Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take turo mai message.

Kai gaskiya dai yau sai nai mata reply. Daga haka abdul ya ajiye spoon d'in hanun sa, ya fara rubutu kamar haka! Ameen ya rabbi Thank you so much dear, pls how are you form where Bayan abdul ya gama gajeran message d'in ya tura sanan ya ajiye wayar a gefe ya cigaba da cin abinci yana tinanin wace haka, kai amma gaskiya wanan ko wace tana da kirki,.

KADUNA.

Zahra kwana biyu duk ta rasa mai yake damun ta kawai ji take tana cikin damuwa sosai, dan duk ta canza lokaci guda ji take gaba d'aya duniyar ta fuce mata daga rai.
Miqewa nana tai tare da cewa aunty Ilham bari naje na d'obo mana breakfast d'in tinda naga kamar aunty zahra ba son sauka qasa take ba nana ta qarasa maganar tana ajiye wayar da ta turawa yaya abdul saqo.

Nana tasa qafa kenan zata fita taji qarar shigowar message. Ilham ce ta duba, cikin zumud'i tace nana zo kika kamar fa reply yayi miki. Da gudu nana ta dawo tare da cewa haba aunty ilham dan ALLAH da gaske. Ta qarasa maganar tana kar6ar wayar daga hanun ilham. Nana jiki na rawa ta fara karanta message d'in, a file ta fara karantawa.

Amen ya rabbi thank you dear how are you from where?. Murmushi ta saki nana ta bayan ta gama qarasa karanta message d'in, ilham cewa tai shikenan abinda ya rubuta. Gyad'a kai nana tai zuciya cike da farin ciki tace shikenan aunty ilham. Oh to kawo a rubuta mai reply ilham ta fad'a tana miqa hannu. Girgiza kai nana tai tare da cewa aunty Ilham yana jim sunana da state d'in da nake zai gane ni.................

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Double page.........

Typing............


To menene ba haka ake so ba. Aa ki bari zan biga mai da kai na na gaya mai da bakina. Yauwa hakan ma sai yafi gwara ki biga mai, jinjina kai nana tai tare da cewa tom aunty zahra mai zan zubo miki?. Girgiza kai zahra tai tare da cewa nana bana cin komai yanzu sai anjima zan ci. Okay aunty ilham taso mu sauka mu sai muje muyi breakfast d'in a qasa. Miqewa ilham tai tare da cewa tom shikenan muje nana.

Suna gama fita wayar zahra ta fara ringing, jiki ba kwari zahra ta d'auko wayar dan ganin wake kira. Mamaki ne ya kama zahra ganin number mashkhur duk da batai save d'in number ba amma ta haddace, sabida yawan message d'in da mashkhur yake turo mata. Mashkhur bai ta6a kiran zahra ba sai yau zahra har ta share shi taji sam bazata iya ba, dan haka kawai sai ta d'aga wayar ta kara a kunne.

Zahra tana d'agawa bata ce komai ba tai shiru abinta, 6angaran mashkhur ma bai ce komai ba yayi shiru sabida miskilanci irin nashi, sai kace ba shi yake nema ba. Zahra da mashkhur sun kai wajan 10 minutes a haka ba wanda yayi magana can zahra tace ina da abun yi wake magana ta fad'a hakan a gadaran ce. Wata ajiyar zuciya mashkur ya sauke da yaji muryar zahra, amma mamaki ya kama mashkhur da jin zahra ta tambayi wanda yake magana amma sai mashkhur sai ya basar yace mijin ki ne.

Lumshe ido zahra tai sabida yadda taji muryar mashkhur tai mata wani dad'i na musamman. Oh ni bani da wani miji malam lpy inaji sauri nake?. Duk da mashkhur yaji zafin maganar zahra sai ya dake kamar yadda ahmad ya koya mai yace sorry my wife da fatan dai ran ki bai 6ace ba. Uhmmm zahra tace tare da lumshe kyawawan idanuwan ta.

Yauwa my zahra dan ALLAH kiyi haquri ki dena jin haushi na wlh ina son ki ina qaunar ki bazan iya rayuwa babu ke ba zahra ta pls ki tai maka ki amince dani zahra wlh son ki ya sani a mawuyacin hali. Duk maganar nan da mashkhur yake a hankula yake kamar wanda akayi mai duke, ko da yake ai dole yayiwa kan ta. Zahra kuwa lokaci guda taji damuwarta ta kau da taji dad'in muryar mashkhur.

Amma a fili cewa tai ok, haba zahra ta kiyi min magana ko zanji dad'i. Hmmmmm abinda zahra tace kenan, haka mashkhur ya gama magiya da surutan ta a bisa dole, amm zahra daga ee sai aa da to take ce mai duk da kuwa tana jin dad'i wayar, dan murayar mashkhur wani kashewa zahra jiki take. Daga qarshe dai mashkhur sabida baqin ciki da 6acin ran zahra kashe wayar yayi gaba d'aya.

Zahra kuwa ajiyar zuciya ta saki ta shiga bedroom tai wanka tsarki sabida tsabar sha'awa irin ta zahra iya muryar mashkhur ma kad'ai sai da ta jefata a wani hali. Bayan ta futo tasa kaya zuciyar ta fass kamar ba itace ta gama baqin cikin d'azu ba. Sanan ta sauka qasa domin yin breakfast. Dama yau ba kowa a gidan su zahra ne kawai mama ta tafi kano, tun da safe yarin gidan kuma sun tafi makaranta, abba ya tafi kasuwa.

KANO.

6angaran mashkhur kuwa miqewa yayi ya shirya zuciya cike fall da 6acin rai domin tafiya office. Bayan ya gama shiryawa, part d'in ammi ya wuce ya gai da ita sanan ya biya wajan hajiya kaka ya itama ya gai da ita, daga nan ya nufin breakfast ya d'auki mota ya fuce daga gidan zuciya cike da tianin zahra. Mashkhur tafiya kawai yake amma a zahirin gaskiya hankalin sa baya kan driven d'in tinanin zahra kawai yake yi duk ya fita daga hayyacin sa.

Lokacin da mashkhur ya dawo cikin hayyacin sa mamaki ne ya kama mashkhur sosai ganin ya kama hanyar zuwa kaduna. Kai wai me yake damuna ne gaskiya zahra kin fara hauka tani. Murmushi ya fad'i hakan a cikin zuciyar shi, har mashkhur zai juya ya koma, yaji wani rin so da qauna da begen zahra da sha'awar ta da san ganin ta sun kama shi. Mashkhur ji yayi bazai iya juyawa ba ko mai zai faru sai yaga zahra yau..........

Hmmm su mashkhur an fara zauce wa fa hmmm ALLAH ya rufa asiri dai.

Zahra tana zaune a falo ita da ilham taji wayar ta tana ringing. Zahra yaya mashkhur ne yake kira gashi ilham da wayar take hanun ta ta miqawa zahra. Hannu na rawa zahra ta kar6a ta d'aga wayar, gani nan nazo ki fito. Cikin mamaki zahra tace kazo ina? Nazo inda kike mana ki fito ki gani. Hmmm to ka shigo mana, Aaa ni bazan shigo ba sai dai ki fito, tabb wlh nima bazan fito ba haka kurum a gudu dani in dai ka matsu da son gani na sai dai ka shigo ciki.

Zahra ta qarasa maganar tana kashe wayar, ilham wai kinji yaya mashkhur ne yazo zahra ta fad'a tana bin ilham da ido. Murmushi ilham tai tare da cewa oh ALLAH sarki yaya mashkhur gaskiya so yayi mai mugun kamu, ke in ba so ba kin isa ya ringa kwantar miki da kai duk izzatar shi da muskilancin da taurin kan sa haba zahra ki tausayawa yaya mashkhur haka nan.

Bara naje na lalla6a shi ya shigo kin san yanzu sai yace zai koma in baki fito ba ilham ta fad'a tana miqewa tsaye. Tom shikenan jeki bari naje na d'auko hijabi na zahra ta qarasa maganar tana miqewa. Zahra tana hawa sama ta wuce bedroom d'in su da yake yau mama bata nan, tun da safe ta tafi kano wajan maman ta daga can kuma zata biya ta gidan su Ilham wajan ammi.

Zahra tana shiga bedroom ta bud'e kwaba domin d'auko hijab dan yanzu bazata qara gangan ci zuwa da ba mayafi ko ba mayafi wajan mashkhur ba tasan da akwan matsala. Bayan zahra ta d'auko hijabi ta fara qoqarin saka tai. Aunty zahra ina zuwa haka koh sallah lafila zakiyi ne? Nana da take kwance akan bed ta tambaya.

Aaa fita zanyi yaya mashkhur ne yazo, zaro ido nana tai tare da cewa kai gaskiya dai yana son ki aunty zahra yanzu dawowa yayi duk wulaqancin da kika yi mai. Hararar nana zahra tai tare da cewa wulanqanci mai nai mai? Hmmm kai aunty zahra wlh kyakyawa da shi kike mai abinda kike so sai yaje ya samo wata madadin ki zaki gane duk muskilancin sa amma yake miki nacin nan ai wlh yaya mashkhur yana son ki.

Cije le6e zahra tai a zuciyar ta tace yarinya kenan baki son muguntar yaya mashkhur bane da wlh da kan ki zaki ce karna yadda mu cigaba da zaman aure. A fili kuma cewa tai hmmm nana kenan bazaki gane ba duk bayanin da zan miki. Zahra tana gama refe bakin ta ilham ta murd'a handel d'in qofar bedroom ta shigo.

Kallan ta zahra tai tare da cewa ya shigo ne? Girgiza kai ilham tai tare da cewa wlh yaqi shigowa kin san shi da taurin kai kamar mutanan farko. Amma yace in lalla 6aki ki futo, kinji zo muje na raka ki wlh ba abinda zai miki kinga yadda jikin sa duk yabi yayi sanyi wlh duk ya koma abin tausayi. Ta6e baki zahra tai tare da cewa ai kuwa bazani ba.

Haba aunty zahra dan ALLAH kiyi haquri nima zan raka ki, ba kyau fa mijin ki ne, kar ALLAH yayi fushi da ke. Harara zahra ta watasawa nana tare da cewa karki sake cewa mijina wlh. To na dena amma yanzu zo muje nana ta qarasa maganar tana d'aukar mayafin ta. Zahra bazaki d'an shafa hoda da jan baki ba kamar yadda mama ta koya miki.

Girgiza kai zahra tai tace aaa barni haka kawai ilham. Daga haka zahra da su nana suka rankaya domin yi mata rakiya. Zahra tun kafin su qarasa take jin zuciyar ta tana bigawa fat-fat. Suna qarasawa bakin mota suka ga mashkhur ya bud'e margin mota yana zaune ya kifa kai da sitiyari. Ilham ce ta fara magana da cewa yaya mashkhur, da sauri ya d'ago kai, idanuwan sa sai wani lumshewa suke kamar mai jin bacci.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwan sa suka sauka akan zahra. Ina wani nana ta fad'a hakan murya a sanyaye, kallo d'aya mashkhur yayiwa nana ya kau da kai tare da cewa lafiya qalau. Ilham kallon zahra tai tare da cewa zahra bari mukoma daga can ko mu jira ki. Kafin zahra ta kai ga magana nana taja hanun ilham sun koma can gefe sosai.

Suna barin wajan mashkhur yace ki shigo ki zauna mana karki gaji da tsayuwa. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aaa ai bazan gaji ba ina wani ya hanya da fatan ka iso lafiya. Lafiya qalau zahra yakike kema da fatan kina lafiya. Lpy qalau nake zahra ta fad'a a taqai ce. Futowa daga motar mashkhur yayi sanan ya rufe ya jin gina da motar ya hard'e hanuwan sa biyu akan qirji yana kallon zahra.

Zahra ina son ki ina qaunar ki dan ALLAH ki dena wahalar dani ki amince dani. Haba yaya mashkhur ni nake wahalar da kai ma yanzu kana so sabida zuciyar ka da kan ka sai na tauye kai na na cigaba da zama da kai al halin bana son ka. Rintse ido mashkhur yayi ji yayi kamar zahra ta watsa mai ruwan zafi a zuciyar shi. Nunfasawa yayi tare da cewa aaa zahra ba haka nake nufi ba.

Dan ALLAH kiyi haquri a duk abinda nai miki a baya nason da shi kike kallo na shi yasa kika kasa amincewa da soyayyah ta. Amma wlh zahra ina qaunar ki tsakani da ALLAH tunda nake ban ta6a qaunar wata mace ba sai ke ban ta6a son wata halitta ba sai ke akan ki na fara sanin soyaya, ba 'yar da ta ta6a bani sha'awa a rayuwa zahra sai ke ki tausaya min mana.

Zahra ta tausayawa mashkhur matuuqa ganin yadda ya canza kuma tabbas ta san maganar da yake fad'a har zuciyar shi take. Zahra ji take kamar taje ta rungume yaya mashkhur sabida tsabar tausayi. Amma dakewa tai tace aaa yaya mashkhur ka rabu dani haka pls wlh bazan amince ba har dai soyayar da kake min gaskiya ce ka tsahirtamin na wuta.

Ina so na roqeka wata alfarma yaya mashkhur dan ALLAH a matsayi na na wadda kake so kuma matar ka. Jiki na rawa mashkhur yace in sha ALLAH nai miki alqawar zan mike ko mene ya fad'i maganar yana qoqarin ruqo hanun ta. Da sauri zahra taja baya tare da cewa aaa yaya mashkhur bana so ka rabu dani karka sake ta6a min jiki na.

Da sauri mashkhur yaja baya jiki na rawa yace tom shikenan zahra tinda bakya so bazan sake ta6aki ba na dena kiyi haquri mai kike so nai miki ina ji?. Yaya mashkhur ina so daga yau sai yau kar ka sake cewa kana sona ka fita daga hanya ta ka manta dani a rayuwar ka ka manta ni matar kace, ka manta ni a rayuwar ka har abada. ka dena zuwa waje na da zummar soyayyah yaya mashkhur ina yi maka son 'yan uwan taka amma bazan iya zaman aure da kai ba sabida bana son ka a matsayin miji.

Wani dogwan nunfashi mashkhur yaja da kyar ya iya bud'e baki ya cewa zahra shine abinda kike so nai miki?. Eee yaya mashkhur shine abinda nake so kai min. Tom zahra shikenan in sha ALLAH zanyi qoqarin ganin nayi miki hakan in dai zai faran ta miki, daga yau bazan sake zuwa wajan ki ba tinda bakya so kuma zan manta da ke, kamar yadda kikace amma ina so na gaya miki ina QAUNARKI bazan ta6a iya dai na so ki ba zahra.

Mashkhur yana qarasa fad'ar haka jiki na rawa ya shige motar shi ya tayar, sanan mai gad'i ya bud'e mai get ya fuce zuciya a raunane. Wasu zafafan hawayan tausayin mashkhur ne suka zubowa zahra, ji take kamar ta kwallara mai kira ya dawo. Ilham da nana qarasowa sukayi hankalin a tashe ilham tace lafiya zahra kike ko ka mai yayi miki?. Aunty zahra mai kika yi mai haka ne nana ta watsawa zahra tambayar tana tsare ta da ido...........

Hmmm nima zuciya ta ta tsinke naso na qarasa muku page d'in nan duk da saura kad'an na gama amma tausayin mashkhur bazai bar ni ba?. πŸ˜₯

Amma dai zahra banga laifin ki ba tinda ba'a so dole. 😍

Mu had'e a next page.
[23/04, 8:29 pm] Oum Farhan❀️🩷: ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ.

BY BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing..............

*page 117*

Ilham da nana qarasowa sukayi hankalin a tashe ilham tace lafiya zahra kike ko ka mai yayi miki?. Aunty zahra mai kika yi mai haka ne nana ta watsawa zahra tambayar tana tsare ta da ido...........

Share hawayan ta zahra tai tare da cewa ni ba abinda nai mai kuma shima bai min komai ba, daga haka zahra ta wuce tabar nana da ilham a tsaye. Kai aunty ilham ko dai wani abu tai mai? Nima ban sani ba nana ALLAH ne dai ya barwa kan sa sani. Kai amma aunty zahra ta cika taurin kai inaga fa ta sake cewa bata son shi. Hmmmm nana zahra fa bata da taurin kai sosai ALLAH ne dai yasan mai ya faru kuma ba lallai ne ta gaya mana ba kawai mu rabu da ita zo mu koma ciki mu d'ora abinci..........

MASHKHUR.

Yana fita titi ya parking d'in motar shi a gefan titi sanan ya kifa kan sa akan sitiyari, yana futar da waucin baqin ciki da 6acin rai daga bakin sa. Mashkhur tinda ya kifa kan sa akan sitiyari sai da yayi awa d'aya a haka ko kwakwaran motsi bai ba. Wani irin baqain cike ne da qaunar zahra suke sake lulu6e mai zuciya. Hmmmmm ya zama dole na ne mawa kai na mafita kafin soyayya zahra ta qarasa kashe ni.

Mashkhur ya fad'i hakan a zuciyar shi, mashkhur ya fara tinani iri-iri a ciki tinanin ma har da na shaye-shaye. Mashkhur gani yake gwara ya koma yin shaye-shaye ko zai manta da zahra cikin sauqi dan mashkhur ya d'au alqawarin bazai sake roqkon zahra akan taso shi ba zai qoqarin ganin ya cika mata burin ta ko d'an qaunar da yake mata.

Da tinani tanani nan mashkhur ya tayar da motar sa ya kama hanyar tafiya kano. A hankula mashkhur yake tafiya yana tafiya yana tinanin mafita. Mashkhur sabida tsabar tinane-tinane da slow driven d'in da yake sai wajan qarfe 3 na yamma ya koma gida. Yana shiga cikin gidan bai zame ko ina ba sai d'akin sa. Bayan mashkhur yayi alwala yayi sallama kwanciya yayi ya fara tinanin taya zai manta da zahra kuwa?.

Hmmmm anya zan iya kuwa? Mashkhur ya tambayi kansa cikin rashin sanan mafita. Wani baqin ciki ne ya sake rufe mashkhur ko ta ina in ya tina wai zahra ce take gasa shi kamar masara. Yana cikin tinanin nan yaji wayar shi ta fara ringing, rai ba dad'i mashkhur ya murgina ya d'auki wayar dan ganin mai kira. Da mashkhur bazai d'aga ba amma daya ga sunan ahmad sai ya d'aga zuciya cike fall da damuwa.

Ko da mashkhur ya d'aga wayar bai iya cewa komai ba sabida tsabar damuwa. Mashkhur ina qofar gida in kana nan ka fito. Wani gajeran nunfashi mashkhur yaja tare da cewa ahmad bazan iya futowa ba bana jin dad'i kawai ka shigo ina jiran ka. Daga haka mashkhur ya ajiye wayar a gefe zuciya cike da tsantsar damuwa.

Baki d'auke da sallama ahmad ya murd'a handel d'in qofar bedroom d'in mashkhur ya shigo,. Yana shigowa ya nufi kan bed ya zauna a gefan mashkhur, da kyar mashkhur ya iya amsa mai sallmar tare da cewa sannu da zuwa. Yauwa dai mashkhur mai yake damun ka haka ko dai tinanin matar taka kake?. Da kyar mashkhur ya iya cewa hmmm ahmad kasan mai ya faru kuwa?.

Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa aa. Hmmm yanzu fa daga wajan ta na dawo kaga magaganun da ta gaya min marasa dad'in sauraro kuwa?. Kai mashkhur ita zahra da kan ta kuma, ahmad kenan ai yanzu zahra ta wuce yadda kake tunani tana gab da d'ora min hawan jini da ciwan zuciya,. Kai gaskiya abun bai yi dad'i ba mashkhur amma dai haka zaka daure har ka shawo kan ta.

Tabb ai na d'aukar wa kai na alqawarin bazan sake zuwa wajan ta ba kuma zan manta da ita kamar yadda ta buqa ta ahmad. Cikin tausayawa ahmad yace kai mashkhur haba dai anya zaka iya kuwa shifa so ba riga bane da zaka cire a duk lokacin da kake so. To ahmad ya zanyi ita tace na manta da ita ba sai nayi hakan ba mashkhur ya qarasa maganar yana had'eye wani qululun baqin ciki.

Kai gaskiya dai zahra tayi fushi da kai sosai mashkhur amma ita da na san ta mai haquri da sauqin kai. Wlh ahmad da na son haka zahra za tai min da banje wajan ta ba, tinda nake ba wanda ya ta6a dubar ido na yace min ya tsane ni sai zahra. Kamar yadda ba wanda ya ta6a dubar idon ta itama yace ya tsane ta ba sai kai, ahmad ya fad'i hakan yana tsare mashkhur da ido.

Jim mashkhur yayi yana tunani tabbas kuwa bazai musa maganar ahmad ba sabida yasan haka zancan yake shima ya sha kallo tsakiyar idon zahra yace mata ya tsane ta, kuma abinda yayiwa zahra a rayuwa na quntatawa ko rabin sa ba tai mai ba dole taji tsoran zama da shi. Gaskiya ne ahmad hakane amma ban ta6a tianin zan so zahra a rayuwa ta ba kai ko mai kama da ita ma amma sai gashi yau soyayar zahra tana neman ta zautar dani.

Mashkhur sai kana yi kana haquri fa, amma tabbas ni nasan zahra zata so ka mashkhur in dai kabi komai a sannu. Kai ahamd anya kuwa zata so ni?, zata soka mana tinda har ta iya yima addu'o'i karyewar asiri ka sha kaga ai da ta d'auke ka a maqiyi ko da gaba da baza ta ta6a yima hakan ba shima wanan ai ba qaramin so bane. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa hakane ahmad amma gaskiya ina ga tayi min ne kawai amma ni nasan zahra bata so na.

Aa mashkhur kar kace haka, ni ina tianin zahra tana son ka amma ita kan ta baza ta sheda tana son ka ba, ko dan zaman da kukayi duk da bana dad'i bane soyayay zata iya shiga tinda kai gashi ka fara son ta. Ko baka son soyayya tana iya komawa qiyayya ba ko kuma qiyayya tana iya komawa soyayya. Yanzu inaga da za'a cewa zahra wani abun ya same ka sai hankalin ta yafi na kowa tashi.

Sabida duk wata qiyayya da tai yawa in dai ta zaman tare ce to tabbas da akwai 6oyayyiyar soyayya a cikin ta wanda ku kan ku baza ku iya gane hakan ba sai wani abun ya samu d'aya daga cikin ku. Hmmm mebi ahmad hakan zata iya faru nima nasan da hakan amma ina kokwan tan zahra tana so na, wlh ahmad da nasan zan fara son zahra kuma zatai min wasa da hankali na a lokacin da muke tare a rasha da tini na nemawa kai na mafita.

Mafita kuma mashkhur mafitar me? , cije le6e mashkhur yayi tare da cewa ai da ranar da muka sa qafar mu a russian ni da ita, da a ranar zan kawar da abinda yake tsakani na da ita, kaga da nayi hakan da tini ma in zamu dawo da d'an mu zamu dawo nigeria harma da wani ciki kaga ai ko tana so ko bata so dole ta yadda mu cigaba da zaman aure. Dariya ahmad yayi sosai bayan ya tsagai ta yace ai kuwa dai mashkhur wlh da tini an wuce wajan................

To fa yanzu mashkhur duk wani lamarin zahra yayi watsi da shi gefe, ya rage yawan tunanin ta, ya mayar da hankali sa wajan aikin sa, amma mai ma kwan son zahra ya ragu a zuciyar mashkhur sai ma qaruwa da yake yi. Dan yanzu duk yabi ya canza ya d'an rame ya yayi wani haske kana ganin shi zaka sheda yana cikin matsanan ciyar damuwa. Amma yana qoqari wajan dakewa, dan yanzu ya dena turawa zahra text message kuma ya dena yiwa kowa zancan ta.

KADUNA.

To fa abu kamar wasa kwana biyu zahra ta rasa mai yake damun ta tun sanda ta cewa mashkhur ya rabu da ita yasa qafa yabar gidan bata sake samun nutsuwa ba. Kullum a cikin tinanin mashkhur zahra take ko bacci kirki bata iya, ita sam ta rasa mai ya sa ta kasa manta da abinda tai wa mashkhur. Ga yawan mafarkan sa da tinanin sa da take, kullum cikin jiran message d'in mashkhur ko kiran sa zahra take amma shiru.

Please Login or Register in order to submit comment