Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin mamaki maman zahra tace lallai ahmad amma bai ta6a gaya miki maman sa tana kama da ke ba, zahra cewa tai ee ya ta6a gayamin mana, amma abinda yasa ban kawo kice ba sabida yace min a kano gidan su yake, kuma kinga ke a kaduna kike.

Maman zahra cewa tai to tayaya kika son a kaduna nake, wani siririn murmushi zahra tai tare da cewa hmmm to ba a kaduna kika bawa hajiya kaka ni ba. Murmushi maman zahra tai tare cewa hakane amma nima ya ta6a gayamin da mukai waya yace yaga wata mai kama dani sak, to a Lokacin na bayar kice amma dana tambaye shi a ina ya ganki sai yace min wai russian, ni kuma sai nai tunanin 'yar qasar ya gani.

Kuma dama bai son zancan ba, nana ce dai kawai ta sani itama sai daga qarshe. Murmushi zahra tai tare da cewa hmm lallai kam da ya sani ai da zai iya gane ni kuwa. Haka dai zahra da maman ta sukai ta hira tun zahra bata iya magana sosai har ta fara sakin jiki ka d'an. Itama dai maman zahra bata da yawan surutu amma ganin zahra ne yasa take yawan yin magana.

Bayan sun gama cin abinci zahra miqewa tai tare da cewa bari na kai plate d'in qasa, kallan ta maman ta tai fuska sake tace saura kiqi dawowa, murmushi zahra tai tare da cewa zan dawo amma dai zani wajan yaya abdul na sake duba jikin sa. Murmushi maman zahra tai tare da cewa to sai kin dawo ina jiran ki karki dad'e daga haka zahra tace to ta fice daga d'akin hannu riqe da tire d'in abinci............

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing..................

Double..

Zahra tana fita ta sauka qasa ta kai plate d'in kicin sanan ta dawo sama direct d'akin ilham ta wuce tare da murd'a handel d'in qofar baki d'auke da sallam ta shige. Zahra tana shiga kamar yadda tai tunani haka ta samu Ilham d'in tana kwance a stakiyar bed ta wani lan kwashe murya tana waya, zahra ko ba'a gaya mata ba tasan da yaya ahmad take waya.

Kunna globe d'in room d'in zahra tai d'akin ya gauraye da haske harara ilham tai tare da cewa mayan naki ne koh?, zahra ta fad'a cikin siririyar murya yadda yaya ahamd bazai jiba ilham kuwa murmushi tai tare da cewa kwarai shine, yaya ahmad kasan wai mai zahra tace? Da sauri zahra ta fara qif tawa ilham ido alamun karta fad'a.

Amma kafin zahra ta farga taji ilham tace wai ta shigo taga ina waya wai sai tace mayan naki ne koh?. Murmushi ilham tai bayan ahamd ya bata amsa tace haka tace mana, zahra kinji wai yana tantama wai anya qanwar sace zata iya fad'ar hakan wlh hubby da gaske nake haka tace kullum ma haka take cewa.

Zahra kuwa hararar ilham tai tare da cewa ni kika tonawa asiri ko wlh sai naje na gayawa ammi ba ta hanaki wayar dare ba?. Zahra ta qasa maganar tana kama hanyar fita, duk a hankula zahra take maganar yadda ahmad bazai jiba. Ilham kuwa da sauri ta cewa ahmad ina zuwa zanki ra ka tana gama fad'i hakan ta kashe wayar tabi bayan zahra da sauri.

Tana cewa haba zahra ta zo kiji mana zo kiji, zahra kuwa dariya tai tare da takawa a kuje tana cewa ina ba wanan zanca wlh sai na fad'a. Itama ilham d'in a guje tabi bayan zahra tana mata magiya akan karta fad'a. Zahra tana zuwa qofar ko knocking ba tai ba ta tura da sauri duk dan ta sake rud'awa ilham ciki. Baki d'auki da sallam zahra ta shiga tana mai da nunfashi.

Ammi ta gani zaune ita da mashkhur ga dukkan alamu magana suke sai abdul baje akan bed yana sharar bacci. Cikin mamaki ammi tace zahra lafiya naga kamar an cillo ki? Kafin zahra ta kai da bawa ammi amsa itama ilham ta shigo da sauri baki d'auke da sallama tana mai da nunfashi. Murmushi ammi tai tare da cewa hmmm ai tinda naga ilham zance ya qare kuwa.

Mai kuka ai kata haka kuke guje-guje kamar marasa gaskiya. Zahra bud'e baki tai tana shirin magana ilham da sauri ta toshe mata baki tare da cewa ammi ba komai fa. Harar ta ammi tai tare da cewa duk yadda akayi ilham kece baki da gaskiya mai ya fari?. Zahra kuwa sai qoqarin cire bakin ta take daga hanun ilham amma ta kasa da yake dai ilham ta d'an fita qarfi.

Mashkhur daya zubawa zahra ido ji yayi kamar shi ilham ta rufewa baki, dan haka bai san sanda yace! Ke ilham meye baza ki sakar mata baki ba. Ilham tana jin hakan tai sauri ta sakarwa zahra baki sabida ita sam bata kula da yaya mashkhur d'in ba kamar yadda itama zahra hankali bai kai kan sa ba. Ba iya ilham ba har ammi tayi mamakin maganar da mashkhur yayi akan a sakarwa zahra baki shida in lamari ba ruwan sa bai fiya magana ba, musamamn ma na zahra.

Zahra kuwa da bakin ta yayi ja kamar tai kuka tace haba ilham bafa fad'a zanyi ba wasa nake miki shine kika riqe min baki haka?. Zahra ta qarasa maganar kamar za tai kuka, ammi kuwa cewa tai kai zahra daga wanan abun sai kiyi kuka sabida ragwanta ba dole kullum ta ringa raina ki ba kuma alhalin kice babba. Da sauri ilham tace kai ammi wai itace babba kwana nawa tabani kwana d'aya ne fa rak.

Wani kallo zahra ta watsawa ilham tare da cewa ee ai ko minti d'aya na baki na rigaki zuwa duniyar amma sabida baki da kunya kike min wanan abun. Murmushi ammi tai sabida yadda taga zahra tana maganar kamar wata babba shi kuma mashkhur sakin baki yayi yana kallon zahra sabida hakan da tai ba qaramin birge shi yake ba, gaba d'aya fad'an nasu ni shad'i yake bashi.

Ammi cewa tai to zahra mai zaki gayamin ta hanaki zo ki gayamin, murmushi zahra tai tare da kallan ilham, ilham marairaice fuska tai alamun karta fad'a. Zahra kuwa qarasawa wajan ammi tai tare da cewa bakomai dama zuwa nai na duba yaya abdul kuma gashi kamar naga yayi bacci, ya jikin na shi?. Ammi cewa tai masha Allah kinga yau jikin nashi yayi kyau ba kamar kullum ba da baya iya samun bacci amma yau gashi yayi bacci da wuri.

Murmushi zahra tai tare da cewa alhamdulillah in sha ALLAH ma zai samu sauqi gaba d'aya. ALLAH Yasa ko ma wuta da kukan nan da kikeyi ammi ta fad'a tana d'an hararar zahra, murmushi zahra tai tare da cewa hmmmm ammina kenan bazaki gane ba ina matuqar son yaya abdul fiye da kai na sam bana son wani abu ya same shi. Kafin ammi ta kai da bawa zahra amsa ilham ta qaraso tare da cewa au kina nufin kina son yaya abdul fiye dani?.

Murgud'a mata baki zahra tai tare da cewa tabb waya gaya miki ina son ki ne ai duk gidan nan kice ta qarshe a wadda nake so kina cin zalina kuma sai na so ki ko ammi zahra ta qarasa maganar tana kallan ammi. Murmushi ammi tai tare da girgiza kai tana cewa aaa ni ba ruwa na kunfi kusa karna shiga fad'an ku anjima ku bani kunya. Mashkhur da yake gefe kuwa ya cika yayi fam jin zahra tace tana son abdul fiye da kan ta.

Ilham kuwa cewa tai hmmm karki soni mana nima ai ba son ki nake ba kinga tafiya ta in kin gama ki koma wajan mama karki manta. Zahra kuwa cewa tai ki tafi kiga kina tafiya sai na gayawa ammi ki jira ni. Ilham kuwa dakatawa tai da tafiyar tana huro hanci alamun ta cika tai fam. Murmushi zahra tai tare da d'an yi mata gwalo, ammi kuwa cewa tai oh na manta kin baro mamanki maza kije ki koma wajan ta.

Zahra yamutsa fuska tai tare da cewa wai mama na nifa kice mama na ba ita ba. Murmushi ammi tai tare da cewa naji amma dai itama maman taki ce tashi kije kuma in kinji ki saki jikin ki kuyi hira sosai kamar dai dani kike tare. Ilham cewa tai inafa itama mama sai da tace bata da sauri sabo kai har qanan tama cewa sukai ko bata son yi musu magana ne.

Ammi cewa tai kai ilham banda sharri ina kika ga qanan zahra?. Murmushi ilham tai tare da cewa kai momy kinga qanan nata masha Allah video call mukayi da su, wayyo kyawawa harda wata mai bin zahra sunan ta nana kyakyswa tafi zahra kyau da qiba kai tama fita komai wama zai had'a ilham ta qarasa maganar cikin tsokana. Zahra harar ta tai tare da cewa qarya take ammi kwai dai dan ta ganta baqa ce shi yasa ta birge ta.

Oho koma dai mene tafiki sakin jiki da fuska kinje kinga yaran mutane sai wani had'e musu rai take ammi nasan wlh kin ma basu tsoro nuna miki ne kawai basuyi ba. Zahra kuwa kuka ta farayi tare da cewa kinga ta ko ammi kinajin abinda take cewa. Kafin ma ammi ta kai da yiwa ilham magana ilham ta fuce tace ammi sai da sake, ammi kuwa cewa tai kai zahra to mene na kuka ki rabu da ita da wasa nake.

Wlh ammi da gaske take zahra ta qarasa maganar tana zubar da hawaye mashkhur kuwa ji yayi kamar a zuciyar shi zahra take kukan amma harga ALLAH abun birge shi yake nan da nan wani mugun son zahra ya kama mashkhur. Ammi cewa tai kiyi haquri kinji qarya take nasan dai duk da bangan su ba amma 'ya ta ta fiso kyau ki dena yiwa ilham kuka maza ki share hawayan ki ki koma wajan mamakin.

Zahra kuwa wani kukan ta saki zuciya cike da jin haushin ilham, mashkhur kuwa da yaji ana rarrashin zahra akan ta koma wajan maman ta miqewa yayi tare da cewa ammi sai da safe daga haka ya fuce. Ammi kuwa da kyar ta iya samu ta rarrashi zahra har ta dena kuka ta miqe tayi mata sallama.

Zahra tana fita ta janyo qofar amma abin mamaki sai gani tai wajan yayi duwo alamun an kashe globe d'in mamaki ne ya kama zahra sosai tana tinanin waye da aikin nan ita dai raban da taga an kashe globe d'in barandar sama har ta manta komin dare kwana yake a kunne, nan da nan tsoro ya kama zahra dan bama sosai take gani ba na sai tin d'akin su ne kawai ba'a kashe ba shi yasa zahra take iya gani kad'an.

Zahra ciki tsoro ta qarasa wajan socket d'in globe d'in domin kunnawa. Tana d'ora hannu taji an riqe mata hannu gam, zahra cikin tsoro ta bud'e baki zatai ihu taji an rufe mata baki. Qoqarin kwacewa zahra tai amma sa kasa dan da tayi tunanin ilham ce amma yadda taji tana jan hanun ko motsi baya yi tasan ba hanun ilham bane ilham sam bata da wanan qarfi.

Lumshe ido zahra tai ta saki ajiyar zuciya saka makwan jin qamshi turaran mashkhur wanda take mutuwar so. Murmushi kuwa a hankula yace karki sake ki ihu anan, gyad'a kai zahra tai alamun to. Sakar mata baki mashkhur yayi tare da ruqo ugunta ta baya yana juyo da ita wajan fuskar sa yadda zasuyi faces d'in jina.

Juyowa zahra tai tare da cewa menene haka yaya mashkhur yau kuma dame kazo mai zaka cemin?. Kallan ta mashkhur yayi tare da cewa da missing d'in ki nazo, zaro ido zahra tai alamun mamaki cikin mamaki tace missing d'in kuma wa ni na isa kawai ka gayamin mai ya kawo ka. Sassauta murya mashkhur yayi tare da cewa au baki yarda ba da gaske nake fa wai ke kina nufin baki missing d'in na kamar yadda nai missing ki ba.

Yau kimani 6 days fa rabo na dana saki a ido na wataran ma bana ganin ko ina nan ba kamar dai a can russian da kullum sai na gan ki ba. Ya mutsa fuska zahra tai sanan tace tab mai zanyi missing a tattare da kai yaya mashkhur hantara ta ko kyarata ko barazana ko punishment d'in da kake bani au ni dad'i ma naji wlh zahra ta qarasa magar tana zubawa mashkhur ido.

Oh iya abinda kika iya tinawa kenan koh? Mashkhur ya fad'a yana sake ruqo zahra ta baya. Ni sake ni ai kai ma kasan muguntar da yawa ba komai zai iya tinawa ba sai a hankula. To naji kin tina sharri saura alkhairi dama ance in mutum ya fad'i sharrin d'an uwansa sai ya riga tinawa da alkhairi ko?.

Zahra cewa tai hakane amma in mutum ya ta6a aikata ma alkhairi ba ai kai baka ta6ayi ba shi yasa nace hakan, zahra ta qarasa maganar tana qoqarin janye hannayan mashkhur daga ugun ta. Haba zahra ta ki tina mana ko saud'aya ne mashkhur ya fad'a cikin siririyar murya. Zahra lumshe ido tai ta bud'e sabida tinda take bata ta6a jin mashkhur ya kira sunan ta ba sai yau.

Kai ko ya ta6a kira bai ta6a kiran shi cikin nutsuwa da dad'in rai da dad'in murya da kwanciyar hankali irin na yau ba. Zahra kafin ta kai da magana taji cikin kasalaliyar murya mashkhur yace to kin tina last night d'in mu da mukayi a russian nida ke a bedroom d'in ki. Da sauri zahra ta girgiza kai sanan tace ban tina ba kuma bazan ta6a tinawa ba.

Sabida mai zakice haka zahra ko bakiji dad'in ba ne ki gaya mun gaskiya. Zahra ji tai jikin ta ya fara mutuwa sabida ta fara tina abinda ya faru a lokacin, kuma ga muryar mashkhur tana sake kashe mata ilahirin jikin ta. Amma zahra sai ta daure tace ni bawani dad'i kai ni ban ma tina mai ya faru a daran ba kuma bazan ta6a tinawa ba, tinda ni ba 'yar iska bace.

Murmushi mashkhur yayi tare da sake janyo zahra jikin sa yana shafa hips d'in ta da suka cika fam masha ALLAH yana cewa kin manta ko?. Cikin wata irin kasalaliyar murya mashkhur yace tom shikenan yanzu zan tina miki komai tinda kin manta ya qarasa maganar yaja zura hanunsa ta qasan rigar zahra da yake riga da siket ne a jikin ta.

A hankula mashkhur ya fara shafawa zahra gefan ciki tare da tura d'an yatsan sa cikin cibiyar ta. Wata siririyar qara zahra ta saki tare da cewa dan Allah ka rabi dani. Mashkhur cewa yayi bazan rabu da ke ba har sai kin cemin kin tina abinda ya faru. Wlh bazan tina ba kawai ka rabu dani, ni wlh bana son wanan iskanci ni ka dena ta6ani. Haba zahra iskanci fa kikaci nifa mijin ki ne mashkhur ya fad'a cikin siririyar murya, yana qara shafa lallausan cikin zahra.

Zahra kuwa cewa tai ba wani miji kai da zaka sake ni, ni na gaji da auran nan kawai ka sake ni na wuta. Mashkhur ji yayi kamar zahra ta watsa mai garwashi a zuciyar shi amma a fili sai ya daure yace haba zahra ki dena d'aga murya ko so kike a jimune?. Ee ai gwara a jimu kowa yasan iskancin da kake min, mashkhur kuwa cewa yayi to bari na tina miki abinda ya faru last night d'in mu a russian mashkhur ya qarasa maganar yana janyo zahra tare da had'e bakin su waje d'aya fara aika mata da hote kiss...............

Mu had'e a next page.



ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing...........

*page 109*


Da qarfi zahra ta fara qoqarin ture mashkhur baya sabida sam bataso wani abu makamanci haka ya sake shiga tsakanin ta da mashkhur d'in. Amma zahra da ta tura mashkhur mai makwan yayi baya sai ya sake ruqota da qarfin gaske kamar zai mayar da ita ciki. Haka zahra tanaji tana gani mashkhur yake kissing d'in bakin ta ga exchange d'in nunfashi da suke.

Nan da nan jikin zahra ya mutu murus ko kwakwaran motsi bata iya yi ga hugging d'in da mashkhur yayi mata bana wasa ba. Abu dai yaqi ci yaqi cinyewa tin zahra tana iya daure hote kisses d'in da mashkhur yake kai mata har ta gaza daurewa itama ta fara mai da mai da reply. Kafin wasu d'an lokaci mashkhur da zahra jiki yayi laqas duk sun had'u sunyi gumi.

Gashi sun gaza dena mayataccan kisses da sukewa junan su yadda kasan zasu cinye bakin juna kowa dai nuna maitar sa yake a fili. To fa abu yaqi ci yaqi cinyewa dan yanzu mashkhur da zahra sun d'au 35 minutes a wanan halin sam basa ji basa gani dan idanuwan su ma a rufe suke gam. Ana cikin haka ammi ta murd'a handel d'in qofar ta ta fito.

Ammi tayi mamakin ganin barandar da duwo duk an kashe globs d'in saura na qofar d'akin su ilham kad'ai. Haka dai ammi ta sauka ta shiga kicin, domin had'a tea, dan sam ji take yau ta kasa bacci sabida abinda ya faru, tana mamakin irin mugun hali na momy. 6angar mashkhur da zahra kuwa sam basu ji qarar futowar ammi ba sabida sunyi nisa a harkar.

Ammi tana dawowa sama bata tsaya ko ina ba sai wajan kunna globs d'in barandar sama. Ammi tun kafin ta kai da qarasawa wa tafara jin sautin kisses da wani mayataccan nunfarfashi yana tashi a wajan. Abun ya d'an bawa ammi tsoro sabida har time d'in bata gama tantace su waye a wajan ba. Dan haka sawa zuciyar ta jarumta tai tasa hannu ta fara kunna globs d'in.

Ammi tana kunna gud'a d'aya tun kafin ta qarasa kunna ragowar ta gane mashkhur da ne zahra a wajan. Da sauri ammi ta d'an ja baya dan gani take kamar idon ta gizo yake mata. Mashkhur da zahra ta gani sunbi sun qanqame junan su kamar zasu mayar da juna ciki. Ga bakunan su a cikin na juna suna yin wani kisses mai ta da hankalin junan su. Ko wanne yana sha da tsotsar bakin d'an uwan sa kamar zai cinye.

Ammi kuwa sake riqe cup d'in hanunta tai gam sabida jin yana bara zanar fad'uwa. Har time d'in zahra da mashkhur basu san ammi tana wajan ba, da sauri ammi ta kashe glob d'in data kunna tare da juya cikin tsantsar mamaki. Amma sabida tsabar su mashkhur sunyi nisa a wata duniyar ko qarar kashe glob d'in basuji ba.

Ammi Tana qarasawa qofar bedroom d'in ta cup d'in hanunta ya su6uce ya fad'i qasa wanwar. Qarar fad'uwar cup d'in ne ya dawo da zahra da mashkhur daga cikin hayyacin su. Ammi kuwa ko takan cup d'in da ya fashe batabi ba ta shige d'akin ta, sabida abinda idon ta ya gane mata ya rud'a ta kuma ya bata mamaki.

Da sauri suka saki juna suka juyo domin ganin mai ke faruwa. Suna jiyowa suga ammi ta shige d'aki da sauri tare da rufo qofar, ga cup d'in tea a fashe a wajan ko ta kansa bata bi ba. Cikin rawar baki zahra tace innalillahi na shiga uku, mashkhur kuwa kawar da idan sa yayi daga kan cup d'in yana tinanin har yaushe ammi ta futo basu ankare ba.

Hankalin zahra in yayi dubu ya tashi tana tinanin mai ya kai ta d'an yan aikin nan har ammi ta Kamasu. Wata zuciyar tace mata ai shi ya jaza miki, a hankula mashkhur ya ruqo hanun zahra tare da cewa daga wanan d'an abun duk kin bi kin tayar da hankalin ki zo mu cigaba ni wlh bai ishe ni ba ko bedroom d'ina zamu tafi. Cikin zafin zuciya zahra ta fincike hanun ta tare da cewa ban sani ba ai duk kai kajefani a cikin matsala.

Wani wahalallan murmushi mai cike da muguwar sha'awa ya saki tare da cewa to menene dan ta gan mu a hakan haramun ne. Cikin mamaki zahra tace lallai to in kai ka saba iskanci an kama ka ni ban saba ba, kawai ina zaman zama na kazo ka jazamin kuma wlh ka sani gobe-goben nan zanje na gayawa dady na gaji da auran nan wlh sai ka sake ni, dan na gaji da iskanci nan da kake min. zahra ta qarasa maganar tana jan tsaki tare da wucewa daga wajan a firgi ce.

Mashkhur yana son riqo zahra amma ya kasa, sabida jikin sa duk ya mutu, itama zahra da kyar take iya tafiya ita kad'ai tasan abinda takeji a jikin ta, dan mashkhur ya gama tayar mata da kololuwar sha'awar ta, kawai daurewa take yi. Zahra tana zuwa qofar d'akin su ta murd'a handel ta shige sabida tasan kafin ta qarasa bedroom d'in da aka sauke mamanta mashkhur ya ruqo ta kuma ma bazata iya zuwa wajan maman tata a haka ba.

Zahra tana shiga ta rufo qofar harda qarawa da key. Tana gama rufe d'akin ta koma kan bed ta zauna tana mayar da nunfashi, ilham da take zaune a gefe tana chat da ahmad da sauri ta ajiye wayar tana cewa lallai zahra bazaki koma wajan maman ba kika dawo nan?. Shiru zahra tai ba amsa, ilham gani tai zahra duk ta had'a wani gumi tana mai da nunfashi idanuwan ta sun canza launi sun d'an yi ja kad'an.

Cikin mamaki ilham tace zahra lafiya kuwa mai yake faruwa. Da kyar zahra ta iya cewa ba komai ilham. Shiru ilham tai tana qarewa zahra kallo cikin mamaki tace kamar ya ba komai zahra, kinga ki fa gaba d'aya kin canza mai ya faru. Shiru zahra tai ba amsa, da ilham ta ishi zahra da tambaya miqewa zahra tai ta shige toilet abin ta.

Mamaki ya kama ilham sosai duk yadda ta kai da tinanin mai yake damun zahra ta kasa ganewa sabida bata ta6a ganin ta a wanan halin ba. Zahra kuwa tana shiga toilet ta sa mai key, sai da ta zauna ta mai da nunfashi ta wuta sosai ta gama dawowa hayyacin ta sanan ta fara qoqarin cire kayan ta domin yin wanka. Bayan ta gama wanka starki ta sake wani saban wanka na soso da sabulo sanan ta futo d'aure da toilet.

zahra ilham ta hanga a zaune ta kunna globs d'in d'akin ta zauna jigum tana tinani. Zahra ciki basarwa da zancan tace to ilham har kin gama waya da mayan naki? Cikin tuwuma ilham tace ba wanan na tambaye ki ba zahra naga ki dazu a wani yaniyi mai yake damun ki. Qarasawa bakin kwaba zahra tai tare da cewa ba komai fa, cikin rashin gamsuwa ilham tace ban yarda ba.

Tsaki zahra taja tare da cewa to uwa ta sai ki shaqe ni kiji gaskiyar tinda baki yarda ba. Wani kallon mamaki ilham ta zubawa zahra tana mamakin lokaci guda yadda zahra ta canza daga mai sanyi zuwa mai fad'a. Har cikin zuciyar ta ilham bataji dad'in abinda zahra tai mata ba amma sai itama ta basar ta juya ta kwanta abinta kamar mai bacci

Please Login or Register in order to submit comment