Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.
Ayya to sannu da zuwa zo mu shiga d’aki koh?, ahh yaya dama kin barini a falon kawai, ke dallan zo mu shiga ae abin sirrine. Tom shikenan kenan yaya mu shiga. Suna shiga saratu ta haye bed ta zauna tare da cewa Wallahi yaya halima wata uwar yunwa na kwaso..........

Typing...........

ADALILINTA.💜❤️💜

BY AMINA BAYERO.💜❤️💜

*free book*💜❤️💜

*ina godiya da masoyana masu bibiyar wanna littafin mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin nana na ADALILINTA...........💜❤️💜

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment.........pls, sabida hakan shi zai bani qarfin guwar cigaba da rubutawa.💜❤️💜

*ga masu buqatar karanta littafin ADALILINTA da nayi posting sai su yimin magana ta wanna number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira. Free book ne bana kud’iba kuma now book.

New book on 2023.

[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing......

*Page 22*
Suna shiga saratu ta haye bed ta zauna tare da cewa Wallahi yaya halima wata uwar yunwa na kwaso.....

Momy cewa tai ahh bari naje na kawo miki abinci sae mu fara maganar ko?. Yauwa yaya halima, ba’a fi minti biyar ba sae ga momy da tire d’in abinci da lemo harda ruwa. Da sauri saratu ta taso ta faracin abinci. Yauwa sae ki fara yimin bayani bokan koh cewar momy.

Sai da saratu ta kae cikalin abincin a bakinta tare da cewa d’an miqomin jaka ta kigabi. Ba musu momy ta miqo mata jakar. Bayan saratu ta karb’i jakar ta zuge ta curo wasu qullum magani guda uku. D’aga d’ayan tai tare da cewa wannan maganin boka yace ki barbad’awa abdul d’in a abinci.

A dai-dai lokacin da saratu ta fara bayani a dai-dai lokacin dady yazo d’akin momy dan ya d’akko wata hularsa da zai sa. Harya tura kai zai shiga, yaji muryar saratu tana magana harya juya zai koma yaji saratu tana cewa Wallahi yaya halima boka yace indai kika barbad’awa abdul a abinci koh Wallahi ji zai yi duk duniya ba wadda yake so kamar ki.

Shi kuma wannan so ake ki zuba mae a qasa ya taka, in dae ya taka koh Wallahi abdul da qafarsa zai dawo wajanki. Sai wannan kuma ta fad’a tana qara d’ago maganin, shi wanan sai ya dawo wajanki zaki yimai wanka da shi indai kikayi mae wanka koh to Wallahi boka yace shida matar can ammi take da suna koh marya, momy tace maryam to Wallahi bashi ba ita.

Kai ji zai yima duk duniya ba wadda ya tsana kamar maryam (ammi). Tafawa sukayi tare da sheqewa da wata uwar dariya. Shiku dady da yake tsaye ji yayi qafarsa ta kasa d’auakr gangar jikinsa. Wani irin mugun jiri yakaeji sae mai-mai ta sunan BOKA, Yake a zuciyar sa. Muryar saratu ce ta dawo da shi daga tunanin da yafi inna takae cewa!!

Amma yanzu yaya halima zaki iya amfani da maganinnan kuwa? Naji kince fa abdul koh wajanki baya zuwa. Murmushin mugunta momy ta saki tace haba saratu mae akai akayi abdul nice fa halima karki damu, aka yiwa uban da ya haife shi bare wani shi d’an cikina.

Tashin hankali da ba’a samai date, ai dady sake rikirkicewa yayi maganar momy ce kawai take mae yawo wato shima anyi mae to me momy tayi mae haka?. Abindda yake ta tanbaya kenan amma ba mae bashi amsa.
A fusace ya fad’a dakin, ai daga momy har halima ba wadda bai sha jinin jikinsa ba musamman ma da suka ga kallon da dady yake watsa musu.

Agigice momy tace am!!! Ahh!! Na!! Ce!!! Ahh!! Yaushe ka shigo ne abban badul?. Wata tsawa dady ya dakama mata. Dallah dakata min dama ke mashirikace ban saniba?. Ahh!! haba!! Abban
abdul ya za’ai kace haka wallahi ni ba!!!!
Dallah yimin shiru banza asarariya Wallahi kika sake yimin magana sai na yi miki mugun duka.

Daga momy har saratu jikin su tsima kawai yake. Dady kallansa ya mayar kan saratu, wata uwar harara ya watsa mata, wadda sae data kad’awa saratu ‘yayan hanjinta. Daga yau sae yau karna sake ganin ki a gida nan, in ba haka ba sai nasa an karya min qafafuwanki gida-gida. Jikin saratu rawa kawai yake sabida tsabar tsuro.

Jin muryar momy sukayi tana cewa haba abban abdul ya zakai kace karta sake zuwa gidan nan?, ‘yar uwa tace fa. Jikake tasss-tasss wani gigi taccan maruka har guda biyu dady ya zubawa momy. Yana huci yace tindda gidan na uban ki ne koh?. kema to kitattara kayanki ki bita ,

Bama sae kina gidan zata ringa zuwaba to NASAKEKI ki tattara kayain ki barmin gidana. Agigice momy ta d’ago zatai magana dady yace kirufe min baki, wallahi in kika qara magana sai na qara sakin ki . Shiru momy tai dan tasan dady zai iya qara sakinta.

Kuma kitattara kayin ki yanzu-yanzun nan ki koma gidanku, in kuma na dawo na samu d’aya daga cikinku Wallahi sae kunyi nadama. Yana gama fad’ar hakan ya bar d’akin a fusace. Hannu momy ta d’ora aka ta fasa uwar qara tare da cewa Wallahi na shiga uku saratu.

Itama saratun kukan take tana cewa shikenan yaya halima asirimu ya tonu.
Ke dallah can zoki tayani had’a kayana dan Wallahi nasan halain abban abdul yanzu ya dowa sae mun gane kuskuran mu.
Ba b’ata lokaci suna had’a kayan su, a salallab’e suka fuce suka kama hanyar kaduna.

6an garan dady kuwa yana fita ya wuce part d’in ammi ya kwanta, sai juyi yake maganganin saratu da momy suna fad’o mae. Ba abidda yafi tsaya mai a rai sai maganar momy wadda tace!! mai akai akayi abdul akayiwa uban da ya haifeshi bare ma shi. Sai tinani yake mae momy tai mae haka.

Sae da momy tai kwana uku a gidan su kafin dady ya sanar da ammi da hajiya kaka. Amma kwata-kwat yaqi ya gaya musu abidda yasa ya saki momy. Ammi kuwa haquri ta shiga bawa dady wae ya dawo da momy, taci darajar abdul. Dady kuma yace mata kinga dae baki tab’a roqana abu nakayi miki ba ko?. Ammi tace ehh hakane.

Dady yace to Wallahi bazai yiwa ammi wanna al farmar ba. Da ammi ta takurawa dady da magiya fishi ya hau yi da ita, a ala dole ammi ta dae na maganar kuma ta rarrashi dady ya dae na fishi da ita. 6an garan abdul kuwa ba abdda ya dame shi rayuwarsa yake mae dad’i.

Har dady ma ya fara tinanin zuwa qarshan shekara shima zai sashi a makaranta.
6an garan su momy kuwa sun shiga cikin tashin hankali. Kullum a yawan zuwa wajan boka suke amma dady shiru bai zo biko ba.

Gashi mahifin momy wato malam garba, yaje kano yafi sau uku bai samu ganin dady ba, gashi yanzu saura sati d’aya iddar momy ta cika. Yauma kamar kullum shiryawa yayi domin zuwa kano wajan dady, sabida umman halima wato hajara ta uzzira mai akan sai ya koma.

Bayan ya sauka garin kano ya nufi gidan dady. Kamar kullum bae samu ganinsa ba. Malam garba zama yayi a qofar gidan yace yau sae ya jira dady ya dawo. Ai kuwa yana cikin zaman nan se ka hajiya kaka da drive zasu fita unguwa. Hajiya kaka tana gain malam garba ta fara tanbayar drive wae wanene?.

Drive yace Wallahi haijiya ban san shi ba amma ina yawan ganinsa yana zuwa, amma mae gadi baya barinsa ya shiga. Hajiya kaka cewa tai drive ya tsaya, baya ya tsaya ta bud’e murfin motar ta fita, tana fita tanufi indda malam garba ke zaune. Cikin nutsuwa hajiya kaka tayiwa malama garba sallam.

Da sauri ya amsa mata tare da cewa barka da war haka hajiya, an wuni lafiya?. Lafiya qalau malam sae da ban ganae wanene ba,. Murmushi malam garba yayi tare da cewa nima hajiya ban sankiba amma ni surikin mae gidannan ne ya fad’a yana nuni da gidan. Ni baban matar mae gidan nan ne wato halima.

Murmushi hajiya kaka tayi tare da cewa sannu da zuwa ai da ka shiga daga ciki. Ehh Wallahi hajiya na so na shiga amma hakan bai samuba sakamakwan mae gidan bayanan. Ehh hakane baya nan amma yanzu zo mushiga daga ciki. Ba musu malam garba ya bi hajiya kaka cikin gidan.

Bayan sun shiga ciki hajiya kaka ta kawo mae lemo da ruwa mae sanyi yasha. Godiya ya hau zibawa Hajiya kaka, ita kuma tana ce mae ba komai. Sae da yayi wajan minti goma, kafin hajiya kaka ta fara gabatar mai da kanta. Nide sunana fatima kuma ni mahifiyar mae gidan nan ce.

Da sauri malam garba ya d’ago yana kallan hajiya tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Alhamdulilah hajiya fatima fad’uwa tazo dae-dae da zama, nayi farin cikin had’uwa da ke Wallahi. Murmushi hajiya kaka tayi tare da cewa nima naji dad’in haduwa da kai.

Yauwa hajiya ni dae zaki iya kirana da garba, kuma nazo ina son magana da d’anki Abubakar, amma baya nan dan ALLAH hajiya in ba damuwa zamu iya magan?. Ehh ba komai malam garba mae ke tafe da kai ne?. Yauwa hajiya fatima ina godiy dama inaso na roqi wata al farma a gare ki ne hajiya dan ALLAH ki tai makeni.............

Typing.......

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

*free book*💜❤️💜

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan ALLAH in kum karanta ku d’inga comment.......pls. Sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.💜❤️💜

ADALILINTA .💜❤️💜

BY AMINA BAYERO.💜❤️💜

Typing........

*page 23*
Dama inaso na roqi wata al farma a gare ki ne hajiya dan ALLAH ki tai makeni .......

Bakomai malam garba ina jinka, sai da malam garba yaja dogwan nunfashi kafin yace!! Dama maganar halima ce ta kawoni wajan Abubakar amma tindda baya nan sae nake ganin kawai na roqeki al farma. Dan ALLAH hajiya fatima ki tema keni in abubakar yazo ki tayani bashi haquri akan, ya dawo da matar sa halima d’akin ta.

Hajiya fatima nima nasan abidda halima tayi bata kyauta ba, kuma Wallahi hajiya na hanata irin wanna halin amma taqiji, kinga yanzu abidda ta jawa kanta. Dan Allah hajiya fatima ku yafeta ta dawo d’akin ta itama tayi ladama.

Jinjina kai hajiya kaka tai tare da cewa hakane malam garba, amma ni ban ma san laifin da tayiwa Abubakar ba haka ya sake ta.
Shiru malam garba yayi na wasu ‘yan mintina kafin yace, Wallahi hajiya fatima abindda ta ai kata koh ince suka aika ta ba dad’in ji.

Shiru hajiya kaka tayi kafin tace in ba damu ka sanar dani mae tayi mae haka ya sake ta, kaga naji dad’in bashi haquri akan ya dawo da ita d’akin ta.
Sae da malam garba yayi jim kafin ya bawa hajiya kaka labarin abidda momy da saratu suka ai kata.

Abin bae bawa hajiya kaka mamaki ba sosai sabida ta dad’e da sanin momy mushirika ce, tin sadda suka yiwa dady asiri ya rikirkice akan halima, daga qarshe sai da ya aure ta.
Maganar malam garba ce ta dawo da hajiya kaka daga zurfin tinanin da ta tafi. Hajiya dan ALLAH karki ce baza ki amince ba ki temaka.

Girgiza kai hajiya kaka tayi tare da cewa gaskiya sai dae malam garba kayi haquri bazan iyayi ma wanna al farmannan ba. Tabbas wannan mugun hali halima ta d’auka, kuma gaskiya baza mu iya zama da mashirika ba. Dama ALLAH ya tai maka yaro d’aya ne a tsakanin ta da abubkar,

Kuma shima yaro ba ita take rainon saba gashi ma basu saba ba, dan haka ALLAH ya had’a kowa sa raban sa. A gigice malam garba ya d’ago yana kallan hajiya kaka magiya ya hau yi mata, kae da ga qarshe ma, har hawaye malam garba ya zubarwa da hajiya kaka.

Hajiya kaka taji tausayin sa sosai, kuma jikinta ya bata malam garba mutumin arziki ne, daga gani halima ba halin malam garaba ta d’akko ba wata qila halin uwar ta ta kwaso. Haka dae malam garba yay ta kuka da bawa hajiya kaka haquri.

Share hawayan ka malam garba komai ya wuce kuma insha ALLAH halima zata koma d’akin ta. Nan da nan malam garba ya hau zibawa kaka godiya da addu’a a.
Malam garba yana shirin koma wa gida sae ga dady ya dawo. Bayan sun gaisa ya fara bashi haquri akan abidda halima tayi mae.

Dady kuwa cewa yayi ba komai amma fa bazai mayar da halima d’akin ta ba. Haka mahaifin halima yay ta bawa dady haquri dady, yace ya haqura amma bazai mae da halima d’akin taba. Hajiya kaka ce tasa baki kuma ta tursasa dady akan sae ya mai da halima d’akin ta.

Cikin baqin ciki dady ya mae da halima, amma da badan hajiya ta tursasa shi ba da ba abidda zai sa ya mayar da momy. Dady sae da ya kafa sharad’i akan momy ta cigaba da zama’ a gida har sai ya neme ta. Haka malam garba ya tafi cike da faran ciki. Dady kuwa zuciya ba dad’i ya wuce part d’in ammi.

Lokacin da su momy suka samu labarin dady ya mayar da ita ba qaramin farin ciki sukayi ba, harda tsalle da juyi. Kuma a take momy ta fara tinanin ramuwar da zatai wa ammi akan rabata da abdul da tayi. Ai kuwa ta yanke shawarar in zata koma da shirin ta zata koma, kuma ba kowa za tae wa shirin ba face MASHKHUR.

6an garan ammi kuwa tana kula da abdul fiye da tinanin mae karatin littafi, dan yanzu gani take kamar ita ta haifeshi. Wata soyayyace ta d’a da uwa ta shiga tsakanin ammi da abdul, duk duniya shima abdul ba wadda yake so kamar ammi. Qafarta qafarsa koh bacci tare suke yi.

Shima mashkhur yana qaunar abdul sosai, kamar yadda abdul yake qaunar sa, dan abdul yana ganin mashkhur ya dawo da ga makaranta zai fara tsalle yana murna. Dan yanzu harya fara iya fad’ar sunan sa, yana cemai yaya mashkhur. Dady kuwa hakan ba qaramin dad’i yake mae ba dan baya so, a raba mae kan yara.

Sai da momy tai wata biyar kafin ta dawo gidan dady da zama. Shima da kyar dady ya amince tare da saharad’in kar saratu tasake zuwa gidan. Hakan bai wa momy dad’i ba amma ba yadda ta iya. Yanzu ma saratu ta kusan yin aure dan ta samu wani mae kud’in gaske a kaduna, duk da kuwa yana da mata.

Lokacin da momy ta dawo sae da dady ya tara mutan gidan a falon ammi. Wato hajiya kaka, ammi, momy. Ba komai ya sanar da suba face daga rana mae kamar ta yau ya barwa ammi ABDUL MAJID halak malak. Sabida momy in aka bar mata abdul zata iya b’ata sa.

Momy bataji dad’i hakan ba amma ta danne bata nunaba. Bayan momy ta koma part d’in ta, tinawa tae da maganin da ta karb’a a wajan boka kafin ta dawo. Tinanin ta fara kala-kala ta yadda zata bawa mashkhur maganin nan, al halin kuma mashkhur ba ya kulata bare ya karbi abinta ya sha.

Wani shu’umin murmushi momy tayi sabida ta gano ta yadda zata bawa mashkhur maganin nan. Momy yanzu ta gyara halin ta ba kamar da ba duk tayi sanyi, duk da kuwa ba dan ALLAH take hakan ba d’an dady ya saki jikinsa da ita ne kuma yaga ta gyara halinta.

6an garan hajiya kaka kuwa ta miqe tsaye sosai kullum cikin addu’a take ALLAH ya tsare dady da ammi kai harma da mashkhur, daga sharin momy. Kuma bayan haka tana zuwa wajan malm Ibrahim domi karb’ar rubutu da addu’o’i. Kuma tana bawa dady da ammi, bata bawa mashkhur sabida a ganinta yaro ne momy ba zata iya cutar sa ba.

Yau juma’a kuma mashkhur bashi da makaranta ranar jumm’a yana d’aki yana karatu. Shi kuma abdul yana tsakar gida yana wasa da kwallo.
A hankali momy ta sauke glass d’in d’ankin nata dan taga waye yake biga kwallon. Tana leqawa taga d’anta abdul, murmushin mugunta momy tayi tare da mayar da glass d’in ta rufe.

A hanzarce ta nufi kicin, tana shiga kicin d’in ta bud’e firic ta d’akko wani jok mae cike da zob’o, zob’an ya sha had’i sae qamshi yake. Da sauri ta hajiye jok d’in ta nufi bed room d’in ta. Cikin qan qanin lokaci ta dawo hannu riqe da maganin boka da ya bata yace ta zubawa mashkhur a lemo,

Kuma ya bata tabbacin cewa inddai mashkhur ya sha leman da maganin a ciki, tofa duk abindda momy tace sai yayi, koh kara ta ajiya ba zai tab’a tsallake ta ba, ba tare da izini momy ba.
Abidda yasa momy takae so ta mallake mashkhur kawai so take ta qunsawa ammi bakin cikin kamar yadda ta qunsa mata, ta rabata da d’anta abdul.

Bugu da qari kuma dama momy taci al washin sae tayi maganin mashkhur, akan ko in kular da yake nuna mata. Kuma ta d’au al washin sae ta lallatawa mashkhur da TARBIYA koh ta halin yaya ne. A hanzar ce ta dakko cup ta fara zuba zob’an sai da ta kusan cika cup d’in. Bayan ta zuba zob’an ta fara barbad’a garin maganin boka.

Bayan ta gama zuba maganin qara dakko wani cup d’in tayi amma bae kai waccan girma ba, ta qara zuba zub’an, tana gama zubawa ta d’auki kofinan tayi hanyar waje. Bata tsaya ko inaba sae indda abdul yake biga kwallo. Abdul yana ganin ta ya taka a guje zai gudu, da sauri ta ajiye kofinan ta roqo shi. Kuka Abdul ya fara yana cewa ni Wallahi bazan biki ba wajan ammina zani.

Wani baqinci kine ya sake turniqe momy, amma tai sauri tace na sani nima ai ba tafiya zanyi da kai ba. Zaka sha lemo ko? D’aga mata kai bdul yayi alamin Eee, yauwa amma fa sai kaje ka fara kai wa yaya mashkhur koh?. Qara D’aga mata kai yayi alamin eee. Yauwa Abdul d’in ammi, abdul kuwa yana jin haka ya fara dariya sabida tace mae Abdul d’in ammi..............

Typing.......

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar wanan littafin mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment......pls,?sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutuwa.💜❤️💜

Ga masu buqatar karanta littafin ADALILINTA da nayi posting, sai suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira. Kuma bana kud’i bane free book ne, kuma new book.

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Page24*
Yauwa abdul d’in ammi, abdul kuwa yana jin haka ya fara dariya sabida tace mae abdul d’in ammi...........

Miqa mae cup d’in da ta zuba zob’o mae maganin boka tai, tare da cewa yauwa abdul d’in ammi kayi sauri ka kaiwa yaya mashkhur kaji, kuma karka bari ammi ta gani kuma karka sha, ga naka nan na ajiye ma in ka dawo sae nabaka. Abdul cewa yayi toh, har zai tafi momy ta ruqo hannun sa tace kuma karkace nina bashi kana bashi karkayi magana kawai ka futo.

D’aga kai abdul yayi sanna ya fara tafiya hanyar part d’in ammin. Wata nannauyar ajiyar zuciya momy ta sauke tare da sakin wani mugun murmushi, a fili tace, mashkhur zai zama qarqashin ikona, ke kuma ammi Wallahi sae nasa kin zubar da hawayan baqin ciki.

6an garan abdul kuwa yana shiga part d’in ammi ya wuce d’akin mashkhur. A kulle d’akin yake dan haka Ajiye leman abdul yayi ya fara kwankwasawa. Ji yayi mashkhur yace wanene, da sauri yace yaya mashkhur nina ka bud’e min, duk da abdul bae iya magana sosai ba amma mashkhur ya ganem mae yake cewa.

Bud’e mae kofar mashkhur yayi. A lokacin duk mashkhur ya har gatsa litattafan makaranta yana home-wrok da kuma karatu. Abdul kuwa koh shiga bae yi ba ya miqawa mashkhur. Mashkhur kuwa qarb’a yayi kafin yayi magana abdul ya jiya, mashkhur kuwa a tinaninsa ammi ce tabawa abdul ya kawo mae, abinka da tinanin yaro,

Sabida a lokacin mashkhur qarami ne kawaid dae yana da qoqari da kwakwalwa mae kyau shiyasa yazama kamar wani babba. Bayan ya karb’a zub’an shima juyawa yayi tare da kulle d’akin ya koma. Da bae yi niyar shaba sabida ba komai yake shaba alokacin amma da yatina abdul ne qaninsa da yafi sone ya kawo me, kawai sae ya fara sha.

6an garin abdul kuwa tindda ya juya bai tsaya a ko inaba sae wajan momy. Momy kuwa tana ganinsa ta fara washe baki tare da cewa yauwa abdul ka kai mae koh? D’aga kai abdul yayi alamin eee. Yauwa yaran kirki kai ma karb’i naka, ta fad’a tare da miqa mai qaramin cup d’in zob’an wadda bata sa mae maganin ba.

Karb’a abdul yayi tare da cewa nagade, dama ammi ta koyawa abdul godiya a duk sandda aka bashi abu. Tab’e baki momy tayi sabida tasan ba wadda zai koyawa abdul wanna face ammi. Shi kuwa abdul juyawa yayi ya wuce 6an garan ammi. 6an garan mashkhur kuwa sae da ya shanye zo6an momy tass sanna ya ajiye cup d’in.

Bayan yasaha zub’on wani bacci ne mae nauyi ya kwashe shi. Ba shi ya tashi ba sae wajan qarfe hud’u na yamma, shima buga qofar da ammi ne take ya tashe shi, daga baccin. A hankula yatashi yaje ya bad’e. Kallan sa ammi tai tare da cewa wae mashkhur sabida mae kake da taurin kai ne? Ban isa na gaya ma magana kajiba ko?.

Dan ALLAH ammi kiyi haquri ki dena yima fad’a ni ban ma san wana lefi yau nayi miki ba. Harara ammi ta watsa mae tare da cewa ba na hanaka rufe qofar d’aki ba? Amma sabida baka jin magana yau ka qara rufowa, wai kae mashkhur mae ka d’aukin kanka ne eyee? Kana yaro qarami kana taurin kai da rashin jin magana, ina da ka girma?.

Lumshe kyawawan idanunsa mashkhur yayi tare da cewa haba ammina yanzu akan wannan kike tayi min fad’a tom insha ALLAH daga yau bazaki qara qorafi akan rufe kofar nan ba sai dae mushiga wani fad’an. Riqe baki momy tayi tana ganin ikwan ALLAH wae yaro qaramin ya iya magana da tsari.

Magar mashkhur ce ta dawo da ita daga tinanin da ta, tafi. Ammina dan ALLAH kiyi haquri ki dae na fushi da ni kinji?, ajiyar zuciya ammi tayi tare da cewa tom zan dena amma sae kai ma sai ka dena rashin jin magana tukunna. Dama shi haka mashkhur yake in dae yayiwa ammi laifi sae ya dawo ya bata haquri.

Tom zan dae na ammi yanzu kiyi min murmushi dan ALLAH. A ala dule ammi tayi murmushi sabida tasan halin mashkhur in batayi mae murmushin nan ba yata binta kenan akan sae tayi dan har bacci bazi batta tayi ba. Kayi sallah ne? Aaa yanzu sanyi alwala na tafi masallaci.

Tom shikenan kayi sauri kar a tayar da sallar, tom ammi, yana gama fad’ar haka ya juya yayi alwala. Yana futowa falan ammi ya tarar da momy da ammi suna hira, kawai mashkhur ya fara bin momy da ido kamar yaga saban abu, ji yake kamar yayi mata magana. Kwatsam yaji momy tana cewa ahh yayan Abdul ba magana?.

Mashkhur kuwa kamar jira yake tayi mae magana da

Please Login or Register in order to submit comment