Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban saniba eyee ? dady ne ya fad’i hakan a tsawace itama hajiya kaka cewa tai mashkhur wanan wana kalar haukane haka? Abdul kuma cikin 6acin rai ya tsuguna ya d’auki zahra yana rarrashin ta, ji yake kamar ya daki yayan nasa amma bazai iya ba.

Tom bari kaji Wallahi tallayi daga rana mae kamar tayau ka sake yiwa mamana haka Wallahi sai na 6ata maka, zaka sha mamaki Wallahi in badda zalinci da mugunta qaramar yarinya zaka kama ka tureta kai da QANWARKA?. Dasauri mashkhur ya d’ago daga sunkuyar da kan dayayi tare da cewa qanwata kuma dady? Mamaki ne ya bayyana a fuskar dady da hajiya kaka, ran dady ya gama 6aci sosai bai ta6a tinanin abin mashkhur ya kai hakaba.

Sautin tafiyar ne yasa kowa juyawa domin suga waye yake futowa daga bedroom d’in. Ae ba wandda bai girgiza da ganin wandda take futowa ba 🙀 dan kowa mutuwar tsaye yayi, bakowa bace face AMMI ahankali take takawa kana ganinta kasan jikinta baiyi gwariba tafiyarma da qyar takeyi. Aguje faruq da hadar suka nufi ammin domi su rongumeta a hanzarce hjy kaka ta ruqosu tare da cewa ku bari mana karku yar da ita, jikinta ba qwari ai.

Alhamdulilah ALLAH mungode ma cewa hjy kaka shikuwa dady sujjada yayi yana godewa ALLAH mashkhur da abdul suma Alhamdulilah kawai suke furtawa. Da sauri hajiya kaka ta qarasa indda ammi take tare da ruqota dan ta temaka mata. A hankula suka ringa takawa har suka qarasa wajan kujera, a hankali hjy kaka tazaunar da ammi. Tofa nanfa yara suka fara rige-rigen hawa kujerar da ammin take.

Kowa sannu yakewa ammi itakuma tana amsa musu da yauwa. Hmmmm tsayawama gayawa mae karatu yau farincin da mutun gidannan suke ciki 6ata bakine sabida farin ciki ko abinci basuciba, batun zalincin da mashkhur yayiwa zahra ma an manta da zancan. 6angaran momy da tasamu labari kuwa baqin cikine yakusan kasheta dan sai da tayi suman tsaye, kuma mamaki take taya akai ammi ta samu sauqi kuma wayakarya mata asirin?. Oho babu mai bata amsa.

Wunin ranar haka momy ta wuni cikin matsanancin baqin ciki. Ji take kamar taje ta shaqe ammi ta mutu.
Dare yayi sosai kowa ya tafi makwancin sa, ammi tana tare da ilham da zahra da kuma hjy kaka sabida har yanzu jikinta bae gama qwari ba, dady kuwa yana part d’in momy da yake yau a part d’in ta yake, su mashkhur da abdul dasu faruq suna d’akin su.

Faruq da haidar da abdul suna gado d’aya suna bacci, bakomai ne yasa abdul ya baro mashkhur a gadan su ba ya dawo kusa da su faruq bace abindda mashkhur yayiwa zahra yau bah, tindda yake bai ta6a tij haushin yayan nasaba ko yaqi kwana a kusa da shi sai yau daya ta6a masa zahran sa, dan abdul da bayasan mashkhur kuma baya jin tsoransa yau sai ya ramawa zahran sa, dan abdul kullum in zahra tana kuka sai ya tuna da abidda mamanta tace mai, akan ya kula da zahra qanwar sace.

6angaran mashkhur kuwa har wajan shabiyun dare ya kasa bacci, sabida baqin ciki, bakomai ne yake damun saba face 6acin rai fad’an da baqakyan maganganun da dady da hajiya kaka sukayi mai ba. Abun d’aya yake furtawa a zuciyarsa shine, ADALILINTA mahifina ya fara yimin fad’a ADALILINTA mahifina yayi fushi dani ADALILINTA kakata tafarayimin fad’a, ADALILINTA aka farayimin tsaya, ADALILINTA ma qanina Abdul wandda nafi so cikin qanne na ya gujeni haushin yakeji.

Abindda mashkhur yake ta fad’a azuciyarsa kenan, wata mumunar tsana da kyamar zahra ce ta kama mashkhur, gawani mugun ciwan kai da yake damunsa. Aganin mashkhur yauce ranar da tafi dacewa yayi bacci mae dad’i, kuma ya dad’e yana fatan ranarnan tazo sai gashi tazo mai a baqin ciki duk adaililin zahra. Tundda ammi ta fara cuta mashkhur baya wani bacci mae dad’i kuma yayai al qawarin duk ranar da ammi ta samu lafiya zai yi bacci mae dad’i sai gashi adalilin zahra ya kasa.

Ya salam abindda mashkhur ya frusta kenan tare da dafe kansa da yake mae ciwo, adaddafe ya miqe ya bud’e durowa ya 6alli maganin ciwan kai yasha, sannan ya koma ya kwanta, haka mashkhur yayi ta tunani kaka-kala zuciya cike da baqin ciki. Sai wajan ukun dare mashkhur ya samu yayi bacci.
In kacire momy da mashkhur daran ranar kowa da farin ciki ya kwana, musamman ma dady, abdul da kuma hajiya kaka.

Tom haka ammi tai ta jinya cikin kulawa da farin ciki da yaranta suka sata, ko quda basa bari ya ta6a ammin tasu musamman ma abdul kullum yana maqale da ammin bacci ne kawai yake rabasu. 6an garan momy kuwa kullum cikin baqin ciki take gashi dady ya hanata zuwa kaduna barema taje wajan bokan nasu. 6angaran mashkhur kuwa ya qara tsanar zahra ko hanya baya son su had’a.

Hjy kaka kuwa ta koma wajan malam Ibrahim ta kar6owa ammi maganin tsari yadda ko asiri da sihiri akayi mata bazi sake kamata ba.
To yau kimanin sati uku da samun sauqin ammi kenan, tasamu sauqi tayi garau abinta, amma sai dai haryanzu jikinta bai dawo ba, amma a hankula take qibar.
Tom rayuwar gidan nan tacanza saka makwan samun lafiyar ammi, kowa cikin farin ciki yake yanzu ammi tana kula da yaranta da kuma mijin sosai, harma da hajiya kaka.

Dan yanzu hajiya kaka ta samu hutu ammi ce takewa su zahra komai kuma a wajanta suke kwana. Yau wata biyu kenan da samun sauqin ammi, sukuma zahra da ilham shekarar su guda sunyi kyau sun qara qiba ga wayo musamman ma zahra dan kamar balarabiya haka take, har sun d’an fara tafiya. Dady ya yanke shawarar mayar da zahra gaban iyayan ta amma sai bayan sun dawo daga saudiya shida ammi da kuma hajiya kaka.

Lokacin da labari ya iske momy za’a je saudiya ba ita ansha bala’i iri-iri a gidan nan, kuma tace wallahi sai antafi da ita. Shikuma dady yace bazai je da itaba sai wata shekarar sai dai ta zauna ta kula da su mashkhur. Tofa bala’i yaqici yaqi cinyewa, hakan ne yasa ammi tace ita ta haqura da zuwa makan atafi da momy wata shekarar taje ita takula da yaran harma dasu rukayya da rumaisan.

Dafarko dady bai yadda da hakan ba sai da hjy kaka tasa baki sanna ya amince badan yason ransa ba.
Tofa su dady sun fara shirye-shiryen tafiya saudiya dan yanzu bai fi saura sati d’aya ba. Momy kuwa ta kafe akan bazata barwa ammi ‘yayanta sae dai ta kai su kduna wajan mahaifiyarta. Masifar momy ta ishi dady dan haka zuba mata ido yayi kawai. Haka momy ta kama hanyar kaduna, ko da taje kadunar gidan qanwarta saratu ta kai rukee da ruma,

duk da kuwa dady bai saniba dan da yasan nan zata kai su bazai bari ba sabida dady ya tsani saratu dan har yanzu baya bari saratu tazo mai gida.
Tom yau su dady da hajiya kaka da kuma momy jirginsu ya d’aga zuwa saudiya.
Ammi kuwa tana gida tana kula da yaranta.............

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

Typing........

*page 36


Masha Allah, inayiwa masoyana barka da sallah da fatan anyi sallah lafiya.. tom Allah ya karbi ibadun mu.

In masukaratun littafin ADALILINTA bazasu manta ba, mun dakata a indda ammi bata da lafiya kuma bata iya komai kullum a kwance take, komai yimata akeyi, abincima bata iyaci sai dai abinci mae ruwa shima sai dae abata ta hanci. Bakomai ne yasa ammi cutar nan ba face sihiri da sammu da momy tayimata. Sabida tanaso taga bayan ta, wato ta kasheta.

6argaran mashkhur kuwa ya fara zawa computer science, kuma yana mayar da hankali yana karatu. 6an garan su zahra kuwa in ba zaku manta ba sinyi wata takwas a duniya, sunyi wayo har sunfara ‘yunqurin miqewa, sunyi kyau musammanma zahra. 6an garan abdul kuwa kullum qara son zahra yake inyaje makaranta har alawa yake suyo musu ita da ilham.

Yanzu kakace take kula dasu mashkhur dasu zahra harma da ammi............

Yauwa yanzu zamu dora.

Haryanzu ammi tana kwance dan yanzu watanta biyar a kwance cutar taqici taqicinyewa. Yanzu kowa yafitar da rai da ammi dan kowa bata mutuwa yake. Alokacin ilham da zahra suna da wata goma a duniya, sunyi wayo sosai sun saba da hajiya kaka dan yanzu suna gane ‘yan uwansu. Zahra dai ta sabada kowa badda mashkhur da momy da rukee dakuma ruma, alokacin ma rumaisa ‘u ko yayeta ba’ayi ba.

Mashkhur kuwa yanzu ya saba da makarantar computer science, kuma yana karatu sosai. 6angaran abudul kuwa shima yana mae da hankali sosai duk da dai bakai mashkhur qoqari a makaranta ba, sabida shi baya daukar ta d’aya a makaranta kamar yadda mashkhur yake d’auka sai dai ta uku ko ta hudu. Kuma kullum abdul qara son zahra yake. Suma su haidar da faruq suna zuwa makaranta kuma suna karatu.

Rukee kuwa tana so taringa zuwa 6angaran ammi wajan ‘yan uwanta amma ina momy ta hanata zuwa, kullum haka take kulleta a part d’inta sai dai tai ta wasa da qanwarta ruma. Tom yanzu momy ta yanke shawarar komawa wajan boka domin ya kashe ammi, sabida momy ta lura da ammi ta gama shan wahalar duniya, kuma gashi duk da rashin lafiyar ammi dady bai dena kulata ba kullum qara sonta yake kuma baya k’yamarta kamar yadda momy tayi tunani.

Yauta kassance ranar alhamis misalin qarfe shabiyu na rana. Su mashkhur duk sun tafi makaranta. hjy kuwa tana part d’in ta ita da su ilham da zahra, sakamakwan dady yana tare da ammi. Dama dady yana yawan zama da ammi dan ranar kwanan ta shi yake mata wanka da safe kuma shiyake kwana tare da ita, ranar kuma da zai kwana a part d’in momy hjy kaka ce take kula da ita.

Ammi tana kwance tayi matashi da qafar dady idonta a lumshe, shikuma dady ya zubawa ammi ido yana kallan yadda ammi ta rame duk tacanza, dady ya rafka tagumi kamar yayi kuka, sai tinani yake kala-kala. Muryar momy ce dawo da dady daga tinanin da yatafi, itama ammi da idonta yake a rufe sai da ta bud’e idanunta sakamakwan tsawar da momy ta daka.

Ai dama nasan kana tare da wanan matacciyar matar taka mara mamora, dan wlh maryam da ita da matacciya duk d’aya ne dan kwara matacciyarma za’a ita yimata addu’a, cikin tsawa momy take fad’ar hakan. Da sauri dady ya janye ammi daga jikinsa tare da miqewa tsaye, cikin bacin rai yace ashe halima baki da mutunci? Matata kike gayawa haka.?

Ehhh nafad’a d’in ai gaskiya!!!! Jikake tassss tassss kyawawan marika dady ya zuba momy wandda yasata kasa qarasa maganar da takeyi. Cikin fishi tace ni kamara akan maryam? Afusace dady yace wlh halima kika qara fad’ar wata mumunar kalma akan matata sai na sakeki. Ae kuwa momy tanajin hakan ta fuce da sauri sabida tasan tsaf zai aikata.

Tana fita dady ya juya yaqarasa wajan ammi, Abin mamaki hawaye ne kawai yake zuba a fuskar ammi. Abin yabawa dady mamaki sosai, bai tab’a tinanin ammi tanajin magana ba tun sandda ta fara cuta, tsugunawa yayi yafara share mata hawayan da tafin hannun sa, bayan ya gama share mata hawayan daukarta yayi yawuce da ita bedroom d’in ta.

Suna shiga bedroom ya wuce da ita toilet , wanka yayi mata sannan ya futo da ita. Bayan ya futo da ita zama yayi ya shirya ta yasa mata kaya, sanan ya samata fulo a fuskar gado bayan ya samata fullon ya jinginar da ita a fuskar gado. Haryanzu ammi bata dena zubar da hawaye ba akan abindda momy tayi mata. Zama dady yayi yana fuskantar ammi.

Hannunta ya ruqo yana fuskantar ta, yakasa cewa komai kawai murza hannun ammi yake, sai da sukayi wajan minti biyar ahaka kafin ya fara magana kamar haka!!
Maryam dan ALLAH kidena kukan nan kinji, dama ita cuta zata iya zuwarwa bawa a duk sandda taso, kuma ke musulmace nasan kin yarda da qaddara mae kyau da mara kyau,

Kuma duk bawan da kikaga ALLAH ya jarrabe shi da cuta, to ALLAH yanason shine sabida ita cuta kankaran zunubice, dan haka kiyi haquri da maganar da halima ta gaya miki kinji? Kirabu da ita ALLAH zai saka miki. Kuma ni a matsayina na mijinki yayanki d’an uwanki na jini kuma uban ‘yayanki bazan tab’a gudinkiba kona kyamace ki a duk halin da kika shiga.

Nifa yanzu kullum qara sonki nake azuciyata jinki nake kamar wata sabuwar amarya, yafad’a yana murmushi tare da shafa kumatunta. Abin mamki itama ammin murmushi tai kamar yadda dady yayi, ajiyar zuciya dady ya sauke tare da furta Alhamdulilah. Matsawa yayi gab da ita tare da sai ta bakinsa dai-dai kunnanta yancewa yauwa my honey wlh ina qaunarki har cikin zuciya ta

In bake bazanji dad’i rayuwata ba, kuma insha ALLAH nan bada jimawa ba zaki samu sauqi da lafiya, kinga sai mucigaba da soyayarmu koh? Nasan zakibani kulawa fiye da jariri koh? Hmmm kede kawai kibari ALLAH yabaki lpy dan kishirya natanadar miki soyayya iri-iri dan sai kin manta a duniya kike kokuwa, kawai dae ki shirya dan sauran ma ba’a fad’a sai dai kiganewa idanunuki.

I love you ❤️ so much my life, ahankula ya qarsa fad’in hakan tare da zare bakin sa daga kunnan ammin, murmushi ammi take sosai dan har zuciyarta takejin kalaman mijin nata, shima dady yaji dad’in hakan sosai dan koba komai yasan yau yafarntawa matar sa rai. Ahankula ya kwantar da ita akan gado, bayan ya kwantar da ita ya sauka yaje ya rufe qofar d’akin

Sanana ya dawo kan gadon shima ya kwanta suna fuskantar juna, sai murmushi suke sakarwa juna. Rungumota dady yayi sosai ajikinsa kamar wandda zai mayar da ita ciki, haka yay ta zuba mata kalamai mae dad’i har bacci yayi awan gaba da su.......

Sai wajan qarfe uku dady ya farka daga bacci, yana farkawa ya zare jikinsa daga na ammi a hankula yadda bazai tasheta ba. 6an d’aki yashiga ya dauro alwala sanana yayi sallah. Bayan ya idar da sallah bud’e qofar d’akin yayi ya fuce. Yana futa babban falan ya tarar dasu abdul da faruq da haidar sun dawo daga school har hjy kaka ta cire musu kaya tazuba musu abinci sunaci.

Dama shi mashkhur sai wajan qarfe hudu yake dawowa. 6an gare guda kuma zahra da ilham suna zaune suna wasa da teddy, gefe guda kuma hajiya kaka tana zaune tana jan carbi. Yana futowa abdul yace dady ina wuni? Lpy qalau my abdul ya school d’in? Alhamdulilah cewar abdul. Shima faruq dayaga abdul ya gaida da dady sai yace dady ina kwana? Dariya dady yayi tare da cewa lpy qalau babban qanina, amma ba ina kwana akecewa ba ina wuni ake cewa tindda yanzu rana tayi, sai da safe ake cewa ina wuni.

Tom dady ina wuni? Yauwa babban qanina lpy qalau, dady kallansa yamayar kan haidar da yake tacin abinci cikin murmushi yace kai haidar bazaka gaishe dani ba, ehh dady saina gama cin abinci yayamu yace ba’a magana in anacin abinci. Jinina kae dady yayi tare da cewa hakane tom in kagama cin abinci sai kazo mu gaisa koh? Tom dady.

Dady qarasawa wajan da hajiya kaka take yayi har qasa ya tsuguna ya gai da ita!! Hajiya kaka an wuni Lpy? Cikin sakin fuska tace lpy qalau ya maryam d’in? Tana nan nabarota a d’aki tana bacci, jinjina kai hjy kaka tayi tare da cewa tom ALLAH ya bata lafiya, Ameen hajiya. Yana gama fad’ar hakan ya miqe ya nufi indda su zahra suke wasa ita da ilham, yana qarasawa ya tsuguna agabansu yana kallansu fuska d’auke da murmushi.

Zahra kuwa tana ganin dady ta fara dariyar su ta yara tare da miqa mai hannu alamin ya d’auke ta. Bamusu dady ya miqa hannu ya dauki zahra murna zahra take sosai sabida ta saba da dady sosai, kuka ilham ta tsala alamun itama dady ya d’auketa dama ilham ta cika kishi bata yadda dady ya d’auki zahra ita bai d’auketa ba. Dasauri dady ya sunkuya ya d’auki ilham da hannu d’aya ai kuwa sai tayi shuru.

Zama yayi akan kujera d’ayan hanun riqe da zahra d’aya kum riqe da ilham. Agefansa ya ajiye ilham ita kuma zahra ya d’orata akan ciyarsa. Zahra kuwa sai kallan dady take tana washe masa baki, dady kuwa zuba mata ido yayi yana kallanta. Har ga ALLAH dady yana qaunar zahra har cikin ransa yake jinta, dan son da yake mata ji yake kamar ‘yarsa ta cikinsa,ga tausayinta da yakeji.

In kuma ya tina an kusan mayar da ita gaban iyayan ta duk sai yaji ba dad’i dan yanzu su zahra sunyi wajan wata goma, kuma tana cika shekara zasu mayar da ita wajan iyayan ta, amma dady ya fara tinanin barin zahra har ammi ta samu sauqi sannan ya mayar da ita. Haka dai dady yay tayiwa zahra da ilham wasa har aka fara kiran sallara la’asar.

Dashi da abdul da faruq da kuma haidar suka wuce massallaci.
Bayan sun dawo suka tarar da mashkhur ya dawo daga makranta, harma ya cire kayansa yayi sallah da wanka yanacin abinci. Ilham kuwa rarrafawa ta farayi har ta qarasa wajan mashkhur d’in, itama zahra dataga haka sai ta fara rararfawa.

Suna qarasawa yasa hannu ya d’auki ilham, bayan ya d’auketa yafara yimata wasa. Zahra kuwa tana ganin haka ta fara dafa mashkhur tana qoqarin miqewa, ai kuwa mashkhur yasa qarfi ya hankad’e ta ji kake qum ta fad’i qasa. Kuka ta farayi sabida taji zafin bad’uwar mai makwan ya rarrasheta sai ya qarasa qafa ya hankad’e ta tare da miqewa hannunsa d’auke da ilham ya shige bedroom d’insa ya barta a wajan tana kuka.

Dama ba kowa a falon daga mashkhur sai faruq sai kuma zahra da ilham. Ahanzarce faruq ya qaraso indda zahra take kwance tana kuka tsugunawa yayi ya fara rarrashin ta, duk da bawani babba bane amma bai ji dad’i abindda yayan nasu yayiwa zahra ba. Ana cikin haka sai ga abdul nan ya shigo, da sauri ya qarasa indda suke ya d’auki zahra hankali a tashe ya fara rarrashinta, dan yasan tabbas zahra bata irin wanan kukan sai dai wani abun ne ya sameta.

da sauri abdul ya kalli faruq tare da cewa faruq mai kayiwa zahra take kuka haka? Girgiza kai faruq yayi tare da cewa bani na yadda itaba, to waye yayar da ita inba kai ba? Zaro ido faruq yayi sabida yana tsoron yace yaya mashkhur ne, sabida yadda suke tsoron yayan nasu. Yadda abdul yaga faruq yana zazzaro ido sai yayi tinanin shi yazo d’aukar zahra a rashin sani yayar da ita.

Faruq daga yau tindda baka iya d’aukarta kadena kaji, d’aga kai faruq yayi alamin Tom, daga haka abdul ya nufi bedroom d’in ammi hannu riqe da zahra. Yana shiga hjy kaka tana gama bawa ammi abinci ta robar hanci kamar yadda aka saba, qarasawa abdul yayi tare da cewa hjy kaka sannu da aiki? Yauwa abdul d’in zahra, ina ilham d’in ne?

Nima bansani ba amma ina tinanin tana wajan yaya mashkhur, jinjina kai hjy kaka tayi tare da cewa to bari nabarka da maman taka koh nikuma naje nayi wanka, tom shikenan hjy kaka, daga haka hiy kaka ta fuce daga bedroom d’in ya rage daga ammi sai abdul da zahra. Qarasawa abdul yayai kusa da ammi ya ajiye zahra.

Nan da nan zahra ta fara dariya tare da qoqarin hawa jikin ammin. Itama ammin murmushi ta fara tana so ta d’auki zahra amma ba hali, abdul yaji dad’i hakan sabida tundda ammi ta kwanta cuta bai tab’a ganin tayi murmushi ba sai yau. Dama zahra da ilham sun saba da ammi sabida yawanci ana kawosu kusa da ammi suyi wasa wataran ma tare suke bacci.

Dai dai sai tin fuskarta abdul ya leqa tare da furta ALLAH ya baki lpy mamana, walli ina qaunarki ammi, kuma nayi rashinki sosai harma da rashin kulawarki, yaqarasa maganar tare da kwantar da kansa a kan ammin. Har zuciyar ammi taji dad’in maganar abdul duk da ba babba bane sosai kuma tana mamakin irin girman qaunar da abdul yake nuna mata fiye da komai a duniya.

Dan abdul yana qaunar ammi fiye da iyayan da suka kawoshi duniya, dan shi har yanzu tattama yake akan ba ammice mahifiyarsa ba, sabida abdul sam baya qaunar ace momy ce mahifiyar sa. Haka ya kwanta a kusa da ammi dan baya son yabarta ita kadai a d’aki, zahra kuma har bacci mae bauyi ya kwasheta ajikin ammin. 6angaran mashkhur kuwa yana shiga d’aki ya kwanta sanan ya kwantar da ilham akan cikinsa.

yanajin tsanar zahra tana qaruwa a zuciyar sa. Ita kuwa ilham sai yaqushinsa take a fuska, hannayan ta biyu ya riqe yana yimata wasa, ahaka bacci ya kwasheta kwantar da ita yayi a kusa da shi,, yatafi duniyar tinani shin wacece zahra? Shin tana da iyaye ko shegiya ce kamar yadda momy tace? Shin intana da iyaye mai yasa iyayan nata suka rabu da ita?. Haka dae mashkhur yay ta saqa da warwara har bacci yayi awan gaba dashi.

Washe gari.....
Yau ta kasance ranar juma’a,misalin qarfe biyar na yamma ,bayan su Mashkhur Sun dawo daga makaranta suna zazzaune a palour ,6angare guda Ammi ce kwance tare d mashkhur a gefen ta yana mata tausa ,Abdul kuma na Dayan gefen ammin yana yanke mata farce,a gefe guda Kuma faruq ne da Haidar suke cin abinci dama haka suke da ci,acan gefe kuma ilham da Zahra ne suke wasan su ,hajiya kaka kuma tana gefe tana karatun Qur’ani.

Wayar kaka ce ta hau ruri,rufe Qur’anin hanun ta tayi a hanzarce ta nufi kan tebur din da wayar ke ta faman ruri,glass din wayar ta duba dan taga wane akan layi ,mamaki ne qarara a fuskarta ,dan ganin sunan da ya baiyana akan screen din waya, bakowa bane face malam Ibrahim. Bakomai ne yasa hajiya kaka mamki ba sai raban da tayi waya da malam ibrahim ko taje wajansa tun lokacin da aka kawo zahra gidan..............

Daga yau one page zan ringa posting amma na qara kuma yawan page d’in.

Dafatan zakuyi hutun weekend lafiya. Sai kuma ALLAH ya kaimu ranar Monday.

*gamasu buqatar littafin ADALILINTA har indda muka tsaya sai suyimin magana ta wanan number 08142246343. Free book ne kuma new book.

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Page 37*

Typing...........

Bakomaii bane yasa hjy kaka mamaki ba sai raban da tayi waya da malam Ibrahim ko taje wajansa tun lokacin da aka kawo zahra gidan..........

Har wayar ta tsinke hajiya kaka bata d’auka ba sabida tsabar mamaki, sai da ta sake shugowa sannan ta samu ta d’aga tare da sallam. Bayan sun gama sallamar hjy fucewa tai daga part d’in tasamu qofar korudo ta zauna. Bayan sun gama gaisawa malam Ibrahim yake tambayar kwana biyu yajita shiru ko lafiya.

Nan da nan hajiya kaka ta bashi labarin rashin lafiyar ammi shiyasama bata zuwa. Malam Ibrahim ya jajantawa hajiya kaka sosai sanan yake shawartatta akan tazo wajansa zuwa gobe ko jibi

Please Login or Register in order to submit comment