Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi wani laifin ne naga kuna bina da wani kallo wanda ni banma san fassarar shiba,  harara mashkhur ya watsa mai tare da kawar da kan shi gefe.  Murmushi dady yayi tare da cewa!  Hmm bari naje na kwanta nifa na gaji,  okay dady kafin ka futu zanma girki mai dad'i girkin da in kaci sai ka qi komawa Nigeria, zahra ta qarasa maganar tana sakin murmushi,  shima dady murmushi yayi tare da cewa tom shikenan mamana sai na futo,  dady yana yin gaba shima abdul yabi bayansa tare da cewa nima zani na kwanta na gaji.

Tom shikenan yaya abdul sai ka tashi cewar zahra,  mashkhur ne ya kalli ilham tare da cewa ilham ke bazaki ki kwanta ba?  Ya qarasa maganar yana shafa amir da yake kwance yana bacci a cinyar sa,  ehh yaya mashkhur ai ni banajin bacci,  gyad'a kai yayi tare da cewa ya ammi da hjy kaka da momy?  Gyara zama ilham tai tare da cewa!  Duk suna lpy,  sabida mai bakuzo dasu ruma ba?  Mashkhur ya jefawa ilham tambayar,  kwa6e baki ilham tai tare da cewa uwar suce ta hanasu zuwa,  wai bazasu zo wajan zahra ba.  Harara mashkhur ya watsawa ilham tare da cewa ok uwarsu ko? momy ce bazaki iya ce mata momy ba?.

Haba yaya mashkhur nifa  bada wata manufa na fad'i hakan ba,  kawai na fad'a ne,  okay ina magana kina magana dan baki da kunya ko?,  had'e rai ilham tai tare da cewa!  Ya haquri ,   Miqewa mashkhur yayi hannu riqe da amir ya wuce d'aki.  Yana tafi ilham ta kalli zahra tare da cewa!  Hmm kinji yaya mashkhur nifa wlh bansan sabida mai suke good time da momy ba,  kallifa dan nace mata uwar su yarda yabi ya wani had'e rai harda yimin fad'a gaskiya kam na yarda momy uwar d'akin yaya mashkhur ce,  zahra a zuciyar ta cewa tai lalai kukan dad'i kikeyi ai da nice da tina jikina ya fara gayamin,  amma a fili zahra cewa tai lalai ilham sai kace ba kisan tsakanin momy da yaya mashkhur?  Taso muje kicin ki rakani na d'ora abinci.

Ba musu ilham ta miqe suka shiga kicin, suna shiga suka fara shirin d'ora abinci,  ilham ce ta kalli zahra tare da cewa wai zahra ke kike dafa abinci da kan ki ko oder yaya mashkhur yake miki na dan na sanki da da lalaci ga ragwanta.  Harara zahra ta watsawa ilham tare da cewa ke ilham gaskiya bana san tsokana daga zuwa ko awa uku ba'a yi ba harkin fara nemana da rigima?.  Dariya ilham tai tare da cewa to ai gaskiya na fad'a,  nan da nan zahra ta had'e rai kamar zatai kuka,  oh sorry my lovely sister wasafa nake miki,  murmushi zahra ta saki tare da cewa kai ilham gaskiya nayi missing d'in ki wlh.

Ajiyar zuciya ilham ta sauke tare da cewa wlh baki kai ni missing d'in kiba, gwarama karmu fara musun nan kawai ki amsamin tambaya ta.  Murya a sanyaye zahra tace aa ni nake dafawa da kai na naci nifa inaga tinda nazo gidan nan yaya mashkhur bai ta6a yimin oder abin ciba,  yaya Ahmad ne kawai ya ta6a siyomin abinci waje lokacin ma bani da lpy ne shiyasa.  Cikin mamaki ilham tace kai to yaya mashkhur d'in shima baya oder ne,  gaba d'aya kike dafa muku?  No ilham shi yana oder nice kawai,  ke dai ki bari da akwai labari sai mun nutsu zan baki,  musamman ma wanda na gaya miki zan baki,  ranar da mukayi video call,  wlh har zuci-zuci nake mu had'u na sanar da ke.

Kai zahra da gaske tom shikenan ALLAH yasa naji alkhairi,  murmushi zahra tai tare da cewa!  Ameen.  Zahra tana rufe bakinta taji ana knocking d'in qofar part d'in,  a lokacin zahra Albassa take yankawa ita kuma ilham kayan miya take wankewa kuma ilham tafi kusa da qofar fita,  dan haka zahra cewa tai!  Ilham  jeki ki bud'e qofar nan inaga yaya abdul ne ko kuma yaya mashkhur ne yayi oder aka kawo   ba musu ilham ta fara wanke hanunta tare da cewa tom,  tana gama wanke hanun ta wuce hanyar qofar tare da fad'in i'm coming.  Ilham tana qarasawa ta bud'e qofar ai kuwa karaf ilham sukayi 4 eyes da Ahmad da yake tsaye a bakin qofar..............

JUMMA'A TUL KAREEM, ai wuto mako lpy. Sai mun had'u a next page.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

my number 09162226240

                      *page 67*
        
                             Typing..........

Ilham  jeki ki bud'e qofar nan inaga yaya abdul ne ko kuma yaya mashkhur ne yayi oder aka kawo   ba musu ilham ta fara wanke hanunta tare da cewa tom,  tana gama wanke hanun ta wuce hanyar qofar tare da fad'in i'm  coming.  Ilham tana qarasawa ta bud'e qofar ai kuwa karaf ilham  sukayi 4 eyes da Ahmad da yake tsaye a bakin qofar..............

Gaban Ahmad ne ya fad'i ras, saka makwan ganin abinda bai zata ba,  dan shi gani yake kamar ba ilham d'in bace gizo take mai da yake bai dad'e da gama tinanin taba,  Sosai Ahmad ya tsirawa ilham ido ba ko qiftawa.  Kawar da kai ilham tai tare da cewa!  Ina wani,  Ahmad kuwa bai masan abinda take cewa ba dan kwata-kwata ya tafi wata duniya  tinani duk a zatan  ilham Ahmad ya sane yayi mata haka,  dan haka ba shiri ta had'e rai sosai tare da d'an galla mai wata qaramar harara ta gefan ido sanan ta wuce ta farshi baki sake.

Fuska a had'e  ilham ta shiga kicin d'in,  d'a gowa zahra tai tare da cewa!  Ilham waye?,  fuska a d'aure ilham tace wlh wanan abokin yaya mashkhur d'in nan ne,  au kice yaya Ahmad ne kenan?,  zahra ta tanbayi ilham,  gyad'a kai ilham tai tare da cewa amma gaskiya mutumin nan bashi da kirki ina gai she shi  ko ya amsa,  yayamin shiru,  ilham ta qarasa zancan tana yamutsa fuska.  D'an zaro ido zahra tai tare da cewa!  Tabb lalai  ilham naga alama bakisan mai mutunci ba,  nifa badaban kar nai  qaryaba sai nace tinda nake had'uwa da mutane ban ta6a ganin mai mutuncin yaya Ahmad ba.

Ta6e baki ilham tai alamun bata gamsu da maganar zahra ba,  zahra kuwa harara ta d'an watsa mata tare da cewa!  Ke dai ilham ki rage wannan halin naki na saurin zuciya da fad'a,  zahra tana gama fad'in hakan bata jira amsar ilham ba ta fuce tare da cewa ina zuwa.  Zahra tana fita ta wuce wajan yaya Ahmad wanda yake tsaye a bakin qofar alamun har yanzu bai zauna ba,  da sauri zahra ta qarasa tare da cewa yaya Ahmad ka shigo mana ka tsaya a nan?.  Firgigit Ahmad ya dawo daga duniyar tinanin daya tafi,  kallan yayi zahra tare da cewa qanwata,  ilham na gani ko idona ne yake min gizau.

Wani siririn murmushi zahra ta saki tare da cewa!  Yaya Ahmad gizau kuma,  itace ka gani ba gizau ba,  d'an zaro ido Ahmad yayi tare da cewa!  Yau she sukazo ne?.  Ehh basu dad'e da sauka ba tare da dady suka zo harma da yaya abdul dan ko awa uku basuyi da sauka ba.  Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa!  Kice nazo a dai-dai,  kinga ai sai na gai da dady koh?,  jinjina kai zahra tai tare da cewa!  Hakane amma sai dai ka bari sai anjima sabida yanzu dady hutawa yake yana bedroom yana bacci.

Gyara tsayuwa  Ahmad yayi tare da cewa!  Gaskiya ne,  amma zahra da fatan baki manta da qudirina  akan ilham ba dai ko?  Gyad'a kai zahra tai alamun ehh tare da cewa ban mantaba,  amma yaya Ahmad ai waqa a bakin mai ita tafi dad'i,  kaga ai sai ma ka fad'a mata da bakin ka koh?.  Da sauri Ahmad ya girgiza kai tare da cewa kai qanwata rufamin asiri ai bazan iya ba,  sabida naga kamar bata da sauqin kai kamar ki,  harfa wata hararata naga tanayi.  Wata siririyar dariya zahra tai ta tare da cewa!  Haba yaya Ahmad yanzu tsoran ilham d'in kakeji,  qanwar kace fa.

Hakane zahra amma ni dai yadda ta tarbe ni naji tsoro inaga na gaya mata abinda yake zuciya ta,  no yaya Ahmad karka damu da hakan dama ita ilham haka take,  inaga baku fahimci junan ku ba,  ita tace min tagai da kai baka amsaba,  kai kuma kace ta harare ka.  Wani siririn murmushi Ahmad yayi tare da cewa! Ok shine abinda yasa take min kallan tara saura kwata,  wlh qanwata banji gaisuwar ba na tafi duniyar tinani ne,  amma ki bata haquri,  ai yaya Ahmad ko baka rantse ba na yarda sabida nasan bazaka ta6a hakan ba,  nima nayi tinanin bakaji bane shiyasa,   jiniina kai Ahmad yayi tare da cewa! Okay, zuwa anjima zan dawo mu gaisa da dady inya tashi, amma dan ALLAH ki sanar  da ilham saqona,  amma ki bari sai na zo gai da dady na fati,  zuwa dare sai ki gaya mata kafin nan na tafi.

Murmushi zahra tai tare da cewa! Tom shikenan yaya Ahmad in sha ALLAH,  gyad'a kai Ahmad yayi tare da cewa! To ALLAH yasa muji alkhairi,  ameen yaya Ahmad daga haka Ahmad bai sake cewa,  Komai ba ya fice daga gidan.  Yana fita zahra ta rufe qofar sanan ta koma kicin,  a lokacin ilham duk ta gama had'a komai na girkin,  kawai d'orawa ya rage,  kan table zahra ta wuce ta dakko tukunya ta kunna gass ta d'ora,  sanan ta d'an saci kallon ilham,  tare da cewa!  Ilham yace kiyi haquri wlh bai jiba,  yamutsa fuska ilham tai tare da cewa oaky shi kurma  ne kenan koh?  Ilham ta watsawa zahra tambayar.

Shiru zahra tai bata ce komai ba,  sabida tasan yanzu ta biyewa ilham wani fad'an zasu farayi.  ilham da zahra sun d'auki awa biyu suna girke-girken nan, prd rice suka dafa da kosilo sai chicken papper,  sanan suka soya dankalin turada,  suka had'a leman kwakwa da dabino.   Kai gida ya karad'e da qamshi ba wai,  abinci a ido ma ka gani sai yawunka ya stinke,  barema ka kai da ci.  Draining suka wuce suka jera abinci,  sanan suka wuce bedroom , wanka ilham ta shiga,  tana futowa itama zahra ta shiga,  bayan sun gama wanka suka shirya.

Ba 6ata lokaci ilham ta fara bud'ewa zahra a kwatinan tsarabar da sukazo mata da shi.  Kayane wajan kala ashirin,  d'inkake,  atanfa goma,  leshi biyar shadda biyar,  duk anyi musu d'inkin zamani,  sai kuma kayan bacci da su andawayas,  ga abaya da mayafai kala-kala,  kai kayan nan sun birge zahra sosai. Sanan harda wata takaddar da hajiya kaka tasa a qasan  akwati wai a kawowa zahra addu'o'i ne,  zahra tana bud'e takarda duk addu'o'i yawanci wanda zata ringa yiwa mashkhur ne,  tunma kafin zahra ta gama karantawa ta rufe,  a zuciyata tace ALLAH sarki hjy kaka baiwar Allah dan datasan,  har yanzu mashkhur bai rage halinsa na shaye-shaye ba da bamata wahalar da kanta ba,  kullum zahra addu'a take amma,  abu sai gaba yake qarawa.

Nikuwa AMINA BAYERO nace ai zahra addu'a bata fad'uwa qasa banza.  Zahra da ilham suna cikin mayar da kayan amir ya turo qofa yana shigowa ya fad'a jikin zahra tare da cewa auntyna wai inji dady kuzo muci abinci,  murmushi zahra tai tare da jan kumatun amir tana cewa!  To d'an gidan aunty tashi muje,  ba musu amir ya miqe,  suma su zahra da ilham miqewa sukayi,  suka nufi bakin qofa hannun zahra riqe dana amir.  Suna zuwa sukaga Ahmad a kusa da dady suna ta hira abinsu,  kamar wasu abokai shi kuwa mashkhur ya hard'e qafa d'aya akan d'aya yana danna wayar shi abansa.

Abdul kuwa ya tafi kan draining ya rafka uban tagumi kamar wani mai ciwan yunwa,  Ahmad kuwa yana ganin ilham nan da nan muryarsa ta fara sarqewa,  Dan harama ya fara canza hirar da sukeyi da dady.  Dady kuwa sam bai lura da abinda yasa Ahmad ya canza hirar ba,  cikin zaula dady yace!  Ahamd kaji qamshin girkin surukata,  ka d'imau ce koh?  Harka fara canza hira sai ma kaci tukunna,  dan ko qafar d'akinka bazaka gane ba,  kowa na wajan sai da ya dara ba wanda bai yi dariya ba in ka cire mashkhur da amir,  sai zahra wanda ta saki siririn murmushi.

Ahmad kuwa cewa yayi!  Allah ko dady ai na dad'e da sanin kayi dacan suruka mai iya girgi nima kusan kullum in ina gida sai ta cikamin hanci da qamshi girgiki,  ashe da raban yau zanci girkin nan Ahmad ya qarasa maganar yana satar kallon ilham.  Dariya dady yayi tare da cewa! Ai wanan girkin  ko da kud'in ka sai da rabanka,  ko da rabanka sai ALLAH ya tsaga,  gabad'aya wajan suka kwashe da dari ko shi mashkhur d'in ma sai da ya d'an murmusa,  sabida maganar  dady ta bashi ni shad'i.  Muryar abdul sukaji yana cewa!  Dady karfa kazo ka cika baki muci girkin surukar taka muji abin ba kanta ya qarasa maganar yana sakin qasai tacan murmushi da yake qara mai kyau da kwarji ni.

Miqewa dady yayi tare da cewa! Kaii abdul na rabaka,  da girkin surukata wlh,  kaga in kaci girkin nan tofa da kuka zata koma Nigeria,  sabida dadin girkin haka zakace sai ka cigaba da zama anan tana yima irinsa,  nanma dariya



Miqewa dady yayi tare da cewa! Kaii abdul na rabaka,  da girkin surukata wlh,  kaga in kaci girkin nan tofa da kuka zata koma Nigeria,  sabida dadin girkin haka zakace sai ka cigaba da zama anan tana yima irinsa,  nanma suka sake sakin wata dariyar  amma banda mashkhur da yayi lamo yana sauraran abinda suke cewa,  to ni dai baby abdul  zo ki zubamin abincin nan,  wlh yunwa nakeji,  kuma Allah yasa kin iya girkin,  dan duk abinda ka fiya cika baki baya lasting,  abdul ya qarasa maganar yana sakarwa zahra wani qasai tancan murmushi wanda azuciyarsa bana komai bane face na tsantasn so da qaunar zahra. 

Murya a shagwa6e zahra tace kai yaya abdul,  kai kuma da kake yabona yau kuma kake kusheni,  kashe mata ido d'aya  Abdul yayi tare da cewa! Ai gaskiya na fad'a tinda naga yaya mashkhur baya rawar jiki akan abincin nan nasan kawai kwa6a kike zuba mai,  haquri yake da girkin nan.

Murmushi dady yayi tare da cewa!  Mamana rabi da yayan nan naki,  dama borin kunya yakeyi,  sabida yasan ba zai iya auro min suruka irinki mai iya girki ba,  nan ma duka wajan suka qara saki dariya,  Ahmad dai kuwa sai fama satar kallon ilham yake.  Zahra kuwa gwalo ta sakarwa yaya abdul,  shima  kuma abdul d'aga mata gira yayi tare da sakar mata murmushi mai nuna tsantsar QAUNA da SO.  Duk abinda zahra da abdul sukai karaf akan idon mashkhur,  ya zubo musu manya idanuwan nan nasa kamar zai cinye su.  Zahra kuwa kamar ance ta juya sukayi 4 eyes da mashkhur,  wani mugun kallo tare da harara ya watsa mata,  wanda zahra bata ma san fassarar shi ba.

Da sauri zahra ta kawar da kanta daga kallon mashkhur d'in.  Ilham da zahra sauko da abinci sukayi daga kan draining,  da yake kujerun bazasu ishe suba,  ba 6ata lokaci kowa yazo ya zauna a qasa suka zagaye abinci  banda mashkhur wanda sam bama shi da niyar tashi.  Ba 6ata lokaci ilham ta fara saving d'in su,  ba wanda bata zubawa ba har Ahmad wanda takejin haushinsa sai da ta zuba masa ita kuma zahra ta zubawa kowa lemo a cup,  suna gama saving d'in kowa suma suka juya suka fara cin nasu abinci,  da yake ilham da zahra harma da amir a plate d'aya suka zuba.

Dady zai kai abincin bakinsa kenan ya hangi mashkhur akan kujera ya kwanta da kansa a gefan kujerar kamar wani saban maraya.  Muryar dady ce ta kara d'e wajan yan cewa!  Kai mai sunan baba bazaka zo kaci abincin ba?,  girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! I'm okay dady.  No muma ai duk nan yours  okay d'in ne amma muke ci koba haka ba dady ya watsa musu tambayar,  har Ahmad da abdul suna had'a baki wajan cewa!  Gaskiya ne dady,  abdul kuwa cigaba da cewa yayi kai zahra haka kika iya girki gaskiya raban danaci girki mai dad'i irin naki harna manta ya qarasa maganar yana kallon zahra, zahra kuwa murmushi tai tare da cewa! Kai yaya abdul ina ka baro girkin ammin.

Da sauri abdul yace au ai ni namanta ma da girkin ammi sabida dad'in girkin ki,  ya qarasa zancan cikin zaulaya,   jinjina kai ilham tai kafin ma tayi magana amir ya cafe zancan da cewa LA!! LA!!  LA!!  Sai na gayawa ammi,  duk wajan dariya sukayi sabida yarda amir ya fad'a yana girgiza kai,  yauwa amir ka fad'awa ammi kaji,  next time yaje cin abinta ta koro shi cewar zahra.  Gyad'a kai amir yayi alamun to,  dady kuwa cewa yayi mai sunan baba ka sauko kaci abicin nan,  ba musu mashkhur ya sauko ya zauna a kusa da Ahmad,  yana zuwa dady ya kalli zahra tare da cewa! Mama zo ki zuba mai,  ba musu zahra ta miqe taje ta fara saving d'in mashkhur.

Tana gamawa ta miqa mai,  mai makwan mashkhur ya kar6a harara ya watsa mata tare da kawar da kansa gefe ba wanda ya kula da hakan sai abdul da yake biya da zahra da idonsa shiyasa ma ya lura,  sunkuyar da kai zahra tai tare da ajiye mai plate d'in abinci sanan tabar wajan.  Tofah waje yayi stit bakajin komai sai qarar cokula da plate,  Ahmad kuwa sam ba abincin ne a gaban saba sai satar kallon ilham yake,  mashkhur kuwa har cikin zuciyar sa yake jin dad'in abinci,  bai ta6a tinin abinci zai yi dad'in hakan ba dan ji yake kamar ammi ce ta dafa,  dama can ya gaji da cin abinci Oder,  karaf idon mashkhur ya sauka akan Ahmad da yake ta kallon ilham.

Da mashkhur yayi tinanin zahra Ahmad yake kallo amma daga baya sai ya gane ilham yake kallo,  qafa mashkhur yasa ya d'an shiru Ahmad da sauri Ahmad ya dawo daga kallon ilham daya tafi,  harara mashkhur ya watsawa Ahmad a hankula yace kai lpy kake mata wanan kallo?,  yarda ba wanda zai ji  mashkhur yayi maganar daga shi sai Ahmad sukaji maganar.  Murmushi Ahmad yayi tare da mai da kansa cikin abinci ya cigaba da ci,  shima mashkhur d'in abincin sa ya cigaba da ci,  yanaci yana nazarin mai Ahmad yake nufi da hakan?.

Tubarakalla mashkhur ALLAH abinci zahra da ilham yayi dad'i sosai sabida duk cikinsu ba wanda yayi ragowa sai mashkhur ka d'ai shima yaso ya cinye abincin ma harda qari,  amma yana tsoran kar dady yayi mai dariya kuma bayaso ya yarfa kansa a wajan zahra shiyasa.  Kowa ya yabi abincin nan sosai banda mashkhur,  ilham kuwa uwar kishi kwa6e fuska tai tare da cewa!  Gaskiy dady na gaji da  wariyar launin fatar da kuke nunamin,  bafa zahra ce ita ka d'ai tai girkin nan ba harda ni,  hakan da tai ba qaramin burge Ahmad tai ba,  dady kuwa cewa yayi ke dai  ilham kin fiya kishi to da ke da zahra duk ba d'aya bane.

Da sauri abdul yace no dady ba d'aya bane ita ilham har wani girkin arziki ta iya ai da ita ka dai ce tayi girkin nan to da tini baku cinye ba kuna ci kuna kuka sabida tsabar rashin dad'in shi,  abdul ya qarasa maganar yana watsawa ilham harara tsokana,  sosai su dady suka kwashe da dariya harda mashkhur sai da yayi murmushi.  Kai yaya abdul hakama zakace kenan ko?  To ai dama kowa yasan zahra ta gidan kace shi yasa kake kusheni ita kuma kake yabanta,  yaya mashkhur kana jinsa koh?  Ilham ta qarasa magar tana kallon yaya mashkhur.

D'agowa mashkhur yayi tare da cewa! Rabu da shi ilham ai ni nasan sabida mai yace hakan!  Kinsan sabi da mai?  Mashkhur yayi tambayar yana kallon ilham d'in, da sauri ilham tace aa yaya mashkhur,   kawai fa sabida bakya mai girki yana ci ne,  shiyasa yake jin haushi amma ai ni nasan kin iya girki mai dad'i,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Hakane yaya mashkhur kamar ka sani  kullun fa  magiya  da  kuka  yake  wai sai na mai girkina mai dad'i yaci,  ni kuma sai naqi shine fa yake jin haushi na.   Kwarai ilham ai nasan wanan tin ina Nigeria nasan hakan mashkhur ya fad'a cikin tsokanar abdul.

Dariya abdul yayi tare da cewa! Ehh mana ai wanan kukan da kuga inayi ba na komai bane face na rashin jin dad'in girkinta,  ranar nan mafa data dafa min idomein  fa kamar tuwo haka indomein ta koma egge d'in ma bansan inda yatafi ba bakajin komai sai qarnin kwai A ciki,  haka dai na daure naci inaci ina kuka,  ya qarasa magar yana yamutsa fuska irin ya tuno abin kyakyamin,  kamar da gaske.  Kamar ilham zatai  kuka tace yaya mashkhur kaga abinda yaya abdul yake cewa ko?,  murmushi mashkhur ya saki sabida shi fad'an ma nishad'i yake bashi,  cewa yayi rabu da shi ilham duk borin kunya yake,  ai in abinci ba dad'i bazai iya ciba,  kina ji yace sai da ya cinye abincin.

Da sauri abdul yace no ai badan dad'i naci abincin ba kawai dai  sabida kar ai asara ne kasan dai ba kayau asara koh?.  Dady yana zaune ya kishin gida sosai yake jin dad'in kallon wanan rigimar da 'yayan nasa suke,  shida Ahmad da zahra,  duk sun koma 'yan kallo.  Ahmad dai sosai ya zubawa ilham ido dan duk abinda takeyi birgesa take.  Mashkhur ne yace!  ba wani ai ko addini yace karkaci abinda kasan zai cuter da kai,  kawai malan kaji girki mai dad'i zakazo kace ba dad'i,  ai wanan baqin ciki ne kawai,  zaro ido abdul  yayi tare da cewa!  Haba yaya mashkhur Ai ba irin wa anan matan akewa baqin cikiba yarinyar da ko ruwan T ta d'ora sai ya qone yayi baqiqirin.


Kai yaya abdul wlh ni dai sharrin ya isheni haka,  harara abdul ya watsa mata tare da cewa!  Ba wani sharri gaskiya ce dole a fad'a,  zahra ta fiki iya girki ba abinda kika iya sai kwa6a.  Ilham  rabu da shi ai shayin ma in ya qone baiwa ce wasu ma su d'ora ya qone cewar mashkhur,  dariya ilham tai sanan ta  yiwa abdul gwalo tare da cewa! Hakane baiwa ce kai kana da irin baiwan nan yaya abdul?.  Girgiza kai abdul yayi tare da ce no ai ni bana buqatar bai war nan karfanci ko baiwa,  ai ni ko ALLAH ya bani baiwar nan sai na kwana a masallaci ina kuka ALLAH yayemin sabida wanan ba   Baiwa bace kai qaddara ce mai zafi da rashin iya girki,  abdul ya fad'a har abdul da zahra suka had'a baki wajan sakin dariyar mugunta. 

Yaya mashkhur kaji abinda ya sake cewa ko?  Cewar ilham,  ilham rabu da shi ai sai ALLAH yana sanka yake d'orama qaddara,  kinga ALLAH yana sanki ne shiya ya dora miki,  tinda yace qaddara ce.  Murmushi ilham tai tare da sake yiwa abdul kwalo a karo na biyu.  Dariya abdul yayi tare da cewa! Okay ashe kun yarda kenan bata iya girki ba,  kun d'auki qaddara.  Mashkhur kuwa shiru yayi ya rufe ido kamar mai bacci ya kifa kansa a guwar shi,  sabida surutun ya fara hawar mai kai dama can shi ba mai san surutu bane,  wanan d'in ma dan ya dad'e bai had'u da su bane.

Dama some times   ko a gida yanaji suna irin fad'an nan musamman ma ilham da haidar  ko da faruq,  shidai yana jinsu baya cewa komai,  in kuma abdul yana wajan sai ya shigewa mai gaskiya.  Ilham ce tace tom shikenan ni dai na gaji da fad'an nan,  karmu sawa yaya mashkhur ciwan kai muyi shiru haka,  harara abdul ya watsa mata tare da cewa!  rufewa mutane baki uwar iyayi,  ke har yaushe akan haife ki  kika girma harma kikasan baya san surutun,  guntuwa da ke sai iyayi. Dariya ilham tai tare da cewa!  To yaya abdul kayi haquri kaji,  dariya shima yayi tare da cewa! Ai dama nace da kanki sai kin nemi sulhu ya fad'a tare da yi mata kwalan wasa.

Gaba d'aya

Please Login or Register in order to submit comment