Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mayafinta ta zaro ta yafa tare da fucewa daga bedroom d'in. Tana tifa bata tsaya ko inaba sai falo, mashkhur ta gani zaune baje da kwayoyi maye a gabansa, ga zee a gefe tana kallo riqe da remote a hanunta.

Kawar da kai zahra tayi tare da shigewa kicin. Haka zahra ta fara aikin dafawa zee pepper soup duk da kuwa batajin dad'i, tanayi tana tinanin halin da mashkhur yasa kansa a ciki na shaye-shaye. Sai da zahra ta d'auki minti talatin tana dafawa zee papper soup, duk gidan ya karad'e da kamshin, papper soup d'in zahra. Har lokacin zahra batajin dad'i jikinta kawai daurewa takeyi. Bayan ta gama pepper soup d'in joye mata tai a flask sanan ta kama hanyar fala domin kai mata.

Lokacin da zahra ta isa falo wajan zee har qasa ta stuguna, ta ajiye mata, sanan ta miqe domib barin wajan. Dawo ai baki gama yimin aikin ba, zee ta fad'a cikin isa da gadara, zahra kuwa ji tayi kamar ta wuce ta gyaleta, amma da ta tina a gaban mashkhur ne, da sauri ta jiyo tare da komawa gaban zee d'in ta stuguna. Girgiza qafa zee ta farayi irin cikakun 'yan barikin nan, tare da mai da kanta kan tv, tafi minti goma batacewa zahra komai ba.

Zahra kuwa damo sarkin haquri bata cewa zee komai ba tana tsugune a wajan, mura da ciwan kai ga zazza6i duk sun addafeta. Can zee ta juyo tacewa zahra!! Kije ki dafamin chip's da chiken papper, kuma ki hanzarta banasan jira, sai yanzu na tinama bana shan pepper soup. Ji zahra tai kamar ta kwallara uwar qara sabida tsabar baqin ciki, sam qarfin ta ya qare, tinda uwarta ta haifeta ba'a ta6a bata wahala irin haka ba, in aka cere dukan da mashkhur ya ta6a yi mata akan ta fasamai laptop. Sai d'aure tan da yayi jiya a taga sanyi yayi mata duka qafafuwanta suka kunbura, sanan ta fasa goshi.

Muryar mashkhur ce ta dawo da zahra daga tinanin data tafi!! Kee ba magana akeyi miki ba ko sai jikinki ya sake gaya miki. Zahra tanajin haka ba shire ta miqe ta shige kicin da sauri. Ranar zahra tasha baqar wahala kafin ta kammalawa zee chip's da chiken papper, ni kai na amina bayero bazan iya rubuta muku wahalar da zahra ta shaba, zahra bata ta6a zatan tana da juriya ba sai yau duk da kuwa bata saba aikin wahala ba. Haka zahra ta d'ibi chip's da chiken papper ta nufi hanyar falo domin kaiwa zee abinci,, tafiyama da gyar zahra takeyi.

Zahra tana direwa zee chips d'in zee ta miqawa zahra key d'in motarta tacewa zahra jeki motata taqasa ki bud'e ki dakko min jakataa, haka zahra ta kar6i key d'in nan hannu na rawa, ta miqe da kyar ta nufi hanyar futa dag falon. Haka zahra ta fita da kyar, ta zubawa matatakalar benan ido tana tinanin taya zata fara sauka tana cikin wanna halin?. Sai da zahra tafi minti biyar a haka can tai ta maza ta fara sauka dafa kan step d'in benan, tana sauka tana hutawa, idan ta sauka daga kan step uku sai ta huta a haka ta qarasa sauka daga step d'in, ga benan da mugun tsayi.

Bayan ta sauka sai data sake wutawa kafin ta nufin inda motar zee d'in take. Duk da motocin ukune a wajan zahra batasha wahalar gane ta zee ba da yake tasan motar mashkhur kuma tasan ta ahmad. Haka zahra ta bud'e motar ta d'auki jakar zee d'in sanan ta juya. Da kyar zahra take iya tafiya sabida tsabar azabar da takeji a jikinta, tana zuwa bakin matatakalar ta zube wanwar ta zauna a wajan sabida tsabar azaba. Kamar daga sama zahra taji muryar Ahmad yana cewa qanwata lafiya dai koh? Da sauri zahra ta d'aga kai alamun ehh.

Girgiza kai Ahmad yayi tare da tsugunowa gaban zahra yana cewa haba qanwata karkimin qarya mana kalli yarda fuskarki ta kunbura goshin ki ya fashe jikinki duk yayu jajawur, tundaga nesa fa na hangoki kina layi kamar zaki fad'i kum kicemin kina lafiya. Murya a raunane kuma a dashe kamar zahra zatai kuka tace yaya ahmad bani da lafiya, kai na ciwo ga zazza6i ga kuma mura da take damuna yanzuma jiri nakeji. Innalilahi amma baki gayamin ba tun yaushe ne baki da lafiya? Murya na rawa zahra tace tun jiya.

Qanwata ki gayamin gaskiya mashkhur ne ya dakeki koh? Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa bai dakeni ba. Kallan tuhuma ahmad ya watsawa zahra tare da cewa haba qanwata kalli goshinki ya fashe ga hannayanki duk sunyi shati, kuma kice ba dukanki yayi ba, bari naje na same shi, wlh sai ya gayamain dalilin dukan ki da yayi, ai dady amana ya bani ke bazan zuba ido naga yana zalintar kiba, ya qarasa maganar yana qoqarin miqewa. Da sauri zahra ta riqe rigar ahamd cikin kuka take cewa dan Allah yaya ahmad ka rabu dashi wlh yanzu kayi mai magana dukana zai yi, kuma ni wlh ba dukana yayi ba pls yaya ahmad ka rabu da shi, karkai mai magana, sai yayi tinanin ni na gayama wani abun.

Dawowa Ahmad yayi, nan da nan tausayin zahra ya kamashi, cikin raunaniyar murya yace haba qanwata, taya zakice mashkhur bai dakeki ba alhalin ga alamun duka a jikinki, karfa shurunki da haquri ki su cutar da ke, Wlh in baki gayamin abinda mashkhur yayi miki ba yau zan gayawa dady abinda yake faruwa. Da sauri zahra ta d'ago tare da girgiza kai, tana cewa!! Aa yaya ahmad dan Allah karkai hakan sometimes yaya mashkhur yana yawan cewa ADALILINA yake fad'awa cikin wani hali ADALILINA iyayansa suka juya mai baya, karka qara jawowa ya tsaneni fiyeda dah pls yaya ahmad karkai hakan, banaso ADALILINA yaya mashkhur ya qara sumun sa6ani da iyayan mu.

Cikin mamaki ahmad yake sauraran abunda zahra take gayama masa, Dan me mashkhur yake cewa ADALILINTA komai wasu abubuwan suke faruwa da shi? Iyayamsu kuma?. Tambayar da ahmad yayiwa kansa kenan amma ba amsa. Cikin kokwanto ahmad yace zahra wai mene dangatakar ki da mashkhur ne haka yake azaftar da ke? Koma wana lefi kikayi masa a rayuwa, taya abubuwa da dama zasu faru da shi ADALILINKI, kuma mai ya ta6a faruwa da mashkhur ADALILINKI?. Ni dai wannan tambayoyin susuka shigemin duwu.

Yaya ahmad kayi haquri a halin yanzu bazan iya yi maka bayani ba, ni dai nasan yayana ne mashkhur kuma iyayanmu d'aya da dashi, kuma ban ta6a yimai wani mumunan abuba a rayuwarsa ba shine abinda kawai na sani. Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa it's okay qanwata, yanzu dan ALLAH ki dena kuka kinji? Jeki ki d'auko hijab d'in ki na kai ki hospital. Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aaa yaya ahmad kawai ka barshi, karna yiwa yaya mashkhur lefi. Kai mashkhur dai mashkhur dai, wai wanna mashkhur d'in dodon kine ko kuwa sai kace shi ya halliceki, look qanwata bazaki zauna da cuta ba, kuma ba abinda zai miki, ai ni nace ki zo mu tafi ko zo muje na rakaki taso, bazan bari yayi miki komai ba in sha ALLAH.

Da kyar zahra ta iya miqewa, suka fara hawa kan step d'in ita da Ahmad. Lokacin da suka shiga basu samu mashkhur a falon ba zee kawai suka samu tana cin abincin da zahra ta dafa mata. Nan da nan Ahmad ya d'aure fuska ya fara gallawa zee harara dama tunda jininsu bezo d'aya da zee ba, koh ba'a gaya masaba yasan zahra ce tai mata wannan girkin sabida yasan ba abinda ta iya dafawa sai iskanci, wata uwar harara ya ringa watsa mata. Zee kuwa tana ganin ahmad ta sha jinin jikinta sabida tasan sam basa good time da shi ko a school.

Zahra kuwa zuwa tai ta direwa zee jakarta sanan ta shige bedroom d'inta. Tana shiga ta wuce toilet ta wanke fuska sanan ta futa ta canza kaya tasa hijab da turare ta fuce daga bedroom d'in. Tana fita falon ba 6ata lokaci suka fuce ita da Ahmad, suna sauka Ahmad ya shiga part d'in sa ya d'auko key d'in motarsa, sanan suka fuce daga gidan a motar. Hospital mafi kusa suka nufa, lokacin da sukaje ba 6ata lokaci akyiwa zahra gwaje-gwaje, kuma akan gano abinda yake damunta.

Ance sanyi ne ya shigeta sosai sai kanta da ya bugu shine ya kawo mata zazza6i da ciwan kai harma da jiri. Sai da aka kwantar da zahra akayi mata qarin ruwa, lokacin da akayi mata alluran bacci, Ahmad tafiya yayi ya suyo mata abinci kala-kala a reswerrens Tun wajan qarfe biyar aka yiwa zahra allurai da qarin ruwa ta kwanta bacci bata tashiba sai takwas na dare. Lokacin data tashi taji dad'in jikinta sosai duk sai taji ba abinda yake damunta sai mura, kuma taci abincin da ahmad ya suyo mata sosai.

Da haka likitocin sukace zahra ta kwana a asibiti, amma zahra tace aa sabida tsabar tsoran mashkhur, haka dai ahmad da likitocin suka haqura suka sallamota, abinka da likitocin turawa ba takura. An bata magunguna kala-kala, kuma ance ta ringa samun bacci kuma ta dai na zama a waje mai sanyi sabida kar cutar sanyi ta kamata. Bayan sun futo daga asibiti sai da ahmad ya tsaya ya siyarwa Zahra bargo sabida sanyi wai ta ringa lili6a. Nikuwa amina bayero nace Allah sarki Ahmad bawan Allah bai san ba rashin shiga bargo bane kawai shika-shikan mugunta irin na mashkhur ne.

Suna cikin tafiya ahmad ya juyo ya kalli zahra da take gefansa yace qanwata yanzu yaushe zan fara kai ki school, yauma nazo nai ta jiranki baki futoba ashe baki da lafiya, harma muku wuce makaranta ni da mashkhur, amma kinga ya dawo da waccan yarinyar zee. Shiru zahra tayi azuciyarta tace wai dama zee 'yar makarantar suce?. A fili kuma tace zuwa gobe ma zan iya fara zuwa in sha ALLAH. Girgiza kai Ahmad yayi tare da cewa aa qanwata kinga fa baki da lafiya gaskiya ki bari sai kin samu sauqi sai na fara kai ki.

Ah yaya ahmad nifa banason zaman gida ni ka dai ba dad'i kwarama na fara zuwa makarantar. Tom shikenan qanwata amma dai ki bari jibi sai ki fara zuwa kafin nan kin warware koh, gyad'a kai zahra tai tare da cewa tom shikenan ALLAH ya kaimu, Ahmad ya amsada ameen daga haka ba wanda ya sake cewa komai har suka qaraso gida.
Misalin qarfe tara na dare suka shiga gidan Ahmad ne ya d'aukarwa zahra bargwan daya siyi mata da yake bargonn yana da nauyi sosai.

Ita kuma ta riqe laidai abinci da maganin da ya suyo mata, ba laifi ahmad ya kashewa zahra kud'i. Suna zuwa bakin qofar zahra ta fara kwankwasawa, cikin zolaya ahmad ya kalli zahra yace aa qanwata ki biga a hankula kar dodonki ya futo ya zane mu fa. Dariya zahra tayi tare da furta to yaya ahmad ngd sosai da hidima, tana gama fad'in haka mashkhur ya wangale qofar, da sauri zahra taja da baya sabida tsabar tsoro.

Ahmad kuwa girgiza kai yayi tare da cewa hmm ai sai ka bamu wuri mu wuce koh? Ya mutsa fuska mashkhur yayi yana mamakin tare da matsa musu su wuce, mamki yake taya akai aham ya futa da zahra shi bai sani ba ko yaushe suka fita oho shi duk a tinaninsa zahra tana cikin gidan. Haka ahmad ya shige zahra tana biye a bayansa jikinta sai rawa yake sabida tsoran mashkhur, dan tasan yau Allah ne ka dai zai kwace ta. Zahra tana had'a ido da mashkhur ya watsa mata kallon wai ke munafuka koh, harda wani abinci ya siyo miki da yake baki saba ciba, wlh jikinki bai gama gaya miki bane, harda bargo da yake baki ta6a shiga bargo ba koh?.

Ahmad ya lura da irin kallo da mashkhur yake watsawa zahra, jijina kai kawai yayi yana mamakin hali irin na abokin nasa. Zahra kuwa nan da nan ta kama hanyar tafiya bedroom d'in ta sabida tasan jikinta yana gab da qara wani tsami. Ahmad ma binta yayi a baya domin a jiye bargon daya suyo mata, suna shiga Ahmad ya ajiye mata bargon ko sakan baiyi ba ya fuce daga bedroom d'in ya koma falo wajan abokina nasa. Tun kafin ahmad ya kai da zama mashkhur yace Ahmad wai sabida mai ka cika shishigi ne?

Bana ce maka karka sake ka siyowa yarinyar nan abincin wajaba? Wana munafurcin tazo ta gayama? Ko ce maka tayi batacin abincin ne? Mashkhur ya qarasa maganar yana kafe Ahmad da manyan idanuwanta. Alamun tuwuma.
Murmushin yaqe Ahmad yayi cikin sakin fuska yace haba mutumina mai da wuqar mana, ni ba wani munafurci da zahra tayimin, kawai naga taji ciwo a goshinta ne, shina nace mata tazo muje asibiti, sam taqi amincewa sai da na ce zan bigawa dady sanan ta amince.

Qara had'e rai mashkhur yayi, tare da cewa to a ina ka had'u da ita da kaga ciwan inba zuwa tai ta gayama ba, kuma uwaban waye yace ka sai mata bargo. Ajiyar zuciya 6acin rai Ahmad ya sauke amma duk da hakan ya danne yacewa mashkhur!! Wanna shed'aniyar yarinyar wato zee, ita ta aiki zahra motarta ta d'auko mata jaka, kuma bargon dana siyo mata dana kai ta, asibitine akace tana zama a waje mai sanyi, ciwan sanyi zai iya kamata shiyasa na siyo mata.

Ahmad yana yiwa mashkhur bayanin nan bawai dan yana jin tsoran sa bane aa, kawai dai dan ya ceci zahra daga muguntar mashkhur karya dake ta. Mashkhur kuwa ya gamsu da maganar Ahmad sabida yasan ahamd bashi da rufi da zahra ta gayamai, ya kulleta a taga sanyi ya dake ta zai gaya mai. Sai da ahmad ya tabbatar zahra tai bacci bar gidan sabida kar mashkhur yayi mata wani abun.

6anran zahra kuwa Ahmad yana fucewa daga d'akin ta shiga toilet ta had'a ruwan zafi tai wanka, sanan ta d'auro alwala ta fito. Tana futowa ta zira kayan bacci tai sallar magriba da isha'i ta jiya data yau, bayan ta idar tai addu'o'i da lazimi, sanan ta d'auko abincin ta taci, tasha magungunan ta, daga haka ta haye kan bed domin yin bacci. Sam zahra ta kasa baccin kawai tinanin halin da zata tsinci kanta harna tsawan shekara guda da rabi take, ga kewar 'yan uwanta da iyayanta da hajiya kaka duk sun dame ta.

Sam zahra ta kasa baccin har qarfe shad'aya, tabbas zahra tasan in dai zata cigaba da zama da mashkhur sai ya kasheta, tunda gashi yanzu ya fara illata ta. Zahra tana cikin wanan halin taji ana kwankwasa mata qofa, shiru zahra tai tana tinanin waye? Can kuma zuciyar ta tace mata mashkhur ne dan haka shiru tai abinta, sabida tasan ba alkhairi ne ya kawo shiba, tanaji yana buga qofara amma tai shiru abinta. Kamar al mara zahra taji an turo qofar an shigo, dama ta manta bata sa mata key ba.

Zahra kuwa ba shiri ta qudindine a cikin bargo ta rintse ido kamar mai bacci. Duk tsoro ya kama zahra, gumi harya tsinke mata, tana cikin wanan halin taji alamun an canza hasken d'akin daga mai duwu zuwa mai haske. Nan da nan tsoro ya qara lulu6e zuciyar zahra, dan ta sandare ko motsi tama kasa, zahra batai aune ba sai ji tayi an janye bargon data lulu6a da shi! Ciki tsoro zahra ta bud'e idonta dan ganin waye? Karaf suka had'a ido da mashkhur ya zuba mata manyan idanuwansa.............

Shin mai mashkhur yazo yi d'akin zahra?

Ku a ganinku mai mashkhur zai zo yi a bedroom d'in zahra?

Kunsan dai baya shigowa d'akin zahra koh?

To mai ya kawo shi?

Sai ku biyoni a next page dan jin ya zata kaya.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240.

Typing............

* page 56*

Nan da nan tsoro ya qara lulu6e zuciyar zahra, ta ma sandare ko motsi tama kasa, zahra batai aune ba sai ji tayi an janye bargon data lulu6a da shi! Cikin tsoro zahra ta bud'e idonta dan ganin waye? Karaf suka had'a ido da mashkhur ya zuba mata manyan idanuwansa.............

Itama zahra zubamai ido tayi cikin tsoro tana jiran saukar duka, sai a lokacin ma ta lura da wayace a kunnansa. Wata uwar harara ya zuba mata ba shiri ta janye idanuwanta daga kallansa. Muryar mashkhur taji yana cewa okay dady ga tanan ai na tasheta, zahra tanajin an ambaci sunan dady nan da nan ta watsake batasan ma, sanda ta miqe zauna ba. Wata uwara harara mashkhur ya zuba mata, sai wani zaro mata ido yake, kamar zai cinye ta, kawar da wayar yayi daga kunnansa yayi nisa da ita ya sai-sai ta muryarsa.

Matso da bakinsa yayi kusa da kunan zahra Kamar wani mai rad'a yake maganar a hankula yace!! Ki kula da kyau karki sake ki gayawa dady maganar da bashikenan ba in ba hakaha hmmm ya qarasa maganar yana girgiza kai. Da sauri zahra ta d'aga kai alamun tom, sai da mashkhur yasa wayar a hans free sanan ya miqawa zahra wayar, kujera yaja ya zauna yana fuskantar zahra. Shiru zahra tai ta kasa cewa komai duk sabida kartayi wata maganar tayiwa mashkhur laifi.

Muryar mashkhur ce ta daki kunanta yana cewa kiyi magana mana! Ya qarasa maganar yana gallamata harara. Baki na rawa zahra tace hello, muryar dady taji ta rasa kunanta yana cewa mama? Wani tautausan murmushi zahra ta saki tare da cewa dady nah kai ne? Ehh mana mamana yakike? Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa dady ina lafiya qalau. Daga can 6anran dady yace aa mamana ki gayamin ko da wana abu? duk naji muryarki ta canza kamar wani abun ya faru da ke? Da sauri zahra ta saci kallon mashkhur karaf suka had'a ido, mashkhur sai zaro ido yake kana ganinsa kasan bashi da gaskiya, hannu ya sa a tsakiyar bakinsa yana girgizawa zahra kai alamun kartace komai.

Murya a tsorace zahra tace aa dady mura nake shiyasa kaji muryata ta dashe, zahra bata jira amsar dady ba ta kawar da maganar da cewa dady ina amminah da hjy kaka, da amir da ilham da su faruq? Gaskiya ina kewarsu sosai ka bani mu gaisa da su, mamana yanzu bana gida duk su faruq suna nan lafiya kullum ilham da amir suna kuka sabida bakya nan, amma banji kin tambayeni yayan kiba, ko kin manta da shine dady ya qarasa maganar cikin zolaya.

Murmushi zahra ta saki tare da cewa aa dady kai ma kasan ba zan manta da farinciki na yaya abdul ba, jiya munyi waya da shi, harma yace zai had'a ni da amir mu gaisa. Mamana da wasa nake miki ai nasan bazaki manta da yayan ki ba koh? Da sauri zahra ta gyad'a kai kamar dady yana kallanta. Cikin muryar shagwa6a zahra tace Dady nifa duk banajin dad'i zama gidanan ba ammi ba kai ba su ilham duk zaman gidan bayamin dad'i. Dariyarsu ta manya dady yayi tare da cewa to ke mene na damuwa da su abinda kina tare da mujinki mai zai dameki kuwa? Ya qarasa maganar cikin zolaya.

Da sauri zahra ta kalli mashkhur gani tai ya kawar da kansa yana jan wani siririn tsaki, zahra kuwa shiru tai basa sake cewa komai ba. Murmushi dady yai tare da cewa to mamana bawa surikin nawa wayar, hannu na rawa ta miqawa mashkhur wayar, duk tabi ta rud'e duk da ba ita tace mashkhur mijinta ba, tasan da kyar in batayi wani laifin ba. Tana miqawa mashkhur wayar taga ya tashi yabar wajan, hajiyar zuciya zahra ta sauke nan da nan taji farin ciki ya kamata dan ko ba komai yau taji muryar dady zatai bacci cikin kwanciyar hankali.

Mashkhur yana kar6ar wayar dady ya fara tuhumarsa kamar haka!! Mai suanna baba da fatan dai ba wani abun kayiwa zahra ba duk naji ta canza, anya ba dukanta kai ba?. No dady ai kasan bazan daketa ba nifa tinda mukazo ko hanunta ban riqe da niyar duka ba, wlh dady bana dukanta. Tom naji baka dukanta amma mai ya sata mura ko dai aikin ruwa kake sata ko kuma a falo take kwana? Aa dady kawai dai ruwan sanyi take yawan sha, kuma kasan garin da sanyi sosai so inaga kawai yanayin weather d'in garin ne kasan bata saba ba.

Hmmm mai sunan baba kenan nasan halin kafa sarai, karkai min qarya yanzu zaka rantse tinda kukazo rasha ko kallan banza bakayiwa mamana ba. Cije le6e mashkhur yayi tare da cewa haba dady ka yarda dani mana kasan dai bazanma qarya ba koh? Ehh mai sunan baba nasan bakai min qarya amma in dai akan mamana ne nasan zaka fara. Shiru mashkhur yayi dan yama rasa mai zai cewa dady, muryar dady ya stinkayo yana cewa da fatan dai duk abinda ya kamata kayi mata a matsayin mijin da kana yi mata kana sauke mata ko wana hakki da yake hanka koh?.

Haba dady wai mai zanyi matane naga dai duk abinda ya dace ka suyo mata ka siyo mata koh? Bata buqatar komai a gidannan da akwai komai fa. Look mai sunan baba karmu fara haka da kai mana kasan dai kai najimin kuma kayi karatun addini, kasan hakkin auren da yake tsakanin ka da matar ka koh?. Kamar mashkhur ya kwall ihun baqin ciki haka yaji, haba dady ai kasan bamuyi haka da kai ba kawai dai kacemin karna daketa, kuma duk abinda takeso na siya mata, haka fa kawai mukayi da kai nifa dady sam bana buqatar hakan.

Au lalai mai sunan baba, sai ma na gaya ma kenen, Tom kai in baka buqatar hakan itafa? Dady ya tambayi mashkhur, kamar mashkhur zai yi kuka yace dady itama bata buqata. Mai sunan baba haka ta gayama?, dady ba gayamin tai ba amma dai kasan qaramar yarinyace nasan wanan bazau demeta ba. Hmm mashkhur kenan har yanzu kana nan da halinka koh? Kawar da zancan mashkhur yayi da cewa amma dai dady har yanzu maganarmu tana nan koh?.

Cikin rashin sani dady yace waca maganar kuma? Dady alqawarin mu mana, wanda kace in mun dawo Nigeria zaka raba auren. Shiru dady yayi can kuma yace ehh alqawarimu yana nan, amma sai ka cika sharid'an dama gindaya maka. Ehh dady in sha ALLAH kafin mu dawo zan dai na,, okay mai sunan baba kaiwa mamana wayar!! Daga haka mashkhur ya miqe ya koma bedroom d'in zahra. Lokacin da mashkhur ya shiga bedroom d'in zahra

Please Login or Register in order to submit comment