Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

plane d'in mu zai tashi zuwa kano. Murmusawa mashkhur yayi sanan yace yauwa teddy na Allah yayi miki albarka ya jikin abdul.

Da sauqi bari naje na kawowa yaya haidar tea d'in ko karyaga na jima. Janyo ta mashkhur yayi tare da cewa nifa ban gaji dake ba kinga yarda kika sake wani kyau. Murmushi zahra tai tare da cewa nagode. Rad'a mashkhur yayi mata, zahra sai da ta rufe fuskar alamun jin kunya sanan ta gyad'a kai akamun eee.

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciya mashkhur sanan yace ok jeki ki kawo mai daga haka zahra ta wuce da sauri mashkhur ya bita da ido cike da begen ta. Mashkhur shi kad'ai yasan yarda yake ji a zuciyar shi game da zahra, da kyar ya iya juyawa ya koma sitroom d'in. Tom haka zahra ta kawowa haidar tea a filas da kayan shayi.

Haka su dady da abba da su haidar harma da abdul suka ci abinci. Mashkhur kuma sam yaqi ci sabida baya jin abinci yawa. Duk da kuwa abinji kala-kala ne kuma yaji komai da komai yaji kayan had'i da nama yayi matuqar dad'i kamar ba abinci yawa ba. Zahra da kyar ta lalla6i mashkhur ya yarda zai ci abinci.

Mashkhur ya amince amma shima sai dai zahra ta dafa mai da hanun ta, dan shi ko a gida in ana taro akai abinci yawa bayaci. Zahra a hanzarce ta shiga kicin ta dafawa mashkhur indomie da nama kaza a ciki, sanan ta soya mai kwai, duk sabida tai sauri ta kai mai. Mashkhur yaci abinci ba laifi, duk dan sabida zahra ce ta dafa.

To misalin qarfe biyu jirgin su dady ya d'aga zuwa kano zuciyar zahra da mashkhur cike da bege, zuciyar nana da abdul cike da zumud'i anjima. Zahra kuwa killace kanta tayi a bedroom d'in dady sabida tam bata son a yawai ta d'aukar abdul, hakan ma dan da Maya mai rubutun masha ALLAH a wuyan abdul, kowa ya gan shi sai ya tanka kuma ya d'auka hakan ne yasa zahra ta boye kanta a 6angaran abba tinda ba mai shigowa.

Zahra ba ita ta futo ba sai wajan qarfe uku shima sabida an fara shirya nana kuma jirgin su ya kusan tashi. Hakan ne yasa zahra ta futo ko wanka bata tsaya yi ba ta goya abdul sanan ta d'auki trolley madedeciya ta had'a kayan ta dana abdul iya wanda zata buqata saura ta had'e su tacewa mama in akazo kawo kayan nana a tawo mata da shi.

Amma mama cewa tai dole zahra ta tafi da sabaya ba yarda zahra ta iya haka ta tafi da ita. Haka mota ta d'auke su hud'u nana da qananan ta sai kuka rabuwa suke. Mama ma taso tai kukan amma ta danne da kyar aka raba nana da mutan gidan sanan motar ta kai su airport.
Koda suka qarasa airport d'in jirgin su bai tashi ba sai wajan qarfe biyar dan har sai da nana ta dena kuka...........

Mu had'e a next page.


ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

*page 148*

Mama ma taso tai kukan amma ta danne da kyar aka raba nana da mutan gidan sanan motar ta kai su airport.
Koda suka qarasa airport d'in jirgin su ya tashi ba sai wajan qarfe biyar dan har sai da nana ta dena kuka...........

To misalin qarfe shidda da rabi na yamma jirgin su zahra ya sauka a garin kano. A lokacin ma har motar da zata d'auki su zahra ta qaraso. Da aunty habiba sai aunty fa'iza sai kuma zahra da nana da kuma baby abdul. Haka mota ta d'auke su daga airport zuwa gidan ammi kamar yarda ko wace amarya ake kai ta gidan uwar miji kafin, a kai ta gidan ta.

Misalin qarfe 7 su zahra suka qarasa shiga gida. Nan da nan gida ya karad'e da bud'a da yake har time d'in da akwai mutane sosai. Haka aka futo da amarya kai rufe aka qarasa da ita ciki wajan ammi. Ita de zahra sai daga baya ta shigo bayan ta samu me d'aukar mata kaya ya raka ciki.

Zahra bata tsaya ko ina ba sai bedroom d'in su. Tana shiga taga ilham tana qoqarin futowa, da sauri zahra ta qarasa wajan ilham da sauri su kai hugging d'in juna cikin farin ciki. Ilham tayi farin ciki sosai da ganin zahra kamar yarda itama zahra tai farin ciki da ganin ilham. Cikin farin ciki ilham tace ai har na gaji da jiranki na d'auka ma kin fasa zuwa sai gobe.

Ah wace ni ilham ai in gaya miki yau a gidan yaya mashkhur zan kwana akan girjin sa nima na gaji da wanan zaman haka. Dariya ilham tai sanan tace ah masha allah, amma zaki je de kai amarya sai ki tafi. Zahra cewa tai ee zani mana bari na shiga yanzu nai wanka kafin mu tafi, zahra ta qarasa maganar tana kwance goyan abdul daga bayan ta.

Tana kwanto shi ta miqawa ilham, ilham kar6ar shi tai tare da cewa ah abdul de masha Allah sai girma yake kyansa yana sake futowa kuma fa wlh na fara ganin kamata da shi. Ee wlh haka ake tacewa nima wataran ina ganin hakan amma ba koda yaushe zahra ta qarasa maganar tana cire mayafin ta. Bayan zahra ta cire mayafin ta komawa tai ta rufo qofar da key sanan ta fara cire kayan ta.

Bayan ta gama cire kayan ta towel ta d'aura sanan ta shige toilet. A hanzarce zahra ta gama wanka ta futo. Sanan ta bud'e trolley d'in da ta shigo da ita ta d'auko wasu sababbin kayan ta fara sawa. Ah masha Allah zahra kin qara kyau sosai komai naki ya ciko kai mama ta iya kyara, murmushi zahra tai sanan tace hmm ke de bari ai ze sha dad'i nake gaya miki ai abun bada ganan yake harda cikin ma ya gyaru.

Ah lallai yaya mashkhur d'an gatan zahra, fari zahra tai da ido tare da cewa fad'i ki qara. Haka zahra da Ilham su kai ta hirar su har zahra ta gama shiryawa. Zahra tana gama shiryawa tai sallah. Sannan ta ciro wayarta a jaka domin kiran mashkhur, tana fara dannawa ta d'auke alamun ba caji. Zahra taga qoqarin wayar ma sabida wajan 3 days bata jona ta a caji ba abinda da masu manya harka I phone 15 pro.😒

Zahra ciro cazarta tai a jaka sanan ta jona, daga haka sukaji an fara knocking. Zahra ce ta bud'e qofar, ruma zahra ta gani tsaye itama da qatan cikin ta haiwuwa ko yau ko gobe. Ah zahra ashe kin zo to ku futo yaya faruq ya kai mu gidan amarya. Zahra dama abinda take jira kenan dan Allah-allah take taje ta dawo ta wuce gida.

Zahra cikin farin ciki tace to, ilham taso mu tafi zahra ta fad'a tana yafa mayafin ta. Kallan ta ilham tai sanan tace to bazaki tafi da wayar ba. Eh barta anan kafin na dawo ta gama caji. Ah gaskiya gwara ki d'auke ta ki kai ta wajan da ba'a shiga yarda gidan nan yake da jama'a. Ee kuma haka ne bari na d'auka naje nasa ta ko a d'akin su haidar ne tinda can ba'a shiga.

Haka zahra da ruma harma da ilham suka fuce. Zahra suna fita ka kar6i abdul a hanun ilham tare da cewa kinga bari naje na kai wa ammi shi tinda ba dad'ewa zan ba, kuje gani nan zuwa. Daga haka zahra ta wuce room d'in ammi. Har lokacin su ammi da sauran manya suna ta yiwa nana nasiha. Zahra a hanzarce ta qarasa wajan ammi sanan miqe mata abdul.

Sanan tace ammi gashi nan zamu wuce gidan amarya ba jimawa zanyi ba ki riqe shi. Kar6ar shi ammi tai tare da cewa to bari na goys shi sai kun dawo. Zahra bata sake cewa komai ba ta fuce da sauri, bayan ta fita sai da ta biya ta part d'in su faruq ta bawa haidar wayarta ya jona mata caji sanan ta wuce, motar in da su ilham suke ta fama jiranta.

Zahra tana qarasawa ba 6ata lokaci, faruq ya wuce dasu gidan yaya abdul da nana a. Suna tafe suna hirar su da dariya abinka da 'yan uwa. Zahra de tana daga gaban mota tabarwa ruma da ilham baya su zauna sabida cikin su. Basu fi 30 mint ba suka qarasa katafaran gidan nana da abdul masha Allah.

Komai yayi kyau sosai kamar yarda gidajan su ilham da zahra da ruma ya had'u itama haka gidan nana ya had'u sosai masha Allah. Lokacin da su zahra suka shiga ba kowa a gidan da yake nan kano ma tun rana suka je duba d'akin. Haka su zahra suka shiga suna ta duba ko ina dama gwara ilham tazo saud'a ana jere amma zahra da ruma basu ta6a zuwa ba.

Su zahra sun kai wajan qarfe takwas sanan aka kawo amarya tare da 'yan rakiyar mota uku. Nan da nan gida ya karad'e da qamshi da bud'a. Ba 6ata lokaci aka kawo nana da d'akin ta. Zahra tun lokacin taso tafiya amma faruq ya d'an fita siyo wani abun dan haka dole zahra ta haqura. Wajan qarfe tara faruq ya dawo zahra tana shirin tafiya aunty habiba yayar mama tace su bari sai zuwa anjima.

Su taya nana zama sabida yanzu suma zasu tafi da sauran mutane kar a barta haka tinda tace tana jin tsoro. Zahra har ga Allah bata ji dad'in hakan ba amma dole ta amsa domin yiwa aunty habiba biyayyah. Bayan mutane sun watse gida ya rage daga amarya nana sai zahra, ilham, ruma sai kuma faruq.

Zahra tana ganin goma ta kusa tace ita fa bazata zauna ba ko ita kad'ai ce yaya faruq ya kai gida sabida tana so ta koma gidan ta. Amma nana kuka ta farayi, tare da riqe zahra wai bazata tafi ba, lallai nana bana son iskanci ki rabuda dani na tafi gida kar yaya mashkhur yau ya cinye d'i d'anya sabida fad'a. Nan ma zahra kuka ta sake fashewa da shi tace aa.

Haka faruq da su ilham su kai ta bawa zahra haquri akan ta jira yaya abdul ya qaraso sai ta tafi. Da kyar zahra ta amince sai da ta cewa faruq da sharad'i komai dare zai kai ta gida in sun koma ta d'auki abdul da wayarta kuma faruq ya yarda haka, hakan ne yasa zahra ta danne zuciyarta ta zauna cike da jin haushin nana,. Zahra tana gidan nana amma hankalinta da tinanin ta yana gidan ta wajan yaya mashkhur.

Tofa abdul ango ba shi ya shigo gidan ba sai wajan qarfe goma da rabi abokan sa suka rakosa. Shima ba zuwan kan sa bane dan zahra ta takura faruq ya biga mai waya ne zasu tafi kuma nana tana jin tsoro. Zahra suna jin qarar shigowar motar abdul da abokan nan sa, suka miqe domin su tafi. Nan ma nana kuka ta saki ta sake riqe zahra.

A zuciyar zahra ta hankad'e ta fuce sai su ilham ne suka tsaya rarrashi bana sun gama su futo suka samu zahra a mota duk tabi ta canza rai a 6ace. Ba wanda yace qala har suka qarasa gida, suna qaraswa suka fita zahra ta shiga da niyar ta d'auko kayan ta da abdul ta futo faruq ya kai ta gida. Lokacin da zahra suka shiga mutane da dama sun tafi saura kad'an.

Direct bedroom d'in ammi ta wuce, kwance taga abdul yana sharar bacci itama ammi a gefan sa tana kwance amma ba bacci take ba. Hannu zahra ta kai zata d'auki abdul, ammi dakatar da ita ta hanya cewa zahra lafiya zaki tashe shi kuma yana bacci. Ammi gida zamu tafi, ammi tashi tai daga kwanciyar da tai cikin mamaki tace gida da wanan dare zahra.

Ee ammi zahra ta fad'a a taqai ce, da wanan uban daran sai kace wanda ake korar ki yanzu fa sha d'aya har da 'yan mintina ammi ta fad'a tana kallon agogo. Ah ammi yaya faruq fa yace zai kai ni ki bari na tafi bana dan ALLAH, kai zahra meye haka zai kace wanda ake tsikarar ki ki bari sai gobe da safe mana.

Nifa ammi yanzu nake son tafiya, to kin san dai dady ku ya hana faruq da haidar driven da daddare, da abdul yana nan ma shi zai iya kai ki ba matsala, kuma nasan in zaku fita dady zai iya ganin ku ta sama. Amma tinda naga a matse kike bazan hanaki tafiya ba ki kira mashkhur ya d'auke ki ban san buqatar ki ba.

Zahra ta d'an ji kunyar abinda ammi ta fad'a, a zuciyarta tana cewa lallai ammi har kin fassara, amma a fili cewa tai aa ni bani da wani uziri kawai dai ban gayawa yaya mashkhur bane kuma kin san zai min fad'a, amma bari na bari zuwa gobe. Yauwa ko kefa amma yanzu kika tafi dare yayi kuma zaki d'auki alakin abdul qarami yana bacci zaki tashe shi.

Zahra juyawa tai ta futa a zuciyarta cikin 6acin rai tace ai in ban d'auki qaramin alhaki ba zaki sa na d'auki babban alhaki na mijina. Zahra ta yanke shawarar ta bugawa mashkhur komin dare yazo ya d'auke ta, dan haka ba 6ata lokaci tana sauka ta fita daga part d'in ammi ta wuce nasu haidar.

Direct bedroom d'in su ta nufa ta fara kwankwasawa, bayan few minutes haidar yazo ya bud'e, tare da cewa sai yanzu kuka dawo kenan. Zahra shiga room d'in tsi sanan tace ee ina wayata nasan ta cika ma, ee taci ka amma yaya mashkhur fa yazo yayi ta nemanki yana jiran ki qarshe nace mai kin bar wayar taki ma anan.

Gaban zahra ne ya fad'i rass cikin tsoro tace tom me yace?. Hmm me kuwa yace amma wlh yarinya yaji haushi, jim zahra tai alamun bataji dad'in hakan ba. Hmm ai ba yanzu zaki shiga rud'u ba sai kun had'u nasan zaki sha fad'a. Hararar sa zahra tai tare da murgud'a baki tace to ni ce maka akai tsoro nake ji. Aa ni ban ce ba amma de duk wanda ya ganki yasan a tsure kike zahra.

Haidar ya qarasa fad'a yana dariyar qeta, wani siririn tsaki zahra taja tare da cewa wlh ni ko a gefen silifas d'ina ni bani wayata. Gata can kije ji d'auka baki da qafa, nama cire miki ita. Zahra tara haidar tai dan tasan da a gaban yaya mashkhur tace ya d'auko mata ba abinda zai hana shi d'auko mata, bayan zahra ta d'auka fucewa tai jiki a sanyaye.

Bayan ta bud'e ko tsaya karanta messages d'in mashkhur batai ba da suke shigowa rututu, direct call ta shiga ta danna number faruq yana, d'auka tace ya faruq ka shigo na fasa tafi ya sai gobe, daga haka zahra ta kashe wayarta zuciya cike fall da takaici ta wuce part d'in ammi, tana zuwa ta haye sama ta wuce bedroom d'in su. Ilham ta tarar da ruma zaune sun cin abinci suna hira.

Zahra kuwa ko ta kan su bata biba ta fara ranga d'awa mashkhur kira. Sau uku zahra tana kira amma mashkhur yaqi d'agawa daga qarshe ma kashe wayar tasa yayi. Zahra da taga haka messages d'in da mashkhur ya turo mata ta fara karantawa. Haka zahra tai ta bin tana karantawa yayi cigiya yiyi magiya ya bata haquri akan ta dawo yau.

Messages d'in qarshe ne da mashkhur ya turo yafi tayarwa da zahra hankali. Mashkhur cewa yayi, dan ALLAH in kinga dama karki dawo gidan kuma daga yau bazan sake cewa ki dawo ba ki ta zama duk sanda ki kai niya kya dawo. Zahra tana kai qarshen message d'in ta cilla wayar kan gado ta zauna ta dafe kan ta da hannu biyu.
Zahra ta jima a hakan can dai ta daure ta miqe ta shiga toilet domin fitsari.

Bayan ta futo dole ta dawo inda su ilham suke zauna suna cin abinci ta zauna domin itama taci sabida ita ma rabanta da abinci tun da sassafe da suka ci da nana. Hmm zahra kin fasa tafiyar kenan ilham ta tambaya tana qunshe dariyar ta. Zahra sake had'e rai tai ko kallan ilham ba tai ba ta cigaba da cin abincin ta zuciya cike da tunanin mijin ta.

Bayan su zahra sun gama cin abinci dole ta haqura ta saki ranta suka cigaba da hira da 'yan uwanta, har wajan qarfe 1 na dare. Daga qarshe dai suka kwanta, domin bacci. Daran ranar dai zahra bata iya bacci ba kwana tai tana tinanin mijin ta mashkhur ba ita ta rintsa ba sai da sukayi sallah asuba sanan ta kwanta kafin gari ya waye, hakan ne yasa bacci mai nauyi ya kwashe ta.

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

typing..........

DOUBLE PAGE.

Zahra misalin qarfe tara na safe ta tashi, tana bud'e idanta ta kalli agogo. Zahra tayi mamakin yarda har tara na safe tayi ita tayi tinanin zata tashi wajan qarfe 7 zuwa 8. Miqewq zahra tai ta shiga toilet tayi wanka da brush a hanzarce. Tana futowa ta canza kaya sanan ta wuce bedroom d'in ammi.

Bayan sun gama gaisawa zama zahra tai a bakin gado tare da cewa nifa yanzu zan tafi. Tom zahra ai ban hanaki tafiya ba, amma dai kya bari kiyiwa abdul wanka. Aa ammi ki bari in na koma zanyi mai zahra ta qarasa maganar tare d'aukar abdul. Ah kai zahra meye haka tinda ke bazaki samu damar yi mai wanka na, ki bari ni zanyi mai kafin ki gama kintsawa.

Zahra cewa tai to shikenan kiyi mai d'in. Bari naje na had'o ruwan kafin nan kya bashi nono ya sha. To zahra ta iya cewa kawai, sanan ta fara bashi. Bayan ammi ta gama had'awa abdul ruwan wanka zahra miqa masa ita tai sanan ta fita ta wuce wajan hajiya kaka domin su gaisa.

Bayan sun gama gaisawa zahra cigiyar ta fara yiwa hjy kaka akan wai ina drive ta yake?. Hajiya kaka ta sanar da zahra cewa drive ta bashi da lpy ne shi yasa. Bayan hjy kaka da zahra sunyi hira kad'an miqewa zahra tai sanan su kai sallah da hjy kaka ta wuce 6angaran su haidar. A hankula zahra ta fara knocking d'in qofar, ta d'auki mintina goma kafin a bud'e qofar.

Kai zahra kin cika naci yanzu kuma me kikazo yi da safan nan? Cewar haidar, cikin langwa6e murya zahra tace yauwa gida zaka kai ni. Oh sai yanzu kika san ina da rana kenan rashin kunyar da kike min ta kai ki. Haidar ya qarasa maganar yana fad'awa kan bed, dan Allah ya haidar, nifa baza ni ba ki tashi faruq ya kai ki.

Au dan ma kaga ina had'a ka da Allah ina langwa6e ma murya karka je d'in bari na kira yaya mashkhur yanzu na gaya mai nace ka kai ni gida kace baza ka ba. Zahra har zata fita yace to tsaya ai nasan bani kad'ai yace na kowoki ba ni ko faru. Kwarai kuwa mamma ni kai zaka kai ni ko kana so ko baka so. Tom shikenan dama ni kika rai na to naji zani aniyar ki ba niki.

murmushi zahra ta saki dama can ta fad'a ne amma tasan yanzu ko zata kwana tana kiran number mashkhur ba zai d'auka ba. Tom sai ka taso mu tafi, ah gaskiya ki bari nai wanka naci abinci tukunna.

Wani kallo zahra tai mai sanan tace bazaka je ba kenan wlh ni yanzu zan gayawa yaya mashkhur d'in, ni zaka kafawa wanan sharad'an na iska. Shima hararar zahra yayi tare da cewa naji uwar naci sai ki bari nai wanka ko? ya mutsa fusaka, zahra tai tare da cewa na baka minti shabiyar.

Ah minti ashirin zanyi kin san dai bana wanka gaggawa, to shikenan amma wlh ka wuce 20 minutes baka futo ba ko hmmm, daga haka zahra ta fuce daga room d'in. Tana fita ta koma 6angaran ammi, lokacin ammi har tayiwa abdul wanka tasa mai kaya. Ammi tayi-tayi zahra taci abinci zahra tace aa ita fa bata ci.

Tom kamar dai yarda haidar yayiwa zahra alqawari bai fi 22 minutes ba ya futo ya d'auki zahra domin ya kai ta gidan ta. Suna tafe suna fad'an su na sakwanni kamar yarda suka saba wani sa'in suyi fad'a wani sa'in suyi shiri. 30 minutes ne ya d'auki su haidar a hanya har zuwa gidan su zahra suka qarasa.

Suna qarasawa zahra taji wani sanyi a zuciyar ta kamar an cire ta daga qaya. Bayan haidar yayi horn mai gadi ya leqo bud'e komawa yayi sanan ya bud'e musu get suka shiga. Bayan haidar yayi parking kallon zahra yayi sanan yace to sai ki fita ko ni zan koma. Ah ka bari ka qarasa rakani qofa ai.

Naqi baki da qafa, ai ba sabida jin dad'i nace ba kayana zaka taya ni d'auka. To ni bawan ki ne bazan d'auka ba. Tom shikenan kar ka d'auka ni zan d'auka amma ga abdul nan ka riqe min shi zahra ta qarasa maganar tana miqawa haidar abdul, hannu biyu haidar yasa ya d'auki abdul.

Daga haka daga shi har zahra suka fuce daga motar zuciya zahra tana dukan uku-uku. Zahra taga motocin mashkhur gaba d'aya a gidan hakan ne yasa ta gane bai fita ba yana nan. Dole de sai haidar ne ya ya d'aukar wa zahra botikin sabayar ta ita kuma ta ja trolley d'in ta sukayi gaba.

Suna qarasawa bakin qofar da zata sada su da cikin gidan zahra suka tsaya, sakamakwan qofar a kulle take,. Zahra saki trolley d'in hanunta tai, sanan ta fara qoqarin zaro wayar ta a jaka, bayan ta zaro ba 6ata lokaci ta fara rangad'awa mashkhur kira har sau uku amma bau d'auka ba.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan ta mayar da wayarta jaka ta kar6i ta haidar domin ta jarraba ko mashkhur zai d'auka. Zahra haka ta fara kiran mashkhur zuciya cike fall da farga ba. Har sai da ta kusan tsikewa sanan mashkhur ya d'aga ba tare da yace komai ba. Zahra kuwa dakewa tai tare da cewa yaya mashkhur na dawo kazo ka bud'e min qofa ina!.

Zahra ko qarasa maganar ba tai ba mashkhur ya katse wayar, daga haka zahra ta miqawa haidar wayarsa sanan ta tsoguna qasa cike da damuwa. Meye kuma na tsugunawa ko bakya jin dad'i ne cewa! Haidar. Ni lafiya ta qalau na gaji da tsayuwa ne shi yasa, hmm dama ai ke raguwa ce dan de 'yar wanan tsayuwar.

Ni ga yaro a hannuna ga botikin nan nake mai shegen nauyi a hannuna, kuma gani a tsaye ban gaji ba se ke. Dariyar dole zahra tai tare da cewa ah kai kasa kan ka ai. Mashkhur ya d'auki 5 minutes kafin ya taso bud'e qofar babban falon gidan dan har sai da zahra ta fara cire rai zai zo ma. A hankula mashkhur ya bud'e qofar.

Suna had'a ido da zahra da take tsugune ya sakar mata wani mugun kallo mai cike da fassarori da dama. Hannu mashkhur yasa ya kar6i abdul da yake hanun haidar sanan ya juya ya shige ciki, yana shiga ciki bai tsaya ko ina ba ya koma sama. Tom bari na tafi haidar ya fad’a yana kallon zahra da take durqushe.

Kai sai kace wanda ake duka a gidan ka bari mu shiga ciki ko ruwan tea na baka zahra ta qarasa maganar tana miqewa. Hmmm ai naga yaya mashkhur d'in ne a fusace harya wuce a kai na banji ba ban gani ba. Janyo trolley d'in ta zahra tai sanan tace kai ya haidar sharri to kar ka shigo ka cigaba da tsayuwa ni kaga tafiya ta.

Zahra tana shiga haidar yafi bayan ta sanan ya kullo qofar. Zahra tana shiga babban falon ta ajiye trolley d'in a gefe ta jefar da mayafin ta da jakarta kan kujera sanan tace ka zauna bari na shiga kicin yanzu zan futo. Oh kiji iyayi harma sai kince min na zauna haidar ya qarasa maganar yana raqe murya sabida kar yace mashkhur bai yi nisa ba ya ji shi.

Zahra bata ce wa haidar komai ta kunna

Please Login or Register in order to submit comment