Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mashkhur cewa yayi tab duk yadda akai takaddar nan tana da matuqar amfani.

Maganar dady ce ta katse momy daga fad’an da take tayi, sanan ta dawo da kowa daga tinanin da yatafi. Haba halima mene na fad’a ko bakisan qadda ba eeye? ALLAH ne yasa hakan ta faru kuma duk abindda kikaga ya faru da sanin uban gida, ALLAH yayi ZAHRA bazamu mayar da ITA wajan IYAYANTABA. Ai ba momy ba har mashkhur sai da gabansa ya fad’i rass agigice ya d’ago yana kallan dady da yake cigaba da kora bayani.

Shikuwa abdul yanajin hakan wani farin cike ne ya lulub’e shi tare da furta ALHAMDULILAH, a cikin zuciyar sa.
Yanzu abindda za’a yi tundda mun rasa takaddar addres d’in gidan su zahra, zahra zata cigaba da zama damu har muga abindda ALLAH zai’yi daman zahra ta saba damu muma mun saba da ita kamar ‘yar gidan nan muka d’auketa, kuma nima ina qaunar zahra inason ta kamar ‘yar da na haifa acikina.

Dady nima walli inason ta dan ALLAH karku mayar da ita, cewar abdul, ai yana qaras fad’ar hakan yaji wani gigitaccan mari a kumatun sa. Bakowa bane ya mari abdul face momy, sai wani huci take kamar zaki!! Ashe abdul baka da hankali taya yarinyar da bamusan asalin taba zamu cigaba da zama da ita, wai har wani cewa kake kana son ta koh? Wlh abdul baka gaji halina ba, in banda hauka mai za’a yi da ‘yar sadaka, yarinyar da uwarta tai sadaka da ita a bakin titi.

Ke maryam wai sabida me ke baki da mutunci ne eyee? Tom wlh bari kiji zahra sai ta zauna a gidan nan, ba indda zata, hajiya kakace ta fad’i hakan cikin fad’a, kuma da kike maganar abdul bai kwashi halinki ba ai sai ki godewa ALLAH da bai kwaso mugun halinki ba dan ke baki da wani hali mae kyau sai baqin hali da mugunta, hajiya kaka ta qarasa maganar tana watsawa momy harara. Shiru momy tayi tana mae qarewa hajiya kaka zagi a zuciyar ta.

Ammi kuwa cewa tai dan ALLAH hajiya kiyi haquri ki dena fad’a nan, tundda ba halima ce take ruqe zahra ba ae shikenan kuma ni zan cigaba da rainon zahra insha ALLAH kuma ina qaunar zahra kamar yadda nake son ilham. Mashkhur dai yayi shiru yanajin abindda yake faruwa dan bai yadda da gaske wannan abun yake faruwa ba yafi tunanin a mafarki ne, ladamace ta kamashi da Kuma dana sani akan takaddar da ya yaga kuma yakai aka qona.

Dady ne ya qatse kuwa da cewa! Shikenan komai ya wuce, kuma ke halima mene na tayar da hankalinki tinda bake zaki riqe zahra ba, kuma daga yau sai yau kar na sakeji kin aibata zahra ko kin muzan tata dan itama ‘yace agidan nan. Bayan haka inaso na gargad’e akan abu d’aya, banaso kuwa ya sake cewa zahra ba ‘yar gidan nan bace. Kai babana wato mashkhur da abdul nasan duk yaran gidan nan ba wani mai wayo sai ku, dan faruq da haidar basusan komai akan zahra ba barema rukayya da rumaisa’u

Dan haka kar naji maganar nan tafito duk wandda ya sake ya tayar da maganar nan har yaran gidan nan suka san zahra ba ‘yar gidan nan bace to Wallahi sai ransa ya 6aci, bama iya kuba harda ke halima(momy) dan nasan zaki aikata, 6angaran maryam da hajiya kuwa bani da haufi hakan su dan nasan zasu iya yin shiru da bakin su. Kunjini koh? Insah ALLAH dady zamu kiyaye cewar abdul.

Momy da mashkhur kuwa shiru sukayi kamar ba dasu ake ba. Mai sunan baba bakaji abindda nace bane? Cewar dady” asanyaye mashkhur yace naji dady kuma in sha ALLAH zan kiyaye. Ok ku tashi ku tafi, ba musu mashkhur da abdul suka tashi su ka shige ciki. 6angaran momy kuwa sai da dady yace wai halim bakiji abindda nace bane?. Yamutsa fuska tayi tare da cewa naji ALLAH yasa mukiyaye daga haka tatashi ta fuce daga d’akin ko sallama batayi musuba.

Tofa mashkhur yau ya shiga matsanancin halin da bai ta6a shigaba” kuma duk ba akan komai bane face zaman zahra gidan” mashkhur yayi ladamar yaga takaddar nan dan dayasan addres d’in gidan su zahra ne a ciki da bai yagaba kuma har an qona. Daran ranar dai mashkhur ko banci kirki bai ba sabida tsabar takaici da baqin ciki ga tsanar zahra ta sake nunkuwa a zuciyar sa.

6angaran abdul kuwa hmmm masu karatu ko ban sheda muku irin farin cikin da abdul yake cikiba zaku sheda, dan tundda aka haifi abdul bai ta6a farin cikiba irin yau ba ” dan ko marin da mahifiyar sa momy taimai yama manta sabida tsabar murna, yanzu shikenan zahrata bazata tafi ba zamu cigaba da zama tare da ita” abundda abdul yake ta fad’a kenan.............

-maman xuhra
-nafisat
-twins
-ummu abdul

Ina yimuku godiya da fatan alkhairi, kuma inajin dad’i qarfafamin guiwair da kuke Allah yabar zumunci” muna tare in sha Allah.....

*Game buqatar littafin ADALILINTA har indda muka tsaya sai yayimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira.FREE book ne bana kud’i ba.

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

Typing..........

*page 39*

Yanzu shikenan zahrata bazata tafi ba zamu cigaba da zama tare da ita” abunda abdul yake ta fad’a kenan.

6angaran momy hmmm tashiga baqin ciki sosai dan kuwa!! ba qaramar tsana tayiwa zahra ba. dama dangin momy basu qaji arziki ba, ‘yan gudin hijira ne sam basaso a ra6e su ko a qaru dasu basu gaji mutunci ba, shiyasama momy ta tsani zahra.
6angaran ammi kuwa tayi farin ciki sosai sabida itama bataso ta rabu da zahra dan ta d’auke ta kamar ‘yar ta.

Hajiya kakama taji dad’i hakan dan ba qaramin so takewa zahra ba, amma tana baqin ciki rashin mayarwa da mahifiyar zahra amanar da ta bata, amma ba yadda ta iya haka ALLAH ya tsara.
A ‘yan kwanakin nan mashkhur sam yana cikin damuwa dan sam baya qaunar zahra, yanzu mashkhur baya iya zama a part d’in ammi duk sabida zahra, sai dai ya tafi part d’in momy. Haka momy zatai ta ziga shi akan zahra, dama gashi mashkhur yana jin maganar momy fiye da kowa a duniya.
Abdul kuwa bayajin dad’i tsanar da yayan sa mashkhur yake nunawa zahra amma ba yadda ya iya.....

Bayan shekara biyar.

Bayan shekara biyar, Abubuwa da dama sun faru daka ciki kuwa harda fara zuwan makarantar Zahar da ilham da rukee da kuma ruma. Yanzu suna nursery 3, sun kusan shiga primary 1, duk sunyi wayo sosai. Zahra bata da surutu sosai salient ce, ilham kuwa hmm harma tafi zahra baki surutu ne da ita sosai.
Su rukee da ruma suna san wasa da ‘yar uwansu wato zahra da ilham amma sam momy bata barinsu, har yau bata dae na kulle su a part d’in ta ba.

Sai za’a kai su makaranta ko a makaranta sannan suke samu su kula juna, rukee da ruma suna qaunar su zahra sosai amma kullum burin momy ta rabasu.
Yanzu zahra tsoran mashkhur take sosai dan ko hanya bata bari su had’a, in kuwa suka had’a hanya dukane yake rabasu dan mashkhur kullum cikin zalintar zahra yake, amma mashkhur ya iya takunsa sam baya dukan zahra a gaban kowa, sai yaga daga ita sai shi.

Zahra kuwa sam bata iya gayawa kowa sabida tana tsoran mashkhur kuma gata da haquri, sai dae ta zauna tasha kukan ta ita kadai.
Kuma Abinda yake qara qonawa mashkhur rai game da zahra shine irin mugun son da dady da kuma hajiya kaka suke nuna mata. A da mashkhur yana ganin shi akafi so a cikin gidan amma sai gashi ADALILINTA an dae na nunamai kulawa sosai, sabida haka mashkhur yake yawan dukan zahra kuma yake qara tsanar zahra.

6an gare guda kuwa wata muguwar sahaquwa ce ta shaga tsakanin zahra da abdul, dan har yanzu abdul yana qaunar zahra kuma bai ta6a d’aga hannu ya daketa ba. Gashi kuma duk abinda zahra take so abdul yana mata yana matuqar qaunar ta har ciki ransa, itama zahra tana son yaya abdul d’in ta sosai.

A bangaren momy kuwa tana nan da mugun halinta ba abinda ya chanza sema abinda ya qaru ,dan yanxu babban burinta shine taga bayan hajiya kaka ,kullum qafarta tana hanyar gidan bokaye duk dan taga bayan hjy kaka amma abin yaci tura sabida hajiya kaka bata wasa da addu’oi kuma ga dafa’i a jikinta.Ba komaine yasa momy take son ganin bayan hjy kaka ba face yadda take shigar mata hanci da qudundine,dan yanxu hjy kaka sam bata daga mata qafa tai abinda ranta take so a cikin gidan nan kulamin a cikin tsawatar mata take .

To haka rayuwa tai ta juyawa, dan yanxu mashkhur ma yayi candy 👨‍🎓yana da shekara 17 kenan,shiyasa yake zaune a gida ba indda yake xuwa, ze huta ne a gida na taawan shekara guda fakin takaddun sa su kama futowa .Hakan kuwa yayi matukar taka rawa wajen qara bawa mashkur damar kuntatawa Zahra dan yanzu ko sunan mashkhur aka kira se gaban zara ya fadi,

kai yanxu takai ta kawo duk mutan gidan sun fahimci rashin jituwar da ke tsanin zahra da mashkhur kuma hakan ba qaramin mamaki yake basu ba musamman ma su Haidar kullum suna tunanin dalilin da yasa yaya mashkhur yake takurawa zahra ,alhalin kuma su ba haka yake musu ba. Babban abinci mamakin ma shine su dai asun san zahra da ilham yan biyu ne amma sabida me yake kyarar Zahra amma ita ilham ko kallon banxa baya yi mata oho🤷🏻‍♀️

Sannan kuwa kowa ya sheda soyayyar da take tsakanin Abdul da Zahra dan sometimes ma su faruq suna tsoran taba zahra a gabansa in tai musu laifi,dan ko kollon banxa baya bari qannen nasa suyi mata.

Bayan shekara guda.

Yanzu mashkhur ya takaddun makaramtar sa duk sun futo ya gama hutun gida, dady ya yanke shawarar zai kai shi makarantar share fagen jami’a duk da kuwa mashkhur yana da qoqarin da zai shiga jami’a, abindda yasa dady ya sashi a makaranta share fagen jami’a shine yanaso kafin ya gama ya canzawa mashkhur ra’ayi, ya amince a fitar da shi waje domin yayi karatu mai inganci, shekara biyu zai yi a makaranta share fagen jami’a kafin nan ya cika 20 years, sai ya fara zuwa jami’a.

Yanzu mashkhur shekararshi 18, in ka kalle sa sai ka qara sabida yazama kyakyawan matashi mai nutsuwa, hankali, tinani, ilimi, uwa uba ga kyau. Mashkhur kyakyawane sosai dan duk wandda ya kalle shi sai ya qara, kana ganinsa kaga cikakyan kyakyawan bahaushe. Mashkhur yana da tsayi ma dai dai ci bashi da wani jiki amma fa ba siriri bane a taqaice dai zamu kira shi da ma dai-dai ci, yana da hanci sosai ga manyan idanuwa, sanan yana da gashin gira dana ido, kuma yana da dimple bugu da qari ga tsagun haqora wato (wushirya). Farine amma ba tass ba, dan bashi da haske kamar su abdul.

Kana ganin mashkhur zaka sheda ammi ce ta haifeshi sabida tsananin kamar da suke. Yanzu mashkhur ya fara zuwa makarantar share fagen jami’a kuma yana karatu sosai.
Shima Abdul kyakyawan sosai, yana da hanci amma shi ancin sa siririne kuma yana da ido amma bai kai mashkhur ba, sanan yana da dimple, gashi fari ne tass, ga sumar kansa a kwance lif, abinka da d’an filani, kuma bashi da jiki zaka iya kiransa da siriri amma fa ba siriri bane sosai, abdul kamarsu d’aya da dady.

Wasuma in sukaga abdul sai su rantse d’an ammi ne sabida tsananin kamar da suke da haidar da kuma faruq.
Zahar kuwa kyakyawace sosai dan in ka ganta sai ka rantse balarabiya ce, idonunta ma dai-dai ta hancintama ma dai-dai cine, gata da saje kuma ga gashi har baya zahra farace qall dan har wani ja take, kuma zahra tana da diri sosai dan sam bata ciki jerin sirara, ma dai-dai ciyace.

Ilhma kuma ruwa biyo ce tana kama da mashkhur sanan tana kama dasu abdul. Rukee kamar ta d’aya da maman ta wato momy, ita kuma ruma ruwa biyu ce itama tana kama da momy kuma tana kama da dady. Wannan kenan.
Zahra tana qoqari sosai a makaranta dan tana d’au kar ta d’aya ko ta biyu, in tayi rashin qoqari shenema take d’aukar ta hudu, zahra tana da qoqari.

Ilham kuwa tana d’aukar ta hudu ko ta biyar, duk suna da qoqari ba laifi.
Yanzu zahra tana samun sakewa a gidan sabida mashkhur baya nan wataran ma sai magriba yake dawowa. Hajiya kaka tana tsananin son zahra dan haka zahra take shagwabar ta iya son ranta, dan yanzu zahra ma ta koma wajan hajiya kaka da kwana, kullum tana maqale da ita. Itama ilham ba yadda ta iya haka zabiyo zahra sabida sam sun saba da junansu kamar wasu ‘yan biyo, in kuwa d’aya daga cikin su bata da lafiya tare suke jinya.

Tom haka rayuwa tai ta juyawa kuma lokuta suna shud’ewa.

Bayan shekara biyu.

Alokacin mashkhur ya gama makaranta share fagen jami’a, yanzu mashkhur shekararsa 20 years, a duniya ya zama saurayi. Abdul kuwa yana da shekara 17 years, dan shima yanzu yayi condy. Faruq yana da shekara 13 years, haidar kuma yana da shekara 12years, zahra da ilham suna da shekara 10 a duniya, rukee kuma 11 years, ruma kuma tana da shekara 9 years da wata bakwai, takusan ta cika shekar goma, dama su zahra wata biyar suka bawa ruma. Tofa a lokacin ne ammi ta haifo santalelen yaron ta namiji kyakyawa, tubarakallah mashkhur ALLAH.

Yarofa kamarsu d’aya da mashkhur, dan haka yau fa yaro ya shiga lis d’in kyawawan gidan, dama yaran gidan sun chanfa kyawawan gidan, mashkhur,abdul zahra, sune sukafi kowa kyau, inji iyalan ALHAJI ABUBAKAR . Haka zasu zauna suna ta za6ar wandda yafi wani kyau a cikin su ukun nan mashkhur, abdul, zahra.
To ranar suna yaro yaci sunan sa Abdullahi kuma ana yimai kara da ameer . Ansha suna anci ansha har da masu guziri, yaran gidan kuwa sai farin ciki suke han haifa musu baby.........

Dan ALLAH kuyi haquri da wanan shima da kyar na rubuta dan banjin dad’i ina roqan addu’ar ku🙏🏼, kuma inayi muku fatan alkhairi....

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

Typing.....

*page 40*

To ranar suna yaro yaci sunan sa Abdullahi kuma ana yimai kara da ameer. Ansha suna, anci ansha harma da masu guziri, yaran gida kuwa sai farin ciki suke an haifa musu baby...........

Bayan suna da sati d’aya dady ya samu mashkhur da maganar cigaba da karatun sa. Dady ba yadda bae yi da mashkhur akan ya fita waje ya cigaba da karatu ba amma sam mashkhur yaqi” ba yadda dady ya iya haka ya haqura. Mashkhur yaro ne mae taurin kai sam in baya son abu tofa bazai so shi ba komai kyan abun kuwa. Sam mashkhur baya ra’ayin fita wata qasar karatu, yafiso kullum ya ringa ganin ammin sa da ‘yan uwansa sabida yana qaunar ammi sosai.

Momy ma sosai take ziga mashkhur akan karya amince da fita wajan, dama mashkhur bashi da ra’ayin haka sannan ga kuma zigar momy, hmm kunsan dae yadda mashkhur yake jin maganar momy fiye da kowa a duniya. Bakomai ne yasa momy take ziga mashkhur akan karya fita waje karatu ba illah sam bataso d’an ammi yafi nata kuma in masu karatu bazaku manta ba momy tana da qudirin daukar fansa akan mashkhur kuma duk ba’a kan komai momy take son daukar fansa ba face, yadda ammi ta kwace mata abdul.

Dan yanzu abdul yafi son ammi akan momy, momy kuwa tana baqin ciki da hakan, gashi har yanzu bata qara samun wani namijin ba, kulluma tana tinanin shikenan yanzu ammi ta had’a maza har hudu kuma gashi ta had’a mata da abdul sun cika har su biyar. Hakan ba qaramin qonawa momy rai yake ba, shiyasama bata bari su rukee su ringa zuwa wajan ammi sosai, amma yanzu abin yayi sauqi tundda su ruma suna shiga part din ammi su zauna.

Shima ba’a son ranta bane sabida dady yayi mata fada sosai yace tanaso ta raba mai kan ‘yaya. Amma duk da haka sai da momy ta raba su rukee da zahra dan ko kallan arziki basa mata, gwarama ruma wataran in ta faki idon rukee da momy tana yiwa zahra magana. Zahra tana mamakin hakan sosai sabida taga rukee tana kula ilham amma ita ko kallanta batayi, inma banda hantara da zagi, ba abindda take mata.

Suma su rukee suna mamakin dalilin da yasa momy take hana su kula zahra ita kadai a gidan, kuma bayan sun san ammi ce ta haife ta. Sometimes rukee da ruma suna tambayar momy mai yasa take cewa karsu kula zahra, ita kadai? Ko da akwai wani laifin da zahra tayi mata ne? Haka momy zatai tai musu Kama-kame.

Momy tana so ta gayawa su rukee gaskiyar zance amma ta kasa sabida tasan in ta gaya musu zancan zai iya komawa kunnan dady, kuma tasan yadda dady yake qaunar zahra yana jin maganar nan sai ya saketa, kuma gashi momy ta saba da zaman hutu da kud’i dan ba qaramin dad’i da hutu take samu a gidan dady ba. Tom yanzu mashkhur ya fara zuwa B U K bayero university kano, ya mayar da hankali sosai yana karatu.

Yanzu dady ya gina tanfatsetsan gida, gida na al farma dan ko kayan gina gidan ma daka waje aka shigo da su. Sabida yanzu dady ya zama attajirin mai kud’i, dan yanzu kana cewa ALHAJI ABUBAKAR DALA, a garin kano ko kaduna an san shi, bama iya kano da kaduna ba harma da sauran state da dama.
Tom yau iyalan alhaji abubakr sun tare a katafaran gidan su, hmm aljannar duniya kenan ae koni amina bayero danaga gidan nan sai da na dalalar da yawu, sabida tsabar tsaruwa.

Hmmm kud’i fa yayi kuka da idan sa, kai iya kacin unguwarma sai wandda ya isa da ‘yayan wance da wane ne suke zaune a unguwar. Part d’in ammi da ban na momy ma daban na hjy kaka da ban na dady ma daban kai harma su mashkhur wato mazan gidan an ware musu part d’in su, kuma ko wane part da bene a ciki. Su zahra ma an ware musu d’akida da bedroom a part d’in hjy kaka.

Zahra da ilham da kuma rukee da ruma dady yace su koma part d’in hajiya kaka su zauna a d’akin su, amma sam momy tace itafa ‘yayan ta bazasuba suan tare da ita, sabida gudin rigima dady ya rabu da ita. zahra da ilham kuwa suka koma d’akin su, kullum hajiya kaka tana numa musu kulawa da qauna.

6angaran jariri ammi kuwa ya fara wayo da giram, zahra kuwa tana qaunar ameer sosai da sosai, kamar ita ammi ta haifawa, kullum in zahra tana gida kuwa tana maqale da ameer.
Zahra tana samun kulawa sosai a agidan nan, dan har yanzu zahra batasan ita ba ‘yar gidan bace! Amma abindda yake damun zahra shine tsanar da mashkhur yake nuna mata da yawan kyara da kuma duka, sanna ga gabar da rukee da ruma sukeyi da ita alhalin tasan ba abindda tayi musu.......

Bayan shekara uku....

Abubuwa da yawa sun faru da marasa dad’i da masu dad’i. Yanzu ameer shekararshi uku, yaro yayi wayo ya girma, yayi kyau abinsa yayi 6ul-6ul. Ameer ya saba da zahra sosai sabida itace uwar rainon sa, yanzu duk yaran gidan nan ameer yafi shaquwa da zahra, yana matuqar qaunar zahra itama zahra tana son ameer. Yanzu sabida tsabar sabon da ameer yayi da zahra a kusa da ita yake kwana, yanzu ko makaranta zahra ta tafi kuka yake tayi, hakan ne yasa akasa ameer shima a makarantar su zahra.

Ko yaje makarantar ma kuka yake har sai an kowo shi ajin su ilham wajan zahra.
6angaran mashkhur kuwa yana qoqari sosai, shi yake daukar first class a ajin su kuma gashi course d’in computer da maths yake karanta. Yanzu ma yana lavel 3 saura shekara d’aya ya fita daga b u k d’in, uhuuum koni amina bayero na jinjinawa qoqari irin na mashkhur ✊🏼
Tom yanzu mashkhur yana gida a zaune kullum yana cikin karatu sakamakwan hoton da aka basu.

Yau ranar wata asabar ce ranar da zahra bazata ta6a MANTAWA da ita a RAYUWARTA ba, ranar da mashkhur bazai taba MANTAWA da itaba a RAYUWARSA ba. Kai bama iya zahra da mashkhur ba hatta sauran mutan gidan bazasu manta da ranar nan ba. Tom masu karatun littafin ADALILINTA nasan zaku so jin mai ya faru a wannan ranar asabar d’in, tom ku biyoni domin kuji mai ya faru.

Faruq, haidar zahra, ilham, rukee ruma duk sun tafi makarantar tafiz, dady, ammi, hajiya kaka, momy harma da ameer auta sun tafi gaisuwar mutuwar kawun hajiya kaka a kaduna tun da safe. Abdul kuwa yana bayan layin su suna ball shida abokan sa da sauran ‘yan layi.
Mashkhur kuwa yana gida shi ka dai yana karatun da ya saba. Aalokacin mashkhur shekarar sa 23 years zahra kuma tana ‘yar shekara 13 yers Alokacin zahra tana j.s 2.

Zahra tunda safe da sukaje makaranta takejin ckinta da mararta yana mata ciwo tundda sukaje ta kasacin komai.
misalin qarfe hudu da rabi 4:30 pm aka taso da su zahra daga makaranta, alokacin ma zahra ta gama jigata sabida tsabar azabar ciwo, ana tashi rukee taja ruma sukayi gaba, ruma taso ta tsaya su tawo da zahra tindda bata da lafiya amma rukee tace wlh in dai ta tsaya sai ta gayawa momy, hakan ne yasa ruma ta haqura.

Haka zahra ta riqe ilham suka cigaba da tafiya a hankula, da yake makaranta bata da nisa da gida. Mashkhur kuwa yana gida ya futo daga part d’in su ya dawo part d’in ammi, ya zaune a kujera yana danna laptop d’in sa, yana cikin danna laptop d’insa yaga battery yayi low hakan ne yasa yasa a charger sanna ya dorata akan hanun kujera. bayan ya jona laptop din a charger kicin ya nufa domin zubo abinci yaci.

Shigar mashkhur ke da wuya su zahra suka shigo, ilham riqe da zahra, zahra kuwa sai nishi take sabida ta jigata. Ilham ce tace zahra zauna anan bari naje firic na daukko miki ruwa, kisha d’aga kai zahra tayi alamun Tom. Da kyar zahra ta samu ta iya cire hijab d’in ta, ta nufi kujera ko gabanta bata gani. Tana isa wajan kujerar cikin rashin sani ta zauna a hannun kujera 😲wato akan LAPTOP d’in MASHKHUR😱. Zahra ji tai kamar ta zauna akan abun a hanzarce ta miqe domin ganin menene?

Ai kuwa tana miqewa laptop d’in mashkhur ta zame qasa ji kake tass. Ai kuwa karaf a kan idon mashkhur da ya futo riqe da flat d’in abinci a hanunsa yasalam, ba zahra ba har ilham wanda hanunta ke ruqe da ruwan faro sai da ta saki ruwan sabida tsabar fargaba. 6angaran zahra kuwa tuni ta nemi ciwon da takeji ta rasa tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskar ta, gumi har ya fara tsa-tsa fo mata.

6angaran oga mashkhur kuwa wani wawan kallo yake bin zahra da shi, cikin tsanann 6acin rai, ai kuwa a dai-dai lokacin faruq da haidar harma da su rukee da ruma suka shigo saka makwan part d’in momy a kulle yake.
Ji kake tasssss, mashkhur ne ya saki flat d’in hanunsa qasa tare da yin kokan kura ya nufi zahra............

Very sorry my fans.......🙏🏼
Dan ALLAH kuyi haquri jiya da yau

Please Login or Register in order to submit comment