Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan a mayar da ni. Da hajiya bata haqura ba amma daga qarshe da taga mutunci mahifiya sai ta haqura, sanan tai wa dadyn abdul dole ya mayar dani na dawo.

Lokacin da na dawo a shirya na dawo da wani saban magungunan asirin d'aukar fansa. Na yanke shawara zan d'au fansa akan d'an maryam wato mashkhur. Maganin mallaka na kar6o sabida na mallake mashkhur nima duk da kuwa har lokacin ko kallo na baya yi. A zo6o na had'a mai maganin na samu abdul a tsakar gida yana wasa na lalla6a shi nai mai dabara ya kai wa mashkhur.

To tun daga ranar mashkhur yake ganin mutunci na dan kullum sai yazo ya gai dani, wataran ma har kawowa yake na taya shi home wrok. Ana haka ana haka har ammi ta sake haifar faruq bayan shekara guda ta haifi haidar. Har lokacin ina baqin cikin hakan sosai sabida ni ta rabani da d'ana kuma gashi sai haihuwa take ni kuma ko oho har lokacin ALLAH bai sake banu wani cikin ba bare na haihu.

Gashj abdul tun a lokacin baya so ace nice maman ta in akace ni na haife shi ma kuka yake yafi so ace maryam ce maman sa. Bama iya lokacin ba har yanzu abdul baya so yaji ance ni na haife shi.

Haka na ringa jan hankali mashkhur, sabida iyayan sa suna hana shi kud'i ni kashe duk sabida karya lalace. Ni kuma dai na ringa bashi kud'i a 6oye duk abinda yake so nake mai duk sabida na sa ya ringa sona fiye da mahaifiyar shi kuma na lalata mai tarbiya. Dan lokacin ba dama ayi mai fad'a sai na nuna banji dad'i ba nai ta shige mai sam bana nuna mai yayi laifi. Ana cikin haka nima ALLAH ya azurtani da ciki, rukee.

Nayi farin ciki sosai da sosai har ALLAH ya sauke ni lafiya. Amma sam ita rukayya bana bari ko d'aukar ta ayi bare ma a kai ta wajan ammi duk sabida kar a rabani da ita. Bayan shekara d'aya da watanni dan har na yaye rukee Ina da qaramin ciki ita kuma kishiya ta marya tana da tsowan ciki haihuwa ko yau ko gobe. A lokacin Akayiwa hajiya mutuwa shine abdul yasa kuka akan sai an tafi da shi.

Haka dadyn abdul ya kai su gidan mutuwa shida hajiya sanan yayi da su bayan kwana biyu zai zo ya d'auke su bayan ya kai su gaisuwa ya dawo. To washe gari maryam ta fara naquda da yamma aka kai ta asibiti sanan da daddare aka sallamo ta muka dawo gida. Bayan mun dawo gida tin daga waje mukaga su hajiya sun dawo.

Muna shigowa cikin gidan muka gan ta da jaririya a hannu. Bayan mun zauna tai mana bayani wai mahaifiyar 'yar ce ta bata amanar ta. Lokacin guda na nuna bana qaunar zahra kuma sai ta bar gidan. Bayan su dadyn da hajiya sun shawar ta da har zasu mayar da ita shine maryam tace a barta ba'a san dalilin da yasa maman ta bayar da ita amana da tsowan daran ba.

Kawai abar ko shekara d'aya tayi wayo duk da kuwa mamanta a pepar cewa tai zuwa shekara uku ko had'u a dawo da ita da yake ta rubuta address. Lokacin banji dad'i ba sosai da sosai ji nai kamar na kashe yarinyar amma ba yadda na iya haka na haqura. Amma tin daga lokacin na fara zuga mashkhur akan ya dena kula zahra nace ko kallanta ya dena yi, ban wani sha wahala ba mashkhur ya dena d'aukar zahra sabida shi dama can bamai son mutane bane.

Lokacin na fara tinanin na kashe kishiya ta na huta sabida naga yadda dadyn abdul yake son ta fiye dani, kuma gashi tana ta riqe zahra wandda na tsana tana kula da itama kamar dai ita ta haife ta duk da alokacin bata shayar da su sabida ruwan ta nono bai zo ba tinda ta haihu. Banyi qasa a guiwa ba na wuce kaduna da tsowan cikin ruma, mukaje wajan boka nida saratu domin ya kashe min maryam.

Boka cewa yayi lokacin maryam tana sallah, bazai iya kashe ta ba amma zai bani wani magani na zuba mata a wani abu taci, domin ta mutu. Ni kuma sai nace ya bani maganin da zai sa maryam tai doguwar cuta ta rame ta dena tashi komai a kwance zata ringa yi, sabida mijin mu ya tsane ta daga qarshe dai tai mutuwa wulaqan ci. Nan da nan waje ya karad'e da salati.

Momy kuwa cigaba da magana tai da cewa, ina dawowa a ranar na haifi ruma bayan mun dawo daga asibiti maryam ta tafi part d'in ta domin dafamin farfeso kafin tazo na samu zuma na barbad'a maganin a cikin zumar sanan na had'a da alkaki. Lokacin dana hango ammi ta tawo da ita da dadyn abdul suna hira domin kawo min farfesu, na sake jin ba dad'i kuma hakan ne ya sake tunzurani akan na bata alkakin nan mai sanye da maganin boka.

Tana kafin ta shigo na d'auko mata alkaki tana zuwa nace daga kaduna nazo da shi taci. Da taqi ci sai na nuna mata banji dad'i ba, sai ta d'auka da niyar in ta koma part d'in ta zata ci. Nan ma na takura mata har sai da taci kuma a lokacin ta manta batayi bismillah ba. To tun daga ranar da maryam taci alkakin tana kwanciya bata sake moruwa ba in aka kai ta asibiti ba ba'a ganin komai haka ta kwanta ta ringa ciwo komai a kwance take.

Ni kuma a lokacin na sake samun dama jan mashkhur a jiki na sake zuga shi sosai akan ko kallan zahra kar ya sake yi. Tun daga lokacin na sawa mashkhur tsanan zahra sosai da sosai in banda dukan ta ba abinda yake kuma na sake mallake shi duk abinda na ce mai shi zai yi. To bayan maryam tasha cuta sosai da sosai tana gab da mutuwa naga ta tashi amma bansan ya akai asirin ya karye ba. Cikin mamaki dady yace wai halima kina nufin wanan cutar da maryam tai ke kika yi mata asiri?.

Cikin muryar kuka momy tace kwari dan ALLAH maryam ki gafarce ni nai miki asiri. Bayan kuma na koma wajan boka ya cemin hajiya ce ta karya mata asirin kuma tai mata dafa'i dan haka bazan iya qara cutar da ita ba. Daga nan na sake tsanar hajiya itama nayi-nayi na kashe ta amma na kasa haka dai na haqura. Nan ma waje sake karad'ewa yayi da salati,. Saratu kuwa sai zaro ido take kamar qasa ta tsake ta shige sabida kunya.

Haka dai aka cigaba da rayuwa ina ta mugunta ta iri-iri har mashkhur ya girma ya gama makaranyar secondary ya shiga jami'a. Mashkhur yana gab da gama jami'a zahra ta fasa mai laptop yayi mata mugun duka, naji dad'i hakan sosai lokacin kamar na zuba ruwa a qasa nasha sabida na tsani zahra. Lokacin da dady ya yankewa mashkhur hukuncin farin gidan ya tafiya qasar waje sabida ya daki zahra hankalina ya tashi sodai da sosai.

Duk da nasan ba sabida so aka kai shi ba sabida ai mai hukunci aka kai shi da yake mashkhur sam baya son fita qasar waje karatu. Abinda yasa hankalina ya tashi sam bana son mashkhur yaci gaba a rayuwar shi, kai bama iya shi kad'ai ba duk 'yayan maryam ma, kuma naga mashkhur yana da qoqari sosai in yaje can zai yi karatu shine na bugawa saratu na sanar da ita. Saratu kuwa cemin tai kawai na rabu da shi ai yaci baya ba gamawa yayi ba ko yaje can wahala zai sha bazai iya karatun ba.

Hakan ne yasa naji dad'i hakan banyi wani yunquri anashi tafiyar ba. Sanan lokacin da mashkhur ya gawa zahra cewa ita ba 'yar gidan nan bace naji dad'i sosai ranar rai na fass na kwanta sabida na dad'e ina zuga shi akan ya gaya mata amma bai ba sai daran da zai tafi russian.
Mashkhur bayan yayi shekara d'aya da wattani yana dawowa hankalina ya tashi sosai sabida ganin yadda ya sake zama nitsatse, sanan ya futo da ruselt mai kyau.

Hankalina ya tashi sosai ganun ruselt d'in mashkhur ina mamaki yanda aka ya futo da ruselt mai kyau kuma wai a qasar waje ya d'auki first class. Daga haka na bugawa saratu na gaya mata. Shine saratu tace nazo muje wajan boka kafin mashkhur ya gama wutun sa ya koma. Haka kuwa na kwashi qafa muka tafi wajan boka.

Boka da ta tambaye mu mai muke so ayiwa mashkhur shine mukacewa boka nida saratu kawai yayi mai asirin shaye-shye da bin mata yadda ko yaje russian ba abinda zai yi sai shaye-shaye. Nan da nan waje ya sake rikid'ewa da salati kowa ya girgiza da jin abinda momy take fad'a. Ammi cikin rud'ani tace yanzu halima ke kika yiwa mashkhur asirin shaye-shye dama?.

Momy share majina tai da bakin zani tace kwarai nice nai mai maryam. Sabida a lokacin ina baqin cikin mashkhur ya tafi waje yayi karatu ni kuma d'ana abdul ya zauna a nan, sam bana so ke da 'yayan ki kiyi gaba. Bayan mashkhur ya tafi russian ya dawo wutu na biyu burina ya cika da muka samu labarin baya karatu Shaye-shaye yake ko ruselt mai kyau bai samu ba.

Lokacin farin ciki kamar ya kashe ni, amma da na samu labarin za'a aura mai zahra su tafi russian tare ko ya gyara halinsa nayi baqin ciki sosai da sosai sabida natsani zahra burina ta auri miji wulaqantacce talaka, bana so ta samu rayuwa mai kuma kuma ni wlh ba abinda zahra tai min haka nan na tsane ta sabida bana so ta ra6i gidan nan,.

Dadyn abdul yana son zahra fiye da yaran gidan nan shi yasa na tsane ta sanan na nunawa mashkhur dadyn su ma yafi santa akan su shiya mashkhur ya sake tsanar ta, nima na rabata da 'yaya na amma nayi-nayi na rabasu da abdul na kasa sabida suna son junan su. Daga haka na bugawa sartu na gaya mata cewa za'a aurawa mashkhur zahra kuma ni bana so zahra ta auri mai gata na fiso ta auri wulaqantacce.

Saratu kuwa cemin tai na bari ya aure ta kawai sabida yanzu shima mashkhur d'an shaye-shaye ne, ai an cuce ta in aka had'a ta da shi, in ma an aura masa ita duka zataci ya kashe ta a banza tinda ba son ta yake ba. sanan kuma saratu tace in na bari haka aurawa mashkhur zahra shikenan, an rabata da abdul hankalin mu kwanta. dama lokacin naga abdul ya fara yiwa zahra son aure. Naji dad'i shawarar saratu sosai hakan ne yasa naje na ziga mashkhur nace mai tinda dadyn abdul yace dole sai an aura mai ita in ya aure ta suka tafi can rasha ya ringa gana mata azaba.

To bayan mashkhur da zahra sun dawo daga russian, naji baqin ciki sosai da mashkhur bai fara zuwa waje na ba yaje wajan mahaifiyar, kuma ni bai zo waje na ba har sai washe gari yazo waje na. Kuma sai naji qishi-qishin d'in wai zahra tana da ciki, hankalina ya tashi sosai da sosai. Bayan mashkhur yazo waje na sai naga kamar asirin da nai mai na shaye-shaye ya karye.

Kuma da na tambaye shi akan zahra tana da ciki yace min aa nayi tunain 6oyemin yake a lokacin ne na fara tunanin ko shima asirin mallakar da nai mai ya karye. Kuma naga ruselt d'in shi yayi kyau sosai wai har yazo ta biyu, kuwa harda offer samun aiki aka ya samu. Hankalina in yayi dubu ya tashi dan hakan banyi qasa a guiwa ba nai wa dadyn abdul qarya akan ya barni naje kaduna kawuna ya rasu, duk dai sabida naje wajan boka.................

Ina masu cewa yaushe zahra taza had'u da iyayan ta hmmm to yau dai ina yi muku congratulations anga iyayan zahra.

Kai gaskiya momy da saratu yau sunji kunya sosai.

Wayyo my abdul. 😪😫

Mu had'e a next page gobe.


AMNAH: ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing.............

*page 105*

Hankalina in yayi dubu ya tashi dan hakan banyi qasa a guiwa ba nai wa dadyn abdul qarya akan ya barni naje kaduna kawuna ya rasu, duk dai sabida naje wajan boka.................

Da kyar na samu dadyn abdul ya barni bayan na gama ci mai mutunci. Ina zuwa kaduna bayan na sauka gidan mu na huta na wuce gidan saratu. Ina zuwa gidan saratu ta bigawa boka waya ta sheda musa zamu zo, shine boka yace kar muzo mu bari zuwa gobe sai mu zo. Hakan ne yasa na kwana a gidan saratu washe gari da safe muka wuce wajan boka.

Muna zuwa wajan boka tun kafin na fara mai bayi ni yace yasan abinda yake tafe dani mai nake so ai min?. Ni kuma nace inaso a haukata min mashkhur yabi duniya, ita kuma zahra ina so a kashe min ita. Nan da nan waje ya sake kacamewa da salati, momy kuwa ci gaba da bayani tai da! Ita kuma ilham nace a rabata da mijin da zata aura yaji duk duniya ya tsane ta baya son ta, itama taji bata son shi.

Sanan kuma nace in an rabasu a mayar da auran kan 'ya ta ruma, sannan kuma a yiwa ilham asirin da zata qare rayuwar ta ba aure, ba wanda zai qara cewa yana son ta har abada. A lokacin saratu sai ta cemin kar nayiwa mashkhur haka ai hauka mai sauqi ne zai iya karyewa kawai shima na kashe shi na wuta kamar yadda zan kashe matar sa zahra.

Banyi wani dogwan tinani ba na amince da boka yaso ya turawa mashkhur asirin amma a lokacin sai akaci sa'a ya karanta azkhar, dan haka boka yace zai bani maganin na zuba mai a abu mai sanyi yasha. Ita kuma zahra nata asirin zai had'a mata da gyad'a sabida tana son gyad'a, ita kuma ilham da sillin gashin kanta za ayi mata nata asirin.

A lokacin sai nayiwa boka complain akan ni bansan yadda zan bawa zahra nata asirin ba sabida bama shiri da ita. Shine boka yace! Kawai na bawa 'yayana su kai mata taci, sai na ce mai ai yanzu 'ya'ya na duk basa bin bayana sam basajin magana ta ko na basu ba lallai ne su kai mata ba. Shine boka yace zai bani maganin mallaka na dafa musu a nama na basu su ci, in dai suka ci duk abinda nace suyi zasu ringa yi ko menene.

Hakan yayi mana dad'i sosai ni da saratu boka yace mu fara bashi kud'i zuwa gobe in mun dawo sai mu cika mai mu kar6i maganin kafin nan ya gama had'awa. Haka muka koma gidan saratu muka kwana washe gari, muka sake komawa wajan boka ya bamu magunguna yayi min baya ni yadda zanyi amfani da su yace min kuma bayan mutuwar zahra da kwana goma mashkhur zai bita. sanan muka bashi ragowar kud'in muka tafi.

Daga haka bayan mun koma da yamma na shirya sanan na tawo kano. Momy ta qarasa maganar tana zubar da hawaye baqin ciki, gaba d'aya wajan yayi stit kuwa sauraran momy yake wasu kuwa ko motsi sun kasa sabida abun ya girgiza su. A cikin wadda suka kasa motsi mutum hud'u ne zahra ilham mashkhur ahmad.

Momy bayan kukan nata ya tsagai ta cigaba da magana tai da cewa! Ina dawowa na wuce part d'ina bayan nayi wanka ko wutawa banyi ba na shige kicin domin dafa naman da zan zubawa su ruma maganin asiri. Bayan na gama dafa naman na fara qoqarin had'a zu6an da zan zubawa mashkhur maganin boka na bashi.

Bayan na gama had'a zu6o mai sanyi dama da maganin na dafa shi sai na wuce sama domin, ina zuwa na fito da gyad'ar sanan na sauka na d'auki zo6an na wuce part d'in mashkhur. Ina shiga part d'in na had'u da haidar shine nace yaje ya kiramin su ruma yace suzo na dawo. Daga haka na wuce bedroom d'in mashkhur na bawa shi zo6an sai ya shiga toilet da niya in ya futo zai sha daga haka ni kuma na fuce daga d'akin na kama hanyar part d'in na zuciya cike taf da farin ciki.

Ina komawa part d'in na har shiga kicin zan d'ora girki, kawai sai na futo na hau sama domin shiga bedroom d'ina na d'auko waya na kira su rukkayya ina zuwa na tarar rukkayya tana cin gyad'ar asirin da na ajiye domin bawa zahra. Momy ta qarasa maganar tana fashewa da kuka, nan da nan waje ya qara rud'ewa cikin tashin hankali ammi tace kina nufin gyad'ar ce ta kashe rukee ba maganin 6era ba.

Cikin kuka momy ta d'aga kai tare da cewa ee shine abinda yasa rukee ta mutu. Kafin rukee ta rasu tana kan gangara ni kuma ina kuka hankali na ya tashi sosai, kawai sai ga abdul ya shigo da cup d'in zo6an da na kaiwa mashkhur kuma bakin sa yayi ja alamun ya sha zu6an. Dana tambaye shi mai ya had'a shi da cup d'in zo6an da na kai wa mashkhur shine yace min shi ya sha ba mashkhur ba.

Momy ta qarasa maganar tana fashewa da kuka mai ba tausayi. nan da nan falo ya sake kacamewa da hayani ya musu salati nayi masu tsinewa momy nayi, zahra kuwa hankalin in yayi dubu ya tashi da taji momy tace abdul ne ya sha zu6an asirin mutuwa zahra tana so ta kwala iwu amma ta kasa dan ko kwakwaran motsi batayi sabida tashin hankali.

Yanzu kina nufin abdul zuwa gobe zai mutu tinda gobe kwanan sa 10 da shan zu6on asirin dady ya tambaya hankali tashe. Cikin kuka momy tace da hakan ta faru shine na bugawa boka akan ya karya min asiri, boka yace shi baya karya asiri amma sabida nice zai gayamin mai zanyi asirin ya karye. Ni zan karya da kai na da na tambaye shi mai zanyi shine yace min dole na samu iyayan mashkhur na gaya musu gaskiyar lamari.

Bama iya haka ba duk wani asirin, da nasan na ta6ayi a wajan sa sai na fad'a sanan asirin abdul ya karye in akaci sa'a ya tashi in kuma kwanan sa ya qare ya mutu, amma in dai nabi komai daki-daki zai tashi sai dai in kwanan sane ya qare. Sanan kuma yace dole sai anyi komai a gaban saratu kamar yadda akayi asirin a gaban ta. Da ban yadda da da hakan ba kawai nace sai dai abdul ya mutu.

Amma daga qarshe dana ga abdul yana jin jiki sosai kuma ina tausaya mai, shine naje na bawa dadyn abdul haquri akan ya yafewa saratu harya amince saratu zato gidan nan. Dama ban gayawa saratu gaskiyar zancan ba sabida nasan zataqi zuwa, haka dai nai wa saratu dabara har kuka zo gidan gaisuwa da dubiyar abdul. Momy ta qarasa maganar tana fashewa da kuka mai cin rai. 6angaran saratu kuwa gumi ko ta ina ke to mata yake har ya fara jiqa mata kaya.

Nan da nan falo ya kaceme da hayaniya kowa yana fad'ar albarkacin bakin sa. 6angaran ruma kuwa sai wani kuka take mai ban tausayi duk sai taji ta tsani momy da kan ta, sai taji ina ma itace ta mutu ta huta da rayuwar nan ba rukee ba, in ta tuna wai mahaifiyar ta ce ta aika ta hakan sai wani kuka ya mai qarfi ya kwace mata.

6angaran abdul kuwa duk abinda momy ta fad'a fass a kunan ta, ya bud'e ido sa biyu yana kallan kowa d'ai d'ai zuciyar shi cike da baqin ciki yana addu'a ALLAH ya d'auke mai rai ya huta da abin kunya da mahaifiyar sa ta aika ta. In ya tina momy ce ta hai fe shi sai yaji nunfashin sa har wani d'aukewa yake sabida baqin ciki.

Kowa ya kasa magana a falon, falon yayi stit sabida lamarin ya bawa kowa tsantsar mamaki kowa da abinda yake saqawa a ransa. Momy kuwa magana ta farayi da cewa dan ALLAH dan annabi ku yafe min nasan nayi kuskure tun a duniya ALLAH ya fara nunamin kuskure na, sabida gashi muguntar da nai wa mashkhur da zahra ta dawo kai na har na rasa 'ya ta rukkayya duk da shima abdul d'in bana sa rai da shi dan ALLAH ku yafe min.

Hajiya kaka rai a 6ace tace halima ai banyi mamaki wanan abu da kika aika ta ba sabida nasan baki da imani zaki iya aika ta abinda yafi wanan. Yanzun ma ai ba dan ALLAH kika fad'i gaskiya ba wata ladama da kikayi kawai sabida ki tsiratar da d'akin ki abdul daga mutuwa dah ba abinda zai sa ki fad'i gaskiya.

Cikin kuka momy tace dan ALLAH dan annabi ki yafe min hajiya wlh shirrin shed'an ne. Maman zahra cikin kuka tace gaskiya saratu ke da 'yar uwar ki sam baku da imani, a dalilin ki saratu naje na bada amanar 'ya ta kwanan ta d'aya a duniya, na bada amanar ta hanun wanda ban saniba duk sabida na tsera tar mata da rayuwa amma anan d'in ma baku kyale ta ba.

Nan da nan mamaki ya sake kama kowa na wajan, cikin mamaki hajiya kaka tace kai innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, ashe sune sanadin da suka sa kika bani zahra tun tana jariri kuma kika gudu. Cikin kuka maman zahra tace kwarai hajiya sune sanadi, na d'auki 'ya ta na baki a gefan jeji al halin a lokacin ita kad'ai na mallaka tai tsawan rai. Cikin mamaki hajiya kaka tace ahmad d'in fa?.

Nan da nan babar zahra ta fara kora jawabi kamar haka!. Ahmad d'ana ne amma sai dai bani na haife shi ba. Maman ahmad aminaya tace sosai tun muna yara da ita muke wasan qasa kuma dama maqotan mune. Lokacin da muka girma muka zama 'yan mata sai ALLAH ya had'a ta baban Ahmad. Duk da dai ba wata babba bace sosai a lokacin dan batafi shekar 13.

Hakan ne yasa ta rigani aure dan ita auran wuri akayi mata. Bayan tayi aure da shekara biyu, shine ta haifi ahmad. A wajan haihuwar shine ta rasu. Bayan ta rasu aka dawo da ahamd gidan su, to shine lokacin na cigaba da rainon ahmad ya dawo kamar dai ni na haife shi har yayi wayo. Lokacin ahmad yana shekara d'aya ni kuma akayi min aure.

Ahamd ya saba da ni sosai baya yarda da kowa shi yasa baban sa ya bar min shi muka tafi tare da shi kaduna da yake can aka kai ni. Sai da ahmad yayi wajan shekara biyar ko 6atan wata ban ta6a ba bare ma na samu ciki, dan lokacin ma ahmad yayi wayo sasai harya fara zuwa makaranta. Sabida bana haiwuwa hakan ne yasa mijina ya auro saratu sabida shi yana son 'yaya sosai.

Please Login or Register in order to submit comment