Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a tana zubawa ilham ido. Eh ammi zan gaya miki wlh nima ina son shi kamar yadda yake so na, duk da ammi tayi mamamkin maganar ilham amma bata numa mata ba cewa tai, to ya sunan shi?.

Sunkuyar da kai ilham tai tare da cewa! Sunan shi AHMAD, kafin ta qarasa rufe baki ammi ta sake cewa! A ina kuka had'u da shi?, uhm a rasha muka had'u da shi, cikin mamaki ammi tace rasha kuma? Gyad'a kai ilham tai tare da cewa! Ehh kin san shi ma ai, wanan fa abokin yaya mashkhur d'in wanda suke karatu tare a rasha.

Gyad'a kai ammi tai tare da cewa! Ehh nasan shi, tom ammi shine. Okay tun yaushe kuka had'u da shi?, tun lokacin da mukaje rasha lokacin muka had'u. Gyara zama ammi tai tare da cewa! Lokacin da kuka fara zuwa ko kuam lokacin da kuka kai musu ziyara. Gyad'a kai ilham tai tare da cewa! Ehh lokacin da muka kai musu ziyara.

Lalai ilham sannun ki da qoqari kin kyauta kuma ban ta6a tianin zakiyi aika ta hakan ba batare da sanin mu ba, ammi ta fad'i hakan fuska ba walwala. Ilham kamar zatai kuka tace ammi kiyi haquri wlh lokacin ji nai bazan iya gaya miki ba, Sabida nasan kona gaya miki ba lallai ki amince ba. Ehh ai gashi yanzu kinyi gaban kan ki, yanzu ilham har kinyi girman da zaki yankewa kanki hukunci ba tare da sanin kowa ba,.

Girgii lza kai ilham tai fuska cike da kwalla, tace aa ammi na gayawa hajiya kaka fa, jinjina kai ammi tai tare da cewa! Shikenan ALLAH ya tai maka tashi kije. Nan da nan hawaye suka fara shararowa ilham, cikin muryar kuka ilham tace! Dan Allah ammi kiyi haquri wlh bazan qara hakan ba.

Murya a shaqe ammi tace to yanzu mai kikaji nace dukan ki nayi ko fad'a nayi miki da kike bani haquri. Cikin kuka ilham tace aa ammi amma nasan fishi kikeyi dani kuma ni da naga kina fishi dani gwara kin dake ni ko kinmin fad'an komai ya wuce. Yo ilham yanzu mai kikeso nayi tinda kin riga da kin za6awa rayuwar ki abindda Ya dace shikena ai.

Girgiza kai ilham tai tare da cewa aaa ammi ni yanzu in bakya so sai na rabu da shi ammi, ni dai kawai so nake ki yafemin. Da sauri ammi ta girgiza kai tare da cewa! Aaa ilham ni bazan ta6a rabaki da abinda kike so ba, kuma komai ya wuce ALLAH ya tai maka, kawai dai inaso nace miki ki kiyaye gaba, ya kamata in zaki abu ki ringa sanar da iyayan ki kuma bana so ki ringa qarya akan gaskiya.

Ajiyar zuciya ilham tai tare da cewa! Yanzu ammi kin amince da ahmad d'in gyad'a kai tai ammi tare da cewa! Ai ahmad yana da hankali sosai mutumin kirki ne ni dai bashi da wani ai bu a waje na, yanzu dai sai ki jira hukuncin da dadyn ki zai yanke. Murmushi ilham tai tare da cewa! In sha ALLAH dady zai amince ma.

D'an hararar ta ammi tai tare da cewa! Wawiya kawai ai ba haka nake nufi ba ina nufin zai amince da aure. D'an zaro ido ilham tai tare da cewa! Haba dan ALLAH ammi yanzu sai yace aa?, to ke kina son ai miki aure yanzu ne? Ammi ta watsawa ilham tambayar on expected, jim ilham tai dan sai taji kunya ta d'an kama ta ka d'an.

Murmushi ammi tai tare da cewa! Hmm bakya son aure yanzu koh? Ai nasani. Wani kallon rashin gamsuwa da maganar ilham ta watsawa ammi tare da cewa! Ina so mana. Sosai ammi ta zaro ido cikin mamaki tare da bud'e bakin ta tasa hannu biyu ta toshe bakin ta, alamun tsantsar mamaki. Ilham kuwa da sauri tasa hannayan ta duka biyun a rufe fuska ta rufe ta gam alamun kunya.

Dan dukan ta ammi tai da hannu tare da sa hannu ta janye wa ilham hannu daga rufe fuskar da tai tare da cewa! Dallah can bud'e fuskar ai ba wata kunya da zaki ji tinda har kika kalli ido na kikace aure kike so, tana bud'e fuskar ilham suna had'a ido da ammi suka had'a baki suka saki dariya mai sauti kamar wasu qawaye, koma nace kamar dai zahra da ilham suna hira.

Suna cikin haka su kaji an murd'a Handel d'in qofar, daga ilham har ammi zubawa qofar ido sukayi dan ganin mai shigowa. Dady ne ya shigo baki d'auke da sallama, ammi da ilham har suna had'a baki wajan amsa sallamar, dady barka da yamma ilham ta fad'a fuska a sake. Shima dady fuska a sake yace yauwa dai ilham, yakike da fatan kina lpy, murmushi ilham tai tare da cewa lpy qalau dady.

Dady kuwa cewa! Yayi masha Allah sanan ya mayar da kallansa kan ammi yace hadair yana nan kuwa? Girgiza kai ammi tai tare da cewa! Aa baya nan, faruq fa dady ya sake tambaya a karo na biyu. Ammi sake girgiza kai tai tare da cewa! Shima baya nan tare suka fita flin ball, basu dad'e da fita ba.

Okay dama ahmad ne abokin yayan su shine nake so su kai mai drinks amma dai tinda basa nan ilham sai ta kai mai, muna sitroom d'in baqi ilham ki kawo mai ruwa kinji, dan gaban ilham ya fad'a kad'an amma sai ta dake kamar batasan da zuwan saba tace tom shikenan dady, daga haka dady yayi fucewar sa.

Ilham kuwa wata siririyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin wani siririn murmushi dan ita tama manta da wata ammi a wajan. Ammi kuwa girgiza kai tai tare da cewa! Ilham kin 6ace da rashin kunya ALLAH Ya shirye ki, dago wa ilham tai tare da cewa! Ammi mai nai, harara ammi ta d'an watsa mata tare da cewa ban sani ba,.

Ni tashi ki bani waje kije ki kai wa masoyin naki ruwa da lemo murmushi ilham tai tare da cewa! Kai ammi, itama ammi murmushi tai tare da cewa au qarya nai ne ko ba masoyin naki bane,, dariya ilham tai tare da miqewa ta d'auki hijab d'in ammi da yake gefen bed d'in, har tana qoqarin sa hijab d'in taji ammi tace, hmm gaskiya anyi sha-sha-sha kuwa haka zaki tafi wajan nasa ko fuskarki baki wanke ba, bayan kinyi kuka.

Au wlh ammi na manta ilham ta fad'a tare da ajiye hijab d'in ta, hmm ke kuwa ba dole ba kin matso kije kuka juna koh? Ammi ta fad'a cikin zaulaya, d'an yamutsa fuska ilham tai tare da cewa! Kai ammi haka nace miki, girgiza kai ammi tai tare da cewa! Bake kika gayamin ba masoyin naki ne naga ya rubo ta, a message ya matsu ya ganki kema, wataran kina wayan ce mai kin matsu ya dawo ki gan shi ko ba'a yi haka ba? ammi ta fad'a tana tsare ilham da ido.

Cikin jin kunya ilham tace kai ammi yanzu sai da kika bi messages d'in kika karanta,, ni dallah shige ki bani waje bana san borin kunya, ammi ta fad'a hakan fuska a sake, murmushi ilham tai tare da wucewa toilet ta wanke fuskar ta. Tana futowa ta zura hijab jikin ta duk sai wani rawa yake, tana gama zurawa ta fuce da sauri.

Ammi kuwa murmushi tai tare da cewa! Kai yaran yanzu ALLAH ka shirya mana su. 6angarn ilham kuwa tana fita daga bedroom d'in ammi qasa ta sauka tana sauka ta wuce kicin ta d'auko plate da cup, sanan ta dawo falo ta bud'e firinji ta d'auki ruwa mai sanyi da holandian sanan ta d'ora a plate d'in ta fuce.

Tana fita dreck sitroom d'in baqi ta nufa, tana zuwa qofar sitroom d'in ta d'an tsaya gabanta sai dukan tara-tara yake kamar ba itace take zumind'in zuwa ba. Sai da tad'an jima a tsaye a bakin qofar sitroom d'in kafin can tayi ta maza ta shiga. A hankula ilham ta sa qarafa a sitroom d'in ta shiga, tana shiga taji dad'in turaran ahmad ya daki hsncin ta, tana d'aga kai idon ta ya sauka akan ahmad, fuskar nan tasa cike da walwala.

Ya qara kyau da girma, ba kamar da ba ilham sai taga ya fiye mata kyau sosai a zahiri fiye da video call d'in da suke. Duk a kallo d'aya ilham ta gane hakan murya a sanyaye ilham tai sallama da sauri ahmad da d'ago ya zuba mata kyawawan idanuwan sa. Suna 4 eyes gaban su ya yanke ya fad'i rass, rass, a tare, ilham kuwa da sauri ta kawar da kai daga kallon ahmad dan kar dady ya gano wani abun...............

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

typing............

Double page.

Yau double page zan muku sabida ranar mondy ban yi muku typing ba.

Suna 4 eyes gaban su ya yanke ya rass, rass, rass, a tare, ilham kuwa da sauri ta kawar da kai kar dady ya gano wani abun...............

Sannu a hankula ilham take takawa tana qarasawa gaban ahmad d'in ta durqusa tare da cewa! Ina wuni, da sauri shima ahmad ya d'an kau da kai kar dady ya gane tare da cewa! Lpy qalau, da fatan kina lpy? A taqai ce ilham tace ina lpy qalau. Daga haka ilham ta miqe har zata fara tafiya dady yace! Haba ilham hake ake kawo ruwa, ki zuba mai a cup mana.

Jiki na sassarfa ilham tace to sanan ta koma ta tsuguna ta bud'e bottle d'in ruwan ta zuba a cup sanan ta d'ago tare da miqawa ahmad cup d'in hannu na rawa ahmad ya sa hannu y kar6i cup d'in. Suna had'a ido ilham ta d'an kashe mai ido d'aya tare da sakar mai wani murmushi mai kashe zuciyar masoya,, da sauki ahmad ya d'an firgita sabida ruwan da yaji yana qoqarin saki, saura qiris cup d'in da ilham ta bashi ya fad'i, sabida yadda ilham ta kashe mai ido ya tafi da shi.

Ilham kuwa tana ganin haka tai sauri ta kama hanyar fucewa daga sitroom d'in. Ahmad kuwa sakin baki yayi ya fara bin ilham da ido harta fuce daga d'akin dan shi yama manta da wani dady a wajan. Dady kuwa shiru yayi yana kallan ikwan ALLAH. Nikuwa amina bayero nace kai ahmad ka bada maza ba wai.

To bari dai mu koma 6angarn su mashkhur dan muje mike going.........

RASHA........

Washe gari............

A cikin kwana d'aya da wunin ranar mashkhur yabi yayi zuru-zuru sabida tsabar yadda zahra ta sa shi a gaba ba wai, abu ka d'an yayi mata kuka take yi, ga jigilar yawan kai zahra toilet, ga flushing d'in audigar zahra, pants d'in zahra kuwa suna ganin ta kansu a wajan mashkhur dan sam mashkhur baya iya wanke su sai dai yayi flushed d'in su sabida qyan-qyami.

Kai tin mashkhur yana jin qyan-qyami flushed harma ya dai na yanzu ya dawo abin tausayi, sabida zahra tana caza mai kai ba wai.

Nights........

Hannu riqe da bottle d'in ruwa mashkhur ya shiga bedroom d'in, zahra kuwa tana kan bed tana zaune hannu riqe da waya tana d'an chat. Mashkhur yana shigowa kallo d'aya yayiwa zahra ya d'auke kai sanan ya bud'e bottle d'in ruwan ya tsiyaya a cup, yana tsiyayawa ya nufi kan table d'in kusa da bed ya ajiye bottle d'in ruwan, yana ajiye jarkar ruwan yaji wayar shi tana ringing.

Zaro wayar mashkhur yayi daga aljiwu tare da zuba mata ido, sunan dady mashkhur ya gani 6aro-6aro ya fito akan screen d'in wayar da sauri mashkhur ya ajiye cup d'in a kusa da bottle d'in ruwan sanan ya fuce daga bedroom d'in a hanzarce. Mashkhur yana fita zahra ta d'ago dan ganin mai ya ajiye a table d'in, har cikin zuciyar zahra taji dad'in hakan sabida tana ta neman damar da zata qarasa tofawa mashkhur addu'ar da take mai bata samu ba.

Dama saura d'aya zahra ta gama tofawa mashkhur addu'ar yau kwana biyu raban ta da ta tofa mai d'an matsawa tai tare da zura haninta sosai ta d'auko cup d'in ruwan sanan ta tofah, bayan ta gama tofawa ta d'akko ragowar na cikin bottle d'in shima tai sanan ta tofa again. Daga haka ta hau online, tana hawa online ta gayawa ilham ta gayawa hajiya kaka yau ta gama tofawa yaya mashkhur addu'ar nan.

Ilham kuwa cewa tai eh dama hajiya kaka tace min ba gaya miki in dai yaya mashkhur ya gama shan addu'ar nan in dai taga yayi amai to daga ranar bazai sake sha'awar shan kayan maye ba. Zahra kuwa ta6e baki tau kamar ilham tana ganin ta tare da yi mata reply da to ALLAH dai yasa hakan, dan ita yanzu zahra ta tsinke da lamarin yaya mashkhur kullum tana addu'a amma abu yaqi ci yaqi cinyewa.

Bayan few minutes ilham ta yiwa zahra voice note, zahra kuwa kwanciya tai tare da bud'e voice note d'in ilham d'in. Cikin mamaki ilham take maganar murya rass ta cewa zahra kee, ban baki labari ba yau fa ammi ta kamani damo-damo, in gaya miki. Cikin mamaki itama zahra tai mata voice note da cewa! Ta kamaki kuma, akan me kenan bani nasha.

Bayan ilham ta bud'e messages d'in batai sanya a guiwa ba wajan fara korawa zahra jawani ta voice note. Haka ilham ta korawa zahra jawabin komai tun yadda akayi messages d'in ahmad ya shigo ammi taga save d'in number da kuma message d'in har zuwan ahmad gida, da yadda ilham ta shawo kan ammi cikin sauqi.

Lokacin da zahra ta gama jin labarin tasha dariya sosai kuma hakan yayi mata dad'i sai ta sake turawa Ilham voice note da!! Hmm ilham lalai Allah ya auna miki arziki kin tsalla ke rijiya da baya yanzu to ya dady ya amince da zancan kuma da fatan dai sunana bai futo a wajan ammi ba dan wlh karma ki sake kice nasan zancan.

Zahra tana gama turawa ilham voice note d'in sai ga mashkhur ya dawo bedroom d'in. Yana shigowa bedroom d'in ya nufi kan table d'in ya d'auki cup d'in ruwan ya kai bakinsa, zahra kuwa kashe data tai tare da ajiye wayar a gefe a zuciyar ta tace yau dai ta faru ta qare, zan gani zaka dai na shaye-shayan nan ko kuwa, duk da kuwa nasan bazaka ta6a iya dai nawa ba.

Mashkhur kuwa yana gama shan ruwan ya koma kan sofa ya zauna tare da bud'e laptop d'in shi ya fara dannawa. Zahra kuwa wani siririn tsaki taja yadda bazai jiba tare da d'akko wayar ta ta cigaba da chat da ilham ta typing, suna chat tana sakin dariya abinta, 6angaran mashkhur kuwa in zahra ta saki dariyar nan sai yaji kamar ya shaqe ta, dan yana tsarguwa sosai.

To mashkhur ya d'au 30 minutes yana danna laptop d'in, zahra kuma tana kwance akan bed, ta rufe ido kamar mai bacci tana ta tunanin yaya abdul d'in ta. Mashkhur kuwa lokaci guda yaji zuciyar shi tana tashi sama-sama, amma mashkhur bai damu ba ya cigaba da danna laptop d'in shi abinsa. Can dai mashkhur yaji zuciyar shi ta sake mugun tashi, jiki na rawa mashkhur ya turo laptop d'in daga gaban sa.

Nan da nan jikin mashkhur yayi mai zafi sosai ga gumin da yake tsatsafo mai ko ta ina, sabida ji yayi wani abo ya tokare mai a qirjin sa ga zuciyar shi tana sake mugun tashi. Miqewa mashkhur yayi tare da komawa kan table ya sake d'aukar bottle d'in ruwan ko tsiyayawa bai yi a cup ba ya kai bakansa da sauri. Mashkhur bai ajiye bottle d'in ruwan ba sai da ya shanye tasss.

Ai kuwa yana shanyewa yaji kamar an qara mai tashin zuciyar nan kafin kace mai wani mugun amai ya taso mai. Da sauri mashkhur ya nufi toilet, yana shiga ya fara sharara wani irin amai. Sosai mashkhur yake amai dan tun yana iya amayo abinda yaci har amai nasa ya canza kala takai ta kawo kamar aman ruwan rubutu yake.

6angaran zahra kuwa tana kwance akan bed, taji sautin amai a toilet, gaban tane ya yanke ya fad'i rass, rass, rass, cikin firgici ta furta inalilahi'wa'ina'ilaihirraji'un,. Sosai zahra ta tsorata da lamarin dan jin yadda yaya mashkhur yake kwararo amai. a zuciyar ta tace yanzu da gaske yaya mashkhur ya dai na shaye-shayan nan kuwa?

Can zahra taji sautin amai yayi yawa,, tashi tai zaune sanan ta fara sauka daga bed d'in bayan ta zuro qafafuwan ta ta fara qoqarin takawa. Cikin ikwan ALLAH zahra ta miqe tsaye sosai, amma dai qafarta tayi tsami sosai dan a qyar ma take iya tafiyar. Sannu a hankula zahra take takawa har ta qarasa toilet d'in, tana qarasawa toilet d'in ta hangi mashkhur durqushe a qasa yana ta sharara uban amai ya gala bai ta sosai dan da kayar yake iya aman ma.

Kamar zai amayo kayan cikin sa tun yana iya amayo abu har ya dai na amayo komai. Zahra kuwa da qyar ta iya qarasawa wajan da mashkhur d'in yake tare da tsugunawa gabansa. Shima mashkhur da kyar ya iya d'agowa ya kalli zahra kallo, d'aya yayi mata ya kawar da kai idanuwan nan nasa sunyi jajir, jijiyoyin kansa duk sun tashi, a hankula zahra ta kai hannu ta dafa kafad'ar mashkhur tare da cewa! Yaya mashkhur sannu...............

Naso na qarasa muku page d'in nan amma na kasa wlh sabida banajin dad'i, ciwan wuya nake ina barar addu'a a gare ku ALLAH ya bani lpy..........

Mu had'e gobe a next page. Allah ya kaimu da rai da lpy, Ina muku fatan alkhairi.


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 93*


Shima mashkhur da kyar ya iya d'agowa ya kalli zahra kallo, d'aya yayi mata ya kawar da kai idanuwan nan nasa sunyi jajir, jijiyoyin kansa duk sun tashi, a hankula zahra ta kai hannu ta dafa kafad'ar mashkhur tare da cewa! Yaya mashkhur sannu...............

Shiru mashkhur yayi bai bawa zahra amsa ba, zahra kuwa qara cewa! Tai ko na d'auko ma ruwane? Gyad'a kai mashkhur yayi alamun ee, miqewa zahra tai ta fuce daga bedroom d'in, tana fita ta wuce fallo tana zuwa falon ta shige kicin sanan ta bud'e dorowar kicin ta d'auko bottle d'in water mara sanyi, tana d'auka ta kama hanyar fucewa daga kicin d'in, haka zahra ta d'inga tafiya a hankula har ta qarasa bedroom d'in mashkhur.

Tana shiga ta wuce toilet d'in, sanan ta koma gaban mashkhur ta tsuguna ta fara qoqarin bud'e ruwan. Haka zahra tai ta kici-kicin bud'e bottle d'in ruwan sabida murfin ya d'an cije ka d'an, zahra tana cikin kici-kicin bud'e bottle d'in ruwan taji mashkhur ya warce jarkar hanunta ta, zahra kuwa zuba mai ido tai tana ganin ikwan ALLAH a zuciyar ta tace sai naga ta yadda zaka bud'e tin da kai ba!!.

Kafin ma zahra ta kai qarshan maganar da take a zuciya taga mashkhur ya bud'e bottle d'in ruwan sanan ya cillar da murfin gefe, yana gama cillar da murfin bottle d'in ya kai bottle d'in ruwan bakinsa, yana sha bai kai da had'iyewa ba ya kuskure bakinsa ya zubar sanan ya ajiye bottle d'in ruwan, ya miqe jiki na rawa ya bar toilet d'in.

Zahra kuwa wata siririyar ajiyar zuciya ta sauke sanan ta kalli aman da mashkhur yayi, sanan ta kawar da kai, da kyar ta miqe sanan ta d'auko tsintsiya ta fara gyara wajan, bayan ta gama gyara wajan ta d'an wanke toilet d'in sama-sama, sanan ta kunna sin ta wanke hanunta bayan tagama wanke hanun nata fucewa tai daga toilet d'in. Tana fita ta hangi mashkhur yayi wanwar akan bed.

Da sauri zahra ta kawar da kai gefe sanan ta kama hanyar fita daga bedroom d'in, tana ficewa direct bedroom d'in ta ta wuce, zahra tana shiga ta saki guntuwar ajiyar zuciya saka makwan yadda taga kaya baje a bed d'in ta, dan ita sam tama manta da ta futo da wasu kayan. A hankula zahra ta nufi kan bed d'in tana zuwa ta zauna a gefe abinta.

Zahra tinani ta farayi taya zata iya mayar da kayan nan yanzu, kuma ga room d'in duk yayi qura, shima yana buqatar gyara. Zahra ji tai bazata iya ba gaba d'aya gwarama ta koma bedroom d'in yaya mashkhur d'in in yaso zuwa gobe sai ta gyara nata. Jiki a sanyaye zahra ta fuce tana fita ta nufi kicin ta d'an dora ruwan tea bayan ya dawu.

Zubawa tai a cup tasha, bayan ta gama sha miqewa tai ta wuce bedroom d'in yaya mashkhur. Zahra tana shiga ta hangi mashkhur jikin sa sai wani rawa yake ya qanqame jikinsa sosai alamun yana jin sanyi. Ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan ta wuce kan table ta d'auki robot d'in A.C ta kashe A. C, bayan ta kashe A. C bed d'in ta nufa jiki a sanyaye.

Yadda zahra taga mashkhur yana rawar sanyi sai ya bata tausayi sosai kuma sai taji ta d'an tsorata dan haka ba shiri ta wuce bed d'in sanna ta d'auki blanket ta fara qoqarin rufawa mashkhur a jikinsa. Jiki na rawa zahra ta rufewa mashkhur jikinsa da blanket d'in tsaf, zahra tana rufa mai blanket d'in maimakwan jikin mashkhur ya dena rawa sai taga abu kamar qara shi ake.

Da sauri zahra ta nufi kan sofa ta sake d'auko d'ayan blanket d'in, sanan tazo ta qara rufawa mashkhur. Bayan ta rufa mai zama tai a gefan kansa ta rafka uban tagumi zuciya ciya fall da sausayin sa. Zahra gani tai duk da hakan jikin mashkhur kamar bai dai na rawa ba, miqewa tai ta nufi wardrobe ta bud'e side d'in bedsheets da blanket, sanan ta sake d'aukko wani blanket.

Bayan ta d'auko a hanzarce ta nufi mashkhur tana zuwa ta haye kan bed sanan ta sake rufawa mashkhur a jikinsa. Bayan ta rufa mai zama tai a gefan kansa tana jimami, har Cikin zuciyar zahra da tasan mashkhur zai shiga cikin wanan halin da bazata tofa mai addu'ar nan yasha a ruwa ba. Nan da nan zahra ta fara karanto addu'a'i kala-kala tana d'an tofawa mashkhur d'in duk da dai jikinsa a rufe yake kansa ne kawai a waje.

Zubawa somar kan mashkhur ido zahra tai tana ta dogwan nazari. Haka nan zahra taga sumar kan mashkhur tayi matuqar birge ta nesa ba kusa ba, saka makwan yadda taga sumar tana wani shining da kyalli, saman sumar

Please Login or Register in order to submit comment