Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Itama zahra bin bayan hajiya kaka tai tare da cewa! Ilham dan ALLAH tinda ba sallah zaki ba ki d'ora mana shinka fa da wake kinji, wlh ita nake son ci na dad'e ban ciba. Hajiya kaka kuwa cewa! Tai ehh ai nasan shi yasa mai sunan malam ya dawo da ke gidanan amma da baki da ciki da bazai dawo mana da ke ba, yanzu ma sabida ki ringa samu abinda kike so kina ci ya dawo da ke.

Zahra kuwa shiru tai batace komai ba dan bama ta da abin cewa!. Ilham kuwa tana tsaye baki sake an barta cikin zulli, tana nazarin maganar cikin zahra, tana mamaki yaushe zahra ta fara 6oye mata wasu abubuwa har da samu cikin ta. Haka dai ilham ta haye sama ta wuce kicin d'in ammi ta fara qoqarin d'orawa zahra shinka fa da wake zuciya cike da jimami.

MOMY BOS. 😠

Baki d'auke da sallama rukee ta shiga cikin babban falon part d'in momy. Rukee tana shiga ta zauna kusa da momy sanan tace kai momy ke dai kinfi gane ki ta zaman kad'ai ci, yanzu hirar da akeyi ranar jumma'a da mutan gudan nan ma bazaki jeba. Ta6e baki momy tai tare da cewa! Bazani ba, in badda qasqanci irin na dadyn ku yama rasa in da zai ringa tara mutan gidan nan suna hira sai a babban falon part d'in maryam, kenan ni sai dai na ringa kwasar qafa naje part d'in kishiya in saki baki ina hira da uwar miji da kishi sai kace mara aikin yi.

Ni ina waccan shashasha take, taje tai ta sakin jiki a cikin su sai sun mallake min ita kamar yadda suka mallake yayan ku abdul, yanzu yaran nan sai yayi wata bai sani a ido ba, duk wani mugun hali irin na maryam da 'yayan ta ya kwasa. A dai-dai lokacin ruma ta shigo baki d'auke da sallama fuska ba walwala da yake ta baro cikin 'yan uwan ta.

Tana shigowa ko sallama momy bata amsa mata ba tace ke kuma lafiya kika shigo kina wani had'e rai, ko wani abun suka yi miki ne nifa shi yasa wlh bana so ki ringa shiga cikin su. Turo baki ruma tai tare da cewa! Wlh momy na gaji da zama a part d'in nan yanzu mu da 'yan uwan mu ace sai sati-sati zaki ringa bari muna zuwa mu wajan su? .

Shegiyar 'yar kutmar uwa kema kikaje suka yi miki wani barbad'an kika taka ko kikaci shikenan sun rabani da ke kamar yadda suka raba ni da yayan ki abdul. Ya mutsa fuska ruma tai murya qasa-qasa tace kika dai raba kanki da shi wani ne yace ki tafi karatu ki barshi, ba dole ya saba a hanun wadda ya taso ba. Wlh kika sake min irin wanan magar sai na zubar miji da haqora shegiya doluwa mai mugun hali.

Dama naga alama wlh baki kwaso halina ba rukee ce kawai ta kwaso halina daga ke har yayan ki abdul duk asarar haiwuwa nai. Nan da nan ruma ta fara zubar da hawaye cikin kuka tace wai kina uwar mu ki ringa cewa kinyi asarar haihuwar mu, haba ba dole ma ya abdul ya fi san ammi akan ki ba, ita ammi haka kikaga tana yiwa 'ya 'yan ta, yanzu yaushe raban mu da yaya mashkhur da zahra, sun dawo gidan ma baza ki bari mu gana da su ba.

Nan da nan momy ta ware hanun ta da ta dunqule da niyar mikewa ta kaiwa ruma duka amma tinda taji an ambaci zahra da mashkhur sun dawo sai mamaki ya kamata. Cikin mamaki tace ke bana son wasa da gaske mashkhur da shegiyar 'yar nan sun dawo gidan nan. Cikin kuka ruma ta gyad'a kai alamun eh, momy mayar da kallanta tai wajan rukee da take kusa da ita a zaune.

Ciki mamaki tace rukee wai da gaske yayanku ya dawo, gyad'a kai rukee tai alamun ee. Amma ke 'yar bura'uba ce, shine tinda kika shigo baki gayamin ba. Wlh momy nayi niyar gaya miki kece kika balbale mu da masifa muna shigowa da niyar na gaya miki na shigo, wai kamar ma naji hajiya kaka tana cewa ciki ne da zahra, kuma nasan da gaske take tinda naga ammi tana murmushi kamar ma dai tasan da maganar.

A zabure momy ta miqe cikin tashin hankali tace ciki?. Cikin mamaki rukee tace ee mana momy naga kinta da hankalin ke ai abun farin ciki ne. Ai momy ko takan rukee bata biba ta d'aukar wayar ta da take gefen kujera ta fara draining number saratu.

A cikin zuciyar momy tana mamakin duk uban asirin da tai wa mashkhur na mallaka har ya shigo gidan nan bai fara zuwa wajan ta ba ya wuce wajan uwar sa lallai da babba matasa ALLAH yasa ma asirin shaye-shayan bai karye ba,. Saratu tana d'agawa momy ta fara tafiya tana cewa! Hello saratu wata sabuwa wai mashkhur ne da wanan shigiyar yarinyar yau a garin nan.

Daga haka su ruma basu sake jin komai ba saka makwan momy ta haye sama bene. Share hawaye ruma tai ta rafka uban tagumi sabida ita har ga ALLAH bataso taji momy suna waya da saratun nan tasan saratu shawarar banza take bawa momy. Rukee miqewa tai ta dawo kusa da ruma ta zauna kusa da ita sanan tace ruma wlh sai yanzu na gane abinda kika gayamin kwata-kwata momy bata da imani bmuyi sa'ar uba.

Cikin mamaki ruma ta d'ago tare da cewa! Ke rukee nasan halinki ki iri-iri wlh yanzu ina sakin baki nayi munafurcin momy sai kije ki gaya mata waye bai san halinki na munafurci ba a gidan nan. Da sauri rukee ta girgiza kai tare da cewa! Wlh ruma bada niyar munafurci nai miki maganar nan ba, sai yanzu nasan momy bata kyautawa kullum acikin zagin ammi da 'yayan ta da hjy kaka take, kuma gashi mu ba haka ammi take mana ba tana son mu.

Hmmm ke dai bari rukee na dad'e da sanin mahaifiyar mu bata da imani, kuma gashi bani da wanda zan gayawa muyi kuka tare, kullum ke bayan ta kike bi bakya ganin laifin ta gaba d'aya. Wlh ruma da bayan momy nake bi amma tinda naga yaya mashkhur da zahra sun dawo lafiyar su qalau sunyi kyau abin su, suka bani sha'awa, kuma dai kinsa malamun mu yace wlh macuci baya gaba sai dai yayi ba, kullum baya yake.

To kinga da zahra macuciyace kamar yadda momy take fad'a ai baza tai kyau haka ba kullum ammi da 'yayan ta gaba suke yi, ke dan ma ranar nan baki ga saurayin ilham da yazo gidan nan ba har sakin baki nai ina kallan sa kyakyawa da shi, ga mutunci kai har mota ne da shi duk inda ake neman namiji kyakyawa mai aji saurayin ilham ya kai.

Wlh ruma yadda kika san namijin novels haka yake back beauty ne, hand some guy ne. Gyad'a kai ruma tai tare da cewa! Kinga ni koh, ilham d'in ma ta bani labarin yadda yake son ta kamar rai, dan bakwa wani shire ne da ita kema da ta baki labari. Hmm wh kuwa ruma yanzu na dawo daga rakiyar momy na bi ALLAH da manza sa yanzu yadda ta rabani da zahra har kunyar ta nake ji.

Hmmm dama abinda nake nuna miki kenan rukee, ni na tsani wanan qanwar momy aunty saratu wlh itama tana zugata. Dan liqe-liqe rukee ta farayi sanan ta raqe murya tare da cewa! Ke ranar nan da muka je gida aunty saratu lokacin da muka barki a gidan su momy waja umma inaji tana cewa! Wai zasuje wajan boka, yayi musu asiri amma dai basuje dani ba.

D'an furgita ruma tai sanan tace boka kuma rukee? Hmmm ke dai bari kawai ruma ai ni na dad'e da sanin momy tana zuwa wajan boka kinga muna shiri da ita tana gaya min wasu abubuwan watarana. Jinjina kai ruma tai tare da cewa kai gaskiya bamuyi dacan uwa ba. Wlh kuwa ni yanzu na koma ga ALLAH anjima ki rakani na roqi yafiyar zahar, murmushi ruma tai cikin jin dad'i tace tom ALLAH ya kaimu taso muje muyi sallah.

6angaran momy tana hawa sama ta shige d'aki sanan ta fara gayawa saratu mai yake faruwa, ke saratu wai mashkhur da shigiyar yarinyar nan ne suka dawo, kuma duk mallakar da nai wa mashkhur bai zo waje na ba wajan uwar sa ya fara zuwa harma yanzu da nake miki magana bai zo ba,. Ke bama shine abun tashin hankalin ba, abin tashin hankalin shine! Wai shigiyar yarinyar nan ciki ne da ita inagama fa yanzu ya fara son ta.

Daga d'ayan 6angaran saratu cewa tai haba yaya halima mai ne na d'aga hankalinki kuma?, ai abinda ya kamata shi zamuyi. Saratu mai zamuyi kuwa!?, kai yaya Halima abinda muka saba mana, kawai muje wajan boka ya dasa musu tsanar junan su, shi kuma mashkhur d'in ma mu haukata shi yabi duniya kowa ya wuta.

Wata dariya momy tai tare da cewa! Yauwa 'yar gari kin kawo shawara mai kyau zan lala6a dadyn su, ya barni nazo sai muje wajan boka amma yanzu dai bari naje na ganewa idanuwa na, gaskiyar lamarin, daga haka momy da saratu sukayi sallama. Suna gama sallama momy ta fuce daga d'akin, bayan ta sauka daga kan benan ta fucewa tai daga part d'in ta gaba d'aya ta kama hanyar part d'in ammi..............

Bayan su ammi sun idar da sallah zama sukai suka cigaba da hira. Suna ciki hira zahar ta kalli ilham tare da cewa! Kai ilham wai har yanzu abinci nawa bai dawu bane? Gaskiya kin cika nauyin hannu. Harara ilham ta d'an watasa mata tare da cewa ke bansa rashin mutunci tai maka miki nai fa, amma zakice na cika nauyin hannu?.

Kafin zahra tai magana hajiya kaka tace ke ilham ban san rashin kunya, ai yanzu zahra gaba take da ke tinda yayan ki take aure. Zahra kuwa murmushi tai tare da yiwa ilham gwalo, turo baki ilham tai tare da cewa! Kai hajiya kaka sai kuma kibi bayan ta,, aaa nabi bayan gaskiya dai. Kallan ammi ilham tai tare da cewa! Ammi kina ji koh sun had'e min kai.

Murmushi ammi tai tare da cewa! Hajiya ai in zahra da ilham ne ba'a shiga fad'an su zakiji kunya ALLAH nima da na gwada banji dad'i ba. Hajiya kaka cewa tai ee kwara da kika tunatar da ni nima kar su bani kunya, ni dai ba ruwana na fita. Murmushi zahra tai tare da cewa to ilham taso mu bawa hajiya kaka kunya, bari na raka ki, sai mu duba abincin tare.

Ilham gwalo tai wa hajiya kaka tare da cewa! Yauwa zahra ta ai gwara mu bawa hajiya kaka kunya nan gaba ta qara shiga tsakanin mu. Murmushi hajiya kaka tai tare da cewa ai muna nan taki zata had'a ki da gyatumar ki zaki zo nai man sulhu. Daga haka zahra da ilham suka haye sama domin duba abincin nasu.

Hajiya kaka kallan ammi tai tare da cewa! Hmmmm ilham da zahra kenan nasan nan gaba ba qaramin zumunci zasuyi ba tun suna yara suke son junan su. Murmushi ammi tai tare da cewa! Ai kuwa hajiya nifa tun ina addu'a ALLAH ya bayyana iyayan zahra harma na dai na sabida nasan baza'a ta6a ganin su ALLAH yayi mune iyayan ta kawai dai maman ta haifo mana ita tai.

Jinjina kai hajiya kaka tai tare d cewa hmm ke dai bari maryam ai zahra 'yar baiwa ce tinda har ALLAH ya nuna mana girman ta tabbas nasan tana tattare da baiwar a tarw da ita kuma ALLAH ne ya kareta da qudurar sa. Murmushi ammi tai tare da cewa! Kai ALLAH mun gode ma da ka bamu zahra a matsayin 'ya kuma kaaa take son mu a matsayan iyayan ta.

Zahra da ilham basu wani dad'e a sama ba suka dawo hanun zahra riqe da plate ta shaqo shi da shinkafa da wake. Tana qarasowa ta zauna a kusa da hajiya kaka, ita kuma ilham ta zauna a gefan zahra. Ammi kinga abinci da zahra ta zubo fah wai zata iya cinyewa ita ka d'ai. Cikin mamaki ammi tace zahra ina zaki kai abincin nan.

A dai-dai lokacin momy ta shigo d'akin amma batai sallama ba shi yasa ba wanda ya lura da shigowar ta. Hajiya kaka kuma cewa tai kee maryam dan ALLAH ku rabu da yarinyar nan haka? Karfa ki manta yanzu ba ita kad'ai bace ita da abinda yake cikin ta zasuci, mai sunana maza kici ki haifowa surukata jika qatoto.

Zahra tana qoqarin magana sukaji muryar momy tana cewa! Jika kuma hajiya ko dai ciki ne da ita. Gaba d'aya sai da su ammi suka d'an tsorata saka makwan ganin momy zundum a gaban su. Cikin sanyayiyar murya zahra tace momy ina wuni, yamutsa fuska momy tai tare da cewa! Lafiya qalau ta fad'a da kayar kamar wanda akayiwa dole.

Hajiya kaka kuma cewa tai wai ke halima mai yake damun kine zaki shigowa mutane ba sallama har yanzu bazaki hankali ba mutum ya girma bai san ya girma ba?. Ya mutsa fuska momy tai sanan tace aa naji kuna zanca wai yarinyar nan tana da ciki ne shi yasa nake so na tabbatar da gaskiyar lamarin. To munafuka bazaki tantance gaskiyar lamarin ba, kuma tubarakallah mashkhur ALLAH.

Haba hajiya sai kace wata mayya kike cemin tubarakallah mashkhur ALLAH ai ba cinye mata d'an zanyi ba. Tsaki hajiya kaka taja tare da cewa! Ke dai ganinki ba alkhairi bane dallah fuce ki bani waje mara kunya kawai, wadda ko uwar mijinta bata d'agawa qafa ina uwar mijinki bakya ganin mutunci na. Momy kuwa ya mutsa fuska tai tare da cewa! ALLAH ya wuce zuciyar uwar mijina daga haka ta kama hanya tai fucewar ta.

Hajiya kaka kuwa cewa! Tai kai wanna mata bata da kirki daba dan ba kyau saki ba da kuma darajar abdul da tini na sa abubukar ya saki 'yar nan walahi, kawai dai dan bakyau saki ne da kuma darajar yaran da suke tsakanin su da tini nasa an saki matar nan. Ammi cewa tai kai hajiya ban sanki da fad'a ba dan ALLAH kiyi haquri haka, ke da kike bani haquri kullum kuma ke kike fad'a yau.

Zahra kuwa shiru tai tana mamaki lokacin guda yadda aka laqaba mata ciki, ita da har yanzu ma bata gama sanin wane d'a namiji ba' aruyuwar ta. Daga haka dai zahra ta sunkuyar da kai ta fara cin abincin ta. Ita zahra ba komai ne yasa ta ciko plate ba face, ta dad'e bata had'u da shinkafa da wake ba tana sha'awar cin ne sosai..................


Nima naga bana sauri in nai single page, shi yasa nai double page, dan wlh na qagu na gama littafin nan. 😰😩
Da page 100 zanyi ma sai naga yayi kad'an bazai isa na isar muku da saqon da littafin ya qunsa ba.

Shin momy za taje wajan boka ko kuwa?.........

Kuna ganin mashkhur da zahra zasu cigaba da zama a matsayin miji da mata ko kuwa?....

Kuna tianin abdul zai auri zahra ko kuwa........

Ku biyo ni a dan jin amso shin tambayr ku...........

Masu zagin abdul akan yayi hugging d'in zahra na gaya mai, yayi murmushi sanan yace yana godiya. 😂


ADALILINTA 💜❤💜
AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 97*

Daga haka dai zahra ta sunkuyar da kai ta fara cin abincin ta. Ita zahra ba komai ne yasa ta ciko plate ba face, ta dad'e bata had'u da shinkafa da wake ba tana sha'awar cin ne sosai..................

To yaufa zahra da mutan gidan wuni sukai suna hira, abin gwanin ban sha'awa. Abdul kuwa sabida tsabar qauna ko kwakwaran motsi, baya bari zahra tai duk abinda ta 'yan qura zata d'auko shi yake d'auko mata. 6angaran mashkhur kuwa yana can yana ta sharar baccin sa hankali kwance. Ana kiran sallah magriba maza gidan suka miqe domin tafi massalaci.

Itama hjy kaka miqewa tai ta wuce part d'in ta, ammi ma tashi tai ta wuce bedroom d'in ta. Zahra kuwa miqewa tai tare da cewa! Ilham tazo mu wuce bedroom d'in mu muma, wlh nayi missing d'in d'akin nan. Dariya ilham tai tare da cewa! Ai kuwa bedroom d'in mu ya canza miki kama kika shigama bazaki gane ba.

Murmushi itama zahra tai tare da cewa! Haba dai taya zan kasa ganewa taso dai muje, daga haka ilham da zahra suka ranka zuwa l bedroom d'in su. A hankula zahra ta murd'a handle d'in qofar ta shige, tana shiga ilham ta biyo bayan ta. Zahra tana shiga ta saki baki tare da cewa! Ilham haka aka canza mana jeran bedroom, kai gaskiya banji dad'i ba.

Yanzu mene bai miki ba a ciki? Furniture's d'in da aka canza ne bai mika ba ko kuwa. Girgiza kai zahra tai tare da cewa! Furnitures sunyi kyau sosai wlh, jeran ne bai min ba kwata-kwata yanzu nan wajan sip d'in namu aka mayar mana da bed d'in kai gaskiya wanan lamarin bai yi dad'i ba. Murmushi ilham tai tare da cewa! Nice nan na canza in gaya miki.

Kai gaskiya ilham baki kyauta ba, ba wani rashin kyautawa 'yar nan da ba an miki jeran yadda kike so ba wai ke 'yar lele ko, yanzu kuma gashi nayi yadda nake so, ai yanzu ki da d'akin nan sai kallo, karma ki sake ki canza fasali wanan d'akin ya zama nawa ke da yaya mashkhur zai gina miki gida mai kyau, kinga sai ai miki jeran son ran ki acan ba dai nan ba,.

Wani sirrin tsaki zahra taja tare da cewa! Ai kuwa sai dai ki tafi ki bar min d'akin nan kina ji kina gani, ke da za'a d'aura miki aure da yaya ahmad very soon. Murmushi ilham tai tare da cewa! Ai kuwa dai fad'i kanki tsaya very soon zan zama amaryar sa, zan tashi daga ilham na koma Mrs ahmad, kamar yadda kema kika tashi daga zahra kika koma mrs Muhammad mashkhur.

Tsaki zahra taja a karo na biyu tare da cewa! Ba wanan zancan wlh, nima very soon zan koma mrs ABDUL MAJEED in sha ALLAH. Cikin mamaki ilham tace zahra anya ki san mai kike fad'i kuwa? Hanyar toilet zahra ta wuce tana cewa! Kwarai kuwa bari naje nai sallah, karki jani da surutu kuma ke ba sallah zaki ba.

Ilham kuwa jinjina kai a zuciya ta tace kai nifa abin nan ya fara d'aure min kai, girgiza kai ilham tai tare da d'an d'aga murya tana cewa! Gaskiya zahra kina barin kai na a cikin duwu amma in kin gama sallah zamuyi zama na musamman, daga haka ilham ta wuce wajan soket ta cire wayar ta daga caji sanan ta hau online,.

Zahra kuwa tana futowa ta zura hijab ta shimfid'a dadduma ta fara gabatar da sallah bayan ta idar ta gama lazimin, miqewa tai ta qarasa bakin qofar ta mird'awa qofar key sanan ta wuce bakin wardrobe. Ke mene kuma na rufo qofar tun kafin dare yayi, ke da kike baquwa a gidan nan yau, ai mutanan gidan nan basu gama zuwa wajanki hirar yaushe gamo ba.
Kaya zan cireni ina so nai wanka na gaji sosai wlh.

Ilham kuwa ajiye wayar tai a gefe tare da cewa ke dawo nan ki zauna inada maganar da zamuyi da ke, in mun gama sai ki wanka. Sannu nace sannu ammi b nazo, zahra ta qarasa maganar tana watsawa ilham kallon up and dwon, ke zahra ni mu kawar da zancan fad'a a gefe wlh da gaske nake inaso dai nasan wani abu mai mahimmanci ne zo muyi magana, wlh ina da tambayoyin da zan miki karsu kashe ni.

Wata siririyar dariya zahra tai tare da cewa! Ke ilham wlh duk da ban sani ba tsaigumi zakiyi, amma tsaigumin bazai kashe ki ba bani 15 minutes zan gama na fito muyu magana. Ilham ta qoqarin magana message ya shigo da saui ta d'auki wayar tare a duba. Wani qasaitaccan murmushi ta sauke tare da cewa! Jeki-jeki inma 30 minutes zakiyi kiyi, yaya ahmad ya hau online hirama zamuyi.

Murmushi zahra tai tana cire rigar ta tare da cewa, kai yaya ahmad wai mai yake miki hakane, anya ba sallah dare yake miki ba. Da sauri ilham ta d'ago ta kalli zahra da niyar zata bata amsa sai ta canza maganar da cewa kut, cikin mamaki zahra ta kalle ta tare da cewa, lpy harda zagi. Jinjina kai ilham tai tare da cewa! Ai ni banma gama ganin qibar da aka cewa! Kinyi ba sai yanzu zahra wanan ma ai kin kamoni a girma.

Murmushi zahra tai tare da cewa! To da haka kike so nai ta zama bana gaba da baya ko, na bari kita fina girma. Murmushi ilham tai tare da cewa! Hmm gaskiya zahra aure ya kar6e ki jifa yadda kika ciga kota ina sama da qasa, towel zahra ta d'auka tare da cewa! Ke ilham wanan kallo kuma ya wuce na muslinci na iskanci ne zahra ta qarasa maganar tana dariya.

Girgiza kai ilham tai tare da cewa! Hmm zahra yanzu nagafa kinyi baki ko yaya mashkhur ne ya koya miki magana ne?. Ta6e baki zahra tai tare da cewa! Lallai wanan dama har wata magana yake ina ma laifi kice mugunta sai nafi yadda da ganewa. Kai wlh kuwa kamar yaji yaya mashkhur d'in ne mugu koh?.

Tsaf ma kuwa maza kice ki fad'a sai kin dawo, daga haka zahra ta shige toilet. Murmushi ilham tai tare da cewa! Hmmm kun dai fi kusa tinda yanzu mijin ki ne, daga haka ta mai da ka ta cigaba da chat. Zahra batafi 15 minutes ta fito jiki d'aure da towel, tana ta fama da gashin kanta tana d'aurewa shi yana warewa.

Daga haka direct zahra ta wuce wardrobe ta bud'e ta fara bincikawa. Ilham ina kika kai min kaya na? Shiru ilham ba amsa, zahra Jiyowa tai tana kallan ikwan ALLAH bakin ilham sake tana kallom waya. hijab zahra ta jawo a kwaba ta cillawa Ilham, a birgice ilham ta d'ago tare da cewa! Kee lpy?. Harara zahra ta d'an watsa mata tare da cewa! Nace miki ina kika kai min kayana.

Ajiyar zuciya ilham ta sauke tare da cewa! Hmmm ke a tinanin ki zasu ta zamane, jifa yadda kika bindime taya zasu shige ki. Ban sani ba ina ruwan ki, ni dai ina kaya na? nasa na sawa an bayar dana bayarwa, amma dai ki du ba ciki duk wanda kikayi niyar sawa sai ki sa tinda naga yanzu

Please Login or Register in order to submit comment