Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dago tare da cewa haba, ya zaki min haka ni bafa dad'e wa zanyi ba inaga in na dad'e na kai one hour fah. Oho ni dai ba in da zaka wlh ah to,. Kallanta mashkhur yayi tare da cewa! Zahra kina SONA kuma kin shirya cigaba da iya zama da NI a matsanyin MIJIN ki kuwa?..........

Mu had'e a next page anjima, wanan na jiya ne anjima zan muku posting d'in na yau.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 88*

Kallanta mashkhur yayi tare da cewa! Zahra kina SONA kuma kin shirya ciba ba da iya zama da NI a matsanyin MIJIN ki kuwa?..........

Da sauri zahra ta d'ago tare da girgiza kai a tsorace tace aa ni bana son ka wlh, yaya abdul nake so shine mijina. Wani sanyi mashkhur yaji har zuciyar shi, afili yace to kinga yanzu fa kina gayawa dady haka zai ce bazan sake kike ba dole mucigaba da zama, kuma kinga bana san junan mu amma kika sake kika gayawa dady shikenan, wlh sai auran nan bazai qare ba yanzu aka fara kuma kin san sai dai ba raga miki zanyi ba jikinki ne zai gaya miki.

Ajiyar zuciya zahra ta saki tare da cewa! Tom shikenan naji bazan gaya mai ba bani wayar, zahra ta qarasa maganar tana miqa hannu fuska a d'aure. Miqa mata wayar mashkhur yayi tare da miqewa ya fuce daga gida. Zahra kuwa yana fita cewa, ALLAH yasa result d'in naka yayi kyau, dan ni na gaji da wanan auran ta qarasa maganar tare da saki dogwan tsaki.

Zahra tana kunna wayar tata direct ta shiga WhatsApp nan kuwa sakwanni ya fara 'yar rige-rigen shigowa. Massage d'in yaya abdul dana ilham sai na candy's class d'in ajinsu ne yake 'yar rige-rigen shigowa. Bayan massage d'in sun gama shigowa, haka zahra ta ringa bud'ewa one by one. Group d'in ajinsu ta fara shiga, haka dai tai ta bin tana d'an karanta massage d'in, duk da ba duka take karantawa ba.

Ga iyayan hotunan da aka turo wanda sukayi ranar candy,, bayan zahra ta gama duba pictures d'im massage d'in yaya abdul ta shiga shima ta karanta iya wanda zata iya ta bashi reply sanan ta shiga na ilham. Tana fara bawa ilham reply taga video call d'in ilham ya shigo, sam zahra qin d'agawa tai sabida batason ilham taga ciwan da taji a goshinta.

Haka dai suka cigaba da magana ta voice note, ilham tana ta bata labarin yaya ahmad da kuma na kaka da ta takura mata akan sai ta turowa zahra wai wasu addu'o'i da zata yiwa yaya mashkhur. Zahra kuwa cewa! Tai shikenan kawai ilham sai kin turo amma ni fah har na gaji da wanan addu'ar kamar ma bata shiga.

Bayan ilham ta turowa zahra addu'o'i haka zahra ta zauna ta karance su tabb, dan ma dai zahra taga duk masu sauqi ne, wai a ruwa za'a tofah sau uku mashkhur ya sha, nan da nan zahra ta fara tinani akan taya zata iya tufawa mashkhur a ruwa yasha ita da ko tafiya ma bata iya yi. To bayan zahra ta gama chat da ilham ajiye wayar tai a gefe bacci mai nauyi ya kwashe ta da yake jiya bata samu tayi wani baccin kirki ba.

Mashkhur kuwa yana fita ya shige motar sa har zai fita daga gidan ya hango ahmad yana d'aga mai hannu. Dan haka tsayawa mashkhur yayi yana jiran ahamd d'in, ahmad yana qarasowa ya shigo motar tare da cewa! Mashkhur ya rayuwarka da haka ko ba school zaka bane?, nan zani mana, ko kai ba'a turoma massage d'in ba ne.

Gyara zama ahmad yayi tare da cewa! Nan zani mana,, ya jikin zahra? Ya mutasa fuska mashkhur yayi tare da cewa! Oho ita ta sani. Ah kamar ya ita ta sani kai da ka kwana da ita gida d'aya kuma kake mata jinya?, ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! hmm kai dai bari kawai ahmad wlh zahra bata da imani, kaga yadda ta ringa hawalar dani jiya ko baccin kirki bata barni nayi ba kai ai naga tashin hankali jiya.

Wata dariya ce ta kwacewa ahmad dan harda riqe ciki. Mashkhur kuwa ciga ba tuqi yayi tare da cewa! Mugu kawai ai dole kayi dariya, tinda ka bani muguwar shawara ba. Da kyar ahmad ya iya sai-sai ta dariya tare da cewa! Hmm ai kai ne ka bani dari wlh wai muguwa zahra ma da batasan hayaniya, ko dai kawai sharri be irin naka.

Ahmad kenan haka kake gani, nima da haka nake gani, wai harfa abinci in na kawo mata sai tace ba shiba, kai kukan dare yarinyar nan ta d'inga yi, ina bacci kwai sai naji kuka a tsakiyar kai na yadda kasan na shaqe ta. Dariya ahmad yayi tare hmm ai kad'an ma ka gani mashkhur in dai bazaka dena wanan shanshan qamshin ba kawai ka saki jiki kai jinya malam ahmad ya fad'a yana sakin dariya. Mashkhur shiru yayi bai ce komai ba, ahmad kuwa haka yayi ta tsokanar mashkhur har suka qarasa makarantar.

Mashkhur suna qarasawa yaji zuciyar shi tana bugun 9-9 dan sam bayan san yaga wani abu ba dai-dai ba a result d'in shi. Sabida yasan har dai bai ci jarabawar nan ba shikenan zahra ta zamar mai qarfan qafa. To haka dai da haka su mashkhur suka qarasa dandazon taran nan suka zauna sam mashkhur ya kasa saqat, Ahmad yana yimai magana amma ina bai ma san abinda yake ce mai ba.

Tofah yanzu kowa ya mai da hankakinsa kan malaman da su fad'i saka mako. To kan art student aka fara wato su ahmad. To mashkhur Allah abu yayi kyau dan acikin muta 100 ahmad yazo ta goma, masha ALLAH ai batun gaskiya ahmad yayi qoqari. To ba'a d'au wasu lokutan masu yawa ba aka gama da 'yar art d yake a iya mutane ashirin aka iya basu result wato suke aka karrama sunyi qoqari sosai

To fah qaqa qara qaqa, yanzu fah an dawo kan science student wato su mashkhur. dan yanzu za'a fara fad'ar saka mako, gaban mashkhur sai fad'uwa yake. sunan wani aka fara kira wato shi ne ya lashe na d'aya acikin su mashkhur. wani d'an qasar rasha ne ya d'au first class, mashkhur kuwa bai yi mamakin hakan ba sabida shi sam baya kawowa kansa zai ci ko ta goma ne. To bayan an gama karrama first class an bashi shidar karrawa.

Sai akan dawo kan na biyu nan da nan mashkhur ya sanqame a zaune saka makwan jin an anbaci sunan shi. An kira sunan shi sau uku amma sam ya kasa motsawa sai da ahmad ya d'an ta6a shi sana ya dawo hayyacinsa. Haka mashkhur ya lala6a ya qarasa wajan zuciya cike taff da mamaki dan maimakwan yayi farin ciki mamaki ne ya kama shin dab bai ta6a tinanin hakan ba duk da kuwa yasan yayi karatu sosai.

Ah wlh koni amina bayero nasan yaya mashkhur yayi karatu dan har hana idon sa bacci yake ga sallar dare ai addu'a tafi
qarfin wasa.
Bama iya mashkhur ba har wasu daga ciki student d'in sunyi mamakin haka daga ciki kuwa harda ahmad sabida yadda sukaga kwana kin baya mashkhur yana wasa da karatu sosai. To fah an karrama mashkhur sosai da sosai, an girmam shi yadda ya kamata, an bashi alamum karramawa.

duk da kuwa ba wanan ne karo na farko da akayi mai hakan ba, dan lokacin da mashkhur ya zo school first exams din su shi ya d'au first class.
Mashkhur har offer aka bashi ta aiki a qasar, in yana da buqata zai iya ciga da zama a qasar yayi aiki shida iyalansa.


Tofah tun kafin a gama taro mashkhur ya takurawa ahmad akan sai sun koma gida, duk sabida zahra, dan mashkhur yasan taf zahra zata iya aikata abinda tace in dai bai dawo da wuri ba.
Suna qarasawa mashkhur yayi parking tare da cewa! To ya kenan zaka shiga ka duba ta ne ko kuwa?.

Mai kuwa zai hana na duba ta, jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa! Ai gwara kaje ka duba ta, jiyama fa da daddare wai na kira mata kai hmmm kai ai yarinyar nan ta cazamin kai, gwarama kaje kayi mata fad'a dan wlh ina kai zuciya ta nesa ne kawai dan wataran ta sake ta kai ni qarshe,, sai jikinta ya gaya mata duka zata ci.

Dariya ahmad yayi tare da cewa! Lallai duka ana zaune qalau to wlh gwara ka cigaba da kai zuciyar taka nesa dan in ka dake ta wata jarabar zaka sake fad'awa baka gama fita daga wannan ba, dan ni ba ruwana bama na qasar za'ayi ah to. Cikin mamaki mashkhur ya kalli ahmad tare da cewa! Komar ya baka qasar to kana ina?.

Gyara zama ahmad yayi tare da cewa! Ehh mana ai tun jiya da aka turomin message a makaranta akace muzo mu kar6i result d'in mu ya fito,, ai tini na sai ticket,, gobe in ALLAH ya kaimu moning plane zan bi, in sha ALLAH gobe sai kwanan nigeria. Cikin mamaki mashkhur yace wai ahmad da gaske kake, amma shine ko kai shawara dani haba ahmad saurin mai kakeyi haka? da ka jira ai mun koma tare.

Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa ai nasan in dai na gayama bazaka barni na sai ticket d'in ba kuma wlh ina da dalilai masu mahimmanci da yasa zan koma nigeria, amma kasan badaban haka ba zan iya jira har zahra ta samu sauqi sai mu koma tare.
Jinjina kai mashkhur yayi yaso ya tambayi ahmad wana dalili ne haka zai hana shi jiran shi, amma sai ya danne sabida shi bayasan yawan shiga abinda ba ruwan sa.

Ahmad kuwa ba dan komai ya yanke shawarar komawa nigeria ba face abu biyu zuwa uku. Na farko dai ya matsu ya koma l sabida ya had'u da ilham, wani mugun qaunar ta da san ganinta ne yake addar shi shi, na biyu kuma, yana so yaje ya samu dady ya gaya mai zancan soyayyar su da ilham, daga nan kuma a tura manya, ayi magarar aure asa rana sabida ahmad da ilham sun matsu ai auren su huta.

Na uku kuma ahmad yana son zahra da mashkhur su fahimci junansu sosai, yadda qiyayyar da take tsakanin su zata kau. sanan su so junan su har wani abun ma ya gifta a tsakanim su, ahmad yasan har dai yana tare da zahra da mashkhur baza su ta6a fahimtar junan suba,, shiyasa ma yake san yabar su su biyu. Hmm nikuwa amina bayero nace anya ahmad kuwa, inaga dai bakasan yadda mashkhur da zahra suke qin junan su ba shi yasa kayi tinanin haka.

To daga haka ahmad da mashkhur suka futa daga motar, sanan suka wuce sama. Lokacin da suka shiga sun tarar da zahra kwance akan sofa tana ta shararar baccinta hankali kwance. Ahmad kuwa tafiya yayi yace zuwa anjima in zahra ta shi zai dawo. Mashkhur kuwa direct ya wuce bedroom yans shiga ya shiga toilet yayi wanka bayan haka ya futo ya kwanta akan bed.

Zuciyar mashkhur tayi fass tass har dad'i yake ji in ya tina yadda result d'in shi ya kasance. Wayar shi ya d'auko ya kira waya yayi musu Oder abinci shida zahra dan mashkhur ya gaji da dafa abinci, yau ko kansa bazai iya dafawa ba barema zahra. Daga haka miqewa mashkhur yayi ya wuce fallo. Yana fita ya hangi zahra tana sauke nunfashi a hankula,, alamum baccinta yayi nisa.

A hankula mashkhur ya qarasa kan sofa da take kwance, yana qarasawa ya zira hannun sa a ahankula ya janyo wayar yadda bazata tashi ba. Yana janyowa ya koma kan wata sofa ya zauna a hankula. Yana zama ya bude wayar yana bud'e wayar direct receive call ya shiga sabida yaga koh zahra tayi waya dady, ta gaya mai abinda yake faruwa. Lumshe ido mashkhur yayi tare da furta alhamdulilahi saka makwan ganin yau zahra kwata-kwata batayi waya da dady ba.

Mashkhur bai ajiye wayar ba bayan ya fita daga receive call d'in WhatsApp ya shiga. Yana shiga ya search d'in sunan dady, nan ma yana shiga massages d'in ya sauke ajiyar zuciya, ganin basuyi magana da dady ba. Mashkhur yana fita daga chat d'in zahra da dady yaga message d'in abdul sai shgowa yake rututu da yake zahra ta manta bata kashe data ba. Mashkhur zubawa screen d'in phone d'in ido yayi yana kallan ikwan ALLAH.

A qalla sai da massage d'in abdul suka shigo wajan talatin kuma bai dad'e da turo suba, dan yana kan online d'in ma. Mashkhur zubawa massage d'in qarshe ido yayi haka nan yaji ya tsinci kansa da karantawa. Haba baby na kin san ina son ki kuma ina son!!!! Daga haka massage d'in ya tsaya, mashkhur har zai bud'e massage d'in abdul ya qarasa karantawa kawai sai ya fasa sabida shi bayasan ya karanta abinda bashi aka turowa ba kuma bai shafe shiba.

Nan da nan mashkhur ya fara tinanin wai ko zahra da abdul soyayya suke, can mashkhur yace okay koh shi yasama tace min shi take so kuma shi zata aura. Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare da ajiye wayar a zuciyar shi yace oho su suka sani ni baruwa na ai ni dai burina na sake ta in na sake ta ma ya aure ta na huta da barazanar dady.

Daga haka mashkhur ya ajiye wayar yana miqewa ya fara ji ana knocking d'in qofar,, da sauri mashkhur ya wuce wajan qofar wai duk sabida knocking d'in mar ya tashi zahra ta takura mai. 6angaran zahra kuwa tana cikin bacci taji ana knocking d'in qofar a hankula ta bud'e idanuwan ta, tana tinanin ko mashkhur ne ya dawo, wata zuciyar tace mata ko dai zee ce?.

Gaban zahra ne ya fad'i rass-rass da sauri ta d'an juya a hankula, ai kuwa tana juyawa ta hangi mashkhur da ledoji ahanunsa yana kulle qofar. Ajiyar zuciya ta sauke a cikin zuciyar ta tace ko yaushe ma ya dawo oho shi ya sani. Mashkhur kuwa yana juyowa yayi tozali da zahra sai da gabansa ya d'an fad'i rass sabida yasan yanzu zahra zata fara takurawa rayuwar sa.

Mashkhur ko kallan zahra bai sake yi ba ya wuce kan draining ya bud'e take away d'in ya zuba a plate ya fara ci a hankula,, yana ci yana tinanin yanzu ya rabu da zee kuma result d'in shi yayi kyau sosai har sun mai tayim aiki a qasar, yanzi abu d'aya ne ya gagare ya dena a gabana wato shaye-shayen nan. Hmmm in sha ALLAH ma nadena daga yau mashkhur ya fad'a a cikin zuciyar sa, wata kuma zuciyar tace anya zaka iya denawa.

Haka dai mashkhur ya cigaba da cin abincin sa yana tinani har ya gama ci. Yana gama ci ya zuba a plate ya nufi inda zahra take. Yana zuwa ya ajiye plate a gefe tare da had'e rai sosai yana cewa kee tashi. Zahra kuwa yamutsa fuska tai tare da cewa! Ah nifah ba sunana ke ba in kana cemin ke sai naga kamar ba dani kake ba. Hannu mashkhur yasa ya janyo zahra da d'an qarfi.

Wata siririyar qara zahra ta saki tare da cewa wash, mashkhur yana zaunar da zahra ya zauna shima a kusa da ita tare da d'aukar plate d'in ya d'ibo abinci a spoon ya kai bakinta. Da sauri zahra ta Kawar da kai tare da cewa! Tabbb wai ba kai ne kace bazan sake cin abinci oder a gidan nan ba, ai tun ranar da kace bazan sake ciba ya fita daga rai na nifa yanzu ko qanshin sama bana so, kawai ka dafamin wani.

Wlh tallahi in baki ci abincin nan ba sai na danne ki na tura miki ta hanci ya shiga cikin ki ko mutuwa zaki banza mara kunya kawai. Turo baki zahra tai tare da cewa! To ni bayanzu zan ciba a qoshe nake bazan ciba. Hannu mashkhur yasa ya saqalo zahra tare da janyo ta gabb da jikinsa yana cewa! Bari na tura miki ko spoon d'aya ne ta hanci dan ki tabbatar da gaske nake. Da sauri zahra tasa ihu tare da fad'awa kan qirjin mashkhur da sauri tana boye bakinta da hancin ta harda sa hannu ta saqalo bayansa da qarfi..................

Mu had'e a next page........


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 89*

Da sauri zahra tasa ihu tare da fad'awa kan qirjin mashkhur da sauri tana boye bakinta da hancin ta harda sa hannu ta saqalo bayansa da qarfi..................

Sosai zahra ta qanqame mashkhur kamar wandda zata koma cikin sa. Lokacin da zahra ta had'a jikin ta da na mashkhur wani irin shock mashkhur yaji, har sai da nunfashinsa ya d'an d'auke na wucin gadi sanan ya dawo. Da kyar mashkhur ya iya kai hanunsa ya fara qoqarin raba zahra daga jikinsa. Zahra kuwa sake riqe shi tai sosai tare da sakin kuka.

Nan da nan jikin mashkhur ya mutu laqas dan ji yayi yama kasa raba zahra daga jikin sa. Dakyar mashkhur ya iya jan dogan nunfashi tare da cewa! Bazaki sake niba, ni dallah sake ni. Sautin kuka zahra ta qara tare da cewa! Wlh bazan sake ka ba ka kashe ni, taya zanci abinci ta hanci. Sassauta murya mashkhur yayi tare da cewa! Naji na fasa baki ta hanci, zan baki ta baki, ki sake ni.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da sakin mashkhur d'in ta fara d'ago fuskar ta hankula. Wani irin kallo taga mashkhur yana mata shiba na arziki ba kuma bana tsiya ba, ita kansa bata san wana irin kallo bane. Wani irin zahra taji sai alokacin taga abinda tai kamar bai dace ba, amma sai ta d'an maze ta kawar da kai gefe, tana turo bakin ta gaba.

Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare da d'abo abinci a spoon yana kai mata baki a karo na biyu. Wanan karan dai zahra ta bud'e bakin nata, haka mashkhur ya cigaba da bawa zahra abinci jikinsa duk ya mace, zahra kuwa a bisa dole take cin abinci kawai dai tana ci ne dan ta gujewa muguntar yaya mashkhur.

Lokacin da zahra tace ta qoshi mashkhur bai takura mata akan sai ta cinye ba,, kallanta yayi tare da cewa! Baki sallah ba koh? Gyad'a kai zahra tai alamun ee. Sake had'a rai mashkhur yayi tare da cewa! Au ni zaki d'agawa kai sai kace wani sa'anki baki da baki, ya mutsa fuska zahra tai kamar yadda ta basa, murya a saqe tace banyi ba.

Miqewa mashkhur yayi ya wuce draining ya ajiye plate d'in bayan ya ajiye plate d'in ya dawo ya d'auki zahra kamar yadda ya saba, ya wuce bedroom d'in sa, da ita yana shiga direct toilet ya kai ta, yana kai ta ya futo ya fara gyara kan bed d'in, ya sake shinfid'a wani bedsheets d'in bayan ya gama ya koma toilet ya taimakawa zahra tayi alwala sanan ya shifid'a mata dadd'uma ya bata hijab ta tayar da salarta a zaune kamar yadda take.

Night...............

Kwance zahra take a kan gado, tana d'an yin chat ita da yaya abdul. 6angaran mashkhur kuwa yana fallo yana kallon wani american flim a laptop, d'aga kai mashkhur yayi yakalli agogo, qarfe tara tayi wato lokacin shan maganin zahra. Wani siririn tsaki yaja tare da cewa ALLAH ka yayemin wanan jinyar. Daga haka ya miqe ya shige kicin, yana shiga ya dafawa zahra indomie da coffee, bayan ya gama da mata ya zuba, sans ya d'auka ya nufi bedroom d'in.

Kwance ya tarar da zahra tana danna waya sau biyu mashkhur yana sallama amma ina zahra bama tasan yana yi ba hankalinta ya karkata akan wayar tata. A hankula mashkhur ya qaraso ya ajiye plate d'in a gefe tare da cewa tashi kici. Nan ma shiru zahra ba amsa, cikin mamaki mashkhur ya kalli zahra.

Wani qasai taccan murmushi yaga zahra tana saki, hankalinta duk yana kan wayar bama tasan da wata hallitta mashkhur ba a wajan. A zuceye mashkhur ya fincike wayar, a zabura zahra ta dawo cikin hayyacin ta, tana cewa innalilahi. Mashkhur zahra ta gani tsaye a kanta, wata ajiyar zuciya zahra ta saki sabida har ga ALLAH ta tsorata sosai.

Mashkhur kallan wayar yayi yana ganin sunan yaya abdul ya d'auke kansa daga wayar a zuciyar shi yace, hm ai sai kai maye kawai. A fili kuma cewa yayi! Ga abinci nan ki d'auka kici daga yau bazan qara baki abinci ba tinda kina da qarfin da zaki riqe ni da hanun ai zaki samu qarfin da ki cin abinci d'auki kici, wlh in ba haka ba yanzu sai kin cinye shi ta hanci ya qarasa maganar yana cilli da wayar zahra a gefan gado.

Zahra kuwa hannu na rawa ta d'auki plate d'in dan yadda taga yaya mashkhur ya had'e rai kuma yana magana a kausa she tasan ba wasa. A hankula zahra ta fara cin abinci alamun dai dole akayi mata. Mashkhur kuwa dogwan tsaki yaja tare da fucewa daga d'akin. Zahra kuwa kallon coffee d'in tai, ita sam coffee ma bai dame taba.

Nan da nan dabara ta fad'owa zahra mai zai hana ta tofa add'ur nan ta karya asiri a cikin coffee d'in, addu'ar da hajiya kaka tasa ilham ta ruro mata d'azu domin ta tofawa yaya mashkhur ya sha. Zahra tasan mashkhur yana son coffee sosai, in tace ba tasha in akaci sa'a zai iya sha tinda shi yana sha. Ma tsar da abinci gefe zahra tai sanan ta d'an mirgina ta d'auko wayar ta.

A hanzarce ta shiga chat d'in su da ilham, ta bud'e, tanan bud'ewa ta lalibo addu'ar a can sama da yake sunyi d'an yi chat da ilham yau sosai. Zahra tana gani a hanzarce ta fara karanta bata d'au wani logwan lokaci ba ta gama karanta addu'ar tass da yake bata da yawa, sanan ta tofa a cikin coffee d'in. Bayan zahra ta gama tofa addu'ar ajiye coffee d'in tai a gefe, sanan ta d'auki indomie d'in ta ta fara ci da yake tai mata dad'i sosai.

Zahra tana gama cin abinci kamar had'i baki mashkhur ya shigo, qarasowa yayi tare da qarewa

Please Login or Register in order to submit comment