Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Har lokacin zahra bata juyo da fuskar taba, ahmad kuwa cewa yayi! Qanwata ya jikin naki?.

Da kyar zahra ta iya jiyo da kanta ta kalli ahmad cikin dashashiyar murya tace da sauqi. Da kyar maganar ta fito dan in bama kasa kunne kayiba bazakaji abinda tace ba. 6angaran mashkhur kuwa, nan da nan ran shi ya 6ace sosai, ganin yanda zahra ta share shi, kuma sai gashi yanzu tana kula ahmad. Ahmad kuwa cewa yayi masha ALLAH" ALLAH ya qara lfy.

Da kyar zahra ta iya cewa ameen,. Daga haka ahmad ya taro ruwa zafi a dispense, sanan ya fara had'awa zahra t. 6angaran mashkhur kuwa shima sharewa yayi ya zaro wayar shi ya fara dannawa abinsa, zuciya cike da baqin cikin abinda zahra tai mai. Ahmad kuwa yana gama had'a mata t d'in ya ajiye a gefe sanan ya qarasa gadan d'in zahran, domin miqar da shin dan ta samu ta zauna.

Bed d'in mai spring ne, dan haka ahmad bai sha wahala ba wajan tayar da bed d'in. Murd'awa kawai yayi, sai ga zahra a zaune. Daga haka ahmad ya koma inda ya ajiye cup d'in sanan ya d'auko ya miqawa mashkhur yana cewa! Mashkhur gashi ka bata in cikinta ya warware sai a bata abincin. Kamar mashkhur bazai kar6a ba sabida yaji haushi abinda zahra tai mai sosai.

Amma dai sa ya daure ya kar6i cup d'in tare da mayar da wayar sa aljiwu, yana miqewa. Ahmad kuwa gefe ya koma ya zauna shima ya d'auko wayar shi ya fara dannawa. Mashkhur yana qaraswa ya zauna a gefen zahra ta yanda zai iya bata t d'in a baki. A hankula mashkhur ya d'ebo t d'in a spoon sai da ya bari ya sha iska sanan ya kai bakin zahra.

Da mamakin mashkhur sai yaga zahra ta sake kawar da kanta gefe, kamar d'azu dai. Nan da nan mashkhur ya sake zuba mata kwala-kwalan idanuwansa yana d'an zuba mata harara ta gefen ido tare da qare mata kallo. Fuskarnan tata har wani jaja-jaja take, da yake rigar jikinta blue ce, wato ta majinyatan asibiti, sai ta sake haske sosai ga gashin nan nata ya bazo baya tubarakalla har ya fara gangarowa ta gefan fusaka ta yana rufe mata fuska.

A hankula mashkhur ya kai hanunsa kan fuskar zahra ya d'an gyara mata gashin ta daya gangaro fuska ya mayar mata da shi baya. Sanan ya qara miqa mata spoon d'in t d'in a baki. Sake kawar da kai zahra tai a karo na biyu. Nan da nan ran mashkhur ya sake baci dan shi ya tsani irin wanan abun, kuma shi sam bazai iya rarrashi taba ko baw ta baki akan ta sha t d'in ba.

Haka mashkhur ya danne zuciyar shi ya sake miqa mata spoon d'in a karo na uku, nan ma zahra qin kar6a tayi, sai ma hawayen daya fara gangarowa daga idanuwan ta. Mashkhur kuwa maimakwan ya rarrashi zahra miqewa yayi tare da ajiye cup d'in t d'in a table d'in kusa da gadon, sanan ya bar wajan.

Direct wajan ahmad mashkhur ya wuce tare da zama a kusa da shi. Da sauri ahmad ya d'ago tare da cewa! Yanaga kazo nan ko harka gama bata t d'in ne. Ya mutsa fuska mashkhur yayi tare da cewa! Aa bata shaba. D'an zaro ido ahmad yayi tare da cewa! Kai sabida me? D'aga qafad'unsa biyu mashkhur yayi tare da cewa! Oho gata can kaje ka tambaye ta mana.

Wani irin kallo ahmad ya watsawa mashkhur tare da cewa! Kai baka tambaye ta da lilin da yasa taqi sha ba kenan?, cikin qosawa da maganar mashkhur yace eh ban tambaya ba, amma ina tinain ta qoshi ne shi yasa. Baki saki ahmad ya kalli mashkhur tare da cewa! Kai kamarya ta qoshi, mashkhur anya lafiyar ka qalau taya mutumin da bai ci abinci ba tun jiya kace a qoshe yake.

Gyara zama mashkhur yayi tare da cewa! Eh ai ba abin mamaki bane,, tinda dah tana jin yunwar ai bazata qi shaba. Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Hmm ALLAH ya kyauta, daga haka bai sake cewa! Komai ba ya nufi bed d'in zahra. Lokacin da ahmad ya qarasa wajan zahra ya sameta fuska cike da ruwan hawaye sai shash shiqa take a hankula.

Cikin tausayawa ahmad ya yago tissue paper ya miqawa zahra tare da cewa! Pls qanwata ki dena kuka, kinji kowa da irin qaddarar shi ke a haka taki tazo dan ALLAH ki qar6i tissue d'in nan ki goge fuskar ki. Hannu na rawa, zahra ta fara qoqarin d'aga hanunta domin qarfar tissue d'in amma ina sam ta kasa.

Da sauri ahmad yace it's okay sorry na manta fa kinji rauni sosai a hannayan naki ki bari ba sai kin wahalar da kanki ba bari na kira mashkhur ya goge miki. Ahmad ya juya kenan zai kira mashkhur zahra tace aa ni bana so ya gogemin kawai ka barshi. Tan gararai abinda zahra ta fad'a a kunan mashkhur da yake yana da lafiyar ji ba laifi, da yake kuma maganar cikin sautin kuka tayi ta d'an futo da qarfi. Nan da nan wani haushi ya sake rufe mashkhur.
.
Ahmad kuwa girgiza kai yayi tare da cewa! Aa ai baza a barshi ba bari na goge miki kinji qanwata ya qarasa maganar yana, sa hanunsa a fuska zahra riqe da tissue yana goge mata. Mashkhur kuwa har cikin ransa yaji wani abun wanda bai masan mene ne ba, shi ba farin ciki ba kuma ba baqin ciki ba, kawai dai yaji abin ya tsaya mai a rai ne. Bayan ahmad ya gama gogewa zahra fuskar t d'in ya d'auko ya fara bata.

Ai kuwa abin mamaki sai gashi zahra ta bud'e baki tana shan t d'in, nan da nan wani malulun baqin ciki ya sake tsayawa mashkhur a rai. A zuciyar shi yace lalai ma yarinyar nan ta raina min hankali wato nine bazata yarda na bata ba koh?. Mashkhur ya watsawa kansa tambayar amma ina ba amsa, mashkhur ji yayi bazai iya jure wannan abin ba dan haka ba 6ata lokaci ya tashi ya fuce daga room d'in.

Ahmad kuwa ci gaba da bawa zahra t d'in yayi a baki, jikinsa duk yayi sanyi saka makwan ganin yanda mashkhur ya canza mai lokaci guda ba wani kwakwaran dalili. Bayan ya gama bata shayin ya so ya bata abinci amma zahra tace ita sam bazata iya ciba, haka dai ahmad ya gangad'a ya bata maganin sanan doctor ya shigo, yayi mata allura, ta koma bacci abinta.

Ahmad kuwa yana fita yaga ba mashkhur ba alamun sa a reception, dan haka hanyar waje ya wuce. Yana fita daga asibitin ya hango mashkhur zaune a kan boot mota. A hanzarce ahmad ya wuce wajan mashkhur d'in yana qarasawa shima ya hau kan boot d'in motar kamar yanda mashkhur yayi, shima ya zauna.

Yana zama ya cewa! Mashkhur ashe nan ka fito? Da kyar ya iya cewa uhumm, shiru ahmad yayi yana qarewa mashkhur kallo. Fuska ba walwala, gaba d'aya ya canza ya zama wani irin. Mashkhur wai me yake daminka ne?. Girgiza kai mashkhur yayi alamun babu komai. Cikin mamaki ahmad yace kai mashkhur bana san iskanci sai kace mai azumin magana.

Murya a shaqe mashkhur yace ahmad na gaji gida zan tafi, cikin mamaki ahmad yace gida kuma mai zakayi a gida mashkhur?, rai a 6ace mashkhur yace wanan wace irin tambayace mai akeyi a gidan. Dama mashkhur a fusace yake qiris yake jira, shi yasa ya fara fad'in. Murya a sanyaye ahmad yace to kayi haquri zuwa anjima sai mu koma dama ai ba kwana zamuyi ba.

In ta farka taci abinci dare sai mu tafi, ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Okay. Daga haka mashkhur bai sake cewa komai ba ya sauko dada boot d'in motar ya shige mota ya ware A C abinsa zuciya a cunku she da abinda zahra tai mai.
To su mashkhur basu suka bar asibint ba sai wajan tare na dare.

Sai da zahra ta farka ahmad ya bata abinci dare, sanan ta koma bacci, suka tawo. Da yake asibitin mara lpy baya kwana da kowa da akwai majinyatan dare a can.
Su suna qara sowa gida, mashkhur yacewa ahmad sai gobe daga haka yayi fucewar shi ko amsar ahmad bai tsaya jiba. Ahmad kuwa ta6e baki yayi a zuciyar shi yace kaji da shi, dan shi yanzu ya fara gajiya da baqin halin mashkhur d'in.

Mashkhur yana shiga ciki bai tsaya ko ina ba sai toilet, yana shiga yayi wanka, bayan ya gama wanka brush yayi sanan ya d'auro alwala, ya fito. Yana fitowa ya sa jallabiya ya fara gabatar da sallah. Bayan ya idar da sallah canza kayansa yayi zuwa na bacci sanan ya kwanta akan bed. Yana kwanciya yaji wayar shi da take gefan sa ta fara ringing. Hannu yasa ya janyo wayar tare da zuba mata kyawawan idanunsa.

Sunan dady ne ya fito 6aro-6aro akan screen d'in wayar, jim mashkhur yayi kamar bazai d'aga ba dan harma ta kusan qatsewa sanan ya d'auka tare da sata a hand's free. Hello dady, ina wuni mashkhur ya fad'a gabansa na dukan uku-uku. 6angaran dady kuwa cewa! Yayi sallama'alai ka, tinda kai baka iya sallamar ba. Murya a sanyaye mashkhur yace! wa'alaikassalam dady a fuwan.

Hmmm mashkhur kenan ka girma baka san ka girma ba, dan ALLAH ka d'inga sanin ya kamata. Tom shikenan dady in sha ALLAH, zan gyara. Dady cewa yayi ALLAH yasa ya kuke da fatan kuna lpy?. Nan ma gaban mashkhur sai da ya sake fad'uwa da dady ya tambaye shi amma sai ya dake yace muna lpy qalau dady, kuma da fatan kuna lpy.

Muma muna lpy mai sunan baba, wai ina mamana ne? Dady ya watsawa mashkhur tambayar on expected, nan da nan gaban mashkhur ya sake fad'uwa amma sai ya dake da cewa! Tana nan dady. Okay jeka ka kai mata wayar mu gaisa naga in na kirata bata d'auka. Jim mashkhur yayi kafin yace am ehh uhmm dama wayar tata ce ta fad'a bayan drowar kicin shi yasa kaji in ka kira bata d'auka.

To sabida mai baka d'auko mata ba? Hmm zan d'auko mata ne dady in sha ALLAH. To shikenan yanzu kaje ka kai mata wayar. Jim mashkhur yayi na wasu daqiqu can kuma yace! Am ehh to dama uhmm dama dady bata da lpy tana! Hmm!! tana!! tana!! zazza6i take kuma ta sha magani ta kwanta sai da zuwa gobe. Shiru dady yayi can kuma yace mai sunan baba ko dai wani abun ne ya faru kuma?.

Dady ya watsawa mashkhur tambayar cikin tuwuma. Haba dady mai kuma zai faru kuwa mai kake tinani?. Komai ma ina tinanin ko wani abun kayi mata ne?,, kai dady mai kuwa zan mata mashkhur tambaya gabansa na sake fad'uwa?. Murmushi dady yayi tare da cewa! Ai kafi kowa sani, shiru mashkhur yayi bai ce komai ba,, 6angaran dady kuwa cewa! Yayi zuwa goban dai ka bugomin mu gaisa da ita, amma dai karka manta Yarinya ce kabi a hankula sosai.

Daga haka dady ya gintse wayar, mashkhur kuwa daskarewa yayi a kwance, yana mamakin magagganun dady. Can kuma yace hmm dady kenan, bama kasan mai yake faruwa ba lalai ma kai ta wanan kake. Daga haka mashkhur bai ya kashe wayar shi gab d'aya ya shige cikin blanket ya rufe idansa kamar mai bacci,, yana sake mai mai ta maganr da dady a zuciyar shi, wai!! amma dai karka manta yarinya ce kabi a hankula sosai' ai mashkhur bai san sanda wani murmushi ya su6uce mai ba.............

Jumma'atul kareem........ Ayi huton weekend lpy, sai mun had'e a next page. Much LOVE ❤️ my fan's ALLAH ya barmu tare...........

ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 83*

Daga haka mashkhur ya kashe wayar shi gaba d'aya ya shige cikin blanket ya rufe idanuwan sa yana sake mai mak ta maganr dady a zuciyar shi, wai!! amma dai karka manta yarinya ce kabi a hankula sosai' ai mashkhur bai san sanda wani murmushi ya su6uce mai ba.............

A zuciyar sa yace dady kenan har yanzu baka gama sanin koni wanene ni ba, ai mace bazata ta6a canza min ra'ayi na ba,, macan ma wai zahra. Hmm dady baza ku gane ni ba mayan mace ba ne sai na dawo muku da 'yar ku salin alin ya qarasa maganar yana saki ajiyar zuciya. Tom da saqe-saqe nan bacci yayi awan gaba da mashkhur.

Washe gari............

Bayan mashkhur ya gama breakfast wanka ya shiga, yana futowa ya fara shiryawa a hanzar ce, duk hankalinsa yayi wajan zahra, domin yaje yaga ya jikin nata yake. Yana gama shiryawa yaji ana knocking d'in qofar gida,. Da sauri mashkhur ya d'suko turare ya fara fesa turaren sai da ga gama fesawa sannan ya kama hanyar fita, dan yasan ahmad ne yake knocking d'in gidan.

Mashkhur yana bud'ewa kamar yanda yayi tunani ahmad ne tsaye a bakin qofar, hannu mashkhur ya miqa mai tare da yimai sallama, cikin sakin fuska shima ahmad d'in ya miqawa mashkhur hannu tare da amsa mai sallamar. Daga haka suka saki hanun junan su har mashkhur zai futo ya manta bai d'auko wayar shi ba.

Kallan ahmad yayi tare da cewa! Ahmad jeka ka kunna motar ganinan futowa na manta wayata a ciki, daga haka mashkhur ya koma ciki shi kuma ahmad ya wuce qasa. Mashkhur ba 6ata Lokacin ya d'auko wayar shi ya futo daga gidan, yana futowa yasa key ya kulle qofar sanan ya fara sauka daga step d'in benan. Yana zuwa ya tarar da ahmad har ya kunna motar, dan haka ba 6ata lokaci mashkhur ya shiga, suka fuce daga gidan.

Suna cikin tafiya mashkhur ya kalli ahmad tare da cewa! Ahmad naga kamar ba hanyar asibitin kake bi ba, wata hanya daban naga kake bi. Dan kallansa ahmad yayi tare da cewa au kai bama kasan in da zamu ba kenan?,, ina muka nufa? Mashkhur ya watsawa ahmad tambayar. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! Lalai ma mashkhur kama manta zamu kotu yau koh?.

Koto kuma mai zamuyi can? Baki a sake ahmad yace au wai har ka manta da shari'ar zee koh?. Da sauri mashkhur ya d'an dafe kansa tare da cewa! Oho yanzu na tuna. Ahmad kuwa cewa yayi hmm mashkhur kenan sam baka da adalci, yanzu dan baka qaunar zahra har ka manta da zee ce ta kusan salwantar mata da rayuwa kenan?.

Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba dan shi sam bayasan yanzu su fara musayar baki shida ahmad. Ahmad kuwa gyad'a kai yayi tare da cewa! ALLAH ya kyauta, mashkhur kuwa a zuciyar shi amsawa yayi da ameen. Daga haka ba wanda ya sake cewa! Komai har suka qarasa koton, lokacin da su mashkhur suka qarasa koton sai da suka d'au awa biyu kafin a shiga shari'a.

Kuma sunci sa'a shari'ar su ce ta farko, ita za'a fara. To fah zee sai da aka d'aukar mata lauyoyi har guda uku, madadin zahra da aka d'aukar mata lauya guda d'aya. Amma abin mamakin shine lokacin da lauyan zahra ya lissafowa zee qunshin tuhumar da ake mata wato aika-aikar da ta aikatawa zahra, ba 6ata lokaci tace kwarai ta aikata duk abinda ake tuhumar ta dashi kuma tana buqatar sassauci.

Ana cikin hakan wani d'an sanda ya shigo da sauri riqe da fayal a hanunsa, yana zuwa ba 6ata lokaci ya roqi mai shara'a munti biyu, akan yanaso ya gabatar da wani abu maimahimmanci game da zee wanda ake tuhuma da laifi. Mai shara'a kuwa cewa yayi ya bawa d'an sandan dama ya gabatar da abinda yake so ya fad'a. D'an sanda kuwa fara magana yayi kamar haka.

Ya mai shari'a Dama abinda nake so na fad'a game da wana yarinyar wanda ake qara shine!! Mun dad'e muna nemanta a garin nan saka makwan sunan ta ya futo dumu-dumu, akan masu laifi da muke nema a baya wato! Wanda suke safarar mugagun kwayoyi. Wani abin mamaki shine! ashe 'yan sanda sun dad'e suna neman zee sabida mai laifice.

D'an sanda ci gaba da magana yayi da cewa! Dan haka mai shari'a munaga yakamata kawai a yau d'in nan a had'a a yanke mata huncinta na, yun qurin kisan kai dana safarar muyagun kwayoyi da tai. Hmmmn ranarfa zee da iyayanta sunga mugun tashin hankali,, daga qarshe dai an yankewa zee hukunci shekara goma (10 YEARS) a gidan yari tare da cinta tarar kud'i mai tarin yawa.

Haka dai zee da iyayan zee sukai ta kuka suna ji suna gani aka tafi da zee. Ahmad kuwa zuciyar shi fari kal kamar ya zuba ruwa a qasa ya shanye, mashkhur kuwa ji yayi ya d'an tausayawa zee kad'an, ko dan dai zaman taran da sukayi. Ba 6ata lokaci ahmad da mashkhur suka futo daga koton suka wuce motar su, suna zuwa suka shiga ahmad yaja motar zuciya cike da farin ciki.

Mashkhur kuwa ta wani 6angaran sai yaji zuciyar shi ta d'an yi mai dad'i dan ko ba komai an biwa zahra haqqin ta.
Tunda ahmad ya futo daga koton bai tsaya ko ina ba sai a cikin asibitin da aka kwantar da zahra. Yana parking d'in motar suka futo" ba 6ata lokaci suka shige cikin hospital d'in, suna shiga basu tsaya a ko ina ba sai a d'akin zahra.

Suna shiga ana gama bawa zahra maganinta na safe, tana zaune cikin blue d'in rigar asibiti fuskar nan tata tayi jajir, ga shinta kanta ya bazo har baya dan ko d'an kwali babu a kanta, sai farin bandejin da aka nad'e mata goshi da shi. Ba 6ata lokaci ahmad da mashkhur suka qarasa bakin gadan zahra har suna had'a baki wajan cewa ya jikin naki?

Fuska ba walwala da kyar zahra iya iya cewa da sauqi,. Sosai zahra ta had'e rai fuskar nan tata ba walwala ko alamun fara'a. Mashkhur kuwa jigum yayi a gefe ya zubawa zahra manya idanuwan nan nasa yana qare mata kallon. Ahmad kuwa murya a sanyaye yace! Zahra lfy dai ko? Ya mutsa fuska zahra tai tare da cewa! Ina san magana da dady ne.

mashkhur da yake gefe sai da gabansa ya fad'i rass rass, shima ahmad d'in sai da gabasa ya d'an fad'i sabida sam baya fatan dady yaji lamarin nan yasan baza'a kwashe da kyau ba. Kwantar da murya ahmad yayi tare da cewa! Haba qanwata dady kuma ki bari kiji sauqi mana kinji qanwasa. Da kyar zahra ta iya girgiza kai tare da cewa! Aa ni yanzu nake so.

Ajiyar zuciya ahmad ya sauke tare da satar kallan mashkhur da yake gefe, da sauri mashkhur ya d'an girgiza mai akai alamun aa karyayi mata abinda take so,, gyad'a kai ahmad yayi tare da zaro wayarsa a aljiwun sa. Short message ya turawa mashkhur, ba komai message d'in yake cewa ba face, ka kashe wayar ka zan kiraka yanzu, in yaso sai nace wayar dady a kashe take.

Mashkhur yana gama karanta sakwan yayi sauri ya kashe wayar shi tare da mayar da ita aljiwu, zahra kuwa sam hankalinta bai kai kan mashkhur da yake gefan ta ba, da yake da gyar take iya juya kan nata. Ahmad kuwa yana ganin lokacin da mashkhur ya kashe wayar, yana kashewa ahmad ya buga mai a hand's free yasa ta dan zahra taji, Ai kuwa yana bugawa kamar yanda suka tsara wayar tace a kashe layin yake.

Gyara zama ahmad yayi tare da cewa! Qanwata kinga Na buga a kashe, ki bari zuwa anjima sai na sake bigawa. Gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Tom yaya ahmda ALLAH ya kaimu, zan sha ruwa ina jin qishirwa, zahra ta fad'a murya a sanyaye. Da sauri ahmad ya d'auko ruwa ya zuba a cup tare da miqawa mashkhur yace mashkhur gashi ka bata ta sha.

Kafin ma mashkhur ya kai da kar6ar cup d'in suka tsinkayi muryar zahra tana cewa! Aa nifa bashi nace ya bani ba kai nace ka bani yaya ahmad. Daga ahmad d'in har mashkhur jin maganar sukayi kamar almara kuma sam basu ji dad'i ba musamman ma mashkhur d'in. Ahmad kuwa jiki ba kwari ya fara bawa zahra ruwan, a bisa dole yake bata , amma sam baya san ya ringa yawan yiwa zahra wani abun alhalin ga mijinta.

Mashkhur kuwa gefe ya koma ya zauna zuciya cike fal da jin haushin zahra" tunda mashkhur yake a cikin qannan sa tun daga abdul har zuwa kan amir basu ta6a yi mai wanna rashin mutuncin ba sai zahra, kawai mashkhur yana danne zuciyar shine, kuma yasan kusan ta sular shine hakan ta samu zahra, amma wlh da ko ta kanta bazai bi ba, dama tun da can ba harkar ta yake shiga ba.

To haka dai ahmad da mashkhur suka wani a asibitin" zahra ta takurawa ahmad sosai akan sai ya bugawa dady, shi kuma ahmad sai ya ringa kawo mata uziri kala-kala, haka dai zahra da ahmad sukai ta fafatawa har dare yayi bacci ya kwashe zahra su kuma suka dawo gida. Mashkhur tunda ya kashe wayar shi a asibiti bai sake kunnawa ba duk sabida kar dady ya kira shi.

Yana shiga yaga wayar zahra tana ta ringing, ba kowa ne yake kira ba face ammi, hannu mashkhur yasa ya d'auko wayar tare da wucewa da ita bedroom d'in shi, kiran ammin yana katsewa mashkhur ya shiga wajan miss call, tunda ga ranar da aka kwantar da zahra a hospital zuwa yau dady yayi mata miss call wajan ashirin, ammi kuwa ta wajan sau goma abdul kuwa wajan sau talatin, ilham kuwa wajan 15 Faruq sau 10, haidar sau 5.

A silent mashkhur yasa wayar tare da ajiye ta a kan table, yana mamakin wanan wana irin so haka iyalinsa suke nunawa zahra? Azuciya shi yace lallai yarinyar nan ta shiga ransu fiye da kowa a cikin gidan, wanna da zasuji abinda ya faru da ita da wani daga cikin su zuciyar shi zata iya bugawa. Daga haka mashkhur ya shige toilet domin yin wanka bacci.

Bayan ya futo daga wanka kwanciya yayi akan gado, yana tinanin yaushe

Please Login or Register in order to submit comment