Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi muku typing... da yawa ba, sabida abubuwa sun yimin yawa, amma in sha ALLAH gobe zanyi muku full typing. Ina yiwa masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA fatan alkhairi ALLAH ya bar zumunci.....

My number 08142246343...

Now book on 2023

[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing........

*page 41*
Ji kake tassss, mashkhur ne ya saki flat d’in hannunsa qasa tare da yin kukan kura ya nufi zahra........

Itama a ilham kukan kurar tayi tare da shan gaban mashkhur din tana cewa dan ALLAH yaya mashkhur karka tab’a zahra wallahi bada sani tayima hakan ba pls yaya mashkhur zahra bata da lafiya. Wani kyakyawan mari mashkhur ya zubawa ilham ji kake tass tare dasa qarfi ya tunkud’a ta gefe ta fad’i qasa warwas. Azafafe mashkhur ya janyo zahra tare da shaqe mata wuya da iyakacin qarfin sa. Yasalm ai duk su haidar kansu sukayi suna yiwa mashkhur magiya akan ya sakar musu ‘yar uwar su dan ALLAH karya kashe ta.

Kai bama su haidar ba harsu rukee hankalinsu ya tashi sai faman magiya sukewa yayan nasu tare da qoqari kwatar zahra daga hanun mashkhur, ilham kuwa sai kurma uban iho da kururwa take tare da fad’in dan ALLAH yaya mashkhur ka sakarmin ‘yar uwata karka kashemin ita. 6an garan zahra kuwa tuni ta fara kakari, numfashi yana qoqarin d’aukewa sabida sosai takejin azabar shaqar wuyan da mashkhur yayi mata.

6angaran mashkhur kuwa sam bama yajin magiyar da qannan nasa suke masa sabida tsabar 6acin rai. Duk sun taru su biyar suna qoqarin kwatar zahra amma ina sun kasa sabida tsabar qarfi da jarumta irin ta mashkhur. Allah sarki nukuwa amina bayero nace ina abdu? Yau da abdul yana nan da anyi kisa a gidan alhaji abubukar dala, amma ina abdul yana wajan ball.
Dasu faruq suka gaji da jan zahra mashkhur d’in suka fara ja suna qoqarin su rabashi da zahra.

Azuciya mashkhur ya saki wuyan zahra tare da kai wa haidar wani mumunan naushin da sai da bakinsa ya fashe, sanan ya juya 6angaran faruq ya qara sakar mishi naushi, shima faruq din hancinsa sai da ya fashe sabida tsabar naushin da ya sha. Rukee da ruma ma hanka d’asu yayi sukayi gefe, ilham kuwa ta qan qame shi da iya kacin qarfinta tana ta fama ihu. Tausayin tane ya kama shi amma duk da hakan sai da ya 6an6are ta yayi wurgi da ita gefe.

Duk su biyar din sunji jiki kowan nan su yana kwance yana juyi sabida tsabar azaba. Azuciye mashkhur ya sake nufar inda zahra take kwance rai a hanun ALLAH, tsugunawa yayi tare da d’aukar ta cankas ya dora ta a kafad’ar sa, ai bai nufi hanyar ko ina da itaba sai bedroom d’in ammi da yake shine d’aki mafi kusa da su. Da sauri ilham ta rufa musu baya a guje, amma ina kafin ta qarasa harya sawa d’akin key.

Yasalm ai nan da nan su faruq suka miqe kowa ya manta da azabar ciwan da yake ji, a guje suka nufi qofar d’akin, amma ina qofar a rufe take gam gashi qofar irin mai kwarin nan ce bata 6allewa da wuri. Ihun da sukaji yana futowa daga d’akin shine ya sake d’aga musu hankalin. 6angaran mashkhur kuwa tundda ya shiga d’aki da zahra ya wurga ta gefan gado, bayan ya wurga ta gefan gadon hannu ya dunqule ya fara kai mata wasu mahaukatan naushi, dukan zahra mashkhur yake baji ba gani.

6angaran su ilham kuwa hankalinsu yagama tashi, sai kuka suke bakajin komai sai tashin kuka hatta rukee da bata da imani kuka take dama kuma can ita ruma tana son zahra kawai dai dan momy tafi qarfinta ne . Ilham kuwa da tagaji da jin kukan zahra ga tashin hankali tuni ta fad’in qasa sumamiya. Tofa hankali su faruq ya sake tashi ga kukan zahra ga suman ilham. Agigice faruq yace haidar jeka ka kira mana yaya abdul.

Cikin kuka haidar yace ai bansa ina yatafi ba? Shima faruq cikin kuka ya bawa haidar amsa da cewa nasan yana filin ball jiya naji yana cewa yau zasuyi ball, haidar bai qara cewa komai ba ya kama hanyar fita da gudu. Fitar haidar ke da wuya suka qarajin zahra ta kwalla wani ihu da iya kacin qarfin ta nan da nan suma suka fara ihu tare da qara gigicewa.
Dukan zahra mashkh ur yake iya qarfinsa, da ya gaji da naushinta da hannu qafar sa yasa yana ball da ita.

Lokacin da haidar ya isa filin ball ya tarar da abdul suna ta ball, a hanzarce haidar ya qarasa tare da ruqo rigar abdul. Da suri abdul ya juyo dumin ganin waye yayi mai wannan ruqon? Yana juyowa sukayi ido hudu da haidar, cikin mamaki abdul yace haidar lafiya naga kamar kayi kuka wa ya fasama baki? koh fad’an kukayi a makaranta? nagama baka cire uniform dinka ba kamarma bakaje gida ba koh? Da sauri haidar yace yaya abdul Wallahi yaya mashkhur zai KWASHE ZAHRA yasa ta!!!!!

Ai tun kafin haidar ya qarasa magana abdul ya kwasa a guje yabar haidar a tsaye a wajan. Shima haidar din bin bayansa yayi. Tundda abdul ya fara gudu bai tsaya ba har sai da yazo gida falon ammi, lokacin da ya isa falon wani uban iho yaji zahra ta kwallara, ai kuwa agigice abdul ya nufi qofar d’akin ya buga qofar da iya kacin qarfinsa, amma ina qofa ko gizau batayi ba. Cikin qarajin murya abdul ya furta wai kai MASHKHUR baka da HANKALI ne ai bansan kai cikaken MAHAUKACI bane sai yau.

Karaf a kunnan mashkhur duk Abunda abdul yace mashkhur yaji. Dai na dukan Zahra mashkhur yayi dan kalaman abdul har kwakwalwarsa yake jin su m, wai yau qanin sa da yake masifar qaunarsa da yimai BIYAYYAH shine yake kiran sa da mahaukaci kuma duk ADALILIN ZAHRA... tab lalai wanan yarinyar ta zama fitina a rayuwar sa, bai kai da qarasa maganar ba yaji abdul ya sake cewa wlh yaya mashkhur ka saki ka illata zahra ko ka kasheta nima sai na KASHEKA DA HANNUNA.

A fusace mashkhur yace tom shikenan abdul zan kashea in yaso kai ma sai ka kashe d’an uwanka ADALILINTA. Duk suna sauraran mai mashkhur yace amma sam su haidar basu gane mai mashkhur yake nufi ba game da abinda yacewa abdul sai ka kashe dan uwanka a dalilin ta su haidar basa cikin hayyacin su da zasu gane abindda mashkhur yake nufi, 6angaran ilham kuma har yanzu tana sume.

Sunajin maganar mashkhur tacewa zai kashe zahra nan hankalinsu ya sake tashi musamman ma abdul hankalinsa yafi na kowa tashi magiya ya hau yiwa mashkhur” haba yaya mashkhur dan ALLAH ka bud’e dakin nan wlh bazan jure dukan zahra da kake ba zuciya ta zata biga. Amma ina mashkhur tuni ya cigaba da dukan zahra dan yanzu zahra harma bata iya ihun muryar ta duk ta dashe in banda sunan yaya Abdul ba abindda take ambata ba. Abdul kuwa sai faman dukan qofar yake duk yafita daga hayyacin sa.

A dai dai lokacin motar su dady ta shigo gidan ai ruma tanajin hroon ta kwasa a guje ta fuce. Ruma tana isa su dady suna parking, da sauri dady harma da su hjy kaka suka bud’e murfin motar suka futo sabiya yanayin da sukaga ruma sunsan ba lafiya ba. Ai ko suna futowa ruma ta fara magana cikin kuka take cewa dady wlh yaya mashkhur zai kashe zahra inagama ya KASHETA. Ai tana gama fadar haka dady da ammi harma da hajiya kaka suka kwasa a guje, shima ameer duk da bai gane abinda ruma take nufiba da sauri ya bisu.

Ruma ta juya kenan zata tafi momy tace to wai in ya kasheta menene? Agigice ruma tace wlh momy baki da imani tana gama fad’ar hakan ta juya ta bi bayan su dady. Momy tayi mamakin maganar da ruma ta gaya mata, kwafa tayi tare da bin bayan ruman itama. Lokacin dasu dady suka qarasa falon harma Zahra ta dai na kuka, su haidar kuwa suna riqe da abdul da ya dakko wuqa yana cewa wlh mashkhur in baka bud’e qofar nan ba sai na kashe kai na yanzun nan sabida bazan iya jore ganin kana yiwa zahra d’an yan hukuncin nan ba.

Mashkhur yana jin haka ya rabu da zahra da take kwance ko motsi batayi, murya a shaqe yace abdul zan bud’e. dady kuwa a hanzarce ya nufi qofar tare da cewa kai mashkhur zoka bud’e qofar dan kutumar uban shege mistiyaci kawai. Ai ba iya su abdul ba har su ammi da momy wandda ta shigo d’akin yanzu sai da sukayi mamakin dan tundda suke basu tab’a ganin dady yayi zagiba. Ita dai ammi agigi ce ta fizge wuqar da abdul ya dakko tare da cewa abdul mai kake qoqarin yi haka.

Wani kyakyawan mari momy ta sakar mai tare da cewa kai sabida zahran kake qoqarin kashe kanka? Maganar dady ce ta jawo hankalin kowa ya dawo bakin qofar da mashkhur ya kulle zahra. Kai dan uwarka ba magana nakema ba shege mahaukaci kawai?
Mashkhur kuwa yana tsaye gaban qofar yana mamakin zagin dady dan tunda yake bai ta6a ji dady yayi zagi ba sai kashi dan ya dakin zahra yake zagi, yana cikin tinanin nan sai gashi saqon zagin dady na biyo ya shigo kunnan sa.

Tundda mashkhur yaji haka yasan dady yaufa fishinsa yazo qarshe, dan haka a hanzarce ya kai hannun ya murda key din domin bude dakin.
Ai yana bud’ewa dady ya sakar mishi wani kyakyawan naushi tare da hankad’e shi gefe, sabida tsafar naushin da mashkhur yasha ai har sai da shima hancin sa ya fashe. A hanzarce dady ya wuce domin ganin mai mashkhur ya aikatawa zahra? Suma su abdul din dasu ammi a guje suka shigo dakin.

Banda ilham da take kwance a sume ameer kuwa sai jijigata yake yana mata wasa, shi baima san abinda yake faruwa ba.
Ai dady yana shiga sai da gabansa ya fadi nunfashinsa ma har d’aukewa ya kusan yi sabida ganin irin illar da mashkhur yayiwa zahra. Kwance take ko mosti batayi bare nunfashi duk yabi ya fasa mata baki da hanci fuskarta ta kunbura suntum ga wuyanta yayi jajawur alamun shaqa, duk jikinta yayi jajir abinka da farar fata jini sai zuba yake ko ta ina.

Ammi kuwa take ta fad’in qasa sumamiya abdul kuwa duk yabi ya fita daga hayyacin, tsugunawa yayi tare da rungumo zahra jikisa sai jijigata yake yana kuka. Hajiya kaka kuwa suman tsaye tayi in banda inalilahi ba abinda take furtawa sauran yaran kuwa sai jijiga ammi suke suna kuka nikuwa amina bayero nace yau wannan gida sunga tashin hankali😢
Dady kuwa ya rasa abinyi tunani yakema dane zai KWASHE Mashkhur dan yau mashkhur yakai dady qarshe.

Dady yana matuqar son mashkhur arayuwar sa, fiye da duk yaran da ya haifa, shiyasama watarana idan mashkhur yayi mai taurin kai yake kyale shi, amma yau mashkhur yakai dady qarshe ji yake kamar ya kashe shi ya huta. A hanzar ce dady ya dakko glass table din daki ya nufi mashkhur da yake tsaye a bakin qofa. Da sauri hajiya kaka ta ruqo rigar dady tare da shan gaban sa. A fusace dady yace dan ALLAH hajiya ki barni yau na kashe d’an ISKAN yaron nan dan wlh bai daki baza ba.

Muryar hajiya kaka tana rawa tace haba Abubakar karfa azo ayi d’a kwance uwa kwance, kana ganin zahra akwance bata iya motsi qilama ya kasheta, kuma ga maryam da ilham a sume mu hanzarta tafiya asibiti in yaso in muka dawo sai kayi mai duk hukuncin da kaga dama. Jiki ba kwari dady ya ajiye glass table din tare da nufar firinji room din. Ruwa mai sanyi dady ya dakko, yana bud’ewa ya yayyafawa ammi ruwan, da salati ammi ta farka tare da cewa shikenan ya kashe ta.

A hajiya kaka zama tayi tare da kwantarwa da ammi hankali. Dady kuwa wacewa yayi inda ilham take itama ya fara yayyafa mata ruwan. Ilham kuwa ko mosti batayi ba, haka dady yay ta watsa mata ruwa amma ina ko mosti ilham. Da sauri dady ya koma room d’in ammi tare da cewa abdul ku futo mu tafi asibiti. Abdul kuwa ina sam ya kasa sakin zahra ya qan qameta sai kuka yake.

A hanzarce dady ya qarasa wajan da abdul yake durqushe rungeme da zahra, tsugunawa dady yayi tare da dafa kafad’ar abdul yana cewa, haba Abdul yanzu fa ba lokacin kuka bane ka daure mu kai ta asibiti ita da ilham kaga tana cikin mawuyacin hali. Daga haka dady ya kar6i zahra daga hanun Abdul , hanyar waje ya nufa hannu dauke da zahra tare da cewa hajiya kufuto ke da maryam da kuma abdul mu tafi asibiti.

Momy kuwa ko ta kansu bata biba lalashin mashkhur ma tahau yi harma da cemai yayi dai-dai. Hajiya kaka da ammi da take tafia da kyar ko kallan su basubi ba suka fuce. Bayan dady ya kai zahra mota ilham ya dawo ya dauka, shima Abdul bayan dadyn yabi. Bayan motar dady zahra ce kwance ko mosti batayi, gaba kuma ammi ce sai dady a mazaunin driver. D’ayar motar kuwa ilham ce kwance a baya hajiya kaka kuma a gaba sai kuma abdul a mazaunin drive. Asukane motocin suka fita daga gidan suka kama hanyar zuwa asibiti..............

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.........

*page 42*
A sukwane motocin suka fita daga gidan suka kama hanyar zuwa asibiti...........

Lokacin da suka isa hospital haka akace baza a kar6i zahra ba sai da ‘yan sanda. Amma sai akaci sa’a mai hospital din abokin dady ne sosai shiya aka kar6i zahra. D’akin agajin gaggawa aka shigar da zahra, dama ita ilham ana zuwa aka kar6e ta, kai hatta ammi ma sai da aka kwantar da ita akayi mata qarun ruwa da allurorin bacci.
6an garan abdul kuwa ya kifa kansa akan guiwarsa sai shar6ar kuka yake, hjy kaka da dady sai faman rarrashin sa suke.

6angaran zahra kuwa likitoci sun duqufa akanta, sosai likitocin suke qoqarin ceto ran zahra sabida tayi doguwar suma sosaii abindai kamar zahra bazata rayuwa ba.
6angaran ilham kuwa ta farfad’o dama doguwar suma tayi. A razane ilham ta farka tana ihu tare da kiran wayyo zahra, zahra, zahra, dan ALLAH yaya mashkhur ka rabi da ita karka kashe ta, wayyo zai kashemin ‘yar uwa.

Sai da likitoci suka yima allurar bacci sannan ta samu tayi shiru.
Tofah su dady hankalin su ya tashi sosai sabida tun sanda aka shiga da zahra dakin asibitin har yanzu ko likita d’aya bai fitoba barema susan a wana hali take ciki. Hankalin abdul ya sake tashi sosai, dady ma kawai jurewa yake sabida hankakinsa a tashe yake sosai, itama hajiya kaka haka amma ita dai kawai addu’a take ta faman yi.

Misalin qarfe tare na dare (9:00 pm) likitoci suka fara futowa daga room din da aka kwantar da zahra. Da sauri dady da abdul harma da hajiya kaka suka nufi wajan likitocin. Har suna had’a baki wanjan cewa ya jikin nata?.
Jinjina kai doctor yayi tare da cewa ku kwantar da hankalin ku, alhaji ka sameni a Office, daga haka doctor ya wuce office.

Lokacin da dady ya isa office d’in doctor habib zama yayi a kan kujera, tare da cewa doctor ya jikin mamana?. Ajiyar zuciya doctor ya sauke take da cewa jiki dai Alhamdulilah, mun samu kan yarinyar nan da kyar, dan ALLAH ne yayi tana da nisan kwana. Shima dady ajiyar zuciya ya saki tare da firta ALHAMDULILAH.... kallan dady doctor habib yayi tare da cewa ammafa gaskiya Alhaji, kunyi sakaci sosai akan yarinyar nan dan dabadan ALLAH yayi tana da nisan kwana ba da tini yanzu kun rasa ta.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa wannan d’in ma tsautasayi ne, in sha ALLAH hakan bazata sake faruwa ba, jinjina kai doctor yayi tare da cewa tom ALLL ya kiyaye gaba, nine likitan da zai ringa kula sa ita har ALLAH yabata lafiya. Okay yanzu nawa ake buqata? Cewar dady, mirmushi doctor habib yayi tare da cewa ai babban likita yace ayi mata komai free ya d’auki nauyin ta. Dady yaji dad’i hakan sosai bawai dan bashi da kud’in biya ba,, kawai sabida tsabar karamcin amin nasa.......

Zahra taji jiki sosai dan har abin shaqar nunfashi aka samata wato (oxygen). Sai washe gari zahra ta farka. Dama su dady basu koma gidan ba anan suka kwana.
Tom yanzu zahra kwanan ta hudu a asibiti dan yanzu jikinta yayi kyau sosai.
Ammi da ilham ne yau kwai a asibitin hjy kaka da abdul da kuma dady sun tafi gida sabida a lokacin dare yayi.

Zahra ce ta miqe daga kan gadon tare da cewa ammi bari na shiga toilet nayi fitsari, girgiza kai ammi tayi tare da miqewa tace bari dai na rakaki, kinga baki da lafiya, girgiza kai zahra tayi tare da cewa aaa nifa ammi na samu sauqi yanzu zan iya zuwa ni da kau na, tom ko in tashi ilham ta rakaki ne? Girgiza kai zahra tayi alamin aa”tom shikenan jeki, cewar ammi.

Zahra batafi minti biyu da shiga toilet ba su ammi sujaji ta kwallara qara mai sauti, wanda hakan sai da yasa ilham dake kwance tana bacci ta farka a firgice. Ammi da ilham har ‘yan rige-rige shiga toilet din suke. Zahra kuwa ta durqushe ta duqun qune Pants din ta” a hannu tana kuka, da sauri ammi ta qarasa inda take tsugune tare dafa kafadar ta, tana ce zahra lafiya naji kin kurma uban ihu haka?.

Boye pants din ta sakeyi tare da cewa bakomai, mamaki ne ya bayyana akan fuskar ammi, haba zahra ki gayamin ko awani abun ne yake miki ciwo? Shiru zahra tayi hawaye na cigaba da zuba akan fuskarta. Da sauri ilham ta qaraso gaban zahra tare da tsugunawa a gabanta, cewa tai zahra me kike 6oyewa haka? Nan da nan zahra ta fara zaro ido alamin mara gaskiya. Ammi kuwa tana ganin Hakan tasan tabbas da akwai abinda yake faruwa da zahra.

Hannu ammi ta miqa mata alamun ta miqo mata abinda take 6oyewa. Jiki ba kwari zahra ta futo da wanda data boye a hanunta ta miqawa ammi. Ammi tana kar6a ta bud’e domin ganin mene acikin wandan. Wanda duk ya jiqe da baqin jini, alamin zahra ta fara jinin al-ada. Dariya ilham tayi tare da cewa yanzu zahra akan wannan kike ta kurma uban ihu haka, ina baccina mai dad’i kin tashe ni.

Zahra kuwa fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan cinyar ta. Hannun zahra ammi ta ruqo tare da cewa taso mu koma daki, to meye na kukan ai wanna ba abin tada hankali bane. Dagowa zahra tayi tare da cewa haba ammi koh baki gani sosai ba jinine fa yake ziba. Girgiza kai ammi tayi tare da cewa to menene in jinin ne, zaro ido zahra tayi tare da cewa ammi ko dai mutuwa zanyi ne?

Haba zahra mene na mutuwa anan ai ba’a kanki aka faraba, itama ilham d’in da take miki dariya ai tanayi, taso mu koma d’aki kinji, sai naje na siyomiki wasu pants din. Da kyar zahra ta iya tasowa sabida ciwan da marar tata take mata.
Bayan sun koma room din kuka zahra ta saka sabida bata saba, kwantar da ita ammi tai a jikin ta tana ta rarrashinta. Bayan ammi ta gama rarrashin zahra tace mata mari na fita na siyo miki audiga kinji.

Girgiza kai zahra tayi tare da cewa itafa ta gaji da zaman asibitin nan gida take son koma. Bayadda ammi batayi da zahra ba akan tabari sai gobe in an sallame su amma zahra qiri-qiri taqi, hakan ne yasa ammi ta dauki waya ta bigawa dady amma wayar sam bata shiga, ana cikin hakan sai ga doctor habib ya shigo, wato likitan dake kula da zahra. Zahra tana ganinsa ta rufe idon ta sabida ta tsani kallan da yake mata, kullum in ya shigo yimata allura ko ya shigo dubata sai yay ta kallan ta ita kuma zahra batasan hakan.

Da sallam ya shigo fuska dauke da fara’a, itama ammi fuska a sake ta amsa mai, ilham ma cikin sakin fuska ta gai da doctor. Murmushi doctor yayi tare da cewa amma dae ga dukkan alamu kece husaina koh? Murmushi ilham tai tare da cewa ehh hakane amma doctor sabida mai ka gane?. Wata siririyar dariya doctor yayi tare da cewa kina wasa da likita mai gani har hanji?. Dariya ilham tai tare da cewa aa, doctor habib mai da kanllan sa yayi kan zahra wanda ta rintse ido akan cinyar ammi kamar mai bacci.

Murmushi ya saki sabida yana ganin ta yasan ba baccin gaske take ba, ya mai jikin inji ?. Jinjina kai ammi tayi tare da cewa jiki da sauqi amma yanzu ta gama kuka wai ita gida take son tafi, gashi na bigawa dadyn su amma wayar bata shiga. Zahra kuwa tanajin maganar gida ta bud’e idon ta tass, sabida batason doctor din ya hanata tafiya gida. Kallan zahra doctor yayi tare da cewa haba zahra ki bari zuwa jibi in an gama yimiki alluran ki, sai a sallame ki kinga kafin nan jikin ki ya qara kwari koh?.

Kuka zahra ta cigaba dayi tare da cewa itafa gida take son tafiya ta gaji da kwana a asibitin. Jijina kai doctor yayi tare da cewa kawai hjy tunda tana son tafiya gwara asallame ku, sabida kinsan shi mara lafiya anaso a ringa yimai abinda yake so. Girgiza kai ammi tayi tare da cewa doctor ai dare yayi kuma kaga yanzu bamu da motar da zamu koma gida gashi wayar dadyn nasu bata shiga.

Ah haba Hajiya ai koni na kai ku gida tinda kinga nine likitan da nake kula da ita kuma nima yanzu zan tafi gida, kinga ai sai na sauke ku. Daga haka doctor habib ko jiran amsar ammi bai yi ba ya nufi hanyar futa yana cewa to husaina bari naje na rubuta mata takaddar sallama kafin na dawo ki had’a kayan. Tom shikenan doctor cuwar ilham daga haka ilham ta miqe ta fara had’a kayan.
Doctor habib kyakywa ne sosai, baqi ne, amma ba can sosai ba, yana da tsayi kuma bashi da jiki sosai, kallo d’aya in kayi mai kasan yana da nutsuwa.

Ba’afi 15 minit ba sai ga doctor habib ya dawo hannunsa riqe da farar takaddar sallamar zahra. Haka su ammi suka bi doctor harwajan mota ita dai zahra da kyar take tafiya sabida tsabar cuwan mara. Haka ammi tai-tai wa doctor habib kwatance har ya kawo su gida. Suna isa qofar gida mai gadi ya wangali musu get, doctor habib yana shiga ciki sai ga motar dady ta turo kai cikin gidan.

Bayan doctor ya sauke su zahra yace zai ringa zuwa har na tsawan kwana biyu ya qarasawa zahra alluran ta. Sai da doctor habib suka gaisa da dady sanan yayi mai bayanin dawowar zahra gida, sanan kuma ya gayawa dady zai ringa zuwa na tsawan kwana biyu yana yiwa zahra Alura, dady yayiwa doctor habib godiya sosai sanna doctor ya tafi.
Lokacin da su zahra suka shiga gida kowa yayi bacci.

Sai da dady ya shigo part d’in ammi yayiwa zahra ya jiki sannan ya wuce 6angaran sa.
Ammi bata tsaya da zahra a ko inba sai bedroom d’in ta. Zahra kuwa har yanzu a tsorace take da jinin da ta gani dazu a asibiti. Suna isa d’aki jini ya sake 6allewa, nan da nan hankali zahra ya sake tashi sabida yanda taga jinin yana silalowa ta tsakiyar cinyoyin ta.

Ammi kuwa cewa ilham tai taje d’akin su tayi wanka ta canza kaya in zata dawo ta tawowa da zahra audiga da pants. Ilham tana fita ammi taja

Please Login or Register in order to submit comment