Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi karatu a waja ba itama nata bazai yiba. Wata uwar dariya suka saki a tare. Sanan momy ta d'ora da cewa wlh yau sai nayimiki kyautar dubu d'ari saratu sabida kin faranta min rai.



Kaii yaya halima godiya nake ALLAH yabar zumunci. Bakomai bari nayi miki transpar yanzu. Ok yaya halima ngd. Bayan momy da ammi sunyi sallam, ba 6ata lokaci ta turawa saratu dubu d'ari kamar yarda tai mata alqawari. Momy ko sallah batayi ba ta wuce part d'in su abdul majid.



Typing........



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYARO💜❤💜



*free book*💜❤💜



*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yimuku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin nan na ADALILINTA.



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment........... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa...........💜❤💜



Typing.........



ADALILINTA💜❤💜



AMINA BAYARO💜❤💜



*Page 6*

Ko sallah batai ba ta wuce part d'in su Abdul majid........



ABDUL MAJID.........

A daddafe ya iya hawa kan bed. Tinda ya abdul ya haukan bed ko kwakwaran motsi ya kasa yi zuciyarsa kuwa a guje take bugawa. Fat fat, sai mai da nunfashi yake sai da yafi minti goma a haka.



Can wasu zafafan hawaye ya fara gangarowa abdul. Yanzu shikenan na rasa zahra, wlh dady ni na dace da zahra ba yaya mashkhur ba. Yaya mashkhur mugune zai zalintar min zahrata, zai iya KASHEMIN zahrata baya santa.



Dady bai kyauta ba, bai zab'awa zahra mutumin ARZIKIBA. Zahra bata cancanci haka daga wajan dady ba, abdul ya qarasa maganar tausayin zahra yana ratsa zuciyar sa.



Nan da nan wasu zafafan hawaye suka fara zubowa abdul daga idanuwan sa. Yana tausayawa zahransa kuma yana tausayawa kansa, sabida yanzu shi ya gane rayuwarsa ba zahra bata da wani amfani.



Abdul yana jin kiran sallah amma ina ya kasa wani kwakwaran motsi. Yana son tashi amma ya kasa duk son abdul da yin sallah kuwa. Dama shi abdul majid baya bari sallah ko wata ibadar ta wuce shi.

Abdul yafin 20 minti a cikin wanan halin
Yana cikin wannan halin yaji ana knocking d'in qofar. Amma ina ko motsi ya kasa yi bare magana. Ai kuwa kawai yaji an bud'e qofar, dama qofar a bud'e take, momy ce ta shigo cikin bedroom d'in.



Tana shigowa kuwa taga abdul majid yana nunfashi sama-sama ga hawaye yana gangarowa shab'e-shab'e daga idanuwan sa. da sauri momy ta qarasa hankali a tashe, tare da cewa haba abdul.



Mai kake yi haka eeyeeh? Amma abdul ina bai masan tanayi ba dan a halin yanzu ya fara fita daga hayyacin sa. Duk nasan ADALILINTA ne ka shiga wannan halin, wai abdul mai ka gani a jikin wanan banzar yarinyar nan ne?

ADALILINTA yanzu kashiga halin nan? Ko so kake ka kashe kan kane sabida ita? Tayi mana asararka a banza a hofi, abdul majid kuwa ina har lokacin bai san abida momy take fad'a ba dan dishi-dishi ma yake kallon ta. Ai kuwa momy tana ganin haka ta fuce a gigice.

Tana futa ta nufi part d'inta, tana shiga ta haye sama ta shiga bedroom d'in ta sanan d'auki wayarta a hanzarce ce t tai daily d'in number family doctor d'in gidan su. Ai kuwa akaci sa'a bugu uku ya d'auka.



Sallama momy tayi kafin tace yauwa doctor dan ALLAH kana ina yanzu ko kana asibiti ne? Eh to yanzu de ban dad'e da fitowa daga asibiti ina kan hanya amma dai lafiya ko?. Wlh doctor abdul ne bashi da lafiya.



Subhananlahi mai ya same shi?. Wlh doctor nima ban sani ba,. Ok ganinan zuwa yanzu zan qaraso na duba shi doctor yana gama fad'in hakan ya kashe wayar. Momy kuwa ajiye wayar tai, sanan ta wuce 6angaran dady domin gaya mai meke faruwa.



DADY.........

Yana fita part d'insa ya wuce zuciya a cun kushe. Yana shiga ya zauna ya rafka uban tagumi. Sabida shima har ga ALLAH basan had'in auran nan yake ba kawai biyayyace.



Ko a mafarki dady bai tab'a tinanin bawa mashkhur zahra ba. Ya fiso ace ya aurar da zahra ga wanda take so kuma mutumin kirki. Ko kuma ya bawa abdul ita.



Sabida abdul majid shi ya dace ya auri zahara. Kuma yasan har ga ALLAH zai iya riqeta amana ko bayan ransa. Sabida yasan abdul tsakani da ALLAH yake son zahra.



Tun tana yarinya abdul yake bata KULAWA sakama kwan mashkhur da yake nuna mataqa zahra TSANA da zalinci qarara a fili. Shi kansa dady yasan mashkhur bai dace da zahra ba kwata-kwata.



Dady yana cikin tinanin nan yaji kiran sallah. Miqewa dady yayi da kayar ya shiga toilet ya d'aura al wala, sanan ya fita domin zuwa masllaci yayi sallaj. Dady Yana fita daga part d'insa yaci karo da hajiya kaka. Hajiya lpy? Hajiya kaka cewa tai dama inaso muyi magana ne? ok bari na dawo daga masallaci ko?.



Ai dama maganar ba wata mai tsayi bace, dama so nake a d'aura auran, nan da q'arshan watan nan, in mai sunan malam zai koma ya TAFI da ZAHARA. Gaban dady yankewa yayi ya fad'i rada rasss.



Amma ya dake yayi ta maza tare da cewa tom hajiya inasha ALLAH za' ai hakan. Dady yana fad'in hakan ya wuce massalacin gidan zuciya cike da zullumi. Da yake massallacin dady ne ya gina shi a kusa da gidan.



Dady yana idar da sallah ya koma part d'insa ya zauna, Tare da tinani kala-kala. Ko minti uku bai yi da zama ba yaji a'na qoqarin bud'e qofa. Da sauri dady ya d'aga ido dan ganin waye haka yake qoqarin shigowa ba neman izini. Momy dady ya gani ta shigo a gigice..............



Typing........



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYERO💜❤💜



*free book*💜❤💜



*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. In yimuku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH In kun karanta ku d'infa comment........... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa..........💜❤💜

Game buqatar a sashi a group d’in littafin ADALILINTA Sai yayi min magana ta wanna number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. Kuma FREE BOOK ne ba na kud’i ba. New book in kuka karanta sai kuyi share zuwa wasu groups d’in pls............

New book on 2023.
[11/06, 22:23] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤💜



AMINA BAYARO💜❤💜



*page 7*

Momy dady ya ganu ta shigo a gigice.......



Kallanta yayi tare da cewa lafiya kika halima shigo ko sallama babu?. Dadyn abdul wallahi abdul ne bashi da lafiya, dady kuwa a tsorace yace mai yake damun sa? Momy girgiza kai tai tare da cewa nima ban san meke damun sa ba amma na kirawo doctor habib yana hanya.

Dady tashi yayi da sauri tare da yace ok muje naga jikin nasa.
Momy da dady Suna fita suka nufi part d'in su mashkhur. Suna isa suka shiga d'akin abdul. Ai kuwa dady ya tsorata da ganin halin da abdul yaka ciki, dady yana mamaki yarda lokaci guda abdul ya koma haka.



Ana cikin haka sai ga doctor hanbib ya qaraso. Yana zuwa ba 6ata lokaci ya fara duba abdul sosai, kuma bai sha wahala ba ya gane damuwace kawai take damunsa. Rubuta mai allurori da magani da kuma drip da za'a qara mai dactor yayi.



Nan da nan dady ya bawa haidar list d'in magunan da alluran da doctor ya rubuta wa abdul d'in, domin ya siyo. Cikin 'yan mintina haidar ya dawo ' da yake basu da nisa da pharmacy d'in. Yana kawowa babu b'ata lokaci doctor ya fara yiwa abdul treatment

Sai da doctor yayi wajan 20 minutes akan abdul ya dawo dai-dai. Ba jimawa bacci mai nauyi ya kwasheshi abdul. Momy kallan doctor tai tare da cewa doctor mai ke damun abdul ne?



Momy tana rufe bakinta sai ga ammi hankali a tsahe ta shigo bedroom d'in. Tana qarsowa tace yajikin abdul d'in? yanzu haidar yake gayamin bashi da lpy ashe. momy amsawa tai a daqile ehh da sauqi.



Ammi ta qarasawa tai gefen abdul ta zauna sanan tace to wai mai yake damunsa?
Doctor habib cewa yayi! ehh to damuwace da yawan tunani kwai, ya kamata ya raqe damuwa da tinani, dan basu da amfani ga lafiyar d'an adam.



Momy ko ba'a fad'a mataba tasan akan zahra abdul yake cikin wannan lalin nan.
Dady da ammi kuwa sunyi mamakin jin hakan. Ammi tinani take ko akan za'a aurawa zahra mashkhur ne, yana farga bar zalincin da yayan mashkhur zai matane!?.

Shima dady abinda yake tinani kenan. Daga dady har ammi ba wanda yayi tinanin ko ya kawo son zahra ne ya jefa abdul a wannan halin.



MARSHKHUR..........

Bashi ya dawo gidan ba sai yamma li'qis. Yana dawowa ana kiran sallar magariba. A hanzarce ya futo daga motar hannun sa ya sha d'inki da bandeji ya kumbura suntum yayi jajawur duk da ba mashkhur ba wani fari bane sosai kall.

Amma yana da haske, gasken fa fayau ba dan bai kai sauran qannan nasa gasken tafa ba. Mashkhur ko ciki bai samu damar shiga ba a farfajiyar gidan ya d'aura alwala cikin dabara yarda bazai jiqa cuwan nasa ba.



Yana gamawa ya nufi masallaci domin yin sallah. Mashkhur bai bari dady ya kula da ciwan da ke hanun sa ba. Dady a sawun gaba yayi sallah shida su faruq. shikuma mashkhur a sawun baya yayi tasa sallah shi yasama su dady kula da shi ba.



Mashkhur yana idar da sallah bayan yayi lazimi ya fuce daga masllacin.
Yana fiya ya shige gida, bayan ya shiga gida part d'in su huce zauciya cike da takaici, mashkhur yana shiga part d'in su ya wuce room d'insa.



Yana shiga ba 6ata lokaci ya rage kayan jikinsa bayan ya gama ya wucd toilet domin watsa watsa ruwa.
Bayan mashkhur ya futo daga toilet kaya ya saka, t-shirt da three kwata. Sannan ya haye kan bed, ya d'auki wayarsa da hannu mara ciwo.



Mashkhur yana dubawa wayarsa yaga 10 missed calls. Guda takwas zee ce biyu kuma AHMAD. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kiran number ahmad d'in, bugu biyu ahmad ya d'auka baki d'auke sallam.



Mashkhur amsawa yayi, murya a shaqe, wa'alai'kassalam. Ahmad ne ya fara magana kamar haka!. Ahhh BIG MAN ya najika muryar ka tayi wani sanyi, kuma nakira kaqi piking ko baka da lpy ne?
Kai dai bari vro ina cikin tashin hankali.

Ahmad cewa yayi big man mai ya faru haka ko baka da lafya ne .
Ai gwara larurar mah da abidda ya sameni.
Toh me ya sameka hakane?



Nan mashkhur ya bawa ahmad labari abinda ya faru, duk da mashkhur mai zurfin ciki ne amma wanan karon sai ya tsinci kan sa da fad'awa ahmad abinda ke damun sa sanida tsabar tshin hankali da baqin ciki.

Ahmad kuwa murmushi najin dad'i yayi dan ya tabbatar ko ba'a fad'a mai ba, abinda yaje yaje ya fad'awa dady ne akan mashkhur yasa aka d'auki wannan matakin akan mashkhur.



Sai da Ahmad ya nunfasa sannan yace haba big man ai wannan abin farin cikine a garemu.
Mashkhur kuwa wani dogwan tsaki yaja tare da cewa haba ahmad hala bakasan wace zahra ba ko?



Ee ahmad yace bansan taba amma tabbas nasan su dady bazasu yima zab'an tumin dare ba. Wani dogwan stoki mashkhur yaja a karo na biyu tare da katse wayar, yana qatsewa ya kashe wayar gaba d'aya.............



Typing...........



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYRO💜❤💜



*Free book*💜❤💜



*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yimuku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment.......... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.........💜❤💜



Typing.........



ADALILINTA💜❤❤



AMINA BAYARO💜❤💜



*Page 8*

Yana katsewa ya kashe wayar gaba d'ata...........



Wani baqin ciki ne ya sake turniqe marshkhur. Yana ta juyi akan bed yana qarewa zahra zagi.

Can yaji kiran sallah i'sha, jiki a sanyaye ya shiga toilet ya d'auro alwala. Yana futowa ya shifid'a dadduma.



Dan a ganinsa bazai iya fita massalaciba.

A daki yayi sallarsa.

Bayan ya idar yaji wata uwar yunwa ta turni qeshi sabida rabansa da abinci tun breaker fast.



Firij ya nufa ya bud'e ya dakko fresh Malik mai sanyi yasha. Yana sha yana yatsuna fuska kamar wandda akayiwa dole. Rabi yasha sannan ya d'akko coca cola ya sha sai da ya sha kwata sannan ya ajiye.



Ya nufi wata qaramar durowa ya bud'e ya dakko maganin mura na manya, Ya dawo indda ya ajiye Coca Cola, ya bud'e murfin maganin mura ya juye a cikin coc d'in. Ya rufe jarkar da murfi ya jijjiga.



Sannan ya bud'e a hankula yadda gas d'in bazai fitaba. D'aga jarkar yayi ya kai bakinsa. bai sauke jarkar ba sai da ya shanye tass.

Bayan haka ya had'a da kwayoyin maye guda biyu. Ai ko minti biyar bai yiba bacci mai nauyi ya kwashe shi.............



ZAHRA..........

kuka take cikin dashashiyar muryar da ba mai jinta sai dai in mutum yana kusa da ita. Ilham kuwa kukan Zahra yana ci mata rai sosai, da yake daga ita sai ilham a bedroom d'in.



Ilham tashi tai ta canza hasken bedroom d'in daga light zuwa white. d'akin kuwa ya gauraye da haske ta koma kusa da zahra da take kwance tana kuka. Tare da cewa haba zahra ya kamata ki dena kukan nan haka.

Yanzufa qarfe biyun dare fa saura haba zahra.



Tashi zahra tai daga kwanciyar da tai tare da share hawaye, Tana cewa ilham in banyi kuka ba mai zanyi? Ilham tace haquri zakiyi tindda mai afkuwa ta afku bamu da wata mafita da ta wuce addu'a.



Zahra shiru tai da alamu tinani take yi. Can zahra ta kalli ilham tana cewa yauwa na tuno wata shawarar. Ilham ta kalli zahra da sauri tana cewa wata shawarar?

Zahra ta nunfasa tace abidda za'ai yanzu



Zanje na samu hajiya kaka nace mata banasan auran nan ta gayawa dady a fasa tindda dady yana jin maganar ta, ta qarasa maganar tana zubawa ilham ido.



Ilham kuwa jinjina kai tai tana cewa haba zahra waya gaya miki ba da amincewar hajiya kaka aka had'a auranan ba?. Ke barima kiji ni zargi nake ma itace tasa dady ya had'a auran.



A firgice zahra tace haba ilham da gaske kike? Ilham tace kwarai ma kuwa. Ai tana qarasa maganar taga zahra ta miqe a firgice tayi hanyar fita daga bedroom d'in. Kafin ilham tai kwakwaran motsi ai tini zahra ta fice.



Ilham da sauri tabi bayanta tana cewa ina zaki da tsakar daran nan?

Zahra kuwa ko kallanta batai ba ta cigaba da tafiyar ta. Tana zuwa qofar fita daga part d'in, tafara qoqarin bud'e qofar.



Ilham tai saurin riqe hannun zahra tana cewa haba sis ina zakine wai da tsakar daran nan?. Zahra tace wajan hajiya kaka zani mana. Tana gama fad'in hakan ta gama bud'e qofar ta fice.



Ilham rufe qofar tayi sannan tabi bayan ta tana cewa haba zahra ki bari sai gobe mana dare yayi fa. Amma zahra ko kallan ta batai ba bare ma tasa ran zata tsaya. Zahra bata tsaya ba har sai da ta isa part d'in hajiya kaka.



Tana isa ta fara buqa qofar part d'in yadda hajiya kaka zataji.

Hajiya kaka tana zaune ta idar da sallah lafila kenan taji bugun zahra. Meqewa tai cikin mamakin waye haka da tsakar dare tana duba agogo.



Alokacin qarfe biyu na dare. Qarasawa bakin qofar tayi tare da cewa waye? Zahra cikin muryar kuka tace nice, hajiya kaka tanajin muryar ta gane mai magana duk da kuwa maryar ta dashe.



A hanzarce ta qarasa ta bud'e kofar. Tana bud'ewa taga zahra da ilham a tsaye, zahra kuwa idanta ya kubbura yayi jajjaaur abinka da farar fata. Hajiya kaka matsawa tai dan basu hanyar shugowa.



Tana matsawa zahra ta shiga ilham tana biye da ita. Suna gama shugowa hajiya kaka ta rufo qofar. Tana gama rifewa ta mai da kallanta wajan da zahra da take tsaye kamar wandda aka dasa.



shalelena lpy kuka futo cikin tsowan daran nan cewar hjy kaka?. Zahra kuwa kuka ne ya sake b'alle mata cikin muryar kuka tace kakata laifin mai nayi miki haka? Ko kin dena so nane?..................




Typing.............



"ADALILINTA"💜❤💜



BY AMINA BAYERO💜❤💜



*free book*💜❤💜



*Ina godiya da masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤💜



*Dan ALLAH in kun karanta ku d'inga comment........... pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.💜❤💜


*ga masu buqatar a sasu a group d’in ADALILINTA sai suyimin magana ta wannan number WhtsApp kawai bandda kira. Free book
ne bana kud’i ba.



Typing.....

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

FREE book.



*page 9*

Kakata laifin mai nayi miki haka? Ko kin dena so nane............



Hajiya kaka kuwa cikin mamaki tace haba shalelena mai zai sa na dena sanki? Karfa ki manta kece farin cikin rayuwata fa.

Zahra ta sake rushewa da kuka mai cin rai tare da zaman dirshan a qasa tana cewa,



Kakata mai yasa kika had'a aurena da yaya mashkhur? Kaka kud'e wani laifi nai miki ne zaki hukun tani da auran yaya mashkhur ne? Ta qarasa maganar cikin kuka mai sauti. Hajiya kaka kuwa jiki ba kwari ta tsuguna a gabanta.



Tana cewa haba zahra kinsan ai bazan tab'a yin abidda zai cuceki ba, kuma wlh da manufa mai kyau na had'a auran nan. Zahra ta zaro manyan idanuwanta tace wace manufa kenan?



Hajiya kaka tace da manufa kala-kala zan gya miki amma ba yanzuba. Zahra kuwa wani saban kuka ta saki, ilham kuwa si faman bata haquri take.

Da kyar hajiya kaka da ilham suka bawa zahra baki ta dena kukan.



Amma duk da hakan zuciyar zahra batayi sanyiba. Jiki ba kwari ta tashi ta nufi toilet d'in kaka dan d'auro alwala. Tana futowa ta zura hijab d'in kaka dama dadduma a shinfid'e taka, ta fara lafulfinu.

Tana kai wa ALLAH kukanta akan batin auran ta ita da yaya mashkhur.



Ba ita ta idar da sallahr ba har sai da taji an fara kiraye-kiyarn sallahr asuba. Tashin ilham tai da hajiya kaka dan yin sallahr asubayi.

Bayan ta idar da sallar asubayi wani bacci mai nauyi ya kwasheta...........



ABDUL MAJID.

Bashi ya tashiba sai kiran sallahr asubar fari. Yana tashi ya ga hannunsa yasha laidar qarin ruwa. Abin ya bashi mamaki sosaii a hankula ya zare allurar sannan ya d'aga kai dan kallan qarfe nawa. Wajan biyar saura ya gani.



Shi a tinaninsa ma biyar d'in yamma ce sai da ya duba wayarsa sannan ya gane ta asubace. Salati yayi jiki ba kwari ya nufi hanyar toilet. Alwala yayi sanna ya futo. Yana fitowa ya fara rama sallolin da ake binsa.



Yana idarwa yayi lazimi. Ji yayi zuciyarsa ba dad'i saka makwan zancan da dady yayi ne ya faradawo mai arai. Komai ya fara dawo mai tiryan-tiryan. Haka yay ta tunani kala-kala, ana cikin haka yaji kiran sallah alamun an tayar.



Da kyar ya tashi jiki yana rawa ya fara bin sallahr, dan a halin da yake ciki bazai iya fita massallaci ba.

Bayan ya idar ya koma kan bed zuciya ba dad'i haka dai bacci ya sake awan gaba da shi............



MURSKHUR.............

Marshkhur kuwa bashi ya tashi ba sai da asubayi, sakamakwan kiran sallar da yaji shine ya tada shi. Haka ya tashi jiki ba kwari. Janyo wayarsa yayi ya kunna ta.



Sannan ya kunna data. Yana kunna data Ko minti biyar baiyi ba ya sai ticket d'in airplane. Jirgin qarfe takwas zai bi, dan shi gani yake in bai koma RASHA ba yau bazai samu sukuni ba. Kuma ya d'au alwashin inde ya koma bazai dawo ba har sai an janye batin auran sa da zahra.



Yana gama siya ya nufi toilet ya d’aura alwala, ya nufi massallaci. Bayan an idar da sallah ya da wo.

Yana dawowa ya fara had'a kayansa da zai biqata a cikin trolley. Yana gama had'awa tsaf ya shiga toilet yayi wanka.



Ai kuwa cikin rashin sa'a ya fama Ciwon hannun sa. A daddafe ya futo daga toilet d'in cikin azaba da rad'ad'i. Zama yayi akan bed sai da ya d'auki tsawan minti goma a zaune yana hutawa.



Can yayi ta maza ya daure ya fara shiryawa. Yana gama shirya wa ya d'ora ruwan zafi ha hita. Bayan ya tafasa ya zufa a cup ya had'a shayi mai kauri, ya had 'a da cake ya fara ci.



bayan ya gama ci ya fara shan magun guna da doctor ya bashi.

wajan qarfe bakwai na safe ya gama shiryawa, sanna ya kama hanyar fita daga part d'in....



In ka cire zahra abdul majid marshkhur Kowa ya hallara a babban falan gidan akan draining table domin yin breaker fast.

Itama ilham ta futo domin d'ibar musu abinci da za su karya ita da zahra.



Rukkayya, rumaisa, amir, duk sun sha uniform d'in school. Suma su haidar da faruq sun shirya domin tafiya makarnta university. B. U. K. Dady ne ya kalli ilham da take d'iban dankalin turawa, tare da cewa ke ina uniform d'in naki kuma ina mamana take?



Ilham tace zahra bata jin dad'i baza ta samu damar zuwa ba.

dady ya nunfasa yace to ke sabida mai baki shirya ba ko kema ba zakiba?

ilham tai shuru dan batasan amasar da zata bawa dady ba.



Rukkayya kuwa cewa tai tindda 'yar gwal d'inta bazata ba ai itama baza taba. rumaisa ta qarb’e zancan da cewa dady ai in zahra bazata makaran taba itama ilham bata zuwa. kafin dady yayi magana sukaji sallama..........

Typing............


ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*FREE BOOK💜❤️💜

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA. Ina muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan ALLAH In kun karanta ku ringa comment......pls sabida hakan shi zai bani qarfin guwai cigaba da rubutawa💜❤️💜

Gamai buqatar littafin ADALILINTA sai yayi min magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. Free book ne bana kud’i ba.

Now book on 2023.
[11/06, 22:23] Maman Xuhra: Typing..........
“AALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Page 10*

Kafin dady yayi magana sukaji sallama..........


mashkhur ne yayi sallam cikin qananin kaya tabbas yayi kyau sosai abinka da kyakyawa , hannunsa janye da trolley.

Yana qarasowa qannansa suka fara gai da shi kamar haka, Good morning yaya marshkhur , yaya mashkhur barka da safiya.

Haka suka ringa gai dashi yana amsawa fuska babu annuri. Bayan sun gama gai dashi shima ya fara gai da su dady.

Ammi ina kwana, dady ina kwana, momy ina kwana, hajiya kaka ina kwana. Da fatan kun tashi lafiya.



Haka yabi ya ringa gai dasu d'aya bayan d'aya, ko wanne yana amsawa cikin mamaki. Kowa fuskar shi ta cika da ayar tanbaya. Kowa so yake yaji mashkhur ina zai je da trolley. Dady ne yayi ta maza cikin da kakkiyar murya yace ina zaka haka da jaka da safiyar nan?.



Mashkhur cikin dakiya da jarumta yace dady RASHA zan koma.

Ammi kuwa gabanta fadad'uwa yayi sabida tasan halin mashkhur in ya tafi ba lallai ne ya DAWO nan kusa ba.



Dady kuwa kallan sama

Please Login or Register in order to submit comment