Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inaso amma ai aunty zahra zata siyar mu.

To taso muje ka rakani, kallan sa ameer yayi tare da cewa, ina zaka?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa, kai dai ka taso mu je ko na d'auke ka ne. D'aga kai ameer yayi alamun ee haka mashkhur ya d'auki ameer a hannu suka fuce daga d'akin. Suna sauka qasa suka tarar da ammi tana ta jera breakfast a kan draining.

Har qasa mashkhur ya tsugana ya gai da ammi, ammi ina kwana da fana an tashi lpy? Fuska a safe ammi tace lpy qalau mashkhur kai ma da fana ka tashi lpy? Shima mashkhur fuska sake yace lafiya qalau tare da miqewa tsaye yana ruqo hanun ameer da yake ya sauke shi. Ammi kin sai me yaya mashkhur!! Da sauri mashkhur ya katse zancan da cewa, haba ameer ka bari sai mun dawo sai ka fad'a mata.

Cikin mamaki ammi tace aa ka fari d'ana ya gayamin menene baby na zo ka gaya min? Aa ammi ba fa wani abin zai ce miki ba gaya miki zai yi zamuje unguwa ko ameer!? Gyad'a kai ameer yayi duk da kuwa ba hakan zai cewa ammi ba. Cikin mamaki ammi tace ina zaku l fita da sassafan nan?. Aa ammi bata waje zamu fita ba ina cikin gidan nan.

Okay sai kin dawo ammi ta qarasa maganar tana kama hanyar shiga kicin mashkhur kuwa jan hanun ameer yayi suka fuce daga part d'in ammi. Suna fita mashkhur yace mai zaka ce wa ammi? dariya ameer yayi tare da cewa, sai ka d'auke ni zan gaya ma. D"aukar shi mashkhur yayi tare da cewa, to gayamin. Suna tafiya ameer yana korawa mashkhur bayani kamar haka!.

Haka zance mata ka ta6awa aunty zahra ta ciki da cibiya. Zaro ido mashkhur yayi cikin mamaki yace kai ameer ba nace ma ba ta6awa nai ba tashin ta fa zanyi. Shiru ameer yayi ba amsa, daga haka shima mashkhur bai sake cewa komai ba har suka qarasa qofar part d'in momy. Suna qarasawa mashkhur ya fara knocking d'in qofar part d'in momy.

Bai wani jima yana bugawa ba sai ga rukee tazo ta bud'e. Tana ganin mashkhur fuska a sake tace yaya mashkhur good morning, fuska sake mashkhur ya shigo tare da cewa, morning too rukee how are you? Fine yaya mashkhur and you?. Murmushi rukee tai tare da cewa, some too I'm very fine. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa, that is good ina momy.

Tana sama okay kije ki kirawo ta mashkhur ya qarasa fad'in hakan yana kutsa kai cikin falo hannu riqe da ameer, itama rukee bayan su tabi sanan ta wuce sama domin kiran momy. Mashkhur kuwa yana qarasawa kujera ya dora ammi sanan ya zauna yana jiran futowar momy.

Mashkhur bai fi 8 minutes a zauna ba momy ta saukko fuska cike da fara'ar mugunta. Tana qasowa tace ah wata saban gani ai tun jiya nake jiran ka bakazo ba har da nace ma zuwa anjima ni sai nazo da kai na. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa, ah momy ai bama zata kai da hakan ba, zama momy tai akan kujera tare da cewa, to gashi kaqi zuwa waje na sai daka kwana ma.

Aa momy ba haka bane wlh, jiya nayi niyar zuwa wajanki amma nace sai na huta bayan sallah la'asar na kwanta bacci ban tashi ba sai da magriba, shine nace yamma tayi bari na bari zuwa yau sai nazo mu gaisa. To ya hanya? Alhamdulilah momy, da fatan dai ka fito da ruselt mai kyau. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa, sosai ma momy.

Ina ruselt d'in naka yake, yana bedroom d'i na amma bari na nuna miki a waya. Mashkhur yana d'auko wayar ya kunno picture d'in ruselt sanan ya miqawa ameer tare da cewa, ameer jeka ka kai wa momy. Kar6a ameer yayi sanan ya miqawa momy wayar yaya mashkhur d'in tare da tsayawa a kusa da ita. Momy tana ganin result d'in mashkhur gaban ta ya fad'i Rass, Rass.

Cikin zuciyar ta tace taya akayi result d'in mashkhur yayi kyau sosai bayan munyi mai asirin rashin son karatu da shaye-shayan da bin mata. Nan da nan baqin ciki ya rufe zuciyar momy, amma a fili sai tace wow mashkhur ALLAH gashi har da offer ka samu ai dama acan ka zauna kai aikin ka hankali kwance.

Ah momy kin san bazan iya zama a can ba na fison nan cewar mashkhur. Jinjina kai momy tai sanan tace naji ance matar ka zahra tana da ciki koh? To ALLAH ya sauke ta lpy. Cikin mamaki yace momy waye ya gaya miki, zama momy ta gyara tare da cewa, hajiya mana. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa, aa gaskiya ba haka bane.

Shiru momy tai tana mamaki wai ita mashkhur zai yiwa qarya anya kuwa asirin da tai mai bai karye ba kuwa?. Momy tana cikin wanan tinanin taji ameer yace momy kin san menene? Qaqalo murmushi dole momy tai tare da cewa, aa ameer sai ka fad'a. Yaya mashkhur ya ta6awa zahra ciki da cibiya kuma yace min wai!!!! uwar harara da mashkhur ya zubawa ameer shi yasa ameer yaji tsoro yayi shiru bai qarasa fad'ar maganar ba.


Momy kuwa wani irin zafi zuciyarta ta sake yi mata, a fili kuma cewa tai ai baby da take cikin ta yake dubawa ko bakaso ta haifar ma baby ne dariya ameer yayi tare da cewa ina so. Mashkhur kuwa miqewa yayi tare da cewa to momy sai anjima ameer kar6o wayar mu tafi. Ameer kar6ar wayar yayi sanna yafi bayan mashkhur.

Momy kuwa sabida baqin ciki da kyar ta iya cewa to sai anjima nagode. Suna gama fita daga part d'in momy mashkhur ya fizge wayar shi daga hanun ameer tare da cewa, banace karka gayawa kowa ba? Shiru ameer yayi bai ce komai ba. To daga yau na dai na kulaka ko magana ka sake yimin sai na kakkarya ma qafafuwa. Nan da nan ameer ya fara kuwa.

Tsugunawa mashkhur yayi tare da cewa, rufe min baki ko na faffasama baki. Shiru ameer yayi tare da sakin ajiyar zuciyar hawaye suna amfaliya a fuskar shi. Hannu mashkhur yasa ya share mai hawaye tare da cewa, kana so na cigaba da kulaka ba? Cikin shasheqar kuka ameer yace ehh. Tom karka qara gayawa kowa kaji.

D'aga kai ameer yayi tare da cewa, to na dai na, kayimin alqawari koh? Har chocolate zan suyoma in baka fad'awa kowa ba. Murmushi ameer yayi tare da cewa, to na yadda na dai na fad'awa kowa, wata uwar ajiyar zuciya mashkhur ya saki tare da kama hanun ameer suka wuce part d'in ammi.

Momy kuwa suna fita ta koma saman cikin bedroom d'in ta sanan ta dannawa saratu kira, saratu tana d'aukar wayar momy ta fara kora jawa bi da! Wlh saratu na shiga uku inga fa asirin da nayiwa mashkhur na shaye-shayan ya karye, cikin mamaki saratu tace kai yaya halima taya kika gane!? Hmmm ke dai bari saratu kinga result d'in mashkhur ta biyu fa yazu har offer d'in samun gurbin aiki a qasar aka bashi, ni kenan d'ana abdul bazai cigaba ba sai dan kishiya ta.

Haba yaya halima mai ne na d'aga murya muna da boka fa ai shine maganin damuwar mu. Hmm saratu kenan ba dole na d'aga hankali na ba, har wani 6oyemin cikin shigiyar matar nan tasa yake, wai bata da ciki anya asirin mallakar ma bai karye ba?. Jinjina kai saratu tai tare da cewa, kika san ko shegiyar kakar nan tasa da uwar sa sunbi bokaye sun karya?.

Amma ki kwantar da hankali ki gobe ko zuwa jibi ki shigo komai zamu rusa shi in sha ALLAH, sai yaji ya tsani wata mai suna zahra ma. Jinjina kai momy tai tare da cewa, bari na gama dafa breakfast ko su ruma su dafa mana ina karayawa zanje wajan dady na zuba mai wata uwar qaryar dan ya barni nazo kaduna.

Ai kuwa yaya gwara ki hanzar ta zuwa dan lokacin rusa mashkhur da zahra yayi, dan in kika zauna ke zasu rusa. Daga haka sukayi sallam momy ta ajiye wayar. A fili tace uhmm mashkhur zahra hjy kaka wlh kun shiga tarkona wanda bai mai iya fitar da ku a duniya, sai na ruguza muku rayuwa a cikin wanan satin..................

Hmmm kuna ganin dady zai bar momy zuwa kaduna?.

Wace irin mugun ta momy zata aika tawa zahra da mashkhur harma da baiwar ALLAH HJY kaka?.

Hmm kuna ganin ameer zai sake fad'ar zancan nan kuwa?.

Mu had'u a next page gobe.



ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

Typing.......

* Page 99*

A fili tace uhmm mashkhur zahra hjy kaka wlh kun shiga tarkona wanda bai mai iya fitar da ku a duniya, sai na ruguza muku rayuwa a cikin wanan satin..................

6angaran mashkhur suna zuwa qofar part d'in ammi ya sake kallan ameer tare da cewa yauwa ameer karfa ka gayawa ammi kaji? Gyad'a kai ameer yayi tare da cewa tom, wlh ka fad'a na dena kulaka kaji, girgiza kai ameer yayi tare da cewa tom bazan fad'a ba. Yauwa ameer d'in tawo mu shiga, daga haka suka ranka suka shige falo tare da zaunawa akan kujera.

Suna zama ammi ta qaraso ta zauna tare da cewa har kun dawo kenan ina kukaje?. Kafin ma mashkhur yayi magana ameer yace wajan momy muka ce, jinjina kai ammi tai tare da cewa gaskiya ne kun kyauta. Shiru mashkhur yayi cikin zuciyar shi yana fargabar kar ameer ya sake yi mai 6arin zance ya tona mai asiri.

Ammi kije ki zubo mana abinda kika dafa yau tare da yaya mashkhur zanyi breakfast,. Kallan sa ameer tai tare da cewa kai ameer breakfast zakayi yanzu ba wanka ba brush? Noqe kafad'a ameer yayi tare da cewa, aa gaskiya ni yanzu nake so in baki zuba mana ba zanje na gayawa hajiya kaka ko dai bakya so yaya mashkhur yaci miki abinci ne?.

Dariya ammi tai tare da cewa to yaushe mukayi haka da kai ameer daga cewa! Sai anyima wanka da brush, ai nayi tinanin bakyaso yaci ne shi yasa ameer ya qarasa maganar yana zafga uban tagumi kamar wani maraya. Miqewa ammi tai tare da cewa to harda tagumi ameer sauke tagumin bari naje na zubi muku ammi ta qarasa magar tana miqewa.

Mashkhur nan da nan ya sake tsinkewa da lamarin ameer yadda yake zaro magana kamar ana gaya mai. Ammi tana wucewa draining mashkhur ya sassauta murya yadda bazataji ba yace ameer karfa ka gayawa ameer kana gaya mata na dena kulaka kaji. Gyad'a kai ameer yayi tare da cewa tom bazan fad'a mata ba.

Bayan few minutes ammi ta dawo hannu riqe da tire mai d'auke da cup biyu na tea da plate biyu, d'aya da farfesun kayan ciki d'aya kuma dankalin turawane da soyayyan kwai a ciki sai kuma fork biyu spoon biyu. Tana zuwa ta ajiye a akan carpet qasan su mashkhur ta, bayan ta ajiye ta koma kan kujera ta zauna. Saukowa ameer da mashkhur sukayi sanan suka fara cin breakfast d'in.

Suna cikin ci ameer yace yaya mashkhur kasan meye? Da sauri mashkhur yace! Ba'a magana in anacin abinci duk dai gudun kar ameer yayi mai 6arin zance a gaban ammi. Ka bari dai na baka labarin dan naji dad'in cin abincin. Cikin fargaba mashkhur yace labarin mai zaka bani? Gyara zama ameer yayi tare da cewa labarin ilham zan baka.

Wata siririyar azuciyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa tom ina jinka. Ranar nan aunty ilham tana waya naji ta cewa wani saurayin ta wai I LOVE YOU. mashkhur da ya kai tea bakin sa da sauri ya janye ya kalli ameer yace kai ameer banda sharri fa. Wlh da gaske nake ma ga ammi nan ka tambaye ta ai na gaya mata.

Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa to na yadda waye saurayin nata, uhm wani ne wai ita ilham d'in tace auran shi zatai ameer ya qarasa maganar yana ta6e baki kamar wani babba. D'an zaro ido mashkhur yayi tare da cewa haka tace ma ameer? Girgiza kai ameer yayi tare da cewa! Haka dai naji ana fad'a a gidan.

Murmushi mashkhur yayi sabida maganar ameer d'in ta bashi dariya, sanan ya kalli ammi tare da cewa ammi wai da gaske ameer yake kuwa?. Itama ammin murmushi tayi tare da cewa to ba gashi ya gaya ma ba ai duk abinda ya gayama ka yadda ai ameer baya qarya iya abinda yaji shi yake fad'a. Ajiyar zuciya mashkhur yayi tare da cewa to waye saurayin nata haka?.

Cikin mamaki ammi tace au kai duk zancan nan da ake baka sani ba kenan?. mashkhur cewa yayi tom ammi ina zan sani kuwa nida bana nan akayi. Jinjina kai ammi tai tare da cewa! To ai abokin ka ne ahmad kuma nan da 3 days zuwa 4 days zasu kawo kud'in zance, ita da rukkayya duk aure za'a yi musu, ni nayi tunanin ma kasan zancan wajan ahmad.

Cikin mamaki mashkhur yace ahmad dai? Kwarai ahmad ko da matsala ne? Ammi ta tambayi mashkhur tana tsare shi da ido. Da sauri mashkhur ya girgiza kai tare da cewa no ba wata matsalar kawai nayi mamki ne yadda har zancan yayi nisa ban ta6a jiba. ALLAH ya sanya alkhairi, ameen mashkhur da fata dai ahmad bashi da wata matsalar duk da dai za'ayi bincike.

Da sauri mashkhur ya girgiza kai tare da cewa aa gaskiya ahmad mutumin kirki ne sosai da sosai, bashi da wata matsala. Haka dai ameer yayi ta warwarewa ilham zani tass a wajan mashkhur har suka gama breakfast d'in. Suna gamawa mashkhur ya sake jawa ameer kunne akan karya fad'a dama lokacin ammi bata wajan ta tafi bedroom d'in ta domin yin wanka.

Daga haka mashkhur ya koma part d'in su cike da zullumi, kar ameer ya tona mai asiri. Ameer kuwa mashkhur yana fucewa ya haye sama yana hawa ya wuce d'akin ammi. Yana zuwa gaya zahra ta tashi daga bacci tana ta karatun arzkar d'in safiya. zama ameer yayi a kusa da zahra yana jira ta gama arzkhar d'in.

Zahra tana gamawa ta miqe tare da cewa ameer zo mu tafi wajan ilham, ba musu ameer yabi zahra yana cewa gaskiya aunty zahra ina son ki fiye da yadda nake son ilham nayi farin cikin dawowar ki da fatan dai baza ku koma ba ke da yaya mashkhur ke ni ko yaya mashkhur zai koma dan ALLAH karki bishi inaso ki zauna tare da ni.

Mamki ne ya kama zahra ganin yadda ameer yake zaro zance ko tsayawa baya yi. Dariya tai tare da riqe hanunsa suna tafiya tana cewa! Nima ina son ka ameer d'ina in sha ALLAH ina tare da kai ba inda zani. Dariya ameer yayi tare da cewa yauwa aunty zahra ko ke fah. Zahra da ameer basu tsaya ko ina ba sai bedroom d'in su ilham.

Suna qarasawa bedroom d'in zahra ta murd'a handel d'in qofar sanan ta shige hanunta riqe da hanun ameer. Suna shiga zahra taji alamun watasa ruwa a toilet hakan ne ya tabbatar mata da ilham wanka take. Zama zahra tai ita da ameer d'in tare da kurawa ameer ido tana mamaki yadda ya sake girma da wayo ga surutu. Ameer naga kamar kayi kuka fuskar ka tayi wani ja alamun kayi kuka mai ya saka kuka?.

Hawa kan ciyar zahra ameer yayi tare da cewa wlh aunty zahra yaya mashkhur ne ya sani kuka. Cikin mamaki zahra tace yaya mashkhur kuwa mai kayi mai ya saka kuka dukan ka yayi ko kuwa?. ba dukana yayi ba wai cewa yayi in na qara kula shi sai ya kakkarayin qafufuwa na, cikin mamaki zahra tace sabida mai ameer ko wani laifin kai mai.

Girgiza kai ameer yayi tare da cewa ba ruwana bazan fad'a miki ba, yace karna sake gayawa kowa in ba haka ba ya dena kulani kuma ni banaso ya dai na kulani. Girgiza kai zahra tai tare da riqe hanun ameer biyu tana cewa! Haba ameer aunty zahra ka cefa kuma kaga ni kad'ai zaka gayawa ba wanda zai ji ai bazan gayawa kowa ba daga ni sai kai zan rufama asiri.

Tom shikenan aunty zahra ta zan gaya miki ke kad'ai kina jina koh? Gyad'a kai zahra tai tare da cewa inajin ka ameer d'ina gayamin. A dai-dai lokacin ilham ta futo daga toilet amma sai ta tsaya a bakin toilet d'in dan jin mai zahra da ameer suke tattaunawa. Gyara zama ameer yayi a kan cinyar zahra tare da cewa! D'azu da safe ina tashi daga bacci sai naga yaya mashkhur akan gadon mu a kusa da ke yana ta6a miki ciki da cibiya.

Da sauri zahra ta zaro ido tare da sa hannu ta tushe bakin ta alamun tsantsar mamaki. Ameer kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Shine na cemai sai na gayawa ammi da dady da aunty zahra da yaya Abdul da aunty ilham da aunty rukee da aunty ruma da hajiya kaka da ya haidar da ya faruq da kuma 'yan makarntar mu. Zahra kuwa sarander tai ganin yadda ameer yake lissafo mutan gidan harda na waje.

Yana gamawa tace kai ameer banda qarya fa yaushe kaga hakan?. Wlh aunty zahra da gaske nake yau da safe akayi shine sai yace min shi ba ta6a ki yake ba tashinki daga bacci zai yi, daga nan yace karna gayawa kowa zai siyar min alawa, ni kuma nace aaa aunty zahra zata siyar min ai zaki siyar min koh?. Gyad'a kai zahra tai tace ee zan siyama shine yace zai karyama qafa.

Girgiza kai ameer yayi tare da cewa aa sai yace nazo na raka shi, muna fita mukaje wajan momy dan na gayawa momy yaya mashkhur ya ta6awa miki ciki da cibiya shine ya harareni da muka fita yace in na sake kula shi sai ya karya min qafa. Shine ni kuma na fara kuka sai yace in banyi shiru ba sai ya faffasamin baki.

Zahra sabida mamakin zancan ameer da yarfin da ya gayawa momy. Shi kuma ameer ya cigaba da cewa! daga qarshe dai yace zai cigaba da kulani kuma zai siyar min chocolate amma in ban gayawa kowa ba. Shine nace tom bazan gayawa kowa ba, daga nan mukayi breakfast shine na bashi labarin ilham tana waya da saurin ta tace mai I LOVE YOU kuma wai tace auran sa zatai.

Kafin zahra ta kai da magana ilham da take tsaye a qofar toilet tana saurarin su tace oh ni ilham na shiga uku wajan ka ameer yanzu sai da ka gayawa yaya mashkhur. Dariya ameer yayi tare da cewa ee bama iya haka na gaya mai ba harda ragowar amma bazan gaya miki ba, ya qarasa maganar yana gwalo.

Qarasowa wajan su ilham tai tare da zama a gefan zahra tana cewa! Ameer mai naji kana gayawa zahra mai yaya mashkhur yayi mata tana bacci?. Ilham ta qarasa maganar tana tsare ameer da ido dan san jin gulma. Girgiza kai ameer yayi tare da cewa bazan gaya miki ba baruwana aunty zahra kema karki gaya mata kinji?.

Tom shikenan ameer bazan fad'a ba amma kai ma karka qara gayawa kowa kuma in ka sake gayawa wani a gidan nan ko a waje na dena kulaka kuma sai kyankyaso ya cinyema baki. Cikin tsoro ameer yace haba aunty zahra zaki dena kulani kuma ki bari kyakyaso ya cinye min baki, ina sonki fa ke bakya sona ne?.

Ina sonka mana ameer amma dai in ka sake gayawa mutane maganar nan sai na dena son ka kaji. Girgiza kai ameer yayi tare da cewa aa wlh bazan sake gayawa kowa ba kinji dan ALLAH aunty zahra ta karki dena sona kinji?. Murmushi zahra tai tare da cewa to ameer d'ina in dai baka gayawa kowa ba bazai dena son ka ba.

Yauwa in sha ALLAH ba wanda zai ji kema karki gayawa kowa kinga amana na baki ko? Karki gayawa ilham d'in nan ameer ya fad'a yana ta6a ilham da d'an yatsan shi d'aya. Gyad'a kai zahra tai tare da cewa bazan gaya mata ba maza jeka kace ammi tai ma wanka kazo nai ma hoto.

Tom bari naje ammi ya fad'a yana sauka daga cinyar zahra ya fuce daga d'akin a guje. Ilham kallan zahra tai tare da cewa oh zahra na shege su wlh yanzu ameer sai da ya kwance min zani a wajan yaya mashkhur wa yasan ma da mai da mai yace mai shi yasa wataran in ina waya ya tsira min ido kamar baya kwasar abinda na fad'a ashe kwashe komai yake.

Hmm gwara ke ai ilham bakiji abinda yace yaga yaya mashkhur ya yimin ba wanan ai na shiga uku da kunya a gidan nan in ya fad'a ko fita na dai na yi. Dariya ilham tai tare da cewa wai mene gaskiyar zancan da gaske yayi miki hakan ko kuwa dai amma nasan dai ameer bazai iya had'a zancan nan ba. Hmmm wlh ilham nima ban saniba ko gaskiya ne ko akasanin haka.

Kai zahra taya har za'a ta6aki baki sani ba?, wlh ilham da gaske nake miki amma dai kamar naji ana ta6ani sama-sama to ni nasha ma ammi ce take gyara min riga ko kuma ameer ne yake wasa, amma kuma nad'an ji muryar yaya mashkhur sama-sama to ni nayi tinanin mafarki ne ashe da gaske ne. Murmushi ilham tai tare kai yaya mashkhur ya fad'a wlh................

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing..........

Double page..........


Tsaki zahra tai tare da cewa a gidan wa, wlh ba wani sona da yake kinsan jiya da na fita shan lemo da daddare mai ya faru kuwa?. Da sauri ilham ta girgiza kai tare da cewa mai ya faru. Ina fita na tarar da shi a falon qasa yana cin abince har zan hau saman nan ya kirani da bazani ba naje sai ya fara jamin kunne akan karna sake na gayawa su dady zancan zee.

Sai nace sai na fad'a ai bata daki banza ba, to shine yace wai an bimin haqqina an kai ta gidan yari kuma in ban yarda ba na tambayi ahmad. Kuma yace in na gayawa dady shikenan ba maganar saki kuma in bai sake niba abuja zamu tafi yayi ta bani wahala har sai nafi kaka hajiya kaka tsufa. Dariya ilham tai tare fa cewa! Wai nida duna gaskiya yaya mashkhur ya iya mugunta.

Hmm ke dai bari ilham sai nace mai na

Please Login or Register in order to submit comment