Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabida taga yarda fuska mama tai alamun bataji dad'i abinda zahra tai ba. sai da dady yasa baki ya rarra shi zahra tukunna zahra ta amince suka shirya, yaya abdul ya kai su airport, ba jimawa jirgin su ya d'aga zuwa kaduna.

Suna sauka mama ta kalli zahra tare da cewa ciromin wayata a jaka ki bigawa nana ko ta qaraso mama ta qarasa maganar tana gyarawa abdul da yake hanunta nannad'e a towel, fuska shi ta sake rufewa sabida rana. Okay zahra tace sannan ta zaro wayar mama a jakar mama da take rataya a kafad'ar ta sanan ta bud'e wayar ta fara dealing d'in number nana.

Wayar tana fara ringing nana ta d'auka kamar jira take, hello mama kun qaraso? Cewar nana, zahra cewa tai ee nana mun qaraso wai kin zo?. Ee tun yaushe nazo ina jiranku anan to ku qaraso mana, bari na fito dan na hango ku da wuri. Okay zahra tace sanan ta kashe waya, ta kalli mama tare da cewa tace ta jima da zuwa mu qarasa koh?. Daga haka mama da zahra suka jera.

Su mama suna qarasowa wajan da ake parking d'in motoci suka hangi nana da qatan mayafinta ta wani lulu6e jikin ta kamar mata aure. Zahra ma tayi mamaki ganin nana a haka sabida da ita duk sanin ta da nana bata ta6a ganin ta da babban mayafi haka ba, kai ko hijab zahra bata ganin nana da shi in dai ba sallah zatai ba, bata ta6a ganin nana ta fita da hijab ba sai dai mayafin, mayafin ma d'an qarami.

Haka mama da zahra suka qarasa zuciyoyin su cike fall da mamaki. Suna qarasawa nana fuska cike da fara'a tace sannu ku da zuwa, mama kuwa ko damar amsawa bata samuyi ba cikin mamaki tace! Nana to yau lafiya na ganki da mayafi na?. Murmushi nana tai tare da cewa hmm ai ni yanzu na dena fita da qaramin mayafi sai dai mayafin naki, ko zo dai mu tafi dan naga ana rana kuma ga baby abdul.

Hmm ni kuwa nace lallai nana anji maganar yaya abdul.

Haka mama da zahra suka shige mota nana ba 6ata lokaci ta tayar da motar suka wuce, suna tafe suna hira sama-sama har suka qarasa gidan. Suna qarasawa suka shiga ciki, dama da yake yaran gidan basa nan sun tafi makaranta shi yasa gidan yaya shiru ba hayaniya. Bayan zahra taci abinci sama-sama ita da nana kwanciya tai zuciya cike da tunanin mijinta har bacci yayi awan gaba da ita.

MASHKHUR......

Misalin qarfe biyar da rabi ya qarasa gidan ammi zuciya cike da kewar zahra da babyn sa.
Baki d'auke da sallama mashkhur ya murd'a handel d'in bedroom d'in ammi ya shiga. Ammi da take zaune akan gado tana ninke ragowar kayan baby, zuciyarta cike fall da kewar zahra da baby abdul da kyar ta iya d'agowa ta amsa sallamar da mashkhur yayi.

Bayan mashkhur ya gaisa da ammi zama yayi zuciya cike fall da mamaki. Cikin mamaki yace! Ammi tana ina? Ajiyar zuciya ammi ta sauke tare da cewa bata nan, bata nan kuma to ina taje?. Ammi a taqai ce ba bawa mashkhur amsa da kaduna gidan su, gidan su kuma ammi zahra tana da wani gidan su da ya wuce nan ne?. Kwarai kuwa gashi kuwa ka gani, wanka jego ta tafi.

Amma kuma ammi sai kika barta ta tafi can, to kamarya na barta ta tafi can mashkhur da hana ta kake so nayi ne, ai ni nace ta tafi ma wai ita da gidan mahaifin ta cinye mana ita zasuyi ne mashkhur?. Aa ammi bance haka ba amma da nan da can ai duk d'aya ne. Ee nasan haka amma ita da iyayan ta sai ace bazata je can ba, nima bada son rai na nace tace ba.

Amma ya kamata a ringa kwatanta adalci, tinda Allah ya bayyana mata iyayan ta ai sai mu dena nuna fin qarfi akan ta, dole a ringa barinta tana zuwa in abun zuwa ya tashi ammi ta fad'a cikin sanyayiyar murya. Rai ba dad'i mashkhur yace to ammi Allah ya baki haquri. Aa ai kai zan bawa haquri mashkhur, amma in kana son ganin ta, zaka iya zuwa kadunan ko zuwa gobe ne, sai ka ringa zuwa akai-akai kuna gaisawa.

Ai kwana arba'in d'in kamar yau ne, ammi ta qarasa maganar tana kallon mashkhur wanda gaba d'aya ta lura bai ji dad'in hakan ba dama tasan bazai ji dad'in hakan ba. Amma ko ba komai dai zahra zata wuta sosai ta gama arba'in d'in ta hankalinta kwance. Ok mashkhur ya iya cewa sanan ya miqe rai ba dad'i. Ka gai da gida kabi anya a hankula banda gudu cewar ammi....

KADUNA.

Zahra tinda ta kwanta ba ita ta tashi ba sai wajan qarfe 4 tana farkawa mama tana shigowa. Yauwa zahra sannu da tashi, dama ga ruwan zafin wanka jegon naki yana can a ice yana tafasa in kinci abinci ki tazo a fara. Tom zahra ta fad'a zuciya cike da fargaba, tom bari nasa nana ta kawo miki abdul haka ai rainan yayi yawa nasan yunwa yake ji yanzu.

Zahra bayan ta gama bawa abdul nono ko abinci bata samu damar ci ba mama ta tusa qeyarta zuwa toilet da ruwan zafin ganyayakin wanka jego ruwan sai wani tiriri yake. Haka dai zahra ta d'aure haka fara wanka, tanajin zafi amma dai ba kamar yarda tai tinani ba mama tana mata komai a hankula har suka gama. Bayan zahra an gama futowa tai tasa kayanta zuciya cike fall da kewar mashkhur.

Zama zahra tai a kan bed sanan ta bud'e wayarta wanda dama tun sanda suka tawo take a kashe. Tana kunnawa taci karo da messages d'in mashkhur yana ta faman jero mata su na kewa da soyayyah, yana ta tambayar wai lafiya yau yake jin wayar a kashe. A dede lokacin nana ta shigo, ko zama nana bata kai da yiba zahra ta miqe tare da cewa bari na fita qasa na sha iska.

Daga haka zahra ta miqe ta fuce, tana fita harabar gidan, garden ta nufa ta fara qoqarin kiran mashkhur. Zahra tayiwa mashkhur kusa 5 miss call amma no piking no reply. Zama zahra tai a jerun kyawawan kujerun garden d'in na shaqatawa, a zuciyar ta tana cewa kai duk yarda akai mashkhur yasa na tawo kaduna.

Zama zahra tai tana tsammanin kiran mashkhur dan tasan bazai iya fushi da ita ba in tai mai wannan kiran qila zai yi calling back. Kamar yarda zahra tai tunani har ta tafi gajeran tunanin mijin nata taji kiran mashkhur ya shigo. Da sauri zahra ta d'auka ta kara a kunan ta. Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba itama zahra shiru tai kamar yarda mashkhur yayi.

Can zahra tai ta maza tace barka da war haka farin cikin rai na. Nan ma mashkhur bai ce komai ba, zahra gyara zama tai sanan tace hero magana nake maka fa. Jim mashkhur yayi sanan yace inaji lafiya kike min wanan kiran. Hmm yaya mashkhur nima bada son rai na nazo ba kasan bazan ta6a nisa da kai da gangan ba, wlh laifin ammi ne ita ce tace dole sai na bi mama.

Mashkhur hmmmm kawai yace alamun bai gamsu ba. Au haka ma zaka ce ya mashkhur ka yarda dani mana kasan bana son 6acin ran ka, yanzu dame kake so naji da rashin ganin ka ko da shariyar da kake nunamin nima ina cikin damuwa fa ba kai kad'ai bane amma tinda kaqi yarda da ni shikenan.

Na yarda dake my wife kuma bana son 6acin ranki ko kad'an amma ya kamata ace kin gayamin kafin ki tafi koh?. Naso na gayama amma na kasa kasan bana son 6acin ran ka. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa to shikenan zahrata amma ina kewar ki sosai. Haka dai zahra tai ta jan mashkhur da hira har ya sauko suka sha hirar su mai dad'i ta masoya da kuma ma'aurata...........


ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

Typing..........

Double page.

Haka dai zahra tai ta jan mashkhur da hira har ya sauko suka sha hirar su mai dad'i ta masoya da kuma ma'aurata..............

To zahra fa tana zaman wanka jego a kaduna lafiya tana jin dad'in zaman kaduna sosai yau satin ta guda kenan a kaduna. A cikin satin nan mashkhur yazo wajan zahra ita da baby abdul sun sha hirar su bawai. Zahra tana ganin kulawa sosai wajan iyayan ta da 'yan uwan ta, musamman hamaifin ta da ya d'auki son duniya ya d'ora akan zahra da babayn ta abdul.

Mama ta lura zahra ta d'an fara fad'awa sabida yawan shayar da abdul da take, sam abdul baya barin zahra ta wuta da daddare kullum cikin shan nono yake, shi yasa masha ALLAH sai girma yake ita kuma zahra tana fad'awa. Hakan ne yasa mama tai gaggawar had'awa zahra sabaya sabida kar ramar tayi yawa. Kuma kullum sai mama ta matawa zahra akan cin abinci.

Masha Allah jikin zahra yana murmurewa sosai ta mai da qibarta, hakan ma ya samo asili ne da kulawar mama da kuma soyayyah da goyan bayan da mashkhur yake bata. Duk sati mashkhur yana zuwa wajan zahra hakan yana yiwa zahra dad'i. Ga shima abdul kusan bayan kwana uku yana zuwa wajan nana, zahra in abdul yazo kamar ta mayar da shi ciki.

Ta kawo mai wanan ta kawo mai wanan yarda kasan wajan ta yazo. Abdul yana jin dad'in hakan da zahra take mai, yana zowa yake d'aukar abdul qarami sam baya bada shi har sai zai tafi, yaya abdul yana qaunar abdul qarami, yarda kasan shine mahaifin sa haka yake ji, a taqaice de qaunar da yaya abdul yake wa zahra ya shafi d'an zahra wato abdul qarami.

Ammi ma har kaduna tazo domin duba lafiyar zahra da jikan ta abdul sabida tayi missing d'in su. Itama ilham tazo sau d'aya yaya ahmad ya kawo ta da tsowo cikin ta, zahra kuwa tayi farin ciki sosai da sosai, haka tai ta yiwa yaya ahmad magiya akan yabar ilham ta kwana, ahmad dai da farko yace aa, amma da maman sa tayi maga tace, ya barta ta wuta ko dan tsowan cikin ta hakan ne yasa ahmad yabar ilham ta kwana.

Ranar dai kuwa kwana su kai suna hirar su, har ilham tana mamakin yarda abdul yake yawan sha nono dare. Cikin mamaki tace haba ai dole yaran nan yayi wanan girma cikin one month da haiwuwa kice haka yake stoste ki zahra. Hmmm ilham ke de bari wlh ai ina fama da abdul sai dai fatan Allah ya raya.

Amma bayan ya cika wata biyu zan fara had'a mai da madara. Hmm ai kuwa de zahra gwara karya shanye mana ke. Dariya zahra tai sanan tace aa kar de ya shanyewa mijina ni. Hmmm zahra kenan baki da dama wlh Allah ya barki ke da yaya mashkhur.

Amen ilham wlh har ALLAH-ALLAH nake na kammala arba'in d'in nan na koma d'akin mijina. Ah kuka dad'i kike zahra kinga ni nan da cikina nan da sati uku zuwa had'u zan haiwu amma har ALLAH-ALLAH nake na sauka na dawo gida na wuta, wlh duk yarda nake so yaya ahmad amma cikin nan yana sawa naji wataran bana son ganin shi.

Dole haka yake min uzuri ya rabi dani ga yawa fad'a da nake mai, amma Allah sarki bawan ALLAH haka yake haquri, sai ma rarrashi, amma na tabbata da yaya mashkhur ne sai dai naci duka. Dariya zahra tai sannan tace hmmm ni ai cikina bai sa ni inajin haushi mijina ba, amma fa yaya mashkhur ya zarce yarda kike tunani.

Ya fad'a kogin soyayyah ta ba zai ta6a yin abinda kike tinani ba, sai dai tinda baya san hayani ya ko ina fad'an ma ya wuce ya barni anan. To haka ilham da zahra su kai ta shan hirar su sai wajan qarfe 2 dare suka kwanta bacci. Washe gari da yamma misalin qarfe 4 ahmad yazo d'aukar ilham haka ilham da zahra suka rabu cike da kewar junan su. To haka zahra ta cigaba da wanka jego cikin kulawar mama.

Bakin nana da abdul ya qarato sosai dan har an kawo lefe yau ya rage saura 4 days a fara biki. Kuma hakan yayi dede da saura 2 days zahra ta gama wanka jegon ta. Duk wani gyara da matsi zahra ta sahshi a wajan mama, wani sa'in ma maganin mata iri d'aya suke sha da amarya zahra jikin ta yayi bul-bul tayi luwai-luwai kamar ba mai shayarwa ba, dan in ka ganta bazaka ta6a tinanin ta haiwu ba tana nan kamar budurwa.

Zaune zahra take a kan gado mama kuma tana daga qasa tanayiwa baby abdul wanka wanda ya girma tabarakallah masha Allah. In ka gan shi sai ka rantse yayi wata biyu girma sosai yayi wayo. Mama nifa banji kina maganar komawata gida ba, ina irgawa fa yau saura kwana biyu na gama arba'in. Dagowa mama tai ta kalli zahra sannan ta mayar da kallanta kan abdul tare da cewa!

Ina sane da hakan zahra amma karki manta bayan kin gama arb'in washe gari za'a fara bikin nana, kuma ga maganin ki har na kwana goma baki qarasa sha ba shine nake ganin kawai ki bari sai an gama biki sai ki koma gaba d'aya. Zahra harda d'an razana da taji maganar mama kamar zatai kuka tace haba mama kin riga da kin sa fa akan dole nazo nan kuma ke kika ce ina arba'in zan koma.

Sanan ga yaya mashkhur can ya kwallafa rai akan dawowa ta mai zance mai? Kuma bikin nana ai da nan da can duk d'aya ne, tinda acan ma su Ammi suna taran biki yaya abdul yana can dan ALLAH mama ki barni na koma gida. Cikin mamaki mama tace wana gidan zaki koma, gidan ki ko gidan Ammi? Zahra da sauri tace gidana mana zan koma ai kullum zan ringa zuwa bikin ina komawa gida da daddare.

Hmmm lallai zahra kalar wannan zumud'i haka, zaki koma daki mijin ki ai kyan mace d'akin mijin ta, amma wanan gaggawa da kike ko kunya ta bakyaji, zahra duk abinda nakeyi miki fa sabida kiji dad'in zaman aure ne, haiwuwa ba wasa ba dole na gama kimtsaki meye dan kin qara 7 days, kuma fa maganin ki nake so ki qarasa shanyewa zahra in kina haka sai naga fa kamar bakya son mu gudun mu kike.

Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa haba mama da bakin ki kike fad'in haka ni sam bana gudun ku wlh ina qaunar ku a matsayin ku na iyayena na biyu. Tom zahra in dai da gaske kike ki daure ki zauna a kammala bikin nana sabida ina so 'yan uwana da dama su same ki a gidan biki harda wanda baki sani ba ki qara sani, wanda kuma kika sani ku qara sabawa.

Da kyar zahra ta iya cewa to mama tinda haka kike so zan lalla6i yaya mashkhur ya amince da hakan duk da nasan da wuya. Ah haba zahra meye na karyewa da wuro sai kace ba mace ba, ita fa mace da kisisina akan santa, wanda su kan su mazan suke tsoranta kawai ki san yarda zaki jawo ra'ayin sa hary ya amince, in kuma yaqi sai ki koma gida amma ni dai so samuna ki bari a kammala bakin nana tinda ya qarato.

Tom mama in sha ALLAH zanyi yarda kika ce bari na kira shi waya. Miqewa mama tai sanan ta kawo zahra abdul wanda ta gama yi masa wanka ta shirya shi. Ta kwashe kayan wanka ta fuce. Yaran sai wani kallon zahra yake yana lumshe ido yana tayi mata fara'a zahra cikin mamaki take tunanin wanan wayo na abdul wato har ya gane ita ce maman sa kenan.

Haka ta d'ago shi cike da qauna ta fara qoqarin ba shi nono sabida tasan abinda mama take nufi kenan da bazata bar mata shi ba da shi zata fita. Haka zahra tayi feeding d'in abdul cike da kulawa da qauna, bayan ta gama gyara rigar ta tai ta ajiye shi a gefan ta, nan da nan abdul ya fara wutsul-wutsul kamar wata tarwad'a.

Murmushi zahra tai dan ta gane abinda abdul yake nufi so yake a d'auke shi ba wai a ajiye shi ba, kai abdul ka cika wayo zahra ta fad'a a fili fuska cike da murmushi. Amma zuciyar ta cike take da damuwar hanata tafiya da mama tai. Wayarta zahra ta d'auko ta fara qoqarin kiran mashkhur, amma sai ta kasa dan bama tasan ta inda zata fara yi masa bayani ba.

A dede lokacin abdul ya fara kuka, zahra tana d'aukar shi nana ta shigo. Ah lafiya nake jin kuka d'ana meke faruwa ta qarasa maganar tana zama kusa da zahra. Kukan jin dad'i yake yi nana wai shi bazan kwantar sa shi ba sai dai na d'auke shi da hannu na. Kai abdul ka cika wayo meye na gaggawa haka ka bari ka cika kwana arba'in d'in tukunna nana ta fad'i haka fuska cike da fara'a.

Tana d'aukar shi a hanun zahra hmm ai kuwa dai gwara ki gaya masa. Nana tana qar6ar abdul wayar zahra ta fara ringing miqewa nana tai tare da cewa! to bari Mude mu futa garden mu sarara ni da baby abdul. Zahra ko damar amsawa nana ba tai ba ta fara qoqarin d'aukar wayar, ta d'auka ta amsa baki d'auke da sallama. Nana kuwa tuni ta fuce hannu riqe da abdul.

Cikin amince da farin ciki mashkhur ya amsa sallamar zahra. Tare da qarawa da gimbiya ta takusan dawowa zuwa gare ni abinda na dad'e ina mafarki. A jiyar zuciya zahra ta sauke sanan tace hmmmm gaskiya ne farin ciki na amma! Shiru zahra tai tama kasa qarasa maganar bakin ta, da sauri mashkhur yace amma lafiya nasan sa akwai magana a bakin ki.

Yaya mashkhur ina tsoron yarda zaka d'auki zance nawa ne. Ah haba zahra kin san zan fahimce ki sosai maza ki gayawa mijinki abinda kike san gaya mai. Dama yaya mashkhur so nake na na na cema ka bari zuwa nan da da shiru zahra tai zuciya cike da zullum abinda take son gayawa mashkhur dan har ga Allah tasan mashkhur yaji buri da dawowar ta over.

Haba wife meye haka kuma, sai kace wani bakwanki kike min wanana kwana-kwana pls ki fad'a min abinda kike son cewa. Ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan tace dama so nake na roqeka alfarma akan ka bari a gama bikin su nana sai na dawo. Dif mashkhur ya d'auke wuta yayi shiru kamar bai ji mai zahra ta fad'a mai ba.

Itama zahra shiru tai dan ta d'au kimanin 5 minutes ba wanda ya sake cewa komai can tai ta maza tace yaya mashkhur kana jina kuwa. Jim mashkhur yayi kamar bazai yi magana can yace dole ki kasa gayamin wanan mumunar kud'irin naki teddy, wai zahra so kike ki kashe ni ne qarfin hali fa kawai nake yi.

Haka mashkhur ya rufe zahra da fad'a ya ringa zazzagawa zahra fad'a ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba zahra dai shiru tai har ya gama ya kashe wayar. Zahra ba tai mamakin hana ba dan tasan mashkhur zai aikata abinda yafi hakan in yaji wanan maganar, zahra tamayi mamki da mashkhur ya iya tsayawa yi mata wanan bayanin dan a tinanin ta kashe mata waya zai yi ba tare da yace komai ba.

Zahra tafi 10 minutes a hakan can wata dabara ta fad'o mata hakan ne yasa tai ta buga wayar mashkhur, amma sam mashkhur yaqi d'agowa daga qarshe ma kashe wayar yayi hakan zahra ta ajiye wayar rai ba dad'i. To ranar zahra kwana tai cikin damuwa dan har dare tabi ta kira mashkhur amma wayar sa a kashe. Washe gari misalin qarfe goma na safe taga kiran mashkhur ya shigo. Dama zahra tasan bazai iya fushi da ita ba dole zai kirawo.

Hannu na rawa zahra ta d'auki wayar baki d'auke da sallama. Kan ciyar ta abdul ne Kwance yana shan nono safe, da sauri zahra ta saki nono ta da take riqe da shi tana bawa abdul. Abdul kuwa haka ya ringa sha ba tare da zahra ta riqe mai ba kamar wanda yayi wani wayo. Ko da zahra ta d'aga wayar mashkhur shiru yayi ba magana. Zahra ce tace haba yaya mashkhur meye na d'aukar zafi haka.

Bayani nake ma amma baka qarasa saurara ta kasan bazanyi hakan da gangaba da akwai dalilina nayim haka. Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba zahra ciga da magana tai da cewa abinda yasa nace ma haka abdul ne yake mura sosai kuma kasan in zamu tawo plane zamu bi kuma da sanyi sosai, nan ma dole nake haquri bama kunna a. c ko canka kullum cikin zafi muke.

Mashkhur shiru yayi alamun bai gamsu da maganar zahra ba, zahra tana qoqarin yin magana taji abdul dake cinyarta ya fara wani irin tari saka makwan gwarewa da yayi da nono. Da sauri zahra ta d'ago shi hankali tashe dan ita sam ta manta ta saki hanunta ta dena bashi nono da kanta, ashe wai cigaba da sha yayi. Haka zahra tayi ta bibbiga bayan sa a hankula kamar yarda mama ta koya mata in ya kware.

Amma wanan karan kwarewar tafi ta kullum dan abdul daya saki nono zahra ruwan nono fuska ya fara zubo mai har ya shigar mai hanci sa. Nan da nan baby abdul ya fara kuka mai had'e da tari, hankalin zahra ya tashi sosai nan da nan ta miqe ta fara jijiga shi, dan tama manta da wayar da take da mashkhur, mashkhur kuwa hankali tashe yakewa zahra magana amma ina zahra bata ma san yanayi ba.

Mashkhur katse wayar yayi ya sake bugowa a lokacin zahra ta rarrashi abdul ya dena kuka amma sai fama atti'shawa yake da tari. Qarasawa zahra tai ta d'auki wayar tasa a hands free sanan ta cigaba da bibigawa abdul baya a hankula. Hello zahra kin san abdul bashi da lafiya haka shine baki gayamin ba,. Nan da nan zahra tayi murmushi wayo.

Sanan tace ai jiya ya fara kuma kaga wayar ka a kashe take. Hakane amma an kai shi asibiti kuwa?. Ee an kai shi mana har an bashi maganu yanzu ma mantawa nai ban bashi maganin ba shi yasa yake tari. Ah maza ki je ki bashi maganin gaskiya ki dena matawa da sakaci da lafiya abdul ki ringa kula sosai zanzo anjima na gan shi.

Da sauri zahra ta zaro ido jin kwabarta zatai ruwa, sanan tace kai mutane da dama sun fara zuwa biki fa kuma nasan baka son hayaniya da yawan jama'a kawai ka zauna, ina kiyaye duk abinda likita yace in sha ALLAH likita yace nan da 3 days zai warke amma a dena kunna mai sanyi na tawan one week.

Mashkhur yana ganewa in zahra tayi mai qarya amma wanan karon ya kasa ganewa sabida soyayyar dan sa abdul ta cika masa zuciya. Jiki a sanyaye mashkhur yace tom shikenan ki zauna kawai har 7 days d'in amma ki kula sosai pls banda kunna a.c ko fanka, kuma ki ringa bashi magani in lokaci sha yayi. Tom shikenan my husband, in sha ALLAH I love, ajiyar zuciya mashkhur yayi sanan tace I love too my wife..........

Mu had'e a next page.

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

*Page 147*

Typing.......

Tom shikenan my husband, in sha ALLAH I love, ajiyar zuciya mashkhur yayi sanan tace I love too my wife..........

Tom saga haka zahra tai sallama da mashkhur yana sake jajjada mata akan ta bawa abdul magani. Bayan sunyi sallama zahra miqewa tai ta d'auki babays towel ta koya abdul da shi tana ta jijiga shi har bacci yayi awan gaba da shi. Daga haka ta d'auko waya ta kira ilham suka sha hirar su, bayan zahra ta kammala ta sauke abdul ta kwantar da shi sanan ta fuce domin yin breakfast.

To bayan zahra ta gama arba'in washe gari nana da qawayanta

Please Login or Register in order to submit comment