Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukayi henna day. Ita dai zahra tace baza tai lalle sai ranar dinner wato ana saura kwana biyu ta koma gida. Tom washe gari haka nana da qawatanta su kai kamu, bayan kamu sukayi qauyawa de sukayi bridal kai haka suka ringa abubuwa kala-kala. Ita dai zahra tana gida dan duk abubuwan da sukeyi na 'yan mata ne.

Tana gida tana sake gyara jikin ta sosai, sai ranar da za'aw yi dinner zahra ta samu akayi mata lalle da flower. Daran ranar sun sha dinner ba qarya dan har sai da ango yazo da abokan sa, dan gi 'yan uwa sa abokan arziki an kashe kud'i ba wai. Washe gari zahra ta samu akayi mata kitso shi wanan ma ranar party ne.

Duk da ba matan aure amma zahra haka nan ta sha kwalliyarta kamar ba matar aure ba ta direwa mama abdul suka wuce wajan party. Hmmm an sha party sosai nana da abdul sunyi kyau sunyi matuqar dacewa sosai, zahra farin ciki take kamar ita ce amaryar. Har wani Allah Allah take gobe tayi a d'aura auran ta wuce gidan ta wajan mijin ta itama.

Zahra tun kafin ma a tashi daga party hankalinta duk yayi gida kuma gashi ta fara tinanin abdul, dan haka ba 6ata lokaci tasa aka mai da ta gida, ga uban kiran da mashkhur yake mata kuma tasan baze so jin ta bafi party tabar abdul a gida ba. Bayan zahra ta dawo wanka tayi taci abinci, sanan ta bugawa mashkhur suka sha hirar ta masoyi suna zumud'in gobe tayi su had'u.

Washe gari.

Tun da asuba fari zahra ta tashi sabida tsabar zumud'i ji take kamar ita za'a d'aurawa aure. Tana sauka qasa taga ana ta aikace-aikacan abinci kala-kala. Kicin zahra ta shiga tana shiga ta samu mama tana ta fama dama mata sabaya. Hmmm mama ina kwana, fuska sake mama tace lafiya qalau zahra, tom mama ki de dama kad'an kin san yau zan tafi zahra ta fad'a cikin zumud'i.

Murmushi mama tai tare da cewa ai na sani zahra ki kwantar da hankalin yau a gidan ki zaki kwana amma dai sai kin jira kin raka qanwarki d'akin miji. Nan da nan fuska zahra ta canza tace tom mama ita sai yaushe za'a kai ta ne?. Ki kwantar da hankalin ki zahra jirgin qarfe 4 zakubi fa. Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa to ya za'ayi da jama'ar rakiyar amarya?.

Ee ae kin san tun sanda aka gama jere ake zuwa ganin gidan, to yanzu ma bayan d'auri aure wasu zasuje su gani a taqaice de kafin a kai amarya kowa ya gama zuwa ganin gida, aunty habiba da fa'iza ne kad'ai zasu raka ta, amma su in suka raka ta zasu koma gidan ammi su kwana washe gari sai su tawo. Wanan da mama take maga d'aya qanwar tace d'aya kuma yayar ta ce.

Hamma zahra tai sanan tace ai gwara da akai hakan dan ni gaba d'aya bana son gayyar kai amaryan nan a cikawa mutane gida. Kai zahra ke de bakya son mutane sosai, haka maryam tace mashkhur ma haka shikenan sai kuje ku cigaba da rayuwar kuramai, amma de kada ku koyawa yaranku rashin son mutane dan mutane rahma ne.

Aa mama ba haka bane, ni kawai in mutane suka taru kunya shiga cikin su nake ji sai naji gaba d'aya na tsargu shi kuma yaya mashkhur baya son hayani ya ne shi yasa. Murmushi mama tai tare da cewa tom shikenan d'auko cup na zuba miki kisha. Qarasawa inda ake ajiya cup d'in zahra tai ta d'auko sanan tace hmmm daga yau shikenan na dena sha zanyi missing.

Zahra ta fad'a tana qun she dariyar ta dan dama bata wani fiya son shan sabaya ba, amma dai da taga tana gyara mata jiki kuma bata sata saurin jin yuwa shi yasa ta d'aure tana sha. Murmushi mama ita tai tare da cewa da sauri haka zahra kenana wai ni zakiyiwa wayo to bari kiji nasa an sake had'a miki wata cikin botiki da ita zaki tafi.

Kai mama wasa de kike, au wasa kika d'auki magana ta kalli can wanan blue d'in robar duk ita ce a ciki kuma ko ta qare sai nasa an kawo miki wata. Ta6e baki zahra tai sanan tace to yana iya da ke mama tinda kina so ai sai nasha. Daga haka zahra qar6i sabayar tasa mata suger da madara sanan ta sha.

Bayan zahra ta gama shanye sabayar ta fara taya ammi girkin breakfast d'in da zata yiwa abba. Bayan mama da zahra sun gama koma zahra d'ibar musu tai a plate ita da nana tare da cewa bari naje na tashi waccan galma shurar tayi sallah muci tare dan ita naga da alama ta manta yau ne d'aurin auran ta.

Dariya mama tai tare da cewa nana ce zata manta tab nan kuwa da zumud'i in ba wasa ba kika tashe ta sai tace miki tayi mafarki an d'aura auran yanda tasa abun a ranta. Itama zahra dariya tai sanan tace hmm nana kenan bari naje na tashe ta, daga haka zahra tai sama hannun ta d'auke da tire, tana hawa ta wuce bedroom d'in nana wanda a halin yanzu ya zama nasu su biyu.

Bayan zahra ta ajiye plate komawa ta tashi nana wanda take sharar baccin gajiya. Nana tana farkawa ta fara hamma da miqa ke shashashar amarya tashi yau fa d'aurin auran ki kuma nasan zakiyi shirya-shirya tinda yau ce ranar barinki gidan nan ki koma can garin mu, mu zauna tare. Murmushi jin dad'i nana tai tare da cewa! Ai wlh aunty zahra sabida nasa abun a rai na har mafarki nai.

Wata dariya zahra ta saki mai sauti harda tafa hannu tace ah haf dama mama ta gayamin tace da kyar in bazaki mafarki ba. Dariya nana tai sanan tace wlh kuwa nayi ga gajiyar party dana kwaso nana ta fad'a tana miqewa da kyar. Hmm ai haka zakiyi haquri ki d'aure ana kai ki gidan ki wahala tazo qarshe sai ki wutu. Wani kallo nana tayiwa zahra na rashin yarda.

Zahra ta gane abinda nana take nufi dan haka murmusawa tai sanan tace hmmm nana sarkin wayo ai wanan dole ne kuma tinda yaya abdul yana sanki zai miki a hankula ki dena jin tsoro. Cikin karaya nana tace hmm ai tsoro dole ne aunty zahra amma dole na daure tinda ina son yaya abdul nana ta fad'a tana sake fad'ad'a fuskarta da murmushi.

Dafa kafad'ar ta zahra tai cikin nishadi tace da kyau ta gidana bakya tsoro shi yasa fa nana kike burge ni hmmmm ai karkiji wani d'ar zafin ba mai yawa bane zahra ta qarasa maganar tana sakin murmushi mugunta. Itama nana murmushi ta saki tare da cewa yauwa aunty zahra kice zafin kad'an ne ma ai ni nasan zanyi iya daurewa, sosai ma nana zo muje muyi alwala kinga har wasu masallatan ma sun idar.

Haka nana da zahra suka shiga toilet zahra dafe da kafad'ar nana. Bayan sunyi fitsari alwala suka d'aura sanan su kai sallah, bayan sun idar da sallah miqewa nana tai tana fara laluban wayarta dan turawa yaya abdul saqo kamar yarda ta saba duk asuba kai ko nana bata sallah sai ta sa alarm dan ta tashi, kuma gashi saqon yau na daba ne nana zata turawa abdul.

Ta dad'e tana ajiyar message d'in tana jira ranar nan tazo. Bayan nana ta lalubo wayar sai a lokacin ta tina ashe wayar ta d'aukr ba caji. A hanzarce nana ta jona a caji sanan ta dawo ta zauna suka fara breakfast ita da zahra. Suna ci nana tana gayawa zahra irin soyayyah da zata nunawa yaya abdul.

Wani kuma abun dangane da aure in nana bata sani ba sai ta tambayi zahra. Zahra kuwa komai take bud'ewa nana daki-daki dan yanzu zahra ta dena jin muguwar kunyar nan kamar da, da take budurwa. Bayan zahra ta gama fayyacewa nana komai cewa tai nasan ki da rawar kai ga surutu, to kada ki sake ki nuna mai kin san komai duk abinda yayi miki koya tambaye ki ki nuna mai kanki a kulle yake baki son komai ba.

Murmushi nana tai tare da cewa to aunty zahra, ai bazan gaya mai ba. Yauwa haka ake so dan in kika nuna mai gani zai yi kamar kin san komai lo kin ta6a. Ah in sha ALLAH ma bazai ji komai ba bazan nuna mai na sani ba. Yauwa nana, nana kaya yau yaya abdul zai sha dad'i fa dan qanwar tawa a cike take komai yaji.

Da sauri nana ta rufe fuska tana dariya, lallai nana yau kece dajin kunya ikwan ALLAH dama ance haka amarya take duk rashin kunya ta ranar da za'a d'aura mata aure ko aka d'aura mata kunya tana hawa kanta. Murmushi nana tai sanan tace hmm nima to tahau kai na, haka nana da zahra suka cigaba da cin abincin su suna hira har suka kammala.

Bayan sun gama nana bud'e wayar ta tai ta turawa yaya abdul messages d'in. Ita kuma zahra fita tai da plate d'in sanan ta dawo ta d'auki abdul da ya jima da bud'e ido sabida yaji hayaniyar su ita da nana, amma sam bai yi kuka ba sai wasan sa yake yana ciccila qafafuwa da hannu a kwance. Zahra tana d'aukar shi ta dan yi mai wasa duk da yayi qanqanta da wasa.

Sosai zahra da dan ta abdul suke ta dariya kamar masu hira, ita de nana ta maqe a gefan gado tana waya da mijinta murya qasa-qasa. Daga haka zahra ta bawa abdul nomo da yake daran jiya ma bai tashi ya sha ba. Bayan zahra ta kammala kwanciya tai ta koma bacci zuwa anjima, ina gari ya gama wayewa.

Zahra ba ita ta tashi ba sai wajan qarfe goma. Lokacin har an fara tafiya d'aurin auran da yake sha d'aya da rabi za'a d'aura auran. A hanzarce ta ta tashi ta shiga toilet tayi wanka bayan ta futo, ta d'ebo ruwan d'imi a bawo domin yawa abdul wanka shima. Sabida yau tasan mama tayi busy da yawa, bazata iya samun damar yiwa abdul wanka ba.

Haka zahra ta farayiwa abdul wanka duk da ba wani iyawa tai ba dan kullum mama ce take mai, sau da yawa in mama zatai wa abdul wanka tana yawan cewa zahra tazo ta gani, amma zahra bata zuwa haka mama zatai ta mita tana cewa yanzu in suka koma gida wa ze yi mai. Tsarki zahra kawai ta iya yiwa abdul shima ba koda yaushe take mai ba sai ta kama in mama ta fita ko bata kusa.

Bayan zahra ta gama yiwa abdul wanka mayar da bawan toilet tayi sanan ta d'auko maya mayan sa da kayan da zata sa mai. Sosai zahra ta shirya abdul yayi kyau, dama gashi kyakyawa. Zahra tana gama shirya abdul ta ajiye shi, ta miqewa tai d'auko saban leshin ta tsadadde mai kyan gaske,. Sanan ta fara sawa bayan zahra tasa hoda ta shafa da jan baki harda kwalli, zahra tayi kyau sosai.

Murmushi zahra tai dan satan dole nan bada jimawa ba su had'u da mashkhur in suka zo d'aurin aure tinda a kaduna za'a d'aura auran. Bayan zahra ta gama saqa haka a zuciyar ta d'aura dan kwalinta tai, rai d'auri m kyau ta d'auko mayafinta ta ajiye a gefe. Zama tai akan gado dan bata son fita cikin mutane. Zahra ko ba'a gaya mata ba tasan su nana an tafi gidan makeup.

Haka zahra ta zauna ita da abdul ta kira wayar mashkhur amma bata shiga ba, zahra ta ayyana duk yarda akai jirgin sune ya tashi shi yasa. Daga haka zahra ta d'auki abdul ta cigada yi mai wasa. Ana haka qanan zahra suka shigo zahra taji dad'in hakan, duk da ba wasu manya bane haka sukayi hirar ita da qanwarta khaulat da batafi shekara 8 zuwa goma ba, sai 'yan biyun qananta maza da suke ta yiwa abdul wasa tare da shafe mai fuska..............

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing........

Double page

Suna cikin haka sai ga nana ta dawo ita da qawayan ta, nana tayi kyau sosai tasha makeup kamar ba ita ba. Nan da nan zahra ta farayi mata hoto masu kyau, ita da qawayanta. Bayan zahra tayi musu hoto suma sunyi mata an sha hotona nan da nan qawaye nana suka fara d'aukar abdul kowacce tana masha ALLAH allahumma'arzuquni.

Dama kunsa abdul da kyau masha ALLAH. D'aya daga cikin qawayan nana ce tace gaskiya masha ALLAH kina da kyau aunty nana amma babyn ki ya fiki kyau. Murmushi zahra tai ba tare da cewa komai ba. Cafe zance wata tai da cewa! Ah itama tana da kyan ta, amma wlh ko kad'an basa kama da yaranta. nana ce ee basa kama ai kun san yaya ahmad ko to in kukaga matarsa, sai kuce ita ta haife shi dan suna d'an kama.

Wow masha ALLAH ai munganta a hoto itama ba laifi tana da kyau, gaskiya to amma taya akai yake kama da ita?. Ee mijin aunty zahra qanwarsa ce ai dashi babyn yake kama kamar dai yayi kaki ya ajiye. Nan da nan matan wajan suka riked'e da salati, dama kun san mata akwai san kyakyawa namiji.

Daya daga cikin suce ta sake cewa kuma shima fari ne?. Murmushi nana tai sanan tace ee fari ne mana amma gaskiya be kai baby da aunty na haske ba fatar shi dai mai kyauce. Wayyo ya ilhahi zan so naga bawan ALLAH nan wata daga ciki ta fad'a. Take fuskar zahra ta canza sabida tsabar mugun kishi. Amma su 'yan matan basu kula da hakan ba.

Nana ce tace ku kwantar da hankalin nasan zai zo zan nuna muku shi, yayan mijin da zan aura ne awnnnnn kai nifa nace dan shima naga abdul d'in ki kyakyawa kai wanan zanso naga dangin su nasan dangi kyawawa ne, wata kuma cewa tai shikenan anyi tuwo na mai na. Murmushi nana ta sakeyi tare da cewa ai duk gidan su ba mummuna gaba d'aya kyawawa ne.

Bayan matar yaya ahmad da akwai mata biyu amma d'aya ta rasu. Nan da nan waje ya rikid'e da salati kowa yana yiwa rukkayya addu'a. Zahra ji tai kamar ta zane nana sai hararar nana take amma ina taqi lura da hakan. Da kyar zahra ta iya sakin fuska sabida kartayi musu rashin mutunci cikin fara'a tace kai nana kin cika su da surutu wai ke bakya gajiya da magana ne? .

Murmushi nana tai tare da cewa ah aunty zahra ai gwara na gaya musu. Wata ce tace to wai shikenan mazan gidan biyu ne?. Girgiza kai nana tai tare da cewa da akwai wasu matasan smari biyu yaya fruq da yaya haidar sai d'an autan su ameer, amma shi qarami ne. Yauwa muma ai kinga nana sai ki mana hanya mu shiga da ciki.

Tabb ai basu isa aure ba basufi 2I to 22ba, kai ni ko a hakan ne sai na jira su kalar wanan jinin kyau haka. Nana tana qoqarin magana taga fawas ya shigo baki d'auke da sallama. Da sauri ta miqe a lokacin wajan 12 da yan mutina tayi cikin farin ciki tace fawas an d'aura. Gyad'a kai yayi tare da cewa har mun dawo. Yauwa ina dadyn zahra da yaya mashkhur sun zo ko.

Gayad'a kai yayi tare da cewa ee sun zo mana, yanzu zasu shigo. Da sauri nana tace ku taso muje na nuna muku su maza-maza. Miqewa sukayi harda zasu fita da abdul abdul ya fara kuka dan haka dole suka miqawa uwarsa zahra. Zahra tayi matuqar godewa Allah da abdul ya fara kuka, duk da tana kishi amma tasan ko matan nan zasu bangaji mashkhur ko kallo basu ishe ahi ba, bare magana.

Amma tasan in suka iya fita da abdul qarami zasu iya cin darajar abdul in mashkhur ya gan shi a hanun su ya kalle su. Kai nana Allah ya wadaran wanan surutun naki, kawai kin sani a fargaba. Daga haka zahra ta riqe abdul ta zagaya ta bud'e qofar barandar bedroom d'in domin leqawa ta sama ko zata samu damar ganin mashkhur.

Zahra tana leqawa adede lokacin su dady, Abba, mashkhur, abdul, faruq, haidar, suka shiga farfajiyar gidan. Adede lokacin nana da qawayanta suka qarasa suna miqawa dady da abba gaisuwa. Zahra sakin baki tai ganin iskanci qawayan nana sai wani iyayi suke suna kallan mashkhur ko ba'a gayawa zahra tasan gai da shi suke.

Mashkhur dai ko kallo basu ishe shi ba dama kunsa yaya mashkhur da musukilanci da kuma shariya. Mashkhur da kyar ya iya amsa musu gaisuwar shima sai da abdul yayi mai magana yace yaya mashkhur ana gai da kai sanan mashkhur ya amsa sau d'aya a daqile hankalin sa yana kan wayarsa da yake dannawa.

Zahra duk da me sanyi ce bata san sanda tace musu shigu mayan maza ba, a fili zahra ta fad'a. Mashkhur kuwa turawa zahra message yake ta famanyi, daga qarshe da ya gaji ya fara kiran ta. Zahra tana ganin mashkhur tasan tabbas yana cikin damuwa ita kad'ai da ammi ne suke iya gane yanayin mashkhur in yana cikin damuwa kuma yana 6oye hakan.

Ko ba'a gayawa zahra ba tasan mashkhur damuwar da yake ciki ba zai rasa nasa ba da rashin ta a kusa da shi ba. Zahra tana cikin tunanin nan taji wayarta ta fara ringing, ko ba'a gaya mata ba tasan mashkhur ne. Nan da nan haushi mashkhur ya rufe zahra, Allah sarki mashkhur shi da bai ji ba be gani ba, amma wanan kishi ne kawai yake damun zahra.

Zahra komawa tai kan gado kamar yarda tai tunani mashkhur d'in ne yake kiran ta wani dogwan tsaki taja dan bataji zata iya d'aga wayar mashkhur ba a halin da take ciki, ga abdul ya cika ta da kuka. Zahra sabida kishi har haushi abdul takeji gani take duk kyan shi ne yajawo 'yan matan nan suke son maqalewa yaya mashkhur.

Rai ba dad'i zahra ta bud'e riqa ta fara bawa abdul nono yana sha tana binsa da wani kallon takaici. Tab ni kuwa nace zahra lamarinki ya bani mamaki ina ruwan abdul bawan ALLAH da baban sa, kar ki wuce akan su mana. 6angaran su nana kuwa da qawayan ta ba jimawa suka fara hotuna. Amarya da ango style kala-kala kai harda faruq da haidar ba'a bar su a baya ba wajan hoto.

Dady da abba harma da mashkhur tuni sun shige stiroom d'in abba na baqi sabida mutane da hayaniya. Ba jimawa dady ya fara cigiya, wai ina mamana da jikana suke a kiramin su na gan su mana. Murmushi abba yayi tare da cewa! Bari nasa a kira maka su tinda de kaqi cin abinci bikin 'yayan ka sai kaga 'yar taka ta gaban goshi.

Murmushi dady yayi tare da cewa ai kuwa bazan iya cin wani abinci ba sai nasa mamana da abdul jikana a ido. Miqewa abba yayi fuska a sake yana ta zaulayar dady cikin mayyan ta, mashkhur yaji dad'i hakan sosai ya rasa mai zahra takeyi haka taqi d'aukar wayarsa kuma bayan tasan da zuwan sa.

Zahra tana cikin bawa abdul nono taji an murd'a handel qofar, da sauri ta zubawa qofar ido dan ganin mai shigowa. Ganin fawas ne qanin ta hakan ne yasa ta sauke ajiyar zuciya. Bayan fawas ya shigo ba 6ata lokaci yace aunty zahra wai abba yace in gaya miki kije inji dady yana kiran ki kizo mai da abdul.

Murmushi zahra tai sanan tace to kace ganinan zuwa daka haka fawas yace to ya juya domin sanar da su abba sakwan zahra. Zahra zare abdul tayi daga shan nono ta gyara rigar ta ta zuge zif d'in ta sanan ta ajiye shi a gefe ta yafa mayafinta a saman kai, bayan ta gama lulu6e jikinta tasa hannu ta d'auki abdul a towel ta fuce.

Duk da zahra ta kammale jikin ta ba qaramin kyau tayi a hakan ba kana ganinto dole ka sake kallan ta. Da ita da babyn sunyi matuqar kyau yadda ta riqe abdul hakan yayi mata kyau kamar ado ya zamar mata hakan, gana kallan zahra da babyn ta sai ka qara sabida dole sai sun burge ka. Haka zahra ta ringa ratsa mutane tana gai da su da wanda ta sani da wanda bata sani na.

Zahra sai da tafita ta fara dosar 6angaran abba taji dad'in sabida ba mutane. Tana qarasawa ta fara jin murya abba da dady suna hira. Takalma uku ta gani a qofar d'akin wata ajiyar zuciya zahra ta sauke, duk da bata ta6a sani ko kula da takalmin ba amma tana gani tasan takalmin mashkhur ne, kawai jikin take ya bata mashkhur ne mammallaki takalmi.

Nan da nan zahra taji bege da qaunar mashkhur sun rufe ta haka ta sake riqe towel d'in abdul sosai sanan tasa qafa ta shiga sitroom baki d'auke da sallama. Zahra tana shiga mashkhur ya d'ago da sauri ya kafe ta a ido, kamar ba shine wanan muskilin mai shariya ba. Ko iya amsawa zahra sallama beba, sai dady ne da abba suka amsawa zahra sallamar.

Fuska a sake dady yace lale lale mamana barka da qaraso maza ki zo ki zauna babbar 'yar ta a kusa dani. Itama fuska a sake ta gai da dadyn ta qarasa tana cewa dadyn sannu da zuwa ya hanya, zahra ta qarasa maganar tana zama a kusa da dady. Murmushi dady yayi tare da cewa gaskiya babbar 'yar ta nayi kewar ki maza ki bani jikana na d'auke shi.

Miqa mai zahra tai dady ya qar6i abdul fuska sake, ah ah ah mashkhur Allah mamana jikana ya girma kai gaskiya kin iya raino dole nai miki kyauta. Murmushi zahra tai sanan tace ai kuwa dai dady ya kamata ayimin kyauta, tinda kullum yana kukan dare ba, baya barina nai bacci. Dariya dady yayi tare da cewa ah mamana bana son sharri ni jikana jarumi ne kamar baban sa baya saurin kuka.

Zahra d'agowa tai ta saci kallon mashkhur karaf suka had'a ido, sai kallonta yake kamar ya cinye ta, nan da nan tausayin mijinta ya kama ta, murmushi tai mai tare da kashe mai ido. Harara mashkhur ya sakarwa zahra tare da kau da kai kamar ba shi yake mata kallon nan ba. Zahra tasan tabbas tayiwa mashkhur lefe bai kamata taqi d'aukar wayar shi ba.

Haka zahra sukai ta hira sama-sama da dady har su abdul da haidar suka shigo. Nan ma ba 6ata lokaci suka fara gaisawa zahra tayi farin cikin ganin 'yar uwanta musamman ma su faruq da haida da ta dan jima bata gan su ba gwara ma abdul yana zuwa akai-akai. Haka zahra ta saki jiki tai ta hira da su haidar amma mashkhur ko gaisawa basuyi ba.

Hakan ba qaramin qonawa mashkhur rai yayi ba, haidar ne yace shi bazai iya cin abinci ba sai ya fara shan tea, miqewa zahra tai domin ta kawowa haidar ruwa zafi kamar yarda ya buqata. Zahra tana fita mashkhur yabi bayan ta zuciya cike da 6acin rai taku iku mashkhur yayi zahra taji an ruqo hanunta gam ta baya.

Ko ba'a gaya mata ba tasan wannan aikin mashkhur, juyowa tai tare da cewa au sai yanzu kasan dani. Wani mugun kallo mashkhur ya watsawa zahra tare da cewa wai zahra sabida me kike son haukata ni ne!? ni ya kamata nayi miki magana kenan, banda kiran danayi miki ba ki d'auka ba mashkhur ya fad'a cikin qololuwar 6acin rai. Zahra bata da abinda zata gayawa mashkhur sabida taga ya fusaka.

Da haka ba shiri zahra ta fad'a jikin mashkhur ta rungume shi. Mashkhur yana jin zahra da tudun qirjinta da suka sake girma sosai a jikin sa, dama tun dazu su sake tsokanewe mashkhur ido. Lumshe ido mashkhur yayi tare da sake ajiyar zuciya, sun jima a hakan sai da zahra ta tabbata zuciya mashkhur tayi sanyi sanan tace tuba nake mijina.

Shafa bayan ta mashkhur yayi sanan yace its okay zahra roqona daya dan ALLAH ki dawo gida yau. Dagowa zahra tai sanan tace in sha ALLAH yaya mashkhur zan dawo yau qarfe 4

Please Login or Register in order to submit comment