Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanun zahra zuwa toilet, suna shiga toilet ammi ta cirewa zahra kayanta qafafuwanta duk sun 6ace da jini. sai da ammi ta fara gaggasawa zahra jiki sabida har yanzu da awaki ciwukan da basu gama warkewa ba a jikinta, bayan ammi ta gama gasa mata jiki tayi mata wanka, sanna ta daura mata towel suka futo.

Itama ammi bayan sun futo wanka ta shiga tayi, ammi tana futowa ta samu zahra ta rafka uban tagumi, a dai dai lokacin ilham ta shigo hanunta riqe da kayan baccin zahra da kuma pants din da ammi tace ta dauko. Kusa da zahra ammi ta qarsa rarrashinta ta farayi tare da nuna mata ko wace mace a duniya indai ta fara girma tana hakan. Sai da ammi ta gama yiwa zahra bayani sannan ta nuna mata yanda zata ringa saka audigar.

Bayan ammi ta gama nuna mata yanda zata ringa sakawa, tasa kayan baccin nata. Kallanta ammi tayi tare da cewa yanzu mai yake damunki? Cuwan mara da kuma yunwa , dafa kafad’ar ta ammi tayi tare da cewa bari naje na dafa muku indomin, in kikaci sai nabaki maganin in sha ALLAH zaki dai na jin ciwan marar, d’aga kai zahra tayi alamun to, daga haka ammi ta fuce tabar zahra da ilham a bedroom d’in.

A hankula zahra tabi lafiyar godan ammi ta kwanta.kallanta Ilhamtai tare da cewa sannu, ko kallanta zahra batayi ba barema ta bata amsa. Murmushi ilham tayi sabida tasan sabida mai zahra take jin haushin ta, a hankula ilham ta hau kan bed d’in tare da cewa haba sis mai kuma nayi miki kike jin haushi na, ilham ta qarasa maganar tana kwanciya a kusa da zahra.

Harara zahra ta watsa mata tare da cewa au harma kin manta da dariyar da kika yimin dazu? Zubawa zahra ido ilham tayi tare da cewa haba zahra ai kece kika bani dariya, kallan tuhuma Zahra tayiwa ilham tare da cewa au dan larura ta kamani she kike min dariya koh?. Girgiza kai ilham taye sanna tace aa wlh ai nima inayi akan me zanyi dariya kawai yanda kika rikece ne shine kika bani dariya. Ajiyar zuciya zahra tayi tare da cewa ke kuwa naga baqwan abu ba dole na rikice ba, amma ilham ai baki ta6a gayamin kina yiba?

Shiru ilham tayi can kuma tace nima ai ban dad’e da farawa ba dan banfi wata uku ba, kawai dai nasanki da tsoro ne shiya ban gaya miki ba. Ta6e baki zahra tayi sannan tace to amma dai zuwa gobe zai dai na zubuwa ko?. Girgiza kai ilham tayi tare da cewa ai, in kika gama da wuri ma kiyi kwana biyu ko uku kinayi dan wasu ma har sati sukeyi suna yi. Zaro ido zahra tayi tare da cewa ai wanna jinin mutun ma sai ya qare, harara ilham ta watsa mata tare da cewa ba wani qarewa da zai yi, matacan jinini fa daga mahifa yake futuwa, kuma duk wata sai yazo.

Ilham tana rufe baki sai ga ammi ta shigo da flat d’in indomin a hanunta. Ajiye shi tayi akan table tare da cewa ku sakko muci, ba musu suka sakko, tare da ammi sukaci abinci. Bayan sun gama ammi ta bawa zahra maganin ciwan marar sanna suka kwanta, zahra sai da tasa ilham ta sawa qofar bedroom d’in key sanna ta iya kwanciya, kuma shima sai data qanqame ammin sabida tsabr storan kar mashkhur ya shigo ya sake dukan ta.

Sosai zahra ta rungeme ammi, can tace ammi wai ina ameer ne?, nasan yana wajan hjy kaka, yana bacci kuma kinga yanzu dare yayi sai da gobe kuma cewar ammi. Shiru zahra tayi can tace wai ammi sabida mai yaya mashkhur baya sonane? Rungumeta ammi tayi tare da cewa haba zahra kusan kullum sai kin tambaye mu wannan, nace mike kawai mashkhur yana kishi dake sabida kafin a haife ki shi aka fuso sabida sunan kakan kune dashi wato baba, lokacin da aka haifeki sai aka samiki sunan hajiya shine kuma akafi sanki shiya. Shiru zahra tayi sabida kullum duk wanda ta tanbaya sabida mai yaya mashkhur ya tsane ta amsar da aka bata kenan, Daga haka bacci yayi awan gaba da su........

Nasan masu karatun littafin ADALILINTA zasuyi tinanin wai ina oga👨🏼‍✈️ mashkhur ne?.
6angaran mashkhur kuwa tun lokacin dasu zahra suka tafi asibiti ya shige part d’in su, yayi wanka ya shirya sannan ya dauki key d’in motar sa ya fice ya tafi wajan cin abinci. Sai wajan qarfe 8:00 pm ya dawo yana dawowa ya shige d’aki yayi kwanciyar sa. To har tsawan kwana uku mashkhur bai bari ko hanya ta had’a su da dady ba, dan yanzu ma ya manta ya daki wata halitta zahra ma dan har ya kar6i kud’i wajan uwar dakin sa momy ya siya wata sabuwar laptop d’in.

Washe gari.

Kowa yay farin ciki da dawowar zahra banda momy da kuma mashkhur da har yanzu bai ma san ta dawo ba dan yanzu baya futowa breakfast dan karya had’u da dady.
Bayan su haidar sun karya suka wuce makaranta shida su ruma, ammer dai bai jeba yace yau yana tare da aunty zahra, itam ilham bataje ba. Zahra da ameer da kuma ilham suna zaune a falo suna breakfast, ammi da hajiya kaka kuwa suna zaune a gife suna hira.

Dady ne ya shigo baki d’auke da sallama, da gudu ameer ya tashi ya nufi dady a guje, da sauri dady shima ya bud’e hanun nasa dan ameer ya hugging din sa. Ilham da zahra kuwa gaishe dashi suka fara yi. Fuska a sake dady yake amsawa. Shima dady har qasa ya tsuguna ya gaida hajiya, bayan ya gaishe da ita suka gaisa da ammi, daga haka dady ya wuce wajan zahra. Zama yayi a kusa da ita tare da dafa kafad’ar ta yana cewa maman ya jikin naki? Murmushi zahra tayi tare da cewa dady ai na sama sauqi.

Shima dady murmushi yayi tare da cewa to ALLAH ya qara sauqi. Dady Mai da kallan sa kan ilham yayi tare da cewa ilham mai yasa baki je school ba?, cikin shagwa6a ilham tace haba dady ai sai mun shanye maganinmu ni nida zahra zamu koma, girgiza kai dady yayi tare da jan kumatun ilham yan cewa mai cuta daban mai shan magani daban, dukkan nunsuda dariya sukayi, shima dady dariya yayi sanna ya miqe yana cewa gashi har kun fara koyawa auta shima in bazaku ba baya zuwa, daga haka dady ya kama hanyar futa daga part d’in ammin.

Dady yana futa bai nufi ko ina ba sai part din mazan gidan, wato part din su mashkhur.... nikuwa amina bayero nace hmm mai kuke tunanin dady zai yi a part d’in su abdul, to ku biyoni domin kuji me dady zai je yayi a part d’in su abdul......💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 nifa nabi bayan dady koma ku biyoni.....😂
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.........

*page 43*
Dady yana futowa bai nufi ko ina ba sai part din mazan gidan, wato part din su mashkhur.........

Dady yana shiga part din su bai tsaya ko inaba sai upstep, wato sama yahau. Yana hawa sama ya nufi d’akin oga mashkhur. Yana zuwa qofar room d’in ya murd’a Handel Ai kuwa qofar dakin a 6ud’e take. Yana shiga ciki ya tarar da mashkhur shi da momy suna hira ga flat da cup a gefan sa ga duk kan alamun momy ce ta kawo mai breakfast d’in. Dama sometimes momy in tana so ta zubawa mashkhur maganin boka a abinci, haka take dafa mai abinci ta kawo mai har room d’in sa.

Dady ko sallam bai yi ba ya kutsa ka cikin room d’in, fakowa a room d’in, dan haka bedroom d’in dady ya kutsa kai. Yana shiga fuska a d’aure ya kalli momy tare da cewa tashi ki fuce, ba musu momy ta fuce daga bedroom din ta koma falon d’akin mashkhur d’in. Tana futa dady ya juya a zuciye ya sawa d’akin key. Yana sawa bedroom d’in key ya juya ya nufi mashkhur dake zauna akan bed gadan-gadan, sai da gaban mashkhur ya fad’i amma da yake namijin gaske ne ko a fuska bai nuna ba.

Dady yana qarasawa ya damiqi wuyan mashkhur tare da aika mai sakwan naushi. Dukan mashkhur dady yake baji ba gani amma sam oga mashkhur yaqi yin ihu barema hawaye. Momy kuwa taji alamun dady dukan mashkhur yake nan da nan tahau magiya akan ya rabu da shi amma ina dady ko amsa bai bata ba. Data gaji da magiya room din abdul ta nufa domi ta taso shi ya taya ta bawa dady haquri, dama abdul bai je makaranta ba sabida yau basu da lakca.

Lokacin da abdul ya futo magiyar duniya yayiwa dady amma ina dady bai dai na dukan mashkhur ba. Mashkhur yaji jiki sosai kawai taurin kai ne ya hana shi ihu barema mutan gidan suji har suzo su taima ke shi. Da sauri abdul ya fice daga falon ya nufi part d’in ammi. Lokacin da yaje su zahra har sun gama cin abinci, ilham tana karatun qur’an azuciyar ta, zahar kuwa suna wasa da ameer., ammi da hajiya kaka suna ta hira har yanzu.

Da sauri abdul ya qarasa wajan hajiya kaka tare da cewa hajiya kaka dan ALLAH kizo ki bawa dady haquri, ya rufe mashkhur a bedroom sai dukan sa yake. Shiru hajiya kaka tayi kafin tace to abdul ya kake so nayi ai mashkhur shi ya jazawa kansa, kuma kasan dadyn ku da zuciya tun ranar da mashkhur ya daki mai sunana yake jin haushin sa. Marairaice fuska abdul yayi tare da cewa dan ALLAH hjy kaka kije, tunfa dazu yake dukan sa.

Ita dai ammi shiru tayi tunda tun da aka haifi mashkhur dady bai ta6a dukan saba sai yau. Tinda yau dady ya dake shi tasan ya kai shi qarshe, kuma bataji haushin hakan ba sabida mashkhur ne ya jawa kwansa. Da sauri hjy kaka ta miqe dumin tasan halin dady da zuciya karya kashe mata jikan ta mashkhur.
Lokacain da hajiya kaka ta qarasa part din su mashkhur, har dady yayiwa mashkhur mugun duka dan shi dukan da dady yayiwa mashkhur ma yafi wanda mashkhur yayiwa zahra kawai sabida mashkhur namijine kuma yana da juriya.

Sosai hajiya kaka ta shiga buga qofar tare da fad’in abubakar zo ka bud’e mun dakin nan. Dady ba asan ransa ya rabuda mashkhur ba kawai sabida yana jin maganar mahifiyar sane, haka dady ya rabu da mashkhur yazo ya bud’e qofar. Lokacin da hajiya kaka taga hanun dady sai da gabanta ya fad’i sabida duk hanunsa ya jiqe da jinin mashkhur. Dady yana futowa ba wanda yayiwa magana ya wuce yabar su a tsaye.

Har ‘yar rige-rigen shiga d’akin su hajiya kaka da momy harma da abdul suke. A baje akan gado suka samu mashkhur yana nunfashi sama-sama, duk dady ya fasawa mashkhur fuska jini sai zuba yake, bedsheet d’in duk ya jiqe da jini. A razane su hajiya kaka suka qarasa tare da ambatar sunan mashkhur, amma ina mashkhur baya cikin hayya cinsa yaji jiki, dan ko ni amina bayero sai da na tausayawa mashkhur sabida ya daku a hannin dady ba waii .

Abdul ma ya tausayawa mashkhur sai sannu yake faman yimai. Hajiya kakama hankalin ta ya tashi, sai fama fad’a takewa mashkhur, haba ai kaga yanzu abinda ka jazawa kanka akan kawai ta fasama wata banzar laptop sai ka kama ‘yar uwar ka kai mata dukan mutuwa, kai kuma yanzu yana dukan ka sabida tsabar taurin kai kaqi bashi haquri bare ma kayi ihu a taimaka ma. Kwa6e baki momy tayi tare da cewa haba hajiya kina ganin halin da yaran nan yake ciki amma kina yi masa fad’a.

Harara hajiya kaka ta watsawa momy tare da cewa ai duk ke kike lalata mashkhur d’in” tinda kullum in yayi laifi bakya ganin laifinsa barema kiyi mai fad’a ya gyara. Shiru momy tayi sabida tasan ba qaramin aikin hajiya kaka bane tayi mata fad’a yanzu.
6angaran dady kuwa yana gama dukan mashkhur ya shiga part d’in sa yayi wanka ya fice, abinsa.

Momy tana ganin dady ya futa ta dauki mukullun motar mashkhur suka wuce da shi asibiti ita da abdul da hajiya kaka, ammi kuwa ko mashkhur ba taje ta duba ba barema ta bisu asibitin. Su momy basu dad’e da futa asibiti ba doctor habib ya zo gidan domin yiwa zahra allura. Sai da suka gaisa da ammi sanna yayiwa zahra alluran, sai jan Zahra da hira yake amma sam zahra taqi sakin jiki dashi da yake bata da surutu. Haka sukai ta hira da ilham daga qarshe kuma ya wuce asibiti.

6angaran su mashkhur kuwa lokacin da sukaje asibiti sunji sa’a han karb’e shi ba’ace sai da d’an sanda ba. Anyi mai treatment sosai har dama alluran bacci aka had’a mai dan har kwantar da shi akayi. Kuma duk da kud’in momy aka yiwa mashkhur komai da komai.
Lokacin da dady ya dawo yaji labarin ankai mashkhur asibiti yayi fad’a sosai kuma a daran yacewa momy sai an sallamo su sun dawo gida, ai kuwa ba yadda momy ta iya haka aka sallamu shi da magungunan sa suka dawo gida.

Kaf mutan gidan kowa ya girgiza da dukan da da dady yayiwa mashkhur, sabida tunda suke basu ta6a ganin dady ya dora hanunsa akan mashkhur da niya duka ba sai yau. Kuwa yaje ya duba mashkhur banda ammi da dady sai kuma zahra. Hakan ne yasa hajiya kaka ta takurawa ammi akan dole sai taje, ba yadda ammi ta iya dole hakan taje duba mashkhur.

Lokacin da ammi taga yanda dady ya daki mashkhur tayi mamaki sosai, kuma sai taji zuciyar ta duk ba dad’i, abinka da uwa. Amma sam ammi bata nuna hakan a fuskar taba, kuma ko ba komai tasan dady ya biwa zahra hkkin ta.
6angaran dady kuwa bayan dukan da yayiwa mashkhur har wani mataki yake qoqarin dauka. Shima dadyn har zuciyarsa yake jin dukan da yayiwa mashkhur, kawai dai yana daurewa ne sabida dady yana matuqar son mashkhur a rayuwarsa.

Amma kuma in dady ya tino d’anyan hukuncin da mashkhur yayi wa zahra sai yaji hankalinsa ya kwanta da hukuncin da yayiwa mashkhur kuma sai yaji kwarin guiwa akan matakin da yake so ya dauka akan mashkhur, hmmmm nikuwa amina bayero nace wannan wana mataki dady zai d’auka? ohoo.

6angaran oga mashkhur kuwa abin ba’a cewa komai, yana kwance akan bed d’in sa wanda hajiya kaka ta gyara mai ta cire bedsheet din ta saka mai wani. Wani irin zafi da turniqiqi da hucin kaqin ciki zuciyarsa take mai. Ba dukan da dady yayi mai ne yafi qona mai rai ba kawai dalilin da yasa dady ya duke shi ne yake qona mai rai ne. Wai duk a ADALILINTA dady yayi mai wannan dukan, shida dady ko marinsa bai ta6a yiba sai gashi yau a adalilin zahra ya kusan kashe shi.

Wani kukan baqin cikine ya silalowa mashkhur yau a karo na biyu kenan a dalilin zahra yake zubar da hawaye. Na tsane ki bana sonki bana qaunar ki bana son na qara ganinki a rayuwata, abinda mashkhur yake fad’a kenan. Ranar dai mashkhur kwana yayi bai yi bacci ba yanda yaga rana haka yaga dare, ga mugun ciwo da jikin sa yake mai.

Washegari

Kowa yazo yayiwa yaya mashkhur ya jiki banda zahra da dady, momy ce take kula da mashkhur ammi tanaji tana gani momy take nuna mata isa da mulki akan mashkhur amma sam ita ammi bata kawo komai a ranta ba, sabida taga har yanzu ita take kula da abdul kuma abdul ya d’auketa kamar uwa, shiya ammi batasan shiga tsakanin mashkhur da momy duk da kuwa ammi tasan momy tana lalatawa mashkhur tarbiya.

Yauma doctor habib yazo yiwa zahra allura, bayan ya gama yimata suka gaisa da dady, dady yayiwa Doctor habib godiya sosai kuma har number sa ya kar6a, sanan dady ya roqi doctor habib akan zai zama family doctor d’in gida. Doctor habib kuwa yaji dad’i hakan kuma ya amince da tayin dady, ba dan komai doctor habin ya amince da tayin dady ba sai a zahirin gaskiya tunda doctor ya d’ora idan sa akan ZAHRA yaji yana QAUNARTA.

Dan haka da dady yayi mai tayin zama family doctor din gida yaji dad’i yasan ko ba komai zai ringa ganin zahra kuma zai jirata har ta gama makaran ta ya AURETA. Haka dady sukayi sallama da doctor habib cikin aminci.
To yau kimanin kwana hudu kenan da dukan da dady yayiwa mashkhur kenan. Jikin mashkhur yayi kyau sosai cikin kulawar hajiya kaka da kuma momy harma da abdul.

6angare guda kuwa zahra tana nan jikin ta yayi kyau, yau kwanan ta hudu da fara jinin al adar ta kuma yau ya d’auke. Ammi da kanta ta koya mata yadda zatai wankan tsarki, bayan sun futo zahra tasa kayan ta tazauna tana shan iska zuwa yanzu zahra ta gama samin sauqi dan tana tinanin gobe zata koma makaranta. Abdul ne ya shigo baki d’auke da sallama, itama zahra fuska a sake ta amsa mai tare da cewa yaya abdul sannu da zuwa.

Fuska d’auke da fara’a abdul ya zauna a kusa da ita tare da da cewa zahran abdul ya jikin naki? Murmushi tayi tare da cewa zahran yaya abdul ta samu sauqi, tom shikenan tunda kin samu sauqi kizo muje har qarshan titin unguwar nan a kafa, zaro ido zahra tayi tare da cewa haba yaya abdul ai sai qafafuna su 6alle, dariya abdul yayi tare da cewa kingani ko ai nasan bazaki iya ba hakan yana nufin bakiji sauqi ba ko?. Yamusta fuska zahra tayi cikin shagwa6a tace ai koh ina da lafiyar ma bazan iya fita titin nan a qafa ba.

Murmushi abdul yayi tare da cewa haba qanwata ki saki fuskarki kinji nima da wasa nake miki bazan so naga babyn abdul tana shan wahala ba. Dariya zahra tayi tare da cewa nifa harma na manta sunan nan sai yau da ka katinamin, murmushi yayi yace to gashinan ai na tina miki inma so kike aringa kiranki da baby abdul d’in sai a ringa kiranki. Haba yaya abdul ai na girma ni yanzu ba baby bace sai dai kuma ameer, atare suka saki dariya mai ciki da nishad’i.

Suna cikin dariyar sai ga ammi ta futo daga toilet tana sanyi da rigar bacci tana goge kanta da towel daga gani wanka tayi. Murmushi ammi tayi tare da cewa dama tinda naji zahra tana ta dariya nasan yayan abdul ne ya shigo. Ammi tana gama rufe baki sai ga ilham nan ta shigo baki d’auke da sallama. Bayan su ammi sun amsa mata sallamar zama tayi tare da cewa dady ne yake kiran ku yace kowa yaje yana neman sa harma da ammi.

Miqewa abdul yayi tare da ruqo hanun zahra yace zahra taso muje kiran dady, ba musu suka zahra ta miqe suka futace . itama ilham d’in miqewa tayi tare da cewa ni dai ammi na tafi in kika gama shiryawa sai kizo, daga haka ilham ita ta fuce.
Ammi batafi mimti biyar ba ta shirya tsaf sanan ta kama hanya zuwa babban falon gidan. Lokacin da ammi ta isa ta tarar da duk mutanan gidan har da mashkhur da momy, harma da hajiya kaka da sauran yaran gidan. Hmmm mai dady zai gayawa mutan gidan nan? Ohoo, ku biyoni domin kuji mai dady zai cewa su
mashkhur..........


Kuyi haquri da wannan yau ban samu nayi muku typing sosai ba.......

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.........

*page 44*
Lokacin da ammi ta isa ta tarar da duk mutanan gidan har da mashkhur da momy da kuma hjy kaka da saurayan yaran gidan......

Kowa ya mayar da hankalinsa kan dady yana sauraran abinda zai ce banda mashkhur da ya sunkuyar da kansa, dan ma karya had’a ido da zahra, dan kwata-kwata bayasan qara ganin zahra a rayuwarsa. Itama zahra tsoran mashkhur takeyi sosai tsoran da take mai ya sake nunkuwa a zuciyar ta, duk tabi ta maqale ajikin abdul, momy kuwa sai bankawa zahra harara take sabida sam bata san kusancin zahra da d’anta abdul.

Sai da dady yabi kowa da ido kafin yayi gyaran murya, bayan yayi gyaran murya cewa yay ! Bakomai ne yasa na taraku anan ba face inaso na sanan daku hukunci da na yanke akan mai sunan baba (wato mashkhur). Na yanke hukuncin zai bar QARASA NAN gaba d’aya. Kowa kallan dady yake cikin rashin fahimtar abinda yake nufa da mashkhur zai bar qasar nan.

Kallan dady hajiya kaka tayi tare da cewa Abubakar wanna wace kalar magana ce haka? To sabida me mai sunan malam ma zai bar qasar nan? Kuma wace qasa zai je?. Jinjina kai dady yayi tare da cewa abinda yasa mai sunan baba zai bar qasar nan shine karatu zai je ya yayi a qasar RASHA. Ai sai da gaban mashkhur ya fad’i sabida in da akwai abinda mashkhur ya tsana shine yabar qasar Najeria.

Momy ce tace wana karatu zai je yayi bayan saura shekara d’aya ya gama karatu kuma?. Kallanta dady yayi tare da cewa ai wanna karatun da yayi ya tashi a banza dan tun daga LEVEL ONE zai fara. kowa sai da gaban sa ya fad’i dajin maganar dady, mashkhur kuwa bai san sanda yace haba dady sabida mai zan dawo level one bayan orady na gama karatuna sauran one year na fah.

Wani mugun kallo dady ya watsa mai tare da cewa au harma tambayata kake akan wani dalilin zaka bar qasar nan koh? To tinda ka manta bari na tina ma!! Adalilin MAMANA (zahra) koh kai a tinaninka ka daki banza ne? Haba dadayn mashkhur ai wanna maganar ta wuce” kuma naga shima ka dake shi ka rama mata, cewar momy. Okay kina nufin ya cigaba da zama kenan ya halaka ta koh? To bari kiji wallahi mai sunan baba sai ya bar qasarnan kuma sai yayi shekaru hudu (4 years) a RASHA, in yaso kafin nan yayi hankali.

Miqewa dady yayi tare da cewa kuma ka shirya nan da sati d’aya (one week) zaka bar qasar nan, daga haka dady ya fucewarsa yabar kowa cikin alhini. Shima mashkhur d’in tashi yayi ya fice cike da baqin ciki. Ammi kuwa baiwar ALLAH ta kasa cewa komai, dan har ga ALLAH bataji dad’i hukuncin dady ba amma ba yanda ta iya baza ta iya yiwa dady musu ba.

Haka kowa ya tashi zuciya ba dad’i ko zahra bataji dad’i hukuncin dady ba, gani take kamar ita ta jaza komai, kuma ko ba komai d’an uwanta ne uwa daya uba daya, inje cewar ta ba inji amina bayero ba.☹️
Momy kuwa tana komawa part d’in ta d’aki ta shiga, safa da marwa kawai take , dan tama rasa abinyi. Babban baqin cikin momy sam bataso mashkhur ya ciga a rayuwa, kawai baqin ciki take mai, sabida tasan tabbas in mashkhur ya fita qasar waje karatu giveted zai zama sabida tasan yana da kwakwalwa sosai.

Da sauri momy tai hanyar drower mudubi domi dakko wayarta, dan tasan sarutu qanwar ta cikakiyar makira ce ita zata bata shwarar ya za’ai ta wargatsa tafiyar mashkhur RASHA.
Bugu biyo momy tayiwa saratu ta dauka, ko sallam babu saratu ta fara yaya halima yau kece kika bugomin ko dai ta samu ne?. Haba saratu wace samu Wallahi da wani baqin labari nazo miki, kai yaya halima mai kuma ya faru ne?.

Hmmmm wai dady abdul ne yace sai ya fitar da mashkhur waje karatu, kuma fa saura shekara daya mashkhur ya gama karatu, wai fa duk akan dukan da na baki labari mashkhur yayiwa wanan shegiyar ‘yar. Hmmm gaskiya yaya halima zan

Please Login or Register in order to submit comment