Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya futo da result mai kyau, domin ya bawa su dady da ammi dama sauran ‘yan gidan mamaki.
Tofah abu kamar wasa har ranar kar6ar saka makwan su mashkhur yayi wato result. Mashkhur da abdul sun shirya tsaf domin, zuwa kar6ar result, ahmad ne yake driven d’in motar sabida mashkhur duk jikinsa yayi sanyi dan bai san mai zai tarar ba.

Taro ne akeyi iya d’ali bai da malamai ba iyayan yara ma a wajan. Haka su mashkhur suka zazauna kowa yana jiran a kira sunan shi. Da ‘yan art aka fara rabawa jarabawar, masha ALLAH lokacin da akazo kan ‘yan ajin su ahmad, ahmad yayi qoqari sabida ya d’au ta biyar a cikin su wajan 300.
6angaran mashkhur kuwa gabansa sai fad’uwa yake sabida anzo kan ‘yan ajinsu kuma bai san mai zai tarar ba.

Kamar daga sama mashkhur yaji ana abbatar sunan shi. Da sauri mashkhur ya miqe, domin zuwa ya kar6o result. Lokacin da mashkhur ya qarasawa ya tsaya, a wajan. Mamaki ne ya kama mashkhur sosai saka makwan jin malamin yana yimai Congratulations 🎊🎉, wai yazo first class, wai a cikin su 200. Kai farin ciki a wajan mashkhur ba’a cewa komai. Suma malaman makarantar da d’alibai sunyi mamakin hakan wai d’an Nigeria shi ya d’auki first class, kai abinda bai ta6a faruwa a makarantar ba tinda aka bud’e ta.

Kowa na wajan nan sai da ya yaba da hazaqa irin ta mashkhur, kai abindai abin mamaki. Sosai d’ali bai suka ringa zuwa suna yiwa mashkhur Congratulations 🎉🎊, bayan an tashi daga raba result d’in. Kai hatta ahmad ma Congratulations ake mai. Hmmm murna a wajan zee ba’a cewa komai, yanda kasan mijinta ne ko wani d’an uwanta ko saurayin ta ne ya d’auke first class d’in.

Bayan mashkhur ya koma gida farin ciki ya hana shi tsaye da zaune dan haka sai da ya bigawa ammi da dady harma da momy da abdul, yayi musu al bishir shi ya d’au first class. Hmmm nikuwa amina bayer bazan iya gaya muku farin cikin da ‘yan gidan su mashkhur suke ciki ba saka makwan bana Nigeria ina rasha tare da mashkhur sai dai in mun koma jibi.💃🏻💃🏻

Tofa yanzu mashkhur ya gama shiryawa tsaf domin komawa Nigeria hutu. Hutun 2 months aka bawa su mashkhur. Dan yanzu mashkhur da ahamd sun gama shiryawa tsaf domin komawa Nigeria. Yanzu dare yayi washegari kawai su mashkhur suke jiri, qarfe bakwai na safe (7:00 am) jirgin su zai tashi......

Washegari.......

Su mashkhur da abdul da sassafe suka tashi suka shirya sanan suka futa da kayan da zasu buqata in sunje Nigeria. Mashkhur kuwa bai d’auki kayansa ko d’aya ba, kawai laptop d’in sa sai wayarsa ya d’auka sai kuma kayan jikinsa, duk kayansa a rasha zai barsu sabuda yana da kayan da zai sa a Nigeria. Tom su mashkhur sun gama shiryawa tsaf, domin tafiya airport, duk sun kullen gidan su, har motar tasu tana cikin gidan, bayan sun gama kullewa suka tari motar haya , sanan suka wuce airport.
To fah su mashkhur fa jirgin su ya tashi, domin zuwa Nigeria..........

Hmmm ku biyoni a sannu dan jin ya zata kaya, in mun koma Nigeria..............

"ADALILINTA"

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                             Typing.......

                    *page 49*

Masha ALLAH jirin su mashkhur ya sauka Nigeria lfy.  Suna futowa mashkhur ya hangi abdul na sakar mai murmushi.  A hanzarce mashkhur ya qarasa inda  abdul d'in yake tare da saurin rungume d'an uwan nasa.  Ciki da matsanancin farin ciki abdul yace u are welcome my bro,  I really miss you,  cike da jin dad'i mashkhur ya qara rungume abdul tare da cewa miss you more my bro.

Muryar Ahmad  sukaji yana cewa inyee su bro ni an manta dani an barni a gefe kenan?.  Sakin mashkhur abdul yayi tare da rungume ahamd yanace cewa sorry my brother tuba nake,  ya za ai na manta da d'an uwana. Murmushi Ahmad yayi tare da cewa don't mind my bro.  Ana haka ahmad ya hangi drivern  su yazo d'aukar shi,  sakin abdul sakin ahmad  yayi,  sukayi sallama.  Sanan mashkhur da ahamd suka yiwa junan su al qawarin zasu hadu.   su mashkhur da abdul shigewa mota sukayi,  suka wuce gida.......... 

Tsayawa gayawa masu karatun littafin ADALILINTA farin cikin da 'yan gidan su mashkhur suke ciki yau sakamakwan,  ganin mashkhur 6ata lokaci ne.  Farin ciki suke sosai musamman ma ammi da dady. 
6an garan zahra kuwa tana d'aki a kwance dan sam bata so, ko hanya su sake had'awa da mashkhur har abada. 
Ai lokacin da su dady suka ga result d'in mashkhur da idon su wani farin ciki ne ya  lili6e, abin ya basu mamaki sosai duk da dai sun san mashkhur ya Sabah d'aukar first class a B U K.

lokacin da momy ta d'ora idon ta akan result d'in mashkhur ta gigice sosai, wani baqin cike ne ya lulu6e ta yaqe take kawa,  sabida ta d'au alwashin bazata ta6a bari mashkhur ya cigba a rayuwar sa ba kamar yandda adul bai yi karatuba a qasar waje ba shima mashkhur bazai ba.   Ba 6ata lokaci momy ta koma part d'inta cikin baqin ciki ta d'auki wayarta ta bugawa saratu,  ta sanar da ita mai ke faruwa. 

Saratu kuwa cewa tai momy ta kwantar da hankalinta wajan boka zasuje kawai.  Ai kuwa haka akayi washe gari momy ta cewa dady baban ta bashi da lafiya zataje duba shi,  dady kuwa ba musu yabar momy ta tafi kaduna.   Momy tana isa kaduna bata tsaya ko ina ba sai gidan saratu,  tana zuwa gidan saratu,  ba 6ata lokaci saratu ta d'auki motar ta sukai gaba.
Suna isa wajan boka tun kafin momy tayi mai bayani mai ke tafe da ita ya kwashe da dariya tare da ce mata,  duk abinda ke tafe da ke na sani,  koh ba akan d'an kishiyar ki bane?.

Da sauri momy ta d'aga kai tare da cewa ehh boka hakane kuwa.  Wata shi'umar dariya boka yasa tare da cewa  yanzu wana mataki kiko a d'auka ko a KASHE SHI ne kawai?.  Da sauri momy ta girgiza kai tare da cewa aa boka ai nafiso ka barshi da ransa kawai ka mayar da shi cikakyan d'an iska yanda zuciyar kishiyar tawa zata buga. Dariya boka yayi tare da cewa wanan shi yafi komai sauqi,  me kike so a yimai ne?.  Kallan qanwar tata  momy tayi tare da cewa saratu me kike ganin za ai wa mashkhur ne?.

  yaya halima kin san mai za'ai ma?,  da sauri momy ta girgiza kai tare da cewa sai kin fad'a.  Gyara zama saratu tayi tare da cewa yaya halima kawai a mayan da shin d'an iska,  wato ya koma d'an shaye-shaye da bin mata,  yanda ko ya koma rasha ba zai yi karatun ba sai dai yayi iskanci. Kwarai kuwa saratu kin kawo shawara, mai kyau haka za ai.  Ba 6ata lokaci boka ya d'auki kaskwan  qasarsa domin yiwa mashkhur asiri.

Amma ina asiri yaqi tafi wajan mashkhur d'agowa  boka yayi tare da kallan su momy yana cewa kaii gaskiya ga dukkan alamu yaran nan yana yawai ta addu'a,  ko kuma yana da taurin kai sosai.  Da sauri momy tace kwarai kuwa mashkhur yana da mugun  taurin kai.  Dariya boka yayi tare da cewa karki damu da wanan zan baki magani ki tabbata kafin  ya koma makarantar  kin zuba mai a binci yaci, sau goma,  tom ina yi miki bushara da shikenan bazai ringa karatuba sai shaye-shaye da bin mata.

Daga hakahaka momy ta ajiyewa boka kud'in sa sa
Daga haka momy gida su ta wuce, ta gai da umma da baba,  bata wani jimaba ta wuce kano.  Tana zuwa gida ta wuce part d’in ta, tayi wanda sanan ta shige kici ta fara dafawa mashkhur abinci,   bayan ta gama ta barbad’a wa mashkhur maganin a abinci sanan ta wuce part d’in su mashkhur.  Lokacin da momy ta bawa mashkhur abinci sam ya manta bai yi bismillah  ba,  dama ina qadda zata same ka,  haka abun yake ALLAH yasa mu dace.

6angaran zahra kuwa har yanzu bata sa mashkhur a idunta ba,  sam bata bari ko hanya ta had'asu,  shima mashkhur d'in ya manta da wata haliita zahra.  Ahamd yana zuwa gidan su mashkhur sosai suyi hira,  shima watarana mashkhur yana zuwa wajan Ahmad d'in.  6angaran momy kuwa ta gama bawa mashkhur maganin boka a abinci har na tswan kwana goma.

Kwanci tashi ba wuya wasa-wasa har lokacin komawa makarar su mashkhur yayi,  dan yanzu bai fi saura sati d'aya su koma ba.  Dan mashkhur ma ya fara shirya-shiryan komawa rasha.
      Yau ya rage saura kwana d'aya su mashkhur su koma makaranta ,  bayan  mashkhur ya gama shirin tasf,  kwanciya yayi,  domin yin bacci.

Washegari da sassafe jirgin su mashkhur ya tashi domin tafiya rasha.
Mutan gidan duk jikinsu yayi sanya,  sabida tafiyar mashkhur,  momy kuwa farin ciki take sosai,  itama zahra taji dad’in tafiyar mashkhur d'in dan ko ba komai zata sake a gidan,  dan tindda yazo har ya koma bata sa shi a idanuwanta ba.

RASHA.

jirgin su. Mashkhur ya sauka garin rasha lafiya kuma sun koma masaukin su.  Bayan one week suaka koma makaran ta domin ci gaba da karatu.  Abu kamar gaske mashkhur ya fara karatu,  amma sai dai zee ta sake matsawa mashkhur sosai fiye da dama.  Abun mamaki shima mashkhur d’in ya fara kula zee, dan yanzu ma zee har gidan su mashkhur ta sani.
Niku amima bayero nace anya asirin bokan momy bai fara aiki ba. 🤔

Kai abu fa kamar wasa har zee ta zama qawar mashkhur sosai,  dan yanzu har gidan su take zuwa suyi hira.  Kuma hakan ne ya bawa zee damar koyawa mashkhur shaye-shaye,  dan yanzu zee ta koyawa mashkhur shan kwayoyin maye da kokyan harma da maganin mura taso ta koyawa mashkhur shan sigari,  amma mashkhur sam ya kasa sabida ko qanshin sigari mashkhur yaji sai yayi a mai.  Hakan kuwa ba qaramin mamaki da d'agawa ahmad hankali yayi ba.

Ahamd yayi-yayi mashkhur ya rabu da zee amma ina abu yaci tura daga qarshema har fad'a sukayi.  Ahamd kuwa dole ya saukko ya cigaba da yiwa mashkhur nasiha akan ya dai na mugayan halin nan.  Yanzu kwata-kwata mashkhur ya dai na karatu wataran ma baya zuwa makarantar sai dai yasha maganin bacci ya kwanta.  Yanzu fa abu yayi qarfi dan zee wuni take a wajan mashkhur,  tayi bacci tayi wanka harma girki take yi.  Babban buri zee mashkhur ya kussan ceta, amma mashkhur yaqi dan sam yaqi bari wata halaqa mara kyau ta shiga tsakanin sa da zee.

Lokacin exam yazo,  hakan ne yasa mashkhur ya raqe wasu abubuwan kuma yana karatu yanzu,  amma dai ba sosai ba.  Bayan sunyi jarabawa aka bawa su mashkhur result d'in su.  Mashkhur kuwa a cikin su 200 ta 20 yazo,  nikuwa amna bayero nace ina laifi tindda ba karatun yake ba.  Malaman su mashkhur sunyi mamaki sosai da sosai yanda lokacin guda mashkhur ya dai na karatu gaba d'aya.

Haka mashkhur da ahmda suka kama hanyar dawowa Nigeria hutu.  Lokacin  da mashkhur ya koma gida sam bai bari su dady sun ga result d'insa ba.
A
6angaran ahamd kuwa ya yanke shawarar ya samu dady ya gaya mai halin da mashkhur yake ciki.  Ba 6ata lokaci ahmad ya d'auki waya yayiwa dady massage da cewa yana so su tattauna magana mai mahimmanci akan mashkhur,  in ya samu lokaci. Dady kuwa ya amince da hakan dan harma sunyi shawarar a inda zasu hadu.

Lokacin da ahamd ya had'u da dady bayan sun gaisa ba 6ata lokaci,  ahamd ya fara yiwa dady bayani akan halin da mashkhur yake ciki,  ba abinda Ahmad  ya rage har halaqar mashkhur da zee  .  Dady ya tabbayi Ahmad hakan mashkhur yana ai kata zena da zee.  Ahamd kuwa cewa dady yayi gaskiya bai sani ba,  amma shima yana zargin haka.  Dady yayiwa ahmad godiya sosai daga haka sukayi sallama,  kowa ya wuce gida.

Hankalin dady ya tashi sosai da jin abinda mashkhur yake ai katawa,  dan da kyarma ya qarasa gida.  Bayan dady ya je gida ammi da hajiya kaka harma da momy ya tara a d'aki ya sanar da su abinda ke faru.  Hmmm bazan iya gaya muku halin baqin ciki da ammi da hjya kaka su shiga ba. Momy kuwa farin Ciki kamarya ka sheta aiki boka ya kama mashkhur.  Dady ammi momy hjya kaka duk suna yiwa Mashkhur kallan muzinaci  kuma d'an shaye-shaye.  Amma abinda basu sani ba shine sam,  Mashkhur baya zina,  amma ba wanda yasan hakan dan ko ahmad ma  zargin mashkhur yake da hakan.

To yanzu su ammi sun tabbar da mashkhur yana shaye-shaye,  sabida kwalaban da suke gani a d'akin sa da kwayoyi,  kai harta  abdul yasan halin da mashkhur yake ciki.  Abdul yayi baqin cikin haka  sosai kuma kullum ciki yiwa mashkhur nasiha yake.  Ba kowa bane  yasan mashkhur yana shaye-shaye a gidan ba sai dady, ammi, momy, hjy kaka, da abdul.  Amma duk sauran yaran  gidan  basu saniba,  sabida mashkhur  yana taka tsam-tsam kuma ya hana su haidar shiga d'akin sa sai da izini.

Abun ya damu hjy kaka sosai hakan ne yasa hjy kaka  ta yanke shawarar had'a mashkhur da zahra aure.  Bayan ta yanke shawarar ta samu dady da zancan.  Da farko dady bai amince da hakan ba amma hjy kaka tace umarni ta bashi, hakan ne yasa dole dady ya amince bada son ransa ba.  Haka dady ya tara mutan gidan ya sanar da su ya had'a auran zahra da mashkhur.........

Tom masu karatun littafin ADALILINTA wanan shine dalilin da yasa  aka had'a  zahra da mashkhur aure.
Kuma wanan shine cikakyan tarihin gidan alhaji Abukar dala.
Kunji abinda ya jawo kiyayya tsakanin mashkhur da zahra,  kuma kunji mai ya kawo soyayya tsakanin abdul da zahra.
Kuma kunji wace zahra............

A lokacin mashkhur yana da she kara 27, dan ya girama sosai ya zama saurayi,. Shima abdul d'in ya girma sosai ya zama sauri dan lokacin shekarar sa 24, kuma a lokacin ne abdul ya kamu da matsanan cin son zahra, ammah sai dai bai gayawa kowa ba a gidan, hatta zahra ma bata sani ba. Lokacin su zahra da rukee suma duk sun zama 'yan mata sosai dan lokacin ma shekarar zahra 17.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing..........

*page 50*

Yanzu mun gama tariyin zamu kowa labarin mu..........

Back to story......

Yau sati d'aya kenan da had'a auran zahra da mashkhur. Abdul dai jiki yayi sauqi, ba laifi, amma lokaci guda yayi zuru-zuru duk yabi ya rame kullum cikin tinani yake. 6angan zahra kuwa kullum tana nan abun dai ba dad'i, sam yanzu ta dai na walwala mussaman ma in ta tuna wai mashkhur za'a aura mata. 6angan mashkhur kuwa ya d'au alwashin bazai ta6a bari a aura mai zahra ba.

Itama ammin yanzu ta de na jin haushin mashkhur tinda hjy kaka tace mata asiri akayiwa mashkhur, tun daga nan ammi ta dage da yi mai addu'a.
Yanzu ya rage saura sati d'aya saukar su zahra da ilham harma da su rukee da ruma. Kuma dady ya gama yanke shawarar zai d'aura auran zahra da mashkhur, ranr saukar su ilham. ba wanda yasan hakan daga ammi sai hjy kaka.

Mashkhur kuwa yana nan yana shirya-shiryan yanda zai rusa auran sa da zahra.
Yanzu zahra ta fawwalawa ALLAH ta d'an saki jikin ta, sabuda saukar qur'ani da zasuyi.

Yau saura kwana d'aya saurakar su zahra, dan haka tun da daddare aka fara girke-girke da yake dady ya buga inventions d'in bikin mashkhur da zahra ya raba, suma ammi da hjy kaka sun rabawa mutane 'yan uwa da abokan arziki duk sun raba musu, sauran gidan kuwa bawanda yasan ma me akeyi ba. Dan haka tun daran ranar aka fara shirin girkin gobe dan an kawo kayan abinci da nama.

Washegari.......
Tunda safe mutan gidan suka fara shirya-shiryan tafiya wajan saukar su ilham. Dady kuwa da biyu ya shirya dan a wajan saukar yake so a d'aurawa zahra da mashkhur aure dan ya gayyaci manyan abokan sa sosai. Dady ya shirya cikin tsadaddiyar shaddar sa mai kyau, sai kyalli take.

Zahra, ilham, rukee, ruma suma duk sun shirya cikin kayansu na ankwan sauka, kayan su mai tsada suka saka, sanan suka d'ora hijab da niqab sunyi kyau sosai, da sosai. Suma ma su faruq da haidar sun shirya tsaf sunyi kyau binsu dama su tun waccan shekarar lokacin da mashkhur ya tafi rasha sukayi sauka. Abdul ma ya shirya cikin shaddar sa tsadadiya, yayi kyau sosai abinka da fara kuma mara jiki sosai.

Su zahra sunyi mamaki sosai yanda suka ga wajan sauka ya cika da mutane maqil, abinda ya basu mamaki ko lokacin saukar su faruq mtane basu zo hakan ba. Ba 6ata lokaci aka fara da addu'a sanan aka kira d'aliban sauka aka fara raba musu allo, da qur'ani, kowa kafin a bashi allan sa sai ya yayi karatun al qu'ani tukunna.

Bayan an gama saukar su zahra nan da nan limaman da malamai sukai sanarwar kar wanda ya tafi za'ai d'aurin auran wata daga cikin d'alibar sauka. Mamaki ya kama su zahra harma da sauran d'aliban sauka kowa sai mamaki yake wace haka zatai aure bata sanar da suba. Suna cikin kokwan tan suka jin an fara shirn d'aura aure, nan da nan kowa ya mai da hankalin sa.

Mamaki ne ya kama su zahra harma da abdul da su faruq, saka makwan ganin dady, da abokan sa harma da 'yan uwansa a kusa da limamin da za'a d'aura aure. Suna cikin kokwanto sukajin an fara d'aura aure. Dady ne wakilin zahra, sai kuma cousin d'in dady ne wakilin mashkhur. Su zahra harma da sauran mutanan wajan basuji su me dady suke tattau nawa ba sabida da tazara sosai.

Kawaii dai sunga course d'in dady ya curo kud'i mai yawa ya ajiye, daga qarshe kuma bayan sunyi magan ganu ya miqawa dady kud'in. Duk anbar su zahra da faruq a cikin duhu. Shikuwa abdul tun kafin a sanar da abinda yake faruwa jikinsa ya bashi dady auran yaya mashkhur da zahra yake so ya d'aura, nan da nan gumi ya rufe abdul , yama kasa motsi gaba d'aya,.

AN daura auran MUHAMMAD MASHKHUT ABUBKAR DALA da FATIMA ZAHRA ABUKAMAR DALA. AKAN SADAKI MILIYAN D'AYA. Abinda kunan zahra suka iya jiye mata kenan daga haka bata sake gana komai ba, kawai dai tana ganin giftawar mutane da hayaniya. Abdul kuwa sake das karewa yayi a wajan, ilham ma da su faruq suma mamaki ne ya rufe su sosai da sun kasa cewa komai, ma.

'Yan aji kuwa sai surutu suke wasu suna cewa ALLAH ya sanya alkhairi, wasu kuma suna cewa zahra da ilham basu kyauta ba da basu gaya musu ba, wasu kuma duk sun 6ata rai suna jin haushi tare da fad'in gananin magagan ganu akan rashin sanar da su auran. Suma su faruq da haidar mamaki ne ya kamasu sosai, haka dai suka kama abdul suka sashi a mota faruq yaja suka wuce gida domin sanar da su ammi meke faruwa.

Zahra kuwa miqewa tai kamar wata mahaukaciya ta tsige niqab d'in fuskarta ta fara tafiya kamar wata mahau kaciya. Itama ilham d'in miqewa tai tare da miqawa ruma qur'anin ta dana zahra tare da cewa ruma ruke mana bari nabi bayan zahra. Zahra kuwa tafiya take kawai, da sauri ilham ta riqe hannun zahra sukayi hanyar gida. Suna shiga gida kuwa matan biki suka fara yiwa zahra bud'a.

Zahra kuwa ko ta kansu bata bi ba suka shige d'aki ita da ilham suka kulle, ba abinda kakeji yana tashi daga d'akin sai sautin kukan zahra da ilham.

Mashkhur...........

Hayaniyar mutane ce ta tashi mashkhur daga bacci. Yayi mamaki yanda yaji hayaniya a har bedroom d'in sa, ko bai fita ba yasan ba qaramin mutane ne a gidan ba, kuma yasan duk saukar su ilham suka zo. Hhhhhh nikwa amina bayero nace ko dai ba gayawa mashkhur ya zama ango zahra ne? 🤔😂

Miqewa mashkhur yayi ya shiga toilet yayi wanka, bayan yayi wanka ya shiya cikin yadinsa mai kyau, yayi tsaf a binsa in ka gan shima bazaka ta6a tinanin yana shan wasu kwayoyi ba, duk ya zama wani gentle man. Mukullin motar sa ya d'auka ya fuce daga bedroom d'in nasa. Ta bayan qofar part d'insu ya fita, sabida sam baya son yaga jama'a sosai.

Yana futa ta qofar bayan part d'in su tafiya kad'an yayi ya qarasa parking space, daga nesa ya hango mutane sosai suna yin bud'a amma mashkhur bai kawo kamai a ransa ba ya wuce wajan motar sa. Yana zuwa ya shige sanan ya zuge baqin glass d'in motar ta yanda ba wandda zai iya gane waye a motar. Hoon yayiwa mai gadi ya zuge mai, get d'in ya fuce.

Mamaki ne ya sake rufe mashkhur saka makwan ganin dady da manyan abokan sa, kuma ga dandazon mutane ko ta Ina, mashkhur dai yasan ko da saukar abdul ba'ai irin wanan taran ba. Bare saukarsu mashkhur d'in da yake lokacin ba'ai taro ba saka makwan ammi bata da lafiya. Mashkhur dai bai kawo komai a ransa ba ya ratsa da motar ta cikin mutane ya wuce gidan su ahmad........

Da kyar ammi ta lala6a zahra akan tayi haquri tai wanka kuma ta shirya. Wajan qarfe hud'u na yamma bayan zahra taci kuka ta qoshi ta tashi ta shirya, shima ba'a san ran taba kawai da sabida ammi ta takura mata. Bayan ta shirya cikin tsadaddan leshinta da mayafi fita tayi wajan qawayanta ta zauna zuciya duk ba dad'i, 'yan biki ma sun fahimci zahra bata so a ce mata amarya ko ayi mata bud'a dan haka denawa sukayi gaba d'aya.
6angaran abdul kuwa tunda ya dawo yana can daki zuciya cika da baqin ciki.

Sai wajan misalin qarfe ( 11:00 am) na dare mashkhur ya dawo gidan, kafin nan duk 'yan biki sun waste, da yake an sanar da su ba a qasar nan zahra zata zauna ba. Mashkhur kuwa yaji dad'in ganin kowa ya tafi da yake dama sabida su yabar gidan. Yana shiga part d'in su ya hangi dady zaune a babban falon part d'in nasu yana danna wayar sa.

Baki d'auke da sallama mashkhur ya shigo, dagowa dady yayi ya fara kallan mashkhur sama da qasa. Dady sannu da war haka, cewar mashkhur. Da sauri dady ya girgiza kai tare da cewa ai mai sunan baba ai kai ya kamata ayiwa sannu da war haka, tinda har ka kai dare haka. Shiru mashkhur yayi bai tanka ba ya kama hanyar hawa step. Da katar da shi dady yayi tare da cewa dawo inason magana da kai.

Ba musu mashkhur ya juyo ya dawo inda dady yake yakeso tare da zama a qasan kujera, shi kuma dady yana saman kujera.
Gyara zama dady yayi tare da cewa dama inaso na gayama abinda ya dace ka sani. Yau misalin qarfe(12:00pm) na rana na d'aura aure kai da MAMANA. A furgice mashkhur ya miqe tare da cewa what!! Dady da wasa kake ko da gaske?.

Harara dady ya watsawa mashkhur tare da cewa na ta6a yi maka kalar wanan wasa ne?. Tom bari kaji yanzu zahra ta zama matar ka ta aure. Ai mashkhur bai san sanda ya furta ALLAH ya sauwaqe mai zanyi da wancan banzar yarinyar?. Ji kake tass-tass wani kyakyawan mari dady ya sakarwa mashkhur tare da cewa mai sunan baba ni kake gayawa

Please Login or Register in order to submit comment