Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ku rabu ba kowa yaje ya auri wanda yake so. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa aa dady gaskiya ni bazan iya sakin ta ba.

Cikin mamaki dady yace sabida mai ko ka fara son ta ne?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ni ban fara son taba kawai dai bazan iya sakin ta bane sabida hakan ba dad'i. Wani irin kallo dady ya watsawa mashkhur tare da cewa haba wanan wana irin abu ne tinda ba son ta kake ba ka sake ta mana wanda suke sanda su aure ta. Haba dady wani ya aure ta fa kace in na sake ta.

Cikin mamaki dady yace to da nufin ka in ka sake ta sai tai ta zama a haka ba aure koh?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ai bazan ma sake ta ba bare wani ya aure ta dady. Dady yana qoqarin magana ammi ta murd'a handle d'in kofar ta shigo bakin ta d'auke da sallama hannu riqe da tire d'in abincin breakfast d'in dady. Bayan dady ya amsa mata cewa yayi yauwa maryam ai gwara da kika zo yanzu zo kiji wani ikwan ALLAH.

Ammi qarasawa tai ta ajiye tire d'in akan table tare da cewa to lafiya mai yake faruwa yaya?. Ni da wanan yaron ne kiji abun mamaki wai a lallai bazai sakar mana 'yar ba. Zama ammi tai tare da cewa to sabida mai kenan?. Oho shi ya sani ba wani dalili, kallan mashkhur ammi tai tare da cewa ko dai ka fara son ta ne bamu sani ba. Mashkhur girgiza kai yayi tare da cewa aa ni bana son ta kawai bazan sake ta bane.

Lallai mashkhur abinda bazai ta6a faruwa ba kenan tinda baka son ta ka sake ta mana ammi ta fad'a tana tsare shi da ido. Haba ammi kema da kanki kika cewa na sake ta gaskiya ni bazan sake taba. Jinjina kai ammi tai tare da cewa to tashi kaje amma ka kwana da sinin cewa har dai ba son ta kake ba ba zamu ta6a amincewa ka zauna da ita a matsayin mata ba. Jiki a sanyaye mashkhur ya miqe tare da cewa sai anijima sanan ya fuce.

Yana fita dady yace lallai wata sabuwa in kana duniya za kaga abin mamaki kala-kala maryam. Murmushi ammi tai tare da cewa hmmm ai kuwa dai amma kasan sabida mai ya qi sakin ta kuwa?. Girgiza kai dady tai tare da cewa aa ina fa na sani, murmushi ammi tai sanan tace son ta yake yi fa. Girgiza kai dady yayi tare da cewa ina ko dai kin manta halinsa ne taya zai so ta ai taurin kansa bazai ta6a bari ya so mamana ba.

Murmushi ammi tai tare da cewa nima da haka nai tinanin amma daga qarshe sai naga zahira hmmm kai dai ka bari ba ya fara hakan ba, to mu zuba mai ido muna nan da kai zai zo yace yana son ta. Jinjina kai dady yayi tare da cewa tom ALLAH yasa ai mu hakan muke fata. Cikin mamaki ammi tace kana nufin in yazo yace yana son ta sai mu amince kenan?.

Gyad'a kai dady yayi tare da cewa eee mana hakan ya kamata ayi ai muma sai mumfi jin dad'i hakan. Tabba ai wlh mashkhur bai isa ba kafin ya cigaba da zama da zahra a matsayin matar sa sai ya gane kuskuran sa, sai ya dai na taurin kan nan nasa gaba d'aya a duniya. Jinjina kai dady yayi tare da cewa hmmm to ALLAH dai ya nuna mana ranar da zai ce yana so, zai ma fad'a yaya kawai mu zuba mai ido zaka gani ne.

Mashkhur sabida tashin hankali da kyar ya iya qarasawa bedroom d'in shi. Yana qarasawa ya baje akan bedroom zuciya na dukan uku-uku. Na shiga uku yanzu fa so suke su rabani da zahra mashkhur ya fad'a a zuciyar shi hankali a tashe. No never for ever wlh bazan ta6a sakin ta ba har a bada ina son ki zahra wlh ina qaunar ki bazan ta6a iya rayuwa babu zahra ba.....

5 days a go.

To fah yanzu hankalin mashkhur ya sake tashi sosai sabida rashin ganin zahra, ga wani irin mugun son ta da yake ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a kusa da zahra. Gashi yaga ammi da dady sun share shi da maganr zahra yana so yaje ya gaya musu akan a dawo mai da matar shi zahra amma yana jin nauyin hakan, sabida yasan baza su ta6a yarda ba har sai yace yana son ta, shi kuma mashkhur gani yake bazai ta6a karya record d'in rayuwar sa ba.

Sabida shi tun yana yaro baya canza magana in ya kafe akan abu d'aya in yace baya so tofa baya son abu, ko mai zai faru amma sai gashi yanzu ALLAH ya jarrabe shi da son zahra.
6angar abdul kuwa jiki yayi kyau masha ALLAH, yanzu yana iya komai da kansa har abinci yana ci abinda ya rage kawai kwarain jiki da kuma mai da jikin sa.

Yau kwana shida kenan mashkhur yana tinanin mafita game da zahra. Ko ishashan abinci mashkhur baya samu yaci kullum tinanin mafita yake amma yanzu ya gama yanke shawarar zuwa wajan ammi da dady ya sanar da su yana son matar sa. Misalin qarfe 5 na yamma mashkhur ya shiga 6angaran ammi yana shiga bai tsaya ko ina ba sai bedroom d'in ammi.

Baki d'auke da sallama mashkhur ya shiga, zaune ya tarar da ammi tana yanke farjan qafar ta. Zama mashkhur yayi a gefan ta tare da cewa ammi ina wani barka da yamma, gyara zama ammi tai tare da cewa barka dai mashkhur sannu da shigowa ka shigo a dai-dai kaga dai ba mai yanke min farce nasan abdul bacci yake su haidar kuwa basa nan ruma tana girki, tinda ka shigo sai ka cigaba da yanke min farce koh?.

Tom ammi shikenan daga haka mashkhur ya kar6i abin yanke farce ya cigaba da yankewa ammi farce zuciya cike fall da tinanin taya zai fara gayawa ammi zancan nan. Bayan mashkhur ya gama yankewa ammi farce gyara zama yayi tare da cewa ammi dama ina so na gaya miki wani abu. Gyara zama itama ammi tai tare da cewa to mashkhur ina jinka menene.

Hmmm ammi da akan maganar zahra ne, cikin zuciyar ammi tace anzo wajan, amma a fili sai tace uhmm ina jinka. Ammi wai yaushe zata dawo ne? Nima mashkhur ban sani ba wlh, ammi to gaskiya ya kamata ta dawo, to kai meye damuwar ka da dawowar ta, ammi ta watsawa mashkhur tambayar. Jim mashkhur yayi can kuma yace sabida matata ce mana.

Hmmm lallai kam matar kace, mene amfanin dawowar ta ita da ba tarewa zatai ba kuma ba santa kakale ba kawai ka rabuda da ita ta zauna a can, ka sake ta ta auri masu son ta. Haba ammi nifa bazan sake taba ina son ta dan ALLAH kuce ta dawo wlh ina son ta. Hmmmm yanzu aka fara wasan, ammi ta fad'a a zuciyi a fili kuma cewa tai gaskiya ne naji kana son ta sai akayi yaya?.

Ee sai ta dawo mana ammi mu tare da ita a gidan mu da ake gina mana, lallai mashkhur kama dena maganar tariya sabida ita ba son ka take ba. Aa ammi zata so ni mana zan sa ta so ni. Jinjina kai ammi tai tare da cewa shikenan kaje kasa ta fara son ka mude namu ido ne ta amince zata tare a gidan ka shikenan, ai ahmad abokin ka gidan su ne kaje ya raka ka.

Jim mashkhur yayi na wasu lokutan can kuma yace gaskiya ammi ni bazan iya zuwa kaduna gidan su ba sai dai ku kuce mata ta dawo. Hmmm lallai mashkhur kana da sauran aiki a gaban ka, sai dai kuwa ka gama zama da zahra a matsayin matar ka har in mu zamu ce ta dawo in kasan kana son ta kaje ka dawo da ita da kan ka kaji ko?. Girgiza kai mashkhur yayi tare cewa nifa ammi bazan iya zuwa gidan su ba.

Hmmm da kyau mashkhur in dai bazaka iya zuwa gidan su ba ka dawo da ita haka zalika muma bazamu iya cewa ta dawo sabida kai ba, kuma ma kai a nufin ka zamu sake yiwa zahra dole akan sai ta so ka ne ko ta cigaba da zama da kai a matsayin mijin ta, wlh baka isa ba mashkhur har sai zahra ta bud'e bakin ta tace tana son ka kuma ta yarda zata zauna da kai a matsayin mijin ta tukunna zamu amince muma.

Rai ba dad'i mashkhur yace to shikenan ammi ALLAH ya wuci zuciyar ki ni zan iya jira ta dawo sai na gaya mata amma bazan ta6a zuwa gidan su ba. Daga haka mashkhur ya miqe ya fuce, hmmmm yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka muje zuwa mashkhur ai yanzu ma aka fara wasa lallai ma hmmm ammi ta qarasa maganar tana saki wani siririn murmushi mai cike da tausayawa mashkhur.

KADUNA.

To fah zahra da ilham sun zama 'yan garin kaduna, suna shan yawo sosai kullum a fita shan ice cream suke da zuwa shoppe nana ce take kai su ko ina da yake ta iya drive. Zahra ba laifi ta saba da mutan gidan sosai ta saki jikin ta da su musamman maman ta da nana. Zahra tana jin dad'i zaman kaduna kamar gida duk abinda suke so ana yi musu, amma sai dai zahra tayi mutuqar d'aga hankalin ta akan sai ta koma kano ta duba yaya abdul.

Duk da kuwa suna waya amma tace ta yarda ma tana so ta koma kano ko dai bazata kwana ba ta duba abdul ta dawo. Abban zahra yace a barta taje ta duba shi sai ta dawo dan haka yanzu zahra sun shirya tsaf ita da ilham harma da nana dumin zuwa duba yaya abdul. Satin su zahra d'aya kenan a kaduna. Washe gari da safe driver ya d'ebe su zuwa kano da yake nana bata iya drive mai tsayi ba............

KANO.

Su zahra sun sauka garin kano lafiya qalau. Drive yana parking su zahra suka futo cike da zumid'i suka shige cikin gidan. Direct 6angaran ammi suka wuce. suna shiga suka tarar da ameer yana wasa a babban falon da gudu ameer ya qaraso wajan zahra tare da cewa oyoyo aunty zahra ta. Itama zahra cikin farin ciki ta rungume shi tare da cewa oyoyo my ameer d'i na.

Bayan zahra da ameer sun gama rungume juna cewa tai ameer ina ammi. Tana kicin tana dafa mana abinci ita da ruma. Murmushi zahra tai tare da cewa yauwa zo muje ko, daga haka zahra ta kama hanyar kicin hannu riqe da ameer nana da ilham suna biye da ita. Suna shiga kicin zahra ta qarasa wajan ammi tare da rungume ta tana cewa oyoyo ammi.

Cikin farin ciki ammi tace ah mutanan kaduna kune?, kwana nawa kika zahra amma kika dawo?. Murmushi zahra tai tare da cewa eee mana ammi wajan yaya abdul nazo ya jikin nasa so nake na duba shi. Murmushi ammi tai tare da cewa jikin abdul da sauqi tun yaushe abdul ya samu sauqi harya koma part d'in su ma yanzu yana can. Sakin ammi zahra tai sanan ta rungume ruma a gaggauce, ta sake ta tare da cewa ilham kuzo muje wajan yaya abdul.

Daga haka zahra ta fuce da sauri, ilham da nana ko gaisawa basuyi da ammi ba suka bi bayan zahra. Zahra da sauri take tafiya burin ta tasa yaya abdul a idon ta kawai, suna shiga part d'in zahra bata tsaya ko ina ba sai bedroom d'in yaya abdul. Fuska d'auke da murmushi zahra ta murd'a handel d'in qofar ta shige tana cewa oyoyo farin cikina yaya abdul.

Zahra ta qaraa maganar ta nufar yaya abdul da yake gefan gado a zaune shi da mashkhur suna hira. Zahra tana zuwa ta fad'a jikin yaya abdul d'in ta hugging shi ciki farin ciki. Mashkhur kuwa da yake gefe a zaune wata nananuyar a jiyar zuciya ya saki sabida ganin shigowar zahra kamar almara, amma da yaga ta rungume abdul d'in sai yaji wani mumunan kishi ya taso mau, a dai dai lokacin ammi da nana suka shigo baki d'auke da sallama.

Yaufa single page na samu damar yi.

Mu had'e a next page.






BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING............

*Page 112*

Mashkhur kuwa da yake gefe a zaune wata nananuyar a jiyar zuciya ya saki sabida ganin shigowar zahra kamar almara, amma da yaga ta rungume abdul d'in sai yaji wani mumunan kishi ya taso mau, a dai dai lokacin ammi da nana suka shigo baki d'auke da sallama.

Cikin farin ciki yaya abdul yace oyoyo my rayuwa ya fad'i hakan yana sake rungume zahra. Wani dogwan nunfashi mashkhur yaja sabida tsabar kishi da kyar ya iya kau da idanun sa gefe. Ilham karasowa tai tare da cewa yaya mashkhur ina wuni fuska ba walwala mashkhur yace lfy ilham. Itama nana qarasowa tai cikin sanyayiyar murya tacewa mashkhur ina wani ta fad'i hakan tana qare mai kallo a zuciya tana mamakin kyan sa kama drawing aka zana ba mutum ba sabida tsabae kyau.

Shiru mashkhur yayi tare da d'agowa ya kalli nana kallo d'aya yayi mata ya kau da kai gefe yace lfy. Hakan da mashkhur yayiwa nana ba qaramin qona mata rai yayi ba, tsayawa tai tana ayyana abubawa da dama a zuciyar ta tace wai wanan daga gani zai yi girma kai ji wani yarda yake ji da kai kamar jinin sarau ta. can kuma ta mayar da kallon ta kan abdul da zahra. Sosai su zahra suka birge nana, a zuciyar nana tana jinjina haske irin na abdul dan har wani ja taga yana yi da yellow.

Wata nannauyar a jiyar zuciya mashkhur ya saki lokacin da yaga zahra ta saki abdul ta bar jikin sa sai lokacin yaji nutsuwa ta d'an saukar mai kad'an yana san qarewa zahra kallo amma sabida ji da kai irin nashi ya kawar da kai gefe kamar bai son da shigowar ta d'akin ba. Ilham fuska a sake tace yaya abdul sannu ya jikin naka?, murmushi abdul yayi tare da cewa lafiya qalau ilham jiki na da sauqi ni yanzu ma sai na zane ki.

Murmushi ilham tai tare da cewa aaa yaya abdul mai yayi zafi na yarda ba sai lamarin ya kai da duka ba. Hmmm baby ina kuka samu wanan babyn mai kyau kamar dai 'yar tsana abdul ya qarasa maganar yana kallon nana, murmushi zahra tai tare da cewa nana kizo ku gai sa da yaya abdul mana. Fuska a sake nana ta qaraso tare da cewa ina kwana, shima abdul fuska a sake ya amsawa nana tare da cewa hmm zahra wai a ina kuka sami wanan kyakyawar ne?.

Had'e rai zahra tai tare da cewa haba yaya abdul ka dena cewa kyakyawa a gaba na taya zaka cewa wata kyakyawa a gaba na ni gaskiya kishi nake. Mashkhur kuwa ji yayi kamar ya sahaqe zahra sabida baqin ciki. Murmushi abdul yayi tare da jan kumatun zahra yana cewa aaa ai dai duk kyanta bata kai kifa. Murmushi zahra tai tare da cewa yauwa yanzu naji zance qanwata ce fa. Kai masha ALLAH dole dai naga kyanta tinda jinin ki ce ai tabarakin ki taci koh?.

Murmushi zahra tai tare da cewa ee haka ne. Kai yaya abdul gaskiya baka gajiya da yabon zahra, nifa gaskiya ban gane ba ni mai kake nufi dani nai bani da kyau ko kuwa?. Murmushi abdul yayi tare da cewa hmmm ilham nifa in zahra tana nan bana ganin kowa sai ita, ni ban ma san kina da kyau ba ko kuwa?.

Murmushi nana tai tare da cewa hmmm gaskiya dai ni kam naji dad'i tinda har aka gane ni ta qarasa maganar tana saki qasai taccan murmushi. Sosai ma ba dai ke qanwar zahra bace ai dole na ganki, ni bana son ganin ki a tsaye maza zo ki zauna. Murmushi nana tai tare da cewa tom godiya nake sosai da wanan karam ci. Nana ta qarasa maganar tana sauke ido akan mashkhur.

Nan da nan nana ta sake jin haushin mashkhur ganin sai wani cin magini yake gashi sam baya fara'a bare magana dai kamar dai yanda abdul yake. Wani mugun kallo nana ta watsawa mashkhur, ai kuwa karaf mashkhur ya d'ago ya kalli nana, mamaki ne ya kama mashkhur ganin yarda nana take zuba mai wani kallo. Hakan da nana tai sai ya d'an bawa mashkhur mamaki a zuciyar shi yace tabb wanan da ita ce zahra ma inaga wataran sai dai muyi damfe da ita.

Kawar da kai nana tai tare da qarasawa ta zauna a kusa da zahra. Mashkhur kuwa miqewa yayi ya fuce daga bedroom d'in zuciya cike da son kasan cewa da zahra. Zahra a zuciyar ta cewa tai ai kullum haka zaka qare da baqar zuciya. Yaya abdul nayi missing d'in ka fa zahra ta fad'a cikin farin ciki, hmmm ke dai bari zahra ai da kin qara one week a can da tini kin zo.

Kai yaya abdul one week fa yanzu har sai kajira sai sati d'aya baka ganni ba?. Hmmm zahra ina son zuwa tun tuni amma ammi ce bata son na fara fita wai sai na qara samun sauqi. Hmm ai gwara dai da bata barin ka fita sai ka sake samun sauqi. Murmushi abdul yayi tare da cewa to ya sunan qanwar nan taki?. Murmushi zahra tai tai tare da cewa nana hafsatsunan ta itama kuma ilham cewa tai kai yaya abdul ni da kai muna son dai baqar fata, duk kabi ka rud'e da ganin nana.

Murmushi yaya abdul yayi tare da cewa ni fa duk duniyar nan in kika cire zahra bana ganin kyan ko wace farar fata. Murmushi nana tai tare da cewa ashe muma baqaqe muna da rana. Sosai ma ai baqaqe sun fi farare kyau, abdul ya fad'a fuska d'auke da murmushi. Girgiza kai nana tai tare da cewa hmmm ba dai kusan kyau ba ai kyau yana wajan fararan fata.

Shifa mutum duk munin sa in dai fari ne ya sha, kai nana a fakai ce dai zagin mu kike koh ai muma munanan ne kice farin mu ya tai make mu cewar abdul. Da sauri nana ta girgiza kai tare da cewa haba dai ai ku ALLAH ya baku ga hasken ga kyan nifa da a hanya nagan ka in ba kai magana ba sai na zata kai ba bahaushe bane dan farin naka ma har yayi yawa.

Kai lalali tab nine ba bahaushe ba ai ni yanzu sai na siyar da ke da hausa baki sani ba. Dariya nana tai tare da cewa haba dai ai duk jahilcin mutum baza'a siyar da shi da yaran sa ba bai sani ba. Au haka kika ce to ki shirya muje kiga na gama cini kin ki na siyar da ke baki sani ba dama ga ki nan masha ALLAH da 'yan kumatun ki zaki yi tsada wanan na sai da ke kaka ta ta yanke saqa ai mayi kud'i.

Dariya nana tai sanan tace lallai wato dani zakayi kud'in koh, hmmm gaskiya dai abun da kamar wuya ai ni duk wanda ya sace ni yasan mai ya satarwa kan sa, in ka siyar dani da kan su zasu dawo dani in gaya ma baza su iya dani ba. Dariya abdul yayi tare da cewa haba dai sai dai ba'ayi cini ki mai kyau ba ai in gaya miki in na samu na kai ki wajan da nake baki labari riqe ki zasuyi qam ba wanda zai sake ganin ki.

Murmushi nana tai tare da cewa hmmm ai nasan ma dai da wasa kake koh ai daga ganin ka kana da kyan halin bazaka sai da mutum ba. Kai ni zakiyiwa wayo wato har kinji tsoro kenan harda yimin wani dad'in baki ai sai na kai ki ba gudu ba ja da baya. Murmushi zahra tai tare da cewa hmmm lalali abin naku azumin ne, ilham kina jin su koh? inaji zahra ai abin ne abin dariya ma nana dai taji tsoro.

Aaa nifa ba wani tsoro da nake ji yanzu ma a tashi aje kuga in zanji tsoro. Murmushi zahra tai tare da cewa hmm lallai nana wato aje ko to wlh duk kumatun nan naki da qibar nan taki kwana d'aya kin zazzage ke ba cika baki ba ko?. Murmushi nana tai tare da cewa ba wani cika baki aje. Rabu da ita zahra zamuje ne yau-yau ma kuwa ba sai gobe ba abdul ya fad'i hakan cikin nishad'i.

Miqewa ilham tai tare da fucewa daga bedroom d'in. Zahra da nana kuwa zama sukayi wajan yaya abdul suna ta hira abun su, cikin anna shuwa da farin ciki. Bayan minti 20 da fitar ilham zahra miqewa tai ta fuce daga bedroom d'in domin d'ebowa yaya abdul abinci. Zahra a hankula ta fuce daga part d'in sabida kar su had'u da mashkhur, tana fita ta wuce part d'in ammi.

Zahra da ta shiga ta jima sosai kafin su fito tare da ilham hannun ta riqe da tire d'in abincin. Suna shigowa part d'in zahra ta hangi mashkhur ya futo daga bedroom d'in shi da duk kan alamu dai fita zai yi, zahra gani tai karo na farko kenan a duniya mashkhur yayi mata kyau sosai sabida baqar shaddar tabi jikin sa ba sosai. Zahra basarwa tai ta kawar da kai suka kama hanyar bedroom d'in yaya abdul.

Ke!!!! Zahra da ilham sukaji mashkhur ya ambaci hakan ko juyawa zahra batai ba kamar ma bataji ba duk da tasan da ita yake. Ilham kuwa juyawa tai tare da cewa na am yaya mashkhur. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ba da ke nake ba, oh ashe zahra ke yake kira cewar ilham. Ya mutsa fuska zahra tai sanan ta miqawa ilham plate d'in hanunta tana cewa gashi nan kai wa yaya abdul kice mai ganinan zuwa.

Kar6a plate d'in ilham tai tare da cewa to ta shige bedroom d'in abdul. Zahra kuwa juyawa tai ta fara tafiya a hankula kamar bata son taka qasa tana wani shashan qamshi. Mashkhur kuwa zuba mata ido yayi yana qare mata kallo, tafiyar nan ta zahra tana rikita mashkhur a zuciyar shi yana mamaki yarda zahra ta fara mai rashin mutunci sanfur sanfur.

Mashkhur dogwan nazari ya tafi dan har zahra ta qaraso bai sani ba. A gadarance zahra tace gani nan fa sauri nake, sai a lokacin mashkhur ya dawo daga hayyacin sa. Da sauri ya mai da idon sa kan zahra ya zuba mata ido kamar yarda itama ta zuba mai kowa yana saqa abinda yake ran shi,. Zahra data ga kallan yayi yawa kawar da kai gefe tai tare da cewa ina jin ka.

Da izinin wa kika tafi kaduna? Mashkhur ya watsa mata tambayar, ba 6ata lokaci zahra tace da izinin iyayae na biyu ammi da dady

Please Login or Register in order to submit comment