Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ta biya mae kud’in rogan. Yana qarasawa yayi mata sallama. Amsawa tai tare da cigaba da yiwa dady murmushi. Malama lafiya kika biyamin kud’i nayi siyayya?. Haba bawan ALLAH ai ka tsaya mu gaisa koh?.

Had’e rai dady yayi tare da cewa ni ba wannan ne ya kawo niba kawai tanbayar ki nayi, kuma nafi buqatar amsarki fiye da gai suwarki ya fad’a fuska a had’e. Tom da farko dae ni sunana HALIMA, kuma abidda yasa na biya ma kud’in rogonnan kwai birgeni kayi shiyasa na biyama.

Wani do gwan tsoki dady yaja tare da cewa toh ni nace ki biyamin ee yee?. Aaa nifa nace ma kawai dae birgeni kayi shiyasa. A fusace dady ya curo 1k ya miqawa mata tare da cewa dalla karb’i kud’in ki. Haba bawan ALLAH dan Allah ka bari Wallahi ni bazan karb’a bah, kawaii ka mae da kud’in ka.

Dady da yaga zata b’ata mae lokaci juyawa yayi ya koma wajan mae rogan ya bata 1k d’in yace ta biya ta kud’in ta. Harya fara tafiya yaji mae rogan tace canji fa?. Ki riqe kawai daga haka bae sake cewa komai ba ya kama hanya ya wuce.

Ban garan budurwar nan kuwa a hanzarce tabi bayan dady, kafin ma ta qarasa wajansa ya haye mota ya tafi. Itama a hanzar ce ta tsari a dae-dae ta, tace yabi motar da dady yake ciki.
Haka tai-ta binsa har sae da suka qarasa hotel d’in. 6an garan dady kuwa bai san ma budurwar nan tana binsa ba.

Bata bari ya gan taba labewa ta ringa yi. A baya a baya ta ringa bin dady cikin hotel d’in in security suka tanbaye ta daga ina? Sae tace tare da dady take. A baya a baya ta d’inga bin dady har sai da tayi nasarar gane room d’in dady. Cikin farin ciki ta koma gida.

Bayan ta koma gida ta samu mahaifin da magar dady. Umma kinga wani d’an gayu yau dana had’u da shi gashi kyakyawa kuma Wallahi daga gani mae kud’in mutumin nan. Ai mahifiyarta tanajin hakan ta gigice, sabida babarta tana san mae kud’i kuma tana so ‘yayan ta su auri mae kud’i.

Haba ‘yar nan a ina kika had’u da shi.?
Nan da nan halima ta kwashe komai ta gayawa babarta. Ai momy qara gigi cewa tai da taji bae saurari halima ba. Ke d’auko min mayafina naje gidan BOKA Wallahi sae ya aure ki. Ba musu halima ta d’aukkowa umma mayafi.

Ai tindda umma ta fita bata tsaya ko inaba sae wajan bokan ta, data saba zuwa. Duk abidda yafaru ta bashi labari. Wata shegiyar dariya boka yayi tare da cewa yanzu mae kikeso ayi mae?. Murmushin mugunta umman halima tayi tare da cewa kwai so nake yaji duk duniya baya son kowa sae halima ‘yata, bayan nan kuma ya aure ta.

Dariya boka ya sake kwashewa da ita kafin yace abu mae sauqi kenan, yanzu zan baki magani da tirare da kwalli. In kikayi ammani da abubuwa ukun nan buqatar ki zata biya. Cikin farin ciki umman halima tace Yauwa boka ka tabbata zae yi kuma ya za’ai an fani da wad’an nan kayan da ka bani?.

Had’e rai boka yayi tare da cewa kee karki raina min hankali mana, na tab’a yimiki aiki bai’yiba ne?. Kayi haquri boka na tuba, harara ya watsa kafin yace kee dallah ya i’sa ki saurare ni kiji yadda za’ai an fani da maganin.

Yauwa inaji boka. Shi wanna maganin a abinci za’a samai yaci, kuma in so samu ne, a zuba mae a nama. Shi kuma turaran nan sa shi za tai a jikinta in zataje kae mai abincin. Shima kwallin sashi za’ tai. In dae sukayi ido hud’u da kwallin nan ba zai iya yi mata musuba ko ta bashi abinci zai ci..........

Typing............

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Free book*💜❤️💜

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina nai muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna zauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜❤️

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment........ pls, sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.💜❤️💜

Typing........

ADALILINTA.💜❤️💜

BY AMINA BAYERO.💜❤️💜

*Free book.💜❤️💜

Typing........

*page 17*
In dae sukayi idanuwa hud’u da kwallin nan ba zae iya yi mata musu, ko ta bashi abinci zae ci........

Shi kuma tiraran nan in dae yaji qam shinsa bazai iya tab’a korarta daga wajan saba. Shikuma maganin nan in dae yaci to fa zai ji duk duniya ba wadda yake so sama da ita kuma sae ya aure ta. Kije kiyi abidda nace kuma karki bani kud’i. Na sae buqatar ku ta biya.
Cikin farin ciki umman halima ta tashi ta tafi.

Washe gari.
Umma da halima suka shiga kasuwa dan yin cefa nan abincin da zasu dafawa dady.
Bayan sun dawo sukayi mae girki mae rai da lafiya. Farfesin kaza ne yasha kayan qamshi da maganin da boka ya basu. Sai farar shinkafa da taliya, sai kuma lafiyayyan lemo.

Wajan qarfe hud’u na yamma (4:00 pm) halima ta kama hanyar zuwa hotel d’in da dady yake zaune. Ba ita ta qarasa ba sae wajan qarfe biyar. Bayan ta sauka daga a dae-dae ta, ta tsallaka ti-ti ta nufi hotel d’in. Ko da ta qarasa security basu hana ta shiga sabida sunga kwandda abinci a hanunta.

Bayan da halima ta shiga ciki sae da tayi da haske kafin ta gane d’akin dady. da kyar ta gano abidda yasama ta gone ta riqe number room d’in. Nocky take tayi ammi ina anqi bud’e qofar. Da ta gaji da danna qararrawar hannu tasa ta d’in ga buga qofar amma shiru.

Tayi wajan rabin awa (30 minit) a wajan ba’a bud’e ba, har ta fidda rai ta juya zata koma. Cikin baqin ciki take ta fiya, ai kuwa tana tafiya taji ta kusan cin karo da mitin, dagowa tae dan ganin wanene?. Wani wahalallan murmushi ta saki saka makwan ganin dady da tayi. Zuba mae ido tae.

Shima idon ya zuba mata dan yana so yasan inda ya sandda amma ya kasa tunawa. Muryarta ce ta katse shi da cewa sannu dazu, ai sai a lokacin dady ya gane ta, abindda yasa bae yi saurin gane ta daga farko ba, sabida kwalliyar da take face d’in ta. Lafiya mae ya kawo ki nan? dady ya tanbaye ta.

Wajanka nazo mana. dady ya bud’e baki kenan zae yi magana qamshin turaran boka da ya bawa halima ta shafa ya daki hanci dady. Bugu da qari kuma halima ta tsare shi da idanuwa ta da suka sha kwallin boka. Ai dady ji yayi ya kasa yi mata musu ko ya kareta kamar yadda yayi niya.

Tab da alama fa maganin boka ya fara ai’ki.🤔

Tom nagode abidda dady yace kenan ya kama hanyar d’akin sa. Itama bin bayansa tayi. Yana bud’e qofa ya shiga kafin dady yayi wani yin qurin ya rufo qofar ita, ta shige. Dady yana son yace mata, ta fuce ta bar mae d’akin sa amma ya kasa kamar wadda aka qullewa baki.

Suna shiga ta zauna a bakin gado tare da cewa nasan ka gaji koh tom ga abinci nan na kawo ma kaci, yau ba sae kaci na hotel ba. Dady ya bud’e baki kenan zae ce baya buqatar cin abincinta halima ta tsare shi da ido.

Da sauri dady ya had’iya magar da zae yi kawai ji yayi yace tom bari nazo naci, shima kansa bae san ya fad’a ba kwai ji yayi maganar tana futowa. Zama yayi akan capert halima ta fara zuba mae abinci. Ai dady tundda ya kai cokali d’aya bakinsa bae sake fahimtar komai ba sae da ya cinye abincin tass.

Ai dady ko kwakwaran matsi bae sake yi a wajan ba yaji duk duniya ba wandda yake so kamar halima.
-Tabb nikuwa nace asiria ya kama dady. Dama haka asiri yake da saurin kama mutum musumman ma a nama.
-koh MANZAN ALLAH (S.A.W) anyi mae asirin nama ya kama shi. Dan haka asiri gaskiya ne kuma anayi sosai. Tom ALLAH YA TAREMU DA AI KATAWA AMEEN.🙏🏼

Continuation.

Ai nan da nan dady ya saki jiki suka fara hira sosai da halima har sae da akayi kiran sallar magari ba. Lokacin da zata tafi dady har kud’i masu yawa ya bata. Wae tayi kid’in mota. Bayan haka sukayi musanyan number ya samata nasa itma ta sa mae.

Tom tundda daga lolacin kulluma dady sae sunyi waya da halima sun sha soyayya, dan wataran har gidan su yake zuwa. A ‘yan kwanaki nan shaquwa mae qarfi ta shiga tsakanin dady da halima. Lokacin da dady zai koma kano sae da halima ta kusan yin hauka, wai sae dai a d’aura musu aure su tafi tare.

Da kyar dady ya shawo kan halima sae da ya ce mata yana komawa kano zai yiwa iyayansa maga suturo magabata. Hakan ne kawai yasa halima ta haqura. Dady ya koma gida cikin qoshin lafiya, kuma yayi farin ciki da ya samu su ammi da mashkhur lafiya qalau.

Suma sunyi farin ciki da dawowar shi cikin qoshin lafiya. Bayan dawowar dady da kwana biyu ammi ta fara fuska tar canji daga wajan dady. Kullum cikin waya da halima yake tun yana b’oyewa ammi da mace yake waya harya dae na.

Yanzu kwata-kwata dady ya dae na bawa ammi kulawa duk hankalinsa ya koma kan halima. Kullum waya yake da ita. Harta kai ta kawo dady yana satar hanya da farra sabiya ya tafi kaduna wajan halima, da sunan kasuwa ya yake zuwa. In kuwa ya futa tun safe bashi zai dawo daga kaduna ba sae sha biyun dare.

Hakan ba qaramin d’agawa ammi da hajiya kaka hankali yake ba musumman ma ammi da take fuskantar canji daga wajan dady. Haiya kaka ce ta samu ammi da maganar sabida mae in dady ya fita tun safe baya dawo wa sae tsakar dare.

Har da ammi zata b’oyewa hajiya kaka sae taga hakan bae dace ba kuma ba lallai ne tasamu mafita ba in bata gayawa hajiya kaka ba. Dan haka ammi ta kwashe komai ta fad’awa hajiya kaka. Da yake dady ya sanarwa ammi komai game da halima, dama dady baya b’oyewa ammi komai.

Da hajiya kaka taji haka, hankalinta ba qaramin tashi yayi ba. haka ammi tai ta bata baki tana kwanttar mata da hankali. Hajiya kaka qin bacci tayi tace sae ta jira dady ya dawo itama ammi batai baccin ba, kawai mashkhur ta kwantar.

Bayan dady ya dawo da tsakiyar dare kamar yadda ya saba hajiya kaka tace in yacci abinci yayi wanka kafin ya kwanta bacci tana son maga da shi. Bayan dady yayi wanka yaci abinci ya amsa kiran hajiya kaka shida ammi sukaje kamar yadda hajiya kaka ta buqata.

Da hajiya kaka ta, tambayi dady game da zancan halima, ai kuwa ba kunya dady ya amsa mata da ehh hakane. Kuma harda qarawa da cewa san ta yake dama yana so ya gayama hajiya kaka a tura magabata su nema mae auran halima.

Ba hajiya kaka ba hatta ammi sae da maganar ta girgiza ta. Nan hajiya kaka ta nunawa dady bata yadda da auran halima ba, kuma dududu yaushe akayi auran sa, da ammi shekara biyune kacal fa. Dady ya rikirkice da hukinci hajiya kaka dan kamar yayi kuka.

Kuma gashi ta hana shi yace komai. Haka suka tafi d’aki shida ammi kowa zuciyar sa ciki da baqin ciki. ALLAH sarki ammi baiwar ALLAH gani take kamar wani laifin ta yiwa dady ya juya mata baya lokaci guda.

Shi kuwa dady bayan sun shiga d’aki magiya ya shiga yiwa ammi akan ta lallab’a hajiya kaka ta aminci da magar auran. Harda tsugunawa a qasa da hawaye yana roqan ammi, ta shawo mae kan hjy kaka.Tabb nikuwa nace abin babba ne, ko da yake ai aikin asiri ne.

Ammi kuwa hankalinta ba qaramin tashi yayi ba da taga hakan. ga baqin cikin halima, ga tashin hankalin rikicewar da dady yayi. Ammi kuwa cikin tashin hakali take bawa dady haquri kuma tayi mae al qawarin ya kwantar da hankalin sa, zata shawo mae kan hajiya kaka har sai ta
amince...........

Typing.........

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Hmmmmm kunga irin matan al janna kenan ba irinmu ba, dan koni AMINA BAYERO bazan yadda da maganar dady ba🙅‍♀️Ahh too 💁🏻‍♀️

*Ina godiya da masoyana masu bibiyar littafin na mae suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi. Kuma da fatan zaku cigba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.......💜❤️💜

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment......pls sabida hakan shi zai bani qarfi guwar cigaba da rubutawa.

*ga masu buqatar littafin ADALILINTA da nayi posting sun d’inga karan tawa sae suyimin magana ta wannan.number 08142247343 WhtsApp kawai badda kira. Free book ne bana kud’i ba koma new book.

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*page 18*
Ya kwantar da hankalinsa zata shawo mae kan hajiya kaka har sai ta amince ...........

Adaran nan dae daga ammi har dady ba wandda ya rintsa, kowa zuciyar sa cike da bakin ciki.
Washe garima dady da ya tashin ba lafiya ya tashi ya kasa aikata komai. sae magiya yakewa ammi taje ta shawo kan ammi. ALLAH sarki ammi bae war haka taje ta samu hajiya da maganar.

Hajiya kaka kuwa taqi amincewa daga qarshe ma hajiya kaka rufe ammi tayi da fad’a wae batasan ciwan kantaba. Yau kwana uku kenan kullum sae ammi tayiwa hajiya kaka magiyar ta amince amma taqi. Shikuwa dady ba ci bare sha har sanbbatu ya farayi.

Ammi kuwa hankalinta yayi dubu ya tashi, tun tana damuwa da halima harta dae na ita yanzu burinta hajiya kaka ta amince kar wani abu ya samu dady. Yauma kamar kullum tashiga d’akin hajiya kaka ta rusketa suna ta wasa da mashkhur, qaraswa tae tare da cewa hjy kaka sannu.

Had’e rae hajiya kaka tayi tare da cewa yauwa. Dama tun sandda ammi takewa hajiya kaka magiya ta aminci da maganar auran dady da halima take fushi da ita koh hira suka dae na. Wai sae tace ammi batasan ciwa kanta ba, dady yana zigata tazo ta shawo kan ta, ai mata kishiya.

Gefan hajiya kaka ammi ta zauna sae da tayi jim kafin ta fara cewa ammi dan ALLAH dan ANNABI, ki saurare ni. Shiru hajiya kaka tayiwa ammi. Wallahi hajiya baki ga yadda yaya Abubakar ya koma abin tausayi ba. Koh abinci baya ci bare bacci kullum kiran sunan halima yake.

Hajiya kaka kuwa tab’e baki tayi tare da cewa ai shi yaga zae iya. Qara kwantar da murya ammi tayi tare da cewa ammi nifa ina tsoran wani abu karya faru sabida na fahimci in dae baki amince da aurarn nan ba zae iya faru. Kallan ta hajiya kaka tayi tare da cewa mae kika fahimta?.

A jiyar zuciya ammi tayi tare da cewa Wallahi hajiya naga alama in dae baki amince da auran nan ba tom Wallahi yaya Abubakar zae iya guduwa kaduna yaje ya auro halima bada sanin kiba. Kuma nasan halinsa in ya tafi ba ranar dawo wa sabida kamar baya cikin hayyacin sa.

Kuma kinga in ya tafi bamu son gidan su yarinyar ba bare mu nemo shi. Jinjina kae hajiya kaka tayi sabida ta yadda da maganar ammi kamar Abubakar baya cikin hayyacinsa. Sabida hajiya kaka ta son in dae ta nuna mae bata son abu tofa ko mene ya barshi, Amma bandda wanna karan.

Da haka dae ammi tai, ta rarrashin hajiya kaka harta amince. Lokacin da dady ya samu labari kuwa zo kaga farin ciki jiyayi son ammi ya qara nunkuwa a zhciyar sa. Sabida yasan ba ko wace mace bace taza iya abidda ammi tayi mae ba. Sabida tsabar dad’i dady har kyauta yayiwa ammi.

Tom tin da daga ranar dady ya fara shirya-shiryan auran halima. Dan harma an tura magaba kaduna domin su nemawa dady auran halima. 6an garan ammi kuwa ta zubawa dady ido tana ganin ikwan ALLAH. Ita kuma hajiya kaka abin ya dae na bata mamaki dan harma ta fara tinanin aikin asiri ne.

Dan haka ta fara neman malami mae karya asiri da sammu. Cikin ikwan ALLAH, ALLAH ya had’a ta da malam Ibrahim, kuma taje ta same shi domin ya karya asiri da sammun da akai wa dady. Bayan ta gayawa malam Ibrahim abidda ya faru, malam Ibrahim ya tabbatar mata da ai kin asirine, mae wuyar karyewa.

Kuma ya sanar da ita dole sae dady ya auri halima za’a iya karya asirin. Sabida sin yi mae abidda dole sae ya auri ta in kuma bae aure taba tom fa duk duniyar nan zata dae nai mae dad’i. A ala dole hajiya kaka ta haqura ta koma gida. Bayan ta koma gida bata gayawa ammi ba kwai dae ta bar abin azuciyar ta.

To fah biki ya kakkama, yanzu d’aurin aure ya rage saura kwana uku. 6an garan dady kuwa ya gama shiryawa, dan har gidan da halima zata zauna ya samar mata kuma har dangin ta sun zo sunyi mata jere duk da dae ba abin arziqi suka zuba mata ba.☹️

6an garan su halima kuwa suna can suna shirya-shirye, biki da bugu da qari ma harda asiri da sammu suke had’awa. Wae in halima taje gidan dady ta malla ke shi, ta rabashi da kowa daga ciki kuwa harda mahaifiyar sa da ammi. Lokacin ma da halima ta samu labarin dady yana da aure hankalinta ba qaramin tashi yayi ba.

Wae harda cewa dady sae ya saki matar sa zata aure shi. Shikuwa dady ya nuna mata bazai iyaba yana son matar sa, ba zae iya rabuwa da itaba. A ala dole halima ta haqura badan sar rantaba. Kuma taci al washin in dae ta shiga gidan dady sae tasa ya saki ammi.

WAE WACECE HALIMA.? KU BIYONI DOMIN SAMUN AMSAR TANBAYAR KU.

Iyayan halima, malam garba da hajara‘yar asalin barno mae duguri ne. Abidda ya barosu da garin su gudun hijira ne. Lokacin ‘yan tada gayar baya suka shugo garin su shine suka gudo suka tawo kaduna. Tom anan kadunar aka d’aurawa mlm garba da hajara aure.

Bayan wata tara suka haifi ‘yarsu halima(momy) bayan momy tayi shekara biyar da haihuwa suka qara haifar ‘yar su mace saratu. Tun daga nan ALLAH bai qara basu haihuwa ba. Hajara mahifiyar momy cikakkyar mushirka ce kullum a bun boka take.

Haka zalika kullum malam garba mahifin su momy a ciki fad’a yake mata. Kai da mahifiyar su momy ta gaji da nasihar da, mlm garba yake mata sae ta kae shi wajan boka sabida a kulle mata bakin mlm garba, dan ya dae na sa mata ido. Ai kuwa haka akayi boka ya bata magani domin ta zuba mae a abinci.

Tun daga ranar bae sake yi mata magana ba duk abidda ya gani. Kullum cikin sallah yake da roqan ALLAH ya shirye ta. Tun su momy da saratu basu koyi zuwa wajan boka da yadda da maganar sa ba har sae da hajara ta hure musu kunne, suka koya. matsala tana taso wa suke tafiya wajan boka.

Boka ne kawae yake gayawa su momy magana su yadda. Hajara gata da masifar son kud’i, burunta kawae ‘yayan ta su auri mae kud’in. Kullum yawo take wajan boka sabida ‘yayan ta su auri mae kud’in har ALLAH ya had’a momy da dady, kuma sukaja hankalinsa ta hanyar asiri.

Wannan kenan

Yau asabar aka d’aura auran Alhji abubkar (dady) da sahibar sa halima (momy) a garin kaduna. Ansha biki an gama biki lafiya, su dae ammi da kaka ba wani baki da sukayi. Bayan an d’aura aure qarfe hud’u aka kama hanya domin kawo amarya kano gidan dady.

An kawo amarya lafiya amma dangin amarya sunce sae washe gari zasu koma a gidan amarya zasu kwana. Ba yadda dady ya iya da su haka ya koma gidan su ammi ya kwana duk da bae soba. Washe gari bayan dangin amarya sun karya suka had’a kayan su dan komawa kaduna. Dady ne ya biya musu kud’in mota.

Bayan tafiyar dangin amarya dady da momy suka fara shan soyayyar su. Sabida tsabar asiri da sammu sae da dady yayi sati d’aya bae futo daga gidan amaryar sa halima ba.
6an garan ammi da hajiya kaka ba qaramin tashin hankali suka shigaba.

Dan koh sun bugawa dady waya ba zuwa yake ba. Dan haka hajiya kaka ta tafi wajan malam Ibrahim dan ya karya mata asiri da sammu dady ya dawo cikin hankalinsa.
Koh da taje malam Ibrahim ya bata shawara akan ayi mae kiranye han kalinsa ya dawo kan su.

Hajiya kaka ta amince kuma ta biya kud’in aikin. Malam Ibrahim yayi mata al’qawari Zuwa gobe dady zai dawo gida, kuma zae bata magani ta zuba mae a nama kamar yadda aka farai mae asirin a gidan su halima, in dae ta zuba mae yaci komai zai karye...........

Wanan page d’in na sadaukar da shi ga doctor
maryam sabida tana yimin comment.

Typing.......


ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*free book*

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi kuma da fatan zaku cigaba da bibiya harna sauke littafin ADALILINTA.

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment........pls, sabida hakan shi zai bani qarfin guwar cigaba da rubutawa.

Typing..........

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*free book*💜❤️💜

Typing..........

*Page 19*
In dae ta zuba mae yaci komai zai karye.........

Ae kuwa cikin ikwan ALLAH washe gari dady ya dawo. hajiya kaka kuwa ta bawa dady farfisin nama da yasha maganin malam Ibrahim.
Ai kuwa a ‘yan kwanankin nan su ammi sun samu canji dan dady ya fara dawowa hayya cinsa.

Dan yanzu yana raba kwana tsakanin ammi da momy, kuma yana zama a gidan su ammi ba kamar daba. A hankali- ahankali dady ya dawo cikin hayya cinsa dan yanzu ya fara tsawatar da momy in tae mae laifi . Ba kamar daba da baya ganin laifinta kwata-kwata.

Ita kuwa hajiya kaka da ta ga dady ya dawo cikin hayyacinsa batai qasa a guiwar ba ta tafi wajan malam musa domin yayi wa dady addu’a yadda koh nan gaba baza a qarai mai asiri ya cishiba. Haka akayi ya bata addu’a yace da ita da ammi da shi kanshi Dady su d’inga yi.

Ai kuwa dady bai qi addu’ar ba dan shi yana da son addu’a. Dady yayiwa halima(momy) magana a kan taje ta gai da hajiya kaka amma ta fafire qasa wae bazata ba. Ai kuwa dady yayi mata jan ido yace mata akan hajiya kaka koh ammi Wallahi zai iya rabuwa da ita.

Hakan ne ya d’agawa momy hankali kuma ba shiri ta shirya suka tafi. Ko da dady ya kai ta gidan su ammi tafiya kasuwa yayi ya barta a gida. Ai kuwa ta kae hannu zata d’auki mashkhur ya stallara mata ihu, alamin bayasan ta d’auke shi hakan ba qaramin b’ata mata rae yayi.

Ai kuwa ta ringa watsawa ammi kallan banza kae har hajiya kaka ma bata gyaleba. Ammi ta yi mata girki kaka-kala ammi qiri-qiri taqi ci. Kae koh ruwa bata shaba haka ta wanu. Da yamma dady yazo ya mayar da ita

Please Login or Register in order to submit comment