Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yafara gwada mata rubutu tasha ko ALLAH zai sa adace. Hajiya kaka tayi na’am da zancan malam Ibrahim kuma ta sheda mai insha ALLAH gobe zata shigo daga haka sukayi sallama hjy kaka ta kashe wayar.

Washegari.....

Mashkhur da su abdul duk sun tafi makaranta, momy kuwa tana 6an garanta rai a 6ace, bakomaii ne yasa ran momy 6acewaba face zuwa kadunar da dady ya hanata, kuma ba komaii zatai a kaduna ba face zuwa wajan boka dan ya kashe mata ammi. Yauma dady bazai futaba dan haka hajiya kaka ta shirya tsaf domin zuwa wajan malam Ibrahim. Driven ta ya d’auketa yakai ta har runfar malam Ibrahim.

Bayan hajiya kaka sun gama gaisawa da malam Ibrahim ta fara koramai jawabi akan yadda cutar ammi take. Tana gama yimai bayani malam Ibrahim ya sheda mata cewa bakomaii ne yake damun ammi ba face SIHIRA da ASIRI. Hjy kaka tayi mamakin hakan sosai dan dama ta dad’e tana tunanin anya ba asiri akayiwa maryam ba.

Maganar Malam Ibrahim ce ta dawo da hjy kaka daga tinanin da ta tafi, amma in sha ALLAH zan yimata rubuta sai ki fara bata muga abindda ALLAH zai yi. Jinjina kai hjy kaka tayi tare da cewa yanzu malam Ibrahim wa yayi mata asirin nan haka, girgiza kai malam Ibrahim yayi tare da cewa gaskiya hajiya fatima ni bazan sheda wandda yayi mata hakan ba kinsan dae ance zato zunubi ko? Hakane malam Ibrahim tom ALLAH yasa mu dace.

Daga haka sukayi sallam sanan malam Ibrahim yace mata zuwa jibi ta dawo dan kar6o mata rubutu.
Wunin ranar haka hajiya kaka tai ta saqe-saqe da warwara, dan tasan ko ba’a gayam mata ba momy ce tayiwa ammi asiri, dan tasan halima zata iya aikata komai, tun alokacin da tace zata raba abdul da ammi, kuma tasan sam ba d’ugwan imani a zuciyar halima (momy). Wunin ranar dai haka hajiya kaka taita saqa da warwara.

Washegari dady bai futaba koma su abdul da mashkhur sun tafi tafiz dan haka hajiya kaka ta shiya tsaf domin zuwa wajan malam Ibrahim. Lokacin da taje malam ibrahim ya gama yuwa ammi rubutun, kuma yayiwa hjy kaka bayanin yadda zatai amfani da shi, bayan hajiya kaka tabawa malam Ibrahim sadaka ta dawo gida. Bayan ta dawo gida tayiwa dady bayani akan rubutun amma bata gayamai cewa asiri akayiwa ammi ba.

Dady yajin dad’in hakan sosai dan shima yanzu ya gaji da maganin asibitin. Washe gari hjy kaka ta fara bawa ammi rubutun da addu’o’in da malam Ibrahim ya bata, dama rubutun na sati guda ne.
Kullum hjy kaka sai ta bawa ammi rubutun yau kimanin kwana uku kenan kuma ana samu cigaba tindda gashi yanzu ammi tana d’an motsa ga6o6in jikinta.

Kuma kowa yana farinci da hakan, badda momy wacce batasan abinddama akeyi ba, tana nan tana shirye-shryen zuwa wajan boka, sabida ta kashe ammi,, amma dady ya hanata zuwa kadunan. Shima dady yanzu ya fara zargi momy akan cutar ammi sabida yasan halinta, amma kuma sai ya kawar da zargin azuciyar sa sabida yasan bakyau zargi kuma ba lallene hakan ta kasance ba, amma sam bai gaya mata cewa ammi ta fara samun sauqi ba.

Yau kimanin kwana uku da gama bawa ammi magani kenan, indda take d’akinta a kwance amma dai har yanzu bata fara tafiya da magana ba.
Daga dady har su mashkhur da hajiya kaka suna zaune a falon ammi suna hiira. Suma su zahra da ilham suna gefan kaka suna wasa kamar yadda suka saba.

Dady ne yake tambayar mashkhur in ya gama karatu yayi condy wace qasa yakeso ya fitar da shi domi ya cigaba da karatu. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ni dae gaskiya dady bana son natafi wata qasa karatu ni dae kawai ka barki a Nigeria na cigaba da karatuna. Murmushi dady yayi tare da cewa babana ai university d’in Nigeria yanzu ba’a wani karatu mai inganci kullum yajin aiki ake tafiya kuma naga kana da qoqari sosai in kasamu kaje kayi karatu acan zaka qara qoqari.

Aaa ni dae dady nifa bana son na tafi bana ganiku nafison kullum na ringa ganin ammina da hjiy kaka da kuma ku, jinjina kai dady yayi a zuciyarsa yana tinanin taya zai shawo kan mashkhur yaje yayi karatun nan, dan yasan mashkhur da taurin kai. Dady tundda yaya mashkhur bazai jeba ni kawai ka kaini wacce qasa zaka kaini, abdul ne yake fad’in hakan. Murmushi jin dad’i dady yayi sabida yasan ko ba komai abdul nan gaba zai zamo yaro mae biyayya da jin maganar sa bakamar mashkhur ba.

Tom abdul shikenan kaza6i wace qasa kakeso kaga kai sai katafi in kayi condry koh?. A dai-dai lokacin zahra ta riqe qafar mashkhur domin ta miqe tsaye, ai kuwa da qarfi mashkhur yasa qafa ya bige ta jikake qumm kamar dae yadda yayi mata a baya. Qararce ta janyo ankalin kowa a wajan abdul har zai bawa dady amsar tambayar yaji qarar wad’owar zahra.

Kuka zahra ta farayi sosai sabida fad’uwar yau tafi ta baya, da sauri dady ya taso ya nufi indda zahra take ta kuka itama kakan tasowa tai rai a 6ace. Kai ashe baka da hankali ban saniba eyee ? dady ne ya fad’i hakan a tsawace itama hajiya kaka cewa tai mashkhur wanan wana kalar haukane haka? Abdul kuma cikin 6acin rai ya tsuguna ya d’auki zahra yana rarrashin ta, ji yake kamar ya daki yayan nasa amma bazai iya ba.

Tom bari kaji Wallahi tallayi daga rana mae kamar tayau ka sake yiwa mamana haka Wallahi sai na 6ata maka, zaka sha mamaki Wallahi in badda zalinci da mugunta qaramar yarinya zaka kama ka tureta kai da QANWARKA?. Dasauri mashkhur ya d’ago daga sunkuyar da kan dayayi tare da cewa qanwata kuma dady? Mamaki ne ya bayyana a fuskar dady da hajiya kaka, ran dady ya gama 6aci sosai bai ta6a tinanin abin mashkhur ya kai hakaba.

Sautin tafiyar ne yasa kowa juyawa domin suga waye yake futowa daga bedroom d’in. Ae ba wandda bai girgiza da ganin wandda take futowa ba 🙀 dan kowa mutuwar tsaye yayi, bakowa bace face AMMI ahankali take takawa kana ganinta kasan jikinta baiyi gwariba tafiyarma da qyar takeyi. Aguje faruq da hadar suka nufi ammin domi su rongumeta a hanzarce hjy kaka ta ruqosu tare da cewa ku bari mana karku yar da ita, jikinta ba qwari ai.

Alhamdulilah ALLAH mungode ma cewa hjy kaka shikuwa dady sujjada yayi yana godewa ALLAH mashkhur da abdul suma Alhamdulilah kawai suke furtawa. Da sauri hajiya kaka ta qarasa indda ammi take tare da ruqota dan ta temaka mata. A hankula suka ringa takawa har suka qarasa wajan kujera, a hankali hjy kaka tazaunar da ammi. Tofa nanfa yara suka fara rige-rigen hawa kujerar da ammin take.

Kowa sannu yakewa ammi itakuma tana amsa musu da yauwa. Hmmmm tsayawama gayawa mae karatu yau farincin da mutun gidannan suke ciki 6ata bakine sabida farin ciki ko abinci basuciba, batun zalincin da mashkhur yayiwa zahra ma an manta da zancan. 6angaran momy da tasamu labari kuwa baqin cikine yakusan kasheta dan sai da tayi suman tsaye, kuma mamaki take taya akai ammi ta samu sauqi kuma wayakarya mata asirin?. Oho babu mai bata amsa.

Wunin ranar haka momy ta wuni cikin matsanancin baqin ciki. Ji take kamar taje ta shaqe ammi ta mutu.
Dare yayi sosai kowa ya tafi makwancin sa, ammi tana tare da ilham da zahra da kuma hjy kaka sabida har yanzu jikinta bae gama qwari ba, dady kuwa yana part d’in momy da yake yau a part d’in ta yake, su mashkhur da abdul dasu faruq suna d’akin su.

Faruq da haidar da abdul suna gado d’aya suna bacci, bakomai ne yasa abdul ya baro mashkhur a gadan su ba ya dawo kusa da su faruq bace abindda mashkhur yayiwa zahra yau bah, tindda yake bai ta6a tij haushin yayan nasaba ko yaqi kwana a kusa da shi sai yau daya ta6a masa zahran sa, dan abdul da bayasan mashkhur kuma baya jin tsoransa yau sai ya ramawa zahran sa, dan abdul kullum in zahra tana kuka sai ya tuna da abidda mamanta tace mai, akan ya kula da zahra qanwar sace.

6angaran mashkhur kuwa har wajan shabiyun dare ya kasa bacci, sabida baqin ciki, bakomai ne yake damun saba face 6acin rai fad’an da baqakyan maganganun da dady da hajiya kaka sukayi mai ba. Abun d’aya yake furtawa a zuciyarsa shine, ADALILINTA mahifina ya fara yimin fad’a ADALILINTA mahifina yayi fushi dani ADALILINTA kakata tafarayimin fad’a, ADALILINTA aka farayimin tsaya, ADALILINTA ma qanina Abdul wandda nafi so cikin qanne na ya gujeni haushin yakeji.

Abindda mashkhur yake ta fad’a azuciyarsa kenan, wata mumunar tsana da kyamar zahra ce ta kama mashkhur, gawani mugun ciwan kai da yake damunsa. Aganin mashkhur yauce ranar da tafi dacewa yayi bacci mae dad’i, kuma ya dad’e yana fatan ranarnan tazo sai gashi tazo mai a baqin ciki duk adaililin zahra. Tundda ammi ta fara cuta mashkhur baya wani bacci mae dad’i kuma yayai al qawarin duk ranar da ammi ta samu lafiya zai yi bacci mae dad’i sai gashi adalilin zahra ya kasa.

Ya salam abindda mashkhur ya frusta kenan tare da dafe kansa da yake mae ciwo, adaddafe ya miqe ya bud’e durowa ya 6alli maganin ciwan kai yasha, sannan ya koma ya kwanta, haka mashkhur yayi ta tunani kaka-kala zuciya cike da baqin ciki. Sai wajan ukun dare mashkhur ya samu yayi bacci.
In kacire momy da mashkhur daran ranar kowa da farin ciki ya kwana, musamman ma dady, abdul da kuma hajiya kaka.

Tom haka ammi tai ta jinya cikin kulawa da farin ciki da yaranta suka sata, ko quda basa bari ya ta6a ammin tasu musamman ma abdul kullum yana maqale da ammin bacci ne kawai yake rabasu. 6an garan momy kuwa kullum cikin baqin ciki take gashi dady ya hanata zuwa kaduna barema taje wajan bokan nasu. 6angaran mashkhur kuwa ya qara tsanar zahra ko hanya baya son su had’a.

Hjy kaka kuwa ta koma wajan malam Ibrahim ta kar6owa ammi maganin tsari yadda ko asiri da sihiri akayi mata bazi sake kamata ba.
To yau kimanin sati uku da samun sauqin ammi kenan, tasamu sauqi tayi garau abinta, amma sai dai haryanzu jikinta bai dawo ba, amma a hankula take qibar.
Tom rayuwar gidan nan tacanza saka makwan samun lafiyar ammi, kowa cikin farin ciki yake yanzu ammi tana kula da yaranta da kuma mijin sosai, harma da hajiya kaka.

Dan yanzu hajiya kaka ta samu hutu ammi ce takewa su zahra komai kuma a wajanta suke kwana. Yau wata biyu kenan da samun sauqin ammi, sukuma zahra da ilham shekarar su guda sunyi kyau sun qara qiba ga wayo musamman ma zahra dan kamar balarabiya haka take, har sun d’an fara tafiya. Dady ya yanke shawarar mayar da zahra gaban iyayan ta amma sai bayan sun dawo daga saudiya shida ammi da kuma hajiya kaka.

Lokacin da labari ya iske momy za’a je saudiya ba ita ansha bala’i iri-iri a gidan nan, kuma tace wallahi sai antafi da ita. Shikuma dady yace bazai je da itaba sai wata shekarar sai dai ta zauna ta kula da su mashkhur. Tofa bala’i yaqici yaqi cinyewa, hakan ne yasa ammi tace ita ta haqura da zuwa makan atafi da momy wata shekarar taje ita takula da yaran harma dasu rukayya da rumaisan.

Dafarko dady bai yadda da hakan ba sai da hjy kaka tasa baki sanna ya amince badan yason ransa ba.
Tofa su dady sun fara shirye-shiryen tafiya saudiya dan yanzu bai fi saura sati d’aya ba. Momy kuwa ta kafe akan bazata barwa ammi ‘yayanta sae dai ta kai su kduna wajan mahaifiyarta. Masifar momy ta ishi dady dan haka zuba mata ido yayi kawai. Haka momy ta kama hanyar kaduna, ko da taje kadunar gidan qanwarta saratu ta kai rukee da ruma,

duk da kuwa dady bai saniba dan da yasan nan zata kai su bazai bari ba sabida dady ya tsani saratu dan har yanzu baya bari saratu tazo mai gida.
Tom yau su dady da hajiya kaka da kuma momy jirginsu ya d’aga zuwa saudiya.
Ammi kuwa tana gida tana kula da yaranta.............

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA I BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*page 38*
Tom yau su dady da hajiya kaka da kuma momy jirgin su ya d’aga zuwa saudiya. Ammi kuwa tana gida tana kula da yaranta.........

Tom yau kimanin sati biyu kenan da tafiyar su dady, ammi kuwa tana gida ita da yaranta hankali kwance, kullum mashkhur da su abdul suna zuwa makaranta, itakuma ammi tana zaune ita da ‘yan biyun ta wato zahra da ilham wandda yanzu har sun fara tafiya.
Yauma mashkhur sun dawo daga makaranta ya baje littattafai yana assignment, yana cikin yin rubutu yaji fitsari, nan da nan ya tashi ya tafi d’akin sa domin yin fitsari.

Zahra da ilham ne suka shigo falo riqe da hannun juna, sun samu falon ba kowa sai littattafan mashkhur abaje a wajan. Da sauri ilham ta nufi indda ya ajiye littafin da biro, tana zuwa ta d’auki biron ta fara jagwalgwalo a littafin da mashkhur yake assignment, bayan ta gama ta miqawa zahra littafin da biron alamin itama tayi jagwalgwalon, kar6a zahra tayi bata kai da rubutun ba mashkhur ya shigo yaga book d’in a hanunta.

Ae kuwa zahra tana ganin mashkhur ya nufo su tai sauri ta yarda littafin da biron ta shige bayan ilham a tsorace, sabida zahra tana mugun tsoran mashkhur sabida zalincin da yake mata. Yana qarasowa ya janyo hannun tare da zafga mata mari har sau biyu, ae kuwa karaf akan idon ammi, ya kai hannu zai bige bakinta yaji wani gigitanccan saukar mari a kuncin sa. A razane ya jiyo domin ganin waye ya mareshi haka?.

Yana juyowa yayi tozali da ammi rai a b’ace take kallan sa. Da sauri ya riqe kumatinsa tare da cewa ammi laifin mai nayi haka, kike dukana cikin mamaki yake maganar, wani wawan kallo ammi ta jefa mai tare da cewa wai mai sunan baba mai zahra tayima haka ne kake takurawa rayuwar ta, na lura kana zalintar Zahra to wlh ka cigaba da dukan yarinyar nan sai ka fuskanci 6acin rai na. Tana gama fad’in hakan mashkhur ya wuce dakin sa da sauri yabar ammi tsaye a wajan.

Jinjina kai ammi tai a zuciyarta tana mamakin zalincin da mashkhur yake yiwa zahra, shida ko kallan banza baya yiwa sauran qannan nasa. Tsugunawa ammi tayi ta fara rarrashin zahra da ilham, dama haka zahra da ilham suke indai d’aya daga cikinsu ta fara kuka haka suke zama sita kuka kamar wasu ‘yan biyu. Haka ammi tai ta rarrashin su zahra har sukayi shiru.
6an garan mashkhur kuwa yana zuwa d’aki ya fad’a kan bed ya saki kuka mai cin rai.

Tinda mashkhur ya mallaki hankalin kansa” ammi bata ta6a sa hannu ta dakesa ba sai yau kuma adalilin zahra, haka mashkhur yay ta kuka yana jin tsanar zahra tana qaruwa a zuciyar sa, kuma yana sake addu’ar ALLAH ya dawo da su dady lafiya a mayar da zahra gidan ubanta. Koma suwaye iyayan nata ohoo ALLAH yasa tana da iyayan ma?, haka dai mashkhur yay ta zancan zuci shi kad’ai a d’aki.

Tom yau su dady sunyi sati uku ya rage saura sati d’aya su dawo. ammi kuwa kwalema take sosai a gidan, tama gama gyara part d’in ta. Yanzu part d’in hajiya kaka ne kawai ya rage dama momy ta kulle part d’inta kuma bata barwa ammi mukullun ba. Yau ya rage saura kwana uku su dady su dawo kuma yau ammi da abdul da kuma mashkhur suka shiga part d’in hjy kaka domin su gyara mata kuma su fitar da tarkace.

falon hajiya kaka ammi ta fara gyarawa su kuma su abdul da mashkhur suka shiga bed room suka fara futo da abubuwa marasa amfani. Sai da mashkhur da abul suka futo da tarkace da takaddu da kuma sauran abubuwa marasa amfani botiki guda suka tara, ammi kuwa cewa tayi tinda da akwai fallan Qur’ani aci su futa waje su kai wa mae gadi ya qona. Haka mashkhur da abul suka tafi suka kai wa mai gadi harda ashanar da zai qona. Ba 6ata lokaci mai gadi ya qone takaddun da su mashkhur suka kawo masa.....

Yau juma’a kuma yau ta kasance ranar da su dady zasu dawo daga saudiya. Ammi kuwa tayi girki kala-kala ta shirya tsaf tayi lalle tayi kitso, su mashkhur sun shirya tsaf sabida murna yau ko makaranta basuje ba. Suma su zahra da ilham an shiraya su ansa musu kaya kala d’aya in kagansu sai ka rantse irin yan biyun nan ne marasa kama duk da basa kama amma da yake fararene ba kowane yake kula da hakan ba.

Tofa su dady sun sauka garin NIGERIA cikin qoshin lafiya, ammi dasu mashkhur dama sauran yaran gidan sunyi farin ciki sosai. shima dady yayi murna da ganin su ammin da sauran yaransa lafiya kuma yayi missing d’in su sosai mussaman ma matar sa ammi. 6an garan hajiya kaka itama tayi farin ciki sosai kuma ta siyowa jikikon ta tsaraba kala-kala musammanma zahra da mashkhur dan duk jikokinta tanaji dasu.

Shima dady yasiyo muso tsaraba kala-kala musammanma matarsa ammi, momy kuwa ba’abindda tasiyiwa ‘yayan ammi ta dae suyowa d’anta abdul da kuma rukayya da rumaisa’u.
Tofa su dady sun kwana cikin qoshin lafiya washe gari momy ta shirya tsaf ta nufi kaduna domin kaiwa saratu tsaraba da iyayanta daga nan kuma ta daukko su ruma. Lokacin da taje kafin ta dawo har wajan boka sukaje amma bayanan haka ta dawo rai ba dad’i.

Tom yau su dady satin su biyu da dawowa daga saudiya, kuma yau dady ya tara matansa dama hajiya kaka domi su shawarta yadda za’a mayar da zahra gaban iyayan ta.
Dady ne zauna akan kujera ammi tana gefansa na dama ita kuma hajiya kaka tana kujera a gefansu itama momy tana kan kujera a zaune, zahra tana kan cinyar hajiya kaka ita kuma ilham tana zaune a gefan qafar ammi tana wasa.

Bakowa a gidan sai su kad’ai mashkhur da abdul da kuma faruq da haidar suna makaranta rukee da ruma suna part d’in momy suna bacci sabida mugunta sam momy bata barinsu su futo suyi wasa da ‘yan uwan su wai ammi kwace su zatai kamar yadda ta kwace abdul.
Dady ne yayi gyaran murya tare da cewa abindda yasa muka taro anan bakomai bane face mu mayar da zahra gaban iyayanta.

Kowa yayi shiru kwalla har ta taro a idon ammi sabida harga ALLAH tanajin zahra a zuciyar ta, dan jinta take kamar ‘yar data haifa a cikinta. Itama hajiya kaka bataji dad’i hakan ba, amma bayadda ta iya sabida itama tanaso ta mayar da amanar da aka bata, shima dady basan tafiyar zahra yake ba sabida harga ALLAH yana son zahra har zuciyarsa. Hajiya kaka ce ta katse shirun da cewa hakane amma yanzu abindda zai fi sauqi shine mu daukko takardar da mahaifiyarta ta bawa abdul ai akwai address d’in gidan a ciki kaga bazamu sha wahalar gano gidan ba.

Kwari hakane zuwa gobe sai muje ni da ke hajiya da kuma maryam d’in, dady ya qarasa fad’i yana kallan ammi, share hawayan ammi tayi tare da cewa hakane yaya ammafa ni gaskiya banason rabuwa da zahra, wani dogwan tsaki momy taja wandda tundda aka fara maganar batace uffan fa, cewa tai ai kuwa maryam rabuwa da zahra ya zama dole tindda bake kika haifeta ba kuma nan ba gidan UBANTA bane.

Tana kai qarshan maganar dady ya dakatar da ita !!! Dakata halima nifa banason rashin mutunci ke kullum bakinki baya furta al khairi, tundda hajiya da maryam ne suka raini zahra dole suji d’acin rabuwa da itama nima kai na ina qaunar zahra ke bama ni kadai ba har sauran yaran gidannan musammanma abdul da ilham dan nasan duk yaran gidan nan ba wandda ya shaqu da zahra sama da abdul da ilham.

Hakane Abubakar dan nasan yaran gidan nan zasuyi maraicin zahra dan in aka cire mashkhur da abdul a yaran gidan nan bawandda yasan zahra ba ‘yar gidan nan bace dan su a tinanin suma ‘yan biyu ita da ilham, cewar hajiya kaka. Hakane hajiya amma bayadda muka iya yanzu kije ki daukko takaddar addres d’in gidan kafin gobe zansa a binciko min gidan nasu, bamusu hajiya kaka ta tashi tare da kwantar da zahra da take ta sharar bacci, sanan ta wuce part d’in ta dan d’akko takaddar.

Momy kuwa a zuciyarta ta qullaci hajiya kaka amma tadau al washin sai taga bayan ta sabida tana shigar mata hanci da qudindine. Tawani fannin kuma tana farin ciki gobe za’a mayar da zahra gida sabida momy ta tsani zahra sosai dan ko kallata bataso tayi.
Tofa kimanin minti talatin kenan su dady suna jiran hajiya kaka amma shiro.

Ammi ce ta shawarci dady akan suje su duba ko lafiya sukaji hajiya kaka shiru, ba musu dady ya amince ita dai momy bata bisu ba tana zaune a falon ammi tana qarewa zahra harara, ita dai zahra batama san abindda take ba dan bacci takewa.
Lokacin dasu ammi suka qarasa wajan hajiya kaka sun sameta duk ta futo da kayan wardrobe d’in ta duk tabi ta hargitsa bedroom D’in. Dady ne yace hajiya lafiya kika hargitsa d’akin ko bakiga takaddar bane?.

Dagowa hajiya kaka tayi tare da cewa ehh wlh tun dazu nake neman takaddar ban gantaba, to hajiya ke a ina kika ajiye takaddar ne wai? Cewar ammi. Wlh maryam a cikin durowar mudubi na ajiye kuma ko kafin mutafi saudiya naganta. Da sauri ammi ta dafe qirji tare da cewa INNALILLAHI wa’inna’ilaihirraji’un da sauri dady da hajiya suka kalle har suna had’a baki wajan cewa maryam lafiya.

Ajiyar zuciya ammi tai tare da cewa ai kuwa kafin ki dawo munyi kwalema a d’akin nan harma su mashkhur sun tara takaddu kuma sun kai mai gadi ya qona shine nake tinanin anya basu had’a da takddarnan ba aciki?
Aaa baza mu yanke hukunci yanzuba wata qila sun ajiyeta a wani wajan bari su dawo daga makarnta sai a tambaye su, cewar dady.

Jinjina kai hajiya kaka tayi tare da cewa gaskiyane to ALLAH ya dawo dasu lafiya, dukkan su suka had’a baki wurin cewa Ameen.
Misalin wajan qarfe biyu abdul ya dawo daga makaranta, dama su faruq da haidar sun rigashi dawowa shikuma mashkhur sai qarfe hadu zai dawo. Bayan sunci abinci sun hutu suka wuce islamiyya. Mashkhur kuwa sai wajan qarfe hudu da wani abu ya dawo gida, ko da yadawo gida yaci abinci sanan yayi wanka ya kwanta bacci.

Bayan dady ya dawo da magriba ya kirawo abdul da mashkhur, domin tambayar su tskaddar address d’in gidan su zahra. Dady, ammi, momy,hajiya kaka, mashkhur, abdul, duk sun hallara a falon. Ammi ce ta fara magana kamar haka!! Yauwa mashkhur dama su muke mu tambayeku, har suna hada baki wajan cewa to ammi munaji, yauwa dama tambayar ku zanyi lokacin da kuna gyarawa hajiya d’aki bakuga wata takadda a durowar mudubi ba????.

Shiru sukayi ko wannan su ya tafi tunani, dady ne ya katse su ta hanyar cewa ko bakuganta bane?. Acin avellinese take? Dasauri hajiya kaka tace ehh aciki take. Ehh NAGANTA, cewar mashkhur, har suna had’a baki wajan cewa to tana ina? NAYAGATA kuma ANQONATA. INNALILLAHI mashkhur mai yasa kayi hakan shikenan ka cucemu! Momy ce mai fadar hakan cikin tashin hankali.

Murya a sanyaye dady yace mai sunan baba meyasa ka yaga takaddar kuma ka kai aka qona? Dady wlh bansan takaddar tanada amfani ba kuma ban karanta kafin na yagaba.
Falon ya dau shiru kowa jimami yake itakuwa momy sai fama zubawa mashkhur bala’i take. Mashkhur yayi mamakin fadan da yaga momy tanayi ita da batayi mai fada sam bata ganin laifin sa, a zuciyar

Please Login or Register in order to submit comment