Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko abinci bata tsaya sun gama girkawa ba,  ta wuce dan ko dady bai ma tashi daga bacci ba.  Tana fita ta wuce motar yaya Ahmad ta tsaya domin jiran shi,  shima bai fi minti 5 ba ya futo yana fitowa suka gaisa da zahra kamar yadda suka saba kullum,  sanan suka shige mota suka fara tafiya.  Suna cikin tafiya Ahmad ya kalli zahra tare da cewa qanwata,  wai ya magana mu kuwa kin gaya mata?  Shiru zahra tai na wasu daqiqu,  kafain tace eh yaya Ahmad na gaya mata,  amma naga kamar bata d'au zancan serious ba,  amma ina ga dai ka dan bata lokaci,  sanan kuma waqa a bakin mai ita yafi dad'in bayan kwana biyu kafin su koma sai ka gaya mata koh?.

Ajiyar zuciyar Ahmad yayi tare da cewa! Okay qanwata ba damuwa,  daga haka ba wanda ya sake cewa! Komai har su kazo school d'in Suna zuwa ya sauke ta ya koma gida.  Yau mashkhur yaje school da yake yana tsoran dady ya gano gaskiyar lamarin........

To yau kimanin sati d'aya kenan da zuwa su dady rayuwa ta canzawa zahra sosai tana samun farin ciki,  ba kamar da ba,  kullum cikin walwala take sam bata baqin ciki
ko school ma da kyar take zuwa sabida batason rabuwa dasu dady.  Shima mashkhur ba laifi yana zuwa makarantar kuma yanzu baya shaye-shaye sai dai yayi a makarantar shida zee,  kuma bama sosai yake yiba.  6angar Ahmad kuwa Kullum sai yazo wajan su mashkhur,  kawai sabida yaga ilham kullum soyayyar ilham qaruwa take a cikin zuciyar sa.
Yau ranar jumma'a ya rage saura kwana biyar su dady su koma gida,  zahra tana dawowa daga school direct ta wuce bedroom d'in ta,  Ilham ta gani zaune ta rafka uwan tagumi ta tafi duniyar tinani.  Zahra batabi takan ilham ba ta cire kayanta,  ta wuce toilet tai wanka,  abin mamaki har lokacin da zahra ta futo daga toilet d'in,  Ilham bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba,  da sauri zahra ta qarasa inda ilham take zaune,  tare da yarfa mata ruwan jikinta wanda bai gama bushewa ba,  da sauri ilham ta dawo daga cikin duniyar  tunanin data tafi,  kallan zahra ilham  tai tare da cewa!  Ke lpy yaushe kika dawo ban sani ba?.

Lalai ma ilham tin yaushe na dawo anna shiga wanka,  haba ilham wanan wana kallar banzan tinani ne,  murmushi yaqe ilham tai tare da cewa!  Kinga ba komai jeki kisa kayan ki ni zan je na zubo mana abinci daga haka ilham bata jira amsar zahra ba tai fucewar ta,  jim zahra tai tabbas tasan da akwai abinda yake damun ilham,  amma tasan ilham bazata iya riqewaba tabbas duk 6oye6oyan da take,  sai ta gaya mata dan tasan ilham bata iya riqe damuwa.  Juyawa zahra tai ta dakko kayanta ta sa,  tana gama sa kayan nata Ilham ta shigo,  hannu riqe da plate d'in abinci.

Da sauri zahra ta qaraso tare da karbar plate d'in  hannun ilham tana cewa!  Ai kuwa kamar kinsan yunwa nake ji zo mu zauna muci,  daga haka suka zauna,  zahra tana sane take d'auko wata hirar daban take bawa ilham labari,  amma sam ilham bata fahimtar abinda zahra take cewa!  Dan ko abincin ma bataci wasa kawai take sa cokalin a cikin abinci.  Zama zahra ta gyara tare da ta6o ilham tan cewa ke bari na baki wani labari kina jina,  da sauri ilham tace ke dallah rabu dani da wanan banzan labarin duk kinbi kin isheni da surutu ki barki da abinda yake damuna mana.

Saura qirasa dariya ta kwacewa zahra,  dama tasan tabbas  hakan zai faru,  dama kwai so take Ilham tace ki barni naji da abinda yake damuna.  Ta6e baki zahra tai tare da cewa oho abinda ya dameki ke ya dama mana tinda bazaki iya gayamin ba,  daga haka zahra ta cigaba da cin abinci ta,  itama dai kawai zahra tanacin abincin ne amma hankalinta yana kan abinda yake damun Ilham,  so take taji ko mene?.    Shiru wajan ya d'auka na tsawan mintina can kuma ilham tace,  zahra?  D'agowa zahra tai tare da cewa na'am,  murya a daqile Ilham tace!  Kinsan mene?,  da sauri zahra ta Girgiza kai tare da cewa sai kin fad'a.

Shiru ilham tai na wasu daqiqu kafin tace pls zahra karki d'auki zancan nan wasa kuma bana san dariya kina jina,   kwarai ilham inajin ki zan d'auki zancan yadda kike so,  kinji?.  Kawar da plate d'in abinci ilham tai daga gabansu tare da cewa! Zahra wlh na fara SON SHI,  cikin rashin fahimta zahra tace shiwa?  Jim ilham tai  kafin tace AHMAD,  saura qiris zahra ta kware da abunci da take taunawa a bakinta,  nan da nan wata dariya tazo mata,  amma sai ta dake ta fara tari-tari dariya-dariya yadda Ilham bazata gane ba.  Haba daga magana sai qwarewa kuma ko nayi laifi ne?  Ilham ta watsawa zahra tabbayar.

Da sauri zahra ta Girgiza kai cikin mamaki tace!  Ilham anya ba mafarki nake ba?  Wai shin wana yaya Ahmad  kike nufi eyee?  Harara ilham ta bankawa zahra tare da cewa! Ke wana Ahmad kika sani banda abokin yaya mashkhur.   Shiru zahra tai tana nazari,  abin ya bata mamaki sosai da sosai,  gani take kamar a mafarki ita bata ta6a tinanin wai Ilham zataso wani d'a namiji ba. Muryar ilham ce ta katse zahra daga tinanin data tafi,  haba zahra naji kinyi shiru kuma?  Ai ilham al amarin naki ne da d'aurewar kai wlh, ni gani nake kamar da wasa kike.

Nan da nan idon Ilham ya ciciko da kwalla,,  murya a shaqe tace au zahra ni nake miki wasan kenan yanzu baki yadda dani ba,  wlh son shi nake.  Cikin mamaki zahra tace to ke taya akayi kika gane kina son shi tinda baki ta6a yin soyayya ba?,  haba zahra muna karanta novels da dama a school,  nasan mene so,  tinanina shine a bacci na shine,  sam bana iya sukuni sai na Ganshi kullum cikin tunanin sa nake.  jinjina kai zahra tai dan yanzu ita lamarin Ilham ma ya fara bata tsoro,  amma a fili cewa!  Tai to shikenan yanzu ya kike so nayi bayan kin cemin naje nace masa bakya son shi.

Nan da nan ilham ta fashe da kuka tare da cewa!  Haba zahra zuwa kikayi yanzu kika cemai bana son shi shikenan kin kashe ni,  ta qarasa maganar tana kifa kanta a cinyoyinta.  Da sauri zahra ta qarasa inda ilham d'in take ta janyota jikinta tana rarashin,  amma ina ilham taqi shiru, haba ilham mene haka nifa wlh ban cemai  bakya son shiba,  wasa nake miki.  Da sauri ilham  ta dago ido jage-jage da hawaye tace dan ALLAH?  D'aga mata kai zahra tai tare da cewa!  Wlh,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Alhamdulilah.  Hmmm nikuwa AMINA BAYERO nace ilham anji kunya🙈 sai kace ba qanwar yaya mashkhur ba. 🙉😂🤐

Zahra zubawa ilham ido tayi tana mamakin dama haka so yake,  tab ALLAH sarki ni zahra banma san mene so ba,  zahra ta furta a zuciyar ta.   Muryar ilham ce ta katse ta daga maganar zuciya da take,  cewa tai to yanzu zahra mai kika cemai,  ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa! Nace mai ya baki wasu lokutan kiyi tinani,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Yauwa jeki kice na amince,  sakin baki zahra tai tana kallon ikwan ALLAH.  Can kuma tace amma ilham sam baki da hankali ke ko iran jan ajin nan na mata baki iya ba?.  Turo baki ilham tai tare da cewa! To tun yaushe naja masa ajin.

Harara zahra ta watsa mata tare da cewa! Au dama tunda kina son shi kenan,  da sauri ilham tace yau kwana hudu kenan san shi ya fara addabamin,  jinjina kai zahra tai tare da cewa!  Kin san ya za'a yi?  Girgiza kai ilham tai tare da cewa!  Sai kin fad'a,  ko yau ma sai da yace na sake tina miki zancan nan ko zai ci sa'a ki amince,  da sauri ilham ta zabura tare da cewa! Da ALLAH da wasa ko da gaske?  Qaramin tsaki Ilham taja tare da cewa! Au qarya zan miki,  ke bakisan yadda yaya Ahmad yake qaunar ki bane wlh,  yacemin tun sanda ya fara ganinki yake son ki.

Murmushi ilham tai tare da cewa!  ALLAH sarki bawan ALLAH wlh wanan shine masoyi gaske,  tabb lalai ilham so yayi miki kamun kazar kuku,  hmmm tom ni dai zuwa gobe zan ce mai na shawo kanki kin yadda kin amince zaki saurari da mai yazo,  ammafa bazance kin yadda kina son shiba,  zaro ido ilham tai tare da cewa!  Sabida mai?,  hmm ilham kenan ai wanan shine mutunci da nake nema miki,  daga baya in kuka d'an zanta sai ki nuna mai kin amince  amma ba'a yiwa namiji haka wlh duk da nasan yaya Ahmad mutumin kirki ne,  ga hankali gashi black beauty wow kai.

Wani shu'umin murmushi ilham ta saki tare da cewa!  Ke na rabaki wlh,  ai dama kin san ni da san baqin namiji kyakyawa nifa sam farin namiji baya birgeni,  lalai ma ilham to ai yaya Ahmad ba wani baqi bane sosai kawai dai bashi da haske ne shi yasa,  murmushi ilham ta saki tare da cewa!  Ehh mana ai nafison irin su mana,  wanda basu cika fari ba kuma basu cika haske ba,  wani siririn murmushi zahra ta saki tare cewa kai ilham gaskiya abinki ya wuce tinani na yaushe kika lalace haka,  ammi bata sani ba?,  itama dariya ilham ta saki tare da cewa!  Ke dai bari kawai,  muda muke karanatun novel dole musan komai ai wlh kai na a bud'e yake ke na bari da kullewar kai.

Murmushi zahra tai tare da cewa,  to gaskiya dai ki kula da kyau kar ammi ta gane ki ALLAH ya shiye ki kuma,  murmushi itama ilham tai tare da cewa,  ALLAH ya shiryamu gaba d'aya,  ameen ya Allah Ilham.
      To yaufa zahra sai data shiga uku da maganar ahmad a wajan ilham,  tun tana iya bata amsa har tai mata banza,  haka ta qaraci surunta ta gama,  da sukazo wajan bacci ma haka akai ta fafatawa har sai da bacci ya d'auke ilham sanan zahra ta huta.

Washing gari.........

Yauma Ahmad ne ya fara yiwa zahra zancan ilham a mota,  dan haka zahra cemai tai,  ehh ta shawo kan ilham harta amince taza saurare shi,  hakan kuwa ba qaramin dad'i yayiwa ahmad ba,  dan raban da yayi farain ciki irin wanan harma ya manta.
       Lokacin da zahra ta koma gida shawara suka farayi da ilham taya ilham da Ahmad zasu had'u su zanta ba tare da dady ko yaya mashkhur ya gansu ba?,  haka dai sukai ta shwartawa,  amma basu samu mafita ba.  Daga qarshe dai suka yanke shawarar,  gobe ilham zata ce taza raka zahra school dan taga makatantar daga nan sai su zanta da yaya Ahmad d'in.  Nan da nan zahra da ilham suka fara tattauna yadda zasu zamu dady da  magana.


Ba 6ata lokaci ilham ta tsarawa zahra bayani akan yadda zasu samj dady da maganar,  ba musu zahra ta amince.
Dan haka basuyi sanya a guiwa ba suka wuce wajan dady domin su shawo kan shi.  A falo suka same shi shida amir suna kallo,  da sallama zahra da ilham suka qarasa,  suna qarasawa zahra ta zauna a kusa da dady kamar yadda ta saba.  Nan da nan dady ya saki fusaka suka fara wasa da dariya kamar yadda suka saba,  itama ilham d'in zama tayi a kusa da zahra tana tayaso wasa da Dariya.  Can kuma zahra ta fara magana kamar yadda ilham ta tsara mata!  Am yauwa dady dama inaso na ruqeka wata alfarka.

Murmushi dady yayi tare da cewa! Fad'i kanki tsaye mamana 'yata kuma surikata,  murmushi zahra tai tare da cewa! Dama dady haka zance ya kama kafin ku tafi ka siyar min waya mu ringa gaisawa da ku kaga ba sai na takurawa yaya mashkhur ba ko?,  kwarai mamana kin fad'i gaskiya,  kuma karki damu waya kamar na siyar miki na gama nan da gobe ma,  nan da nan zahra ta saki murmushin farin ciki dan ita ta fad'a ne kawai dan batai tinanin dady zai amince ba,  duk da kuwa bata ta6a roqan alfarma a wajansa ta rasa ba.  Ilham  kuwa cafe zancan tai da hmm 'yar gatan dady nifa wlh dady na gaji da zaman gidan nan ba fita ko ina,  da sauri zahra ta cafe zancan da cewa! Lah gobe in yaya Ahmad zai kai ni school ki biyoni sai kiga hanya koh?  Kinga in kika rakani sai ya dawo da ke.

Ehh to amma zai yadda ya tafi dani kuwa?  Cewar ilham,  murmushin jin dad'in zahra tai sabida aikin su yana tafiya yadda ya dace,  haba ilham yaya Ahmad ai yana da kirki,  zai yadda mana sai dai in dady ne bai yadda ba,  murmushi dady yayi tare da cewa!  Ah ai ni duk abinda kike so mamana tinda kina so  sai kuje,  ta rakaki in dai kin amnce shikenan nima na amince mamana........

Yauwa naji qorafinku akan littafin yaqici yaqi cinyewa,  ku kwantar da hankalinku na kusan gama littafin bazan qara jan labarin ba kamar yadda na ja shi a baya,  in sha ALLAH in dai da rai na da lfy ta da waya ta da caji na da data ta,  zanyi qoqari ganin ina yi muku posting kullum koda page 2  biyu ne,  in sha ALLAH a cikin watanan nan mai shigowa zan sauke littafin nan,  sabida duk gajiyarku baku kai ni ba,  nida nake tsarawa na rubuta na turo,  kufa kawai aikin ku karatune.  Fatan alkhairi gareku Allah yabar zumunci masoyana masu qarfafamim guiwa ina godiya mara adadi.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                                    Typing............

                                    *page 71*

Ehh to amma zai yadda ya tafi dani kuwa?  Cewar ilham,  murmushin jin dad'in zahra tai sabida aikin su yana tafiya yadda ya dace,  haba ilham yaya Ahmad ai yana da kirki,  zai yadda mana sai dai in dady ne bai yadda ba,  murmushi dady yayi tare da cewa!  Ah ai ni duk abinda kike so mamana tinda kina so  sai kuje,  ta rakaki in dai kin amnce shikenan nima na amince mamana.........

A tare ilham da zahra suka saki murmushin samun nasara,  zahra kuwa cewa tai!   tom shikenan dady ni dai inaso ta rakani,  tinda ka amnince shikenan. Gyad'a kai dady yayi tare da cewa kwarai na amince.  Wani farin ciki ya lalu6e ilham da zahra,  musamman ma ita ilham d'in wanda tama kasa rufe bakinta sabida farain ciki.  Da sauri  zahra tace ilham taso mu tafi tana fad'in hakan tana jan hanunta,  sabida karta tona musu asiri sai wani washe baki take.  Suna shiga d'akin zahra tace haba ilham sai kinsa dady ya ganemu jifa yadda kike wani washe baki.
Yi haquri zahra wlh farin ciki ne yayimin yawa,  nama kasa 6oye farin cikina shiyasa,  jinjina kai zahra tai tare da cewa! ALLAH ya kyauta.

Washe gari..........

Ilham da zahra sunayin sallar asubayi suka shige kicin domin su gama breakfast dan su samu su fita da wuri.  Misalin qarfe shida da rabi suka gama girki dama,  tun da suka tashi sallar asuba sunyi wanka.  Shiryawa zahra tai bayan ta gama shiryawa ta fara cin abinci,  ilham kuwa tama kasa cin komai sai azazalawa zahra take akan tai sauri  su tafi,  karta 6ata musu lokaci zahra ko qoshi batayi ba amma sabida jarabar ilham haqura tai da cin abinci ta sa6i jakarta suka fuce,  suna fita suka tafi bakin motar yaya Ahmad d'in suka tsaya suna hira kad'an-kad'an.

Ilham ce ta kalli zahra tace wlh ni zahra gabana fad'uwa yake,  zuba mata ido zahra tai tare da cewa! To mene na fad'uwar gaba a cikin wanan zancan?  Hmm zahra kenan bazaki gane ba kawai sabida nasan baki ta6a san wani ba shiyasa,  zahra ta bud'e baki kenan zatai magana ta hango ahmad yana nufosu,  murmushi tai tare da cewa!  To gama shinan ya tawo.  Gaban ilham ne ya sake yankewa ya fad'i rass nan da nan ta fara dabircewa,  kallan ta zahra tai tare da cewa!  Haba ilham karki bada mata mana,  ki dake sosai ki nuna kamar zancan be dame ki ba,  irin dolen nan akayi miki kika futo maza ki had'e rai gashinan ya kusan qarasowa.

Baki na rawa ilham tace to,  da kyar ta iya yakito jarumta ta dora akan ta,  nan da nan ta kawar da idonta gefe ta d'an had'e rai kad'an kamar yadda zahra tasata.  Shima 6angaran Ahmad d'in tun daga nesa da ya hango ilham d'in gabansa yake fad'uwa rass,  amma da yake shi namijine dakewa yayi ya cigaba da tafiyar shi a nitse.  Yana qarasowa gaban ilham ya sake fad'uwa rass shima Ahmad d'in da yayi tozali da kyakyawar farar fuskar ilham qara rud'ewa yayi amma sai ya dake,  yace qanwata sannunku  da futowa,  murmushi zahra tai tare da cewa!  Yaya Ahmad ina kwana?.

Fuska a sake Ahmad ya amsawa zahra gaisuwar da cewa!  Lpy qalau qanwata da fatan kun tashi lafiya ya qarasa maganar yana satar kallom ilham  da ta kawar da kai gefe kamar ma batasan da wani Ahmad a wajan ba.  Ta6ota zahra tai tare da cewa ilham gafa yaya Ahmad ya futo ko baki kulaba ki gaishe shi mana,  dagowa Ilham tai tana kallon Ahmad gabanta ya qara fad'uwa amma sai ta dake ta sake kawar da kai gefe tace ina kwana?  A wani daqile take magana kamar an mata dole,  ni kuwa AMINA BAYERO nace tabb kaji matan duniya kenan sai kace ba itace jiya da ishe mu da sambatu ba.

Murmushi Ahmad ya saki tare da cewa!  Lafiya qalau hajiya ilham da fatan kin tashi lpy,  lokacin da Ahmad ya ambaci sunan ilham ji take duk duniya ba wanda ya iya fad'ar sunan kamar shi,  amma dakewa tai a taqai ce tace!  Lpy.  Zahra kuwa mamaki ne ya kashe ta a tsaye tabbas ta sake jinjinawa,   dama haka Ilham ta iya qaramin makirci na mata?  Ah lalai ilham ta iya takunta, zahra ta fad'a a zuciyar ta,  Ahmad kuwa qarasawa yayi ya bud'e musu murfin mota suka shiga cikin,  suka zauna daga haka ba wanda ya sake cewa komai suka kama hanya tafiya makarantar su zahra.

Ahmad yana driven yana satar kallon ilham ta mudubin gaba,  zahra ta kula da hakan amma sai ta basar kamar bata gani ba data gaji da had'a ido da yaya Ahmad ta mudubi kifa kanta akan cinyoyinta tayi domin ta huta da ganin wannan kallan qaunar.   Zahra bata sake d'agowa ba har sai da Ahmad yace qanwata mun qaraso makarantar, sanan zahra ta d'ago.  A hanzar ta d'auki jakarta tare da cewa!  To ilham ni zan shiga amma ya kamata ki koma gaba ki zauna bazakiji dad'in zama ke kadai a baya ba,  daga haka zahra bata jira amsar ilham ba ta fuce tana matse siririyar dariya da take so ta kwace mata.

Ilham kuwa shiru tai tana so ta dawo gaba kamar yadda zahra ta bata shawara amma kwata-kwata kunya ta hanata kwakwaran motsi,.  Shuru wajan ya d'auka na tsawan minti goma shi Ahmad bai tuqa motar ba,  kuma bai ce komai ba,  itama Ilham batai magana ba.  Can dai Ahmad ya dake yayi ta maza yace ilham kefa nake jira ki dawo sit d'in gaba mana koh?  Shiru ilham tai na wasu daqiqu,  can tace no dama ka bar ni anan tinda na riga dana zauna,  jinjina kai Ahmad yayi yana mamaki hali irin na ilham ba kamar zahra ba mai sauqin kai,  amma a fili cewa! Yayi aa ai ba dad'i mu zauna shiru kinga kika dawo ko hirace mayi ko?.

Yamutsa fuska ilham tai tare da cewa,  to shikenan tinda dai ka takura bari na dawo,,  murmushi Ahmad yayi tare da cewa!  Yauwa ilham ko ke fa yana qarasa fad'in haka ilham ta fara qoqarin fita,  shima Ahmad d'in da sauri ya bud'e morfin motar ya futo yana futowa ya zagaya ya bud'ewa ilham murfin motar gaba tare da cewa!  Bismillah hajiya Ilham,  ba musu Ilham ta shiga ta zauna,  tana zama Ahmad ya rufe murfin motar ya mayar sanan ya koma ma zaunin sa ya zauna,  yana zama ya tayar da motar suka fara tafiya.

A hankula Ahmad yake jan motar akan kyakyawan titin qasar rasha mai cike da ban sha'awa.  Wajan ya d'au shiru ba abinda  yake tashi sai qamshi turare Ahmad da kuma na Ilham d'in,  da air freshener motar.   Motar tayi sanyi sosai sabida yanda aka qure A. C kamar ba sanyi ake a garin ba,  sanyi ya fara isar ilham dan duk ta lulu6e jikinta da mayafinta amma bata dena ji ba,  dan haka data gaji da sanyi hannu tasa ta rage sanyi A. C,  da sauri Ahmad ya kalle ta tare da cewa!  Oho I'm sorry bansan bakya buqatar sanyi ba dama na kashe ai,  ya qarasa maganar yana qoqarin kashe A. C motar gaba d'aya.

Da sauri  ilham ta da katar da shi ta hanyar cewa!  Aa ka barshi haka,  bawai bana son A. C bane kawai naji tayi yawa ne,  yanzu in ka kashe ai zafi zamuji tinda glass d'in motar arufe suke.  Da sauri  Ahmad ya cafe zancan da cewa! Ehh hakane kuwa kin kawo shawara mai kyau hajiya Ilham.  D'an had'e rai ilham tai tare da cewa!  Nifa ba sunana hajiya ba sabida ban ta6a zuwa saudiya ba.  Murmushi Ahmad yayi tare da cewa,  ah karki damu in sha ALLAH nan bada jimawa zakije,  ki ringa zacewa kanki alkhairi mana.  Ehh hakane amma banaso ka dena cemin hajiya ka bari sai na fara zuwa tukuna sai ka cegaba da cemin hajiyar.

Satar kallon ta Ahmad ya sake tare da cewa!  Hmm tom shikenan na dai na kiyi haquri,  murya qasa-qasa ilham tace it's okay komai ya wuce.   Sosai Ahmad ya juyo ya sake kallanta tare da cewa!  Dama kina magana sosai kamar haka?  Murmushi kad'an Ilham,  ta saki wanda murmushi ba qaramin kyau ya qara mata ba har sai da dimple d'in ta ya losa,  nan da nan Ahmad ya sake rud'ewa,  amma dakewa yayi ya cigaba da tuqi.  Qara mai mai ta mata tambayar Ahmad yayi da cewa!  Na tambaye ki kinyi shiru,  had'e rai ilham tai tare da cewa!  Kai ka ta6a ganin mutum yayi magana kuma ka tambaye shi baya magana sau nawa kake ganin ina magana a ganka?.




Oho sorry ilham nifa ba haka nake nufi ba,  dan hararar gefan ido ilham ta sakar mai tare da cewa!  To me kake nufi?  Murmushi Ahmad yayi tare da cewa!  Haba ilham mai da wuqar saurin fushi fah baya yiwa kyawawa irin ku kyau,  Ilham kuwa tanajin haka ta sake sakin murmushi tare da cewa!  Hmm ai kai ne da wata tambaya,  mai kake nifi da bana magana bayan yanzuma ita nake?  Ta qara watsawa Ahmad tambayar a karo na biyu.  Da sauri Ahmad yace nifa abinds nake nufi da hakan shine!  Dama kina magana sosai kamar haka naga,  tun lokacin dana fara had'uwa da ke a wani daqile kike magana shi yasa nayi tinanin bakya yiwa almajirai irin mu magana.

Da sauri ilham ta zaro ido tare da cewa!  Lallai da kanka kake cewa kanka almajiri gaskiya abin ba tsari,  murmushi Ahmad yayi tare da cewa!  Ehh mana ai a wajan ku mu almajirai ne masu nema tai mako,  cikin mamaki ilham tace tai mako kuma tai makwan me kuke nema?  Jim Ahmad yayi na wasu lokutan kafin yace hmm zan gaya miki amma ba yau ba,  itama ilham d'in jim tai tare da cewa! To shikenan ALLAH ya kai mu lokacin da zaka fad'a.  Murmushi Ahmad yayi tare da cewa! Ameen ilham mai harara,  ya qarasa maganar yana d'an kashe mata ido d'aya.

Hakan da yayi ba qarin rud'a ilham yayi ba,  amma sai ta dake tace ilham mai harara kuwa?  Ta karasa maganar tana kafe shi da idanuwan nan nata masu kama dana mashkhur,  da sauri Ahmad ya kawar da kai daga kallanta sabida wani irin so da shauqi daji ya qara d'iban shi.  Murya a shaqe Ahmad yace eh mana ranar nan da nazo kika bud'e min ba hararata naga kina yi ba,  yanzuma sai da kika harareni ta gefan ido.  Murmushi ilham

Please Login or Register in order to submit comment