Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo da abdul gida, abun mamaki shine likitoci sunyi iya binci kyansu amma sam basu gano mai yake damun abdul ba. Hmm zo kaga tashin hankali a wajan 'yan gidan musamman ma momy ammi zahra Hankali su ya tashi sosai. Amma dai duk cikin su hankalim momy ya fi tashin dan duk ta koma kamar mahaukaciya.

Gashi mamanta ta tafi kaduna yau da safe, bare su zauna suyi shawara. Hankali tashe momy ta koma part d'in ta ta d'auko wayar ta da ta dad'e bata d'auka ba tun mutuwar rukee yau kwana hud'u kenan raban momy ta ta6a wayar. Momy tana d'auka taga miss call d'in saratu da yawa. Hankali a tashe momy ta dannawa saratu kira.

Ringing biyu saratu tai parking, saratu ce ta fara magana da yaya halima ina ta kiran ki baki d'aga ba garin yaya mai ya samu rukee ta rasu?. Wani dogwan nunfashi baqin ciki momy taja tare da cewa saratu ina cikin tashin hankali dama ance in zaka gina ramun mugunta ka gina dai-dai kai wataran zaka iya fad'awa gashi ni yanzu na fad'a abu ya koma kai na.

Cikin tashin hankali saratu tace yaya halima mai kike nufi nifa ban gane maganar nan ba. Hmm saratu asirin da mukayiwa zahra shi ya fad'a kan rukee ta mutu. A firgice saratu tace kai yaya halima garin yaya kika fari hakan ta faru?. Nan da nan momy ta kwashe labari ta bawa saratu abinda ya faru tass har zo6an da abdul ya sha madadin mashkhur.

Wani dogwan salati saratu tayi tare da cewa yauzu kina nufo shima abdul yana kan hanyar bin rukee koh?. Cikin tashin hankali momy tace kwarai dan yanzu jikin sa ya fara rikicewa ko magana baya iya yi kuma anje asibi sun ce basu ga komai ba. Amma yanzu abinda nake so ki bigawa boka ki gaya mai komai kice nace yayi maza ya karya asirin abdul.

Wani gauran nunfashin tashin hankali saratu ta saki sanan tace aa yaya halima kin san dai halin boka qa'ida kece zaki mai bayani bani ba tinda ke yayiwa aiki bari na turo miki number shi. Momy ajiyar zuciya tashin hankali ta saki tare da cewa to saratu ba damuwa maza ki turomin. Daga haka sukayi sallama.

Basu wani dad'e da sallama ba momy taji alamun shigowar message tana dubawa taga saratu ce ta turo mata number boka. A hanzarce momy ta kwafi number ta fara rangad'awa boka kiya. Sai da ta kusan katsewa sanan boka ya d'aga. Boka yana d'agawa ya saki wata shed'aniyar dariya. Bayan ya tsagai ta momy gace boka wlh aikin nan ba nasara ya fad'a kan 'ya ta har ta rasu yau kwanan ta hud'i da mutuwar ta.

Wata shu'umar dariya boka ya sake saki tare da cewa duk abinda ya faru dan guduwa ya gayamin na sani, kuma kinyi sakaci sosai ke kika jawo komai akan mai zaki ajiye gyad'ar a fili kuma kin san kina da yara. Cikin muryar kuka momy tace boka qaddara ce ta sani hakan. yanzu d'an ki namiji shima yana kan hanyar mutuwa ko? Boka ya qarasa maganar yana sheqa dariyar mugunta.

Yau single page zan iya yi, sabida inada abunyi.

Happy jumm'a.

Ayi hutun weekend lafiya.

Mu had'u a next page ranar monday.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

TYPING..........

*Page 103*


Cikin muryar kuka momy tace boka qaddara ce ta sani hakan. yanzu d'an ki namiji shima yana kan hanyar mutuwa ko? Boka ya qarasa maganar yana sheqa dariyar mugunta.............

Har cikin zuciyar momy bataji dad'in abinda boka yayi mata ba amma sai ta daure tace boka ka tai maka ka karyamin asirin nan wlh bana so d'ana ya mutu ka tema keni momy ta qarasa maganar tana fashewa da kuka mai cin rai. Wata muguwar dariya boka ya sake saki a karo na biyu. Bayan ya tsagai ta da dariya ya ce! Ke dallah ki dai nai min kuka ki saurare ni kiji da kyau kina jina?.

Da sauri momy ta dena kukan tare da cewa, ee wlh inajin ka boka. Kawai sabida ke ce zan karya miki asirin nan amma da wata ce bazan karya ba sabida in nai asiri bana karyawa. Da sauri cikin rawar baki momy tace yauwa boka nagode wlh ko nawa kake so zan biya ka in dai zaka karyamin asiri nan ya bar kan d'ana.

Ni bana buqatar ko sisin ki kuma ke zaki karya a sirin da kan ki bani ba, in dai kin bi matakan nan asirin kan d'an ki zai karye amma ban ce miki baze mutu ba kuma ban ce miki bazai rayuwa ba, a cikin buyun nan dole ai d'aya in kin karya asirin,. Wani rikitaccan kuka momy tasa tare da cewa haba boka yanzu kana nufin ko asirin ya karye ba lailai ne ya rayuwa.

Wata shed'aniyar dariya boka ya sake saki sanan yace kwarai amma in dai kika bi komai daki-daki zai tashi sai dai in kwanan sane ya qare. Ajiyar zuciya momy ta saki tare da zama akan bed tana cewa boka ina jinka taya zan karya a sirin da kai na?. Sosai boka ya sake sakin dariya sanan ya fara magana kamar haka?.

Nasan abin zai miki wuya bama lailai ne ki iya ba, amma in kina so asirin ya karye tabbas sai kin samu kishiyar ki wato babar yaron da mahaifin yaro ke da duk wandda abin ya dangan ta, ki gaya musu gaskiya abinda ya faru ?. Cikin tashin hankali momy tace to boka mai kake nufi kana nufin in gaya musu ni nai wa mashkhur asiri ya fad'a kan abdul.

Kwarai-kwarai haka nake nufi bama iya haka ba, duk wani asiri da kuka sani kinyi musu a waje na to ya zama dole ki gaya musu gaskiya, kuma harda wanan qanwar taki saratu yadda akai asirin a gaban ta ya zama dole a gabanta za'a karya, ko kin sanar musu gaskiya zancan, in dai qanwarki saratu bata nan to fa kinyi a banza dole sai a gabanta zaki tonawa kan ku asiri, boka ya qarasa maganar yana sheqa dariyar mugun ta.

Cikin tashin hankali momy tace wlh boka bazan iya wanan ba sai dai ka canza min wani. Girgiza kai boka yayi kamar momy tana kusa da shi yace! Babu wata hanyar dole wanan zaki bi in kuma ba haka ba sai dai ki haqura da d'an ki kawai dan saura kwana shida cif in baki karya asirin nan ba ya sheqa barzawu.

Cikin tashin hankali momy tace gaskiya bazan iya ba boka ban shirya kwancewa kai na zani a kasuwa ba. Dariya boka yayi tare da cewa, ga dukkan alamu zaki rabu da d'an ki kuwa boka ya qarasa maganar yana sheqa wata uwar dariya, daga haka boka ya gintse wayar kittt. Wani kuka momy ta saki mai ban tausayi tare da cewa wayyo na shiga uku kai ma abdul rasaka zanyi kamar yadda na rasa 'yar uwar ka rukkayya?.

Abdul kayi haquri sai dai ALLAH ya jiqan ka abdul ka gafarce ni bazan iya tai makwan ka a wanan halin ba momy ta qarasa maganar tana sakin kuka mai cin rai matuqa. Na shiga uku ni halima ALLAH na tuba ka yafemin, nayi ladamar wanan abu dana aika ta yanzu shikenan zan rasa 'ya'ya biyu gashi ni ba wasu 'ya'ya ne dani masu yawa ba, wayyoo ALLAH na ALLAH na tuba............

6angaran abdul kuwa jiki nan yana nan ba dad'i dan yanzu sam baya iya gane waye a kansa zahra kawai yake iya ganewa. Hmmm lokaci guda zahra tayi zuru-zuru ta rame ta shiga matsanan cin tashin hankali kullum tana maqale da yaya abdul bacci ne kawai yake raba su. Gashi ba irin asibitin da ba'a kai abdul ba amma ina basa ganin komai.

Gaba d'aya gidan yayi jigum ba dad'i, kowa tinanin yaya abdul yake, gashi abin yana sake d'agawa kowa hankali ganin har yanzu ba a gano mai yake damun abdul ba. Ba irin asibitin da kwararun likitoci da ba'a kai yaya abdul ba amma ina basa ganin ko wace cuta a tattare da shi. Dady ya gaji da lamarin dan haka ya fara tinanin zai futar da abdul waje a duba shi ko za'a samu nasarar gano mai ke damun sa......

6angaran mashkhur kuwa yana can bai san wace wai na ake toyawa ba dan bai ma san jikin abdul yayi tsanani haka ba,. Duk wasu takaddun sa da suka dace, ya riga da ya tattara ya kai, yanzu dai one week kawai zai qara letter shi ta gurbin aiki tana futo sanan ya koma gida, amma haka nan mashkhur yake jin duk Hankali sa yayi gida, sai ya ringa jin kamar da akwai wani abu mai mahimmanci da ya bari a gidan amma shi kansa ya rasa ko menene shi?.

After 3 days.

Yau abdul ya cika kwana 7 yana cuta kuma yau akayi sadakar 7 rukee. Misalin qarfe goma na dare lokacin duk yan gaisuwar mutuwa sun tafi iya yan gida ne kawai suka rage. Duk mutan gidan suna falo sunyi jigum-jigum, saka makwan rashin lafiyar abdul. Abdul yana kwance a tsakiyar fallo sam baya iya wani kwakwaran motsi nunfashi ma a hankula yake fita.

Zahra da hajiya kaka da ilham suna gefan sa a zaune. Ita kuma ammi da momy suna kujera d'aya a zaune kowannan su zuciya cike da damuwa. Shima dady shida ameer suna zaune a kan kujera, can kuma gefan faruq ne da haidar sai ruma da ta shiga tsakiyar su kamar wata gambun su. Kowa da abinda yake saqawa a zuciyar sa, kuma duk akan abdul ne zuciya ciki da damuwa.

Nan da kwana uku za'a fitar da abdul waje sabida a duba mai lafiya.
Ana cikin wanan zaman sukaji abdul ya sarqafe da tari mai qarfi. Nan da nan hankalin kowa ya dawo kan abdul, amma abin tashin hankali shine abdul yana tari jini yana futowa ta bakin sa. Kafin kace mene tini waje ya rikid'e da salati, zahra kuwa sabida tsabar rud'ewa da tsoran kar yaya abdul ya mutu fad'uwa qasa tai sumamiya.

Nan da nan hankalin mutane ya sake tashi ga abdul abun tausayi tun yana iya tarin da qara harma ya zamana da kyar yake iya yi. Zahra kuwa ana zuba mata ruwa mai sanyi tana farfad'owa ta saki kuku mai sauti, kuka mai tayar da hankali, kai zahra dai kamar mai iskoki haka ta koma duk tabi ta wani fita hayyacin ta ba abinda take iya fad'a sai sunan yaya abdul.

Kai a taqaice dai zahra bata samu sukuni ba sai da aka kira doctor yayi mata allurar bacci ita da badul sanan komai ya lafa. Hmmmmm zo kaga tashin hankali a wajan iyayan abdul biyu. Wato da uwar sa ta haihuwa momy da kuma uwarsa ta goyo ammi, kai abin ba'a cewa komai, dan itama ammi abin ya bata tsoro sosai da sosai dan duk haqurin ta sai da tai kuka.

Haka kowa ya koma d'akin shi zuciya cike da rauni. Su kuwa zahra da abdul sai d'aukar su akayi saka sabida nannauyan bacci da suke saka makwan allurar bacci da akayi musu. Bayan an kai abdul bedroom d'in ammi dama anan ya saba jinyar sa, hajiya kaka da sauran yaran sun wuce makwancin su shima dady haka.

Momy kuwa kasa tsaye tai da zaune hankali ta ya tashe haiqan, sai zagaye take a bedroom d'in ta. Zuciya ta sai wani zafi take, tanajin kewar 'ya'yan ta duka ukun musamman rukkayya da abdul, gashi ita ruma yanzu ta koma wajan su ilham da kwana tunda rukee ta rasu ruma bata sake kwana a part d'in momy ba, sai dai abar momy ita d'aya kwal kamar Mayya.

Kai wlh bazan iya ba bazan ta6a iya jurar rashin abdul ba sai dai dadyn abdul da mahaifiyar shi su kashe ni ya zama dole na tsiratar da abdul daga hanyar mutuwa. Daga haka momy ta fuce daga part d'in fuuuuu kamar wata mahaukaciya. Momy tana fita bata tsaya ko ina ba sai part d'in dady. Lokacin da ta isa part d'in taci sa'a dady bai rufe part d'in ba, dan haka kutsa kai momy tai ta shige.

Tana isa ta wuce sama, momy bata tsaya ko ina ba sai qofar bedroom d'in dady. Sanan ta fara knocking a hankula, tabb lallai yau wai su momy ne suke knocking a nitse ita da take shiga d'aki ba sallama ma?. Momy bata d'au wani lokaci mai tsayi tana knocking ba dady ya bud'e qofar. Cikin mamaki dady yace to, abin mamaki baya qarewa yau kuwa kice kikazo da tsowan daran nan ai ni nayi tinanin maryam ce ma, duk da dai bana sa ran ganinta nasan tana tare da abdul.

Cikin sanyayiyar murya momy tace haba dadyn abdul mene abin mamaki dan nazo ni kenan bazan iya zuwa da daddare ba sai aunty maryam ce zata zo kenan?. Cikin mamaki dady ya kalli momy a zuciya shi yana mamki wai momy ce take cewa ammi aunty a fili kuma cewa yayi kwarai, ai nasan bakya zuwa ne shi yasa, kuma wanan knocking d'in, maryam ce kawai take irin shi. Jinjina kai momy tai tare da cewa ai gashi yau nazo bari dai na shigo daga ciki.

Daga haka dady ya matsawa momy ta shigo sanan ya wuce kan bed ya zauna, itama momy bayan ta rufe qofar dawowa tai ta zauna a gefan dady. Bayan sunyi shiru na wasu lokutan momy tace am dadyn abdul in ba damuwa zamuyi wata magana da kai. Jinjina kai dady yayi tare da cewa ba komai inajin ki?. Gyara zama momy tai sanan tace!

Dadyn abdul dan ALLAH ka tai make ni ina so kai min alfarma guda d'aya. Shima dady gyara zama yayi sanan yace tom fad'i muji ko zan iya?. Uhmm dama gani nai tunda dai abin nan da saratu tai ya wuce kuma kasan mun dena wanan abu, mun shiryu wancan karan ma yarinta ce amma yanzu hankali yazo dadyn, abdul dan ALLAH ka yafewa saratu qanwa ta wlh tana son zuwa yimin gaisuwa ka barta tazo.

Nan da nan dady ya had'e rai tare da cewa, kinga halima ki rabuda ni da maganar nan in wanan ne ya kawoki kawai tashi kije. Nan da nan idon momy ya ja ruwa cikin sanyayiwar murya tace pls dadyn abdul kaga hakan zai iya 6ata mana zumunci kuma karka manta 'yar uwata ce uwa d'aya uba d'aya duk duniya bani da 'yar uwar da ta fita.

Yanzu misalin ace ALLAH bai yiwa rukee rasuwa ba tana da tsawan rai, tom yanzu dan ruma tai wa mijin rukee laifu sai ya rabasu na har abada kaga dadyn abdul in hakan ta kasance bazakaji dady. Fuska cike da hawaye momy ta stuguna a gaban dady cikin kuka tace dan ALLAH dadyn abdul dan annabi, ka gafarce saratu mu cigaba da zumuncin mu wlh nayi ma alqawari makamancin haka bazai sake faruwa ba.

Momy da tai haka sai ta bawa dady tausayi sosai, dady gani yayi duk ta rame kuma yasan har yanzu jimamin rukee bai sake ta ba, kuma ga larurar abdul, hakan ne dady yasa ya tausayawa momy. Cikin sanyayiyar murya dady yace ya isa halima tashi ki zauna komai ya wuce amma a kiyaye gaba. Da sauri momy tace ngd ALLAH ya saka da alkhairi kuma in sha ALLAH daga yau makamancin abdun da ya faru a baya bazai sake faruwa ba.

Ajiyar zuciya dady yayi sanan yace ALLAH yasa. Daga haka momy ta miqe da niyar fita ta bugawa saratu. Dady kuwa cewa yayi ki zauna anan mana zuwa gobe sai ki koma tinda kinga yanzu ba rukkayya ruma kuma tana wajan su ilham. Momy bataji dad'in tayin dady ba amma haka ta danne zuciyar ta ta zauna amma sam hankali momy baya nan Allah- Allah take gariya ya waye. Itama dai momy tasan rashin ammi ne a kusa da shi da ba abinda zai sa yace ta zauna.

Washe gari.

Dady yana fita sallah asubayi itama momy ta wuce part d'in ta. Tana zuwa ta shiga toilet tai wanka ta d'oro alwala sanan ta fito domin sallah. Dan yanzu momy ta dena wasa da sallah, kullum in tai sallah sai tayiwa abdul addu'a ALLAH ya bashi sauqi sanan tayiwa rukayya addu'a ALLAH ya jiqanta, daga haka tai wa ruma addu'a ALLAH ya bata miji na gari.

Hmmm lalai momy anga rayuwa. 🤔

Momy tana idar da sallah ta miqe ta d'auki wayarta ta dannawa number saratu. Har wayar ta tsinke saratu bata d'aga ba. Haka momy tai ta ranga d'awa saratu kira, sai da ta biga sau uku ana hud'un ne saratu ta d'aga cikin muryar bacci tace hello yaya halima lafiya mai ya faru ko abdul d'in ne ya rasu?. Momy cewa tai aaa abdul yana nan dai jiki ba sauqi abin tausayi.............

Double page..............

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Cikin tashin hankali saratu tace wai yaya halima boka bai karya miki asirin bane. Jim momy tai dan sam bataso saratu satan yadda asirin zai karye sabida in tasan boka yace sai tazo a gabanta za'a tona asirin ba lallai ne tazo ba, sai dai abdul ya mutu. Momy tana kawo nan taji saratu tace yaya halima naji kinyi shiru ko da matsala ne? . Momy cewa tai aa ba matsala baki ji abinda nace miki bane?.

Saratu cikin mamaki tace aa banji ba mai kikace? Inaga laifin network ne haka nace miki boka ya gayamin da wana abubuwa zan karya asirin da kai na zan karya, kuma na siyo duk abinda yace zuwa gobe zan gama karya asirin gaba d'aya. Momy tayiwa saratu qaryar nan ne sabida tasan saratu da wayo zata iya gano wani abu da take 6oyewa kuma ita momy sam bata so saratu tasan komai sai tazo ta gani.

Saratu cewa tai yau har naji dad'i Alhamdulilah. Momy cewa tai ameen saratu saura magana ta gaba kina jina?. Ee yaya halima inaji?. Gyara zama momy tai sanan tace gaskiya saratu na gaji da gorin nan da kishiya ta da uwar mijina suke min akan ki. Cikin mamaki saratu tace akai na kuma yaya halima mai suke ce miki akai na ko dai har yanzu laifin da nai basu manta ba.

Da sauri momy tace aaa wlh ai inaga ko dadyn abdul ya manta da laifin da kika aikata, sai gore sike min wai 'ya ta ta rasu bakizo gaisuwa ba a matsayin ki na 'yar uwata qanwata kuma gashi abdul bashi da lafiya ko kizo ki duba shi kullum haka suke cewa. Ajiyar zuciya saratu ta sauke sanan tace yaya halima nima kinsa ina son zuwa wajanki amma karki manta dadyn abdul ne fa yace karna sake zuwa gidan.

Hmmmm saratu kenan tun yaushe dadyn abdul ya yafe miki ko yau ma da kansa yace, ya kamata kizo gaisuwa kuma ki duba abdul kullum sai yayi zancan ki. Cikin farin ciki saratu tace kai yaya halima da gaske bana son irin wanan wasan?. Momy cewa tai kai zan miki qarya ne kema kinsa da dady abdul baya son ki zo da bazan ce kizo ba sabida nima jefani zaki a matsala.

Cikin farin ciki saratu tace kai gaskiya naji dad'i sosai shikenan zumuncin mu zai dawo kamar da in sha ALLAH ni yauma zanzo in kuma mijin nawa bai barni ba sai gobe. Momy cewa tai dama sun dawo ne?. Ee wlh shekaran jiya suka dawo, jinjina kai momy tai tare da cewa to dan ALLAH saratu kizo karki wuce yau ko gobe.

In sha ALLAH yaya halima ni yauma aso samuna zanzo, ke yauwa zanzo nasan zai barni. Tom shikenan saratu in zaki tawo ki bigomin waya ki gayamin. Tom shikenan yaya halima in sha ALLAH. Daga haka sukayi sallama. Momy tana sauke wayar tace alhamdulilah, ALLAH na godema komai yazo min cikin sauqi ALLAH ka yafemin wanan qaryar da na sheka amma nasan in banyi qaryar nan ba ko zan mutu saratu bazata zo ba.

Momy tinani ta farayi kar aje saratu ta bugawa boka ya gaya mata gaskiya lamari. Dan haka gari yana gama wayewa misalin qarfe 8 momy ta d'auki waya ta bugawa boka. Bayan boka ya gama yin dariyarsa ta qa'ida, momy bayani tai mai kan amincewa zata tona asiri a gaba kowa domin abdul ya samu lafiya. Sanan ta roqe shi akan karya gayawa saratu komai sabida in ya gaya mata zata qi zuwa, momy bata sha wahala ba boka ya kyalkyala dariyar sa ta mugun ta sanan ya amince...................

Misalin qarfe 3 ahmad ya kawo qannan sa gidan domin yiwa su ammi gaisuwa. 'Yan mata ne su uku kyawawa masha ALLAH. sun jima a gidan suna sha hira sosai lokaci guda sukaji zahra ta kwanta musu a rai fiye da ilham ma, sabida tana da sakin fuska sosai da sosai. Haka su kai ta kallan zahra sabida gani suke kamar sun ta6a ganin mai kama da ita, amma basu gaya mata hakan ba kawai basarwa su kai.

ABUJA.
MASHKHUR.......

Mashkhur haka nan yau yaji duk duniyar bata mai dad'i, burinsa kawai yasa zahra a idanuwan sa ga wani irin mafarkin zahra da yake ba dare ba rana. A ''yan kwanakin nan mashkhur kawai tunanin zahra yake. Mashkhur yana daga zaune ya fara tinanin wai mai yasa nake yawan tinanin ta da mafarkin ta sanan kuma nake son ganin ta?. Shima kansa ya kasa bawa kan sa amsar tambayar, wata zuciyar tasa tace mai ko dai son ta kake.....

MOMY............

Misalin qarfe 4 momy tana zaune akan kujera tana tunanin rukee, taji wayar ta da take gefan ta tana ringing. Da sauri momy ta kalli wayar, sunan saratu ta gani cikin hanzari ta d'auki wayar hannu na rawa ta amsa tare da karawa a kunan ta tana cewa! Hello saratu kin tawo ne?. Aa wlh yaya halima na tambayi mijin nawa ne yace sai zuwa gobe sai mu tawo tare.
Jinjina kai momy tai tare da cewa to ALLAH ya kawo ku lafiya. Daga haka momy da saratu sukayi hirar su sanan sukayi sallama.

Washe gari......

Momy yau ciki take da farin ciki duk da kuwa tasan watan tonan asirin ta ya kama. Tun da safe take sanarwa da mutan gidan yau qanwar ta saratu harma da mijin ta zasu zo, duba jikin abdul. Kowa sai zumud'in son ganin qarwar momy yake banda hajiya kaka da ammi da dady wanda suka san mugun halin ta. 6angaran abdul kuwa abun ba'a cewa komai jiki ya sake riki cewa dan jikin ma yafi na kullum..........

MASHKHUR.

Wata irin kewar zahra da shauqin ta ne suka rufe mashkhur. Ga wani mugun son ta da ya lulu6e mashkhur lokaci guda. Yana daga kwance yana tuna rayuwar su ta da, a Russian wani abun ya bashi dariya wani abun yaji ba dad'i. Musamman ma daran su na qarshe a Russian sam mashkhur komai

Please Login or Register in order to submit comment