Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma mashkhur.

Rai ba dad'i mashkhur yace ahmad wanan wace irin tambayar rainin hankali ce, ni da matata har sai ka tambaye ni dalilina na son dawowar ta. Wani siririn murmushi ahmad ya saki tare da cewa ya haquri hakane ashe matar kace nifa mantawa nake da hakan, kuma kaga kai kace min kuna komawa nigeria zaka sake ta ni sai nai tinanin kama sake ta.

Wani mugun kallo mashkhur ya watasa wa ahmad tare da cewa kai ma ashe har da kai a 'yan jiran na saki matata to wlh ko zaka mutu bazan ta6a sakin taba. Dariya ahamd yayi sosai tare da cewa aa ni ai bance ka sake ta ba mashkhur kai ne fa da bakin ka kace zaka sake ta, karka manta har haquri nake baka amma kace sai ka sake ta. To yanzu kuma ni muhammad mashkhur, nace ma bazan sake ta ba yauwa.

Hmmm aa mai da wuqar mashkhur to ALLAH ya qara qulla igiyoyin auran katamau, ai muma bama son saki. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa wlh ahmad bazaka gane ba ina cikin damuwa. Murmushi ahmad yayi tare da cewa hmmm dama ai nace in tai wari zamuji, mai yake faruwa. Ahmad dan ALLAH kaje ka dawomin da zahra gidan nan.

Wah ni rufamin asiri mashkhur ai kai da kake mijin ta kai ya kama ta kaje, duk da nasan ko kaje ba lallai 'yan gidan su bari ka tawo da ita ba. Cikin mamaki mashkhur yace sabida mai? Hmm sabida suna san ta basa so tabar gida,. Tabb to ai kuwa dole ta dawo wajan mijin ta ko suna so ko basa so, mashkhur ya fad'a a gadaran ce. Hmmmm mashkhur kenan kabi komai a sannu fa.

Ahmad bazan iya ba ni burina kawai zahra ta dawo hannu na,. Wai kai mashkhur kana nufin ka fara son zahra ne ko kuwa?, ahmad ya tambaya cike da son tabbatar da abinda yake zargi. Ba wani kwana-kwana bare 6ata lokaci mashkhur yace kwarai ahmad ciwan son zahra ne yake damuna. Tabb lallai mashkhur inaga abin nan kamar sai ka miqe tsaye, cikin mamaki mashkhur yace sabida mai kace haka ahmad.

Hmmmm to ita zahra tana son kane? Oho ban damu da ta soni ko karta so ni ba ni dai tinda ina son ta shikenan. Tab lallai mashkhur zaka sha wahala in baka bi so a sannu ba, shifa so ba siyar da shi ake ba kuma ba qarfi ne yake kwata ba, dabara, jarum ta, kalamai masu dad'i lalla6awa, da kuma kyautatawa su suke sa mutum ya so ka, kuma har dai zahra bata fara son ka ba wlh ko kun tare da ita bazaka ta6a jin dad'in ta ba dan wahala zaka sha.

Jiki a sanyaye mashkhur yace da gaske kake ahamd abinda kake fad'a. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa kwarai mashkhur, sai ka zamo mai jure duk wulaqanci da 6aacin rai in dai akan soyayya ne ka kau da kai, sai ka zamo mai yawan yiwa abinda kake so kalamai masu dad'i. Hakan ne zai sa ka shawo kan zahra ta lallami har taji ta fara son ka, amma yanzu nasan zahra tana jin haushi yadda ka ringa azbtar da ita a baya to dole sai ka goge wanan a ranta kafin ta fara son ka mashkhur.

Cikin karyewar zuciya mashkhur yace ahmad tayaya zanyi hakan sai nake ganin kamar bazan iya ba, kasan dai ni ban ta6a soyayya ba dama haka soyayya take da wahala?. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa hakane mashkhur musamman irin soyayar ku da zahra tana da wuyar sha'ani dole sai kabi a sannu zaka samu yadda kake so. Hmm ahmad in sha ALLAH zan jure komai in dai zahra zata so ni, taso muje ka rakani gidan su wlh zani.

Da kyar ahmad ya iya qunshe Dariya da take qoqarin kwace mai yace aaa haba mashkhur, ai ba yanzu ba ka bari sai ka fara tura mata message na ban hquri zuciyar ta wuce sanan zakaje ka sanar da ita soyayar ka. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa aa ahmad zuwa da kai yafi saqo zan gaya mata da bakina, wlh in na sake kwan d'aya banga ta ba zuciya ta zata iya bigawa ahmad baka san yadda nake ji a zuciya ta ba kamar ana huramin wuta.

Kayi haquri mashkhur mu bari sai zuwa gobe sai muje zan raka in sha ALLAH. Ajiyar zuciya mashkhur ya saki tare da cewa to ahmad nagode ALLAH ya kai mu goban. Hmmmm mashkhur kenan dama nasan dole zaka fara son zahra shi yasa nake ta nuna maka hanya amma ka kasa ganewa cewar ahmad. Hmmm kai dai bari ahamd wlh zaman da mukayi da zahra na saba da ita sosai, shi yasa nake ji bazan iya rayuwa babu ita ba.

Hmmm kaga mashkhur ka samu damar da zaka shawo kan zahra amma bakayi hakan ba, ni na fahimta ka dad'e da fara son zahra amma, ina tsoran na gayama a lokacin. Cikin mamaki mashkhur yace haba ahmad yaushe ka fahimci hakan. Tun lokacin da zee ta cillo zahra daga sama, zahra ta fara jinya tun a lokacin na gane ka fara son zahra amma kai baka sani ba, shi yasa na tawo daga russian na barku acan dan ku fahimci junan ku.

Amma kash hakan bai yiba duk da dai naga kun d'an shaqu kad'an. Kai ahamd amma da ka gaya min a lokacin ai da nasan mai zanyi wlh da tini wani zanca ake ba wanan ba mashkhur ya qarasa maganar yana cizar le6e. Murmushi ahmad yayi tare da cewa ai a lokacin kona gayama mashkhur bazaka yarda ba kuma da na gaya ma mai za kai?.

Wani siririn murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmmm kai dai abar zancan kawai. Shima ahmad murmushi yayi sanan yace tab wayaga so ya kama maza lallai mashkhur kaga yadda kabi ka canza ana ganinka ansan kana cikin damuwa dama ance irin ku wanda bakwa yin soyayya kuka tashi soyayya kunfi masuyi fad'awa. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmmm ALLAH dai ya kyauta kawai ahmad.

Mashkhur da ahamd sun sha hira sosai, kafin ahmad ya tafi sukai sallama, da niyar gobe misalin qarfe goma zasu tafi kaduna. Mashkhur yau rai fass ya kwanta zuciya cike da farin ciki gobe zai ga sahibar sa masoyiyar shi zahra matar sa.

KADUNA.

Nana tana zaune ta rafka uban tagumi ta tafi duniyar tunani kwana biyu duk tafi ta canza kamar ba nana mai surutu ba kowa ya kasa gane mata. Zahra kuwa tana daga gefan tana chat da yaya abdul ita kuma ilham tana tsakiyar bed tana waya da ahmad. Zahra da hankalinta ya karka ta da wayar ta cikin jin dad'i da shauqin chat da yaya abdul tace nana jeki ki d'auko min ruwa na sha.

Shiru zahra taji ba amsa, da sauri zahra ta d'ago ta kalli nana dan ganin mene ya hanata magana. Gani tai nana ta rafka wani uban tagumi ta tafi duniyar tinani. Hannu zahra tasa ta ta6o nana tana cewa nana. Firgigit nana ta dawo daga hayyacin ta tare da cewa na'am aunty zahra. Kai nana kwana biyu duk kin canza kamar ba ke ba wai mai yake damun ki ne?. Girgiza kai nana tai tare da cewa ba komai kawai dai kin san wataran mood d'in mutun yana iya canzawa shine kawai.

To jeki ki d'auko min ruwa na sha kuma yaya abdul yace nace mike yana gai da ke. Nan da nan nana ta saki fuska tace oh yau kice yaya abdul ya tina dani. Murmushi zahra tai tare da cewa kai nana daga jin sunan yaya abdul har kin saki ranki gaskiya dai kam kina son yaya abdul. Murmushi nana tai tare da cewa ke dai bari aunty zahra ai duk wani mutum fari mai mutunci da fara'a da sakin fuska yana birge ni.

Murmushi zahra tai tare da cewa gaskiya ne, ni dai tashi ki d'auko min ruwa. Miqewa nana tai fuska ciki da fara'a tace to, sanan ta fuce daga bedroom d'in. Bayan fewa minutes nana ta dawo riqe da bottle d'in watar da glass cup a hanun. Tana zuwa ta miqawa zahra, zahra ta fara qoqarin bud'e bottle d'in ruwa. Ilham da ta ajiye wayar cikin zumud'i tace kee zahra kin san menene kuwa?.

Zahra tsiyaya ruwan tai a cup tai tare da cewa aaa menene. Wai gobe yaya mashkhur zai zo, cikin mamaki zahra tace da gaske ilham? Ee mana haka ahmad yace. Murmushi zahra tai tare da cewa oh dama yaya mashkhur zai iya zuwa gidan nan a duniya, to ni kuwa mai zai kawo shi. Murmushi ilham tai tare da cewa aaa ba a baki na ba in yazo zakiji dan yaya ahmad yace kar na gaya miki nima da kyar ya gayamin.

Murmushi nana tai tare da cewa to lallai kam aunty llham inaga addu'ar ki tana gab da kar6uwa ni nasan ai mai zai zo yi. Murmushi ilham tai tare da cewa da kyau nana ai dad'i na dake kina saurin kwashewa. Tsaki zahra taja tare da cewa kai ilham ban san iskanci ke wai kin tabbata da zuwan shi kuwa tambayar mana ammi.

Haba zahra ke ki tambaye ta mana cewar ilham, zaro ido zahra tai tare da cewa tab wane ni, kin manta abinda nace miki ammi ta gani haka kurum tayi tinanin shi zamu sakeyi in yazo. Dariya ilham tai tare da cewa to bari na buga mata na tambaye ta. Daga haka ilham ta d'auki wayar ta ta fara bigawa number ammi, ita kuma zahra ta fara shan ruwan ta.

Tana d'agawa ilham ta dawo kusa da su zahra tare da sa wayar a hands- free. Bayan ilham sun gama gai sawa da ammi tace ammi wai da gaske gobe yaya mashkhur zai zo kaduna?. A dai-dai lokacin maman zahra ta shigo, tana shigowa ta zauna a gefan gado tana sauraran wayar da ilham take da ammi. Ammi cewa tai aa ni ban sani ba waya gaya miki.

Ilham cewa tai hmm yaya ahmad ne ya gayamin yanzu da muka gama waya wai yaya mashkhur yace mai gobe ya rako shi nan wajan zahra. Okay ni bai ma gayamin zai zo ba amma nasan zai zo d'in tinda ya fad'a amma ki gayawa zahra, kamar yadda na gaya mata ranar nan haka zatai kar ta sake ta sakar mai fuska bare ta aminci, sai ya gane kuskuran sa sosai kafin ta amince in ma tana so ta cigaba da zama da shi kenan in kuma bata so baza muyi mata dole ba shikenan.

To ammi ai tana jinki, yauwa zahra kinji abinda nace koh?. Rai ba dad'i zahra tace naji ammi, nafa sanki da saurin kuka da tausayi karki sake ki yafe mai nan kusa sai ya gane kuskuran shi, to ammi ki gai da min da hajiya kaka. To zahra zataji ina maman ki ce ina gai da ita. Oh to zataji gata nan ba bari a kai mata wayar ku gaisa, daga haka ilham ta miqe ta kai wa mama wayar.

Bayan ammi da mama sun gama gaisawa har 'yar hira sukayi game da lamarin zahra da mashkhur daga haka sukayi sallama. Zahra kuwa duk sai taji ba dad'i ita sam baza taso yaya mashkhur yazo gidan su ba taqi sakar mai fuska amma tinda ammi tace tayi hakan ba yadda ta iya. Amma har lokacin zahra bata dai na tinanin mai ya zai kawo mashkhur gidan ba dan ita bama tasa a ranta cewa son ta yake ba.



ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Double page.

Washe gari.

Misalin qarfe biyu zahra ta gama shiryawa tsaf cikin leshin ta baqi da ja sai ratsin fari. Sam zahra ta rasa sabida mai take d'auki zuwan yaya mashkhur gidan. Nana ce Ta shigo bedroom d'in, tare da cewa aunty zahra wai kije inji mama. Miqewa zahra tai tare da cewa ilham nace ki tambayi yaya ahmad sun kusan qarasowa?. Kai zahra yanzufa muka gama waya da shi yace sun shigo unguwar nan suna gab da qarasowa gidan haba.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa yauwa bari naje kiran mama, daga haka ta miqe ta fuce. Bayan zahra ta murd'a handel d'in qofar bedroom d'in baki d'auke da sallama ta shiga. Zaune ta samu mama a bakin bed, qarasawa zahra tai tare da zama a kusa da mama tana cewa mama gani. Kallan ta maman tai tare da cewa haba zahra kinga fuskar ki sai kace ta maza kuwa?. Cikin mamaki zahra tace kai mama mai kika gani kuma?.

zahra meye ma ban gani ba sai kace ba mace ba na lura dai kam sam bakya son kwalliya. Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa nifa bana son yawan kwalliyar nan mama in na cika shafe-shafe a fuska ta in na wanke ja take kuma tai-tai min zafi. Miqewa maman zahra tai ta nufi qaramar wardrobe d'in mudubi tana cewa haba ai ko jan baki kyasa a bakin ki zahra.

Daga haka mama ta bud'e ta d'auko hoda da janbaki harma da kwalli ta dawo ta zauna tare da ce cire d'an kwali na shafa miki. Aa mama sai kace wata yarinya ni zan shafa abu na, hararar zahra maman tai tare da cewa sannu babba, to ai kuwa sai na sahafa miki dama ba so kike ba ni dallah tsaya, maman ta qarasa magana tana cire d'an kwalin kan zahra. Daga haka mama ta shafawa zahra hoda da janbaki harma da kwalli.

Wow duk da ba wata kwalliya mai yawa mama tayiwa zahra ba amma zahra ta fita sosai da sosai. D'an kwalin zahra mama ta d'auka tare da cewa bari kiga irin d'auri da zan miki zakiyi kyau. Kai mama nifa bana son d'auri mai hawa-hawa, wani siririn tsaki mama ta saki tare da cewa ke dallah wa ya gaya miki shi zanyi miki irin d'aurin 'yan gayu isasun mata zan miki mama ta qarasa maganar tana fara yiwa zahra d'auri.

Ke bakya so ki sake rud'a mijin naki in yazo, mama ta watsawa zahra tambayar. ALLAH ya sauwaqe nifa rabuwa zamuyi yaya abdul zan aura. A uzibillahi amma dai kam zahra baki da tinani kina da aure kike cewa sai an sake ki kin auri wani, wanan ai haramun ne ba kyau kina qarama da ke amma kike neman saki, wlh baki isa ba to in sha ALLAH har ki mutu baza'a ta6a sakar min ke ba, bare ki qara wani bana son jin kalmar sakin nan ta sake fita daga bakin ki, kin mini koh?.

Amma mama wlh ni bana son yaya mashkhur, to naji zaki fara son shi ne kinji zahra ta kiyi haquri. Zahra a ziciyar ta cewa tai tabb ALLAH ya kiyaye na so mugun nan amma a fili sai tai shiru bata ce komai ba. Bayan maman zahra ta gama yi mata d'auri da yayi mata kyau wow masha ALLAH, ko mace in taga zahra sai ta yaba duk da kuwa ba wata kwalliya mai yawa tai ba. Murmushi maman zahra tai tare da da cewa wow my daughter kin ga yadda kikayi kyau ki dena had'e rai simple mana.

Murmushi zahra ta saki, wow my zahra kinyi kyau irin wanan murmushi zaki mai ammafa sau d'aya tak zaki mai daga shi karki qara. Mama tana rufe baki nana ta shigo tare da cewa finally dai ga su yaya ahmad da mijin yaya ta sun shigo gidan nan. Cikin zumud'i zahra ta miqe tare da cewa da gaske nana. Wlh aunty da gaske nake, sun ma shigo falon fa.

Kai nana mene haka maza kice ki gai da shi ki kai ma ruwa da lemo da sauran abinda aka dafa musu. Tom shikenan mama daga haka nana ta fuce, itama zahra cikin zumud'i ta fara qoqarin tafiya,. Ruqo hanun ta mama tai tare da cewa kee zahra meye haka kuma?. Cikin mamaki zahra ta juyo tare da cewa mama wajan su nima zani. Kaiii kina nufin haka zaki tafi kina yashe baki kamar gonar audiga bakiji abinda maman ki ta kano ammi tace miki ba.

Sunkuyar da kai zahra tai tare da turo baki tace naji amma mama yanzu dan yazo gidan mu sai na ringa sha mai kunu ai bazai ji dad'i ba. Murmushi maman zahra tai tare da cewa aa ai ba haka muke nufu ba, ina nufin ki kama kanki, karki shamai kunu kuma karki sakar mai fuska ki zama dai jentul kin gane koh?. Gyad'a kai zahra tai alamun to. Yauwa ki ringa tafiya mai kyau magana ma a nitse amma ba sosai ba fara'a sau d'aya.

Kuma in yace miki yana son ki karki amince yanzu kinji, to mama in sha ALLAH ma bazai ce ba. Tsaki mama taja tare da koma kan merro ta d'auki turare ta fesawa zahra, sanan tace yauwa muje bari naga irin tafiyar da zakiyi. Rai ba dad'i zahra ta bara tafiya tana wani shan qamshi alamun bataji dad'i abinda maman ta fad'a ba. Wani dogwan tsaki mama tace tare da cewa haka zaki tafiyar kamar wanda ake turawa.

Tafiyar qasai tataun mata zakiyi yauwa kin gane, tafiya zahra ta farayi cikin rangwad'a yauwa haka nake nufi amma ki qara slow ka d'an. Kamar dai yadda mama tace haka zahra ta sake slow zuciya ba dad'i. Murmushi mama tai tare da cewa good my daughter haka nake so amma had'e ran yayi yawa ki saki fuskar ki kad'an. Kamar yadda mama tace haka zahra ta saki fuskar nan tata kad'an.

Yauwa my zahra komai yayi muje na taka miki zuwa bakin qofa. Daga haka mama da zahra suka rankaya suna fita daga d'akin mama ta hangi ahmad ya nufo ta. Yana qarasowa ahmad yace oh mama da yarta kenan mai kuma ake haka na, tun dazu mashkhur yana jiran ta amma kin riqe ta. Murmushi mama tai tare da cewa sanun ku da zuwa ya hanya. Lafiya qalau mama komai lafiya amma nayi missing d'in ki fa.

Yaya ahmad ina kwana, murmushi ahmad yayi tare da cewa lafiya qalau qanwata kai gaskiya dai abin da abin mamki duk kin canza kuma yau kece da shafa jan baki tab inaga ban ta6a ganin kwalliya a fuskar ki ba sai yau. Hmmm yanzu ma bada son ranta na shafa mata ba dole ne, maza ki wuce ki tafi. To zahra tace sanan ta wuce ta far wajan zuciyar ta sai wani dukan uku-uku take.

A hankula zahra take sauka daga step d'in benan, tana tafiya kamar yadda mama tace, ugunta da qirjin ta sai wani motsawa suke. Sai wani qara step d'in yake sabida takalmin qafarta yana da dan tsini. Tun daga nesa zahra ta hangi mashkhur akan kujera cikin wata blue d'in shadda d'inki yayi mai matuqar kyau ya amshi jikin sa. Mashkhur yayiwa zahra kyau sosai ya duqufa yana danna waya, sabida miskilacci irin na mashkhur duk yadda step d'in benan yake qarar tafiyar zahra amma bai d'agowa.

Can kuma mashkhur da yaji takun yaqi ya qare sai wani sauti yake bayarwa kamar yadda jikin zahra yake motsi in tana tafiya haka ne yasa mashkhur ya gane zahra ce take wanan tafiyar. Da sauri mashkhur ya d'ago ya zubawa zahra ido wanda take gab da sakkowa gaba d'aya. Sakin baki mashkhur yayi ganin yadda zahra tai kyau kamar ba ita ba, ga jikin ta yana motsawa dai kamar kullum in tana sauka daga bene musamman breast d'in ta da suka cika dam a Riga, ai mashkhur sabida shagala bai san sanda ya yarda wayar hanunsa qasa ba ya saki baki yana kallon zahra.............

Naso na qarasa muku double page d'in nana amma bazan iya ba bacci nake ji kuma inaso komai dare na cika alqawari na nayi muku posting.

Kuna ganim mashkhur zai iya bayyanawa zahra soyayar shi gare ta ko kuwa?.

Kuna ganin zahra zata amince da mashkhur ko kuwa?.

Mai kuke tinanin zai faru in mashkhur da zahra suka gama had'uwa had'u.

Hmmm mu had'e a next page dan jin amsar tambayar ku.

hmmm sorry yaya mashkhur su mashkhur an ga halittafa an rud'e. 😂


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing...........

*page 115*

Sakin baki mashkhur yayi ganin yadda zahra tai kyau kamar ba ita ba, ga jikin ta yana motsawa dai kamar kullum in tana sauka daga bene musamman breast d'in ta da suka cika dam a Riga, ai mashkhur sabida shagala bai san sanda ya yarda wayar hanunsa qasa ba ya saki baki yana kallon zahra.............

Mamaki ne ya kama zahra ganin mashkhur ya saki wayar shi ta fad'i qasa amma bai bi ta kan wayar ba ya tsaya kallon ta. Zahra tinani ta farayi akan mai mashkhur ya gani a jikin ta ko wani aibu ko abin mamaki ya gani yake mata wanan kallon. 6angaran mashkhur kuwa ya qurawa zahra ido ko qiftawa bayayi ya tafi duniyar shagala da shauqi da son zahra. Gani yayi tai mai wani irin kyau na musamman, shi tunda yake a rayuwar shi bai ta6a ganin zahra tai mai kyau ba sai yan.

Zahra ji tai sabida kallon da mashkhur yake mata da kyar take tafiya duk tabi ta tsargu da wanan kallon. Amma haka ta daure ta cigaba da tafiya zuciya cike fall da zullumi. 6angaran mashkhur kuwa sai bin zahra da ido yake duk inda tai dan shi yama manta a wace duniyar yake. Zahra tana qarasowa tin daga nesa ta d'an russuna tare da cewa yaya mashkhur ina wani ya hanya ta fad'i hakan fuska d'auke da murmushi.

Nan da nan mashkhur ya sake zaucewa da sauri ya taso zai nufo zahra. Mashkhur ji yayi kamar ya taka wani abu yana dubawa qasa yaga ashe wai wayar shi ce. Mamaki mashkhur ya farayi yana tunanin taya akai wayar tashi ta fad'i qasa bai sani ba. Amma sai ya share ya d'auki a bar sa sanan ya d'ago ya kalli zahra. A lokacin ma zahra har ta miqe ta koma daga can gefe ta zauna akan kujera ta d'an had'e rai kamar dai ba itace ta gama murmushi da ya rud'a mashkhur ba.

Wani gauran nunfashi mashkhur ya saki tare da lumshe ido yana shafa 6angaran zuciyar shi da hannu. Sanan ya nufi kujerar da zahra take zaune, yana qarasawa ya zauna a gefan ta yana cewa zahra ba gaisuwa ti tinda bazaki gai she niba ni zan gai she da ke ina wani?. Mamaki ne ya kama zahra, wato yanzu mashkhur yana nufin bai ji gaisuwar da tai mai ba.

Kai lokaci guda zahra taga mashkhur duk yabi ya zauca kamar wani mai cutar mantuwa. Kai gaskiya matata kinyi kyau sosai, mashkhur ya qarasa maganar yana shafa gefan fuskar zahra. Ture hanunsa zahra tai tare da cewa yaya mashkhur meye haka dan ALLAH ka dena ta6a ni bana

Please Login or Register in order to submit comment