Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cewa! Ahmad yanzu mai kake ganin za ayiwa waccan yarinyar ta warke da wuri? Kuma wa kake ganin zan samo ya ringa jinyar ta?. Ahmad kuwa jinjina kai yayi tare da cewa! Amsarka ta farko itace! kulawa sosai da jinya mai kyau ya kamata a nuna mata shine zata warke da wuri.

Amsa ta biyi kuma, ba wanda zai cigaba da yiwa zahra jinya sai kai,,. Haba ahmad ni kuma taya zan iya yi mata jinya, kana nufin ni zan ringa kai ta toilet ina bata abinci, in ta kamafa harda wanka?. Gyara zama ahmad yayi tare da cewa! To sai mai in kayi mata?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! Bazan iya ba macace fa, ba namiji ba ni mai ya had'a ni da yiwa wata mace jinya?.

Mashkhur wai sabida mai watara na kake furta magana ba tare da ka tauna taba,, haba kana magana wai kamar zahra ba matar ka bace?. A taqaice mashkhur yace eh to ni nama manta ma matata ce sai yanzu da ka tinamin. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! Tom shikenan kayi yadda kake so mashkhur, ni kada ka sake neman shawara a waje na ina baka shawara kana yarfamin baqar magana, to ni na gaji wlh.

Murya a tausashe mashkhur yace am sorry ahmad, ina cikin damuwa ne, yanzufa dady ya bigomin waya yace nan da 2 week's in bamu dawo ba zai zo, kuma gashi har yanzu bata samu sauqi ba karyazo ya riske mu a haka, ka san da matsala. Gyara zama ahmad yayi tare da cewa! Mashkhur zan baka shawarar qarshe wadda daga ita bani da wata kana jina?.

Gyad'a kai mashkhur yayi alamun to. Magana ahmad ya fara kamar haka! mashkhur ya zama dole kayiwa zahra jinya, na farko dai kasan ta sularka wanan cutar ta sameta, kai in ma ba ta sular ka bane ai zahra matace a wajanka ko baka qaunarta in kayi jinyar ta lada zaka samu. Sanan kasan in kaqi yiwa zahra jinya, dady yazo ya sameta a hakan, zaka shiga cikin babbar matsala, kuma bazai raba auran ku da zahra ba.

Da sauri mashkhur yace! Hakane ahmad wlh, kuma gashi ni bazan iya ci gaba da zama da ita a matsayin matata ba!! Amma ahmad ni gani nake kamar bazan iya ba abin yayi yawa. Mashkhur in kana d'aukar zahra a matsayin, wata can daban to kafin ka fara jinyar nan ka d'auke ta a matsayin matar ka! Wani kallo mashkhur ya watsawa ahmad tare da cewa! Aaa gaskiya bazan d'auke ta a matsayin matata ba.

Tom shikenan ka d'auke ta a matsayin qanwarka kamar dai ilham, haka zaka d'auke ta komai zai zoma da sauqi. Jim mashkhur yayi can kuma yace yanzu ahmad dole dai sai nayi mata jinyar nan? Ba wata mafitar?. Gyad'a kai ahmad yayi tare cewa! Kwarai wanan itace mafita mai sauqi kawai. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! To ahmad zan gwada naga ko zan iya.

Murmushi ahmad yayi tare da cewa! Zama ka iya, harara Ahmad mashkhur yayi tare da cewa! Ai ni ba d'an iska bane irinka ka gane koh?. Dariya ahmad yayi tare da cewa! Hmm ni bazan ce komai ba ALLAH dai ya tai maka kwai. Miqewa mashkhur yayi tare da cewa! Sai anjima,, murmushi ahmad yayi tare da cewa! Okay by, ka kula dai da kyau, kasan ita jinya ba'a mata mugunta, zaka sake komawa wata chakwakiyar ne, kuma ni ba ruwana ahmad ya qarasa maganar yana sheqa wata uwar dariya.

Mashkhur kuwa ko ta kansa bai biba yayi fucewar sa. Ahmad kuwa yana fita ya saki ajiyar zuciya tare da cewa! Hmm ALLAH yasa yadda na tsara komai ya tafi dai-dai, ahmad ya fad'i akan a zuciyar sa.
6angaran mashkhur kuwa har lokacin daya koma zahra tana waya da dady dan hira suke sosai.

Mashkhur kuwa qarasowa yayi ya d'auke wayar tare da kasheta gaba d'aya. Nan da nan zahra ta had'e rai ta cin kushe fuskar nan tata. Shima mashkhur cin kushe fuskar tasa yayi tare da cewa! Ke uban waye yasa kikace sai an sallamo ki alhalin baki warke ba, yanzu wa kike so ya cigaba da yi miki jinyar? . Zahra kuwa cikin dakakiyar murya tace, eh sabida na gaji da zaman asibitin shi yasa na dawo gida.

Dan bazan iya zama asibiti ba, in bama dole ba da cutar da akayi min ni mai ma zai aki ni asibitin nayi kwanakin nan?. Mamaki ne ya kama mashkhur ganin yadda zahra take mayar mi da magana ga tsai haka. Muryar ta ya qara tsinkaya tana cewa ni inaso ma nayi fitsari kuma ina so naci abinci yunwa nake ji, kaje ka kiramin yaya ahmad dan ya tai makamin.

Fuska ba wasa mashkhur yace ke ki shiga hankalinki, kinga nai miki kama da d'an aike ne da zakice na kira miki wani, in ma banda iskanci irin naki namiji ba maharramin kiba, kina matar aure har kike cewa! Aje a kira miki wani gardi ya kai ki toilet koh?, zaki ga qarshan iskan ci wlh, sa'ar ki d'aya baki da lpy da yau sai jikinki ya gaya miki,, zahra kuwa tana jin ruwan bala'in mashkhur ta kama bakinta ta rufe gam dan har yanzu tana jin tsoran sa.

Mashkhur kuwa yana kai aya ya wuce ya bar zahra kwance a wajan. Zahra kuwa shiru tai tana nazari taya zata iya shiga toilet tai fitsari? Ita da bata iya tafiya ma.
To fah wajan rabin awa zahra tai a zaune tana tinanin yadda zata shiga toilet dan har fitsarin ya matse ta kamar zai zuba. Zahra da taji yana qoqarin zubowa da kyar ta iya rarrafawa ta miqe ta zauna.

Tana so ta tashi amma ta kasa, hakan ne yasa ta fashe da kuka harda majina, dan fitsarin ya matseta sosai. A dai-dai lokacin mashkhur ya fito daga bedroom d'in shi, yana fitowa ya hango zahra tana ta fama shasheqar kuka. Da sauri ya qarasa in da take, yana qarasa wa ya d'an tsuguna tare da cewa! Ke lpy kike kuka. Zahra kuwa cikin muryar kuka tace ni fitsari nake ji ya matsa ni kuma.

Wani siririn tsaki mashkhur yaja dan shi da duk a zatan sa wani abun ne ya same ta dan har ta d'an d'aga mai hankali. Cikin takaici mashkhur yace raguwar banza sai rashin kunya, zahra kuwa shiru tai bata ce komai ba, dan ita yanzu bata da bakin fad'a. Jim mashkhur yayi na wasu daqiqun kamar mai nazari,, ai zahra batayi aune ba sai ji tai mashkhur ya sunkuce ta kamar wata jaririya. 🙊🙊🙊

Da sauri zahra tasa hannayan ta biyu ta saqalo wuyan mashkhur dan ji tai kamar zata fad'i in batayi hakan ba. Ai kuwa karaf sukayi 4 eyes da mashkhur, ai kuwa mashkhur ya sakar mata wani mugun kallo, zahra kuwa sake qanqame wuyan shi tai kamar wanda zata fad'o tare da lumshe jajayan idanuwanta wanda sukaci kuka, ba komai ne yasa zahra lumshe idon ba sai jin qamshin mayan turaran nan na mashkhur wanda take mutuwar so.

direct toilet d'in falo mashkhur ya nufa da zahra yana zuwa ya zaunar da ita akan masan a hankula da yake masan na zama ne. Daga haka kuwa kallon kallo suka farayi da mashkhur kowa da abidda yake saqawa a ransa. Can kuma mashkhur ya tsuguna a gabanta yana tantama taya ma zai iya fara tai makawa zahra wajan cire wandan nata dan rai fitsarin?. Can kuma yayi ta maza yace bari na d'agaki sai ki cire.

Girgiza kai zahra tai tare da cewa! Kawai kaje zan iya, ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Okay,. Miqewa yayi ya fuce yana mai godewa ALLAH a zuciyar shi, da zahra zata iya cire wandan ta da kanta.
Zahra kuwa da kyar da dabara ta iya cire pants d'in nata a zaune da yake har yanzu 'yan yatsun nata basu gama warkewa ba. Bayan ta gama qaramar shower tsarki ta ciro tai sarki sannan ta mayar da pants d'in nata da kyar, ta gyara rigar tata.

Sai da mashkhur ya d'au 10 minute sanan ya koma toilet d'in, yana koma ya tarar da zahra a zaune, kamar dai yanda ya barta, fuska ba walwala yace kin gama? Gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Ehh. Qarasowa mashkhur yayi tare da sake d'aukar ta, amma wanna karan a hankula ya d'auke ta ba sunkutar tai yayi ba kamar d'azu. Itama zahra a hankula ta sake saqalo wuyan nasa gudun karta zame ta fad'i.

A kan sofa daya d'auke ta nan ya mayar da ita, yana sauke ta ya juya ya wuce kicin. Bayan few minutes sai gashi ya dawo da cup a hanunsa. T ne a ciki cup d'in ajiye mata yayi a gefan ta tare da cewa! Gashinan sai ki sha ai. Murya a sanyaye zahra tace bazan iya ba hannuna ciwo yake min. Cikin fad'a-fad'a mashkhur yace eh kinsan hannun naki yana yi miki ciwo kikace sai an sallamo ki?.

Gashi yanzu kinzo kina wahalar da kan ki nima kina wahalar da ni. Zahra kuwa kawar da fuska tai ba tare da tace komai ba. Mashkhur kuwa dogwan tsaki yayi tare da d'aukar cup d'in t d'in. Ya d'an zauna a gefan zahra.,, cikin ji haushin zahra ya d'ebo t d'in tare da kai mata bakin ta. Da sauri zahra ta kawar da fuskar ta gefe tare da cewa! Da zafi fa, gaskiya bazan iya shaba, ka fifita min.

Inayiwa masoyana 'yan uwa na musulmai happy takutaha , ALLAH ya qara mana qaunar annibi Muhammad s❤A❤W, yasa ya cecemu ranar gobe qiyama, ALLAH ya mai-mai ta mana.

*hmm nikuwa amina bayero nace ya jinyar nan zata qarke kuwa?.

*za'a wanye lpy ko ko a kasin haka?.

Ku biyoni a littafin ADALILINTA, dan jin amsar tambayar nan.

Mu had'e a next page


ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 86*

Ya d'an zauna a gefan zahra.,, cikin ji haushin zahra ya d'ebo t d'in tare da kai mata bakin ta. Da sauri zahra ta kawar da fuskar ta gefe tare da cewa! Da zafi fa, gaskiya bazan iya shaba, ka fifita min.............

Wani banza kallo mashkhur ya watsawa zahra tare da cewa! Sannu ammi kinji nace sannu uwata, in nace bazan fifita ba duka na zakiyi? Shiru zahra tai sabida tasan a halin yanzu itace mai nema, amma bada ban haka ba sai ta mayarwa da mashkhur martani. Cikin jin haushi mashkhur ya miqe ya wuce draining ya d'auko kofi sanan ya dawo, ya sake zama a gefan zahra.

A hankula mashkhur ya fara fifita t d'in, sai da shayin ya huci sosai sannan ya dena fifitawa. Rai ba dad'i mashkhur ya d'ebo t d'in a cokali ya kai bakin zahra, a hankula zahra ta bud'e kyakyawan jan bakinta ta fara sha a hankula. Nan ma mashkhur ya sake qulewa sosai ganin yadda take wani shan t d'in kamar wadda ake mata dole.

Haka dai mashkhur ya daure ya cigaba da bata t d'in sabida shima ya gaji da maga. Sai da zahra da mashkhur suka d'au 15 minutes suna abu d'aya sanan zahra ta gama shan t d'in. Tana gama sha t d'in mashkhur ya miqe riqe da cup d'in a hanunsa ya wuce kicin. Bayan few minutes ya futo riqe da plate d'in abinci a hanunsa.

Yana zuwa ya dire plate d'in a gefan zahra, sanan ya zauna, a inda ya tashi da. Kallo d'aya zahra tai wa abinci ta kau da kanta gefe,, zahra muryar mashkhur taji ta daki kunnan yana cewa! kee bazaki jiyo kici abinci ba nifa ba bawan ki bane kawai taimaka miki nake,, ya mutsa fuska zahra tayi tare da cewa! Hmm nifa bana buqatar cin abinci yanzu fruit nake san sha ba abinci ba.

Jim mashkhur yayi yana kallan yadda zahra take ya mutsa fuska kamar wata mage. Dogwan tsaki mashkhur yaja tare da miqewa ya bar wajan zuciya ciki da takaici. Mashkhur bai tsaya ko inaba sai bedroom d'in shi, yana shiga ya cire rigar sa yayi willi da ita gefe tare da fad'awa kan gadon ya baje. Lumshe ido mashkhur yayi kamar mai bacci, sam lamarin nan ya ishe shi wai a hakan ma yanzu aka fara jinyar..

Sam mashkhur baya san hayaniya ko yawan zirga-zirga a rayuwarsa yayi nan yayi can sam baya qaunar haka, amma wai shine yanzu zai yi jinya. Wani siririn tsaki mashkhur yaja yana tinanin yanzu taya ma zai iya yin bacci kenan da daddare?, inma ya kai ta bedroom d'in ta ya zama dole ya ringa zuwa akai-akai. Miqewa mashkhur yayi sanan ya wuce toilet domin yin wanka da ruwan sanyi ko ya samu zuciyar shi tai sanyi.

6angaran zahra kuwa tana ganin mashkhur ya tashi ya tafi a zuciyarta ta saki wani siririn murmushi,, dan zahra ta d'au alwashin sai ta bawa mashkhur wahala sosai, shima sai yaji a jikinsa,, ta fara mai tsirfe-tsirfe kala-kala a cikin gidan ba zata barshi ya huta ba.
6angaran mashkhur kuwa bayan ya futo daga toilet d'in kayan bacci yasa sanan ya koma kan gado ya kwanta.

Sai da mashkhur ya d'au 30 minutes yana kwance a kan gado. Sai da zuciyar shi ta wuce d'an wuce kad'an kwakwalwar shi ta fara dawo fresh sanan ya miqe ya wuce falo inda yabar zahra, a zaune ya ganta kamar yadda ya batta bacci har ya kwasheta, ga abinci a gefe kamar yadda ya ajiye. A jiyar zuciya mashkhur ya sauke sannan ya juya ya nufi hanyar bedroom d'in zahra.

Yana zuwa ya murd'a Handel d'in qofar ya shiga ciki, bedroom d'in duk ya d'anyi qura, ga bed d'in zahra ta tila uban kaya akai, da dukkan alamun wankakune, futo da su tai daga wardrobe d'in, sabida wardrobe d'in a bud'e take. Wani siririn tsaki mashkhur yaja, dan shi burinsa yazo ya d'an gyara mata bedsheet sanan ya d'akota ya kwantar da ita. Tinani mashkhur ya farayi taya zai iya mayar da kayan nan mai uban yawa?.

Kai gaskiya bazan iya ba, yanzu dai mene mafita? Mashkhur ya fad'a hakan a zuciyar sa. Can qasan zuciyar shi, yaji tace ai qwarama ka mayar da ita d'akin ka sai kafi hutawa da zirga-zirga nan. Mashkhur kuwa cewa yayi tab akan mai zan kai ta bedroom d'in na, ni na kwana a ina?. Amma ina ba mai basa amsa. Sai da mashkhur ya d'au 20 minutes yana tinani kafin ya gama yanke shwara abinda zai yi.

Mashkhur ya yanke shawarar ya kai zahra bedroom d'in shi kawai ya kwantar da ita akan bed d'in sa. Juyawa mashkhur yayi ya fuce daga bedroom d'in zahran. Bayan ya fita direct sofa da zahra take kwance, ya nufa,. Yana zuwa ya sa hannu ya d'auke plate d'in abinci ya kai shi kan draining ya ajiye. Yana ajiyewa ya dawo inda yabar zahra a kwance tana bacci.

Hannu mashkhur yasa yad'auki zahra kamar dai yadda ya d'auke ta dazo. Da sauri zahra ta bud'e ido dan jin an d'auke ta ba shiri, tana bud'e idon ta taganta a hanun mashkhur ya d'auke ta kamar dai dazu. Da sauri zahra tasa hannayan ta biyu ta saqalo wuyan mashkhur kamar dai d'azu tare da sakin nauyin ta iya qarfinta.

Dan ita a yanzu burinta ta wahalar da mashkhur kawai,, 6angaran mashkhur kuwa kamar ma bai san abinda zahra take ba ya cigaba da tafiyar shi nml dan ya gane ta tana sane ta qara sakin jikin ta. Direct mashkhur bedroom d'in sa ya nufa da zahra, yana shiga ya wuce kan bed ya ajiyeta, zahra kuwa cikin mamaki tace yana ga haka, ka kawo ni nan mai makwan bedroom d'i na.

Mashkhur ko kallan ta bai yi ba bare ma ya tanka mata,, dan yana ajiye ta akan gadon ya fuce daga bedroom d'in. Zahra kuwa a hankula ta miqe qafarta tana tinanin dalilin da yasa mashkhur ya kawo ta nan,, can kuma sai zahra ta tina ranar da zata candy ta hargatso da kayan wardrobe d'in ta gaba d'ayan su ta futo da su sabida tana neman kayan candy, a cikin wardrobe d'in.

Zahra tinani tai ko ya shiga bedroom d'in ya gan shi a hargatse ne shi yasa ya kawo ta nan. Bayan kamar 10 minutes mashkhur ya shigo hannu d'auke da plate, da kayan fruit a cikin plate d'in, yana zuwa gefan zahra ya ajiye tare da cewa! In kinga dama kici in kuma baki gani ba ki barshi sabida ni ba wahalale bane da zan zauna in ta baki a bu abaki, ya qarasaagana yana had'a mata da wani kallan banza.

Zahra kuwa a zuciyar ta cewa tai aikuwa sai ka bani a baki in ba haka ba bazan ciba sai dai ka kwashe abinka yadda ka kawo su mugu kawai. Mashkhur kuwa daga haka ficewa yayi ya koma fallo ya zauna. Yana zama ya aji qarar shigowar text a wayar shi da take kan kujerar a ajiye. Hannu mashkhur yasa ya d'auki wayar tare da shiga message contact d'in. Daga school d'in su ne aka turo mai message d'in. wai gobe yazao ya kar6i result jarabawar shi.

Ajiye wayar mashkhur yayi a gefe,, yana tinanin ya result d'in shi zai kasance kuwa? Shi dai a tinanin sa yayi iya qoqarinsa wajan zana jarabawar nan, amma in qaddara ta gifta bai ciba shikenan dady bazai bari ya saki zahra ba? Mashkhur ya watasawa kansa tambayar nan, amma zuciyar mashkhur sai tace mai ka dena munanawa kan ka zato in sha ALLAH baza fad'i ba.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da addu'a a zuciyar ALLAH ya bashi nasara. Daga haka miqewa yayi ya d'auki wayar shi da farar ledar maganin zahra, sanan ya nufi firinji ya d'auko ruwa mara sanyi sanan ya wuce bedroom d'in sa. Mashkhur yana shiga ya hangi zahra ta d'an kishin gid'a, a fuskar bed d'in ta tafi duniyar tinani. Fruit d'in kuwa yana nan yadda ya ajiye ko motsa plate d'in batai ba bare ma taci.

Nan da nan mashkhur yaji ran shi ya 6aci, wato da gaske-gaske jinyar zai yi, qarasawa kan bed d'in yayi tare da a ajiye ledar maganin a gefe. Sanan shima ya d'an zauna akan bed d'in. Har lokacin da ya zauna zahra bata dawo daga dogwan tinanin data tafi ba. Hannu mashkhur yasa ya d'auki plate d'in fruit d'in sana ya cire fork d'in daga cikin plate d'in fruit d'in, bayan ya cire d'an dago plate d'in sama yayi dai-dai fuskar zahra ya fara bigawa da yake plate din na tangaran ne.

Firgita zahra tai sabida qarar da taji ba shiri, mashkhur zahra ta gani riqe da plate d'in fruit d'in da fork da dukkan alamun shi ya biga, fuskar nan tasa ba walwala. Cikin 6acin rai mashkhur yace ke wai sabida mai kike rai namin hankali ne wai bawanki kika mayar da nine, sabida tsabar iskanci sai na zauna na baki a baki koh? Sai kace wata yarinya. Itama zahra fuska ba walwala tace eh ai bazan iya ci bane da zan iya da tina naci ai.

Shiru mashkhur yayi yana jinjina rashin nutunci irin na zahra,, a ganin mashkhur sa'a d'aya zahra take ci dan bata da lpy da wlh tana gaya mai abinda bai gamsu da shifa ba sai dai taji kyawawan mari a fuskar ta,, amma yanzu yasan in ya dake ta ya sake janyowa kansa matsala ne shi yasa kawai yake kyale ta. Mai da fork d'in cikin fruit mashkhur yayi sanan ya tsikaro watarmilo

Sanan ya ciro cokalin ya kai bakin zahra, a hankula zahra ta bud'e kyakyawan bakinta, tare da gutsira kand'an. Mashkhur kuwa sakin baki yayi yana kalan ikwan ALLAH bai ta6a zatan zahra zata iya wanan rashin mutuncin ba. Sai da ta d'au 3 minutes sanan ta gama cinye wadda ta gutsira. haka zahra ta d'in ga tsirfe-tsirfe kala-kala, sai da suka d'au 30 minutes tana shan fruit d'in, mashkhur kuwa yana sane yayi mata shiru sabida yasan tana sane itama take iskanci so take ya tanka.

Bayan zahra ta gama shanye fruit d'in, ledar magaguna ta mashkhur ya janyo ya zazzage su yana dubawa. Bayan ya gama dubawa ya fitar da wanda zata sha yanzu da wanda zai shafa mata sanan ya mayar da ragowar. Bayan ya mayar miqewa yayi ya fuce daga bedroom d'in hannunsa riqe da plate d'in fruit d'in da zahra ta gama sha. Bayan few minutes ya dawo da riqe da cup a hannunsa.

Yana qarsowa ya hau kan bed d'in ya zauna a kusa da zahra suna faces d'in juna, a hankula mashkhur ya ajiye cup d'in ruwan a kan gadan sanan ya d'auki maganin ya fara 6allo su. Sai da ya gama 6aro iya wanda zata sha, sanan ya fara bata. Miqa mata yayi tare da cewa qar6i ki sha,, zahra kuwa nuqe kafad'a tai tare da cewa! A a gaskiya ni na gaji da shan magungunan nan.

Shiru mashkhur yayi tare da sa kyawawan 'yan yatsun guda biyu ya d'auki kwayar maganin guda d'aya sanan ya kai qofar bakin zahra. Zahra kuwa qin bud'e bakin tai ta sake matse bakin nata. Rai a 6ace mashkhur yace wlh in baki bud'e bakin kin sha magangunan nan ba sai na zubasu a cofi sun narke, sanan zan matse miki baki na zuba miki, kuma na toshe miki hanci sai kin shanye tsaf, duk d'acin sa kuwa.

Zahra tana jin hakan tai sauri bud'e bakin ta sabida tasan halin mashkhur tsaf zai iya, wanan kad'an kenan ma daga cikin shika shikan mugun tar sa. Mashkhur kuwa harara ya watsa mata tare da cewa! Da karma ki bud'e da kinga fad'a da cikawa in yaso naga qaryar rashin kunyar taki ya qarasa maganar yana jefa mata maganin a bakinta.

Zahra kuwa yamutsa fuska tai tare da turo bakin ta gaba, mashkhur kuwa cup d'in ruwan ya d'auko ya sake kai wa bakinta shima ruwa da kyar tasha, a wani gayance take shan sa. To haka dai mashkhur yay ta bata magungunan har ta gama shanyewa. Bayan ta gama shanyewa magani ruwa na matsawa mashkhur ya ta tsawa zahra a hanunta sanan yace ta shafa a goshinta, wato inda ya fashe.

A hankula zahra ta fara d'aga hanun nata, tana qoqarin shafawa,. A hankula ta d'an fara shafawa tana d'an shafawa tana ghutawa,. Mashkhur kuwa tsayawa yayi yana kallan ikwan ALLAH yadda zahra take shafawa, bama a wajan ciwan take shafawa ba

Please Login or Register in order to submit comment