Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auka ta turawa maman zahra ta kaduna gajeran message, na ALLAH ya sauki zahra lafiya kuma ta samu yaro namiji.

Bayan ammi ta gama tura message d'in ajiye wayar tai, sanan ta miqe domin taji an fara hiqama. Haka ta gabatar da sallah ta, sanan tayi lazimi da addu'o'i ta, tana cikin azkhar d'in safiya taji baby ya bara kukan su na jarirai. Nan da nan ammi ta d'an tausaya masa sabida tasan may be yunwa yake ji, kafin ammi ta miqe zahra harta bud'e idanuwan ta sabida kukan babyn daya tashe ta.

A hankula zahra ta yaye blanket d'in da aka rufa mata,. Ta miqe zaune da kyar sabida tsabar yunwar data tashi da ita. Tana miqewa ta zare allurar ledar ruwan da aka sa mata sabida ruwan ma ya d'an jima da qarewa. Ammi tasowa tai tare da cewa, zahra sannu da farkawa fatan kin tashi lafiya.

Murya a dashe zahra tace lafiya qalau ammi, to masha ALLAH, Allah ya qara miki lafiya ki d'auke shi mana bakyaji yana kuka. Kawar da kai zahra tai tare da cewa hmm ni fa ammi yunwa nake ji, ba abinci ne. Okay bari na had'a miki tea ki fara sha, ba 6ata lokaci ammi ta fara qoqarin had'awa zahra tea. Zahra kuwa sai satar kallon babyn nata take wanda har yayi shiru.

Tana son d'aukar shi amma tana jin nauyin ammi. Bayan ammi ta gama had'awa zahra tea d'in bread ta d'auko sanan ta kawowa zahra. Jiki na rawa zahra ta faraci, zahra tana cin bread d'in ne kawai badan tanajin dad'i ba, kawai sabida yunwa take ci, gaba d'aya a time d'in bata son cin bread. Ba lefe zahra ta sha tea da bread sosai har sai da cikin ta ya cika.

Daga nan kuma ta biqaci ruwa tasha bayan tasha, tayi gyatsa hamdala tai. Ammi kuwa bayan ta mai da kayan tea d'in dawowa tai ta d'auki babyn zahra tare da d'ora mata shi akan cinyarta. Zahra hannu biyu tasa ta riqe shi ba tare da tace komai ba. Yaron abin tausayi sai hamma yake alamun yanajin yunwa.

Zahra kuwa tama kasa tsayar da idon ta akan yaron tana mamaki wai wanan babyn tane oh rayuwa kenan. Nan da nan babyn ya fara inya-inya, zahra kuwa ta riqe shi ne kawai amma ko irin jijjiga shi batayi yarda kasan mutum-mutumi. Cikin mamki ammi tace zahra meye haka kuka fa yake yi. Kallon ta zahra tai tare da cewa to ammi me zan mai?.

Lallai zahra sai ma an gaya miki yarda za'ai ko d'an jijiga shi bazaki iya ba. Ammi kinsa dai ban iya ba kar6e shi ki rarrashe shi kinga sai na gana yarda ake ko nan gaba koh?. Ai yanzu ba rarrashi yake buqata ba yunwa yake ji. Jim zahra tai batace komai ba, ammi cewa tai kinji koh?. Ee ammi naji, tom maza ki bashi ya sha. Zahra cikin mamaki tace na bashi me?.

Murmushi ammi tai tare da cewa! Kai zahra harda wani tsorata sai kace na fad'i wani abun tsoro, ki shayar da shi mana nake nufi. Zahra rausayar da kai tai cikin jin kunya tace aa gaskiya bazan iya bani. To zahra bazaki iya ba ammi ta fad'a cikin mamaki. Gyad'a kai zahra tai alamun eee. Hmmm zahra kenan jaririne fa bashi da baki, karki d'auki alhakin shi ni sai na baki waje ma tinda kunya ta kike ji.

Ammi ta qarasa maganar tana qoqarin miqewa, d'an ruqo hanunta zahra tai tare da cewa haba ammi ki zauna mana, ni ba haka nake nufi ba, kinsan ai ban iya ba shi yasa. Tom shikenan ai a haka zaki koya, jim zahra tai tana d'an tinani. Ki daure zahra da haka zaki saba kinji, zahra to ta iya cewa amma bata da alamun ko kwakwaran motsi.

Sai to kike cewa nifa nake miki magana, yanzu ana gama idar da sallah asubayi zaki fara ganin mutan gidan suna zuwa kinga ai kyaji kunya mai wujja kuma dole ki bashi. Hmmm zahra tana jin haka ta yunqura tare da cewa tom taya zan fara, kinga fa rigar a matse. Hannu ammi ta kai bayan rigar zahra ta bud'e zip d'in. Zahra wata ajiyar zuciya kunya ta saki.

Tom gashi na bud'e miki bismillah koh? Zahra haka ta fara noqe-noqe wajan 5 minutes tana abu guda. Hmmm bari dai na tashi na baki waje zahra wanan lamarin naki sai addu'a. Ruqo ammi zahra ta sakeyi tare da cewa tom ya haquri kin san dai ban iya ba in kika tafi waye zai koya min ammi?. Tom naji amma wlh kika qara ko minti d'aya sai na fita.

Zahra haka ta gyara zama cikin jin kuya ta fara qoqarin bud'e brest d'in nata guda d'aya. Haka zahra ta bud'e da kyar cikin jin kunya. Tom sai ki bashi ammi ta fad'a haka tana gyara zama. Zahra tama rasa yarda zata fara bawa babyn, sabida babyn yana kan cinyar ta brest kuma yana qirji. To ammi taya kinga fa yayi qasa sosai. Kai zahra bade shashan shi ba ke da zaki d'ago kan sa.

Hannu ammi tasa ta d'auki babyn sanan ta kwantar da kansa a damtsan hanun zahra ya d'anyi sama sosai, haka ammi tai ta gyarawa zahra kwanciyar babyn har sai da kansa ya kawo dai-dai brest d'in zahra. Tom gashi nan sai ki bashi ya sha. Jiki a sanyaye zahra ta sake d'aga damtse hanunta kan babyn ya sake sama.

Kai zahra kina da matasala wlh keda zaki sa hannu ki bashi taya zai kama a haka shida ba sabawa yayi ba bai ma ta6a shafa bare ya kama ba sai kin bashi da hanunki zai shafa. Haka zahra dai ta kama brest d'in nata kamar zatai kuka ta kai bakin babyn. Shima babyn a hankula ya bud'e bakin ya kama sannan ya fara sha a hankula.

Ko second 30 beyi da fara shaba zahra ta janye jikin ta, zahra meye haka kuma kin fara abun arziki. To ammi ba sai ya shanye ba. Hmmm kai zahra a kwai gab'in ta may be ma ruwan be zoba ko sha babe zaki wani janye jiki waya gaya miki haka akeyi ai in kika bashi sai yasah sosai. Zahra qarasa mai brest d'in tai a baki, da kyar babyn ya iya kamawa duk zahra tabi wani sai gumi take kamar mara gaskiya.

Yauwa ko kefa amma ki ringa kula da hancin sa karki toshe mai, zahra da kyar ta iya cewa to. Haka ammi da zahra su kai ta abu d'aya sai faman gyarawa zahra ammi take. Bayan yayi wajan 20 minutes zhara zare brest d'in ta tai daga bakin babayn tare da cewa wash nifa na gaji zafi nake ji.

To ai dama dole kiji zafi ki daure mana, girgiza kai zahra tai tare da cewa wlh ammi bakiji zafi ba ji nake kamar yanka ta ake kawai a barshi haka. Tom shikenan tinda ya fara miki zafi sai ki bashi ta d'ayan gefan koh. Haka ammi tai ta lalla6a zahra harta yarda ta mayar da d'ayan sanan ta futo da d'ayan brest d'in. Shima d'ayan bai wani jima yana shaba zahra aka fara complain d'in zafi.

Haka dai ammi ta cigaba da rarrashi har yaro de ya samu abinda ya samu ya sha, sanan zahra ta zare shi duk da be qoshi ba. Ammi kuwa ba yarda ta iya a hakan ma taga qoqarin zahra tinda taga bata so. Ammi tana gama mayarwa da zahra zif d'in rigar sukaji sallamar mashkhur.

Kai mashkhur kalar wanan asubanci haka.😏😏

To jama'a ta mu had'e a next page.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING..........

*Page 144*

Ammi tana gama mayarwa da zahra zif d'in rigar sukaji sallamar mashkhur...........

Zahra tanajin sallamar mashkhur taji wani sanyi a zuciyarta, amma qasa-qasa ta iya amsa sallamar sanan ta mayar da ido kan babyn ta da yake riqe a hanunta. Itama ammi amsawa tai a zuciyar ta tana mamakin uban sammakwan da mashkhur ya biga. Bayan ya shigo satar kallon zahra ya farayi sanan ya gaida ammi, bayan sun gama gaisawa kallon sa ya mayar kan zahra tare da cewa zahra ya jikin naki?.

Zahra da kyar ta iya cewa da sauqi a taqaice. Ammi da wayar hanunta ta fara ringing miqewa tai tare da cewa tom bari na d'an fita waje nayi waya, ammi tayi hakan ne sabida ta bawa su mashkhur damar ganawa da junan su. Zahra cewa tai to ammi sai kin shigo, mashkhur kuwa ammi tana fita ya qaraso inda ta tashi wato kusa da zahra ya zauna.

Cikin zumud'i ya ruqo zahra ta baya tare da cewa my teddy ya jikin naki fatan koma lpy. Ajiyar zuciyar zahra tai tare da cewa lafiya qalau yaya mashkhur, sai dai kewarka da ta cikamin rai. Wani kallon rashin gamsuwa mashkhur ya zubawa zahra a zuciyar shi yana ayyana yarda jiya ta ringa kiran sunan abdul.

A fili kuwa cewa yayi da gaske mommyn babyna, zahra d'agowa tai tana kallon mashkhur cikin mamaki tace amma my hero naga kana yimin wani kallo kamar baka gamsu da abinda na fad'ama ba nice fa. Sake ruqo zahra yayi tare da cewa no my wife ba komai fa, kawai ina mamakin yarda kewata ta cika miki zuciya.

Kuma wahalar da kika sha wajan haifo mana babyn mu batasa kin manta dani a zuciyar ki ba. Wata harara zahra ta watsawa mashkhur sanan tace au yanzu yaya mashkhur sai kace baka yarda da son da nake maka ba, kasan dai so a zuciya yake, kullum kai har mun haiwu amma kullum gani kake kamar kafi sona bayan nima nasa ina sonka.

Cikim kulawa mashkhur ya fara shafa bayan zahra tare da cewa I'm sorry my teddy ba haka nake nufi ba kiyi haquri kinji, yanzu fa wutawa ya kamata kiyi ba magana ba nasan kin sha wuya koh. Zahra kwantar da kanta a wuyan mashkhur tai tare da cewa ba qarama ba yaya mashkhur dama haka haiwuwa take da wahala gaskiya ni dai daga wanan na gama shikenan.

Murmushi tausayawa mashkhur yayiwa zahra tare da cewa sannu teddyna dama ita haiwuwa ai ba sauqi, sanan fa kinga ALLAH ne ya baki wasu nema suke bai basu ba, dan haka kiyi haquri sanan kuma ki godewa ALLAH bisa kyautar da ya baki kuma ya sauke ki lafiya, bugu da qari kuma ya bar mana babyn mu a raye, sanan kema ya barki a raye.

Zahra sauke ajiyar zuciya tai tare da cewa haka ne my husband but nifa bazan sake haiwuwa ba kaji, ai ka yarda koh?. Shafa jikin zahra mashkhur yayi tare da cewa tom shikenan my wife yarda kike so haka za'ai kinji. Zahra cikin shagwa6a tace amma to baka cemin ka yarda ba, lumshe ido mashkhur yayi ya bud'e tare da cewa hmmm ni dai bani babyn na sake d'aukar shi.

Miqewa zahra tai daga kwanciyar da tai a jikin mashkhur sanan ta miqawa mashkhur babyn nasu zuciyar ta cike da qaunar babyn da ya tsareta da ido kamar ya santa. Kar6ar shi mashkhur yayi tare da cewa to yanzu kin gane dawa babyn yake kama ko. Wani kallon qauna zahra ta watsa masa tare da cewa ee na gane mana dani yake kama.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa koh? Itama zahra murmushi tai tare da cewa ka dena jin dad'i yana kama da kai, to ba dakai yake kamaba da ilham yake kama kaga kai da ilham kuwa bakwa wata kama. Hmm bakyason fad'in gaskiya koh tom shikenan nan dai. Ki gayawa babyn nan naki munyi missing d'in shi sosai kafin ya futo sabida me yay letti.

Wata siririyar dariya zahra ta saki tare da cewa da wana yaran zanwa babyn bayani?. Kallanta mashkhur yayi cike da qauna sanan yace tindake bakyajin yaran to ni bari nai mai yaran uba da d'a kin san dai yanzu na zama dady ko? Mashkhur ya qarasa maganar yana d'ago babyn qirjinsa. Dariya zahra tai tare da cewa sannu uba yauwa uwa.

Mashkhur d'an yatsan sa yasa ya rufewa babyn baki sabida hammar da yake tare da cewa kai wanan maman babyn anya kin feeding d'in babyn nan namu kinga hamma yake. Harar mashkhur zahra tai tare da cewa gashi nan ka tambaye shi mana. Kai teddy serious fa nake miki magana?. Zahra cikin 'yar jin kunya tace ee.

Kin bashi kenan to taya kika iya? Ni wanan wace kalar tambaya ce ko tayama na bashi ba na bashi ba. Kai teddy nine fa, naga kina wani canzamin kamar kinajin kunya ta. Wani kallo zahra tayiwa mashkhur tare da cewa ba wata kunya ni,. To yanzu bashi a gabana inaso na gani kinji my teddy.

Girgiza kai zahra tai sanan tace ni gaskiya bazan iyaba, dazuma da wuya ammi ta koyamin kuma inajin zafi sosai ni ka rabu dani ko bakajin tausayina ne?. Mashkhur yana qoqarin yin magana yaji wayar shi ta fara ringing. Kallon zahra yayi tare da cewa ahmad ne yake kira bari na dauka ina zuwa. Mashkhur yana dauka bayan sun gama gaisawa da ahmad cewa yayi ok ganinan zuwa.

Kallon mashkhur zahra tai tare da cewa ina zaka? Wajan ahmad zani zuwa sukai bari naje na shigo dasu. Murmushi jin dad'i zahra tai tare da cewa tom shikenan kai sauri kaji. Ok mashkhur ya fad'a tare da miqawa zahra babyn, hannu biyu zahra tasa ta kar6i babyn har lokacin tana mamakin wai itace yau da d'a kai ALLAH mai iko kenan.

Mashkhur baifi 8 minutes da fita ba zahra taji sallamar ilham. Da sauri zahra ta miqe da kyar, ilham tana hango zahra ta qaraso da sauri sukai hugging d'in juna cikin farin ciki, suka qanqame juna kamar wanda sukai shekara basuga junan suba. Sai da sukai 2 minutes rungume da junan sanan suka saki junan su, ilham tace awnnn my zahra congratulations ta qarasa magar tana nufar babyn da yake kan gado d sauri.

Tana zuwa tasa hannu ta d'auke shi cikin farin ciki, wow ashe yamafi kyau a zahiri fiye da camera gaskiya wanan yaron harma yafi yaya mashkhur kyau mashkhur ALLAH. Zahra qarasowa tai ta zauna kan gadon da kyar sanan tace hmmm. Itama ilham zama tai sanan tace au ni zaki cewa hmmm to ba surukar ki bace.

Murmushi zahra tai tare da cewa mude Allah ya sauke mu lafiya bayan munsha wahala, kema ALLAH ya sauke ki lafiya. Ilham fuska cike da farin ciki tace amen au dama da gaske haiwuwar da wahala kenan ai na d'auka kawai fad'a ake, kana zaune sai kaji hance mutum ya haiwu sai kai tinanin abun kamar shan ruwane ashe ba haka bane.

Hmm ai ni ilham bazan ce miki komai ba ki bari sai kinzo haiwuwa tukunna sai kiji abinda akeji. Ilham tana qoqarin magana sukaji sallamar ahmad da mashkhur. Bayan sun shigo ahmad da zahra sun gama gaisawa zama sukai sanan mashkhur ya kar6o babyn daga hanun ilham ya kaiwa ahmad....

To misalin qarfe takwas asibiti ya cika da mutan gidan su mashkhur, kowa da kowa yazo har hjy kaka dady ne kawai bai zuba ammal ranka takaf kowa yazo. Zo kaga ribibin d'aukar babyn har fad'a ake awan d'aukar babyn zahra da mashkhur. A cikin masu fad'an harda hajiya kaka da abdul, haidar kuma da faruq yake faruq kuma da ilhma kai abun dai abin dariya.

6angaran gidan su zahra kuwa suma suna can suna shirya-shiryan tawowa kano.

Zahra kuwa lokaci guda tabi ta d'aga hankalita sosai kamar zatai hauka ita sai an sallameta daga hospital sabida gaba d'aya ita dama kunsan bata son zama asibiti tun tana yarinya. Ammi tayi rarrashin mashkhur yayi, yaya abdul shima yayi nasa hajiya kaka tayi, dadyma dabe dade da zuwaba yayi rarrashin amma zahra taqi ita de tace sai ankoma gida.

Ji take kamar ta mutu in tana zaman asibiti, dole su dady suka nemawa zahra sallamar dole duk da sai jikinta ya qara kwari tayi kwana d'aya zuwa biyu asibiti sukaso su sallameta. Amma haka dai haka sallami zahra aka bata magungunan ta da shawarwari. Zahra kuwa da aka sallame ta wani irin farin ciki ne ya rufeta ba 6ata lokaci gaba d'aya mutan gidan suka fara shirin tafiya gida.

Su zahra suna isa gida aka baje a babban falon ammi, nan ma aka d'ora da d'aukar baby. Ita dai zahra wucewa sama tai bedroom d'in ammi ko ta samu ta wuta da wanan hayaniyar tai bacci mai dad'i. Zahra da ilham basu wani jima da hawa sama ba mutanan kaduna suka rangad'a sallama a gidan, a lokacin qarfe shabiyun rana saura.

Nanma waje ya sake cikewa da hayaniya sosai, mutan gidan suna farin ciki da zuwan surukar su nana sabida sun san 'yar shaftace sosai. Maman zahra dai bata wani tsaya wajan baby ba direct tace ammi ta rakata wajan zahra sabida ita hankalinta duk yana kan zahra. Baki d'auke da sallama ammi da mama suka shiga bedroom d'in ammin.

Zahra tana kwance ita kuma ilham tana daga zauke suna hirarsu kamar yarda suka saba in suka had'u. Har zahra da ilham suna had'a baki wajan amsa sallamar mama. Bayan sun shigo fuska d'auke da farin ciki ilham ta gaida surukarta maman zahra sabida suna shiri sosai, mama tana son ilham kamar yarda take son ahmad.

Bayan ilham ta gama gaida mama, mama zama tai tare da yiwa zahra sannu ya jiki. Mamace tace ai ni nayi tinanin kuna hospital dan ma nayi waya da ahmad ne shi yasa nasan kun dawo gida. Ke dai bari aisha kinsan 'yar taki bata son zaman asibiti kinga yarda ta ringayi kamar zata mutu, wai sai an sallamo ta ai yanzu muka shigo bamu dad'e ba dan ko wanka ma banyi mata ba.

Ruwan zafin yana wuta yanzu zan sauke shi. Ah ai kuwa ya kamata a sauke yanzu ki mata wanka nan ko jikinta ya sace,. Ee a dama amma dai haiwuwar tayi mata kyau sosai kinga fa cikin nata ya koma kamar ba ita ta haiwuwa babu girman nan cewar ammi. Ee wlh na gani amma ya kamar ai mata wanka nan yanzu.

Kai mama daga zuwan ki nifa bana son wankan nan yanzu. Aa zahra sai anyi miki wanka nan ko kina so ko bakyaso. Ni gaskiya ammi bana son wanka jego fa, ah zahra ki kwantar da hankalin ai ba yanzu za'a fara yi miki wanka jegoba sai bayan suna in d'inki da akai miki ya warke yanzu kawai gasa miki jiki naki za a d'anyi ayi miki wanka, haiwuwa fa kika kuma sai aqiyi miki wanka sabida qazanta kiyi haquri.

Hmm ke dai kije ki d'ebo ruwan ki rabu da ita, har wani haquri kike bata, da a zamanin da kike zamanin mu kenan ba rarrashi mari kawai zaki ringa ji kuma wanka ma ba irin wannan ba mama ta qarasa maganar tana murmushi. Itama ammi murmushi tai sanan tace to bari naje na d'ebo ruwan zafi. Zahra cewa tai mama ina nana?.

Nana da su fawas suna qasa, kinsan nana anyi d'a kuma ga mijinta acan ai bazakiga qafarta a wajanki ba. Kai nana kenan bata da dama, miqewa ilham tai tare da cewa to ni bari naje kar ayi bani sabida nana in ta zauna a waje ai anacin nishad'i. Dariya zahra tai sanan tace aikuwa dai kije ki jiyo mana shaftar nana amaryar yaya abdul..............


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING..........

*Page 145*

Dariya zahra tai sanan tace aikuwa dai kije ki jiyo mana shaftar nana amaryar yaya abdul..............

Ilham bata wani dad'e da fita ba ammi ta shigo hannu d'auke da botikin ruwan zafin daya sha ganye iri-iri. Tana shigowa baki d'auke da sallama ta wuce toilet, bayan ta kai ruwan ta dawo ta zaune tare da cewa to gashi nan sai ki tashi mama tai miki wanka. Tab gaskiya ni bana son wanka ta ammi naki nake so. Murmushi maman zahra tai tare da cewa ai gwara da kika ceci kanki dan in ni zan miki ko sirka ruwan bazan ba.

Maman zahra ta qarasa maganar cikin zaulaya murmushi ammi tai tare da cewa to wanan wana kalar wanka ne ai qonata kawai zakiyi. Daga haka ammi ta d'aukowa zahra kayan da zata sa in tayi wanka da abubuwan dai daya kamata. Bayan haka ammi wucewa tai toilet tana cewa zahra taso koh, bari na surka ruwan. Zahra kuwa da kyar ta miqe sabida wani irin bacci da takeji.

A hankula zahra take takawa harta qarasa toilet d'in, bayan ta qarasa ba 6ata lokaci ammi ta fara yi mata wanka tare da gasa mata jikinta sosai. Sun d'au 20 minutes sanan suka gama wanka, daga haka ammi ta futo ta wuce kicin tabar zahra a toilet tana shiryawa, zahra a toilet d'in ta gama sa kayanta tana gama shiryawa sanan ta futo. Tana futowa ta zauna a gefan gado sannan ta fara qoqarin jona wayarta a caji.

Baya 5 minutes ammi ta dawo hannu riqe da plate d'in farfesun nama,. Bayan ta qaraso zahra ta miqawa, kar6a zahra tai tare da cewa ngd. Ya kamata tinda anyiwa uwa wanka shima babyn ayimai cewar maman zahra. Ee shima yanzu zan kar6o shi ayi mai ammi ta fad'a tana kama hanyar fita daga bedroom d'in. Bayan 10 minutes ammi ta dawo hanunta riqe da babyn zahra.

Daga haka ta miqawa mama shi, hannu mama tasa ta qar6a ciki farin ciki wai itace da jika yau oh. Ammi kuwa wucewa tai toilet domin d'ebo ruwan zafin da za'a yiwa baby wanka dama shi da normal ruwan zafin hita za'a iya yima ba sai an dafa mai mai ganyayaki ba irin na zahra. Ammi bata dad'e da shiga ba ta futo hanun riqe da saban bawon wanka baby.

Bayan ta ajiye ruwan ta d'auko baby soap kala-kala da water soap, da turarukan wanka baby. Sanan ta ajiye su kusa da bowan ruwan wanka tare da cewa gashinan kafin ki gama yi mai wanka bari na d'auko mai kayan da za'a samai. Miqewa mama tai sanan tace tom shikenan, direct ta nufi inda ammi ta ajiye bawan sanan ta zauna.

Bayan mama ta gama zuba turarikan wanka babyn kaya ta cire mai sanan ta sa shi a ruwan wanka. Nan da nan baby ya fara kuka, haka mama tai ta juya shi a ruwan wanka har yayi shiru sanan ta fara yi mai wanka. Kafin ta gama yimai wanka ammi ta kawo towel da kayan baby da mai da turaran baby.

Bayan mama ta gama mai wanka mai ta shafa mai. Bayan ta gama shafawa babayn mai kayan sa ta fara sa masa, bayan ta gama sa masa kayan ta shafa mai turare masha ALLAH yaro ya sake kyau sosai gwanin ban sha'awa. Amma ya kamata zuwa anjima a qasa mai cibiya koh?, cewar mama.

Ee yanzu ma ba gawayi ne amma anjima in za'a yi masa wanka dare sai a fara gasa masa kafin nan an siyo gawayin. Daga haka ammi ta kwashe kayan ta mai da komai sanan tai mopping d'in wajan. Babyn zahra kuwa sai kuka yake mama tana faman rarrashi. Daga qarshe dai mama ta miqawa zahra shi tare da cewa zahra qar6e shi haka yunwa yake ji.

Zahra kuwa cewa tai ajiye shi mama kina ganin abinci nake ci. Ammi miqewa tai tare da cewa bari naje na d'ora abinci rana tayi. Mama cewa tai kai naga aiki yayi miki yawa bari nazo na tayaki mama ta qarasa maganar tana ajiye babyn a gefan zahra sannan suka jera da ammi suka fuce suna tafe suna hirar su kamar dai wasu 'yan uwan.

Zahra suna fita ta ajiye plate d'in a gefe sabida ta qoshi dama can ci take amma tasa tana ajiyewa ammi zata ce sai ta cinye. Daga haka ta miqe ta d'auko ruwa a frig ta sha. Sanan ta dawo ta d'auki babyn ta da yake kuka ta fara jijiga shi tana rarrashi. Haka zahra tai ta jijiga babyn tana rarrashi amma yaqi yin shiru ko yayi shiru sai ya cigaba da kuka.

Ana cikin haka ilham ta shigo tana shigowa ta d'auki plate d'in ragowar farfesu zahra ta faraci. Zahra

Please Login or Register in order to submit comment