Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dafa musu indomi comples da madara ya fara jiqa musu suna sha. 6an garan momy akan idon ta aka futar da ammi zuwa asibiti, a lokacin tana leqowa ta taga.

Bayan sun fita wata uwar dariya ta saki, tana gama dariyar tata, ta d’auki wayarta ta bugawa mahifiyarta ta bata labari, bayan sun gama magana da mahaifiyar ta, saratu ta sake bugawa ta gaya mata, duk cikin su dae ba wandda bai yi farin ciki da hakan ba. Bayan ta gama wayar ta wuce kicin ta dafa abinci, bayan taci ta qoshi ta kullo qafar part d’in ta shige d’aki da ita da rukee da aririyar ta suka fara bacci. Hmm nikuwa nace koh momy ta tuna da su mashkhur.

Haka dae momy ta wuni part d’inta a kulle ita da yaran ta biyu, in bandda farin ciki ba abindda yake damun ta, tana so taje part d’in ammi ta duba abdul, amma bata so taje mashkhur yace ta dafa musu abinci koh ta rarrashi ilham.
6an garan su mashkhur kuwa haka suka wuni cikin maraicin ammi.

Abdul kuwa yana riqe da zahran sa koh quda baya bari ya tab’a ta, shima mashkhur yana riqe da ilham, in kuma suna jin yunwa ya basu madara su sha, mashkhur yana so yayi wa su ilhma wanka amma bazai iyaba sabida bae san yandda akewa yara wanka ba, amma dae yayiwa haidar da faruq shikuma abdul yayiwa kansa. Tom fa har wajan qarfe tara na dare ba labarin su ammi, hankalin mashkhur da abdul ya sake tashi sosai.

Haka dae mashkhur yaje ya gyara kan gadon ammi ya kwantar da ilham da zahra, suma su haidar da faruq ya kwantar da su a d’akin su. Falo dae ya rage daga abdul sae mashkhur, sunyi jigum suna jiran dawowar su ammi. Har wajan qarfe goman dare basu dawo ba, a lokacin ma abdul har bacci ya kwashe shi a falo. Mashkhur kuwa kwata-kwata ya kasa bacci tinanin mahaifiyarsa kawai yake yi.

Wajan qarfe sha d’ayan dare dady ya shigo gidan, yana shugowa part d’in ammi ya nufa. A bud’e yaga qofar part d’in ammin, duk sae yaji ba dad’i sabida yasan da ammi tana nan bazata tab’a barin qofar part d’in a bud’e ba. Ciki a sanyaye ya shiga part d’in ammin, bayan ya shige ya kullo part d’in. yana shiga babban falon ba kowa a ciki, jiki ba kwari ya sake tura kansa qarafin falan da zai sada kowa da d’akin sa.

Mashkhur ya gani a zaune ya rafka uban tagumi ga abdul kwance a kusa da shi, da zauri dady ya qarasa indda su mashkhur suke, koh da ya qarasa mashkhur bae ma san yazo ba sabida ya tafi duniyar tinani. Sunan sa dady ya fara ambata mashkhur!!! Mashkhur!! A firgice mashkhur ya dawo daga tinanin da ya tafi. Yana ganin dady a gaban sa da sauri ya miqe tare da cewa dady ina ammi ya jikin nata?

Dady karka cemin ta mutu dan ALLAH, duk yabi ya dabarbarce ya koma abin tausayi. Duk sai yabi ya bawa dady tausayi, da sauri dady ya dafa kafad’ar mashkhur tare da cewa haba mae sunan abba ka kwantar da hankalinka kaji ammin ka tana nan da ranta bata mutuwar. Ajiyar zuciya mashkhur ya saki tare da furta Alhamdulilah.

Riqo hannun mashkhur dady yayi tare da zaunar da shi a kan kujera, bayan ya zaunar da shi shima ya zauna a kusa da shi. Kwantar da murya dady yayi kafin ya fara magana kamar haka!! Mae sunan babana ka kwantar da hankalinka, cuta ba mutuwa bace, kuma cuta tana kan kowa, dan haka ka kwantar da hankalinka ALLAH zai bawa ammin ka lafiya,

Ka dae na damuwa kamar haka, kaga kai ne babba ka ringa kwantarwa da qannan ka hankali in kana shiga damuwa ‘yan uwanka ma zasu shiga damuwa, insha ALLAH ammi zata samu sauqi ka ringa yi mata addu’a kaji?. D’aga kai mashkhur yayi tare da cewa insha ALLAH dady zanyi abindda kace. Jinjina kae dady yayi tare da cewa yauwa mae suna abba kaci abinci? Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa bana jin yunwa dady.

Girgiza kae dady yayi tare da cewa nasan tinanin ammi ne ya hanaka cin abinci, yanzu zanje nayi mana girki mae dad’i kamar na ammin ka, ya kai qarshan zancan yana murmushi tare da jan kumatun mashkhur, shima mashkhur d’in murmushi yayi tare da cewa tom shikenan dady amma fa zan tayaka?. Jinjina kae dady yayi, sanan yace tom shikenan bari naje na kwantar da abdul, kuma na canza kayan jikina.

Tom shikenan dady sai ka dawo, daga haka dady ya d’auki abdul ya kai shi d’akin su, bayan ya kwantar dashi ya wuce d’akin ammi domin canza kayan jikinsa. Yana futowa suka shiga kicin shida mashkhur suka fara girki. Kalaln mashkhur dady yayi tare da cewa momy ta kawo muku abinci ne, girgiza kai mashkhur yayi sannan yace ae momy yau ka part d’in nan bata shigo ba.

Jinjina kae dady yayi yana mamakin mugunta irin ta momy, sabida dady yasan momy tana sun tafi asibiti, sabida lokacin da suka futo da ammi yana ganinta tana leqowa ta taga, kuma yasan da ammi ce bazata tab’a haka ba. Sae da su dady da mashkhur sukayi minti talatin kafin su kammala girkin, jalaf d’in taliya da shayi mae kayan qamshi suka dafa. a farati d’aya dady ya zuba musu shida mashkhur, bayan sun futo suka zauna suka fara ci.

Bayan sun gama ci mashkhur ya kwashe farantan ya mayar kicin, sai da dady ya raka mashkhur har d’akinsu ya kwanta, sanan shima ya wuce dakin ammi. Yana shiga yaga ilham da zahra suna ta bacci, ban d’aki ya shiga yayi wanka, bayan ya futo ya zura kayan bacci. Yana gama sawa ya had’awa zahra da ilham madara, zahra ya fara tashi ya bawa madarar, bayan ya gama bata ya tashi ilham itama ya bata, daga haka ya kwantar da su, suka tafi wani saban baccin.

Shima kwanciya yayi akan gadon, juyi yay tayi dan ya kasa bacci, yana ritse ido sai ya ringa ganin ammi tana yi mae gizau, kewar ammi kawai yake, sabida ya riga da yasaba indae yana 6an garan ammi a maqale da juna suke kwana. Haka dae dady yay ta juyi akan gado, sae wajan qarfe ukun dare bacci ya kwashe shi.

Kiran sallar asubar fari ne ya tashi dady daga bacci, yana tashi daga bacci ya d’aura alwala, bayan ya d’aura alwala d’akin su mashkhur ya shiga, mashkhur ya tasa da abdul, yace suyi alwala, in sunyi su jira shi yanzu zai dawo. Dady yana fpart d’in momy ya wuce, yana zuwa ya fara qwanqwasa qofar part d’in, sae da yayi wajan minti goma yana bugawa kafin momy tazo ta bud’e qofar.

Momy tana bud’e wa tayi turus tana kallan dady, harara dady ya watsa mata tare da cewa lafiya kika zubamin ido kike kallo na haka kamar baki tab’a ganina ba?. Tabb dama dady mashkhur ka kwana a gidan nan? Ban saniba, wae ke sabida mae baki da tausayi ne halima?. A fringice tace mai kuma nayima dadyn mashkhur?. Yanzu ace yaran nan su wuni su kad’ai koh kije ki kai musu abinci bare ki taya su zama.

Turo baki momy tayi tare da cewa haba dadyn mashkhur kana gani dae jego nake nima in zan samu mai kula da ni so nake. Jinjina kae dady yayi yana tunanin mugun hali irin na halima, yasan da ammi ce bazata tab’a hakan ba hakan yana d’aya daga cikin abindda dady yake son ammi...........

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.........

*page 34*

d’agowa dady yayi ya kalli momy tare da cewa an jima zan koma asibita ki dafa abinci zan tafi da shi, kuma ki had’a harda su mashkhur. Had’e rai momy tayi tare da cewa ni dae gaskiya bazan iyaba, harara dady ya watsa mata a fusace yace wallahi na dawo baki dafa abincin nan ba ran ki sae ya b’ace, ba dole ki fitar min daga rai ba ke kullum a matsayina na mijinki ban isa na gaya miki kiji ba, Wallahi nasan da maryam na gayawa ko musu bazata yimin ba.

Yana gama fad’ar hakan ya wuce ya bar momy a tsaye baki a sake, cikin baqinci ta shigeciki, tana shiga ciki ta wuce kicin ta fara dafa abinci zuciya ba dad’i, a ala dole take dafa abinci sabida tasan in bata dafa ba sae dady ya bata mata sosai, har sakinta ma zai iya yi. Dady yana fita daga part d’in momy part d’in ammi ya wuce, yana shiga ya wuce d’akin su mashkhur. Alokacin har sun gama alwalar suna jiran dawowar shi.

Dady yana shiga yace musu ku tawo mu tafi massallaci. Bayan sun dawo daga masallaci dady yacewa mashkhur ya tashi faruq da haidar yayi musu wanka, yau zai sasu a makaranta, haka mashkhur ya tashe su yayi musu wanka. Bayan ya gama yi musu wanka ya had’a wa abdul ruwan wanka shima, yana gama had’a mae abdul ya shiga wankan. Bayan abdul ya shiga wanka mashkhur ya shafawa su faruq mae tare da sa musu kaya.

Abdul yana futowa daga wanka shima mashkhur ya shiga wankan. 6an garan dady kuwa yana komawa d’akin ammi ya tashi zahra da ilham yayi musu wanka, bayan ya gama yi musu wanka ya sa musu wasu kayan, sanan ya had’a musu madara ya basu. Wajan qarfe bakwai na safe ya koma part d’in momy, yaci sa’a ta dafa abincin. Dankalin turawa ne da farfeson nama sai shayi.

Ta zubawa su mashkhur daban sanan ta ware wandda dady zai kaiwa su hajiya kaka asibiti. A hanzarce ya d’auka ya fuce da su. Bayan ya koma ya bawa mashkhur ya zuba musu sukaci. Dady kicin ya sake shiga ya dafa musu abincin da zasu je makaranta da shi sabida wuni sukeyi, indomi ce da kwai, zubawa kowa yayi a filas sanan ya had’a musu da biskit da lemo.

Alokacin da dady ya gama dafa musu abinci alokacin sun gama cin abinci. Mashkhur ka d’auki abincin ku da nasu hajiya ka kae mota, kuma ku shiga motar ku jirani yanzu zan zo, ya fad’a yana miqawa mashkhur mukullun motar, qarasawa mashkhur yayi ya qarb’i mukulin motar. Shida abdul suka kwashe kayan abincin suka kai motar daga nan kuma suka d’auki faruq da haidar, suka wuce motar suna jiran dady.

Dady kuwa d’aki ya koma ya d’auko ilham da zahra ya wuce dasu part d’in momy. Yana shiga falon a zaune ya sameta tana cin abinci ita da rukee. Yana sallam rukee ta taso da gudu ta rungume shi, murmushi dady yayi tare da cewa my baby kina lafiya d’aga kai rukee tayi alamin ee, masha Allah. Da sauri Dady ya qarasa indda momy take tare da ajiye zahra da ilma.

Kafin ma yayi magana momy tace wa’annan yaran fa?. Fuska a had’e dady yace au baki gane su ba kenan? Yamutsa fuska momy tayi tare da cewa na ganesu mana ina dae nufin sabida mae aka kawo min su?. Jinjina kae dady yayi tare da cewa sabida ki riqesu mana, ai kinsan maman su bata da lafiya kuma hajiya tanacan, dan haka ki kula da su sae na dawo.

Gaskiya ni bazan iya kula dasu ba, nima ka barni naji da jaririya ta yau kwana na biyu da haihuwa fa. A fusace dady yace wai halima sabida mae baki da mitinci ne ehhyee?. Kwab’e fuska momy tayi tare da cewa daga fad’ar gaskiya sae a ce bani da mutunci, gwarama ilham d’in zan iya riqeta amma Wallahi bandda wanna yarinyar, ta fad’a tana nuni da zahra.

Sabida baqin ciki dady yama kasa magana, Wallahi momy tarajar yaranta kawai takeji dabadan hakan ba da tini ya saketa. Har ya juya zae futa kawai ya dawo ya d’auki zahra da ilham sabida yasan halin momy da mugunta yanzu sae taqi bawa zahra abinci. Afusace dady ya fuce daga part d’in, yana futa momy ta tab’e baki tare da cewa ALLAH ya raka taki gona.

Dady yana fita ya wuce wajan motar sa, gidan gaba ya bud’e abdul ne zaune a gaba. Dady cewa yayi abdul kuma baya kaji zan ajiye su ilham ba musu abdul ya koma baya kusa da ‘yan uwansa. Dady yana sa ilham da zahra a gaban mota ya nufi hankar fita, tin kafin ma yayi hroon mae gadi ya bud’e masa qofa ya futa.

Koh da yaje makaran ma koh shiga bae yi ba waya yayiwa mae makaranta akan a kae su faruq da haidar aji kuma ayi musu duk abindda ya kamata in aka gama a yi masa lis d’in kud’in dama yana da account d’in mae makarantar tanan yake biywa su mashkhur kud’in makaranta. Dady yana saukesu, mashkhur har office ya raka su faruq sanna ya wuce ajin su.

Dady kuwa yana sauke su mashkhur a makaranta ya wuce asibiti, ladamar auran momy kawai yakeyi azuciyar sa, sabida yasan sam bae yi dacan auran momy, ta wani 6an garan kuma in ya tuna da abdul sae yaji dad’i, sabida yasan sam abdul bai kwaso mugun halin momy ba.

Shi dady gani yake da, dahalima duk yaran momy kwashe su zai ringa yi yana mayar dasu wajan ammi, sabida yasan indae suka cigana da zama da momy tofa tabbas sae ta lallata su. Da wannan tinanin ya qarasa asibi. Yana qarasawa ya d’auki ilham da zahra suka shiga cikin asibitin. Suna shiga d’akin da aka kwantar da ammi ya samu ammi a kwance kamar yadda ya batta.

Kwance take hancita yasha robar abinci, 6an gare guda kuwa hajiya kaka ce akan sallaya tana ta lazumi. Sallam yayi da sauri hajiya kaka ta taso tare da amsa sallamar da dady yayi, tana qarasowa ta kar6i zahra. Hajiya ya mae jiki?. Ajiyar zuciya hajiya tayi tare da cewa toh jiki dae sae godiyar uban giji, dan har yanzu basu gano mae yake damunta ba.

Jijjina kae dady yayi murya a raunane kamar zae yi kuka yace tom ALLAH ya bata lafiya, Ameen Abubakar. Mae yasa ka tawo da su zahra asibiti ne? Wlh hajiya naso na barsu a gidan halima tace bazata riqe su ba, kuma su mashkhur sun tafi makaranta. Jinjina kae hajiya tae tare da cewa yanzusu su haidar d’in suna ina?.

Na sakasu a makarantar su mashkhur, suma daga yau zasu ringa zuwa makaranta. Tom shikenan ALLAH yabada sa’a, murya a sanyaye dady yace ammen hajiya, miqa mata ilham yayi tare da cewa itama riqeta bari naje na d’aukko muku abinci koh. Jiki ya sanyaye hajiya kaka tace ae sae dai ni naci, ita bata iya cin abincci baka ga an sa mata robar abinci ta hanci ba?

Wani siririn hawaye ne ya zubowa dady tare da cewa na gani hajiya. Jinjina kae hajiya tayi tare da cewa yanzu maryam bazata iya cin abinci ba sae dae koko ko madara ko kwast haka dae abu mae ruwa-ruwa. Da sauri dady ya juya tare da cewa bari naje na kawo miki abinci, yana tafiya yana sahare hawayan da ya zubo mae.

Bayan dady ya kawowa hajiya kaka abincin wajan ammi ya wuce, a gefan gadan ya zauna ya zuba mata ido yana kallan ta, bacci kawai take yi. Addu’a ya farayi mata yana tofa mata a fuska. Bayan ya gama yi mata addu’a ya wuce wajan hajiya kaka, yana zuwa yace hajiya bari naje na siyo mata abubuwan da zata iya sha karta tashi tana jin yunwa koh? Tom shikenan Abubakar a dawo lafiya.

Daga haka dady ya wuce ya tafi. Hajiya kaka kuwa da qyar ta iya samu taci abinci, shima dae ba wani mae yawa taci ba. Yau ma haka likitoci suka taru akan ammi amma basu gano mae yake damun ta ba. Wunin ranar hajiya kaka ce ta kula dasu zahra. Dady ma wuni yayi a asibitin dan koh nan da can ya kasa zuwa, ya zauna ya zubawa ammi ido, koh abinci ma ya kasa ci, sae da ammi tayi mae dole, sanan ya samu yaci kad’an.

6an garan su mashkhur kuwa sae da yamma suka dawo gida dama wuni suke a makaranta, drive sune ya dawo da su. Bayan sun dawo mashkhur ya bud’e musu part d’in ammi suka shiga, dama dady ya bashi mukulin part d’in. Suna shiya ya cire kayan makarantarsa, shima abdul cire nasa yayi sukasa na gida. Daga haka mashkhur ya shiga kicin domin dafa musu abinci.

Firinji ya bud’e yana bud’ewa yaga tukunya a rufe, fud’e tukunyar yayi dan ganin menene?. Miyar kifice acikin tukunyar, wajan kwana miyar uku amma bata lallace ba sabida sanyin firinjin, ammi ce ta dafa miyar. Cirota yayi daga firinjin ya ajiye ta akan table d’in kicin d’in. Shinkafa ya dafa musu bayan ya gama ya d’imama miyar sanan ya zubawa haidar da faruq a flat d’iya, shi kuma ya zuba musu shida abdul.

Bayan sun gama ci ya fara bud’e littafin da aka bawa su haidar a makaranta koh an basu home-work. Bayan ya gama yi musu home-work d’in shim abdul ya dakko littafin sa mashkhur ya tayashi home-work d’insa. Bayan sun gama mashkhur da abdul sukayi sallar magariba agida, bayan sun idar mashkhur ya kunna musu kallo suka farayi.

Shi dae mashkhur kwata-kwata hankalinsa baya kan tv, kawai tinanin ammi yake, lokacin sallar i’sha ma mashkhur da abdul sukayi. Bayan sun idar mashkhur yayiwa su haidar wanka sanna ya canza musu kaya, ya kwantar dasu. Bayan sun kwanta shida abdul suma sukayi wanka, suna gamawa mashkhur ya fara kowaya abdul hadda.

Bayan mashkhur ya gama kowayawa abdul hadda kuma ya tabbatar abdul d’in ya iya shima karatun Qur’ani ya farayi...........

Kuyi haquri jiya ban yimuku typing... ba wlh bani da time ne kunsa muna celebrate ne ‘yan kano abba gida-gida yaci zab’e shiyasa.🎉🎉

Gamasu buqatar da nayi posting sun d’inga karantawa sae suyimin magan ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. Free book ne kuma new book on 2023.

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Page 37*

Typing...........

Bakomaii bane yasa hjy kaka mamaki ba sai raban da tayi waya da malam Ibrahim ko taje wajansa tun lokacin da aka kawo zahra gidan..........

Har wayar ta tsinke hajiya kaka bata d’auka ba sabida tsabar mamaki, sai da ta sake shugowa sannan ta samu ta d’aga tare da sallam. Bayan sun gama sallamar hjy fucewa tai daga part d’in tasamu qofar korudo ta zauna. Bayan sun gama gaisawa malam Ibrahim yake tambayar kwana biyu yajita shiru ko lafiya.

Nan da nan hajiya kaka ta bashi labarin rashin lafiyar ammi shiyasama bata zuwa. Malam Ibrahim ya jajantawa hajiya kaka sosai sanan yake shawartatta akan tazo wajansa zuwa gobe ko jibi sai yafara gwada mata rubutu tasha ko ALLAH zai sa adace. Hajiya kaka tayi na’am da zancan malam Ibrahim kuma ta sheda mai insha ALLAH gobe zata shigo daga haka sukayi sallama hjy kaka ta kashe wayar.

Washegari.....

Mashkhur da su abdul duk sun tafi makaranta, momy kuwa tana 6an garanta rai a 6ace, bakomaii ne yasa ran momy 6acewaba face zuwa kadunar da dady ya hanata, kuma ba komaii zatai a kaduna ba face zuwa wajan boka dan ya kashe mata ammi. Yauma dady bazai futaba dan haka hajiya kaka ta shirya tsaf domin zuwa wajan malam Ibrahim. Driven ta ya d’auketa yakai ta har runfar malam Ibrahim.

Bayan hajiya kaka sun gama gaisawa da malam Ibrahim ta fara koramai jawabi akan yadda cutar ammi take. Tana gama yimai bayani malam Ibrahim ya sheda mata cewa bakomaii ne yake damun ammi ba face SIHIRA da ASIRI. Hjy kaka tayi mamakin hakan sosai dan dama ta dad’e tana tunanin anya ba asiri akayiwa maryam ba.

Maganar Malam Ibrahim ce ta dawo da hjy kaka daga tinanin da ta tafi, amma in sha ALLAH zan yimata rubuta sai ki fara bata muga abindda ALLAH zai yi. Jinjina kai hjy kaka tayi tare da cewa yanzu malam Ibrahim wa yayi mata asirin nan haka, girgiza kai malam Ibrahim yayi tare da cewa gaskiya hajiya fatima ni bazan sheda wandda yayi mata hakan ba kinsan dae ance zato zunubi ko? Hakane malam Ibrahim tom ALLAH yasa mu dace.

Daga haka sukayi sallam sanan malam Ibrahim yace mata zuwa jibi ta dawo dan kar6o mata rubutu.
Wunin ranar haka hajiya kaka tai ta saqe-saqe da warwara, dan tasan ko ba’a gayam mata ba momy ce tayiwa ammi asiri, dan tasan halima zata iya aikata komai, tun alokacin da tace zata raba abdul da ammi, kuma tasan sam ba d’ugwan imani a zuciyar halima (momy). Wunin ranar dai haka hajiya kaka taita saqa da warwara.

Washegari dady bai futaba koma su abdul da mashkhur sun tafi tafiz dan haka hajiya kaka ta shiya tsaf domin zuwa wajan malam Ibrahim. Lokacin da taje malam ibrahim ya gama yuwa ammi rubutun, kuma yayiwa hjy kaka bayanin yadda zatai amfani da shi, bayan hajiya kaka tabawa malam Ibrahim sadaka ta dawo gida. Bayan ta dawo gida tayiwa dady bayani akan rubutun amma bata gayamai cewa asiri akayiwa ammi ba.

Dady yajin dad’in hakan sosai dan shima yanzu ya gaji da maganin asibitin. Washe gari hjy kaka ta fara bawa ammi rubutun da addu’o’in da malam Ibrahim ya bata, dama rubutun na sati guda ne.
Kullum hjy kaka sai ta bawa ammi rubutun yau kimanin kwana uku kenan kuma ana samu cigaba tindda gashi yanzu ammi tana d’an motsa ga6o6in jikinta.

Kuma kowa yana farinci da hakan, badda momy wacce batasan abinddama akeyi ba, tana nan tana shirye-shryen zuwa wajan boka, sabida ta kashe ammi,, amma dady ya hanata zuwa kadunan. Shima dady yanzu ya fara zargi momy akan cutar ammi sabida yasan halinta, amma kuma sai ya kawar da zargin azuciyar sa sabida yasan bakyau zargi kuma ba lallene hakan ta kasance ba, amma sam bai gaya mata cewa ammi ta fara samun sauqi ba.

Yau kimanin kwana uku da gama bawa ammi magani kenan, indda take d’akinta a kwance amma dai har yanzu bata fara tafiya da magana ba.
Daga dady har su mashkhur da hajiya kaka suna zaune a falon ammi suna hiira. Suma su zahra da ilham suna gefan kaka suna wasa kamar yadda suka saba.

Dady ne yake tambayar mashkhur in ya gama karatu yayi condy wace qasa yakeso ya fitar da shi domi ya cigaba da karatu. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ni dae gaskiya dady bana son natafi wata qasa karatu ni dae kawai ka barki a Nigeria na cigaba da karatuna. Murmushi dady yayi tare da cewa babana ai university d’in Nigeria yanzu ba’a wani karatu mai inganci kullum yajin aiki ake tafiya kuma naga kana da qoqari sosai in kasamu kaje kayi karatu acan zaka qara qoqari.

Aaa ni dae dady nifa bana son na tafi bana ganiku nafison kullum na ringa ganin ammina da hjiy kaka da kuma ku, jinjina kai dady yayi a zuciyarsa yana tinanin taya zai shawo kan mashkhur yaje yayi karatun nan, dan yasan mashkhur da taurin kai. Dady tundda yaya mashkhur bazai jeba ni kawai ka kaini wacce qasa zaka kaini, abdul ne yake fad’in hakan. Murmushi jin dad’i dady yayi sabida yasan ko ba komai abdul nan gaba zai zamo yaro mae biyayya da jin maganar sa bakamar mashkhur ba.

Tom abdul shikenan kaza6i wace qasa kakeso kaga kai sai katafi in kayi condry koh?. A dai-dai lokacin zahra ta riqe qafar mashkhur domin ta miqe tsaye, ai kuwa da qarfi mashkhur yasa qafa ya bige ta jikake qumm kamar dae yadda yayi mata a baya. Qararce ta janyo ankalin kowa a wajan abdul har zai bawa dady amsar tambayar yaji qarar wad’owar zahra.

Kuka zahra ta farayi sosai sabida fad’uwar yau tafi ta baya, da sauri dady ya taso ya nufi indda zahra take ta kuka itama kakan tasowa tai rai a 6ace. Kai ashe baka da hankali

Please Login or Register in order to submit comment