kenan taji zee tace kee zonan, gaban zahra ne ya fad'i rasss amma dak da hakan sai ta cigaba da tafiyarta abinta, ji tai zee ta sake cewa ke house girl dake fa nake, da katawa zahra tai zuciya cike da tsoro, zuciya ya tana raya mata abubuwa da dama game da zee amma tana jin tsoro. Tsayuwa zahra tai tana tinanin mene ma futa, kee dallah ba kiranki nake ba? Zee ta fad'i hakan cikin tsawa nan da nan ran zahra ya 6ace, dan haka dakewa zahra tai ta danne tsoranta ta nufi zee.

Zahra tana qarasawa cikin harshan turanci kamar yadda ita zee d'in take mata magana tace gani lpy kike kwala min wanan kira haka? Zahra ta qarasa fad'in haka hannu riqe da ugu, gabanta sai qara fad'uwa yake sabida tsabar tsoro, ai ba iya zee ba har mashkhur da yake zaune sai da mamaki ya kusan kashe shi a zaune, nan da nan ya daskare a zaunke riqe da cup a hannu. Zee kuwa baki a sake ta tsaya kallan zahra dan itama mamakin ya daskarar da ita. Ya mutsa fuska zahra tai kamar wata jaruma ta fara magana kamar haka! Ke nifa kinga na gaji da tsayuwa ki gayamin dalilin kiran nan da kike min ina jin ki dan ni bana son jira kin gane.

Baki na rawa zee ta fara magana da yake itama zee d'in tana da tsoro ba lai fi, am!! Am!! Dama cewa nai abinci nake so ki dafamin yunwa nake ji, zahra kuwa da taga zee ta rikece qarfin guiwa ta samu, dan haka wata uwar harara zahra ta bankawa zee tare da cewa lalai ma to bari kiji daga rana mai kama da ta yau karki sake sani aiki sabida ni ba baiwar ki bace kuma baki haife niba, kije can ki nemi baiwar da zata dafa miki, ko ke ko tashi ki dafa kayanki da kanki, tinda kina da hannu da qafa, zahra ta qarasa magara tana jan wani tsaki.

Daga haka zahra ta juya tai tafiyar ta gabanta sai fad'uwa yake dan da kyar take iya maganar ma sabida storo kawai ta dake ne, itama zee d'in jikinta har wani rawa yake sabida tsabar tsoro, dama can matsoraciya ce kawai dai dan ta samu kwarin guiwar yiwa zahra rashin mutunci ne a wajan mashkhur amma da bazata iya ba. 6an garan mashkhur kuwa tini yayi suman zaune dan ganin lamarin yake kamar a makarki, tunda yake a rayuwar shi bai ta6a ganin zahra tana fad'a ba sai yau.

Mashkhur yana jin zee tana kawo mai qarar zahra amma ina sam ya kasa wani kwakwaran motsima,. Zee kuwa jakarta ta sa6a zuciya cike da tsoro da haushin mashkhur tabar gidan,. 6angaran zahra kuwa tana shiga bedroom d'in ta saki ajiyar zuciya tare da dafe qirjinta, har wani mamaki take wai itace yau ta iya yiwa zee haka a gaban mashkhur, murmushin jin dad'i zahra tai a fili tace alhamdulilah, kai gaskiya shawarar ilham ta fara aiki. Saura kuma yaya mashkhur shima zai gane kuskuransa in ya sake zalinta ta wlh.

Wata zuciyar ce ta cewa zahra kee anya zaki iya yiwa yaya mashkhur kuwa yafi qarfin kifa? Shiru zahra tai tana nazarin abinda zuciyarta ta gaya mata, d'ayar zuciyarta ta kuwa cewa tai zaki iya yi masa mana, in kika sa kanki. Zahra kuwa tinani ya farayi anya zata iya yiwa yaya mashkhur abinda tayiwa zee kuma tasha lpy? Dan tasan yaya mashkhur ba kanwar lasa bane ba, jikinta ne zai gaya mata. Haka dai zahra tai ta saqada warwara, daga qarshe ta shiga toilet tai wanka sanan ta d'aura alwala, ta futo jikinta d'aure da toilet.

Tana fitowa ta saka kayanta, sanan ta shinfid'a dadduma ta fara gabatar da sallah, lokacin da zahra tai sujjadar qarshe sai da ta yiwa yaya mashkhur addu'o'in da hajiya kaka ta rubuto a takadda ta bawa ilham ta kawowa zahra, zahra tanayin addu'o'in ne bawai dan tana son mashkhur ba, aa kawai dai tana son ta cika umarnin hajiya kakak ne, kawai duk da kuwa ita zahra a tinanin ta tana addu'o'in ne kawai, amma tasan yaya mashkhur bazai shiryu ba.

Night...........

Sai da dare yayi sanan zahra ta iya futowa ta shiga kicin domin dafawa kanta abinda zataci, a tsorace ta futo sabida karta had'u da mashkhur dan tasan tayi mai babban laifi. Haka zahra ta shige kicin a salala6e sabida karta had'u da mashkhur, sam zahra hankalinta baya gabanta sai wai gen bayanta take duk da kuwa ta shigo kicin d'in, a dai-dai lokacin mashkhur shima ya tawo riqe da cup d'in t a hanunsa, sam ya tafi duniyar tinani, ai kuwa basuyi aune ba sai sukaji sunyi tinti6e da junan su, wani mugun karo sukayi wanda har sai da hakan yasa cup d'in hanun mashkhur ya fad'i qasa wanwar.

Yau kunga banyi muku typing da yawa ba wlh bana jin dad'i ne, wanan d'in ma da kyar na iya rubutawa.

Mu had'e a next page dan jin ya zata kaya tsakanin mashkhur da zahra.....


ADALILINTA💜❤💜

BY AMMINA BAYERO💜❤💜

                                  *page 75*

                                   Typing..........

Sam zahra hankalinta baya gabanta sai wai gen bayanta take duk da kuwa ta shigo kicin d'in, madai-dai lokacin mashkhur shima ya tawo riqe da cup d'in t a hanunsa,  sam ya tafi duniyar tinani,  ai kuwa basuyi aune ba sai sukaji sunyi  tintu6e da junan su, wani mugun karo sukayi wanda har sai da hakan yasa cup d'in hanun mashkhur ya fad'i qasa wanwar.

Wani mugun kallo mashkhur ya watsawa zahra,  dama ga idon shi yayi ja abin tsoro,  nan da nan hantar jikin zahra ya kad'a,  maganar ilham ce ta fad'omata a rai da take cewa haba zahra wai bazaki dena jin tsoran yaya mashkhur,  d'in nan ba,  ajiyar zuciya zahra taja,  sanan ta kewaye tabar mashkhur ya tsaye sake da baki.  Zahra tana kewaye mashkhur ta wuce bedroom d'in ta, zuciyata sai bugun tara-tara take.

Mashkhur kuwa,  mamaki ne ya kusan kashe shi sam ya kasa Wani kwakwaran motsi a wajan,  gani yake abin kamar a makarki,  wai shi zahra zatai wa laifi ta wuce ta barshi a tsaye,  fuskarta ba alamun nadama bare tsoro.  Mashkhur yafi minti goma yana jimamin lamarin ko motsi bayayi,  can yayi ta maza ya yakitowa jikinta qarfi ya wuce bedroom d'in sa.  Mashkhur yana shiga bedroom d'in ya fad'a gado jiki ba kwari,,  wani mugun mamaki ne ya kama mashkhur.

A zuciyarsa yace yanzu wana hukunci ya kamata na yiwa wannan yarinyar?  Can wata zuciyar tasa tace kawai ka rabu da ita.  Tabb akan me zan rabu da ita?  Zuciyar mashkhur ta bashi amsa kamar haka?  Yanzu fa ta dena jin tsoranka tinda tayi ma haka,  yanzu in kayi wasa sai ta rai na ka kawai ka rabu da ita,  jinjina kai mashkhur yayi alamun ya amince da shawarar da zuciyarsa take bashi.
6angar zahra kuwa cikinta ya gama tsurewa,  sabida abinda tayiwa yaya mashkhur.

Sabida tsoro sai da zahra ta rufe qofifin bedroom da tagogi,  a ganinta tayi namijin qoqari da tayiwa mashkhur haka,  dan bata ta6a tinanin zata iya yiwa yaya mashkhur haka ba,  tana cikin wanan tinanin taji alamun shogowar message ta WhatsApp da yake datar ta a kunne take,  jiki a sanyaye zahra ta miqe sanan ta janyo wayarta.  Massage ne ta gani ya shigo,  da wata number Nigeria,  hakanan jikin zahra ya bata ilham ce.

Ba 6ata lokaci zahra ta bud'e massage tare da duba sunan,  cikin manya baqi zahra taga an rubuta SAKINA ABUBKAR (ILHAM)  murmushi zahra tai tare da yi mata reply d'in slm d'in da tayi mata.  Nan da nan hira ta 6arke tsakanin ilham da zahra,  sai da sukayi wajan awa biyu suna hira  a WhatsApp,  zahra tana yiwa ilham typing ita kuma ilham tai mata voice,  sai da zahra ta bawa ilham labarin abinda ya faru dazu tsakanin ta da zee da kuma mashkhur.

Ilham tayi dariya sosai da sosai kuma tayo farin cikin da hakan sanan ta qara ziga zahra da bata shawarar kala-kala game da mashkhur.  Har sunyi sallama zahra zata kwanta sai ta tuno da yaya ahmad,  ai kuwa ba 6ata lokaci zahra ta tayiwa ilham voice tana cewa ilham,  da fatan dai kinyiwa yaya ahmad magana koh,  wlh dazuma sai da yayi min maganar ki duk ya shiga damuwa gani yake kamar bazaki bugo mai ba.

Itama ilham d'in reply tai wa zahra ta voice note d'in!  Dariya ilham tai sanan tace hmm ke dai bari nima ganinan sai tinaninsa nake wlh cuwan son shi sai damuna yake amma,  bazan buga mai ba sai na jamai aji nan da kwana uku saura kuma ki bashi number tawa,.  Zahra da ta gama jin voice d'in ilham kuwa,  murmushi tai tare da girgiza kai,  sanan tayiwa ilham reply da hmm to ALLAH ya shirgeki ilham ni zan kwanta sai da safe,  daga haka zahra ta kashe wayar ta sata a qarqashe folo tai addu'o'i bacci ba jimawa bacci ya kwashe ta.

5 days letting.........

Yau kwana biyar kenan da tafiyar su ilham Nigeria,  6angaran ahmad kuwa har ya gaji da jiran kiran ilham yau kwana biyu kenan ahmad bai kai zahra makaranta ba sabida rashin lafiyar da take damunsa kuma ba komai bane ya jazawa ahmad cutar ba face rashin kiran shi da ilham tai.  Juye ahmad yake kwai akan bed jiki sa duk yayi zafi rau da kyar yake motsi,  yana cikin wanan halin yaji alamun shogowar message ta wayar shi qilin.

Ahmad yanaso ya duba wayar shi,  yaga massage d'in daya shigo amma sam ya kasa,  sai da ahmad yafi minti goma a haka yanaso ya d'ago ya dauki wayar shi amma ya kasa.  Can kuma yayi ta maza ya mirgina da kyar ya iya miqa hannu ya janyo wayar tashi har tana shirin fad'uwa ya damqeta da iya qarfinsa na marasa lafiya.  Ajiyar zuciya ahmad ya sauke sanan ya bud'e wayar tasa ya zuba mata raunanan idanuwan sa.
Gabansa ne ya fad'i rass tun kafin ya karanta sakamakwan ganin number Nigeria.

Cikin zuciyar shi yace ALLAH yasa ilham ce, ko tsaya bud'e wayar bai ba ahmad ya fara karanta messages d'in da yake wayar I phone ce.  Massage d'in ya fara kamar haka!  Slm yaya ahmad ilham ce,  wanna shine line nawa.  Ahmad yana kai qarshan zancan ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya, sanan ya bud'e wayar, sanan yayi save d'in number,   kai tsaye ya fara kiran ilham, amma sam line baya shiga,  wani siriri tsaki ahmad ya saki  sannan yaja qasan wayar shi ya kunna data.

Yana kunna data direct ya shiga WhatsApp,  yana shiga yayi lalabo number ilham,  ba 6ata lokaci ya shiga contact d'in,  ya fara qoqarin tura mata saqo,  har ya fara typing sai yaga tana online,  dan haka direct ya danna mata video call,  tana shiga tana ta ringing amma ilham, taqi ta d'auka,  wani baqin ciki ne ya sake rufe ahmad har zuciyar sa yasan ilham tana sane taqi d'aukan video call.  Rai ba dad'i ahmad ya danna voice ya fara magana cikin murya raunaniya ta masu larura ya fara cewa!.

Haba ilham mai yasa kike min haka wana laifi nayi miki?  Tinda kika tafi nake jiran kiranki ko message amma shiru,  haba ilham mai yasa kike min haka,  wlh sabida da tinanin ki yanzu bani da lpy ko school banje ba bare na kai zahra pls ilham ki d'aga video call d'in ko zan samu sukuni ya qarasa maganar da kyar,  dama tin da kawai daurewa yakeyi dan maganar ma da kyar yake.  Lokacin daya tura sai da ilham, ta d'auki 5 minit kafin ta bud'e wai ita jan aji.

Ahmad kuwa sam ya kasa fita daga chat d'in su da ilham sai kallon voice note d'in da yayi mata yake,  yana jiran ilham ta bud'e tai mai reply,  da ahmad yaga ilham bata bud'e ba sabida tsabar baqin ciki har hawaye ya fara zubo mai,  sanan ya fara tinanin anya ilham tana qaunar shi kuwa? ba wahalar da shi kawai take ba?.  Yana cikin tinanin nan yaji alamun shigowar saqo,  da sauri ya bud'e wayar shi dan yasa ilham ce tai mai reply.

Ai kuwa kamar yadda yayi tinani itace,  tai mai reply amma typing tai ba voice note ba.  Gajeran typing tai wanda take cewa! Banje anyimin sim d'in ba sai shekaran jiya,  kuma yau na bud'e WhatsApp d'in shi yasa.  Ciki rawar murya ahmad yace pls ilham ki bari muyi video call ko zan samu nutsuwa a zuciya ta.  Lokacin da ilham ta bud'e voice d'in ahmad, da taji yace ta bari suyi video call taji dad'i sosai, sabida itama tana son ganinsa sosai,  itama kanta son ahmad ya adda beta ko bacci bata samu tayi.

Amma sai taja mai rai da cewa! Aaa gaskiya ni bana san video call yanzu,  haka ahmad yayiwa ilham reply ta voice murya na rawa ido na zubar da kwalla, Yace!  Dan Allah ilham ki tai makamin ko voice note kiyimin naji muryarki,  wlh zuciya tana yimin zafi gani nake anya ilham kina sona ki gayamin gaskiya ilham, tin kafin sanki ya kashe ni sabida nasan sanki ne ajali na.  Ahmad yana tura mata voice d'in ya ajiye wayar ya saki kuka kamar wani qaramin yaro.





Kai ni kuwa amina bayero nace gaskiya ilham abinda kike bakya kyautawa sam. 

Sai da ahmad yasha kunansa ya qoshi sanan ya duba messages d'in ilham.  Voice ya gani tai mai,  ai bai san sanda ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya ba,  hannu na rawa ahmad ya fara qoqarin bud'e voice d'in ilham d'in.  Cikin sanyayar muryar ilham mai dad'i sauti da sauraro tace!  Haba my hubby taya sona zai kashe ka,  ka dena fad'in haka,  pls ka dena kuka my hubby ko nima so kake ka sani kuka? Ilham ta qarasa maganar kamar zatai kuka sabida itama harga ALLAH taji tausayin ahmad sosai,  itama tasan sam bata kyauta mai ba.

Ahmad kuwa cikin raunaniyar muryar nan ya danna voice note yace!  Hmm ilham kenan ai har in kinga na dena zubar da hawaye,  to na aure kine ko kuma kin amince da soyayyata kina qaunata sosai yadda nake qaunarki.  Lokacin da ilham ta bud'e voice d'in ahmad, ya ta6a maza zuciya sosai har itama sai da ta zubar da kwalla,  cikin muryar kuka ilham, tai wa ahmad voice note da!  Haba yaya ahmad yanzu kana tinanin bana qaunar ka ne?  Wlh ina qaunarka sosai yadda baka tinani ina sanka san da ban ta6a yiwa wani d'a namijiba a rayuwata.

Yaya ahmad da wani ne yace min bana qaunar ka ba kai ba sai inda qarfina ya qare wlh yaya ahmad ina sanka sosao da sosai, inda ka sake zubar da hawayanka akan kokwanto ina qaunar ka ko ka sake zubar da hawayanka a kan baqin cikin soyayyata gaskiya ban yafema ba,  sabida ni yanzu ina qaunar sosai ina sanka san muddin rai.  Ahmad yana gama jin voice d'in ilham,  ya saki wani tatausan murmushi farin ciki,  nan da nan annurin kyakyawar fuskarsa ya dawo,  muryar shi ta fara dawowa dai-dai.

Cikin muryar farin ciki ahmad yayiwa ilham voice da!  Kai da gaske my pretty na?  Dama kina qaunar ta, haka amma kika bari na kusan kashe kai na da ciwan son ki,  kai gaskiya pretty baki yimana adalci ba sam yanzu akan mai kike hukunta zuqatan mu haka?  So pls yanzu ki bari muyi video call ko, zan samu naga kyakyawar fuskar ki zuciyata tai sanyi dan nayi missing d'in kk over pls,  ilham ki amince miyi video call karkice aaa.

Ilham tana gama jin voice d'in ahmad ta saki nanauyar ajiyar zuciya, sabida itama ta matsu suyi video call d'in ko dan taga kyakyawar fuskar masoyinta,  ahmad ko ta samu nutsuwa,  a hanzarce ilham ta miqe ta d'auki mayafinta ta rufe duka jikinta sanan ta wuce zuwa qofar bedroom d'in ta rufe gam sabida kar wani ya shigo ya isketa tana video call da ahmad.  Ai kuwa tana dawo tana gama hawa kan bed kafin ma ta d'auki wayarta ta taji ahmad yana kiranta.

Wata nanauyar ajiyar zuciya, ilham ta sauke sanan ta d'auki wayar sai da ta sai ta face d'in ta ta fara qoqarin d'aukar video call d'in.  Lokacin da ta d'auka sai da video call d'in ya d'anyi reconnect sanan yayi.  A lokacin guda gama ahmad da ilham ya fad'i rass-rass saka makwan ganin fuskokin junansu,  nan da nan suka fara yiwa junan su kallan qurillah,  ko kiftawa basayi.  Sosai suka ringa kallan junan su ba wanda yacewa d'an uwan sa qala,  sai ajiyar zuciya, kawai suke saukewa.

Sam ilham ta manta dawa take wanan kallan dan da a zahirine bazata ta6a iya wannan kallan ba da wani d'a namiji komai san da take mai.  Can ilham ta dawo daga duniyar da suka tafi ita da ahmad, ba shiri ta janye idanuwanta daga kallan ahmad d'in ta kawar da fuskarta gefe.  Shima ahmad d'in nanauyar ajiyar zuciya ya sauke sanan ya dawo daga duniyar da suka tafiya,  ilham kiwa sunkuyar da kai tayi kamar bada ita ake wanan kallan ba.

Gyaran murya ahmad yayi tare da cewa! Sannun ki kin kyauta,  d'an had'e fuska ilham tai sanan ta d'ago tare da cewa! Yauwa na kyauta da me fah?  Au sai ma na gaya miki mai kikayi kika kyauta koh? ahmad ya qarasa maganar yana zuba mata ido,  ta6e baki ilham tai tare da cewa! Aa gwara dai ayimin bayani dan nasan me nai,  jim ahmad yayi ya zuba mata ido yana kallan ikwan ALLAH. Duk tabi ta had'e rai kamar ba itace tai mai voice d'in dazu ba tana gaya mai irin qaunar da take mai,  cikin zuciyar shi yace kai ilham kina da wuyar sha'ani.

Cikin mamaki ahmad yace!  Ilham are you okay?  Juyar da kai ilham tai cikin ko in kula tace I'm very okay.  Jim ahmad yayi kafin yace ilham anya baki da almastutsai kuwa?  Nan da nan ilham ta sake had'e rai gam tare da cewa! Oho nima ban saniba amma inaga ka gansu ne a kai na shiyasa ka tambaya,  ta qarasa magar fuska ba alamun annuri.  D'an zaro ido ahmad yayi cikin murya mai ban tausayi yace haba my pretty mai yayi zafi shi ba wuta ba daga tambaya,  pls ki dena had'e rai bakya kyau,  haba my future wife pls simple?.

Ilham taso sakin murmushi sabida har zuciyar ta take jin rarrashin masoyin nata,  amma sai ta sake tamke fuska tare da cewa! Tab wace future wife d'in taka,  badai ni ba mai zakai da mai almatsutsai ko so kake in anyi auran na ringa shaqeka in almatsutsan sun tashi.  Murmushi ahmad ya saki tare da cewa! To mene dan kin shaqeni ai ni dad'in shaqarma zanji,  ba komai in dai kece.  Harara ilham ta watsawa ahmad tare da cewa! Aa ai kawai ka bari naje na auro d'an uwana mai al matsutsan kaga zaman sai ya fi mana dad'in.

Murmushi ahmad ya sake yi a karo na biyi sanan yace shikenan tazo gidan sauqi,  ai nima almatsutsan ne da ni na dad'e ina neman mai almatsutsan dan na aura ban samuba,  daga qarshe dana fara sanki sai na haqura da ita,  ashe-ashe ke kyauta uban giji ce a gareni a she kema kina da su kai

Please Login or Register in order to submit comment