Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abdul shi kuma dady ya d’auki babyn ammi suka shiga ciki.

Suna shiga d’akin ammi suka tarar da su faruq da haidar suna ta sharar bacci akan bed d’in ammin. Kalan dady ammi tae tare da cewa yanzu yaya yaza muyi da su faruq nasan dae gadan bazai ishe muba koh?. Jinjina kae dady yayi tare da cewa bari kiga yadda zamuyi da su, ajiye babyn ammi yayi akan sofa sanan, ya d’auki faruq a kafad’arsa ya fuce da shi.

Ba jimawa ya dawo ya d’auki haidar shima ya fuce da shi. Bayan ya dawo ya kalli ammi tare da cewa madam bisimilla koh, murmushi ammi tae sanan tace aa bari na fara kwantar da twins d’ina, murmushi shima dady yayi tare da cewa tom shikenan kwantar da su, amma fa daga yau su haidar sun dae na kwana a d’akin nan, na mayar da su d’akin mae sunan baba wato mashkhur.

Ai yanzu sun girma da kwana a wajan mu gwara da kamayar da su can, cewar ammi. Zaga yowa bayan ammi dady yayi tare da ringome ammi ta baya yana cewa hmm kinga yanzu sae mu ringa shan sha’a ninmu hankali kwance, ba fargabar tashin su faruq. Ture shi ammi tae tare da cewa ae sae ka bari nayi arba’in, in yaso ka d’ora daga indda ka tsaya.

Dariya dady yayi tare da cewa ya za’ai kice haka mu dae d’ora daga inda muka tsaya koh, tindda dae ba dole nake mike ba, ke ma ae kina so koh maman twins ya fad’a yana jan kumatin ammi. Murmushi ammi tae ba tare da ta sake cewa komai ba, ta qarasa kan gado ta kwantar da babyn abdul, bayan ta kwantar da ita, ta dawo kan sofa ta d’auki babyn ta, itama ta kwantar da ita a kusa da babyn abdul.

Daga haka itama ta kwanta gefan baby’s d’in. Shima dady tawowa yayi ya kwanta, d’ayan gefan tare da cewa nima bari na kwant tindda yau ba ta tawa kike ba ta yaran ki kike. da yake yau a part d’in ammi yake, murmushi ammi tae tare da cewa ehh mana yau ta twins d’ina nake, daga haka suka cigaba da hira har bacci yayi awan gaba da su.

Washegari

Washegari duk mutan gidan basu tashi da wuri ba, sabida basu kwanta da wuri ba. Shiya ma su abdul da mashkhur basu je makaranta ba. Har wajan qarfe goma na safe ammi bata samu ruwan nonon da zata bawa jaririn ba dan haka madara ta cigaba da basu. Abdul kuwa yana maqale da babyn sa, baya bari kowa ya d’auke ta sae ammi.

Haka dady ya tara su ammi da momy harma da hajiya kaka yace duk wadda yazo barka koh suna, kar suce jaririyar nan ajiyar ta aka basu, kawai suce mahifiyar tace ta mutu a wajan haihuwar ta a, asibiti da ammi ta haihu kuma bata da dangi a kusa anyi cigiya ba’a samu dangin taba shiyasa suka tawo da ita. Kowa ya gamsu da hakan badda momy da tana shiga ta kunnanta tana fita.

Haka ammi tae ta kula da jariran ta cikin kulawa da qauna. Amma 6an garan momy kuwa koh kallo babyn abdul bata isheta ba, bare ta d’auke ta. Yanzu duk duniya ba wadda momy take jin haushi sama da babyn abdul dan ta tsani zaman ta a gidan nan kwata-kwata. Hmm 🤔 nikuwa Amina bayero nace tabb wanna wana kalar mugun haline yarinyar da kwana bakwai batayi ba.

har wajan kwana hud’u ruwan nono bae zowa ammi ba, dan haka ta cigaba da bawa jariran madara. 6an garan mashkhur kuwa yana d’aukar jariran ba laifi, duk da shi bae fiya d’aukar yaraba. Itama hajiya kaka tana jin dad’i yadda ammi da dady suke bawa babyn abdul kulawa kamar su suka haife ta.

Dady ya lura da kalar qaunar da hajiya kaka takewa babyn abdul dan haka ya yanke shawarar zai sawa babyn abdul sunan hajiya kaka.
Haka kuwa akayi ranar suna dady ya sawa babyn abdul FATIMA ZAHRA. Ita kuma babyn ammi aka sa mata SAKINA ake mata karada ilham. Hajiya kaka taji dad’i hakan sosai kuma tayi farin ciki da hakan.

Momy taso ta ringa gayawa ‘yan suna gaskiyar yadda akai aka kawo zahra gidan amma, in sabida kwata-kwata dan gin su hajiya kaka basu bata fuska ba, sabida wulaqancin da take musu. Dan gin momy ma ba wadda yazo gidan sunan. Dama saratu ce mae zuwa wajan halima gashi dady yanzu ya hanata zuwa gidan.

Anyi suna lafiya kuma an gama lafiya, sanan kowa ya koma gidan sa lafiya. Amma fa har kwanan yau ammi madara take bawa baby’s d’in sabida har yanzu ruwan nonon bae zoba, dan haka ita da dady suka yanke shwarar zuwa wajan likita. Haka kuwa akayai da sukaje asibiti aka bawa ammi magunguna da kuma shawarwarin abinci da zata ringa ci.

6an garan momy kuwa ta lura da yadda yaran gidan suke qaunar zahra sosai, kuma abidda ya bata mamaki harda mashkhur shida bama ya son mutane suzo gidan su. Amma sae gashi yana son zahra kuma tasan mashkhur baya son d’aukar yara musumman ma mace sae gashi yana d’aukar zahra.

Hakan ba qaramin bawa momy haushi yayi ba dan haka ta d’au alwashin sae ta sa mashkhur da yaran gidan sun tsani zahra kuma sun dae na d’aukar ta.
Yau wajan satin su zahra uku a duniya, amma har yanzu ammi madara take basu. Dan ammi sae shan maganin likitan take amma har yanzu ruwan nono bae zoba.

Yanzu ammi harta dae na shan maganin da likita ya bata ta haqura, ta cigaba da bawa su zahra madara. 6an garan abdul kuwa yana nunawa zahra kulawa biye da yaran gidan, kullum in ya dawo daga makaranta yana maqale da zahra. Ba abidda yake rabashi da zahra sae bacci, yanzu kowa agidan ya lura da yadda abdul yake son zahara, shiyasama yanzu ‘yan gidan suke kiran zahra da babyn abdul.🤗

*ina godiya da masoyana masu bibiyar wanna littafin na ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA........💜❤️💜

*ga masu buqatar karanta littafin ADALILINTA da nayi posting sae suyimin maga ta wanna number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira. Free book ne littafin bana kud’i ba kuma new book.

New book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing...........

*page 30*
Shiyasama yanzu ‘yan gidan suke kiran zahra da babyn abdul........

Yau watan su zahra d’aya a duniya, kuma yau ta kama ranar jumma’a su mashkhur da abdul ba makaranta. Dan haka yau mashkhur yana zaune a d’akin su yana kallo. Yana cikin kallan wani film a ABC 2 yaji an turo qofar d’akin, juyowa yayi dan yaga waye ya turo d’akin, Ba kowa bane face abdul.

Bakin sa dauke da sallama ya shiga, amsa mishi mashkhur yayi tare da mayar da idon sa kan tv da yake kallan. Da sauri abdul ya qaraso tare da cewa yaya mashkhur ana kiran ka, kallan sa mashkhur yayi tare da cewa waye yake kirana?. Maman rukee ce take kiran ka. Ya mutsa fuska mashkhur yayi sabida baya san yaje kiran kallan ya wuce shi.

Mae da kallan sa kan abdul yayi tare da ce mae, ba maman rukee zaka ringa cemata ba mamanka ce fa!. Kwab’e fuska abdul yayi tare da cewa ni Wallahi ba mamata bace, harara mashkhur ya watsa masa tare da cewa toh in ba itace maman taka ba wacece to?. Ni ammi ce mamana, ta6e baki mashkhur yayi kamar wani babba tare da cewa ai shikenan,

Amma daga yau ka dae na ce mata maman rukee ka d’inga ce mata momy kaji abdul d’ina.D’aga kae abdul yayi alamin tom. Daga haka mashkhur ya wuce kiran momy. Da sallama ya shiga part d’in nata. Tana zaune a falo ga rukee a gefanta tana ta wasa. Amsa mishi sallamar tayi tare da washe baki tana cewa ahh mashkhur harga zo kenan.

Ehh Wallahi momy ina wuni? Lafiya qalau ga waje nan zauan ina son magana da kae cewar momy, ba musu ya kama guri kan kujera ya zauna. Yana zama ya zubawa momy ido alamin yana sauraran ta. Gyara zama tayi tare da cewa, wae mashkhur baka gaji da zaman yarinyar nan a gidan nan ba, nasan kae ba mae son mutane bane.

Kallan momy mashkhur yayi tare da cewa momy wace yarinya kenan? Jinjina kae momy tayi tare da cewa au wae kae har ka manta da zaman waccan banzar jaririyar da kakar ka ta tsunto kenan?. Cikin mamaki mashkhur ya ce momy jaririya ce fa taya zan gaji da zaman ta tundda ba takuramin take ba?. Tsaki momy taja tare da cewa yanzu mashkhur kana nufin kae ma kana son zaman yarinyar nan a gidan nan kenan?.

Cikin mamaki mashkhur yace to momy in badda abinki, ni na isa na hanata ta zauna a gidan nan, kina ganinfa yadda ammi da dady harma da hajiya kaka suke qaunar ta, kuma shima kinga abdul yana son ta sosai, kai bama abdul ba harda su faruq da haidar, tom nima momy ae dole na sota tindda ‘yan uwana suna sonta koh?.

Ni Wallahi momy tausayi ma yrinyar take bani. A firgice momy take sauraran abidda mashkhur yake cewa. Yana gama fad’in hakan momy tace amma Wallahi mashkhur ka bani kunya haba mashkhur, yanzu karasa wadda zaka tausayawa sae waccan shegiyar yarinyar?. Zoro ido waje mashkhur yayi tare da cewa haba momy ki dae na zakinta jaririya ce fa.

Tsaki momy taja tare da cewa wallahi mashkhur yanzu na fara zagin yarinyar nan dan wallahi na tsane ta. Shiru mashkhur yayi a zuciya yake tina magar dady da yacewa momy bata da imani, ranar da hajiya kaka ta kawo zahra da daddare. Maganar momy ce ta katse mashkhur daga tinanin daya tafi cewa tai, mashkhur naji kayi shiru?.

Murya a sanyaye yace wae dan ALLAH momy sabida mae kika tsani zahra haka?. Murmushin qeta momy tayi sabida anzo dae-dae inda take so tasan tabbas in tayiwa mashkhur bayanin nan dole yaji ya fara tsanar zahra. Gyara zama momy tayi tare da cewa yauwa mashkhur abidda yasa kaji na tsani yarinyar nan shene,

Na farko dae, bamu san asalinta ba, na biyu kuma bamusan halin iyayan ta ba. Kae wayasani ma koh yar SHEGIYACE bata da uba. Zaro ido mashkhur yayi tare da cewa shegiya kuma? Duk da a lokacin mashkhur bae gama sanin cikin shegeba, amma tabbas yasan shege ba abin arziki bane.

Ehhh mana ‘yar shegiya ce mana, uwar ta tayi cikin shegenta ta haife ta, tazo tayi sada da ita. Yanzu ke momy taya akai kikansa zahra ‘yar shege ce?. Haba mashkhur taya za’ai uwa tayi sadakar ‘yar ta in ba ‘yar shegiya bace?. Shuru mashkhur yayi kafin yace amma ae momy ba sadakarta maman ta tayi da itaba kina dae ji amanarta tabawa hajiya kaka.

Wani dogan tsaki momy ta sake ja tare da cewa hmmm au wae kai ka yadda da rainin hankalin nan kenan?, kawae fa qarya ta zubawa hajiya dan ta karb’i ‘yar tata. Wae kae mashkhur ka manta da film d’in da muka kalla jiya ne?.zabura mashkhur yayi, sabida ya tuna da abidda ya faru a film d’in jiya, da momy ta kunna musa a laptop d’in ta suka kallan.

Abidda ya faru a cikin film d’in shine wata ‘yar aiki ce taje aiki a gidan masu kud’i, sukuma mutanan gidan suka ringa tausaya mata suna siyar mata abubuwa daga qarshe ma ‘yar gidan suka mayar da ita, da yake ‘yar aikin bata da uwa bare uba. Haka dae suka ringa nunawa mata gata har a makaranta suka sakata, amma daga qarshe sae da ‘yar aikin nan ta had’a baki da wasu aka kashe mutan gidan.

Dama momy tana sane ta kira mashkhur ta nuna mae film d’in nan sabida ta hure mae kunne ya dae na son Zahra. Jiki a mace mashkhur yace hakane momy, gaskiya ‘yar aikin nan batayi musu adalci ba. Jinjina kae momy tae tare da cewa tom kagani yanzu abidda nake so da kae karka qara kula yarinyar nan bare ka d’auke ta, kai koh kallanta kar ka qarayi.

Momy tana sane ta hana mashkhur kula Zahra sabida tasan ta mallake shi. Mashkhur bae so hakan ba amma ba yadda ya iya da momy a ala dole yace mata to. Daga haka yayi sallama da momy yayi hanyar fita, zai fita kenan rukee ta fara kuka alamin ya tafi da ita. Amma mashkhur koh juyowa bae yi ba, sabida yasan momy bazata bari akai ta b’an garan ammi ba, dama shi bayasan d’aukar ta sabida kukane da ita sosai.

Bayan mashkhur ya fita daga wajan mimy, part d’in ammi ya wuce, yana zuwa ya wuce d’akin su. Ko da ya shiga bae samu abdul ba, sae dai tv daya bari a kunne, zama yayi yaciga da kallan film d’in duk da an kusan gamawa. Yana kallon amma kwata-kwata hankalinsa baya kan tv.

Kawai tinanin magagganin da sukayi da momy yake. Haka nan yaji ya fara jin haushin zahra, amma dae duk da haka bae dae na tausayin taba. Haka dae yay ta tinani-tinani har bacci ya kwashe shi. Tinddagara ranar da mashkhur sukayi maga da momy akan zahra ai kuwa bae sake d’aukar taba, kai koh kallo bata ishe shi ba. Haka zai tsallake zahra ya d’auki ilham.

Tin ammi bata lura har ta fara ganewa, amma bata kawo komai a ranta ba, sabida tasan halin mashkhur da tsirfan tsiya. Har yau ammi madara take bawa su zahra sabida ruwan nonon yaqi zuwa tun ammi tana sa ran zuwan sa harta dae na. 6an garan abdul kuwa kullum kara son qanwar sa zahra yake, in dae yana kusa da ita baya bari ko quda ya tab’a ta.

6an garan hajiya kaka kuwa sae da taje takanas ta kano wajan malam Ibrahim, akan zancan zahra. Ko da ta gaya mae yadda akayi game da samun zahra, ya qarfafawa hajiya kaka guiwa game da rokwan zahra, kuma ya nuna mata ae aikin lada ne. Hajiya kaka taji dad’i hakan sosai shiya jininta ya had’u da malam Ibrahim, sabida shi malami ne mae tsoran ALLAH.

Kuma gashi in dae zai baka magani da sunan ALLAH da ayoyin AL QUR’ANI yake baka, ba kamar wasu malam da suke SHIRKA ba.
yanzu momy kullum in mashkhur yazo gunta da irin zigar da take mae akan zahra, kullum cikin 6ata zahra take a wajan mashkhur, tun mashkhur yana jin ba dad’i harya dae na.

Yanzu mashkhur ma ya dae na tausayawa zahra kwata-kwata, sabida ba qaramin ziga momy takewa mashkhur ba. Momy taso ta ziga abdul akan ya dae na kula zahra amma ina dan abdul in tana yimae maganar ma baya fahimta, kawai ba abidda yake ce mata sae shi zahra babyn sa ce kuma yana son ta, Wallahi bazai dai na d’aukar ta ba kuma sae ya kulata.

Kai da abdul ya gaji da zigar momy ma dae na zuwa wajan ta yayi gaba d’aya. Momy taso ta hana su haidar kula zahra amma hakan bazai yuba sabida su yarana ne, koh ta gaya musu baza su gane ba. Sabida alokacin faruq shekarar sa uku (3 years) shi kuma haidar shikarar shi biyu (2 years). Dan haka dole ta haqura.

Yanzu su zahra sunyi wata biyar da haihuwa. sunyi wayo sun girma, inka gansu kamar ‘yan biyu duk da basa kama kuwa. Kawae dae yanayin hasken fatar su ne yazo d’aya sae kuma giram jikin. Sunyi luwai-luwai abinsu, sabida madarar da ake basu ta karb’e su.
6an garan momy kuwa ta fara shirin zuwa kaduna sabida taje wajan BOKAN su.

Yanzu momy haushin ammi take ji sosai, taci alwashin sae ta KASHETA. Abidda yasa momy take jin haushin ammi shine!! Taga yadda dady kullum yake qara son ammi. Duk abindda zai yi sae yayi shawara da ita. Kuma sau da dama in dady yana tare da momy sae ya ringa ambatar sunar ammi, sabida ammi tana ransa, kuma gashi ammi tafi momy iya kula da miji..............

Dan Allah kuyi haquri da ni, yau page d’aya na iya rubutuwa, sabida bani da ishashan lokaci.

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar wanna littafin mai suna ADALILINTA. ina yi muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*ga masu buqatar karnta littafin ADALILINTA da nayi posting sae suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. kuma free book ne bana kud’i ba new book.

Now book on 2023

[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*page 31*
Sabida ammi tana ransa, kuma ammi tafi momy iya kula da miji.........

Yanzu momy fara shirye-shiryan tafiya kaduna wajan boka. Haka ta samu dady da maganar zata je kaduna ta duba mahifiyar ta. Dady kuwa hanata yayi sabida a lokacin momy tana da tsowan ciki. Da ALLAH da ANNABI momy ta ringa had’a dady akan ya barta ta tafi, wae harda ce mae ummanta ce take ta kiran sunanta jikin ta yayi tsanani sosai.

Dady kuwa yasan momy qarya take amma ala dole ya barta, sabida yasan in ya hanata tatafi kollum da masifar da zata tayar a gidan nan, har sae ta wuce. Sae da dady ya had’a momy da driven gidan kuma ya ja musu kunne akan kwana d’aya zatai ta dawo. Momy tayi farin ciki da hakan sosai, kuma taso ta tafi da abdul amma qiri-qiri yaqi binta.

Haka abdul yace bazai bita ba sabida babyn sa zahra da kuma ammin sa. A ala dole momy ta haqura ta tafi da rukee, alokacin rukee ta fara girma zatai shekara d’aya (1 years).
Momy sun isa garin kaduna lafiya. Tana isa ko hutawa batai ba suka fara shirye-shiryen tafi wajan boka. Driven yaso ya kae momy da umman ta, amma suka hana shi zuwa wae ba nisa zasuyi ba.

Haka ya haqura ya zauna a wajan malam garba su kai ta hira. Su momy suna fita fasu tsaya a koh inaba sae wajan boka. Suna zuwa wajan boka momy ta fara yiwa boka bayanin abidda ammi take mata!!! Ni wlh boka abidda yake damuna shine kwata-kwata mijina baya saurarata koh shawara zai yi sai dae yayi da kishiya ta.

Yanzu fa yama fi son ta fiye da ni, koh da yake ae ni yanzu ma ya dae na sona. Gashi in muna tare da shi har subitar baki yake ya ringa kiran sunan ta. Kae ko wata mu’a malar aure muke wlh sae kaji yana kiran sunan ta. Ni dae gaskiya abin nan ya isheni shiyasa ma nazo wajan ka dan kayi min maganin ta.

Wata shu’u’mar dariya boka ya saki, sae da yayi mae isar shi sanan ya daka ta. Kallan momy yayi tare da cewa kinzo kuwa indda za’a share miki kukan ki. Daga momyn har umman ta dariya samun nasa sukayi, maganar boka ce ta katse su daga dariyar da suke. Yanzu mae kikeso a yiwa kishiyar taki? Gyara zama tayi tare da cewa yauwa yanzu boka ka fara lissafomin abuban da zaka iya yima.

Dariyar mugunta boka ya saki tare da cewa keee ‘yar nan ae ba abidda bazamu iya ba, nida nake aiki da aljanuma, tom bari kiji zan iya zamar miki da ita MAHAUKACIYA, zan iya zamar da ita KARUWA MAI BIN MAZA, zan iya zamar miki da ita B’ARAU NIYA, kuma zan iya sa mata CUTAR da bazata iya morar kanta ba bare ta kula da ‘yayan ta da mijin ma gaba d’aya.

Ke inma so kike na KASHETA har lahira sae na kasheta. Jinjina kae momy tayi tare da cewa gaskiya boka ba qaramin shu’u’mi bane kai yanzu duk zaka iya wanan? Wata dariya boka yayi tare da cewa harma abidda ya fi wannan. Juyawa momy tae ta kalli mahifiyar ta tare da cewa yanzu umma wana aiki za’ai mata aciki?.

Ya mutsa fuska mahifiyar momy tayi tare da cewa kawai a KASHE ‘yar banza. Momy da taji hakan koh gizau batayi ba, fuska ba alamin imani koh karaya tace amma umma ga wata shawara mana. Zubawa momy ido tayi tare da cewa inajiki halima. Amma umma in aka kashe maryam farar d’aya ai an ta qai ta mata wahala, ni dae a ganina ya tura mata cutar da zata kasa komai, ta ringa kwana a kwance tana wuni a kwance

Kae ko d’aga yatsan ta ma ta dae na yi. Haka za tai ta jinya har sae tayi wata biyar a kwance, kinga shima dadyn abdul d’in tsanar ta zai yi kuma ya gaji da ita, kinga daga haka kawai sae mu dawo wajan boka ya kashe mana banza, kinga kuwa ae ta sha wahala kuma taji jiki.

Kafin umman momy tayi magana sukaji boka ya fasa wata uwar dariya tare da cewa kwarai kuwa ‘yar nan kin kawo shawara mae kyau hakama za’ai. Itama umman momy ta yadda da shawarar dan haka a take a wajan boka ya fara qoqarin turawa ammi cutar. Ba irin abidda boka bae yi ba akan ya tura ammi cutar amma ya kasa har al janu ya tura mata amma ina abin ya faskara.

Saka makwan alokacin ma ammi salla take yi, kuma bayan ta idar da sallar addu’a ta fara yi. Kallan su momy boka yayi tare da cewa gaskiya an samu matsa, kallan sa su momy sukai a gigice har suna had’a baki wajan cewa boka mae ya faru ne?. Had’e fuska boka yayi tare da cewa sallah take yi kuma in dae mutum yana sallah da addu’a bama iya yi mae aiki.

A gigice momy tace yanzu boka bamu da wata mafutar? Shiru boka yayi can kuma ya kwashe da wata dariyar, sae da yayi mae isar sa kafin yace da akwai wata hanya d’aya da ta rage. Dariya momy tayi tare da cewa yauwa boka waca hanya ce haka?. Yanzu hanyar data rage mana shine sae da a zuba mata magani a bu taci, zaki iya koh?. A hanzar ce momy tace zan iya mana.

Daga haka boka ya bawa momy magani yayi mata bayanin yadda zata yi amfani da shi, bayan ya gama basu maganin suka cake mai kud’ad’e sukayi gaba. Washe gari da safe momy ta gama shiryawa domin ta koma kano, tayi sallam da malam garba da mahifiyar ta, amma sae ta biya ta gidan qanwar ta saratu kafin ta tafi.

Bayan drive ya sauke momy a gidan saratu shigewa tai. Gidan saratu babba ne sosai kuma kana ganin gidan zaka sheda gidan attajiri ne. Bayan ta shiga suka gai sa, sanan suka hau hira. Sae da momy ta kwashe duk labarin zuwan zahra da yadda take zuga mashkhur ya dae na kulata, da kuma yadda mashkhur ya tsane ta, har wajan bokan da suka je sai da momy ta kwashe ta gayawa saratu.

Saratu kuwa qara ziga momy tayi akan zaman zahra a gidan kuma tace wa momy ta yi mata dae-dae, akan abidda tayiwa zahra, kuma ta qara uzzira mata har sae tabar gidan. Daga haka momy ta fara shirya-shiyan tafi gida. Laa yaya na manta ban gaya miki ba kwaniki fa kishiya ta ta haihu amma ‘yar ta rasu, koh zan rakaki 6an garan ta kiyi mata jaje, saratu ta qarasa maganar tana dariya.

Itama momyn dariya tayi tare da cewa shegiya kawai mae cikin haihuwa, kinga kuwa ae kud’in ki ya huta da KASHE ‘yar, dama ae duk sauran yaran ke kike KASHA SU. Dariya saratu tayi tare da cewa ke dae bari yaya halima, ina zan barta ta haihu, haka kawai ta kwashe dukiyar mae gidan nan, ta barni a baya, kuma gashi ni ba haihuwa nake ba, haryau fama nake ban samu cikin ba.

Aii ki kwantar da hankalin ki saratu zaki haihu insha ALLAH ni dae bari na wuce ba wani jaje da zanwa kishiyar ki Wallahi, ke ni koh fuskar ta mah bana son gani. Dariya saratu tayi tare da cewa au haka ne fa yaya ashe baki

Please Login or Register in order to submit comment