Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Yau kimanin sati biyu kenan zahra tun tana iya boye damuwar ta har ta kasa. Itama 6angaran nana har yau tana fama da son abdul kuma bata dena tura mai message ba in ya tambaya wace sai tace mai zata fad'a mai amma ba yanzu ba, tun yaya abdul yana tambayar wacece nana har ya dai na. 6angaran ilham da ahmad kuwa kullum soyayay qaruwa take ga lokacin aure yana matsowa dan har ilham ta fara tianin komawa gida mama ce ta hana ta tace da can da nan ai duk d'aya ne.

zahra tana zaune a gefe ta kifa kai akan guiwar ta tana tunanin yaya mashkhur, wani irin mugun son ganin yaya mashkhur zahra take, ji take kamar ta rufe ido ta gan shi a kusa da shi. Zahra tana cikin wanan halin taji an dafa kafad'ar ta, da sauri ta d'ago dan ganin waye?. Ilham ta gani tana shirin zama a kusa da ita. Zahra kwana biyu na kasa gane maki wai mai yake damun ki.

Wlh ilham kwana biyu duk bana jin dad'i wai mai yake kawo yawan tinanin mutum da mafarkin sane ne, kaji kana mugun son ganin shi?. Cikin mamaki ilham tace SO mana zahra tinanin wa kike yi haka ne?. Zaro ido zahra tai tare da cewa haba dai ilham so kuma aaa wlh ni ba son shi nake ba kwai dai inajin abun da nai mai ne ban kyau ta ba shi yasa nake yawan tinanin.

Wlh zahra I'm serious nake gaya miki kina nufin wai kin fara son yaya mashkhur d'in ne ko kuwa?. Nan da nan zahra ta fara zazzaro ido tana girgiza kai tare da cewa ALLAH ya kiyaye ilham kema kin san ai bazan so shi ba. Wani qasai taccan murmushi ilham ta saki sare da cewa tom shikenan zahra tinda kin ce haka mu zuba mu gani, wanan abubuwa da kika lissafo shine alamun so ai.

KANO.

Yau kimanin sati biyu kenan da mashkhur ya share zahra,. Yana zaune akan sofa ga laptop a gaban sa ya zuba mata ido amma a zahiri gaskiya ba laptop d'on mashkhur yake kallo ba tinanin zahra kawai yake. Jiki ba kwari mashkhur ya janyo wayar shi ya shiga content ya fara lalubo number zahra dan har ga ALLAH ya gaji da shariyar da yake nunawa zahra.

Yayi qoqarin mantawa da ita amma ya kasa, mashkhur ya dannawa number zahra kira yaji wayar a kashe. Wani dogwan tsaki mashkhur yaja tare da yar da wayar gefe a fusace ya miqe ya fuce daga d'akin. Yana fita bai tsaya ko ina ba sai part d'in ammi, a zaune ya tarar da ruma da ameer, ruma tana koyawa ameer home-wrok. Ko ta kan su mashkhur bai biba bare ya amsa gaisuwar da ruma take mai ya haye kan bene.

Yana hawa bai tsay ko ina bai sai d'akin ammi, mashkhur da ya shiga bai tarar da ammi ba toilet ma abud'e yake bare yayi tinanin tana ciki. Mashkhur sai da ya duba duk in da yake tunanin ammi tana nan amma bai same ta ba, rai ba dad'i ya sauko qasa yana sakowa ya nufi wajan ruma. Yana zuwa yace ruma ina ammi take?, ta tafi kai wa dady abinci, ruma ta bawa mashkhur amsa a taqai ce.

Daga haka mashkhur bai sake cewa komai ba ya fuce daga d'akin, direct part d'in dady mashkhur ya nufa yana zuwa bai tsaya ko ina ba sai qofar bedroom d'in dady. Mashkhur yana zuwa qofar d'akin mai makwan yayi knocking kamar yadda ya saba, kawai ya murd'a handel d'in qofar da qarfin gaske ya shige d'akin. Tinda mashkhur ya mallaki hankalin kan sa bai ta6a shiga d'akin dady ba knocking ba musamman in ammi tana ciki sai yau.

Mashkhur yana shiga bedroom d'in ya tarar da dady zaune yana cin abinci, ita kuma ammi tana daga gefe tana zaune da dukkan alamu dai hira suke. Amma jin an turo qofar da qarfi ba knocking bare neman izi ne yasa ammi da dady suka d'aga ido dan ganin wake shigowa. Mashkhur suka gani ya shigo a zuciye fuska ba walwala.

Cikin mamaki ammi tace mashkhur menene haka kuma mashkhur, baka da hankali ne? abinda ba kai da yarintar kaba shi za kai yanzu iyayan ka suna cikin d'aki zaka banko qofa ba izini bare knocking ko sallama mashkhur wanan fa haramun ne. Haba ammi da dady dan ALLAH ku tausayawa rayuwa ta ku dawo mun da matata ku dena yimin wasa da hankali na haka?.

Cikin mamaki ammi da dady suka kalli juna, mai sunan baba mu muke ma wasa da hankali menene laifin mu a ciki ai kasan inda matar taka take kaje ka d'auko ta mana. Haba dady sau biyu fa nake zuwa wajan ta amma taqi ta amince qarshe ma bama rabuwar kirki tace karna sake dawowa wajan ta na manta da ita. Oh to dama ai shi masoyi majin yaci ne mashkhur ka dai cigaba da haquri da lalla6a ta harta sauko.

Ko yaya cewar ammi, dady cefe zancan yayi da cewa kwarai ma kuwa maryam, kasan dai da in munyiwa mamana dole to yanzu baza muyi mata ba bawai dan bamu isa da ita bane aaa, sabida itama ta samu 'yan cin kan ta dan sabida kai bazamu sake tursasa ta tai abinda kake so ba. Yadda muke son ka haka itama muke son ta, dady ya qarasa maganar yana cigaba da cikin abincin sa. Haba dady ammi ya kuke min haka ne wai anya ma ku kuka haife ni gaskiya na fara tanta ma.

Hmmm mashkhur kenan in rai ya 6aci hankali baya gushewa fa, bai kama ta suna iyayan ka ka tsaya a tsaye a kan su kana gaya musu magagganu ba. Cewar amina bayero amma in bakaji dad'in nasihata ba kayi haquri karka wuce a kai na. πŸ˜‚

Yau ma naso nayi muku double page amma ALLAH bai ba wanan d'in ma da kyar kuka samu wlh. πŸ˜‚

ALLAH sarki yaya mashkhur. πŸ˜₯

Anya zahra bata fad'a ba kuwa. πŸ€”

Mu had'e a next page.

[23/04, 8:29 pm] Oum Farhan❀️🩷:

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing.............

*page 118*

Yadda muke son ka haka itama muke son ta, dady ya qarasa maganar yana cigaba da cikin abincin sa. Haba dady ammi ya kuke min haka ne wai anya ma ku kuka haife ni gaskiya na fara ta

Au mashkhur tantama ma kake akan mune iyayan ka anya kana cikin hankalin ka kuwa mu kake cewa haka?. Mashkhur kamar yayi kuwa yace haba ammi ba dole nai tantama ba sai ku ringa yimin abu kamar bakwa sona ko kamar ba ku kaka haife ni ba, duk kunbi kun share ni, baza ku iya yimin abinda nake so ba gaskiya dai kam abu nan yana ban mamaki kuma sam bana jin dad'in hakan da kuke min.

Daga haka mashkhur ya juya ya fuce a fusace ko qofar ma bai samu damar rufowa ba. Cikin mamaki dady ya kalli ammi tare da cewa to maryam anya wanan yaran ba shaye-shaye ya dawo yi ba, jifa yadda yake magana magana ba respect kamar shi ya haife mu. Nima haka nake gani yaya gaskiya dai kam ina ga kwakwalwar mashkhur ta fara ta6uwa, ina ga kawai zan lalla6a zahra ta haqura su cigaba da zaman aure.

Ammi ta fad'a hakan ciki tausayawa mashkhur, aaa kawai ki rabu da su kar kiyi hakan in mamana tana son shi da kan ta zata amince in kuma bata son shi baza'a yi mata dole ba, dole kuwa ya haqura tinda duk abinda ya faru shi ya jazawa kan sa. Kai amma dai gaskiya ina tausayawa mashkhur ni kam karfa dai wata cutar ta kama shi, tin da dai bai ta6a soyayar nan ba kuma yayi ladama sai ai mai uziri.

Girgiza kai dady yayi tare da cewa a hakan za'a ba shi ita, ai har yanzu bai yi laushi ba tinda har zai iya tsayawa a gaban mu ya gaya mana magana ki bari sai ya qara hankali sosai zamu sa baki a lamrin nan, amma gaskiya ina tausayawa mashkhur tinda fa yake ni ban ta6a ganin abinda ya tashi hankali sa akan abinda yake so ba sai wanan karan, yaci ace yayi zuciya da zahra ya haqura amma ya kasa, ammi ta fad'i hakan cikin tausayawa.

Nima ina tausaya mai maryam amma ya zama dole mu danne tausayin nan, ta hakan zai gane darajar ta ko an bashi ita nan gaba zai tattala mana ita fiye da kansa amma in ya same ta ta sauqi bazai riqe ta sosai kamar yadda muke muradi ba kawai mu rabu da shi ya cigaba ba da rarrashin mamana har ta amince. Jiki a sanyaye ammi tace gaskiya ne to ALLAH yasa komai yazo da sauqi. Amen dai, cewar dady......

Mashkhur yana fita bai zame ko ina ba sai bedroom d'in shi, yana shiga ya fad'a kan gado zuciyar shi sai wani quna take. Mashkhur ya rasa mafita ji yake rayuwar gaba d'aya ta mai zafi gwara ya mutu ya huta ko zai samu salama. Tinda yake a rayuwa sa ba abinda ya ta6a sa shi damuwa mai tsanani irin soyayyar zahra. Mashkhur yana so ya koma shaye-shaye amma ya kasa.

Sabida tsabar damuwa har nunfashin sa d'aukewa yake na wasu daqiqu,. Wani irin mugun son zahra ne yake damun mashkhur, sam baya iya minti 2 bai yi tinanin zahra ba sam mashkhur baya samun salama sai ya kwanta bacci shima bacci ba sosai yake iya yi ba sai yaci qarfin sa. Ko yaci qarfin nasa yana farawa yake mafarkin zahra iri-iri yanzu dai mashkhur ya koma abin tausayi ba wai.

To daran ranar dai mashkhur ko rintsawa bai iya yiba, a zaune ya kwana yana tinanin zahra,. Washe gari da asuba kuwa yana idar da sallah ya sheme akan gado, wani mugun zazza6i da ciwan kan damuwa ya rufe shi ruff dan ko d'an ya tsan shi baya iya d'agawa, yana so ya tashi yaje wajan aiki amma ya kasa..........

Misalin qarfe 4 na yamma abdul da ammi suna zaune suna cin abinci. Ammi wai ina yaya mashkhur ne? Cewar abdul, gaskiya nima ban sani ba abdul amma ina tinanin tinda ya fita da safe wajan aiki bai dawo dan yau ni ko shigowa nan bai ba. Aa yaufa inaga yaya mashkhur bai fita ba, wajan qarfe goma da na fita naga yana nan kuma dana dawo ma naga motocinsa duk suna nan alamun dai bai fita ba.

To ai ni ban sani ba, fushi yake dani inaga ga shi yasa bai shigo ba. Cikin mamki abdul yace fushi kuma ammi yaya mashkhur ai bazai yi fushi da ke ba tinda bai ta6a hakan ba mai ma zaki mai yayi fushi da ke. Hmmm to daga ni dai har dadyn ku fushi yake damu wai sabida zahra. Cikin mamaki abdul yace zahra kuma ammi mai zahra tai.

Girgiza kai ammi tai tare da cewa ba abinda zahra tai, kawai dai ya fara son tane shine mukace ba ruwan mu yaje ya bata haquri har ta amince zata cigaba da zama da shi, kuma da yaje bata amince ba, shine wai yake jin haushi dan bamu sa baki ba zahra ta amince, jiya baka ga yadda yayi mana ni da dady ku ba har d'aga mana murya yake abin dai ba dad'i wlh abdul.

In hankalin abdul yayi dubu kuwa ya tashi da yaji ammi tace yana son zahra dan tin daga nan bai sake gane abin ammi take cewa ba. Inalilahi'wa'inna'ilaihirraji'un, abinda abdul yake ta fad'i a zuciya shi kenan, dan yasan yanzu lamarin zai qara kwa6ewa yana barazanar rasa zahra. Abdul abdul, firgigit abdul ya dawo daga dogwan tunanin da ya tafi.

Na'am ammi cikin mamaki ammi tace abdul lafiya naga lokacin guda ka canza. Amm uhmm ammi ba komai kawai dai abin ne yaban mamaki gaskiya dai nasan mashkhur duk yadda ya kai da yi miki laifi bazai qi zuwa gaishe ki ba inaga dai ko sun fita tare da ahmad ko kuma yaran nan nasa ne yazo d'aukar shi ko kuma tun da safe bai fito ba baya jin dad'i amma bari naje na duba.

Daga haka abdul ya miqe zuciya cike fall da takaici sabida wannan mumunan labarin da ya samu a wajan ammi. Abdul tafiya yake amma ji yake kamar ya fad'a sabida tsabar rud'a ni da tashin hankali, dan shi duk duniya baya son abinda zai raba shi da zahra, ba abinda yake furtawa sai qalu Inalilahi'wa'inna'ilaihirraji'un, yana tafe yana had'a hanya har ya qarasa part d'in nasu.

Yana zuwa part d'in shi direct d'akin shi ya nufa ya fad'a kan gado zuciya cike da baqin ciki kamar zai mutu haka abdul yake ji. Tabbas yasan tunda mashkhur yace yana son zahra to abun ya kwa6e mai lokacin rabuwar sa da zahra ya qara to. Abdul ji yayi yana tantama akan zancan da ammi ta gaya mai na cewa mashkhur yana son zahra, gani yake kamar mashkhur wasa yake da hankalin su so yake kawai ya cigaba da zalintar zahra.

Abdul ya d'au kusan awa uku a wanan halin sai da yaji ana kiran sallah sanan ya miqe ya d'aura alwala ya nufi masallaci. 6angaran mashkhur kuwa yau wuni yayi a d'aki yana aman jini sabida tsabar damuwa, tun yana iya miqewa ya shiga toilet yayi aman jini harya kasa. Duk yabi ya fita daga hayyacin sa sunan zahra kawai yake kira,.

6angaran abdul kuwa bayan ya dawo daga masallaci direct ya nufi hanyar d'akin mashkhur, sabida ya tabbatar da gaskiyar lamarin wai da gaske mashkhur yana son zahra ko kuwa?. Abdul yana zuwa qofar d'aki mashkhur ya fara knocking. Ya d'au kamar 5 minutes yana knocking amma yaji shiru ba'a bud'e ba kuma ba'a bashi izinin shigowa ba.

Zuciya ciki da damuwa abdul yasa hannu ya murd'a handel d'in qofar bedroom d'in, sanan ya shiga baki d'auke da sallama. Amma shiru yaji mashkhur bai amsa mai, ya wani nan nad'e a kan gado ya shige cikin blanket. A hankula abdul ya fara qarasowa wajan mashkhur, abdul in idon sa ya gane mai dai-dai gani yayi kamar jikin mashkhur yana rawa, ga jini-jini a farin blanket d'in.

Cikin tashin hankali da mamaki abdul ya qarasa ya yaye blanket d'in da mashkhur ya rufa. Gani yayi jikin mashkhur yana rawa-rawa haqoransa suna had'ewa kamar mai jijiga, ga bakin sa duk jini-jini harma ya ta6a rigar shi ga dukkan alamu dai aman jini yayi. Cikin tashin hankali abdul yace yaya mashkhur lafiya mai yake damun ka haka?. Mai makwan mashkhur ya bawa abdul amsar da ya tambaye shi sai ya fara cewa zahra.

Ina zahra take yaushe zata zo zahra! Zahra! Zahra kina jina kuwa?. Cikin mamaki abdul yace yaya mashkhur zahra kuma abdul ne fa yake ma magana. Baki na rawa mashkhur ya cigaba da cewa zahra zahra dan ALLAH ki yafe min zahra wlh ina son ki zahra ina qaunar ki zahra, bazan iya rabuwa da ke ba zahra. Nan da nan mamaki ya sake kashe abdul sai a lokacin abdul ya gane mashkhur ma baya cikin hankalin sa ya fuce daga hayyacin sa gaba d'aya.

Hospital.

Bayan an kai mashkhur asibiti an duba shi, likitoci sun gano yawan damuwa ne da tunani suka sa shi aman jini, kuma sunce in bai rage yawan damuwa da tinanin ba hawan jini ko ciwan zuciya zai iya kama shi ko da yau she. Sanan sunyi mai allurori da qarin ruwa, kuma sun bashi gado wato an dai kwantar da mashkhur a asibiti. Hmm hankalin mutan gidan ya d'an tashi ba laifi musamman ma ammi da abdul da hjy kaka. Bayan dare yayi kowa ya koma gida abdul ne kawai ya zauna domin kula da mashkhur.

KADUNA.

Zahra tana daga kwance a kan bed nana da ilham sun dad'e da yin baccin. Ita kuma ta kasa bacci haka nan taji gaban ta yana fad'uwa ga mugun tinanin mashkhur da take dan har ta biga wayar shi amma taji bata tafiya. Yanzu zahra ko ba'a gaya mata ba ta sheda tana mugun son mashkhur. Idon zahra ya soye har wajan 12 dare ta kasa bacci tunanin mashkhur kawai take.

Zahra tana cikin wanan halin taji wayar ta tana ringing, a hankula ta zura hanun ta a qarqashin fulo ta d'auko wayar tata. Sunan abdul zahra ta gani a kan wayar, farin cikin rai na sai jan heart guda biyu d'aya da mashi d'aya kuma babu, a haka zahra tai save d'in number yaya abdul. jiki a sanyaye zahra ta d'auka tare da karawa a kunan ta tana cewa hello farin ciki na. Abdul rintse ido yayi zuciya cike fall da baqin ciki yace na am my zahra ykk?. Zuciya cike da damuwa zahra tace lafiya qalau yaya na, amma naji muryar ka ta canza anya kana lafiya kuwa?.

Ina lafiya zahra, zahra ta ina so muyi magana kina jina?. Gyara kwanciya zahra tai tare da cewa ina jinka yaya na, gyaran murya abdul yayi sanan yace zahra ina so muyiwa kan mu adalci ni da ke, muyi abunda ya dace karmu kasance masu son zuciyar mu. Cikin mamaki zahra tace yaya abdul yaudarar kai kuma mai yayi zafi haka dan ALLAH ka dena cewa haka mai ya faru?.

Wani gauran nunfashi abdul ya sauke sanan yace zahra, kiyi haquri ki koma wajan yaya mashkhur shine mijin ki kuma shi ya dace ya cigaba da zama dake a matsayin mata bani ba. Gaban zahra fad'uwa yayi rass, rass, rass cikin firgici tace haba yaya abdul sabida mai zaka ce haka kai ma kasan nice mallakin ka ko, ba yaya mashkhur da kai na dace ba da shi ba.

No zahra ki dena cewa haka, tun da ido na ya rufe shi yasa ban gane haka ba tun sanda aka d'aura miki aure da yaya mashkhur ya kama ta na cire rai da samun ki a matsayin mata. Zahra cikin kuka tace haba yaya abdul ka dena fad'in hakan in wani laifin nai ma ka gaya min karka hukunta ni da wanan yaya mashkhur zai sake ni kuma zan aure ka in sha ALLAH.

Rintse ido abdul yayi cikin baqin ciki yace zahra ba wani laifi da kika yimin kuma bazaki ta6a yimin laifi ba kawai dai abunda ya dace na gaya miki, yaya mashkhur yana son ki zahra ku amince da shi mana. Aaa yaya abdul nifa kai nake so ba shi ba, aaa zahra dan ALLAH ki dai na fad'in haka in dai kina so na kiyi mim alfarmar nan yaya mashkhur yana son ki.

Yanzu haka da nake gaya miki yana kwance a gadon asibiti ya zauce in banda sunan ki ba abinda yake kira har aman jini yake. Kuma likita yace yawan tunani ne da damuwa kuma zahra duk san ki ne ya jefa yaya mashkhur a wanan halin zan iya sadaukar da komai a rayuwa ta in dai a kan ki ne ko akan yaya mashkhur, bazan so yaya mashkhur ya shiga wani hali, sabida ni ba, zahra in sonki.

Amma na sadaukar wa yaya mashkhur ke ki cigaba da zama da shi a matsayin mijin ki, dan ALLAH ki so shi duk son da kike min ya koma wajan yaya mashkhur, zahra daga yau ki dai na min kallon masoyi kawai ki cigaba da kallo na a matsayin yayan ki dan ALLAH zahra ki min wanan alfarmar, daga haka abdul ya kashe wayar. Wani kuka tashin hankali ne ya kwacewa zahra.

Ga rashin lafiyar yaya mashkhur ga kuma rabuwar ta da abdul ga wani mugun tausayin abdul da mashkhur da ya rufe ta lokaci guda. Kukan da zahra take ne ya tashi ilham da nana, da sauri ilham ta mitstsike idanuwan ta tare da cewa zahra lafiya mai yake faruwa. Cikin kuka zahra tace ilham na shiga uku ina zan sa kai na yaya abdul yace bazai aure ni ba, na koma gidan yaya mashkhur da zama.

Oh su yaya mashkhur anga ta kai.

Wayyo zahra ciwo biyu. 😒

Wayyo my yaya abdul sorry πŸ’”πŸ˜’πŸ˜’ kunji mutumin kirki ko, shi yasa nace ku dai na zagin sa, ya sa daukar wa da d'an uwan sa soyayyar sa.

Hmmm ya za'a yi a warware wanan cakwakiyar? mu had'e a next page dan jin yadda zata kaya.


[23/04, 8:29 pm] Oum Farhan❀️🩷: ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing.............

*119*

Cikin kuka zahra tace ilham na shiga uku ina zan sa kai na yaya abdul yace bazai aure ni ba, na koma gidan yaya mashkhur da zama.

Wata daguwar ajiyar zuciya ilham ta sauke sanan tace, to zahra sai akayi mai dama abinda ya dace kenan inaga shima ya gane cewa kin fara son yaya mashkhur. Fuska sha6e-sha6e da hawaye zahra tace aa ilham ba haka bane wai sabida yaga yaya mashkhur bashi da lafiya wai yana aman jini kuma ya fita daga hayyacin sa sai sunana yake kira shine fa yace ya haqura.

Dafe qirjin ilham tai tare da cewa wayyo yaya mashkhur ALLAH sarki yaban tausayi gaskiya zahra yana son ki kawai kiyi haquri tinda kema kin fara son shi. Haba ilham amma yanzu in nai haka banwa yaya abdul adalci ba wlh, shine fa yake sona tsakani da ALLAH, tin ban san koni wace ba, amma yanzu ai ban mai adalci ba.

Aaa aunty zahra karki ce haka ai shine yace ya haqura ba ki kika qi shiba kawai kiyi haquri cewar nana. Share hawaya zahra tai tare da miqewa ta shige toilet, tana shiga nana tace alhamdulilah ta fad'i hakan tana sakin wani qasai taccan murmushi. Cikin mamaki ilham tace haba nana yayar ki tana cikin wanan halin amma naga kina farin ciki. Hmmm aunty ilham bazaki gane bane wlh raban da na samu farin ciki irin wanan har na manta.

Damo na ya kama harawa ai dole ki ganni cikin farin ciki aunty ilham. Cikin mamaki ilham tace to mai kuma ya same ki na farin ciki?, murmushi nana tai tare da cewa zan gaya miki ki bari sai gobe. Ya mutsa fuska ilham tai cikin murya san jin gulma tace aaa ke gaya min yanzu. Matsowa nana tai ta rage murya sanan ta sai ta bakin ta dai-dai kunan ilham tace, kin san wannan wanda muke turawa text message?.

Da sauri ilham tace ee na gane shi, cikin jin dad'i nana tace yaya abdul ne fa, bana son aunty zahra ta sani sabida naga tana son shi shiyasa nake 6oye muku. Dafe qirjin ilham tai cikin mamaki tace ke nana da gaske yaya abdul ne. Haba aunty ilham kiyi a hankula mana kar aunty zahra taji, da gaske nake mana ko da matsala ne naga kin d'an tsora ta.

Girgiza kai ilham tai cikin sassauta murya tace aaa ba wata matsala abin ne yaban mamaki dama duk yaya abdul muke turawa message d'in nan?. Jiki

Please Login or Register in order to submit comment