Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajan suka saki dariya harda mashkhur wanda ya kifa kansa a guiwa.  Daga haka akayi fara kiran sallah,  ba 6ata lokaci dady da mashkhur harda Ahmad da abdul suka d'aura alwala suka wuce masallaci,  sukuma ilham da zahra kwashe kwanikan abinci suka farayi, bayan sun gama  a hanzarce suka share wajan suna gama share wajan,  suka shige bedroom d'in zahra suma suka d'auro alwala sanan suka gabatar da sallahr magriba..............

Mu had'u a next page.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

my number 09162226240

                                    *page 68*
        
                                Typing..........

Daga haka akayi fara kiran sallah,  ba 6ata lokaci dady da mashkhur harda Ahmad da abdul suka d'aura alwala suka wuce masallaci,  sukuma ilham da zahra kwashe kwanikan abinci suka farayi, bayan sun gama  a hanzarce suka share wajan suna gama share wajan,  suka shige bedroom d'in zahra suma suka d'auro alwala sanan suka gabatar da sallahr magriba..............

Su dady kuwa sai da sukayi sallar isha'i sanan suka dawo lokacin da suka dawo ba ahmad suka shigo shi ya wuce part d'in shi.  Nan ma wata sabuwar hirar haka  zauna aka qara dasawa kai basu sukaje suka kwanta ba sai waja 12:00 na dare.  Zahra ta kwanta a gefan dama a bed  ita kuma ilham ta kwanta a gefan hagu shi kuma amir ya kwanta a tsakiyar su.  Suna kwanciya ilham tace yauwa zahra ai kinga yanzu mun samu lokaci koh?  Ki gayamin abinda kikace zaki gayamin,  murmushi zahra tai tare da cewa!  Haba ilham yanzu fa dare yayi karmu kasa tashi gobe ki bari sai gobe zan gaya miki.

Kai zahra wlh kina jamin rai,  aa  wlh kawai bacci nakeji shi yasa dare yayi,  kinsan yanzu na saba kwanciya da wuri tinda ni ka d'ai ce,  okay shi yaya mashkhur d'in ba mutum bane zakice ke ka d'ai ce?  Hmm Ilham kenan in ana sallah ba'a magana,  baki fahimci abinda nake nufi ba, good night kawai,  daga haka ba wanda ya sake cewa komai har bacci yayi awan gaba da su.......

Kiran sallah asubar fari ne ya tashi zahra da yake ta saba tashi da kanta tinda tazo rasha. Miqewa tai ta sauko daga bed d'in,  sanan ta canza glob d'in d'akin  daga blue  zuwa white, tana gama canzawa ta fara tashi ilham,  Ilham!  Ilham!  Tashi muyi sallah,  cikin mungagin bacci Ilham tace kai zahra har asuba tayi yaushe muna kwanta,  bansani ba wlh ko ki tashi ko na watsa miki ruwa a jikin ki,  Ilham tana qarasa jin haka tai sauri ta miqe tare da bud'e idon ta tangararai,  kai zahra amma kin iya mugunta yanzu sai ki watsamin ruwa?  Dariya zahra tai tare da cewa!  Sawasa wlh in baki tashi ba ruwa zan watsa miki dan bazan iya ganin sallah ta wuce ki ba.

Miqewa ilham tai tare da cewa ai ba haka ake tashin mutune ba ke haka ammi take tashin mu,  oh ai ke nauyin bacci ne da ke shiyasa,  daga haka zahra ta wuce toilet,  ilham ma takalmi ta zura ta wice cike toilet d'in,  zahra tana cikin fitsari taga ilham ta fad'o toilet d'in kamar wata aljana.  Kai ilham wai ke har yanzu bazaki girma ba basai ki bari na futoba tukunna,  ta6e baki ilham tai tare da cewa au da gaske lalai zahra kin girma aure ya kar6e ki,  ai ni ko wanka kike ba fitsariba sai na shigo toilet d'in nan kinjima na gaya miki.  Kai ilham mai ya kawo kuma zancan aure zahra ta fad'a kamar tazai kuka,  murmushi ilham tai tare da cewa ai nayi tinanin abinda kake nufi kenan,  da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa nifa ba haka nake nufi ba.

Tom shikenan gwara da kika fahimtar dani ai,  daga haka zahra ta fara alwala ita kuma ilham tai fara kama ruwa bayan ta gama itama tayi alwala,  a tare suka futo daga toilet d'in,  lokacin da suka futo suna jin qarar fitar su dady masallaci,  Ilham ce ta kalli zahra tare da cewa!  Masallacin bashi da nisa ne daga gidan nan?  Naji duk sanda akayi kiran sallah kamar a gidan nan akeyi,  hanyar wardrobe  zahra ta nufa tare da cewa ehh inaga gaskiya a bayan gidan nan yake sabida nima ban ta6a ganin saba,  jinjina kai Ilham tai tare da cewa!  Ai ni duk a tinani na ba masallaci qasar nan.

Dariya zahra tai tare da cewa kai ilham gaskiya baki da dama taya za'a rasa masallaci a qasar nan kuwa?  Sai kace ba musulmai,  murmushi ilham tai sanan tace to ai naga garin arna sunfi yawa musulman kad'an ne shiyasa,  ehh mana arna sunfi yawa shiyasa ma ba ko ina aka fiya samun masallaci a wajan ba kinga nan unguwar musulmai ce, daga haka zahra ta zaro dadduma da hijaban ta guda biyu na sallah,  tana zuwa ta miqawa ilham hijab d'aya itama ta zira d'aya sanan ta shin fid'a musu daddumar suka fara gabatar da sallahr.  Bayan sun idar sun gama lazumin sallah,  azkar d'in safiya sukayi  sanan suka koma kan bed.

Zahra tana hawa ta rufawa amir bargo da yake lokacin da suka tashi sun yaye mai bargwan daga jikin sa kuma ga sanyi asuba da akeyi dama garin gashi kwanin sanyi.  Yauwa zahra inajin ki mai zaki fad'a min?  Ilham ta watsowa zahra tambayar,  kai ilham ki bari sai gari ya gama wayewa mana,  da sauri ilham ta miqe tare da cewa aa wlh baki isaba,  tun yaushe kike jamin rai?  Nifa banajin wani bacci sanin kanki ne in muka tashi ba mu fiya komawa bacci asuba ba,  koke yanzu kina komawa ne? Ilham  Tana qarasa fad'in hakan ta zauna a kusa da zahra,  girgiza kai zahra tai tare da cewa nima ai bana komawa bacci sabida school qarfe bakwai fa akevshiga sai dai in weekend,  shine nake komawa baccin.

Yauwa to yauma bazaki koma ba hira zamiyi,  murmushi zahra tai tare da juyowa suna face d'in juna ita da ilham d'in,  ilham kin san mene?  Da sauri ilham tace aa, sai kin fad'a,  hmm Ilham wlh harna fara tsoran gaya miki ma,  harara ilham ta d'an watsawa zahra tare da cewa tsoro kuma ni dodan kice ko kuwa?  Girgiza kai zahra tai tare da cewa aa ina nufin bansan yadda zaki d'auki lamarin bane.  Ah zahra in sha ALLAH zan d'auke shi yarda kike so na d'auka gayamin kinji ' yar uwata ilham har wani lanqwashe murya take sabida tana san taji,  dan tureta zahra tai tare da cewa!  Kijifa sai kace da gaske,  murmushi ilham sanan tace da gasken ne mana.

Gyara zama zahra tai tare da cewa!  Ilham kin san mene?  Aa sai kin gayamin,  ilham wlh wani ne yake mugun son ki yau wajan!!  Da sauri ilham ta katse zahra da cewa kai sona kuma wanene hakan ta fad'a cikin tsawa.  Ban sani ba bazan qarasa gaya miki zancan ba,  zahra ta fad'i hakan tana niyar kwanciya,  da sauri ilham ta ruqo ta tare da cewa! Ya haquri dan ALLAH,  ki cigaba da gayamin,  to taya zan gaya miki ki isheni da bala'i girgiza kai ilham tai tare dace wlh bazan isheki da bala'i ba kawai ki gayamin waye haka yake sona?. YAYA AHMAD ne yake SON ki,  wani irin zabura ilham tai tare da dafe qirjin ta tana cewa!  yaya Ahmad kuwa?.

Gyad'a kai zahra tai alamun ehh,  abokin yaya mashkhur dai wanda yazo jiya mukaci abinci?.  Ehh shi fah  cewar zahra,  nan da nan ilham ta had'e rai sosai tare da cewa! To wlh bai isa ba shi harma ya isa yace yana sona shi bai san ba'acewa ana sona ba koh?  To kije kice masa bana san shi bana qaunar shi.  Itama zahra ciki fad'a tace to karki so shi ai ba dole akayi miki ba,  da kike cewa ba'a cewa ana sonki haka zaki zauna koh?  Bazaki aure ba kenan.  Harara ilham ta watsa mata tare da cewa da yake auran na isa koh ki bari kiga na isa auran mana.

To in ba'a saba cewa ana sanki ba taya zaki iya auran? Cewar zahra,  turo baki ilham tai tare da cewa ki bari lokacin yazo ai zaki gani,  amma wlh ya qara cewa yana sona sai na yimin rashin mutunci da bazai manta da shi ba.  To shikenan zan gaya mishi bakya son shi shikenan?  Amma karki qara fad'ar wata kalmar da bata dace ba akan yaya Ahmad ,  murgud'a baki ilham tai tare da cewa gwara dai tun wuri ki gayamai ah to.  Shiru zahra tai tare da rafka uwaban  tagumi tana kallon ilham,  a zuciyar zahra tana cewa!  Lalai ilham kukan dad'i ma kike ke harma kina da bakin cewa bakya son wanan.

Ilham kuwa da taga zahra tayi tagumi zuba mata ido tai dan san gano mai yake damunta,  dan dai tasan ba akan maganar ahmad ce take tagumin nan ba wani abin ne na daban,  shiru ilham tai ta zubawa zahra ido tana son gano mai ke damunta.  Hannu Ilham tasa ta janye wa zahra hanunta daga tagumin da tai tare da cewa,  ke mai yake damun kine ko tinanin yaya mashkhur kike yau baku sha soyayya ba wai ke tantabara uwar aure koh?,  ajiyar zuciya zahra tai tare da cewa ilham kenan ina mamakin yarda lokacin guda kika manta da qiyayyar da take tsakanina da yaya mashkhur.






Haba zahra ai duk wata qiyayyar da take tsakanin ki da yaya mashkhur,  dole ta qare tinda har hanyi aure, ke gayamin ya first night d'in ki da yaya mashkhur ya kance,  bani na sha ilham ta qarasa  maganar tana sakin murmushi. Zaro ido zahra tai tare da dafa qirjinta tana cewa first night fa kikace ilham.  Murmushi ilham tai tare da cewa ke zahra karki min qarya fa,  harfa ALLAH- ALLAH nake nazo naji labarin ya first night d'in ki ya kasan ce da yaya mashkhur. 

Ilham ban ta6a tinanin baki da hankali ba sai yau first night fa kikace ke kinsan mai ake nufi da hakan ma?   Ilham tai tare da cewa!  Eh gani daqiqiya bansan mai ne first night ba koh?  Ai ko amir yasan fassarar first night bare ni,  to bari na yi miki gwari-gwari ina nufin daran farkon ki  da yaya mashkhur,  ya ta Maya ta qarasa magar tana sakin murmushi mugunta.  Tsaki zahra taja tare da cewa! Ai ni ba cewa nai baki san fassarar first night ba,  ina nufin anya kin ma san mai akeyi a first night ne da kike min irin wanna tambayar?.

Taya zan sani tinda ba aure akayimmin ba,  Oh nifa bana san kama-kame  yanzu kins so kice harda ni baza ki gayawa me ya faru a first night d'in ki ba?  ko dan kinga kin rigani aure ne kinga bani da aure ai a zato na ko zaki 6oyewa kowa banda ni ilham ta fad'a tana had'e rai alamun taji haushi.  Zahra kuwa uban ta gumi ta rafka tana bin ilham da ido yanzu gani take ilham tafi qarfin kanta,  au shiruma kika yimin kenan?  Cewar ilham rai a bace.  D'agowa zahra tai tare da cewa to ilham mai zan ce miki?,  ban sani ba ilham ta fad'a,  kamar zahra zatai kuka tace ilham wai kin manta qiyayyar da take tsakanina da yaya mashkhur ne?,  girgiza kai Ilham tare da cewa ban manta ba zahra amma ai dole ya sauke makaman yaqinsa tunda an riga da anyi muku aure harkun tafi gari d'aya kuna zaune a gida d'aya.

Murmushi takaici zahra tai tare da cewa ilham kenan ke iya tinanin ke koh?  To bari kiji yaya mashkhur ya qara tsanar da yayaimin fiye data da ma,  dan ni ka dai nasan halin da nake ciki a gidan nan,  zaro ido ilham tare da cewa yanzu zahra kina nufi har yanzu yaya mashkhur yana gaba da ke,   Kuma baya kulaki, bakwa wata ma'amala ta aure?.  Gyad'a kai zahra tai tare da cewa kwar ilham,  tab yanzu kuma haka kuke zama baya baki haqqin ki na aure?  Tsaki zahra tai tare da cewa!  Ke kika damu da wanan ni bama shine a gabana ba,  ko zai yimin ma ba yarda zan ba bare ma ko kallo ban ishe shiba ta wanan fanin,  dan har gwara namiji ma zai kallesa akai na in dai a wajan yaya mashkhur ne.

Kai zahra yanzu sai ki cemin baki damu da hakan ba,  nifa zahra nasan koke wace,  tabbas daga ni har ke ba wanda zai bigi qirji yace zai iya rayuwa ba tare da namiji ba,  girgiza kai zahra tai tare da cewa!  Wlh ilham ni bana damuwa da hakan,  sabida ban saba da hakan ba,  ni tsoro ma hakan yake bani,  kuma ko zan iya hakan da kowa bazan ta6a iya hakan da yaya mashkhur  ba,  bare ma shi naga alamun hakan ma bai dame shiba,  ke koma ya dame shi bazai ta6ayi da niba ninasan da hakan,  Nifa ilham ni duk yanzu ba wanan ne a gaba na ba kawai burina yaya mashkhur ya dai na azaftar da ni.

Da sauri ilham ta bud'e baki tare da cewa azaftarwa kuma? Zahra dama yaya mashkhur yana azaftar da ke?  Girgiza kai zahra tai tare da cewa ilham karki damu da sai kinji azaftarwar da yaya mashkhur yake yimin kawai ki bar maganar nan haka zahra ta qarasa maganar tana zubar da kwalla,  kafin ilham ta qara yin wata magar zahra ta silale ta kwata a bed d'in.   Itama ilham d'in kwantawa tai a bayan zahra ta rungume ta ta baya tare da cewa! Zahra baki da 'yar uwar data fini  duk aduniya nima haka,  dan haka dole ki gayamin abinda yake damunki ko zan iya samar miki mafuta.  Murya qasa-qasa zahra tace aa ilham ni na d'aukarwa kai na alqawarin zan shinye komai har a bada bazan ta6a gayawa kowa ba.

Itama ilham d'in  hawaye suka fara zubo mata sabida tausayin 'yar uwata ta,  cikin muryar kuka ilham tace qarya kike zahra baki isa kice kin kai level d'in da zaki ringa 6oye min abinda yake damun kiba,  duk duniya bamu da 'yan uwanda suka wuce junan mu,  muna sanar da junan mu sirrin mu,  sanan muyi maganinsa a tsakanin mu ba wanda ya sani,  amma yanzu zahra zaki fara 6oyemin abinda yake damun ki,  kawai dan munyi nesa da juna na wasu lokutan,  ki sani in kikayi hakan tofah zaki fara rusa amincin da yake tsakanina da ke,  mufa 'yan uwan junane kuma aminan juna,  qawayan juna,  kuma mu abokan sirrin junan mune,  muyi fad'a muyi shiri amma zahra kece zakimin haka in kika yimin hakan kamar kin ci amana tane kuma bazan ta6a mantawa da hakan ba ilham ta qarasa magana tana zubar da hawaye.

Juyowa zahra tayi suka fara face d'in juna da ilham,  nan da nan kuka ya kwacewa zahra,  da sauri ilham ta jawota jikinta daga kwance suka rungume junan su, nan da nan ilham ta fara rarashin zahra da bata baki har sai da zahra tayi shiru.  Murya a sanyaye Ilham tace pls zahra ki gayamin mai yake damunki kinji,  ajiyar zuciya zahra tai itama cikim sanyayiyar murya tace ilham zan gaya miki,  amma fa banaso ki gayawa su ammi da dady kawai dai amanace a tsakanin mu kinji,  da sauri ilham ta gyad'a kai tare da cewa in sha ALLAH zahra zan riqe miki amana ba wanda zai ji daga ni sai ke sai ALLAH kuma.

Ajiyar zuciyar zahra ta sauke tare da cewa! Ilham tinda nazo rasha ban qara samu kwanciyar hankali ba,  tin da yaya mashkhur ya dawo daga kai ku airport na fara ganin tashin hankali,  ranar sai da ya kulle a toilet na wani baci ba sha ba sallah, sai daga qarshe ya bud'e ni.  Ke tindaga ranar ko motsi nai wanda yaya mashkhur bai yarda da shiba sai ya sani punishment,  har sai dana kwan mace gwara ya riga dukana ni da muguntar da yake min,  dan ko banyi laifiba punishment yake bani.  da a kwai wata rana wai dan na kunna  tv ina kallo  ya kulleni a taga da igi ya bud'e tagar kuma ga garin da sanyi sosai,  har sai da nayi wajan awa koma a tsaye,  murada da cuwan kai da zazza6i suka rufe ni,  jikina duk ba kwari,  lokacin da ya kwance ni haka na fad'i a qasa sabida banajin dad'in jikina.

Yana gani na fad'i bai tare niba,  har sai dana fasa kai da baki,  kuma washe gari budurwarsa ZEE tazo tasani girki iri-iri kamar dai zan mutu haka nayi mata.  Haka na rinva cuta kamr zan mutu, daga qarshe sai da yaya Ahmad ya kai ni asibiti akamin qarin ruwa aka bani magani.  Cikin  mamaki ilham  tace budurwarsa kuma,  dama yaya mashkhur yana da budurwa.  Gyada kai  zahra tai nan da nan ta fara bawa ilham labarin zee da kuma yarda take lalata mashkhur har take kawo mai kayan shaye-shaye har yadda suke azabtar da ita duk sai da zahra ta  kwashe ta gayawa Ilham.  Ilham kuwa kuka ta saki sabida mugun tausayi da zahra ta bata,  kuma ga baqin cikin shaye-shayen da taji yaya mashkhur yanayi hankalinta ya tashi sosai.

Rarrashin Ilham zahra ta farayi har sai da tayi shiru,  cikin muryar kuka ilham tace yanzu zahra  har yanzu yaya mashkhur yana shaye-shayen?  Ehh maba ilham har gobe d'azuma ina ganin lokacim daya kwashe magugunan shaye-shaye a firj. Sabida kar dady ya gani,  cikin mamaki ilham tace au wai su dady basu san yaya mashkhur yana shaye-shaye ba kenan?  Aa sun sani mana iya mune kawai basu sani ba,  nima sai da nazo na fahimci hakan,  amma kema inaso hakan ya zama amana a tsakanin mu ko haidar da faruq karki gayawa kinji. In sha ALLAH zahra bazan gayawa kowa ba dagani sai ke wanan maganar,  kuma karki damu in sha ALLAH  ko kallan banza yaya mashkhur ya dena yi miki,  dan zan gaya miki yadda zakiyi maganinsa shida wanan shegiyar budurwar tashi.

Zaro ido zahra tai tare da cewa!  Tayaya ilham wlh bazan iya ba,  ina jin tsoran yaya mashkhur sosai da sosai,  daga shi har budurwar bazan iya yi musu komai ba,  tsaki Ilham taja tare dace ke dai zahra kin fiya tsoro wlh ya zama dole ki cire wannan tsoran da raunin naki kafin ki fara hukunta yaya mashkhur da budurwar shi.  Ke wlh in kika bi shawarar da zan baki duk duniya sai yaya mashkhur yaji ba wanda yake so sama da ke bazai ta6a iya rayuwa babu ke ba.  

Tofa jannert anzo wajan 😂 so zai wa mashkhur faka-faka.

Zaro ido zahra tai tare da cewa!  Ke ilham rufamin asiri ai ni bana soma ya sone nafi so ya sake ni,  dama ranar nan yacemin muna komawa Nigeria zai min saki uku bazai cigaba da zama da ni a matsayin mata ba.

Zaro ido ilham tai tare da cewa saki kuma haba zahra, yanzu mai ne amfanin saki,  in ya sakeki wa zaki aura qaramace ke fa sosai da sosai bai kamata ma ki futo daga gidan aure ba kinya qanqanta da zawarci.  Ilham kenan ai bazan ta6a iya ci gaba da zama da yaya mashkhur a matsayin mijiba kamar shima yarda bazai iya ci gaba da zama da niba a matsayin matar sa,  duk fa bama san junan mu,  zaman aure bazai ta6a yuwuwa a tsakanin muba,  in ya sake ni yaya ABDUL zan AURA ni wlh shi nake SO,  what zahra kina cikin hayyacin ki kuwa,  kina da aure kike cewa kina son qanin Mijinki?  Kamar zahra ta zai kuka tace!  Eh mana ilham ai gaskiya na gaya miki kuma ai ba' a gaba kowa na fad'a ba,  ke kawai na gayawa. 

Girgiza kai ilham tai tare da cewa!  Tab ki sauri istigfari ai in ba'a gaba kowa kika fad'a ba a gaba ALLAH kika fad'a haba zahra sai kace bakije islamiyya ba? Kin san dai ba kyau mace tana da aure tana tinanin wani ko tana san shi,  ba kayau.  Hakane ilham,  ALLAH na tuba amma ni nasan dole yaya mashkhur ya sake ni,  sabida qiyayyar da take tsakanin mu tayi yawa wlh,  hakane zahra amma ai in yaya mashkhur ya fara sonki ai zaki so shi koh?,  shiru zahra tai tana nazirin maganar ilham,  can kuma tace gaskiya ilham bazan ta6a son yaya mashkhur ba,  tunfa ina yarinya qarama  tsanar shi ta shi zuciyata kin ga kuwa ba ta yarda zan so shi.

Gaskiya zahra da zaku fahimci junan ku ke da yaya mashkhur da kwa kunji dad'in ku sabida wlh kun dace sosai,  yaya mashkhur ya cika namiji kyakyawa mai ilimi matsalar shi guda shaye-shaye nan,  kema kin cika mace mai kyau ga diri ga ilmi ga  addini ga haquri wlh zahra duk namijin daya aureki na muddin rayuwarsa ya dace.  Ajiyar zuciyar zahra tai tare da cewa hmm ilham kenan ki dena tinanin zamu iya rayuwar aure da yaya  mashkhur,  kamar fa wuta ne da audiga fah a had'a su waje guda ai kinga baza a zauna lpy ba koh?.  Murmushi ilham tai tare da ce ke dai bari zahra ai zan baki course d'in da wlh yaya mashkhur sai ya soki,  in ba'a yi wasa bama to fah da JARIRINKI zaki dawo Nigeria ko da tsowan CIKI...............


Mu had'u a next page


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                                    Typing............

                                    *page 69*

Ajiyar zuciyar zahra tai tare da cewa hmm ilham kenne  ki dena tinanin zamu iya rayuwar aure da yaya  mashkhur,  kamar fa wuta ne da audiga fah a had'a su waje guda ai kinga baza a zauna lpy ba koh?.  Murmushi ilham tai tare da ce ke dai bari zahra ai zan baki course d'in da wlh yaya mashkhur sai ya soki,  in ba'a yi wasa bama to fah da JARIRINKI zaki dawo Nigeria ko da tsowan CIKI............... 

Da sauri zahra ta fir gita had'i da zaro ido tare da cewa! Ciki kuma ilham  rufamin asiri,  hararar zahra ilham tai tare da cewa!  To menene Haramin ne?  Rausayar da kai zahra tai tare da cewa!  Ai naji kin fad'i abinda bazai ta6a yuwowa bane,  hmm haka kika gani ai sai ma yafi komai sauqin yuwuwa in dai kinsa kanki,  Ilham ta qarasa maganar tana zubawa zahra ido,  shiru zahra tai tana nazari maganar ilham dan ita ko da wasa mah gani take hakan bazai ta6a faruwa ba.  Ilham ta bud'e baki zatai magana kenan dady ya shigo baki d'auke da sallama,  had'a baki zahra da ilham sukayi wajan amsa mai sallamar.

Yana qarasowa wajan da suke zaune zahra tace dady ina kwan an tashi lpy?  Murmushi dady yayi tare da cewa lpy qalau mamana kema da fatan kin tashi lpy? Na tashi lpy qalau dady,  dady good morning cewar ilham,  morning ilham how are you,  I'm fine dady zama dady yayi a kusa da zahra tare da cewa masha ALLAH.  Mamana ya kikaji zaman qasarnan dad'i kuwa? Dady ya tambayi zahra yana binta da ido,   Gyara zama zahra tai ta qara matsawa kusa inda dady yake tai tare da cewa! Uh balefi amma kasan dady tinda bana ganin ku ai bazan ji dad'i zama ba,  kullum tunanin ku nakeyi,  ni nafi so na zauna tare da ku.

Sabida mai mamana ko yayan naki yana takura miki ne?  Dady ya tambayi zahra yana binta da ido.  Ajiyar zuciyar zahra tai a zuciyar ta cewa tai sosai mah,  amma a fili cewa tai aa ni baya takuramin,  ba abinda yake min zahra ta qarasa maganar tana sunkuyar da kai,  ilham kuwa shiru tai tana sauraran abinda zahra take cewa!  Dan da itace sai ta fad'awa dady abinda yaya mashkhur yake mata,  yanzunma tana so ta fad'awa dady gaskiya abinda zahra ta gaya mata amma tasan sirri ne tsakaninsu da zahra amana Ta bata kuma in ta tona zahra bazataji dad'i ba.

Girgiza kai dady yayi tare da cewa no mamana,  karki min qarya mana,  ki gayamin gaskiya abinda yake faruwa nifa tinda muka baro ku daga rashan nan ko kwakwaran bacci bana iyayi,  sabida fargabar kar mashkhur ya ringa zalintar ki,  itama ammi kusan kullum sai gabanta ya fad'i duk tabi ta d'aga hankalinta,  kullum zancan ki take shiyasa ma da akayi hutun school mukazo dubaki,  nifa ina tinanin zaman haquri kawai kike mamana ki gayamin gaskiya.
Murmushi

Please Login or Register in order to submit comment