Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

plate d'in hanunta da ta gama cin abinci kallo da coffee d'in da ta ajiye gefe. Fuska a d'aure mashkhur yace shi coffee d'in ba zaki shaba ko ta hanci kike so na dora kimi? Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa! Aa wlh bana shan coffee ne shi yasa.

Jinjina kai mashkhur yayi tare da wucewa qaramar dorowar ya d'auko magungunan zahra, ya ajiye su a kan bed sanan ya warce plate d'in hanun zahra ya fuce. Zahra kuwa murmushi tai tare da cewa! Hmm wahalama yanzu ka fara sha mugu kawai. Bayan few minutes mashkhur ya dawo hanunsa riqe da cup da bottle d'in ruwa, yana qarasowa kan bed d'in ya d'auki coffee d'in ya ajiye shi a sama qaramar dorowar gadan sanan ya dawo kan bed d'in ya zauna a gefan zahra.

Yana zama ya bud'e magunguna ya fara 6allowa zahra one by one, yana 6allo mata yana bata tana sha. Bayan ta gama shanyewa ya d'auko mata na shafawa a kai ya tatsa mata a hannu sanan yace ta shafa a kanta. Bayan zahra ta gama shafawa a kanta, na 'yan yatsu mashkhur ya qara tasa mata shima ta shafe yan yantsun nata duk da kuwa yanzu 'yam ya tsun zahra sun fara warke dan kuwa sun dena yi mata ciwo sosai kamar da.

Bayan zahra ta gama shafawa, haka mashkhur ya zauna ya shafa mata a qafa. Yana gama shafa mata ya wuce toilet ya wanke hanunsa sanna ya futo,. Sanan ya dawo wajan ga mamaki zahra kamar yadda tai tunani ai kuwa sai taga mashkhur ya d'auki coffee d'in nan, yana d'auka zahra ta fara addu'a a cikin zuciyar ta ALLAH yasa ya sha. Mashkhur kuwa sai da ya qarewa coffee d'in kallon sai wani ya mutsa fuska yake, da kamar dai bazai shaba, kawai sai ya kai bakinsa ya fara sha.

fuce yayi daga bedroom d'in hannu riqe da cup d'in coffee ya koma fallo, haka mashkhur ya zauna akansofa ya fara shan coffee d'in sa, haka mashkhur ya shanye coffee d'in tass. Bayan ya gama sha zama yayi ya cigaba da kallonsa a laptop d'in shi. To fah ba mashkhur ne ya gama kallon nan ba sai sha biyun dare a lokacin ma zahra har tayi nisa a bacci.

Bayan mashkhur ya gama kallan america film d'in kashe laptop d'in yayi sanan ya d'auka ya shige cikin bedroom d'in. Yana shiga ya tarar da zahra tana ta sharar baccin ta hankali kwance, ajiye laptop d'in yayi sanan ya canza hasken room d'in daga fari zuwa blue, bayan ya canza direct wardrobe ya wuce ya dakko towel sanan ya rage kayan jikinsa ya wuce toilet, domin yin wanka bacci.

Bayyan ya fito ya sa kayan bacci A. C ya kunna bayan ya kunna ya nufi bed ya lulu6e zahra da blanket, sanan shima ya koma kan sofa ya kwanta abinsa, yana kwanciya ya lulu6e jikinsa, daga nan bacci yayi awan gaba da shi.................

Washe gari.

Bayan mashkhur ya dawo daga sallar asubayi kicin ya shiga ya had'a musu breakfast shida zahra. Bayan ya gama, ya zubawa zahra ya kai mata, lokacin ma zahra harta koma bacci bayan sallar asubar da tai. Tashinta mashkhur yayi sanan ya bata yace tashi. Yana bata shima ya fita ya fara cin nasa a hanzarce, sabida yana so ya kai ahmad airport akan lokaci.

Bayan ya gamaci mashkhur ya gama cin abinci, bedroom ya shiga ya d'ebo kayansa da zai sa ya d'ebo yayi wanka a toilet d'in fallo sanan ya shirya. Yana gama shiryawa ya koma bedroom d'in shi a hanzarce, yana shiga ya fesa dad'an turaren nan nasa wanda zahra take mutuwar so bayan ya gama fesawa qoqarin sa agogo ya farayi. Zahra kuwa zuba mai ido tai tana tinan ina mashkhur zai je da sassafan nan. Sosai zahra ta zuba mai ido tana kallan dressing d'in shi.

Dress d'in mashkhur yayiwa zahra kyau sosai, ga kamarsu da ammi ta sake futowa sosai zahra ta zuba mai ido sabida kamar da taga yana yi mata da ammi, sai taji kamar ammi take kallo, duk da dai mashkhur d'in ma yafi ammin kyau. Karaf mashkhur ya d'ago sukayi 4 eyes da zahra tana mai kallon qurillah,. Fuska a d'aure mashkhur yace kee lafiya kika kallona da mayun idanuwan nan baki.

Zahra batasan sanda dariya ta kwace mata ba sabida abinda mashkhur ya fad'a wai itace mai mayun ido shida yake da kwala-kwala ido ai shine mai mayun idon a ganin zahra. Mashkhur kuwa tsaki yaja, ya cigaba da abinda yake, ana cikin haka suka fara jin ana knocking d'in gidan. A hanzarce mashkhur ya fuce daga bedroom d'in.

Bayan wasu 'yan muntuna sai ga mashkhur da ahmad sun shigo bedroom d'in bakin ahmad d'auke da sallama. Da sauri zahra ta d'ago fuska d'auke da fara'a tace yaya ahmad sannu da zuwa, murmushi ahmad yayi tare da cewa! Yauwa qanwata ya qarasa maganar yana shigowa d'akin. Gyara kwanciya zahra tai tare da jan blanket ta rufe jikinta sosai da yake a kwance take.

Gaskiya yaya ahmad nayi fishi baka zuwa ka dubani fah? Zahra ta qarasa maganar a shagwa6e. Mashkhur kuwa wani haushi zahra ta bashi ganin yadda take lanqwashewa ahmad murya kamar wata mage. Ahmad kuwa cewa! Yayi am sorry qanwata tuba nake, jiya da muka dawo daga makaranta nazo kina bacci naso na dawo, aiki yayi min yawa sabida ina had'a kayana yau zan koma nigeria fa.

D'an zabira zahra tai tare da cewa! Nigeria kuma yaya ahmad tafiya zakai ka barni kenan?. Mashkhur kuwa da yake gefe wata uwar harara ya zubawa zahra, ahmad kuwa cewa yayi! Aa qanwata ina da abinda zanyi mai mahimmanci, ne acan amma kuma ai kun kusa dawowa kina samun sauqi zaku dawo. Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa! Tom shikenan yaya ahmad ALLAH ya tsare ya kiyaye in kaje ka gai da mutuniyar, nasan ma itace take hurema kunne ka dawo.

Wata qasai tacciyar dariya ahmad ya sauki bayan ya tsagai ta yace, aaa ni dai ba ruwana karkisa in naje tayi fushi dani. Itama zahra dariyar tai sanan tace tom shikenan, in kaje ka miqamim gaisuwa kafin na dawo, gyad'a kai ahmad yayi tare da cewa! Zataji in sha ALLAH qanwata, bari mu wuce karna makara koh?. Zahra kwata-kwata batasan tafiyar yaya ahmad d'in amma dole ta danne zuciyar ta tace okay ALLAH ya tsare hanya ya kai ka lpy yaya ahmad.

Murmushi ahmad ya saki tare da cewa! Ameen qanwata ngd mashkhur zo mu wuce koh? Ahmad ya qarasa maganar yana kallon mashkhur da yake gefe wanda suka bari cikin kokwantan maganar da suke dan shi sam bai san akan waca yarinyar suke maganar ba. Amma dai haka mashkhur ya d'auke kai suka fuce yana so ya tabbayi ahmad amma ya kasa sabida shi bai cika bin kwakwafi ba kuma yana ganin, tinda ahmad bai mai zancan ba mai zai sa shi ya tambaye shi.

Haka dai Ahmad da mashkhur suka kama hanyar airport, suna tafiya ahmad yana qara jan kunnan mashkhur akan ya kiyaye ko da wasa kar ya sake ya ce zai daki zahra sabida zai qara janyowa kansa matsala, kuma ya bata kulawa sosai, kuma yayi mata jinya mai kyau duk abinda take buqata ya kau da kai yayi mata karya zalince ta. Haka ahmad yayi ta yiwa mashkhur nasiha har suka qaraso airport.

Lokacin da suka qarasa airport d'in sosai ahmad da mashkhur suka rungume junansu suna jimamin rabuwa. Haka dai suka danne zuciyar su ahmad ya wuce cikin jirgi yana d'agowa mashkhur hannu zuciyoyin su cike da kewar junansu. Jirgin su ahmad yana tashi mashkhur ya juyo gida zuciya ciki da kewar abokin nasa.

Haka mashkhur ya dawo gida jikinsa duk yayi sanyi. Haka dai suka wuni a gidan shida zahra kuwa zuciya ba dad'i sabida tafiyar ahmad. Ga zahra duk batajin dad'in jikinta tana so tai wanka amma ta rasa taya zata gayawa mashkhur ya d'auko mata kayanta da dai saura su ga ciwan ciki da mara da yake damunta.

Night..............

Zahra tana kan bed a zaune mashkhur ya shigo hannu d'auke da plate d'in abinci ya miqawa zahra. Zahra kuwa da kyar ta iya sa hannu ta kar6a sabida cjwan marar da yake damunta, tunda yau ta tashi takeji ciwan mara ya addabe ta, alamun dai jinin ta na wata yana kan hanya. Haka dai zahra ta fara cin abinci tana ta taradadin yanzu in jini ya isketa a wanan halin ya zatayi?.

Da qyar zahra ta iya cin rabin abinci shima taci a bisa dole ne sabida kar mashkhur yace zai dura mata shi ta hanci. Tana cin rabi ta ajiye ta kalli mashkhur da yake gefe tace! Na qoshi ina san shan ruwa. Mashkhur kuwa share zahra yayi kamar bai jiba sai da ya gama shanshan qamshi da miskilancin sa sanan ya miqe ya fuce da ragowar abinci.

Bayan few minutes mashkhur ya dawo hannu d'auke da bottle d'in wata mai sanyi. Sai da ya bud'e ya tsiyaya mata a cup sanan ya ajiye bottle d'in ruwan a gefe, ya miqawa zahra, yana miqawa zahra tai sauri ta ajiye tare da cewa! Nifah bana son ruwan sanyi, rashin lpy yake sani. Mashkhur bai ce komai ba ya fuce daga bedroom d'in.

Hannu na rawa zahra ta d'akko jarkar ruwan ta fara karanto addu'o'in da tai mai jiya domin ta tofa mai a coffee. Da sauri zahra ta fara karantawa a hanzarce tana gamawa tai sauri ta tofa a jarkar ruwan sanan ta sake tofawa a cup d'in da ta ajiye. Ai kuwa tana gamawa mashkhur ya shigo, hannu d'auke da bottle d'in wani ruwan. zahra tasan mashkhur yana shan ruwan sanyi sosai shi yasa ta tofa, kuma tasan zai iya sha tinda ita bata shaba.

Ai kuwa abu kamar al mara mashkhur yana miqawa zhar ruwan da ya sake d'akko mata ya d'auki mai sanyi na cup wanda zahra ta gama tofa addu'a ya fara sha. Sai da ya shanye tass bayan ya shanye harda qara tsiyayar na jarkar yasha. Yana gama sha ya kwasowa zahra magungunan ta, sanna ya fara 6are mata kamar yadda ya saba.

Bayan ta gama sha da shafawa, shima ya shafa mata na qafa canza globe d'in d'akin yayi sanan ya lulu6awa zahra blanket, bayan ya gama ya ware A. C kamar yadda ya saba, sanna shima yaje ya kwata akan sofa.
Zahra kuwa wani siririn tsaki ta yaja a cikin zuciyar ta sabida ita harga ALLAH batasan A. C nan da mashkhur yake kunnawa kawai dai haquri takeyi dan ba yadda zata iya da shi.

To har dai mashkhur yayi bacci wajan sha biyun dare zahra batayi bacci ba saka makwan farga ba da ciwan mara da yake addabarta. Tana tsoran in jinin nan yazo ya zasu qarke ita da mashkhur. Ai kuwa zahra tana cikin wanan nazari taji jini ya fara futowa a hankula, gaban zahra ne ya fad'i rass-rass, a hankula ta miqe ta yaye blanket d'in da mashkhur ya lulu6a mata sanan ta fara qoqarin sauka qasa.

Zahra tana sa qafarta taji sam qafar tata tai mata nauyi sosai dan haka batama gwada miqewa ba bare ta taka ta janyowa kanta wata jarabar. Cikin rashin samu mafita zahra ta koma, kan bed ta kwanta tai lamo tana tinanin mai ne mafita. Tana jin jinin nan yana sake gangarowa, har sai da ya jiqa mata pant.

Ji zahra take kamar ta kwallawa yaya mashkhur Kira, amma tana jin nauyi da kunya dan bama tasan taya zata farayiw yaya mashkhur bayanin mai yake damun taba. Zahra da ta gaji da kokwanto da tinani ga ciwan ciki da mara kawai bargo taja, ta lulu6e jikinta tare da matse cinyoyinta sosai, wai duk dan dai kar jinin ya cigaba da zubawa, to da haka dai bacci yayi awan gaba da zahra.


Mu had'e a text page dan jin ya zata kaya tsakanin zahra da oga mashkhur.


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 90*

Zahra da ta gaji da kokwanto da tinani ga ciwan ciki da mara kawai bargo taja, ta lulu6e jikinta tare da matse cinyoyinta sosai, wai duk dan dai kar jinin ya cigaba da zubawa, to da haka dai bacci yayi awan gaba da zahra.

ASUBA.

Yau mashkhur ya d'an makara sallar asuba dan haka yana tashi bai bi takan zahra ba ya d'aura alwala yayi wuce warshi masallaci. Bayan mashkhur ya dawo daga massalaci, yana shigowa bedroom ya canza globe d'in d'akin daga blue zuwa white, yana canza hasken bedroom d'in ya qarasa bed ya fara tashin zahra.

Kee kee tashi kiyi sallah! Shiru zahra ba amsa, hannu mashkhur yasa ya fara dukan folun da ta tayar da kanta. Da sauri zahra ta bud'e kyawawan idanuwan ta, mashkhur ta kani a tsaye a kanta, lumshe ido zahra tai ta sake bud'ewa,, wani dan shi dan shi ta faraji a bedsheets d'in kamar an zubar da ruwa, ko zahra bata gani ba tasan jini ne.

Yah ALLAH ko ya zamu kare da wanan bawan naka? Zahra ta fad'i hakan a zuciyar ta, bazaki tashi ba ka ba magana nake miki ba ne? Mashkhur ya fad'i hakan a tsawa ce. Zahra kuwa mai ma kwan ta tashi kamar yadda mashkhur yace sake duqunqunewa tai a blanket d'in. A zuciye mashkhur ya kai hannu zai yaye blanket d'in, da sauri zahra ta riqe shi da iya qarfinta, ta saqe duqunqunewa a ciki.

Mamaki ne ya kama mashkhur cikin mamaki yace wai wanan wana kalar iskanci ne haka bazaki saki ba,, wlh na tafi sai dai ki nemi wanda zai kai ki kiyi alwalar, kuma ke da ALLAH. nan ma zahra shiru ba amsa, da qarfi gaske mashkhur yaja blanket d'in ya fuzo shi. Ai kuwa sai ga blanket a hanun mashkhur.

Zahra kuwa tana kwance tsamo-stamo akan bed, ta jiqa jikin ta da farin bed sheets d'in da jini sosai, dan har rigar ta bad sheet d'in ma yayi dama dama da jini. Mashkhur yana ganin haka yayi sauri ya yar da blanket d'in gefe tare da hawa kan bed d'in da sauri cikin tashin hankali ya d'ago zahra tare da cewa! Mai yake damunki haka ciwo kikaji?.

Ya qarasa maganar yana d'ago ta zaune, zahra kuwa shiru tai ba tare da tace komai ba. Da sauki mashkhur ya kai hannun sa cikin zahra ya fara shafa cikin zahra a tsorace dan shi a tinanin sa jinin daga cikin ta yake futowa. Sosai mashkhur ya shafa cikin zahra amma bai ji wani alamu na ciwo ba. Hankali tashe mashkhur ya kamo hannayan zahra yana lalabasu ko zai ga ciwo amma babu.

Baki na rawa mashkhur yace wai a ina kikaji ciwo ne haka? Ya qarasa maganar yana kafe zahra da idanuwan sa. Da sauri zahra ta sunkuyar da kai cikin siririyar murya tace! Ni fa ba ciwo naji ba, shiru mashkhur yayi yana qarewa dogowar rigar da take jikin zahra kallo, a zuciyar shi yana tinanin to in ba ciwo ba mai zai kawo jini haka.

Wata zuciyar tacewa mashkhur period mana,, da sauri mashkhur ya kalli zahra wanda kanta yake sunkuye sai wasa take da yatsun hanunta. Mashkhur yana kallan mood d'in zahra ya tabbatar da abinda yake zargi wato period ne. Wata 'yar qaramar ajiyar zuciya mashkhur ya sauke, sabida da ya d'an tsorata sosai yasha wani abin ne ya samu zahran.

Kafin kace kwabo zuciyar mashkhur ta rikid'e daga fargaba zuwa jin haushi, nan da nan fuskar mashkhur ta canza kana ganin sa zaka sheda a zuciye yake. Cikin fad'a mashkhur ya d'ago yace, sannu mara mutunci muguwa kawai in banda baki da mutunci ni zakiyiwa rashin mutuncin nan a bed d'in na koh? Duk abinda zaki wahalar da ni shi kike koh?.

Zahra dai shiru ba amsa dan har yanzu kanta yana sunkuye a qasa kunya ta rufeta ko ta ina. Cikin tsawa mashkhur yace! Au shiruma kikayi ba magana nake miki ba, d'an zabira zahra tai baki nawa rawa tace! Nima bada sanina ba hakan ta faru, rai 6ace mashkhur yace qarya kike munafuka dama duk abinda zaki wahalar dani shi kike yi, in banda mugunta irin taki bazaki iya tashina ba?.

Nan ma zahra shiru tai ba amsa, a fusace mashkhur yace wlh na sake yi miki magana kika yimin shiru sai na sharara miki mari, baki ba rawa zahra tace uh um kamanta kace na dena tashinka in kana bacci baka so. To bazaki iya matsewa ba sai kin 6ata min bed sabida mugunta mashkhur ya fad'a rai a 6ace. Zahra kuwa a zuciyar ta cewa! Tai to ce maka akayi fitsari ne da zan iya matse shi, karaf maganar a kunan mashkhur, amma ita zahra ta d'auka iya zuciya tai magana.

Rai 6ace mashkhur ya d'aga hannu a zuciya ya bige bakin zahra. Da sauri zahra ta riqe bakin ta tare sakin kuka, tana mamakin taya akayi yaji abinda tace dan ita batayi tinanin maganar zata futo fili ba. Kuka zahra ta hauyi mai sauti dan harda shasheqa, wlh tallahi baki rufemin baki ba yanzu sai jikinki ya gaya miki. Da sauri zahra ta rufe bakin ta dan tasan mugunta mashkhur zai aikata ma abinda yafi haka.

D'agowa zahra tai fuska sha6e-sha6e da hawaye, aki kuwa sukayi 4 eyes da mashkhur wata uwar harara mashkhur ya sakar mata kamar zai cinye ta d'an ya. Zahra kuwa da sauri ta kawar da idanuwan ta gefe tare da d'an toro jan bakinta gaba wanda harya ya sake rinewa yayi jajir sabida bugun da mashkhur ya kai mata.

A zuciye mashkhur ya miqe ya wuce kan sofa ya zauna tare da kifa hannayansa da kansa a guiwowin qadar sa, kamar wani mai kuka. Zahra kuwa zuba mai ido tai tana kallan ikwan ALLAH,, har wajan 5 minutes mashkhur bai dago kansa ba, zahra kuwa abin dariya ya bata da sauri tasa hannayan ta biyu ta toshe bakinta tana qonshe dariyar ta, dan karta futo.

Mashkhur kuwa sosai ya shiga damuwa sam bayasan takura ko aikin da bai iya ba a rayuwar sa. Jinyar zahra ma kawai kai zuciyar shi nesa yake yana daurewa bisa dole sai gashi yau tayi mai aika-aika nan akan bed d'in shi. Sam mashkhur ya rasa taya zai fara gyara wanan aikin da zahra ta jawo mai, shida ba mace ba bai ma san yazai yiba.

Sai da mashkhur ya d'au 10 minutes yana a wanan yanayin sannan ya d'ago, yana d'agowa ya miqe tare da fucewa daga d'akin gaba d'aya. Zahra kuwa ajiyar zuciya ta sauki cikin jin nauyin mashkhur d'in tace uhmmm ALLAH yasa mu wanye lafiya dai.

6angaran mashkhur kuwa yana fita bai tsaya ko ina ba sai bedroom d'in zahra, yana shiga ya nufi kan bed ya fara hargitsa kayan, sosai mashkhur ya ringa hargitsa kayan gadan ko zai samu audiga da pants amma ina ba abinda ya gani. Wani sirrin tsaki mashkhur yaja sanan ya nufi wardrobe ya bud'e a zuciye. Ya zuba ido sama da qasa. Can ya hango tarin pants d'in zahra a qasa wardrobe d'in da sauri ya tsuguna yana stugunawa ya fara bincika qasa pants d'in.

Cikin sa'a can qasan pants d'in ya samo ledar audiga, wata siririyar ajiyar zuciya mashkhur ya sauke sanan ya zaro ledar, yana zaro ledar ya d'auko qaramar ledar d'aya ta audiga sanan ya had'a da pants d'in zahra guda hudu, yana d'auka ya fuce daga bedroom d'in.
Zahra tana cikin tinanin yaya lamarin zai qarke kawai taji alamun shigowar mashkhur.

Da sauri ta d'aga kanta, tana d'aga kanta ta hangi mashkhur a zuciye ya shigo bedroom d'in hannu riqe da ledar audiga da kuma pants. A kan sofa ya cillah audigar da pants d'in sanan ya wuce toilet. Yana shiga ya had'awa zahra ruwan wanka sanan ya fito, yana fitowa ya nufo bed d'in yana zuwa ya zubawa, zahra ido dan yama rasa taya zai fara d'aukar ta cikin jinin na,, dan kuwa mashkhur yana da kyankyami sosai.

A hankula mashkhur ya kai kai tare da sa hannun sa ya zai kai jikin zahra ai kuwa yaji qarnin jinin nan ya daki hancin sa. Da sauri mashkhur yaja baya, tare da watsawa zahra wata harara, zahra kuwa azuciyar ta cewa tai duk iyayinka da kyankyami da jan ajinka dole ka ta6a qazantar nan tawa mugu kawai. Tsaki mashkhur yaja sanan ya sake nufar zahra.

Sai da mashkhur ya rintse ido sosai sanan ya iya kai hanunsa jikin zahra, yana kai hanunsa ya d'aga ta sama cak kamar wata 'yar tsana duk da kuwa nauyin ta da 'yar qibar ta, sam mashkhur bayasan zahra ta ta6a jikinsa sabida tsabar tsantsami. Yana kai ta toilet ya ajiye ta a kusa da ruwan daya had'a mata. Murya a daqile yace ina zuwa karki fara wanka.

Mashkhur yana fita daga toilet d'in ya fuce daga bedroom d'in sanan ya wuce bedroom d'in zahra, yana shiga ya nufi bed ya fara bincika kaya kan bed d'in. Yana cikin binci kawa ya samu doguwar rigar zahra, mara nauyi d'auka yayi ya had'a da d'an kwali sanan ya fuce daga bedroom d'in. Yana komawa bedroom d'in shi ya nufi wardrobe ya dakko towel d'in shi, sanan ya dawo sofa ya d'auki ledar audiga ya bud'e ledar ya zaro d'aya sanan ya d'auki pants d'in ya wuce toilet.

Yana shiga ya ajiye mata kayan a kusa da ita sabida karta sha wahala, mai makwan ya ajiye mata rogar a inda ya ajiye mata towel da pants d'in sai mashkhur ya sha'afa ya ajiye mata rigar a kan sin d'i toilet d'in sanan ya fuce tare da janyo qofar toilet d'in. Zahra kuwa ajiyar zuciya ta sauke sanan ta fara qoqarin cire rigar ta. Dama Allah ya sani zahra ta gaji da zama da rigar asibitin nan tunda aka sallamota ko wanka batayi ba, gwarama a asibitin ana qoqe mata jikinta.

Da kyar zahra ta iya cire rigar, bayan ta cire rigar ta cire bre d'in ta tana cirewa ta fara wanke kanta da kayar zahra ta iya wanke kanta shima ba wani sosai ya fita ba. Bayan ta gama wanke gashin nata wanka ta farayi, tana wanka tana jin qoshinta yana mata zafi wato inda ya fashe a kanta. Amma dai haka zahra ta daure ta qarasa wankan.

Bayan ta gama wankan goge jikinta tai sosai da towel bayan ta gama goge jikinta mayar da bre d'in

Please Login or Register in order to submit comment