Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mashkhur ya gaji da hayaniyar da suke mai cewa yayi! shikenan su tafi su bashi guri, ba yarda suka iya haka kowa ya kama gaban sa.

shima yaya abdul d'in sallama yayiwa zahra ya tafi sabida ya bawa su dady waje suyi magana da su, zahra tanaji abdul ya cewa su ilham kowa ya tashi ya wuce bedroom d'in su ya kwanta dare yayi, haka duk suka tafi zuciya ba dad'i. suna fucewa zahra taga ammi da dady sun qaraso wajan laptop d'in sun zauna, nan da nan zahra ta fara washe baki kamar taga saban abun da bata ta6a gani ba. farin ciki ga zahra ba kama hanun yaro, zahra ji take kamar yau take sallah a wajan ta.

baki na rawa zahra tace ammi na? murmushi ammi tai tare da cewa na'am zahra?, ajiyar zuciya zahra tai tare da cewa dady ina wuni, murmushi Shima dady yayi tare da cewa lpy qalau mamana da fatan kina lpy da sauri zahra ta gyad'a kai tare da cewa ina lpy qalau dady. muryar mashkhur ce ta katse su! dady ammi ina wuni?, murmushi suka saki har Suna had'a baki wurin cewa lpy qalau kuma da fatan kuna lpy. shafa fuska mashkhur yayi da hanun hagu tare da cewa muna lpy qalau.

daga haka hira ta 6arke tsakanin zahra da su dady, daga qarshe mashkhur d'an kallo ya zama. can ammi ta dan tsirawa zahra ido tare da cewa! zahra mai ya samu le6anki naga kamar yayi ja, nan da nan zahra ta daburce tare da cewa am! hmm! wlh bigewa nai, daga dady har ammi kallan rashin yarda da abinda zahra ta fad'a suke mata. ammi ce tace no zahra ban sanki da qarya ba sai kace bakya gani ko kuma wata qaramar yarin ko dai mashkhur ne ya dake ki?.

ammi ta qarasa maganar tare da bin mashkhur da kallan zargi, shima dady zubawa mashkhur ido yayi dan shima zarginsa yake. gaban mashkhur ne ya fad'i rass, amma duk da haka dakewa yayi kamar wani mai gaskiya, d'an zaro ido mashkhur yayi tare da girgiza kai yana cewa! haba ammi ya zakice ninaji mata nifa bansan da cuwan maba sai yanzu da kika fad'a, zahra kuwa shiru tai a zuciyarta tana jinjina qarya irin ta mashkhur. kallon sa dady yayi tare da cewa mai sunan baba karfa ka rai na min hankali kasan al qawarin da yake tsakanin mu da kai ko? to wlh na kamaka da laifin dukanta bazan Cikama al qawarin ba.

nan da nan hankalin mashkhur ya tashi, sabida yasan al qawarin da dady yake nufi, ba kowana al qawari bane face na sakin zahra. amma dakewa mashkhur yayi tare da cewa haba dady ka yarda dani mana, wlh tinda mukazo rasha ban ta6a dukan taba ai gata nan ka tambayeta ya qarasa maganar yana Zubawa zahra manyan idanunsa tare da taka qafar zahra da qafarsa alamun gargad'i. baki na rawa zahra tace eh wlh dady tunda mukazo bai ta6a dukana ba.

nan da nan dady da ammi suka amince da maganar sabida sunji mashkhur yayi ranstuwa kuma sunsan bai cika rantsuwa akan qarya ba. mashkhur har cikin zuciyarsa yayi rantsuwar sabida yasan bai ta6a dukan zahra ba tun sanda Suka zo rasha sai dai ya bata punishment d'in mugunta kala- kala. itama zahra tayi mamaki wayon irin na mashkhur da ya rantse bai ta6a dukan taba, al halin kuma yana bata horo mai kyau.

ammi ce ta qara da cewa zahra amma naga kin rame ko baki da lpy ne?, aa ammi lpy ta qalau kawai kinsan kad'ai cine yake damuna shiyasa gida shiru, komai ni kad'ai nake, bacci ma da gyar nake sabida na saba kwanciya da ilham da amir shiya kikaga haka kawai kewarku nake. zahra ji tai mashkhur ya sake taka mata qafar da qarfin gaske kawai mazewa tai dan haka ba shiri tai shiru, nan da nan dady ya fara jefawa mashkhur wani irin kallan wanda ba wanda zai fahimci wani irin kallo ne sai mashkhur din da akeyiwa.

fuska ba annuri ammi tace kiyi haquri zahra komai lokacine wata rana sai lbr, murmushi dole zahra ta kwakwalo tare da cewa no ammi ai ba komai na saba, zahra kawar da maganar tai da wai ina hjy kakane?. gyara zama ammi tai tare da cewa! wlh hjy kaka tayi tafi mutuwa akayi mata a kaduna shiyasa, amma tace in munyi waya na gai sheki kuma tace da fatan kina addu'o'i data baki ko?, shiru zahra tai tana naziri dan ita tama manta da wasu addu'o'i da hjy kaka ta bata sai yanzu ta tuno da su.

muryar dady taji yana cewa kin manta koh? gyad'a kai zahra tai alamun ehh, ammi ce tace to yanzu ai mun tuna miki, ki dena wasa da addu'a da sallah, da fatan kina azzukar d'in safe da yamma ko?. da sauri zahra ta d'aga kai tare da cewa inayi kullum, dady ne ya cafe zancan da cewa! yauwa mamana haka akeso ki rinka kula da addinin ki gaba da komai da fatan kina maraji'a ko? ehh dady inayi mana, yauwa mamana, sanan kuma ki mai da hankali a makaranta. tom dady in sha ALLAH, daga haka so kayi sallama amma dady yace mashkhur ya kira shi zasuyi magana.

laptop d'in tana katsewa mashkhur ya saki ajiyar zuciya, har yanzu qafar mashkhur tana kan ta zahra sabida mugunta bai d'aga ta ba, amma ba wani sosai ya taka taba kawai dai ya d'orata ne, dan shi harma ya manta. rai a had'e mashkhur ya juyo ya kalleta tare da cewa kee dama 'yar iska ce ko? ya fad'a tare da zuba mata ido kamar zai cinye ta. jiki na rawa zahra ta girgiza kai tana cewa aa wlh niba 'yar iska bace, harara ya watsa mata tare da sake taka qafarta da qarfin yana cewa! to me kike nufi da ke kad'ai kike kwana da ke dawa kikeso ki kwana.

cikin rashin fahimtar abinda mashkhur ya fad'a zahra tace wlh ba abinda nake nufi na rasa mai zan cewa ammi da tace na rame shi yasa nace mata haka, amma wlh nibada wata manufar na fad'a ba. shiru mashkhur yayi yana qarewa bakin zahra kallon wanan da yayi jajawur gashi sai rawa yake alamun tsoro. mashkhur da yaga zahra bata fahimci inda ya dosav ba kuma da gaske take bada wata manufar ta fad'a ba bai qara jan maganar ba shiru yayi ya tafi dogwan tinanin, ya zasu kwashe da dady inya buga mai?.

zahra kuwa zubawa qafar mashkhur ido tai wanda ya d'ora akan tata, fara ce qafar tass dan harma tafi, fuskar mashkhur d'in haske ka faracan nan a jere masha ALLAH farare tass, irin farcan ammi ne amma na mashkhur d'inma haryafi kyau, sai wani mamotsa faracan yake kamar mage, haka nan mashkhur yaji yana jin dad'i shafa qafar zahra da yatsun sa, dan shi sam yama manta qafarsa tana kan ta zahra dan ya tafi duniyar tinani. wani iri zahra takejin abinda mashkhur yake mata da yatsunsa, tanaso ta janye qafarta amma ta kasa sabida qafar mashkhur din tana da nauyi.

ajiyar zuciya da zahra ta sauke ne yasa mashkhur ya dawo daga dogwan tinanin daya tafi, kallan zahra mashkhur yayi wanda ta jiqe da gumi jikinta sai rawa yake, mamaki ne ya kama mashkhur sabida ganin yarda zahra take gumi, kuma har yanzu bata bar wajan ba tana zaune a kusa da shi. murya a kausasashe mashkhur yace kee me kikeyi anan?, dan shi mashkhur yama manta da qafar zahra da yake wasa da ita da yatsunsa, shi dai kawai laushi yakaeji, kuma yana jin dad'in wasan da yake da yatsunsa a hakan.

hannu na rawa zahra ta nunawa mashkhur qafarsa da take kan qafarta, a hankula mashkhur ya sauke idonsa a inda zahra take nuna mai. karaf idon mashkhur ya sauka akan qafarsa daya d'ora akan ta zahra Yana wasa da ita, gaban mashkhur ne ya fad'i rass, dan shi harga ALLAH ya manta ya d'ora qafarsa akan ta zahra. da sauri mashkhur ya dena wasa da yatsunsa tare da saurin janye qafar tasa daga kan ta zahra tai.

kawar da kai mashkhur yayi jiki ba kwari ji yayi sam bai ji dad'in hakan ba, zahra kuwa yana d'agata ta miqe da sassarfa ta wuce bedroom d'in ta hanunta riaqe da farin hankicif d'in. wani siririn tsaki mashkhur yaja nan da nan haushin kansa ya rufe shi, dan shi bai ta6a tinanin zai aikata Hakan ba, ko ta kan wayarsa da laptop din shi bai biba ya wuce d'aki, dan sam bayaso ya bigawa dady waya yasan abinda zai cemai! bazai wuce ya ringa kwana da zahra a bedroom d'aya ba kuma shi bazai ta6a iya hakan ba.

ZAHRA.......

Tana shiga bedroom d'inta ta fad'a kan gado ta saki wata ajiyar zuciya, gumi ne yake tsatsafo mata kota ina, haka tai ta sauke ajiyar zuciya tayi lamo akan gadon kamar mai bacci, a hankula zahra take jin fitar wani abu mai d'imi ta gabanta wanda ita kanta bata san mene ba, dan pant d'in tama harya fara jiqewa, zahra dan tayi tinanin jini ne ma. jiki ba kwari zahra ta miqe ta shige toilet, tana shiga ta ciro pant d'in ta, gabanta naya fad'i rass, ganin abinda yake jiki pant din.

ita a tunaninta jini ne, amma sai taga wanan ruwan wanda ita kanta bata san name ba, tasan dai a baya ta ta6a irin hakan, har ammi ta koya mata yanda ake wanka in ruwan ya futo, amma zahra bata san sabida mai yake futuwa. ruwan Kamar an jiqa ruwan ku6ewa d'anya haka yake futowa fari tass ya gyauqi, pant din zahra ta cire sanan ta tsarkake jikinta yarda shari'a ta tanadar, bayan ta gama tai wanka ta futo d'aure da toilet, kaya ta sanya a jikinta sanan ta fara bin cike kwabar dan neman takardar da hajiya kaka ta bawa zahra.

can qasan kwaba zahra taga takar da, duk tabi ta harqatso da kayan ta, a jiye takar dar tai a gefe, sanan ta fara qoqarin mai da kayan data futo da su, bayan ta gama ta dawo gefan gado ta zauna sanan ta fara bud'e takardun. addu'o'i ne a ciki wanda hjy kaka ta rubutawa zahra ta ringa yiwa mashkhur,wai dan ya shiryu. one by one zahra ta fara bin addu'o'i, tana karanta wa, da wanda zata ringayi mai da safe da yamma da kuma wanda zata ringa mai in tayi sallah.

zahra tafi minti 20 tana karanta takar dan nan, sai da ta haddace addu'o'i tass sanan ta ajiye takaddar. duk jikin zahra ya mutu bacci kawai take son yi, dan haka jiki ba kwari ta wuce kan bed ta kwanta, yau zuciyar zahra fas take da yake taga 'iyayanta da'yan uwanta. tana cikin wanan tinanin taji qamshin turaran mashkhur ya bud'e ta ko ta ina, lumshe ido zahra tai, dan harga ALLAH tana qaunar qamshin turaran nan.

zahra ji tai qamshin yayi yawa dan haka bud'e idon ta tai, karaf idon ta ya sauka akan farin hankicif d'in da mashkhur ya bata dan ta goge fuskarta. jiki ba kwari zahra ta miqa hannu ta d'auki hankicif d'in, duk wani abu daya danganci mashkhur zahra bata qaunar shi amma haka nan, zahra taji tana matuqar qaunar farin hankicif d'in, hannu na rawa zahra ta d'ora hankicif d'in akan fuskar ta, lumshe ido tai kawai sabida dad'in da taji, har cikin kwakwalwarta zahra take jin qamshin nan. miqewa zahra tai taje tayiwa hankicif d'in nan kyakyawan 6uya...

NIGHT........

Juyi mashkhur yake tayi kawai sam ya kasa bacci koya ya rufe ido tunowa yake da yarda ya ringa wasa da yatsun qafarsa akan lalausar qafar zahra, sam mashkhur bayajin dad'in hakan wani irin haushin kansa dana zahra ne ya rufe shi, sai wani dogwan saki yake ja, ji yake Kamar ya aika ta wani haramci, ko da yake shi a wajansa haramci ne sabida tsanar da yakewa zahra, zuciyar mashkhur ta kasa samu nutsuwa har sai da ya afa kayan mayansa sanan yaji dai-dai ba jimawa bacci ya kwashe shi..............

kuyi haquri kwana biyu kunjini shiru wayata ce ta samu problem shiyasa, amma in sha ALLAH, daga yau zan cigaba da yi muku posting.
ina miqawa masoyana dubu godiya masu bibiyar littafin adalilinta, ALLAH ya barmu tare.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

my number 09162226240

                      *page 66*
        
                             Typing..........

Juyi mashkhur yake tayi kawai sam ya kasa bacci koya ya rufe ido tunowa yake da yarda ya ringa wasa da yatsun qafarsa akan lalausar qafar zahra, sam mashkhur bayajin dad'in hakan wani irin haushin kansa dana zahra ne ya rufe shi, sai wani dogwan saki yake ja, ji yake Kamar ya aika ta  wani haramci, ko da yake shi a wajansa haramci ne sabida tsanar da yakewa zahra, zuciyar mashkhur ta kasa samu nutsuwa har sai da ya afa kayan mayansa sanan yaji dai-dai ba jimawa bacci ya kwashe shi..............

MORNING.......

A hanzarce zahra ta shiga kici domin samarwa kanta abinda zataci, yau dankalin turawa take sha'awa dan haka a hanzarce ta kwaso shi ta fara ferayewa. tana gama ferayewa ta zuba mai gishiri da magi ta fara soyawa tana gama soyawa ta d'ora ruwab zafi, ko eggs zahra bata tsaya soyawa ba shayin yana dawuwa ta zuba a cup sanan ta kwashi kayan abincinta ta wuce bedroom d'in ta.  tana zuwa ta zauna a gefan bed ta fara ci abincin, bayan ta gama ci unifrom ta fara sawa dama tun bayan da tayi sallar asuba tayi wanka.

tana gama shiryawa ta zauna a gefan gado ta fara karanta wannan addu'o'i da hjy kaka tace tayiwa mashkhur da safe, bayan ta gama jakarta ta d'auka sanan tai hanyar fita daga bedroom d'in. kamar had'in baki zahra tana futa shi kuma ahmad yana qarasowa dan haka ba 6ata lokaci suka wuce school.

MASHKHUR.........

sallahr asuba ma da kyar mashkhur ya iya yi duk jikinsa a mace yake, dan har wajan qarfe goma na safe bai tashi daga bacci ba.  knockg d'in gidan da akeyi ne ya farka da mashkhur daga nanauyan bacci da yake yi, jiki ba kwari mashkhur ya miqe ya shiga toilet yayi wanka sanan yayi brush, har lokacin da mashkhur ya futo daga toilet ba'a dai na buga qofar gidan ba, a hanzarce mashkhur ya shirya, yana gama sa kayan nasa ya fuce falo a hanzarce, ya nufi qofa.

mashkhur yana bud'e qofar sukayi 4 eyes da zee, nan da nan mashkhur ya had'e rai tamau tare da cewa! kee mai ya kawo ki gidan nan? fuska ba walwala mashkhur ya jefawa zee tambayar, ya mutsa fuska zee tai cikin mamaki tace au tambayata ma kake mai ya kawo ni baya jiya kayimin al qawari na dawo, bayan kuma na dawo kaqi bud'e qofar, tsaki mashkhur yaja tare da fara qoqarin rufe qofar falon. da sauri zee ta dagatar da shi ta hanyar sa hanunta da tayi a tsakakanin qofar fuska a marai ce zee tace pls honey kar kai min haka.

shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba, qara karyar dac murya zee tai tare da cewa haba honey kayi haquri duk abinda kakeso zanyi na haqura da sex d'in. nan ma mashkhur bai ce mata komai ba juyawama yayi ya barta a tsaya a wajan, da sauri zee ta rufawa mashkhur baya tana tai mai magiya.
      da kyar zee ta shawo kan mashkhur, sai da mashkhur ya gindaya mata shara dod'i kamar haka!!.

yace mata karta sake ta qarayi mai zancan suyi sex kuma ko da wasa karta qara kallan zahra da niyar sha'awa, ko kuma tayi niyar lesbian da ita. yamutsa fuska zee tai cikin kishi take tambayar shi sabida mai zai hanata yin lesbian da zahra? tinda ba 'yar uwarsa bace hours gil d'in sace. zaro ido mashkhur yayi a zuciyarsa yana saqa tabbas in zee tai lesbian da zahra shi zata jefa a matsala, dan yasan dady sai iya sallama shi ammi kuma zata iya yimai baki kuma yasan dady ba zai raba auran su da zahra ba,, kai koma ba haka ba mashkhur bazai so zee ta lalata zahra ba, sabida hakan ya sa6awa addinin muslinci.

a fili kuma ce mata yayi kawai shida koda wasa karta yiwa zahra sabida ba kyau a addinin muslinci. a ala dole zee ta yarda da shara d'an mashkhur. sai da mashkhur ya qara da cewa zee! wlh ko kallan da bai gamsu da shi tai wa zahra da niyar lesbian tofa bashi ba ita, haka dai zee ta amince da tsauraran dokokin mashkhur da su zauna lafiya, duk da kuwa tinda ta d'ora idonta akan zahra take sha'awar ta. shima nashkhur ya lura da hakan sabida yaga zee tana yiwa zahra wani irin kallo, tinda zee tace mai ita 'yar lesbian ce ya gane abinda zee take nufi da kallon zahra,  shiya ya ja mata sharad'i karta jefa shi a matsala........


tom  haka rayuwa tai ta juyawa tsakanin zahra da mashkhur, har yau mashkhur bai dai na zalintar zahra ba, sai ma abinda yayi gaba. itama zee ta mayar da zahra kamar jaka kullum aiki take sata amma ko da wasa batayi gigin gwadawa zahra lesbian ba, shima mashkhur yana taka tsam-tsam da hakan. 6an garan zahra ta mayar da hankalinta da karatunta, sam bata wasa da addinin ta da karatun qur'ani,  kuma har yau tana yiwa mashkhur addu'o'in hjy kaka duk da kuwa har yau mashkhur bai dai na shaye-shaye da kula zee ba.

8 montly a go..

bayan wata takwas.
yanzu wata su zahra da mashkhur takwas a rasha, dan yanzu zahra harta saba da zaman rasha sosai. har yau mashkhur bai mayar da hankalin sa a school ba, koyay niya baya iyawa sabida kullum zee qara lalata shi take da shaye-shaye da fashin school, mskarantar ma ba kullum take zuwa ba, sai yayi niya, zahra kuwa tun abin baya damunta harya fara damunta. 'yan kwana kin nan zee da mashkhur sun takurawa zahra musamman ma mashkhur da ko kwakwaran motsin da bai gamsu da shiba zahra tai jikinta sai ya gaya mata, dan yanzu zahra harta fara gazawa akan haka ta fara tinanin d'aukar fansa dan bazata tsaya bakin cikin mashkhur da zee ya kashe taba musamman ma mashkhur d'in............

yau ta kasance asabar mashkhur yana bedroom d'in yana bacci, da yake basu da lectures zahra kuwa tana fallo sai fama gyara gidan take. tana gamawa ta wuce bedroom d'in ta tayi wanka, tana futowa ta shirya cikin doguwar rigarta ta atanfa. haka nan zahra taji gaji da zama d'aki dan yanzu ba sosai take futawa fallon ba sabida takurawar da mashkhur yake mata. yau zahra ji tai bazata iya jure zaman bedroom d'in taba sai dai  ko mai zai faru sai da ya faru.

mayafinta ta sunkuta ta yafa akan ta sanan ta fuce fallon, tana zuwa falo ta zauna a akan kujera, haka nan zahra taji tana sha'awar kallo duk da kuwa mashkhur ya hanata kunna tv d'in. ba 6ata lokaci zahra ta fara kunna kallon dan ita yanzu zuciyarta ta qeqashe sam ta dena tsoran muguntar yaya mashkhur. zahra tana gama jona tv ta d'auki rumot, ta haye kan kujera ta zauna ta d'ora qafa d'aya kan d'aya.  Zahra batafi minti biyar da fala kallon ba taji ana knocking d'in qofar fallon,  zahra tayi tunanin ahmad ce ko zee, dan haka mayafin ta d'auka ta nufi hanyar bud'e qofar.


A dai-dai lokacin mashkhur, ya kama hanyar futowa daga bedroom d'in shi,  tun daga baki qofa mashkhur ya daskare ganin tv a kunne,  azuciyarsa yace lalai iskancin yarinyar nan yayi qarfi,  wato harda kunna tv wlh yau sai jikin ta ya gaya mata.  Ai mashkhur yana gama fad'in hakan yaji zahra ta saki wani uban iwu,  wanda sai daya razana shi,  ciki na sasarfa mashkhur ya fara tafiya dan ganin mai ke faruwa?,  ai karaf idon mashkhur ya sauka akan zahra data qanqame dady kamar bazata cika shiba,  d'aya 6angar kuma ilham ce da yaya abdul a tsaye suna saki murmushi sai kuma amir da abdul yake riqe da hanunsa.

Shima mashkhur murmushi ya saki a fili,  cikin sauri ya qarasa inda suke tsaye,  dady ne yace haba mamana ki cikani mana sai kace wanda zan gudu ya qarasa magar yana shafa bayan zahra fuska d'auke da murmushi.  Dariya zahra tai ta saki dady ta nufi yaya abdul,  zahra batai wani dogwan tinani ba tai hugg d'in yaya abdul.   mashkhur kuwa mamaki ne ya kama shi,  amma bai nuna ba sai ya danne,  zahra bata wani jima a jikin yaya abdul ba ta sake shi ta koma kan amir ta janyoshi tare da tsugunawa dai-dai tsayin sa,  dama lokacin da zahra ta bud'e qofar ilham ta fara rugumewa kafinma dady. 

Zahra tana tsugunawa amir ya fad'a jikinta suka rungume juna oyoyo auntyna cewar!  Amir,  itama zahra cewa tai oyoyo my amir I miss you.  6angar mashkhur,  kuwa shima zuwa tayi ya rungume dady,  amma shi cikin nutsuwa da hankali yayi ba  kamar yarda  zahra tai ba,  yana rungume dady ya sake shi tare da cewa!  Dady barka da zuwa da fatan kun iso lpy?  Cikin sakin fuska dady yace mun iso lpy qalau kuma da fatan na sameku lpy?,  ehh dady kun same mu lpy qalau,  Shima mashkhur qarasawa wajan dady yayi tare da rungume shi, sai dai shi mashkhur rungumar hankali yayiwa dady ba irin ta zahra ba,  kuma yana rungume ya sake shi tare da cewa!  Dady sanunku da zuwa da fatan ko iso lpy ya hanya?.

murmushi dady yayi tare da cewa!  Alhamdulilah mun iso lpy kai ma da fatan mun sameku cikin qoshin lpy?,  ehh dady kun same mu lpy qalau.
Shima abdul qarasowa yayi wajan mashkhur d'in wani tatausan murmushi mashkhur da abdul suka sakarwa juna tare da rungume junansu cikin farin ciki.  Yaya mashkhur I miss wlh cewar!  Abdul,  wata siririyar dariya mashkhur yayi tare da sakin abdul yana cewa!  Miss you to my realy bro.

Zahra kuwa sakin amir tai ta rufo qofar sanan ta dawo ta sake rungume ilham a karo na biyu.  Bayan sun gama hug d'in junan nasu qarasawa sukayi suka zauna akan kujere,  ilham kuwa wajan yaya mashkhur ta qara ta rungume shi tare da cewa yaya mashkhur I miss you, murmushi mashkhur yayi tare da cewa miss you too my sis,  daga haka suka saki juna sanan mashkhur ya bud'awa amir hannu tare da cewa amir common,  da sauri amir ya qarasa wajan yaya mashkhur,  mashkhur kuwa d'aukan sa yayi nan da nan amir ya fara dariya.

Tofah ai tsayawa na gaya muku farin cikin da zahra ta shiga a yau 6ata baki ne dan harna qarasa page d'in nan bazan gama rubutawa ba,  dan yau zahra tayi farin ciki sosai.  Kafin kace kwabo hira ta 6alle tsakanin su zahra da dady dan ko kwakwaran motsi basa iyayi,  ilham da zahra kuwa suna maqale da juna kamar cewa akayi za'a rabu yanzu.  Mashkhur ne yace wa dady! Dady wai ina su haidar da faruq?  Gyara zama dady yayi tare da cewa! suna school jarabawa zasuyi shiyasa bamuzo da suba,  dady yana fad'in hakan mashkhur yace ruma da rukayya fa? Jimm dady yayi can kuma yace suna gida,  mashkhur yana so ya tambaya sabida mai ba'a zo dasu ba,  amma ya lura dady baya san maganar shi yasa yayi shiru.

Mashkhur kallan dady yayi tare da sake cewa! dady abdul mai zakuci ayi muku oder?,   wani kallo dady ya watsawa mashkhur tare da tace habawa nazo gidan 'yata guda kace kuma zakayi min oder mai kake nufi da hakan ne?  Ka bakaso naci girkin 'yata ai yau ni girkin mamana zanci ko mamana,  dady ya qarasa maganar yana sauke idonsa akan zahra da take maqale da ilham.  Murmushi zahra ta saka tare da  cewa ehh dadyna hakane,  abdul ne ya cafe zancan da cewa ehh gaskiya dady ya fad'a yau girkin matar yayan mu zamuci.

Zahra da mashkhur har suna 'yar rige-rigen watsawa abdul wani kallo mai wuyar fassaruwa,  wani siririn murmushi abdul ya saki tare da cewa!  Yane ko

Please Login or Register in order to submit comment