Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zahra tasaha jinin jikinta, murya a kausashe mashkhur yace! Kee naga kanki yana miki rawa to wlh ki shiga hankalin ki dama jikinki ya dad'e bai yi tsami ba! Daga dawowarki zakizo ki ishi mutane, to wlh ko da wasa on mistake naga yau kin qara futowa fallon nan sai jikinki ya gaya miki, murya na rawa zahra tace kayi haquri, zaro mata manyan idanunsa mashkhur yayi tare da cewa keee wlh watarana in inagana kina magana sai na zubar miki da haquran rashin kunyar taki zaki bar nan wajan KO sai nazo na taka wuyanki?.

Ai zahra batai wata-wata ba tai sauri ta kama hanyar bedroom d'in ta, tana qarasawa ta shige a hanzarce, tana shiga murya qasa-qasa tace! MUGU kawai komai nai laifi. Daga haka zama zahra tai ta fara cin abincin ta, bayan ta gamaci tasha ruwa sanan ta ajiye plate d'in a gefan bed tana so ta fita ta kai kicin tana tsoran mashkhur a ala dole zahra ta haqura. Hawa kan bed tayi ta zauna, ai zahra tana zama zancan da sukayi da yaya Ahmad akan ILHAM ya fad'o mata, wani tatausan murmushi zahra ta saki.

Tinani zahra tai da yau ilham zataji yaya Ahmad yana sonta tofa sai ta kwana tana zaginsa,  dan ita ilham ma in da akwai abinda ta a duniya to wani namijin yace yana son ta, in kace inason ilham tofa ranar basa bacci dare dan sai ta kwana tana mita tana qarewa wanda yace yana son ta tsiya, ita kuwa zahra duk wanda yace yana son ta tana dawowa gida take sa kuka ranar dai ko abinci bazata iya ciba haka dai ammi da hajiya kaka harma da yaya abdul zasu sha rarrashi.

A taqaice dai sam zahra da ilham basa so ace ana son su. Haka zahra ta zauna tana ta tinanin yadda suke rayuwa ita da ilham, tabbas zahra tasan tayi missing d'in ilham sosai, wata dariya zahra ta saki saka makwan tunawa tai da wata rana da suka sha dambe da ilham. Ranar sun tashi a makara zasu makaranta basuyi wanka ba! To ranar zahra ta riga ilham tashi daga bacci, zahra tana tashi ta cire kayanta ta d'aura toilet, tana shirin shiga towel ilham ta tashi ilham tana tashi itama ta cire kayan ta sanan tace wanka zata shiga itama.

Zahra tacewa ilham itama wanka zatai a toilet d'in ta tafi wani towel d'in a gidan tayi, nan fa ilham tai tsalle ta dire tace wlh zahra bata isaba itafa a toilet d'in bedroom d'in su zatai sai dai ita zahra ta tafi wani, a lokacin zahra tajin haushin ilham sosai, duk da zahra tana da haquri a lokacin ta kasan dan haka itama tacewa ilham bata isa ba, daga haka zahra ta banka qofar toilet ta fara qoqarin shinewa, da sauri ilham ta ruqota tace wlh zahra baki isa ni zan fara shiga, itama zahra tace wlh baki isaba in zan shiga, kuma bazanyi kaffara ba, sai dai ke kiyi azumun kaffara.

Ai itama ilham cewa tai wlh nima bazanyi ba sai dai kuwa mu shiga wankan nan tare, tsaki zahra tai ta shige toilet, ai zahra tana shiga ilham ta biyo bayanta ta banko qofar toilet d'in, ko kallan ilham zahra batai ba ta cire towel d'in ta tafara wanka. Itama ilham d'in towel d'inta ta cire, tana cirewa sabida nema tsokana ga soso guda biyu a cikin toilet d'in amma ilham tace dole sai zahra ta bata na hannunta, shiru zahra tai wa ilham ta cigaba da wanka ta.

Ilham kuwa da sauri tazo ta warce soson da zahra take wanka, zahra fa taji haushin hakan sosai, dan haka a zociye ta miqe ta kifawa ilham mari, ai zahra bata d'auke hanunta daga fuskar ilham ba itama ilham ta mayarwa da zahra mari, ai kafin kace kwabo dambe ya kaceme tsakanin zahra da ilham, ko kaya babu a jikinsu haka suke damban. Da yake zahra ba wani qarfin arziki ne da itaba sai da ilham ta zane zahra a cikin toilet d'in nan! Haka zahra ta zauna ta ringa rai-rai kuka a toilet d'in nan, itam ilham jikinta yayi sanyi sosai da ganin zahra duk haquri tana kuka.

Itama ilham d'in zama tayi suka ringa rafsa kuka abinsu, daga qarshe kuma ilham tazo ta rarrashi zahra, da yake zahra tana ba haquri a ala dole ta haqura, tunma kafin su futo daga toilet d'in suka shirya. Tun daga ranar in dai suka tashi a makare kuma ranar zasu makaranta tare suke shiga wanka, ko ranar da sukayi sauka wato ranar da aka d'aura auran mashkhur tare sukayi shiga wanka, suna kwanka suna hira abin nasu dai kwanin sha'awa kamar ta gawayan gaske.

Zahra ji tayi kamar tai kuka data tuno hakan, da tini yanzu maraici bazai ishetaba tana zaune tana hira da 'yan uwanta. Zahra tana cikin tinanin nan taji ana nocking d'in qofar gida, shiru zahra tai tana tinanin waye? Can kuma zahra da taji bugun yayi yawa sai tai tinanin mashkhur ne, dan haka ba 6ata lokaci ta kama hanyar fita daga d'akin nata. Lokacin da zahra ta futa falo bata kula da mashkhur yana nan ba da yake ya sauka daga kan sofa yana can carpet a zaune.

Da sauri zahra ta nufi hanyar bud'e qofar tana hawa tsakiyar cafpet d'in tai kici bus da mashkhur yana watasa mata wani mugun kallo. Nan da nan jikin zahra ya fara rawa ita tama manta da kashe din da mashkhur yayi mata kan in taji bugu karta bud'e!! Kuma yace mata karta sake yau ta qara futuwa fallon nan ai duk zahra ta manta da wanan sai yanzu, bakin zahra ne ya fara rawa, cikin rwar murya ta fara cewa dan!! Dan!! Da!! Allah!! Zaro mata ido mashkhur yayi tare da d'ora babban d'a yatsan ta a tsakiyar bakinsa yana cewa! Shiiii!!!.

Gumi ne ya tsinkewa zahra sabida tasan yau kashinta fa ya bushe ta shiga uku. Har time d'in ba'a dai na buga qofar ba, kuama wayar mashkhur bata dai na ringing ba, ba kowa bace take buguwa mashkhur face ZEE. da sauri mashkhur ya miqe tare da nufo inda zahra take, ai da sauri zahra tasa juya domin guduwa. Ai kuwa gam mashkhur ya ruqo gashinta da ta baya wanda parking d'in shi a qasa-qasa.

Okay kice wuyanki yayi kauri haka guduwama zaki ko ya qarasa maganar tare da qara ja mafa gashin da qarfi, wani siririn ihu zahra ta saki tare da cewa! Dan
ALLAH kayi haquri na dena, ai kanki ya kamata ki bawa haquri wai ke marajin magana ko? Basai da nace kar na sake ganin qafarki a fallon nan ba, kuma in akayi bugu karki bud'e! Ke ga marajin magana mara kunya uwar'yan shishigi, harda wani kwaso qafa zaki bud'e koh? To wlh yau sai kin sha azabar da tinda kikazo duniya baki ta6a shanta ba....................


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

                                Typing..............

                                 *page 64*

Okay kice wuyanki yayi kauri haka guduwama zaki ko ya qarasa maganar tare da qara ja mafa gashin da qarfi,  wani siririn ihu zahra ta saki tare da cewa!  Dan
ALLAH  kayi haquri na dena,  ai kanki ya kamata ki bawa haquri wai ke marajin magana ko? Basai da nace kar na sake ganin qafarki a fallon nan ba,  kuma in akayi bugu karki bud'e!  Ke ga marajin magana mara kunya uwar'yan shishigi, harda wani kwaso qafa zaki bud'e koh?  To wlh yau sai kin sha azabar da tinda kikazo duniya baki ta6a shanta ba....................

Murya na rawa zahra tace kayi haquri wlh na zata kai kake buga qofar shiyasa nazo bud'ema,  dalah rufemin baki ko nine nake buguwa tinda nace karki bud'e ai sai ki rabuda ni wlh yau sai kin gane baki da wayo banza kawai,  ya  qarasa fad'a yana ja mata gashinta da garfi,  azaba zahra taji hakane ya sata saki wata gigitacciyar qara mai sautin gaske.  Hannu mashkhur yasa ya toshe mata baki da mayafinta tare da saki jan gashin nata,  nan da nan hawayen azaba suka wankewa zahra fuska.

Da qarfi mashkhur yake jawa zahra gashinta har sai da kanta ya farayi mata ciwo gashi ya toshe mata bakinta da mayafinta. Nan da nan gumi ya jiqa zahra ga hawaye da yake ta sharara ta idonta,  sakin gashin nata yayi sanan  ya juyo  da ita suka fara faces d'in juna!  Har yanzu idanuwan zahra basu dai na zubar da hawayen ba,  wani  mugun kallo mashkhur ya watsa mata tare da cewa!!  yau sai kin gane baki da wayo sai kin fuskanci hukunci da zaki sha mamki tinda ke yanzu kin zama 'YAR ISKA mara jin magana ya qarasa maganar yana watsa mata wani mugun kallo.

A dai-dai lokacin,  wayar mashkhur ta cigaba da ringing wani dogwan saki mashkhur ya saki tare da sakin hanun zahra ya nufi inda ya ajiye wayar,  shi duk a tinanin mashkhur zee ce ta cigaba da kiran wayar,  kuma yayi niyar kashe wayar gaba d'aya ya huta da nacin zee.  A fusace mashkhur ya d'auki wayar zai katse kenan yaga sunan DADY 6aro-6aro ya bayyana akan screen d'in wayar,  da sauri mashkhur ya d'ago ya kalli zahra da take durqushe tana kuka.

Murya a kausashe mashkhur yace!  KE rufemin baki wlh ko kwakwaran tari kikayi sai kin gane baki da wayo ya qarasa maganar yana jifan ta,  da mugun kallo,  sanan ya d'auki wayar ya kara a kunan sa,  yana cewa hello dady!.  Zahra tanaji yaya mashkhur yace dady ta zuba mai ido kamar wata mayya ji take kamar taje ta finciki wayar ta gayawa dady  muguntar da yaya mashkhur yake mata, dan ita yanzu ta fara gazawa da zalincin yaya mashkhur.

Duk da zahra suna da d'an nisa da inda mashkhur yake hakan bai hana ta jin abinda dady!  Daga can 6angaran dady yace mai sunan baba ya kuke da fatan kuna lfy?    Shafa sumar kansa mashkhur yayi sanan yace!  Wlh dady muna lpy qalau da fatan kuma duk kuna lpy?.  Daga can 6angar dady yace muna nan lpy qalau kana gida ne?,  ehh dady ina gida,  ina mamana take?  Sai a lokacin mashkhur yayi dana sanin cewa yana gida!  Murya a kausashe mashkhur yace!  Dady ai bacci take ya qarasa maganar tare da gallawa zahra mugun kallo.

Zahra da take gefe kuwa ji tai kamar ta kwallara ihu sabida tsabar baqin ciki,  kifa kanta tai a guiwar ta hawaye masu zafi   da majina suna gangaro mata.  Zahra ji tai dady yace bacci kuma,  bacci mai take nasan dai yanzu a garin nan ranace tindda mu dare ne anan,  am!!  Ehh hakane dady ranace anan ai baccin rana take shiyasa,  daga can 6angarn haka dady yace yaushe mamana ta koyi bacci rana?  Ai ni iya sanin na bata yawan bacci rana indai ba bata da lafiya ba, ko wani dalilin.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa ehh hakane, amma nima bansan sabida mai take bacci ba kuma kaga ita kad'ai ce, inaga gajiya tai da zaman ka d'ai ci shiyasa yanzu ta fara baccin ranar.  Zahra kuwa jinjina kai tai hawaye na cigaba da gangaro mata tana tinanin yaushe yaya mashkhur ya fara qarya haka dama yaya mashkhur ya iya qarya?  Ita dai a iya saninta da shi bai cika yawan qarya ba.  Zahra kasa kunne tai dan jin mai dady zai ce, daga can 6angarn dady yace!   okay  jeka ka taso ta,  munaso muyi VIDEO CALL da ita,  ga shinan kowa da kowa sai jira yake.

Gaban mashkhur ne ya fad'i rass,  amma da yake mashkhur,  yana da wayo cewa yayi tom dady bari naje na taso ta,  tom muna jira in ka taso ta sai ka kirani video call,  ina jiran ka,  a online?  Tom shikenan dady bari naje na taso ta,  daga haka mashkhur ya katse wayar.  Zahra kuwa da take gefe kanta yana kife a cinyoyinta murmushi jin dad'i kawai take,  har wata ajiyar zuciyar farin ciki take saukewa.  Muryar mashkhur zahra taji a kausashe yace!  KEE!!  Da sauri zahra Ta d'ago ido cike da hawaye, ga majinar kuka ta hanci,  wata uwar harara mashkhur ya watsa mata tare da cewa zo nan?.

Ba musu zahra ta taso jiki na rawa,  tana qarasowa wajan mashkhur ta durqusa tace gani?  Wani banzan kallo mashkhur ya watsawa zahra tare da cewa jeki ki wanke face d'in ki a toilet,  ba musu zahra ta miqe ta wuce hanyar toilet d'in fallon.  Tana zuwa ba 6ata lokaci ta fara wanke fuskarta sabida itama a matse take taga 'yan uwan nata.  Ko cikakyan minti biyu zahra ba tai ba ta futo daga toilet d'in,  sanan ta dawo fallon lokacin da ta dawo a zaune taga mashkhur  akan sofa,  jiki a sanyaye zahra ta qarasa inda mashkhur yake ta tsuguna daga gefe tare da cewa na wanke.

Dagowa mashkhur yayi ya kallin face d'in tata,  kallo d'aya yiyiwa face d'in ya kawar da kai, tare da cewa ki goge face d'in da maya finki,  hannu na rawa zahra ta ja mayafinta ta tara goge fuskar tata,  ba wani sosai fuskar ta goguba da yake mayafin nata ba shi da laushi.  Murya na rawa zahra tace na goge, a hankula mashkhur ya d'ago ya kalli zahra,  wani siririn tsaki yaja ganin fuskar tata har yanzu da ruwa,  hannu ya zira a aljihu ya zaro wani farin hankicif mai laushi ya cilla mata tare da cewa! Ki  qara gogewa da wanan.

Hannu na rawa zahra ta d'auki hankicif d'in ta fara goge fuskar ta,  hankicif d'in sai qamshin wanan tiraran mashkhur d'in yake,  wanda zahra take mutuwar so, kuma kwana kin baya ta ta6a fasawa.  Nan da nan fuskar zahra ta karad'e da qamshin turaran,  tana gamawa ta miqamai farin hankicif d'in,  tare da cewa gashi na gama.  Wata muguwar harara mashkhur ya watso mata tare da jan wani dogwan tsaki.

Da sauri zahra ta janye hanunta tare da sunkuyar da kanta,  muryar mashkhur zahra taji ta ratsa kunanta yana cewa jeki ki d'auko table d'in can, duk da mashkhur bai nunawa zahra wana table ba, tasan wanda yake nufi,  dan haka ba 6ata lokaci ta kama hanyar in da table d'in yake,  tana qarasawa ba 6ata lokaci ta,  d'auko shi da yake ba shi da nauyi sosai kuma ba wani babba bane.  Tana qarasowa ta ajiye shi a gaban kujerar da mashkhur yake zaune.

Tana qarasa ajiye shi taji mashkhur yace zauna,  ba musu zahra ta zauna a qasa,  a dai-dai inda ta tashi,  kee anan nace ki zauna,  zaki dawo kan sofa ko sai na  sharara miki mari tinda ke yanzu bakya ganewa sai an had'a miki da duku,  ya qarasa  yana watsa mata harara.  Nan da nan jikin zahra ya fara rawa ta kasa ganewa kwata-kwata,  ita dai tasan sofa d'aya ce, a wajan kuma mashkhur yana kanta a zaune,  kuma tasan mashkhur bazai ta6a cewa ta zauna a kusa da shiba,  wani mugun kallo taga mashkhur yana watsa mata,  dan haka ba shiri zahra ta zauna akan kujerar da mashkhur yake zaune.

Rai a 6ace mashkhur yace matso,  jiki na rawa zahra ta fara matsawa inda mashkhur yake,  juyowa mashkhur yayi ya kalleta tare da cewa! Kibi a hankula, karki sake ki nunawa dady komai,  wlh kika sake kika nanawa dady inayi miki wani abin, wlh yau da karnikan gidan nan zaki kwana.  Da sauri zahra ta d'ago ta kalli mashkhur,  zaro mata manyan idanun nan nasa yayi tare da cewa yes, kika sake kika gayawa dady wani abin ko kikayi mai kuka, ko kikace kin gaji da zaman rasha wlh yau da karnikan gidan nan zaki kwana.

Jiki na rawa zahra ta fara girgiza kai tana cewa! Wlh bazan cemai komai ba,  harara mashkhur ya watsa mata tare da cewa kima fad'a kanki kika yiwa. 



Bawai dan mashkhur yana tsoran fad'a ko hukuncin dady ne yasa yace zahra karta fad'a ba,  aa kawai dai tsoran shi dady yace bazai sake taba, da ita zai cigaba da zama, shine abinda mashkhur yake tsoro.  Gyara zama mashkhur yayi tare da cewa zahra SMILE?  Da sauri zahra ta d'ago cikin mamaki tace   ME?  Harara mashkhur ya watsa mata tare da cewa ni da waye a wajan.

Ya fad'a tare da kafeta da manyan idanuwan nan nasa,  wanda suke razana ta,  sunkuyar da kai zahra tayi ta saki wani siririn murmushi wanda in baka qura mata ido ba,  bama zaka san tanayi ba.   Muryar mashkhur zahra taji yana cewa kee!  Haka ake murmushi,  banasan rai nin hankalin,  naga alama su kike jikinki yayi ciwo,  da sauri ta saki wani qayatacan murmushi mai tafiya da hankalin d'an Adam.  Zuba mata ido mashkhur yayi,  na wasu daqiqu,  sanan yace yawwa haka zakiyi in muna video call da su dady,  karki sake ki 6ata rai?.

Da sauri zahra tace tom,  daga haka mashkhur ya juya daga fuskantar zahra da yake,  sanan ya d'ora laptop d'in kan table d'in da zahra ta d'akko,  sanan ya fara danawa.  Yana shiga app d'in WhatsApp,  tin kafin ya fara video call d'in ya juyo ya kalli zahra tare da cewa matso,  ba musu zahra ta matso kusa da shi tare da zubawa laptop d'in ido,  wani dugun tsaki mashkhur yaja,  sanan ya cigaba da danna laptop d'in.  Yana hawa yaga dady a online ba 6ata lokaci ta ya shiga ya contact message d'in ya fara qoqarin kiran video call d'in.

Tana shiga mashkhur yayi sauri ya kalli zahra tare da cewa ki kula da kyau fa,  kuma ki saki fuskarki kamar yarda na numa miki,   Da sauri zahra tace to tare da sakin murmushi,  a dai- dai lokacin su dady suka d'aga video call d'in su mashkhur.  Zahra dai taga yaran gidan a bakin laptop amma bata gama tantance waye-waye ba taji sun saki wani uban iwu.  Nan da nan zahra ta farin ciki ya kamata sosai itama ji take kamar ta saki nata iwun,  amma tana tsoran,  yaya mashkhur.

Sosai zahra take murmushi farin ciki tare da bin kowanne daga cikin si da kallo. Duka yaran gidan ne a wajan  Haidar,  faruq,  ilham,  rukee, ruma sai amir Auta. Sai faman musu suke wanan yana cewa shi zai fara magana da zahra wanan yana cewa shi zai fara.  Muryar faruq zahra ta tsinkaya,  yana cewa!  Lalai ma zahra in banda kin rai na mana hankali muna ta faman yi miki iwu,  muna nuna miki frin ciki,  amma kin share mu,  yana saukewa haidar ya d'ora da cewa!  Eh mana lalai zahra kice kin qaro muskilanci.

Wata siririr dariya zahra tai tare da cewa!  Haba yaya faruq,  wlh ba haka bane, taya zan yi muku magana kujini bayan kun cikani da iwu.  Ehh lalai ma yarinyar nan wato da iwu muka cikaki koh?  Cewar ilham,  murmushi zahra tayi tare da cewa ahh ilham mai yayi zafi haka,  ni dawasa nake.  Murmushi ilham tai tare da cewa!  Hmm to mene lbr ki bani lbr nasan kin fara zuwa makaranta koh?  Kinga school d'in tasu ba irin tamu ba,  kee ya kikaga student d'in?  Ta garasa maganar tana saki dare.

Itama zahra dariya tai tare da cewa ke dai bari ilham ai abin ba'a cewa komai, murmushi ilham tai tare da cewa kamarya ba'a cewa komai, gaskiya dai ki bani lbr nasha.  Murmushi zahra tai tare da cewa hmm ke dallah akwai lbr fah!  Wani siririn ihu ilham ta saki tare da cewa ah mene gaya nasha,  girgiza kai zahra tai tare da cewa, aaa ai abin sirri ne daga ni sai ke,  da sauri faruq ya hankad'e ilham tare da cewa kedallah matsa ke kad'ai zaki yi magana da ita,  kafin faruq ya rufe baki haidar ya ce!  Ehh mana sai wani turo kai take kamar zata shige laptop d'in.

Muryar amir ce ta katse su daga fad'an da suke!  Amir cewa yayi aunty ya fad'a yana shafa laptop d'in.  Kamar zahra za tai kuka tace na'am amir d'in na?   Shine kika gudu kika barni da ilham kullum sau ta dake ni,  kai kowa na wajan sai da ya kwashe da dariya har da su ammi da suke bayan laptop d'in,  sabida sun san amir qarya yake wai shi wayo zai wa zahra Dan ta dawo ta tafi da shi.  Dariya zahra tai tare da cewa!  Kai gaskiya ilham baki kyauta ba.

To aunty zahra yaushe zaki zo mu tafi tare?  Ajiyar zuciya zahra tai tare da cewa! Karka damu my amir ina nan tafe ta qarasa maganar fuska ba walwala.  Ruma da take gefe tace zahra kin manta da ni koh?  Da sauri zahra ta saki fuska tare da cewa! Ah ni na isa wlh ban manta dake ba.  Haka dai zahra suka zauna sukai ta hira da 'yan uwanta sai da suka rabin awa, suna hira abin mamaki kuma ya bawa mashkhur haushi shine kwata-kwata, koh kallansa basu yiba, dan daya gaji ma matsawa yayi.

Suna cikin hira zahra tace!  Wai ina ammi da dady,  ne sanan ina yaya abdul da hjy kaka.  Da sauri ilham tace gasu nan a gefe suna jinki, wai sai mun gama gaisawa,  zaku gaisa,  ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa yaya abdul ta fad'a cikin sauti mai qarfi,  muryar abdul zahra taji yana cewa!  Na'am baby abdul.  Au dama yaya abdul kana jina,  amma bakazo na ganka ba,  zahra tana kai haka mashkhur da yake gefe ya watso mata wata muguwar harara,  abdul kuwa qarasowa yayi baki laptop d'in tare da cewa su ilham,  to ai sai ku tashi muma ku bamu guri koh?.............


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

my number 09162226240

*page 65*

Typing..........

Au dama yaya abdul kana jina, amma bakazo na ganka ba, zahra tana kai haka mashkhur da yake gefe ya watsa mata wata muguwar harara abdul kuwa qarasowa yayi bakin laptop d'in tare da cewa! su ilham to ai sai ku tashi muma ku bamu guri koh?..........

ba musu su faruq suka watse suka bawa yaya abdul waje amma banda ilham da amir da suka qara zama ma alamun basu da niyar tashi. yaya abdul zama yayi a kusa da ilham tare da sakarwa zahra wani murmushi mai kashe zuciya, itama zahra mai dar mai tai da martani ji take kamar ta saki wana uban ihu amma tasan muguntar mashkhur shiyasa ma batayi gigin hakan ba. sosai zahra ta saki jiki sukai hira da yaya abdul. can kuma abdul ya kalli mashkhur da yake gefe wanda ya shagala da danna wayar shi.

gyara murya abdul yayi tare da cewa yaya na ykk dafatan dai kana cikin qoshin lpy? sai da mashkhur yaja aji sanan ya d'ago ya mutsa fuska ya kalli abdul d'in tare da cewa ai nasha kai ma zaka shareni ne kamar yarda su haidar da su ilham su kai yimin. d'an zaro ido abdul yayi tare da cewa ah haba ni na isa yayana guda na share shi? ai kafin abdul ya qarasa magar su ilham da haidar harma da su ruma suka dawo da sauri.

nan da nan suka rufe laptop d'in kowa yana qoqarin cewa yaya mashkhur ina wani, harara mashkhur ya watsa musu zuciya cike da kishin yarda suka ringa kula zahra basu kula shiba! kowa ya riqe gaisuwar sa bana buqata, ya qarasa maganar tare da had'e rai. nan da nan suka fara bawa mashkhur haquri da wanan ya rufe baki wanan sai ya bud'e.

Please Login or Register in order to submit comment